bai amsa ya wuce part dinsa
Yashirya cikin kananan kaya masu kyau sun karbi jikinsa sosai
Yafito yana waya suhaila tace ga aika nan ankawo daga gurin mummy yace OK yadauki basket din
Ya wuce dakin maryam yana shiga yasamu har ta tasha tana kokarin gyara dakin
Hanu ya harde yana kallonta yace kintashi shine bazaki huta ba
Bata kalleshiba ganin bata da niyar kulashi yasa kama hanunta suka zauna yace kibari zansa masu aiki su gyara miki
Cikin shagwaba maryam ta juya baya tace Allah yasauwake nikabarni kawai zangyara dakina
Zagewa yayi yatayata suka gyara komai a inda yake dakin yadau kamshi kafin tashiga wanka abinta
Tana fito tasamu ya fito mata da Riga da skirt Wanda yasiyo mata daga India Jane kuma yana da ado falawa masu kyau
Taki sawa sai yafita ganin hakan yasa dagash yafita abinsa yana dariya yace afuwan baby ni ai me lefi ne
Yana fita tashirya abinta cikin kayan sunyi matukar yimata kyau sosai ta gyara gashinta tayi parking dinsu da ribbon mai kyau sosai
Tana gamawa tasake feshe jikinta da turare ta fito falon Tana tafiyar ta na haliita
Ganin dagash ya tsareta da kallo yasa ta turo baki tayi gurin daning din
Da kanshi ya yayi saving dinta yabata farfesun kayan ciki taji dadin farfesun sosai
Lipton tasha kafin dagash yayi break din shima
Soyayya mai tsafta da kaunar juna dagash ya ke gwadawa maryam
Saida yayi sati cas baifita ko ina ba duk nacin su zayyad suka ringa kiran number dinsa kin dagawa yayi
Yau suka cika kwana bakwai da aure sosai maryam tasaba da soyayyarsa sosai sunshaku a wannan a kwanakin
Yashirya yafita aiki maryam kuwa tana gama aikinta ta takunna kallo tanayi
A part dinta can taji muryarsu rahma da shafa'atu
Taji dadin ganin su kuwa da murnar suka shige dakin maryam nan hira ta barke tsakanin su
Rahma tace kin ganki kuwa maryam sati daya kawai amma kinzama abin kallo
Shafa tace kin rigani ne amma wallahi yaya na ya iya kiwo
Murmushi maryam tayi tace Allah ko
Kokuma ni na iya kiwoba bari yadawo kiganshi ai bazakiganshiba
Shafa tayi ihu tace maryam kece da baki haka
Maryam tayi murmushi tace kina mamaki ko kafin suyi magana wayar maryam yayi kara
Ta dauka tace hello my Prince
Dagash bai tabajin dadin sunan Prince ba sai da maryam takirashi da Prince
Ya dai daita kanshi yace my princess dafatan ba bacci kikeyi na tashekiba
Murmushi tace kodaya gasu rahama ma sunzo kana fita yace bawa shafa wayar
Tamika wa shafa wayar yace banyarda kutafi gidaba harsai kunga nadawo saboda banason princess tayi wani abin da kanta
Shafa tace shikenan yaya angama munan har sai kawadawo
******
Bayan shekara goma dagash Nada yara biyar hudu maza daya mace kuma duk princess ce ta tahaifa mishi
Suhaila da aymana ko batan wata basu tabayiba sakamakon kwayoyin da sukasha a baya suna dai zaune zaman aure da kyauta tawar miji
BARRISTER MARAM zaune cikin library na na part dinta tana nazarin wani Case da yashigo ta hanunta
Sai dagash yashigo cikin kayata alfarma yace princess yakamata kitashi mutafi wurin gasar nan haka ko
Tace to my Prince kasan wanna case din Dana baka labarin yashigo hanuna shine naketa nazarin abin yace my princess tashi idan mundawo zan tayaki
Nan ya rungumo ta suka fita Aisha sukagani zaune an mata ado cikin shadda irin Wanda yake jikin daddynta
Tana ganin su ta taso da gudu daga maryam har dagash suka ware hannuwansu
Sai ta wuce uwarta tayi gurin daddynta
Maryam tace la niza awa sonkai
Dagash yamata gwalo yana rungume da yarsa wacce yake kiranta da mummynshi saboda taci sunan mummyn shi Aisha
Yace kidage kihaifo naki kema
Maryam ta balla mishi harara tace naki din wadan nima sa'ib yafisona akan kai
Dagash yayi murmushi yace wayafada miki bari mudawo agwada
Yana dariya tace ai dariya kake min ko
Tashi yayi dauke da mummynshi suka gudu kar maryam takamasu ai kuwa ta biyo su
Suna fitowa falo sukaga suhaila tana gyarawa sai'b wuyar rigarshi
Sai'b shine Dan dagash na uku kuma shine mai sunan daddyn maryam wato Ahmad alhaji imam kenan shine suke kiransa da sai'b yaron yashiga ran suhaila shiyasa ta daukeshi take mishi komai
Dagash yace yauwa kinga mummyn sai'b ko kedai kiyarda bakida kowa
Maryam tashiga shagwaba tace shikenan naji amma ai Abba da daddy suna bayana ko
Dagash yace wayafada miki
Yaran dasuki zama anan gidan ma su saida gidan kakansu
Maryam ta turo baki tace Prince fa ai shidai Dan baya kasar ne amma ai yana bayana ko
Suhaila tace turkashi ai gwara kowa da da Prince ma
Wannan ai photocopy din doctor ne
Dagash yayi dariya yace yakikaji sunanshi namijin duniya
Prince shine Dan dagash na farko kuma shine yayi gadon komai na dagash kuma shi akasawa sunan daddyn dagash wato su'ad shine
Ranar da aka haifi su'ad a ranar daddyn dagash yace yanzu mukasamu Prince kuma inaso acigaba da kiransa da sunan Prince din
Shekarasa tara ayanzu yana karatu a can libiya ne
Maryam tace shikenan na yarda zan dauko baby yarinyar rahma tazo muzauna abinmu ai ita tana sona dagash dai yayi tadariya
Da shi da suhaila aymana ta shigo tana waya
Maryam tagaisheta ta amsa bayabo ba fallasa saboda ita haka take bata wani ja yaran ajikinta acewarta bata Haifa ba baruwanta da 'ya'yan wata
Dagash yace to zamuje gasar karatun da aka gayyaceni
Aymana tace adawo lafiya
Suhaila tace idan badamuwa nima zan iya zuwa
Yace why not jeki dauko hijabin ki mutafi
Maryam taji dadin yadda suhaila ta maida komai ba komai ba
Atare suka fita zuwa wajen mota
Maryam ta bude gaba tace anty suhaila kishiga nan zamu zauna a baya nida yara
Suhaila tace a a Maryam ke kishiga gaban
Dagash yace OK wato ba maison zama kusadani shiyasa kuketa musu mai zama ko to duk kuzauna a baya kubani yarana su zauna a gaban
Hakan kuwa akayi maryam da suhaila suka zauna baya suna tawa dagash dariya
To masu karatu anan zan tsaya da littafina maisuna AL'AMIN DAGASH
kuskurena Allah ya yafemin
Ina godiya sosai da kaunarku a gareni masoyana
Allah ya hadamu da alkairi
*Signed by ummu afan* 💻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 18