Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasa suka amince akancewa nan da shekara daya ai kaman yaune gurin ubangiji Alhaji imam ya kudiri niyar komawa Nigeria yaje yayita bincike akan maryam ko Allah zaisa adace *** Nigeria Dagash ne zaune kan resting chair dinshi yana aiki a computarshi Maryam tashigo cikin duguwar hijabinta tace sannu da aiki yaya yace yauwa batare da yakalletaba Tace yaya Dan Allah inason zanje gidansu rahma Daga nan zamuje gidansu fareeda Ya watsamata harara yace bazakijeba Zatayi magana yadaga mata hanu ta tashi jiki bakwari tafito Tana fitowa shafa'atu na sallama maryam taji dadin ganin shafa'atu sosai tace La anty ashe kina hanya Shafa'atu tace kinyi mamaki ko Kinga jiya nabar nan yau kuma nadawoko Maryam tayi murmushi tace a a anty nimurna ma nayi wallahi saboda naji dadin hirar mu najiya Shafa'atu tayi murmushi ta harareta tace to yau zuwan banaki bane my hubby ne zaizo muhadu a nan Yafi sakewa anan akan can gida Bata karasa maganarba ta makale saboda dagash hango can bayan maryam ya folding hannayensa yana jinta Maryam dabatasan meshafa tagani ba tayi murmushi tace wallahi anty na soyayyarku da yaya Faisal yana burgeni gaskiya kunyi dace da juna Ganin shafa'atu takasa magana yasa maryam juyawa tankalli inda shafa'atu ke kallo itama ta tsorata sosai Yace kuna kanananku daku kunsan soyayya ko ke shafa bakiji kunya ba kizauna da wannan yarinyar wai kina mata maganar saurayinko metasani Kekanki mekikasani bare ita da secondary school dinma yanzu tagama Maryam ta turo baki tana kunkuni Shafa'atu dai batace komaiba Sai kayi hakuri yaya take fada Yace ke baby biyoni yajuya yakoma falonshi Shafa'atu kanta yadaure tarasa wacece babyn gani tayi maryam tana Dan dire direnta da kafa tana turo bakin tayi hanyar dakin yayan nata Shafa'atu kusan suman tsaye tayi saboda ganin bakon lamari Dan ko a mafarki bazatayi tunanin yayan nasu yana da sauki hakaba Wai baby to kodai daman haka sunanta yake Tayi murmushi tace ikon Allah tana kan tunaninta taji anyi tafi da hanu firgit tafigita Sai dai ganin me tafin yasata murmushi Faisal tagani Yace matsoraciya harkin tsorata tayi murmushi ta ai dole ina gidan boss ne fa suka yi dariya gaba dayansu Dagash kuwa yana zaune yana aikin gabanshi maryam hartagaji dazaman jiranshi Sai daya gama komai kafin yajuyo yace wayo shafa'atu suna burgeki ko Maryam ta turo baki tace nifa bance ba Yace mekikace tace bakomai yace nayi karya kenan ko tace nidai bance kayi karya ba Yace wato bakyason cigaba da karatu ko kinfison soyayya ko ana hure miki kunne Maryam tace kodaya ni insha Allah saina cika burina nazama abinda nakeso nazama a rayuwa kafin nayi aure Ya kalleta da mamaki yace aure wai ke harkinsan Kalmar aure baby Maryam tace bansaniba amma dai hakan nacewa yaya jabeer yayi hakuri bazan iya auransaba har sai gama karatu Kuma yanzu yace zaijirani dagash yayi saurin Daga mata yace enough baby Oya get out of my room stupid girl Maryam ta kalleshi ta rau rau da ido aikuwa tafashe da kuka abinta Mamakin kukan nata yakeyi yace lafiya kike min kuka Cikin murya me sanyi da shagwaba tace bakaibane ka tsoratani Dagash yace God help me yadafe kai Yatashi ya haura samanshi itakuwa maryam nan tacigaba da kukanta Zuwa yayi wanka yafada yafito cikin kananun kayansa Ya ganta tana gun daya barta yace baby haryanzu oya jeki dauko mayafi kizo kirakani Maryam tayi mugun mamaki Dan baitaba Neman rakiyarta ba sai yau amma sai boye mamakinta Tatashi batare da ta kalleshiba tayi dakinta wanka tashiga tafito ta zura doguwar Riga abinta ta haugado Dan bacci tariga tasaba da baccin rana Dagash kuwa yayi tajira kozata fito amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa Shigowar Faisal da shafa'atu ne yadawo da shi daga tunaninshi Ya kalli shafa yace ke kiramin yarinyar nan Shafa'atu tayi kofar maryam tashiga da sallama taga tana ta risgar baccinta takure AC din dakin Shafa'atu murmushi tayi tace kai wannan yarinyar akwai kyau ita bacci ma kyau yake mata Fita tayi abinta tace yaya bacci take Cikin mamaki yace bacci fa kikace tace a bacci Yace jeki taso ta batayi musuba takoma Faisal yakalli dagash yace babban yaya yakamn kana bawa matana wahala ne haba Dan Allah kabarta haka ai zaryar tayi yawa Dagash ya watsa mai harara yace Dan iska ka wani nanikewa yarinya karama kazama kaman soko Faisal yayi murmushi yashafa gemunsa yace ai nadade dazama sokonta tuntuni Kaga kuwa kobakomai dole ta kalleta a matsayin abokin mijin ta kaikuma ka kalleta a matsayin matar abokinka Bawani batun wada kanwa sai anzo gida Takaici Yakama dagash ya dauki trowing pillow ya wullawa Faisal Faisal kuwa yasan yagama kular da dagash cikin tsanin dariya yakasa magana yazauna kawai yanacigaba da dariyarsa Itakuwa shafa'atu suna drama da maryam ne maryam tace alamfur kanta naciwo shafa tayi murmushi tace kitashi muje kifada naga kedin tadabance a gurinshi zaijiki Maryam tazaro ido tace wa ni caf Dan bakiga tsawar dazu yadaka minbane Nan dai shafa'atu ta rarasheta suka Maryam dake rataye dankwalin dohuwar rigar dake jikin ta Tazauna kasan carpet tace yaya Faisal ina wuni suka gaisa Maryam ta kalli dagash tace gani yaya baikulataba yacigaba da danna wayarsa Sai dayaga dama kafin yace menace kiyi tace kayi hakuri namanta Yace ok tashi kije kishare compound din gidan kaf a Garden area kije duk kigoge kujeru da komai nagurin Maryam tace to ta tashi tayi hanyar waje yabita da kallo cike da mamaki shifa jira yake tabashi hakuri amma saiyaga ta nufi aikin dayasata Hada ido sukayi Faisal yaga alamun dariya yakesonyi Cikin haushi yace Faisal dauki budurwarka or what ever kubar min gida Inkuma kaki zakasamu kafarta akarye Faisal yarike kunne yace afuwan muntafi karka illata min mata Dan tafi matanka kyau Shafa'atu dama tana waje can gurin maryam yace Honey zo inkaiki gida kinji Inkika biye maryam da dagash zaki kwana dukansu taurin Kaine dasu Duk yadda zakice tabada hakuri bazata bayarba yakarasa maganar yana dariya Shafa'atu tace kuma wallahi hakuri kawai zatabashi zai barta Maryam tayi murmushi tace wai Dan badama yaya yasa kanwarsa aiki saikuyita tunanin lafinayi Kodaya ba abinda nayi kawai dai yayi niyyar sani aiki ne Takarasa maganar tana murmushi Faisal yace wa shafa'atu kinko honey Shafa'atu tace naji aidaman nasan halin kayana Maryam dai murmushi tayi abinta tacigaba da abinda akasata Dagash ne daga can samanshi yana kallon maryam a wahale take aikin Cikin takaici dagash ya zago saijitayi kawai an damki kunnenta Cikin shagwaba tace yaya zafi wallahi mena maka kayi hakuri bazan sakeba Yana janta yace ok saikinga za a taba lafiyar jikinki zakibada hakuri ko Tace kayi hakuri bazan sakeba Har cikin dakinta yakaita yace change your slipas Ta turo baki tadauki plashoe tasaka yasake kama kunnenta har mota da kanshi yabude motar yasata ya kullo Ba maryam ba harta security dinsa na gidan sun jinjina al'amarin nan Saboda duk yadda kuke tunanin dagash yawuce nan akan zafin kai dajinkai Saigashi yau dakanshi yabude wa mace kofa Sundade suna mamaki Shikuwa dagash ba abinda yadameshi da kowa abinda yagadama yakeyi Maryam kuwa ta rike kunnanta tace wallahi rikonka dazafi Ya harareta yace oya tied your head tace a a yaya aidan kwalin karamine kabarni na dauko babba Yace roll it as I said dasauri maryam tayi Rollin Dan karamin dankwalin doguwar rigar a akanta Itafa wannan kayan manyan mayafai take samusu saboda yadda suke bin jikinta Ita daya barta ma kawai tayafa akan zaifi mata amma wannan rolling ita duk surar jikin a waje Ta turo baki yana tafiya haka kawai yake jin nishadi Sai daya farazuwa dagash shopping complex Yashiga batare da yace tafito ba yana shiga kuwa ma'aikatan sukayi ta kawo gaisuwa sai dai daga hanu kawai yake musu Yabada umarnin a kawo ice cream masu kyau yadan na wayarsa sakamon ganin sunan sweet mom dayagani Yace mummy wai yaushe zaki dawo nayi missing dinki Mummy tayi murmushi daga bangarenta tace to sarkin korafi gani air Port dinka nayi landing Cikin murna yace waw dagaske tace kaci danku karya zanma Cikin dariya yace am sorry mom gani nan zuwa karshiga kowani mota Mummy tace na nawa kuma sunbada mota akaini gida Dagash yace ok ganinan zuwa gidan Yakashe suka kawo mishi ice cream din suka wuce dashi mota Ya bisu a baya nan suka bude mai yashiga ya tada motar Yadauko ice cream din dasuka saka a kurar baya ya ajiye kan cinyar maryam Tabude farinciki yaka mata Dan tana matukar son vanilla ice cream irin Wanda yaya jabeer yake kawo musu school ne kullum sai yakai musu Cikin murna tace yaya nagode sosai batare da takalleshiba tabude abinta tafara sha Ganin bagidanshi suka nufa yasa takalleshi tace yaya ina kuma zamu baikulataba Sai gani tayi sunyi hanyar gidan daddy Suna isa masu get man yabude musu kofa Dai dai lokacin mummy mata fito daga motar da aka wota Dagash yafito da sauri ya rungume mummyn shi saboda sunyi missing din juna Tace kai Son anya kuwa kayi missing mom dinka kuwa Yace meyasa kika ce haka mom tace yadda kayi kyau kayi fresh mana Murmushi kawai dagash yayi Maryam dake ganin uwa da danta tafito daga motar ta durkusa harkasa tace sannu da dawowa mummy Mummy cikin mamaki ta kalli dagash shima yakalleta Tsaki taja tayi hanyar cikin gida dagash yayi bayanta Maryam cikin mota takoma abinta Next page Your comment is needed Fans More comment more typing Voted & share *Signed by ummu afan*πŸ’» [15/07, 1:09 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑 πŸŽ€ *BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM* *Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI* 🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟 G.W.F🌟 *Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest* I DEDICATE THIS PAGE TO ummu afan fans group Allah yabar zumunci ina jin dadin comment dinku over wallahi Allah yabar zumunci ❀❀❀❀❀❀❀❀❀ _🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 4🎑 Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH* *PAGE* 3⃣6⃣to4⃣0⃣ Al'amin yabi mummy har part dinta yace meyafaru ne mom Mummy ta mishi kallon banza tace son Ashe dagaske ne abinda ake fada min akanka Yadda suka gama da mahaifinka kaima sukeson gamamin dakai Dagash yace am sorry mom ban fahimci mekike nufiba Nan mummy tace me yarinyar takeyi a motarka Dagash ya dafa kai yace God help me Haba mom kidaina bin maganganun ummy fa Yarinyar nan amana dad yabani kuma am very sure ina riketa kamar yadda yace Kuma kema ina son kirage tsanarsu a ranki saboda rayuwa Cike da mamaki mom take kallon dagash tace son yau Kaine da min wa'azi Tadaga hanu tace Allah nagode maka da kanuna min wannan rana Ta dafa shi tace nabari son amma ina kamin alkawari ba abinda zaishiga tsakaninnka da wannan yar matsiyatar Dagash yace haba mummy bazaki daina bako tace am sorry son Da wannan yarinyar amaryar dad dinka Murmushi yayi ya kamo hanun mummy suka zauna kan bed yace haba mummy keda kanki zakibada shaidar danki kananun yara basa gabana Kuma namiki alkawarin da zaran dad yadawo zan dawo da ita nan Ina bata kulawa ne saboda my dad requested Mummy tayi murmushi hankalinta ya kwanta da jin maganganun son din nata Tace shikenan my son nayarda dakai Dagash yace that's my mom Yace to yanzu dai me wannan tsohuwar tabayar akawo min Mum tayi murmushi tace sai kakirata katambayeta kunfi kusa Dagash yace kedai mum kifadi gaskiya idan bata bada komai akawo min yanzu namata saki talatin tawaya Mummy tayi murmushi tace a a to maida wukar ai sako sosai ma tabayar abaka Yace Allah yasota Dagash yace mummy ya my dad imam Mummy tace yana nan ai yace kuna gaisawa Yaya nurane baka kiransa sosai Dagash yace ai shidinne number dinsa baicika shiga Nan sukayi ta hira da Mum Sai kusan karfe shida saura yafarga da yar mutane a mota aikuwa yawa mom sallama aikuwa abin yaba mom mamaki sosai da baisa mata rigimar abinci ba Tace to Allah yasa dai bawani abinsuka sakawa danta a abincinsu ba inbaka ba ai abindubawane ace tun tasowarshi baitaba cin abincin kowaba sai nata Tashi daya ace yafara cin na yarinya karama abin yabani mamaki sosai Mummy kenan maganar zuciya take tayi itakadai Dagash yaga maryam bata mota harzai koma ciki yadubota sai ya hangota gurin sweeming pool tasaka kafarta a ruwa tana waya abinta Cike da mamaki ya laluba wayarsa yaga baya taredashi ya tabbatar wayarsace Tsayawa yayi yakasa kunne yaji dawa take wayar Sai yafahimci da maman take wayar Sai data gama ta ankara da mutum agun Ashe Yace tashi mutafi gida batayi musu ba tabishi suka dau hanya Nazeefa dake tsaye daga inda take tace to kodai soyayya suke da yaya sai kuma wata zuciyar tace kai mezaiyi da wannan karamar yarinyar Tsaki taja takoma ciki abinta *** Yau jumma'atu babbar rana Wanda yayi sati daya da dawowar mummy Shafa'atu da maryam zaune a falon tare da matan gidan kowacce tana abinda ke gabanta Shafa'atu da maryam dai kallon sukeyi abinsu kowacce tayi kyau kamar asaceta Tsabanin matan gidan da kullum cikin English wear suke su aganin su hakan yana faranta ran dagash tunda shima baya mu'amala da manyan kaya Maryam kuwa sanye take cikin atampa super Holland Riga da skirt Wanda yayi kaman angwada ta cas ajikinta komai ya zauna mata tayi dauri mai kyau abinta Shafa'atu kuma tana sanye ne da Arabian dress sunmata kyau sosai Kowa yayi nisa kan abin dayakeyi Dagash ne yafito cikin shirinsa na kanun kaya as usual dai Tunda ya doro ido kan maryam yaga tabalain tafiya dashi kai wannan yarinyar duk kayan data saka saisun mata kyau kamar wata aljana Ya dade a tsaye basu saniba suhaila ce ta Ankara dashi taga maryam ya kura wa ido kishi yakamata Gashi badama tayi magana Shafa'atu tace sannu da fitowa yaya maryam ma tajuya danufin tagaisheshi taganshi yayi cikin shigarshi dayasaba Ta turo baki ta kalleshi tace haba yayana yaufa Friday ne Yatsare ta da ido Dan bai fahimci abinda take nufiba Tace Dan Allah kacanja kayan nan kasa manya shafa'atu cikin tsananin tsoro tadinga tabo maryam akan tayi shiru kar tajawa kan ta Maryam ta lura da abinda shafa'atu take nufi hakan baisa tayi shiruba saida ta dire a point dinta Dagash murmushi yasake yace baby wadan nan basa min kyaune maryam tace kodaya ai nasan danka lura suna maka kyaune yasa kakason sasu Murmushi yayi Dan kadan Wanda yabawa dimple dinshi daman lotsawa Yace oya tashi kije kizabo min Wanda kikeso nasa Maryam ta tashi da murna tawuce part dinshi Ba su suhaila ba hatta shafa'atu saidatayi suman zaune saboda tsananin mamakin wannan al'amari ko a amafarki bata taba tunanin yayanta zaibi ra'ayin daba nashiba Saboda ba yadda daddy da mummy basuyiba akan yadinga saka manyan kaya yaki sai ranar sallah shima yana dawowa daga masallaci zaicire ya ajiye shikenan Aymana tafashe da kuka ta tashi tadauki key din motarta tayi hanyar gidansu Suhaila kuwa takaici bakin ciki ba abinda bai hadu yamata yawaba Dagash kuwa tunda maryam tawuce dauko mai kayan dazaicanza yake waya baibi takansu ba balle yasan halin da suke ciki Maryam kuwa tafito dawata haddadiyar shadda harda babbar rigarta da hula da alamu dai ma baitaba sawa ba Ya kalleta ya kalli kayan yace baby wannan ai kin hadani da wahala Maryam ta zumburo baki tace gaskiya suzaka saka yaya Murmushi yayi yakarba yakoma ciki Maryam kuwa tadawo tazauna a inda ta tashi shafa'atu ta tsareta da ido Maryam tace kai anty shafa'atu wannan kallon haka saikace kinsamu yaya Faisal Shafa'atu tayi murmushi tace ai al'amarin naku ne keda yaya abin al'ajabi Maryam bayasa Mayan kayafa sai ranar sallah amma kiga abin mamaki wallahi yau inbishi inga yadda su mummy dama mutanansa zasu dauki al'amarin Maryam batace komaiba tayi murmushi tace anty kenan Dagash ne yafito cikin kayansa da maryam tabashi Kai masha Dan gaskiya Al'amin dagash dayasan irin kyau da tsari da manyan kayan nan suka mishi dayacigaba sasu Maryam tace kai yaya na wallahi kafito wallahi Dan da daurin aure zaka ba Wanda zaikalli angon kaizaka koma abin kallo Tace saura hular yasaka akansa saboda baisaba ba bai iya saka hularbama Maryam tace yayana barin gyara maka Shafa'atu tayi saurin daukar wayarta tabude camera Dai dai lokacin da dagash yadan sunkuyo saboda maryam tsamu saukin samasa shafa'atu tadauka kai baramin kyau yayi ba hoton saikace irin free wedding pictures din nan Sai kuma lokacin data saka din yayi murmushi yana kallon itakuma irin tana so tayi dariyar nan bata so hada ido Tarike rike hancinta tana dariya a hankali Kai gaskiya hotunan bakarya sunyi kyau sosai Guda biyu kawai tasamu damar dauka tayi sauri maida kanta TV gudun karyaganta Suhaila ta tashi itama tazari mayafi tayi gidansu Kai kara Dagash yatafi masallaci abinshi Yana fita shafa'atu ta tashi ta dafa kafadun maryam tace maryam Dan Allah kifada min gaskiya Kuna soyayya da yaya na ko Maryam jitayi maganar yamata girma ina ita ina wannan basarake mutumin dahar zatayi tunanin soyayya suke Maryam ta kalli shafa'atu tace anty mekikqa gani yasa kika fadi haka Nan shafa'atu ta mata bayani Maryam tace anty shafa'atu wallahi babu soyayya tsakanin Nina da yaya Yaya yana daukana ne kamar yadda yake daukarku Kuma batun saboda da kike magana zaiya yuwuwa zama dana yi agidan nan ne Shafa'atu tayi murmushi ganin yadda maryam duk tabi ta rude Tace shikenan maryam intayi wari maji Amma fa ko ahaka kuka tsaya kin yaki wadan nan matan nasa masu siffar mazan shashai Maryam batace komai ba sai yanzu talura da basa falon Tace ina su antyn suke shafa'atu tayi murmushi tace duk sunyi waje cikin fushi Maryam tace nashiga uku Wallahi bada wata niyar nasa yaya yacanja kaya ba Allah yasa badan haka sukaji haushiba Shafa'atu tayi murmushi tace kai amma kema akwai yarinta sosai maryam agunki Inbahaka ba aikema kinajin maganar nan kinsan saboda abinda kika wanda suyakamata suyi amma basu da tunanin hakan aini kina mugun burgeni shiyasa kikaga na nace miki ina koyan wasu kyawawan halayenkine maryam Maryam dai bataji dadin abinba *** Daddy yakira wayar dagash alokacin yana motane zuwa gida daga airport Dagash cikin murna yace dad yanaga number Nigeria Dad yayi murmushi yace ai ina mota ma zuwa gida nacewa mummynka kartafada maka surprise dinne Kaga yanzu masallaci zanwuce tunda lokacin juma'a yayi saikazo Dagash yaji dadin dawowar daddy sai dai yana adduar Allah yasa kar dadddy yace maryam takoma gida Tunda mamanta tadawo haka kawai yaji yadamu Ana idar da sallah dadddy ya wuce gidansa yasamu an yi komai Dan tarbarshi Mummy tasha kwalliya da lapaya saikace wata balarabiya tayi kyau sosai Hajiya zabbau ma ba laifi tayi kyau da ita saidai batakama kafar uwargida sarautar mata ba mummy an zazzauna sai dai abinda bai wa daddy dadiba shine ba Wanda yatambayi matarshi lalle ba karamin tsana sukawa maryam ba Daddy yadauki waya yakira dagash yace kataho min da 'yata naganta Yakashe wayar su afnan da nazeefa duk suma suna zaune kan dining din ana shirin cin abincin gaba daya Shafa'atu tashigo dawowarta kenan daga gidan Dagash tace la sannu da zuwa daddy ya amsa yauwa shafa'atu tace dady ina anty kobatare kukazoba Daddy yaji dadin tambayar shafa'atu yace tana can nima nazo nadubakune na koma yar albarka Shafa'atu tace Allah sarki antyna barinzo nakirata mugaisa Sallmar dagash yasa kowa yamaida hankalinsa kanshi Tabbas dai dagash ne a fuska amma banda jikin Daddy da mummy suka kalli juna cikin tsananin mamakin son yau shine da manyan kaya Dagash murmushi yayi yaja kujerar gefen daddy da mummy Yazauna shafa'atu dai ta kunshe dariya daman za arina wai ansaci zanin mahaukaciya Shigowar maryam ne cikin falon yasa itama suka maida kallonsu kanta Haka kawai daddy yaga dacewar Dagash da maryam shiyasa yayi wani murmushin manya Dagash yace duk kunsamin ido kufadi abinda yake cikinku mana kafin dad yayi magana Maryam tadurkusa harkasa tanagaida daddy tare da tambayar mamanta Daddy yayi yayi maryam tazauna kan dining taci abinci taredasu taki Shafa'atu ta sauko kasa suka zauna kan carpet Dad yace wai mekefaruwane son you are totally change Tell me the secret my Son Mummy tace ai yanzu al'amarin son abin tsorone Hajiya zabbau tasaka tsalam tace to ai dole yacanza tunda anbashi abinda akabawa mahaifinsa Dad zaiyi magana Dagash yarufe mishi baki Dagash yace daddy aini aganina ba abin mamakibane tunda watanku biyu saudiya kaida mummyna kuna min addua Kunga Dan kundawo kunga canji ai baikamata kuyi mamakiba Daddy yace hakane son nafi kowa murnar kasancewarka a haka my son Dagash yayi murmushi sukayi ido biyu da maryam yasakar mata murmushi ta sunkuyar dakanta kasa *** Aymana da mummynta zaune gaban kasurgumin boka Suna fada mishi matsalar su yakece da dariya yace mekukeso a muku akanshi Mummyn Aymana tace somuke yazama sai abinda tace dashi zaiyi ta mallakeshi kawai tako ta ina ko iyayensa karyaji maganarsu sai namu boka yakece dariya yace angama Zanbaki magani kije kiyi wanka dashi kitabbatar ya kusance ki bayan kinyi wanka da wannan maganin duk yadda zakiyi kiyi ya kusanceki bayan kinyi wankan idan bahakaba akwai matsala Nan sukabada kudi sukayi godiya suka dawo gida Dagash kuwa dayamma yasamu wani kiran gaggawa daga America suna da meeting Ya kalli daddy yamishi bayani daddy yace sai katashi kaje kashirya bara nasa amaka booking kona night flight ne ko Dagash yace ok to dad dama suna lambun gidan ne shida dad dinsa Next page Your comment is needed fans Ina alfahari daku over wallahi Vote & share *Signed by ummu afan* πŸ’» [15/07, 1:09 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑 πŸŽ€ *BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM* *Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI* 🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟 G.W.F🌟 *Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest* I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS SIS DUMMY'S GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN YADDA KIKE YI A GROUP DINKI KEEP IT UP ❀ _🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑 Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH* *PAGE* 4⃣1⃣to4⃣5⃣ DAGASH na isa gida yakira maryam yace tahada mai kaya kala biyar Tace yaya tafiya zakayi yace a tace yau yadaga mata kai kawai yazauna yana dannawa Maryam ta zazzaba mishi kayan tsab tagama komai Yace yauwa good girl tayi murmushi tace to Allah ya kiyaye hanya yace amin nagode baby Sai can kuma kaman me aljanu ya danki kunnanta yace karkifita koina Cikin shagwaba tace wash yaya dazafi yace ai daman zafin nakeson ya miki saboda kar kisaba maganata Yasaketa bayan yagama mata warning Har gurin mota tarakashi Sai alokacin yatuna da mutanen gidan yadauki wayarsa rana tafarko kenan daya taba kiransu Nan da nan ya shaida musu zaiyi tafiya na sati Zasuji alert ta accounts dinsu Aymana da suhaila suka dawo gida Itadai suhaila basu je Ga bokaba Sai munafurci da aka koya mata yadda zatayi ta kori maryam agidan Kwanan dagash uku datafiya Maryam nadakinta bayan tagama komai ta kwanta abinta Dagash yayi diran bazata karfe Tara nadare yadawo Suhaila daman tana gida tace yau can zata kwana Aymana ce kawai tayi murnar dawowarsa ganin zata samu daman aiwatar da aikinta Nan tawage bakin tana mishi sannu da dazuwa bai ki amsawaba ganin Dan sakin fuska sai taji dadi cikin yanga tabishi zuwa part dinsa tana yanga Yana shiga bedroom din shi yafada wanka Aymana tayi saurin dauko swan water a fridge tabude ta wurga desire tablets wato maganin kara karfin sha'awa sosai Wanda idan har mutum yasha maganin tofa idan baisamu maceba Akwai matsala dan sai yayi karamin hauka sosai maganin yanada karfi Dan tasan halin wulakancinsa sai yajuya mata baya yayi baccinsa shiyasa tayi maganinsa da wannan maganin Dagash nafitowa aymana tace sannu

Chapter 12 of 18