Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutum ba tashikibani guri nan da wata zan daura miki aure da mutum daya acikin mane manki Aikuwa cikin tashin hankali natashi nayi dakinmu inazuwa nafada jikin innarmu Tace ya akayi maryama nace innan mu nashiga ukuna wallahi Abba zai aura min Wanda banaso Inna tace kiyi shiru maryama insha allahu aliyu zaki aura Yau idan yazo kice ina nemansa nace to innan mu Dan ina yadda damaganar innanar mu Dan tana sadaukar da farincikinta saboda yaranta Aliyu yazo kiran innan mu Bayan sungaisa tace mishi aliyu idan dagaske kake yakamata katuro magabatanka gashi mahaifinta har yafara shirin bada ita gawani Aliyu cikin tashin hankali yace inna Dan Allah kar amin haka wallahi idan na rasa maryam zan iya rasa raina Inna tace bazaka rasata ba aliyu kawai katuro magaba tanka asan abinyi Haka kuwa duk abin abbana burinshi na aurar dani baicikaba saboda magabantan aliyu sunzo An tsaida magana nan da wata biyu za ayi bikin mu da aliyu Hakan yasa aliyu tafiya Neman kudi kafin lokacin yazo Munyi bikin kawata deeje yarage saura nikadai shiyasa ma nadaina zuwa ko ina Wata ranar alhamis ranar da bazan taba mantawa dashiba a rayuwata takarasa maganar tanakuka Dad ya miko mata robar ruwan swan water batayi musuba tasan tana bukatar ruwan kam Bayan tasha ruwan tacigaba da basu labarinta Ina cikin tafiya kan hanyar zuwa islamiyyata naga wata bakar mota sun tsaya agabana naga sunbude kofar motar sunfito Duk fiskarsu a rufe yake Suka nuna min bindiga sukace wuce muje ganin bindiga nayita basu hakuri sukaki karshe kawai ma sai suka fesa min wani Abu Bude ido kawai nayi naganni a wani hadaddan gida mai kyau sosai da haduwa Kuka nakarka dashi hankalina yatashi can sai naga anbude kofar anshigo Wani alhaji nagani fari mai mutunci dashi a fuska Yafi zubin larabawa haka dashi Yayi dariya yace barka da tashi yake kyakykyawar yarinya Nace Dan Allah alhaji kaiyi hakuri kafitar dani daga gidan nan Wasu ne suka satone daga kauyenmu Wani dariya naga alhaji yayi yace ke yarinya dena hadani da Allah kicuceni Dan kozaki kukan jini ba kyaleki zanyiba Tabas ninasa akawo minke gidan nan saboda tun ranar danaganki nakwadaitu da surar da Allah yamiki da kyan hallitarki duk da acikin hijabi naganki Hakan bai hanani ganin wasu sirrika atare dake ba Na nunawa yarana ke sukaganki shine yau nace akawo minke na huta dake saboda bani da niyyar aure a yanzu Dan da inada niyyar aure zan aureki kodan kyau da Allah ya miki Cikin tashin hankali nace Dan Allah alhaji kar keta min haddi Wallahi niba yar iskabace alhaji aurena ya kusa alhaji Kabarni naje da mutuncina gidan mijina karka bata abinda nayi shekeru ina tattalinsa alhaji karufa min asiri Dan Allah Alhaji yace wayafada miki nima ba auranki zanyiba Ai bazan yadda na hada shimfida dakeba sai an daura min aure dake saboda kikwantar da hankalinki auren sunna zakiyi Sannan kuma kiraya sunna da ni mijinki Aikuwa nasake shiga tashin hankali sosai yace yanzu dare yayi amma zuwa gobe karfe tara za a daura min aure dake a masallacin anguwar nan Zanbaki sadakin ki gobe yasa aka kawo min abinci da ruwan sha nisaboda tashin hankali ko yunwar ma da kishin ruwan bana ji Yadda naga rana haka naga dare saboda tashin hankali ba abinda nakeyi sai salloli da addua Dasafe karfe Takwas alhaji yashigo yace 'yanmata sunanki saboda liman ne yake zai miki wakilci Ban dago ba bare naga fuskarshi saboda babu mutumninda natsana a duniya sama da wannan alhajin Alhaji yayi magana yaji shiru yace toshikenan daman bana son kusantarki batare da aure. Bane tunda kinfi son hakan shikenan bari kiga aiki da gamawa yafara cire kayansa Cikin tsananin kuka da tashin hankali nace sunana maryam Yayi murmushin mugunta ya ce Ashe kina da wayo yarinya Bayan daura auren Alhaji da maryam yadawo cikin gidan yabata sadakinta dubu ashirin Bata karba ajiye mata yayi yace hakkin kine fa idan baki karba kinyi wa kanki Har video din daurin auran yakawo mata dan ta tabbatar da andaura Sati na daya agidan Alhaji a matsayin matarsa Abinci inacinsa ne kawai Dan yunwa karya kasheni Amma bawai Dan tana jin dadin komaiba Ina zaune a falon gidan Dan Alhaji kullewa yake idan zaifita Sai naga yadawo da wuri yabani takarda yace nasake ki saki daya Tunda nazo gidan banyi dariyaba sai daya bani takardar sakina Yace zan koma kasan mu saboda amin waya mama na bata da lafiya Ina so kisa a ranki baki taba sanina ba a rayuwarki Saboda bazaki sake ganinaba maryam Nayi murmushi nace Alhaji nima bana fatan na sake haduwa da mutum kamarka a rayuwata Nisakin da kamin ma yafi komai dadi a rayuwata Sai dai kacuceni Allah ya isa bazan taba yafe maka ba Allah ya isa Murmishi yayi yace wannan damuwarkice kinji nabaki hakuri ne to bana bukatar hakurinki All what I know dai banyi zaman zina dakeba auranki nayi Dakin na koma namaida kayana da yasato nidashi harda hijabin da da jakar makarnta nawa tunda nazo nafito yace yauwa ai sai an maidake tace bana bukatar sumaidani Kafada min kawai nan inane Alhaji yayi murmushi yace ai abinda bazaki sani ba kenan Dan haka ma ko compound din gidan nan bazakiganiba yadda kikazo hakazi koma Banyi aune aune ba naji sunfesa min wani Abu aikuwa Sai bude ido nayi naganni a dakin innata sunata min fiffita ancika akaina Yaya aliya tace inna ta bude ido sunyi murnan farkawata Ruwan zafi inna tasa aka hada min nayi wanka suka hada min kunun gyada mai dadi Ina zaune a kan gadon innata yayuna duk sun zagayeni Abba yashigo yace sannu maryama nace yauwa Abba sannu Yace wai ina sukaiki ne wannan tambayar da Abba yamin yadaga min hankali Dana tuno da abinda yafaru dani Nasan idan nafadi gaskiya Abba bazai amince min ba Sai kawai nazabi da nayi karya akaro na farko a rayuwata Nace Abba masu garkuwa da mutane sun tambayeni ko babana mai kudine nace musu a a nafada musu sana arka shine suka min duka suka saka naketa musu wanke wanke kullum muna dayawa Wanda aka kama amma yawancinsu iyayensu masu kudine shine sukace bazasu smdawo damu gidaba sai randa iyayen yaran nan suka kawo musu kudin da suka bukata Ba a gama turo musu kudinba sai jiya shine duk suka fesa mana wani Abu Dan kar muga inda za a fito da mu Abba yayi ajiyar zuciya jin cewa ba a musu komaiba Nan da nan kowa yashiga fadin albarkacin bakinshi na ta tatsallake rijiya da baya Abba yace Allah yarufa asiri yafita Innan mu tace kai munshiga tashin hankalin rashinki maryama dagani har mahaifinki ba maici ba maisha Har gurin hukama ankai maganar amma dayake bamu da gata ba awani damu a yi bincikenba Yaya aliya tace sannu kinji maryam allah yadada karewa to ai tunda yanzu dai dama can kinsauke kinyi hadda ki hakura da zuwa islamiyyar nan Har sai kinyi aure kuma sai ki fara zuwa na matan aure Innan mu tace wannan haka yake tunda ai an kusa ma Maryama na ki hakura kinji da zuwa makarantar nan har sai kinyi aure kuma sai kicigaba da zuwa makarantar ko Na daga kai nace to innan mu insha Allah Yaya sumayya tace ikon Allah duniya ya lalace ace sace mutum ba abin komai bane a gurinsu Na dawo normal kamar yadda nake da sai dai ansamu canji saboda innan mu ta lura dayawan damuwar Dana ke ciki Bayan sati uku da dawowata lokacin al'adata yayi banga komai ba hankalin yatashi sosai Ga kuma yawan tashin zuciya danakeyi Ina zaune innar tayi miyar taushe yana ta kamshi nikuwa cikin yana ta juyawa aikuwa sai amai amai sosai nayi inna hankalinta yayi matukartashi Kishiyoyinta suka taso sukayi wa maryam ca suna salati wai kardai zarginsu ya tabbata akan maryam Inna ta taimaka wa maryam sukashiga daki akuwa uwargidan tace wallahi bazaa haifama na cikin shege a gida Anje anyi abin kunya za azo ana rurrufewa to bari malam din yadawo dole aje asibiti a tabbatar da abunda muke zargi Innan mu gabanta yafadi ras jin sun ambaci ciki Ya ma za a yi hakan takasance da maryam yarinyar arziki kamila baruwanta da duniya Abba ne yashigo har sun guntsa mishi aikuwa yabanko kofar dakin innan mu yace ke maryam meke damunki tace ba komai Abba Yace maza dauko mayafinki muje asibiti innan mu hankalinta ya tashi tace malam yadaga amai sai ace za aje asibiti kobaka yarda da yarkabace Abba yayi murmushi yace halima kenan 'Dan yau ai ba abin yarda bane balle yarinya baliga irin maryam shekarar ta shatakwas ba aure kuma muga tafara amaye amaye acikin gida ai dole hankali ya tashi Harda innna akaje asibitin aka min duk wasu gawaje gwaje dayawa kamata amin muka zauna jiran sakamoko Yaya aliya da taje gidan bata samu kowaba ance duk suna asibiti Itama tayo asibitin Antyn maryam data kawo nan sai kuka ta fashe da shi mai tsuma jiki harda sheshsheka Maryam kanta kuka takeyi na tausayin mahaifiyarta daddy da megari ma duk jikinsu yayi sanyi dajin labarin maryam mai ban tausayi Daddy yace Ashe daman haka masu kudin mu suke basu da imani kokadan Megari yace hakane abinkam ai sai addua Megari yace maryam muna sauraronki cigaba da bayaninki Next page Your comment is needed fans Love u love your comment More comment more typing *Signed by ummu afan* πŸ’» [26/06, 11:54 AM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑 πŸŽ€ *BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM* *Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI* 🌟GORGEOUSE WRITERS FORUM🌟 🌟 G.W.F🌟 *Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest* I DEDICATE THIS PAGE TO YOU MAMAN IMAM allah yabar kauna ina matukar alfahari dake over sis keep it up wajen nice comment din ki ❀ _🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑 πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH* *PAGE* 9⃣ Anty maryam tacigaba da ba su dad labarinta Tace nurse tafito dauke da sakakamakon gwajin da aka min Gaba na yafadi dan nasan yau kam asirina ta tonu ga mutanen gidan dam asibitin sai kace wacce nakashe mutum aikuwa tana karasowa Abba yace yauwa malama yadai tace baba a sakamakon da gwajin yabamu yarka tana dauke da ciki harna tsawan wata daya aikuwa guri yadau salati da maganganu Yaya aliya juyawar dazatayi taga innan mu tana shirin faduwa tayi saurin zuwa ta tare ta fadi ajikinta sumammiya Akayi cikin asibintin da ita Abba kuwa durkushewa yayi a inda yake zaune yana salati duniyar yashiga juya mishi Yace halima kincuceni Dakika bari na aurar da yarinyar nan kamar yadda nake aurar da yan'uwanta Uwargidan Abba tace daman bawani saceta da akayi yawon iskancinta ta tafi za a rainawa mutane hankali wai ansaceta Abun yasake tu zura baba na ya taso yafara kaimun duka yana tsine mun yana cewa yacireni daga cikin 'ya'yansa Ina kuka incewa wallahi Abba bacikin shege bane ina gani yake ma na raina mishi hankali Da kyar mutanen anguwar suka karbeni a hanun abban mu yace daga nan kuma karna koma mai gida ya koreni Ya sallamawa duniya ni kwatata kwatata yaki yabani daman nayi magana Haka yatasani agaba yana dukana yana korani har bakin titin garin yace natafi inda aka min ciki shiya yafeni Nazauna agurin nacikuka nakoshi bansan inda zan nufa ba danni ba bazan iya komawa kauyen muba saboda babu Wanda zai yadda dani Ina cikin kukana naji andafani na juyo da sauri naga ko waye sainaga deeja ce kawata tana kuka ganinta sai na rungume ta muna kuka sosai Mijinta ne yakawota a mashin dinsa sunji abinda yafaru tace lalle tasan ina hanya sai dai yakawota kozata ganni Nace deeja kinga yadda allah yayi daniko deeja tace karkice komai maryam wallahi na yarda dake nasan akwai wani Abu amma bazaki taba aikata abinda wannan abinda kunyar da ganganba Nayi murmushi nace nagodewa allah dayasa nasamu mutum daya data yarda dani Nan nabata labarin komai abinda yafaru sosai deeja tayi kuka tace kizo mukoma gida mumu su bayanin komai Nayi murmushi nasan daman zakice haka amman sai dai kufara zuwa kumusu bayani inan idan sun amince to na yarda saikudawo mukoma gida Cike da doki deeja takoma inda mijinta yake dan daman yana jinsu tace yakaita gida suje suwa su abban maryam bayanin komai dan allah Suna tafiya nayi murmushi na duba lalitar innan mu Dana dauko dan daman nike sayar da komai akazo siya shiyasa tabani lalitar na daura saboda bada canji alokacin da abban yace nafito muje asibiti dama lalitar tana jikina baciireba Ina ganin haka nayi hamdala natashi da kyar na tari muta akace ina cikin gari Wato meduguri kenan Muna isa tasha akace kowa yakawo kudin mota Bayar danawa Daga can gefe naga kawai mota na Lodi naje nashiga mota yacika aka dau hanya Tunda muka fara tafiya ba abinda nake tunani sai bansan ma me motar take ciki ba Sai ji kawai nayi anacewa kowa yafito na fito natambayi kudin mota Akafada min nabayar nakara gaba sai kuma tunanin yazomin na wai a wani garima nake Juyawa gurin motar nayi nakarewa wa memotar kallo Can na nufa daga gefe naga wata mata da alama akwai abin da take jira ta Tara kayanta a gefe Namata sallama ta amsa nace baiwar allah Dan Allah nan wani garine Tambayar Dana mata yabata mamaki dan na fahinci hakan a fuskarta Tace yanzu kebaiwar allah Ashe bakimasan wani gari kikazoba Na daga mata kai alamun bansaniba tace to abuja kike tarayyar Nigeria Mamaki yacikani wai abuja Matar tace idan bazan damuba zata min tambaya akan rayuwata dan kuma inda zanje Nan dai na takaita mata kadan tace idan ta fahimceni dai bani da inda zanje kenan nace kwarai kuwa tace idan bazan damuba zata tafidani gidan nace nayarda Nafara zama da anty hassana me abinci ina tai maka mata a wajen sana'arta tana bani gurin kwana da abinci sai sabulun wanki haka amma ba albashi hakan ma nagode Ina nan ina rainon cikina har yakai watan haiuwarsa Tsakar dare natashida nakuda anty hasssana ta kira ungurzoma dan bazata iya da tsadar asibin abuja ba Akullum addua ta shine allah karyabani yarinya mace saboda renon 'ya mace akwai hatsari musamamn ma a wannan rayuwar danake ciki na rashin gata Idan kuma yabani macen yabani mummuna yadda bazata ja hankalin mutane har su cutar da itaba Na haihu lafiya na haifi 'yata kyakkyawa allah bai karbi addua taba don yarinyar harta finima sosai Anty hassana tana tayaba kyan yarinyar gata fara Sol da ita Nayi kuka danaga yarinyar da allah yabani saboda ina tsoron abinda yafaru dani yafaru da ita Ranar da nacika kwana bakwai da haihuwa nawa 'yata huduba da suna na Maryam Sosai nake kokarin kula da ita dan anty hassana kullum tana kasuwa Nikuma sainayi arba'in zanfara zuwa nima kasuwar Muna haka ina ta renon maryam yarinya me wayo da farinjini itama tun tana karamarta anty hassana gaskiya ta taimaka min a rayuwata duk da bawai tana biyana albashibane amma zanci zansha zata sai wa maryam gwanjo masu saukin kudi idan tasamu dama amma fa nima ina bautuwa a wajenta Muna haka shekarar Maryam hudu aduniya anty hassana tafara ciwo bayan kwana biyu kuwa allah yama ta rasuwa Nayi kukan rashin anty hassana sosai bayan makokin anty maryam narasa abin yi Gashi maryam tayi wayo kullum setamin maganan makaranta insata amakaranta Ina zaune nida maryam ina bata abinci abaki aiki naje nayi nasamu akaban abincin Sallama naji shugowa kawai sukayi Ashe wai dillalan gidan ne sunbani nan gobe na kwashe komai nawa zasu zuba wasu agidan ba tausayi a fuskokinsu Shiyasa ma bansamu damar basu hakuriba Haka washagari mukabar gidan na tattara mana kayanmu naja hanun maryam muka fita tafiya kawai nakeyi amma bansan inda zanje ba Bamuzame koinaba sai kofarwani asibiti kawai nasa kai nashiga cikin asibitin Har dare yayi bansamu abinda zanba maryam taciba Gashi bani da kosisi Muna zaune kusada wata mata da alama jinya yakawota saita fito shan iska ta shimfida taburma sunata hira da masu zuwa gaisuwa Wani katon kula ne agabansu kuma wai anemo musu almajiri yakarbi abinci Banyi sanya ba nace musu inaso da mamaki matar ta kalleni tace to bawair allah dauka kijuye to Jikina har bari yakeyi nadubo bakar Leda a jakarmu najuye shinkafa ne haddadiya da miya Harda nama ma aciki Nan naje fanfo na wanko flask nakawo mata na mata godiya kafin nadawo gurin maryam natasheta a baccin wahalar datakeyi nabata abinci sosai maryam taji dadi nagani a fuskarta Tabani tausayi sosai kukanayi sosai saida ta koshi da kanta nadebo mata ruwa fanfo nabata tasha sai bacci kuma na shimfida mata zani ta kwanta kafin naci abinci nima Anan muka kwana abinmu kasancewar akwai masu kawana a wajen ba Wanda yadamu damu Inatashi naga wata guntuwar tsintsinya nashare asibintin nan tas kaman jaka Haka dai har mukayi sati a asibitin nan kuma kullum allah baya hanamu abinci idan mutane suna Neman almajirai zankarba kuma kullum ina share asibitin nan tas Muna zaune da maryam ina mata tatsuniya sai naga wata ma'aikaciyar asibita tazo tace baiwar allah waikizo inji likita nace nashiga uku badai sungaji damu bane zasu koremu Nan dai nakama hanun maryam mukabi bayan nurse dinan Muna zuwa muka zube akasa likitan ma ba musulmi bane Dakyar hausar tashi yake fita Yace sannu ko nace yauwa likita allah yasa ba laifi mukayiba Yace a a no karkidamu kece mesharemana hospital kullum ko nadaga kaina yace good Ya kalli maryam Yace beautiful girl zonan maryam taki zuwa dan bata yadda dakowa sai antynta kamar yadda take cemin Murmushi yayi yace idan kina so zakicigaba da aikin zamu daukeki murinka biyarki zamu baki dakin dazaki zauna da yarki acikin hospital din nan Dan farinciki ma rasa mezanyi nayi saboda dadi Sosai ma mishi godiya yace karkidamu malama zamu ringa biyarki dubo goma kafin muga kokarinki akan aki sai mukara miki albashi zuwa dubu goma shabiyar sosai nayi godiya yace bakomai Yacewa nurse ta Nina mata dakin dazata zauna acikin reception tace OK sir Har munyi gaba yace am malama najiyo yace amma kiringa kula da lafiyar babynki karkibarta tacikomai a hanun mutane kinji ko sosai naji dadin shawarar dayabani Takaimu ta nuna mana dan karamin dakin da toilet aciki da alamu ma office ne suka maidashi daki nan tace to baiwar allah ga dakin nan dazaku zauna ga toilet nan akwai ruwa aciki saiki tsabtace dakin Sosai naji dadi itama namata godiya nashiga gyaran o koina yayi fes dashi Likita yakirani yabani Rabin albashina wato dubu biyar wai kozan bukata naji dadi dan muna bukatar abinci A da lilin aiki a asibitin nan nasa maryam a makaranta tana zuwa school din ta sosai mukejin dadin rayuwarmu a asibitin nan Munaki kusan shekara goma zaune a asibitin nan munsaba da likitan nan sosai dan yana temaka mana a arayuwa kaman wani musulmi Shekarar goma sha hudu sukayi sauka a islamiyyarsu tana Jss two sakamakon rashin shiga makaranta da wuri Kwatsam muna zaune nida maryam tana min kitso sai mukaji hayaniyya a waje naje mukatashi gaba dayanmu mukafita wazamu gani doctor Patrick ne mukaga 'yansanda sunsashi a mota suntafi dashi Nayi tambaya meyayi akace min wai ana zargin asibitin nan da saida sassan jiki mutane Kuma ana zargin dasa hanunsa aciki Nafasheda da kuka nace ya Allah kasa yazauna a matsayin zargi allah karka tabbatar da wannan Abu haba mutumin kirki irin doctor Patrick Mukazauna cikin jimami abinda za azo a fada mana Bayan sati daya naji wai za a rufe asibitin har ankai doctor fursuna Haka muna ji muna gani mukarbar cikin asibin doctor Patrick dake garki village Maryam tace anty yanzu ina zamuje nace mata sai inda allah yayi zaman abuja kam bazai mana ba saboda tsadar rayuwa Haka muka hau motar mararrabar abuja dan inayawan jin sunan a bakin mutane Munje kuwa alhamdullahi munkarbu dan gidan nan ina magari muka fara sauka na nemi da megari yabamu waje zamufara Sana'a shine yabamu wannan runfar Wanda muke zaune acikinta Yanzu dai shekarar mu daya da wata biyu agarin nan To wannan shine takaicaccan tarihin rayuwata Takaarasa tana share hawayenta maryam matso cikin kuka ta rungume anty tace antyna allah ya isa miki allah saiyasaka miki Danasan abinda zanji kenan na labarin mahaifina da banbiyokiba kuma ina rokonki gafara akan kiyafe na matsamiki danakeyi kibani labarin babana Anty dai takasa magana sai kuka kawai Megari da dad sunma kasa magana saboda tausayin maryam da yarta Megari yace to Alhaji yanzu zabi ya rage naka akan maryam Dad yayi murmushi yace ai wato wannan labarinta data fada min yasake samin tsananin sonta a raina Saboda maryam zan aureki zan rike maryam tamkar 'yata zan hadata 'ya'yana narikesu tsakanina da allah Sannan kuma bayan bikin zan dauki maryam muje garinsu dan ama iyayenta bayanin komai Anty maryam ta tashe da kukan murna tace mungode Alhaji Allah yabiyaka duniya da lahira Daddy yace ai bake zaki gode minba maryam nizan gode miki da kikayarda zaki aureni Megari yace kai amma naji dadin wannan Abu Alhaji allah yasa masu kudin irinku su yawaita aduniya Daddy yace amin amin Abinda nake Neman alfarma niba yarobane dan haka banson maganar auren ya wuce nan sati biyu Megari yace masha Allah hakan ma yayi amma bari muji ra'ayun malama maryam din Anty maryam tace ba amince amma ina rokon wani alfarma da abari sai bayan maryam tayi jarabawarta na makaranta Daddy yayi murmushi yace wannan kadai uzirinki anty tadaga kai alamun a Daddy yayi murmushi yace ai yanzu baki da iko da maryam nikeda iko da ita a matsayina na mahaifinta saboda haka karma tasake zuwa wannan ma karanta zan canjamata Wani a kano anty da maryam suka kalli juna maryam tace nagode daddy Allah yakara girma Daddy yace amin yar daddy Nan dai daddy da megari sukagama shirya komai Daddy yace kai zakazama waliyyinta idan allah yaimu nan da sati daya zanturo kanina da abokina sukuga juna amma yanzu inaso amatsayinka na waliyyin maryam inaso zanbiya sadakinta a yanzu Megari yace masha Allah hakan yayi kyau sosai kuma ya nuna min kai babban mutumne alhaji baka magana biyu Daddy yaje mota ya dauko brief case dinshi yadawo yaciro bandry din yan 1000 ya ajiyesu agaban megari yace wannan kuma kudinkuma na menene Dady yace sadakin maryam ne dubu Dari biyarne Yace zanturo za amaka gyaran gidan nan gone gobe insha ga cheque na 5 million kasa aljihunka Yajiyo yace gurin maryam zanturo driver yakaiki kihada lefenki da kanji maryam 'yatama inason kimata sayayya yadda takeso Ya tura mata kudin dake cikin brief case din Anty kusan suman zaune sukayi itada maryam Ganin yadda suke kallon kudin cike da rashin yadda da kuma tsoro Megari yayi malama maryam kokinajin sunan hamshakin mekudin nan dayashara a kafafen yada labarai na duniya wato AL'HAJI SU'AD BABANGIDA anty Maryam tace kwarai kuwa jin sunan abakin jama'a Megari yace to yau baki Gashi Ya nuna Alhaji da hanunsa Anty maryam cike da mamaki tace yanzu alhaji daman Kaine wannan shaharraren mutumin amma meyasa kaboye min kanka Daddy yace saboda ba matsayina nazo infada miki ba soyayyarki nazo nema Nan dai komai ya kammala tsakanin anty da daddy amma fa da temakon megari dan anty dataji waye dady tace allanfur yafi karfin ta Hartaba daddy dariya ma sosai Daddy dakanshi yakaisu gida yace oh my God maryam daman airin wannan gidan kukeciki anty murmushi kawai tayi zatafita yace tsaya bansallamekiba Maryam karama tafito da brief case din da alhaji ya basu cikin dogon hijabi Tace daddy yar dady Allah yayi miki Albarko tace amin dady Ya miki mata wata Leda yace ga tsarabarki Maryam takarba tayi cikin gida Daddy yace wa anty maryam to amaryata nizankoma kano yau sainasake dawowa kafin ranar daurin auren Anty maryam kunya yakamata takasa tace to shikenan agaida yayuna Daddy yayi murmushi

Chapter 6 of 18