nasa ya amince yasa ya hakura shima
Yanzu babban damuwasa shine inda zaici abin buda baki Dan jiya ma da mom tayi tafiyar nan yasha wahala sosai
Daddyn sane yamishi coffee yasha da cake
Danshi bayacin abincin hajiya zabbau bare na nakannanshi wato yaranta kenan
Shiyasa daddy ya je da kanshi yadafa mishi coffee da cake da dambun naman da momy tabar wa daddy yadinga bawa al'amin
Sai kace wani karamin yaro shifa al'amin inabanda wanka da zuwa office da kuma business dinshi bai iya yiwa kanshi komai ba shiyasa da mom dinsa tayi tafiya yakeshan wahala daddy ma yasha
Dan zaice sai daddy yadafa mishi abinci da kanshi tun dady be iya dafa indomie da coffee ba har koya yazama gwani
Dan ko ayanzu mummy tayi tafiya daddy ne yake hidimar al'amin na abinci
In bahakaba bazaici ba
Shiyasa yaji duk hankalinsa yatashi to ga daddyn ma yayi tafiya shima sai gobe zai dawo yazai kenan yau
Zayyad ne yasa al'amin a gaba shida Faisal suna ta dariya
Ya bata rai yace wai Ku Dan uwarku wakuke was dariya haka abin kutausaya min shine zaku min dariya
Sai da mummy tace zata tafi dani naki saboda naga da wadan nan yaran zasu
Dayanzu duk banshiga matsala hakaba
aikuwa wanann maganar ma dayayi dariya suka sake yi Faisal yace yanzu Dan Allah dagash Dan mummy tayi tafiya saitace zata tafi dakai kai Kuma yanzu harda wani Dana sanin rashin binta dakayi
Faisal yace gaskiya shagwaba tamaka yawa dagash ai gwamma da za a daura ma aure da biyu at the same time
Guda daya ai tamaka kadan Dan bazata iya daukan tension dinkaba guy
Zayyd dariya yayi yace wallahi kam tun bayauba na nulura da Dagash ya na da mugun shagwaba
Shagwaba ce tamishi yawa ba wani abuba amma badamuwa kayi lokacin Kane kana ajiye yara ai dole ka hakura ko
Dagash shidai ko kallonsu beba duk damuwarshi yadda za a yi yaci abinci ne in ansha ruwa
Karfe biyar da rabi su Faisal sukace dagash yatashi suje daya daga cikin restaurant dinshi zuci abinci
Dagash yace Sai kundawo zayyad yace to tashi muje gida gurin mum dina musha ruwa acan
Yace kuje kawai fa niba inda zanje kubarni kawai naji da damuwata
Faisal yace wa zayyad mutafi kaji guy rabudashi yunwa ai kanin Dad bane bakuma kanin mom bace ai dole zai nemi abinci dai zaiyi azumi ne yazauna haka
Dagash yaraka su da harara dariya sukayi sutafi abinsu
Bayan anyi sallaar magriba ne dagash yadawo daga masallaci direct falon hajiya zabbau ya wuce abinda bai taba yiba
Suna shan ruwa ita da yan mataan ta suka ga AL'amin kaman daga sama
Rai a hade yace ke nazeeefa zonan baijira amsarta ba yayi waje abinta
Nazeefa ta tashi tabi bayansa
Hajiya zabbau ta kebe baki tace mutum Sai isa saikace shiya haifar min yaran
Sai kace wani ubansu sha sha kawai dan giya
Afanan da kanwarta suka kalli junaa sunsan ummyn tasu akwai cika baki bazata taba cemishi Dan giya agabanshi ko agaban mom dinshiba
Nazeefa tace gani yaya yanuna mata fridge
Basai tafada ba tasan meyake nufi zuwa tayi ta hado mishi fruit su ta kawo ta ajiye mishi
Ta dauko ruwan faro ta ajiye mishi
Tace shekenan hanu ya nuna mata alamun taje
Zamayayi yasha kankana yaci ayaba yaci apple
Amma jiyayi ba inda yake zuwa mishi
Tashi yayi yaje kitchen din mom dinsa
Yafara kalle kalle nan yaga gwan gwan min coffee yadauko ya ajiye yadauko shuga ya ajiye
Ya instruction din yadda ake kunna gas cooker din ya kunna danshi bai taba zuwa kusa da kitchen ba
Bai kiba dai lokacin yana karami amma da wayonsa kam baishigo ba
Ya zuba ruwa cup daya a tukunya yadauko shugar yazuba yafi cokali biyar haka ma coffee din yazuba yafi Rabin gwan gwamin shifa duk adole saisha coffee ya baki sosai ya tafasa yajuye a cup yadauko snacks da danbun nama yafita abinshi yaje dakin shi wanka yafara shiga tukun yagabar da isha kafin yazauna ya nutsu zai sha ruwa aikuwa kurba daya ya zuka da kyau kuwa aikuwa da sauri ya zubar da nabakin nashi saboda wani azaban daci dayaji yace o my God what's this
Yayi saurin shiga bathroom yayi ta brush kaman zai cire bakin
Yadawo ya zauna yana maida numfashi fresh milk ya dauko yaci da danbun naman
Waya ya dauka yayi try din number din dad dinsa not available
Yayi na mom ringin biyu yayi mom tadauka haba nan yafara zuba mata shagwabarshi
Akan yaushe zata dawo ne yagaji fa
****
Fitan su daddy suka dau hanyar abuja suna Bayan mota shida aminin sa driver kuma na gaban mota shi kadai
Sun kusa kaiwa Abuja dai dai wani kauye da akekira da mararraban abuja motar ta lalace abin yabasu mamaki lalle karfen nasara bashida tabbas
Duk irin duba motar nan da akayi amma saida ya lalace musu
Dad din Al'amin yace kagani Dan asabe shiyasa nace maka mubi jirgi amma ka insisting Sai dai mota kaga sharrin mota ko
Alhaji Dan asabe yace aiba wannan bane ma damuwar hadarin da hadu gan ga gashi ba network bare mikira his Excellency ya turo mana helicopter ya karasa damu
Dad din al'amin yace kuma kosun nememu bazasu samu ba tunda gabadaya ma network ya tatsya
Komawa gefen titi sukayi suka tsaya ga wani ga garumin hadari da iska dayake hade gari
Driver ne yace alhaji kuzo muje tacan ga runfa can kufake saboda wannan iskar
Kallon juna sukayi su alhajin
Basu da zabi haka sukabi driver sukayi wajen runfar nan suna zuwa driver yaje yasamu matar dayake tunanin itace mai runfar nan yace mata Dan tayi hakuri su uban gidansa zasu Dan fake
Tace Bakomai bari a dauko musu benci ta kwala wa yarinyar ta kira
*MARYAM MARYAM MARYAM*
Ta amsa na'am anty tace dauko wa baki bencin nan su zauna tace to anty
Nan yarinyar da akakira da maryam ta dauko takawo runfar nan tasa tsumma ta goge sannan tace sannunku da zuwa
Abin mamaki daddyn DAGASH shiyafara amsawa cikin saukin kai yace Yauwa yarinya sannu ko Allah yayi albarka ko tace ameen antynta tasake kiranta akaro na biyu
Tace maza kifara bada kunun nikuma insa hankali na nagama tuyar kosan nan kafin ruwa tsinki
MARYAM tace to anty, ankira magriba Dan haka masu zuwa siyan kunu da kosai suna ta zuwa
Dad din al'amin ya kalli abokainsa yace yanzu yazamuyi ne ansha ruwafa
Alhaji Dan asabe yayi murmushi yace kai su'ad baka wasa da cikinka fa driver yace bissimilla ga ruwan awala
Ganin ruwa sukayi a gwangwamin madara wai a matsayin buta
Bayadda zasuyi haka sukayi alwala sukayi sallah
Bayan sun dawo ne dad din al'amin yakalli driver yace za asamu mota da saika hau mubaka sako kawai zuwa Villa kasanar dashi hallin da muke ciki
Driver yace ai ba mota saidai kozuwa anjima idan ruwan yayi sauki wataki nasamu
Daddy yace OK
alhaji Dan asabe yace abokina gaskiya zansha kunun matar nan Dan na lura suna da tsafta sosai
Daddy yace toya zamuyi ba network ba restaurant me kyau ai dole musha haka
Nan driver yawa matashiyar matar nan wacce bazata wuce shekaru talatin da Biyar ba aduniya
Yace suna bukatar kunu da kosai
Anty tace to ta aika maryam tadauko mata kwanan sha masu murfi acikin Dan dakinsu dake jikin rumfar da alama anan suke rayuwarsu biyun
Tadauko takawo wa antyn tata
Akazubawa su dady cike da tatsafta tabawa driver din yakai musu
Kai mai zafi ta kwashe musu aka kai musu
Daddyn Al'amin da Alhaji Dan asabe sunci sunsha sosai
Mamaki yagama Yakama driver dan baitaba tu nanin wadan nan mutane zasu ci abincin sayarwar talakawa ba
Lalle agaida yunwa yayita dariya a ranshi sosai
Anty tace Maryam kije kish ruwa mana maryam tayi murmushi tace ai kema kinsan bazan iya shan ruwa alhalin kebakishaba Sai dai kitashi muje musha tare tunda kingama soya kosan
Murmushi anty tayi tace maryam kenan Allah miki albarka Allah yarabaki da sharrin duniya
Takarasa tana megoge hawayen da ya zubo mata maryam tace wai anty kullum saikin zubar da hawaye akaina kokina tuna mutuwar nane
Dan Allah kidaina zan ga kaman akwai wani Abu da kike boye min ne
Ta share mata hawayen tace ina alfahari dake mahaifiyata
Bani da kamarki a aduniya mamana kinsadau kar da komai saboda ni insha Allah zaki yi dariya wataran anty na
Murmushi anty tayi tace kinga maryam tashi muje kisha ruwa karmutane su fuskanci wani Abu maryam tace to mamana
Anty tayi murmishi tace bakisaba da fadin maman ba ma shiyasa ba dadi nafison kirani da sunan da kikasamin antyn
MARYAM tayi dariya tace wallahi kam nima bazance maman ba saboda uwata ba tsohuwa bace takarasa maganar tana dauka musu kunu da kosan zasu Shiga cikin dakin langalangar dage jikin rumfar
Jiyo war uwar suka hada ido da daddy gabbanshi yabada dammmmmm
Kyakkyawar mace mace duk tana cikin wahala hakan baihanaka aga zahirin kyau da Allah yamata ba Ashe ba banzaba kanwarta kyakkyawar yarinya Ashe ma gadonsu ce kyau din
anty takau da kallonta daga kallon daddyn al'amin suka wuce cikin dakin nan Dan shan ruwa
Daddy dai yarasa nutsuwarsa tunda ga ganin anty maman MARYAM
MARYAM yarinyace kyakkyawar gaske Dan kyanta yana bawa antynta tsoro Dan antynta ita tasan sharrin kyau aduniya kafin ta haifi maryam batawa kanta adduar samun kyakykyaqar yarinya ba saboda ta hadu da sharri kalala a rayuwarta asakamakon kyan datake dashi
Saikuma Allah bai karbi adduartaba
Yabata maryam wacce harta tama fita kyau sosai
Shiyasa kullum acikin addua da kuka take Allah yakare mata yar'ta
Maryam shekararta shabiyar aduniya yarince mai tausayi dasanin yakamata
Bata taba zama ba hijabi
Yarinya nutsatsiyya
Can dai kusan karfe goma na dare network yadawo aikuwa su daddy sukaji kira yana dubawa kuwa yaga his Excellency ne nan yafada mishi komai
Hi Excellency yace subhanallah
Yanzu zansa azo akaraso daku
Nan daddy kashe wayarshi
Daddy ya kalli driver yace ga matar nan kaman sun kawanta ya za ayi mubasu kudinsu driver yace a haba alhaji ai nabiyata
Daddy yace duk da haka Dan kwankwasa musu kofar dai
Bai musaba ya kwankwasa musu daman idon anty biyu Dan bazata iya bacci ba idan bata ji tafiyar mutanen nan ba karsu cutar da su
Tabude tace sannu bawan Allah
Yace Yauwa daman megida ne yake miki magana tace lafiya aika Riga kabiyani kudina
Jin abinda tace yasa daddyn al'amin yataso yace mungode baiwar bana yawo kudi amma ban account number dinki
Anty tace accounts kuma alhaji ai yariga yabiya karka damu
Ya kalli driver yace jeka cikin brief cake dina kawaso kudin dayake ciki
Haka kuwa akayi yadauko jakar ma gaba daya
Daddy yace Ciro gabasu zatayi magana daddy ya daga mata hanu alamun bayason musu
Tayi shiru kawai tana kallon ikon Allah
Nan gefe kuma wasu hadaddun motocine harda me jiniya
Suka karaso su daddy suka shiga aka wuce dasu sukabar anty da sakin baki tana kallon kudin da suka ajiye musu akasa
Kawashewa tayi takoma ta rufe musu dakin
Tofa
WAI SHIN MEYE LABARIN MARYAM DA MAHAIFIYARTA
Next page fans your comment is needed
Love u much ππ
*SIGNED BY UMMU AFAN* π»
[26/06, 11:52 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
πππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU UMMU FARHAN INA ALFAHARI DAKE OVER WALLAHI ALLAH YABAR ZUMUNCI β€β€β€
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 4β£
Antyn maryam tajuyo dan takoma cikin dakin da kudin a hanunta jiki asanyaye
Sai taga Maryam zaune akan katifarsu
Anty tace maryam bakiyi bacci ba
Maryam tayi murmushi tace anty ai kina tashi na tashi
Anty tayi murmushi tace to barin zauna muyi magana
Anty ta ajiye kudin akan cinyar maryam zatayi magana maryam tace ai naji komai anty
Mungode allah yasaka musu da alkairi yasa Dan Allah sukayi badan sucutar da muba
Anty tace amin maryam
Kirga kudin mugani
Maryam ta kirga kudin nan cas suka ga dubu dari da hamsin
Maryam da anty saida zufa ya jikasu
Dan maganar gaskiya dai ko dubo goma basu taba rikewa ba
Anty tace anya kuwa maryam muatanen nan ba da wani manufa suka bada kudin nan ba
Maryam tace insha Allah allah bazai bari su cutar damuba
Anty tace amin maryam amma duk da haka gobe zamu bar gurim nan mukoma can cikin kyauyen nan musamu wani gida mushiga haya mubiya kudin wata shida
Kinga ko sundawo sutar damu allah bazai basu ikoba kuma bazasu ganmu agun ba
Maryam tace kuma fa hakane anty
Anty tace kinga zaki koma makaranta insha Allah gobe saikije kibiya ko
Kisamu kizana jenior waec dinko
Maryam tace kai anty wallahi naji dadi Allah yacika min burina anty namiki gatan da aduniya zakiyi alfahari dani a matsayin 'Ya
Anty ta janyo ta jikinta ta kwantar da kanta akan cinyar ta tace amin maryam
Allah yakareki da sharrin mutane da aljanu
Maryam tace amin anty
Tace anty yaushe zakibani labarin babana
Anty tace zan baki maryam insha lokaci ya kusa kisan koke wacece
Maryam tace to anty allah ya nuna mana
*****
Daddy dai dasu anty ya kawana a ranshi yakasa bacci saboda tunanin su
Yana mamakin kanshi wai meya damu da matar nan ne
Duk da yasan bawai kyau ne ya rudeshi ba
Dan bazai iya tantance wacce tafi kyau tsakaninta da mom din AL'AMIN ba
Sai anty zata nuna wa mom yarinta
Haka yakwana baiyi bacci ba har washagasuka shiga meeting suka fito
Dagash air line suka tafi
****
*Dubai*
Mom da surakanta ne a wani shagon siyar da kayan mata
Ta nemi guri ta zauna su suke ta zazzaban kayansu
Kaman hauka haka suke daukar kaya
Sai da suka gama mom din AL'AMIN na kallonsu
Akaje gurin biyan kudi akayi lissfa mom din AL'AMIN ta biya suka fita dama yau shine zuwan karshe sungama sayayyar kaf Dan dama kullum sai sunfito siyan kaya
Sun koma masaukinsu mom din Al'amin tashiga bathroom ta Dan watsa ruwa
Aymana kuwa da suhaila a fall suka zube kowacce tana shan kamshi tana ganin tafi yar uwarta
Mummyn Aymana tadawo itama daga nata sayayyar Dan batare suka fita ba
Aymana tace oyoyo mummy tace a Ku harkundawo kenan kunrigani dawowa yau
Suhaila kota daga ido ta kalli mom din Aymana itama bata damu da rashin gaishetan da suhailabatayiba
Taja haunun Aymana sukayi ciki
Suhaila tabisu da harara
Wayarta ta dauka takira mummynta
Tace yau sungama sayyaya zuwa jibi zasu taso
Mummyn suhaila tace masha Allah kindai zabu kaya masu kyau da tsada ko
Suhaila tayi murmushi tace ai mummy nera tayi kuka wallahi kinga tsadaddun kayan da mukazaba
amma haka mummyn Al'amin take biya batare da taji komaiba
Mummyn suhaila tayi dariyan jin dadi tace ai nafada miki su fa tawajen kudi basu da matsala zamu kwashi rabonmu gaskiya
Suhaila tayi murmushi tace aike dai bari mummy ai wani abumma sai anyi auran tukun zamu warke Dan wallahi duk sati sai na tambayeshi kudi
Mummy tayi wani shewa daga wayar tace saiki yar gidana nasan zaki iya allah dai yamiki albarka kuma nasan Al'amin sai yafi sonki Dan irinku ake yayi siraran mata ba irin wanann fan kamar yar'uwartashi ba
Suhaila tayi dariya kanta yasake kato tace se mom dina kina fasamin kai dayawa
Haka sukayita hirarsu saida mom din Al'amin tafito kafin takashe wayar tace sannu da fitowa mummy
Mom din al'amin tace yauwa suhaila tana zama tadauki wayarta takira Dagash
Itakuwa suhaila mom tazuba wa ido gaskiya mom akwai kyau ga tsafta bata yarda kazanta Sam
Ba banza al'amin yabiyo tsaftarta
*****
DAGASH yana cikin ruwa sweemingful na gidansu la'asar ce sakaliya yafito daga wajen training kenan yafada ruwa Dan yayi wanka
Yau ne su mom din shi zasu dawo
Yana cikin wankanshi a ruwa security dinsa ya matso yace sir ana kiran phone naka
Dagash yace sunan
Security din yace lovely yace bani yafito daga ruwan ya karbi wayar yace mom ko kunyi landing ne
Mom tace a a amma nan 15 minutes we will be there insha allah
Yace OK on my zanzo na daukoki tace that's my son sai nazo to i miss u son
Yace me too mom shiyasa nagaji da gidan babu ke tace
Don't worry son yanzu zakaga mummy
Nan suka kashe wayar baikoma ruwan kawai part dinsa yawuce yaje yashirya cikin wasu balain kaya Jim's ne dark blue sai kuma T shirt dinsa light blue sai ya dauki farin glass yasaka
Ba abinda ketashi ajikinsa sai kamshin turarruka masu tsada yadauki wayoyinsa da wallet dinshi yayi waje
Direct wurin motocinsa ya wuce yakai kallonsa ga gabadaya motocin dasuke wajen
Yazabi wata hadaddiyar homer jeeep mai matukar kyau da daukar ido
Shima jeep dark blue ne gaskiya duk wanda yakalli dagash cikin motar nan yasan Sundance da juna
Yana isa DAGASH AIRPORT girgin su mummy na sauka ma'aikatan wurin suka taso sukazo suka bude mishi kofa
Suka Sara mishi dayan yace sir ai dabaka zo dakanka ba munta nadi motar da za akai su hajiya har gida
Dagash yace akwai wadan zaku tafi dasu ai Ku kawo matar nan
Suka bi umarnin ubangidan nasu shikuma jirgin nagama sauka motanen ciki suka fara fitowa
Idonshi akai ya hango suhaila a gaba mom abaya
Suhaila tayi shiga cikin Riga da wondo kamar yadda tasaba sai Dan karamin mayafin data yafa akanta ga uban dogon takalmi itakuwa Aymana dogowar Riga tasa tayi rolling dashi saboda gimbiya ce
Dagash cikin missing din mom dinsa yakara ya rumgume mom dinsa yana mata welcome itama taji dadin ganin shi
Sai dai tace meyasameka son ka rame yace badole na rame ba mom kin San dad ba abinda ya iya dafawa sai indomie shinayi ta ci kinga kuwa ai dole na rame nasaba abincin mom na
Yakarasa maganar yana murmushi mom ta shafa kumatunsa tace kuma ga azumi ko
Yace wallahi tace ai balefina bane sayyayar matanka najeyi
Sai alokacin yakai kallonsa ga mom din Aymana yace oh mom harda ke akatafi
Abin yaba mom din Aymana mamaki tace au dama bakasan tare mukaje ba
Yace naman ta yakk irin gaisuwarsa kenan yawanci
Cike da mamaki mom din Aymana tace lafiya kunya yakamata da irin gaisuwar da al'amin yamata
Suhaila kuwa dady abin yamata
Mom dinsa kuwa dama ita yar baruwankace
Aymana tace yaya ina wuni
Ya kalleta ya watsa mata wani kallon rainin hankali
Ganin haka yasa suhaila kama bakinta
Can kuma ya kalli suhaila ya ce kekuma kinfi karfin gaisuwar ne
Jiki na bari tace am sorry doctor munsame Ku lafiya wani wawan kallo yamata baice komai ba Yakama hanun mummynsa data keta faman waya da daddy yace less go mummy
Ya kira security yace yakarbi jakan mom din Aymana sutafi
Dagash ya kalleta yace to mummy sai anjima kigaida da dady king sai na shigo
Yaja hanun mummy sukatafi mummy tace to hajiya sai munyi waya ko
Mummyn Aymana tace OK by
Takaici Yakama suhaila saida tafaki idon su Aymana ta goge guntun hawayen wulakancin da dagash yayi musu wai damma ba ita kadai ya wulakantaba bare sumata dariya
Dagash suna isa gida ana kiran magriba mummy tace zanyi sallah kafin kadawo daga mosque zan dafa mana abinci maisauki
Yace that's my mom yabata fek a kumatu yayi waje
Tayi sallahi kafin tafito zuwa kitchen duk da gajiyar datake tare dashi hakan baihanata son faranta wa danta raiba
Couscous tayi da miya shaf shaf miyar amma za aiya cewa ta kazace Dan naman yafi yawa nan takwashe komai tafito dashi falon alokacin Al'amin yana shan kankana yana ganin mummy yace kai mummy tunkafin naci kamshin ya kosar dani mom tace aikuwa baka isaba
Sai kacinye komai Dana maka yayi dariya yace ai wasa manake miki
Ba abinda zanbari a abincin nan
Mom tayi dariya tace kaman gaske
Dagash na cikin cin abinci kona ce mummy na feeding nashi dad yashigo yace a a son rigima ya kareko mom tadawo
Murmushi mom tayi tace ai son badama
Al'amin yace dad wallahi harnaji nadawo mutum haba ai nasha wahala kwana biyu
Yadda al'amin yake zuba wa iyayenshi shagwaba kai zaka dauka Dan shekara biyar ne
***
Bayan kwana biyu da dawowar su mummy da daddare mummy tayi shirin kwanciya ranar kwanantane taga daddy yazuba wa guri daya ido yana kallo
Tace Alhaji wai mekefaruwa da Kaine tunda nadawo na lura akwai wani Abu akasa wanda yake damunka kakasa fada min
Shere your problems with me mana haba sweet heart
Murmushi dad yayi yace matata kema kinsan da akwai wani Abu bazan boye miki ba zo ki kwanta dare yayi yajanyo ta suka kwanta
Mom dai taji shine amma bata amince bakomaiba Dan bata taba ganin shi cikin damuwa hakaba amma zatayi kokari tasan komenene
****
Alhaji su'ad zaune shida alhaji Dan asabe suna tattaunawa kan matsalar data damu alhajin
Alhaji Dan asabe yace anya kuwa abokina ba gamo kayiba kayi sanyi lokaci daya akan talakawa da basu da wani gata a rayuwarsu duk kabi kadamu kanka akansu
Wai tsaya ma meyaja hankalinka har kafada son yarinyar nan Dan yarinya zankirata Dan munhaifi wadan da sukafita
Alhaji su'ad yace wallahi nima bansaniba kawai nasan nakamu da matar nan sosai kuwa
Alhaji Dan asabe yace to sonawa muna komawa taki sauraronmu itafa gani take ma zamu cutar da ita da yarinyar tane
Dan Allah kabar maganan matar nan idan auran kakebukata wayayyo gasunan kanema mana
Dad din al'amin yayi murmushi yace kodaya banida ra'ayi wasu matan Bayan wannan baiwar Allahn
Kawai bani wani shawarar amma banda na inrabuda ita bazai yiwuba I can't please
Alhaji Dan asabe yace ok nafahimceka abokina yanzu dai kagani munje kauyen nan yafi sau biyar
Taki bamu hadin kai ganitake cutar dasu zamuyi
Saboda haka mubi komai a sannu mubari ayi auran yaran nan sai musake komawa muje mata da kokon barar mu
Alhaji su'ad yayi murmushi yace yauwa abokina yanzu naji magana amma zakace narabu da ita
Wallahi ko bacci bana iyawa yakai ma har matana sunfara gane ina da matsala
Alhaji Dan asabe yayi murmushi yace gaskiya ka kamu dayawa abokina amma dai kasan waje zaka kaita a polishing dinta ko yafada da tsokana
Dad din yace babban burina ma dai ta amince da bukatuna sunfi min komai
Alhaji Dan asabe yace to wai yazakayi da matanka Alhaji su'ad yayi murmushi yace duk bazamana sukeyi ba dole sukarbi abinda nazo musu dashi
Alhaji Dan asabe yace se namijin duniya wallahi ina son nakoyi jarumta irin taka abokina kwata kwata baka shakkan mata
Nima fa wallahi ina da bukatar karin auran nan amma bana son fitina shiyasa kawai nabar komai
Dad din Al'amin yace lafinkane tunfarko abokina
Alhaji Dan asabe yace hakane kam
*****
Yau take sallah Doctor al'amin dagash na hango cikin wata shadda ash colour dark tunda daga kan shaddar zuwa dinkin bakina da hanuna bazai iya fayyacewaba amma komai na Al'amin daban ne kawai
Ya kalli kanshi a madubi yaga shikanshi yasan kayan sunkarbi jikinshi sosai
amma shidai bazai iya cigaba da amfanida manyan kayaba shi aganinsa takurace kawai bawani abuba
Faisal da zayyad sukashigo suma cikin shaddodi na alfarma duk sunyi kyau
Zayyda da Faisal kusan atare suka hada baki wajen ihun ganin dagash
Harda babbar Riga sosai sukayi mamaki zayyad anya mutumina Kaine kuwa ai yau kafito a Prince din naka sosai
Al'amin ya watsa musu harara yace muna fukai wallahi wannan ma da kuke gani aikin dadine
Shiya bata kudinsa aka yi amma sanin kankune bazan sake amfani dasuba
Faisal yaceaikuwa dakaga yadda suka maka kyau da kacigaba amsawa
Zayyad yace kana bata bakinka ne fa Dan tunda yace basawar zaiba bazai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 18