kidauko kayanki
Maryam ta gwalo ido waje Wanda hakan bakaramin kyau suka kara mataba cike da shagwaba
Tace yaya bazan iyaba da nauyifa sosai
Tsaki ja yayi hanyar waje ya nufa suhaila da Aymana mamaki yakashesu a tsaye
Suhaila tace Aymana menake gani badai kayan nata dagash yaje daukowa bako
Aymana tace gashi kuwa kina gani bata gama mishi karuwanci da ido ba
Maryam najinsu tace subhanallah Allah yamana tsari da wannan Kalmar
Zasuyi magana Dagash nashigowa da akwatuna biyu yashiga dakin dake cikin falon dakayan ya ajiye
Ya kalli maryam yace ga dakinki maza wuce ki kwanta bana son hayaniya
Maryam tawuce abinta tabarsu da bake sake kallon idonsuba
Aymana tace ai wallahi za ayi tashin hankali a gidan nan caf
Suhaila tace gaskiya kam dasake kiga yarinya hartasamu darajar doctor da kanshi yadauko mata kaya
Aymana tace wallahi ko asiyace bazai dauko wa Abu haka direct ba sai dai yasa masu aiki
Suhaila tace kisani koba banzaba tunda su mummy ma suna kuka da uwarta
Nan dai sukayi ta Neman mafita
Washagari maryam ta tashi sallar asuba tayi sallarta tayi karatun alkur'ani megirma wayar yafara kara taga bakuwar lamba ce tadauka aiku wa taji muryar antyce
Cikin murba tace antyna
Nayi ta Neman layinki bansamu anty beshigaba
Anty tace ai bazai shiga ba amma yanzu gasabon layina ki saving
Nan sukasha hirarsu ta ya da uwa
Tana kashewa shafa'atu takirata nan sukayi hira
Maryam bata koma bacci ba saida tagyara dakinta tas ko ina yadau kamshi hadadan turaran wuta
Kafin tafito zuwa kitchen ta shirya lafiyayyar break fast dan kadan
Dankali soya sai soyayyar kwai da soyayyar bread dayaji kwai gurin suyar
Saita dafa hadaddan shayinta tadauko flask mecin cups biyu tazuba tadauko tacika Irish potatoe chips tashinfida soyayyar kwai akai Wanda yasha albasa da attaruhu
Tadauki kofuna biyu tasa kan tiren da spoon
Haba nan da nan gida yakaure da kamshin abinci Dana turaren wuta
Lokacin karfe Tara da rabi su aymana an fita gurin business dinsu dan wataran ma acan suke break
Maryam taje part din Dagash falon kasa tayi sallama taji shiru sai ta je tsakiyar falon taja center table ta ajiye mai akai
Tafita abinta kitchen ta koma ta hada nata tafito takai dakinta ta ajiye tashiga wanka
Dagash kuwa yana tashi yayi wanka yashirya cikin kananun kaya kamar yadda yasaba
Kitchen din cikin part din shi yashiga yadebo danbun nama da da snacks
Ya dauki hollandia milk yasauko falon kasa yazauna idonshi kai kan center table
Tashi yayi yabude da mamaki yaga abindake ciki girgiza kai yayi yasan wannan yarinyar ce
Shi beci abinci masu hankali ba saina wannan chick little girl din zaici
Fitowa yayi yaganta zaune a falo ta na break tayi kyau sosai sanye take cikin Riga da zani na atamfa zanin 6 piece ne ya mugun zama akugunta sosai
Gashi tayi daurinta nagaban goshi tadaure gashinta da farin ribom kasancewar atamfar pink ce da fari Zane ajiki
Hankalinta kwance take break fast dinta saijin maganar ya al'amin tayi acikin kunnenta
Ke ni sa'an wasankine zakiyi jagwalgwalonki kikai min falo
Maryam kuwa bata jiyoba sai biyo shida gaisuwa ma datayi
Tace yaya antashi lafiya
Yace aranshi lalle yarinyar nan ta tarainani wato magana natake ignoring
Zanyi maganinki ne yace kafin nabude ido na rufe kizo kikwashe jagwalgwalon abincinki a falona
Maryam najinshi tayi banza dashi abinta yakoma falon yakai dabun naman bakinsa
Sai kawai suffar Maryam yake aiyanawa a ranshi yadda tayi kwaliyarta tamishi sosai yarinyar saikace aljana gata karamar yarinyar amma dakayan manya yayi tsaki shikadai
Wai me yasame shine yake yawan tunanin wannan yar mitsitsiyar yarinyar
Tashi yayi kawai dai yace bari dai yadansha tea kadan ya hada tea din can kuma kamshin dankali da kwai yadaki hancinsa
Nan yabude yakai kadan baki
aikuwa shidai bude ido yayi yaga yacinye tas yasake hada tea din yasha sosai yaji dadin abinci
Yace ashedai yarinyar ta iya abinci ga tsabta dan tsabtarta yasa ya dan Dana abincinta aikuwa ba abinda yabari
Danbun naman barinshi yayi ya haura sama yadauko Abu
Maryam tayi sallama tashigo direct gurin abincin ta wuce tabude taga wayam ta jijjiga flasks din tea shima babu abin yabata mamaki toko zuburwa yayi
Saukowarsa suka hada ido da Maryam
Tace yaya banga abinci dakace nafitar ba
Harara yadankara mata yayi waje abinshi tazauna kan kujerar tafara dariya kaman allah ya aiko ta har dan kwalinta yafadi bata damu ta mayarba saboda tasan bakowa
Dan ta tabbatar shiya sha saboda ga cups din nan sun bata amsa
Cikin dariyar tace kai amma yaya akwai pretending
Abinda maryam batasaniba tunda tafara mishi dariya yafasa fitar yadawo yaji dalilin dariyarta
Dagowar dazatayi suka hada ido da PRINCE AL'AMIN DAGASH
Next page
Your comments is needed fans
Love u love your comments fans
*Signed by ummu afan* π»
[26/06, 11:56 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS SURRY BABY GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
Comment harda read more π€much love to your love and care
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 1β£7β£To2β£0β£
Cikin tsoro maryam ta hadiye dariyarta
Dagash yace dawakike wannan dariyar
Maryam cikin rashin gaskiya tace ba dariya nayi ba yaya kwarewa nayi nake tari
Yace OK yanzu zakiga kwarewa idan na fasa miki jiki da belt
Maryam ta gwalo ido tace nashiga uku dan allah yaya kayi hakuri bazan sakeba
Taga dai tabbas dagaske yakeyi aikuwa ta tashi takoma bayan kujera
Tana rokonshi yayi hakuri
Shikuwa ina dariyar ta yabata mishi rai sosai dan ta rainashi zata zauna tana mishi dariya yanufoto aikuwa suka shiga zagage dakin nan
Baisamu nasarar kamo maryam ba yatsaya yace kina karawa kanki lefine fa kina wahalar dani
Da wayo tazo gurin kofa aikuwa tabude tayi waje da gudu dakinta ta fada ta banko kofar
Sallamar da akayine ya hanashi zuwa kofar dakin
Zayyad ne da Faisal suka shigo
Zayyad yace kaikuma mezakayi da wannan belt din haka a hanu
Dagash yace wannan Mara kunyar yarinyar mana
Faisal yayi dariya yace kai Prince shine karike belt saikace zaka daki babban mutum
Wannan yarinyar ka zuba mata wannan belts din ai saita suma maka
Dagash yace ai maganin takenan amata dukan dazataji ajikinta
Zayyad yace kokuma maganinka ba
Dagash yace mekace zayyad yace bance komaiba
Dagash ya kalli Faisal yace kaikuma dan rainin wayo bazaka dena kirana. Da sunan gargajiyar nan ba ko
Faisal yace tuba nake ranka yadade
Suka yi dariya gaba dayansu
Dagash yace ya zanyi daku yadaafa kanshi
Shigowar rahma yasa dagash ya kalli Faisal yace daman Baku kadai bane
Wannan yar karamar yarinyar kuma daga ina kuka samota
Zayyad yace kai kanwatace fa rahma yar gidan amaryar dad ce fa
Tace zatazo gurin kawarta maryam shine nace tashirya nakawota
Rahma ta durkusa tagaida da al'amin amma baiko daga ido ya kaleta ba saboda sarauta
Zayyad yace tashi kinji rahama nemi inda maryam din take wannan yayan naku haka yake sai hakuri
Dagash ya watsa mishi harara
Rahma kuwa cikin ikon allah dakin maryam tanufa direct dan tafara dubawa konan ne
Tana bugawa taji a kulle maryam tace waye dan tayi tunanin yaya al'amin ne
Aikuwa rahma tace itace maryam ta kwalla wani ihu tabude suka rungume juna
Duk yan falon idonsu yadawo kan gashin maryam
Maryam tace kai amma naji dadin zuwanki yar uwa juyawar dazatayi taga su yaya zayyad aikuwa tasake rahma tayi dakin ta dauko hijabinta taje tagaishesu
Zayyad yace maryam yagidan ya hakuri da yayanki
Maryam tayi murmushi zatayi magana taji an damki kunnenta tace Dan Allah yaya kayi hakuri bazansake ba
Yace ina wasa dake ne ta girgiza kai yace ok bakida baki ko
Zanyi maganin ki tayi saurin cewa a a yaya Dan Allah natuba wallahi
Yace nonsense tashi kibar nan
Dasauri ta tashi tayi dakinta
Faisal da zayyad sukayi murmushi
Faisal for the first time a rayuwar dagash ya playing very nice game da baby
Zayyad yace Dan rainin hankali ba yasamu dai dai dashi
Dagash yace kuna wannan maganar fa zakuja wa yarinya duka Dan zankirata na faffasa mata jiki
Zayyad yace Allah huci ran yarima
Amata afuwa
Dagash yayi tsaki yace kutashi mushiga konan ya muku
Faisal yace a a muje dai abamu abin tabawa Dan na San mum zatayi tafiya bata barinka ba snacks da danbun nama
Dagash yayi murmushi kadan dansun tuno mishi da draman su da yarinyar nan
Maryam" tace rahma amma kwana zakiyi ko rahma tace wa ni baruwana wallahi kafin anty suhaila tadawo ta zazzageni kinsan munzo sodaya wai inga yar uwata daddy yasa driver yakawoni
Tazazzageni harda ce agola yan cin arziki rahma ta fashe da kuka
Maryam kaicin kukan yakamata tace to saimeye idan sunce miki agola kinsan Allah abinda ake miki Wanda ba amin
Kawai abinda zakiyi idan anmiki kinuna su da banza duk daya suke kebaki basu amsa ba kebaki nuna musu kinji haushiba
Rahma ta goge hawayenta tace kinsan agidan yaya zayyad yafi kirki wallahi har yakan daukeni yazaga dani inga gari
Bayanshikam duo sauran mutan gidan basu da kirki
Maryam tace karkidamu kiyi hakuri kinga nimkuma suk gidan anty shafa'atuce mekirkin gidan sosai
Dan tana mugun kaunata kuma nima haka kinga wannan yayan Dan rainin wayone waishi bayason raini
Koda kannenshi ma bantaba ganin yayi wasaba fa sai uban jinkai
Maryam tace muna ta surutu ban baki komai rahma tayi murmushi
Maryam ta tashi tabude Dan karamin fridge din dakin nata taga bakomai aciki ta fita fridge din falo nan ma babu direct kawai tayi falon yayan nata cikin sallama
Bata ko kallesu ba tayi hanyar fridge din falon direct
Zayyad da Faisal da dagash suka kalle juna at the same time
Cikin daure fuska dagash yace ke mezakiyi anan bata ko saurareshiba tabude abinda tagani ya mugun razanata
Bakomai bane face giya kala kala Dan duk ta karanta sunansu daga gefe kuma drinks ne kamansu maltina, exotic fanta ,etc
Ta juya takallesu taga ita suke kallo taga gabansu duk kwalaben giyan ne
Tajuyo abinta tasa hanu tadauki kwalban giya biyu zata fita dagash yayi saurin shan gabanta yace inazaki da wannan
Tamishi wani irin kallo dashi kanshi baisan yazai fassara kallonba
Tace zamuje musha ne nida rahma yace kuma wadan nan kadai kigani acikin fridge din
Maryam tace a a ganinayi shikuma kukesha wataki la yafi dadine
Yamika hanu yace banisu nan maryam tamatsa tace a a haba yaya kabarmu mana musha muma
Cikin tsawa yace bakida hankali ne zakisha whisky
Takalli su zayyad ta kalli kwalban dake gabansu
Tace kenan yaya sai marasa hankaline suke shan wannan
Babu kyau kenan me hankali yasha
To shikenan zan mayar tunda na marasa hankaline
Cikin bacin rai tawuce fridge din ta ajiye tadauko musu holandia milk mesanyi abinsu
Bata sake kallon inda suke ba dagash kuwa kusan mutuwan tsaye yayi
Da kyar yaja kafarsa yakoma
Zayyad yace shikenan mutuncinmu yazube a idon yaran nan
Faisal yace rana ta farko Dana fara danasanin shangiya a rayuwata
Zayyad yace kaiko ni na tabbatar sai tafadawa rahma
Rahma tana kallona da mutunci sosai
O my God ! Yadafe kai cike da takaicin halinsu
Dagash kam tsaban miskilanci bai fadi komaiba dayake cikiba karshema tashi yayai ya haura sama abinshi
Maryam tashiga dakinta jiki a sanyaye tazauna rahma tace lafiya kuwa maryam kinfita bada wannan yanayinba kindawo da wannan yanayin
Maryam ta kalli rahma tace rahma Ashe suyaya mashayane
Rahma tadafe kirji tace mekikagani
Maryam tabata labarin komai
Sannan maryam tace kince yaya zayyad yana daukanki kufita ko tadaga kidaina yadda saboda babu abinda mashayi bazai iya aikatawa ba saboda wani lokacin ba a hayyacinsu sukeba
Kiringa taka tsantsan da rayuwarki
Rahma cikin tsoro tace insha Allah nadaina kogyaran dakin shin dayake sani nadaina
Maryam tace a a karkiyi haka sai kitabbatar yanan kafin kishiga dakinshi ki gyara mishi
Rahma itadai duk ta tsorata da jin wannann magana
Can sukaji zayyad yanakiran rahma sufito sutafi
Har gurin Mota maryam taraka rahma sukayi sallama dagash yana daga can farandar shi nasama yana kallon maryam
Takomo ciki abinta direct bathroom ta wuce tayi tasake wanka tayi alwala tayi sallar azahar taroka wa yayan nata Allah yashiryesu
Tasaka duguwar riga kasancewar bacci zatayi yasata tasaka duguwar rigar baccinta
Ta kashe wutar dakin Dan tana baccin rana dama tasaba
Saida ta tabbatar ta kulle dakinta
Sannan bacci mai nauyi yadauketa
Dagash kuwa yama rasa meyake damunshi
Suhaila ce tashigo gidan yana ganin motarta ya yi tsaki yadauki waya yakira mummy sukayita hira abinsu
Nan yadauki wayarshi da key din motarshi yafita abinshi daga gidan gaba daya
Suhaila tace sannu doctor yace yauwa kawai tace inazakaje kuma daga dawowata gidan
Yakalleta yace ok idan zanfita saina sanardake ko
Ya wuce abinshi suhaila tace nikam wannan wani irin miji Allah yabamu haka
Ace tsakaninka da miji ba gana medadi
Amma shine jiya harda dauko wa wannan kodaddiyar yarinyar kaya
Tayi tsaki tayi ciki Dan ta huta
Maryam tashi tayi sallar la'asar tashige kitchen abinta ta dudduba taga ba nama ba kaji tasan kuma saboda ba anfani da kitchen dinne yasa ba akula anzuba komai ba
Fitowa tayi taje ta aiki driver yasiyo mata kaza fresh guda daya da kayan cikin rago
Nan da nan kuwa yakawo mata tashiga sarra fawa
Macaroni tadafa Wanda yasha kayan lambu da kayan ciki kafin ta gyara kazarta tayi shawarma dakanta abinta Dan tana shawa'ar shi sosai
Ta gama ta hada kunun ayarta Wanda madarar ruwa ta kai fridge din dakinta
Komai ta kwashe takai dakinta tasamu kula mekyau sosai Dan karami tazubawa dagash abincin a ciki shawarmar kuma tasamu dish bowl me murfi tasaka aciki ta ajiye a oven ta barshi warm saboda bata bukatar yayi sanyi
Tashiga tagyara dakinta ko ina yadaukamshin girki da abinci kishi ya turnuke su Aymana dake zaune a falon
Suhaila tace ke zonan maryam ce zata wuce maryam kota juyo ta kara gaba abinta kaman batasan da ita akeba
Aymana sarkin zuciya ta tashi tajuyo da maryam kawai ta bata mari
Maryam kuwa batayi tsammaniba taji mari a fuskarta kau
akuwa ta dafa gurin Aymana tace Dan ubanki kina da right da zamu kiraki agidan nan kidaga mana kai
Ko kannen megidan ma basu da wannan damar bareke agola
Maryam tayi murmushi takaici tace tabbas kinshammaceni kin mareni
amma ina maki gargadi da babban murya karkisake kasadar daukar hanu kimareni
Suhaila ta task jin amsar da maryam takeba Aymana
Suhaila tace mezakiyi idan ansake marinki zaki ramane
Maryam tayi murmushi tace kodaya bazan ramaba amma shiwanda nake zamanshi agidan dakanshi zai ramamin kunga kuwa ai kunji kunya tunda akan agola mikinku zai Baku mamaki
Kuma kugwada kugani tayi tsaki tawuce tabarsu da mamaki
Aymana tace suahaila anya kuwa
Ba abinda yashiga tsakanin wannan yarinyar da yaya al'amin kuwa
Suhaila tace da alamar tambaya kam Dan idan bahakaba yaushe zata samu damar fadin magana haka da kwarin gwiwa
Aymana tace idan hakane kuwa munshiga uku gaskiya yakamata mu aje zuwa kasuwar nan haka muga meke tafiya acikin gidan nan idan ba ma nan
Suhaila tace da dai yafikam nan suka zauna suna ta tufka da warwara
Bayan sallar isha maryam ta idar da sallarta tayi adduointa datasaba sanye take cikin Riga da skirt din material ja ya mata kyau sosai
Ta saka jambaki maroon colour shikenan sai giranta data gyara sai tsadaddiyar powdar din
Zata fara cin abinci kenan taji tsayuwar mota ta leka window taga dagash ne
Ta koma tadauki abincinshi saida tajira yashigo tukun ta bude kofarta
Kallo suka bita dashi kosu dasuke mata kwalliyar maryam yaburgesu bare dagash
Shawarmar tadauko tasa kan tire din tayi part din dagash
Aymana zata bita suhaila tayi saurin kamota tace mezakiyi
Aymana tace zanyi maganinta mezai kaita falon mijinmu inba iskanciba
Suhaila tayi murmushi tace kwantar da hankalinki yanzu zai mana maganin me ruwankai ai
ai takwashi abinci takai mishi a tarihin rayuwar doctor baitaba cin abinci ako inaba idan mummynshine tadafa ba
Sainata zaici Dan itace wa kwantar da hankalinki
Aymana tace kuma ma fa hakane to bari muzuba ido yadda zasu kwashe
Maryam tana shiga ta ajiye mishi a tsakiyar falon tafito zata tafita tana fita dagash na saukowa kasa
Idonshi yakai kan abincin data ajiye mishi
Karasawa yayi bude nan da nan kuwa abincin ya attracting dinshi yazauna
Yafara ci sosai yaci Dan bairageba yabude shawarmar nan ma yaci yasha kunun aya
Yana kai baitashiba su suhaila suka shigo gulma abinda idonsu yagani yabasu mamaki kuma yadaga musu hankali ganin dagash zaune a kasa yanacin abincin
Next page
Your comment is needed fan's
More comments more typing
Voted & share
*Signed by ummu afan* π»
[15/07, 1:05 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS SHAFA'ATU GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
Gaisuwarki dabance my twins sis Allah yabar zumunci sosai ina alfahari dake over wallahi
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_
Jinjina agareku kawayen amana
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
Sis Ummy
Ummu farhan
Fatima sunusi sanata
Mummyn jidder
Fatima zahra
Nana
Suryy baby
Mom imam and hanifa
Mom isqah e t c
Adda khady
Da dai sauransu Wanda insha Allah zakuji sunan su saboda very hot comment da sukeyi π
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 2β£1β£to2β£5β£
Cike da mamaki aymana da suhaila suke kallon ikon Allah
Aymana tace menake gani yaya dagash yadago kai yamusu wani matsiyacin kallo
Ya tashi ya haura sama abinshi
Suhaila tace munshiga uku aymana yanzu meye abinyi
Aymana tace abinyi shine muci ubanta tafada mana meke tsakaninsu kawai suhaila da aymana suka nufi dakin maryam itakuwa maryam ta baje ne tana karatunta
Saboda jibi Monday zasu fara waec
Sosai take jin dadin karatun yana shigarta yadda yakamata
Kamardaga sama taji muryarsu aymana suna cewa sainaci ubanta sai fada min meketsakaninta da mijinmu aikuwa maryam ta tashi tayi bayan kofa
Suka banko da karfi suka shigo aikuwa shigewa maryam ta falla da gudu tayi
Falon dagash bataganshi anan ba ta haura saman da gudu
Yayi shirin shiga wanka kenan dagashi sai gajeran wando ya daura towel a kan kafada yaji anbanko kofar dakin
Maryam yagani kai va dankwali dama baigantaba gaskiya wannan yarinyar Allah yayi halillta anan tana zuwa tayi bayan dagash
Kafin yakai ga tambayarta abinda yakorata su aymana sun banko kofar sunshigo
Suhaila tana kokarin fisgo maryam daga bayan dagash aikuwa maryam bata San lokacin data rungume dagash din ta baya ba
Itada take cikin tashin hankali ba abinda taji amma shikuwa gogan naku wani shocking yaji Wanda baitaba jinsaba
Saikace Wanda mace bata taba tabashiba haka yaji
Maryam tace Dan Allah yaya kabasu hakuri wallahi bansan menamusuba
Bazansakeba aymana tafara surfo ruwan ashar tana saukewa akan maryam sosai maryam ta tsorata dasu saboda yanayin kerar jikin Aymana na yan dambe ne
Itakuma suhaila daga zatayi zafi hanu gurin duka gashi maryam anty bata taba dukanta ba
Ita wallahi zata iya lissafa dukan da akama ko school ne bare tabari wadan nan su saka hanu ajikinta
Dagash yayi karfin halin janyo maryam daga bayansa ba dukanta zakuyiba gata kudake ta
Tunda bakuda kunya ta gudo harnan kubiyota zakudaketa saboda kun rainani ko
Yace gata kufara dukanta mana Aymana cikin zafin nama ta zabga wa maryam mari
Saboda tsananin zafin marin maryam ta kwalla kara ta zube kan gadon dagash
Cikin tsananin bacin rai dagash yace what Aymana raini tsakaninmu bazaiyuba
Ya danko ta yakasheta da mari yadauki yaci ubanta da kyau tuntana bashi hakuri harta kasa
Suhaila uwar wayo tana ganin aymana ta mari maryam ta gudu
Aymana dakyar tasamu ta kwaci kanta ta gudu daga part din shi
Yajiyo yaga maryam haryanzu ajiyar zuciya takeyi
Yace saura ke wato bakida kunya ko yakamo kunnenta yace matan nawa kikewa raini
Mekika musu harsuka hadu zasu dakeki
Cikin kuka maryam tace nima bansaniba nikawai ka maidani gidansu rahma
Bazan iya zama anan ba wallahi tsoronsu nakeji suna bani tsoro
Dagash yaso yayi dariya saboda yadda take baganan harcikin zuciyarta ce gaskiyarta take fada
Yace tsoro horo ne su dazakiji tsoaronsu inkina tsoron duka kidaina abin dazaisa sudakesu
Maryam tadaga kai ta kalleshi tace haka kace yadaga mata gira yes tace shikenan nadaina insha Allah bazan sakeba
Ta tashi tayi waje fuuuuuu abinta dagash yanemi guri yazauna yarasa dalilin dayasa baya iya tsawatar ya yarinyar nan
Ya rasa dalilin dayasa yake iya dogon surutu akan lamarinta
Wani zuciyar yace kawai Dan tana da tsabtane shiyasa
Ya yarda da zuciyarshi baitaba jin jiki mailaushi irin maryam ba hanunta datasa ta rungumeshi jiyayi yafi audiga laushi ya tsinci kanshi da lumshe ido yana murmushi dakyar yaja kafarsa zuwa bathroom saboda tashi daya kasala ya dirar mai
Maryam kuwa tana fitowa falon taga suhaila da aymana suna fada
Aymana tana ta zagin suhaila wai zasuyi Abu tare saita zame tabarta
Bazasu hada kai su yaki Abu tare ba saboda haka kowa tashi ya feshsheshi
Suhaila kuma tace kinfiye saurin hanu haka kawai naga yana jibgarki sainasa baki
Sosai fada da ca car baki
Maryam kuwa ko kallon India suke batayiba tashige abinta
Washagari maryam ta tashi ta hada lafiyayyan break fast dinta ita kadai dai cikinta tayi wanka ta shiyar cikin Riga da wando amma na India wato Indian dress
Sai da tagama gyaran dakinta tas sannan tadauki break fast din tayi main falo dashi akuwa
Matan gidan suna nan bata ko kalli inda suke ba ta ajiye a tsakiyar falon ta zauna akasa ta nade kafafunta
Zata fara break kenan sai sukaji a nocking a kofa
Maryam ganin itace karama yasa ta tashi taje tabude kofar aikuwa ganin mata tayi cikin wasu arnan shiga
Maryam tace to kikekuma fa cikin gadara Vicky tace matsa min nawuce
Maryam tayi murmushi tace ba inda zaki wuce wallahi dubekifa gurinwa ma kika zo tukun
Ta kalli su aymana tace anty kokunsanta aymana tayi tsaki suhaila kuma ta maka mata harara
Maryam tayi murmushi tace kinga wannan ya tabbatar basusankiba may be wrong address akabaki
Vicky tayi murmushi tace idan kebakisanni ba aisu sunsanni sunsan karonmu dasu
Dagash ne yafito jin hayaniya ganin Vicky da maryam yasa yatsaya ya rike hanu a kirji yana kallon ikon Allah
Vicky tace hello sir dagash ya watsa mata harara yace you again ?
Ya yakaraso cikin tafiyarsa na kasaita yanuna wa Vicky hanyar waje if i ever see in my house again kinsan sauran nonsense oya get out before a get u there
Jiki a sanyaye Vicky tasha kunya tafita
Suhaila da aymana kuwa sunjike da ruwan jikinsu ganisukeyi kaman maryam zata kwashi kashinta a hanu sai ganisukayi ya rufe Vicky da fada
Dagash yajiyo kan maryam ya watsa mata harara yace wato kekuma bazakiji maganaba kowa kika dama saikin mishi rashin kunya
Ya rike kun nanta yayi part dinshi da ita haba suhaila murna yakamata Ashe ba barinta zaiba
Dagash kuwa yanashiga falonshi nakasa yace maza yi neel down
Maryam ta zube a kasa tace to yaya mena maka kuma dan Allah yace au baki ma San abinda kikayi
Tadaga kai yace meyasa bakiyi abincinba maganar yazo mata a bazata tace abinci kuma caf
Nayi dakai matan ka sunmin duka beside ma ai kai kace karnasake yimushu laifi a iya sanina kuma lefin danayi kenan
Dagash bakin kawai yake kallo tana maganar
Baice komaiba yace ina naki abincin tace yana falo
Baicemata komaiba ya tashi yafito falon su aymana yan labe suna jikin kofar sukaji alamun fitowarsa suka koma gurin zamansu
Gani sukayi ya nemi guri ya zauna yajanyo
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 18