yaya nan ma ya amsa mata yashirya cikin kayan bacci
Zai kwanta aymana tace dauki robar ruwan ta siyaya mishi tace Ga ruwa yaya
Yakarba Dan yana bukatar ruwan sanyi sosai yasha har yabata kofin takara mai
Tace barinje nayi wanka nadawo
Baice mata komaiba saboda wani bacci dayakeji Ga gajiyar daya kwaso nan da nan bacci yadaukeshi
Aymana ba inda bata duba ba amma ba maganin data karbo daga gidan boka
Hankalin aymana yatashi tadauki waya takira mummy dinta amma bai shigaba
Tace aikuwa yazama dole naje gida yanzu inbahakaba ai akwai matsala
Ta tashi tadauki key din motarta Dan taje gidan
Tadauko tana da tabbacin a jakar mummy tabari
Taduba agogo karfe goma na dare
Megadi ma saidaya tambayeta hajiya lafiya kuwa
Ta harareshi tace bansaniba
Tayi waje abinta fuuuuu gudu take sosai
Tana danyi nisa kuwa yansanda suka tareta
Dagash cikin dare yaji kaman ana mintsinin sa yatashi aikuwa ba abinda yake bukata sai matanshi
Mika yayi sosai yatashi kaman wani mahaukaci yayi dakin aymana amma bata nan yayi dakin suhaila itakam ma a kulle a lamun bata nan
Yadauki wayarsa yakira Vicky ina itama wai bata dawoba daman dazai tafi America itama suka wuce Lagos da saurayinta
Ina hankalinsa yafara barin jikinsa idan baibiya bukatarsaba zai iya hauka
Tashi yayi cikin tashin hankali yanufi dakin maryam
Ya na shiga ya kunna hasken dakin maryam yaganta kunce da alamun tana jin dadin baccinta sosai
Yace kiyi hakuri baby I can't control my self
Komawa dakinsa yayi fesa turaren dayake da tabbacin maryam bata sanshi da wannan turaren ba
Yafito jiki narawa ya turo kofar dakin maryam yasake kunnan wuta da alamu akwai abinda yake nema can yaga dankwalinta
Yayi saurin dauka ya kashe wutar dakin gaba daya duhu sosai ba yadda za ayi kaga Wanda kedakin
Ya haugadon yasa Dan kwalin dai dai bakin maryam ya daure
Jin ana daure mata baki kaman a mafarki yasa tabude ido ba ba halin ihu
Sosai sukafara fada da maryam
Sai dai ina karfi badayaba nan da nan yasamu daman cire mata komai najikin ta
Jikinshi na rawa saboda bakon al'amarin dabai taba tsintar kanshi aciki ba
Maryam tun tana kuka tana yakarsa da hanunta yasamu ma yadamke hanunta
Allah yabashi ikon maida maryam babbar mace wani ihu tasa wanda baya fita
Tashidaya kuma tayi shiru Ashe suma tayi shikuwa dagash ina baisan abinda kefaruwaba saboda yafita a hayyacinsa akan ni'imar da Allah ya hurewa maryam
Saida hankalinsa yadawo jikin sa jin bata motsi yasa hankalisa yatashi Dan ya tabbatar ba numfashi ajikinta
Yace nashiga uku nakashe musu yar mutane
Dasauri yadauko ruwa yayyafa mata aikuwa ta farfado dawani mahaukacin ihu tana kuka mai cinrai
Yaso ya taimaka mata amma ba halin hakan haka yayi saurin komawa part dinsa
Yana shiga bedroom dinsa hasken dakin shi ya haska kashi ganin jini ajikinsa yace oh my God baby kiyafemin
Yakama ta nakasance dake a wannan lokaci amma hakan bazai yuwu ba saboda bazaso kisan Nina keta miki budurcinkiba
Wai meyasameshi meyasa ya aikata wa innocent girl haka wannan aikin
Shiba giya yashaba balle yace a buge yaje dasanin sa yaje gareta
Sosai ya damu akan abinda ya aikata wa maryam ko a wani hali take oho
Allah yabaki lafiya baby na Allah yamiki albarka kiyafemin
I can't control my self that's why
Wurin fridge yanufa danufin daukar ruwa daga can gefe yaga gidan magani yadauka kuwa yagani
Tabbas wannan maganin Aymana tasamishi a ruwa
Da badan bayason asiranshi ya tonu ba da zata raina kanta sai ya wulakanta mishi rayuwa
To waima meye asalin dalilin daya sa tasamishi wannan abun bayan tasan bazama zatayi agidan ba
Yace Allah ya isa tsakanina dake Aymana dole zan miki hukunci dai dai da abinda kikasa na aikata wa yar mutane
Shiryawa yayi cikin daren yabar gidan gidanshi na G R A yatafi yaje ya kwanta amma bacci ya gagareshi sosai yake tunanin kasancewar shi da maryam
Jiyayi kaman duk su aymana su suhaila harma da Vicky duk yaji azuciyarshi cewan kaman da maza yakasance kwatata bawacce ta kamo kafar maryam
Ashe manyan matan ma suna sukatara baiwa da ni'ima yana tare da babyn sa
****
Maryam kuwa tayi kuka kaman ranta zaifita ajikinta taga mummunar kaddara
Ancuceta acuci rayuwarta yanzu mezatacewa antynta mezatace wa yayan ta
Sai da akaga ba yayanta za shigo mata cikin dare
Tace ya Allah kadauki raina kar antyna taga wannan mummunar kaddarar daya afka mata
Idonta ya kumbura sosai gashi ta kasa tashi duk yadda takai tamotsa azaba ne yake damunta
Dakyar dai ta tashi tayi wanka tagyara jikinta amma fa zazzabi mezafi yarufeta amma haka tayi saurin cire bedsheet din gadon Dan ya baci takai bathroom haka wanke dakyar Dan gudun tunuwar asirinta idan tabarshi yasa ta lallba ta wanke
Ko shimfida wani batayiba haka ta kwanta taja bargo harkanta tana rawar sanyin
Sosai zazzabi ya cafketa har asuba idonta biyu dakyar ta tashi tayi sallah takoma gado bacci mekarfi ya dauketa
Washagari
****
Shafa'atu na tashiryawa abinta Dan tana son zuwa gidan yayan nata wajen maryam
Hajiya zabbau tace shasha kawai kedai kullum a hanyar zuwa gurin wannan matsiyaciyar yarinyar nan
Nazeefa tace ai su riga sunshenyeta sai dai addua kuma
Afnan tace ai wallahi kekam shafa'atu kinji jiki kullum kina hanyar zuwa wajen Mara kunyar yarinyar nan ita ba komaiba sai girmankai
Shafa'atu ta kalli afnan a yamutse tace kingama to naji zanje ina ruwanku danine
Konima zaku hanani ne 'yan rainin hankali kawai
Hajiya zabbau tadau salati tace shafa'atu saboda sunfadi gaskiya shine kikeson kimusu rashin kunya
Shafa'atu batace komai ba tayi waje abinta tana isa gidan taga bakowa a falon direct dakin maryam ta wuce
Tana shiga taga maryam kwance cikin bargo dasauri takarasa ta yaye bargon aikuwa ta razana da jin jikin maryam zafi rau
Cikin rudewa shafa'atu tace meyasa meki haka maryam
Ina ba baki sai hawaye kawai kefita daga idon maryam
Shafa'atu ta tashi tace barin taimaka miki mutafi asibiti
Maryam tace a a kibarni kawai anty bana son asibiti
Shafa'atu tace yazakice bazakije asibiti ba bayan jikin ki yayi zafi sosai
maryam dai taki tafiya asibiti
Shafa'atu ta tashi tashiga cikin bathroom tahada mata ruwan wanka
Ta taima kamata aikuwa maryam tana sakafa akansa tanafara tayi wani ihu sosai saboda azaba
Shafa'atu ta rikice tace sannu maryam ko kafarce take ciwo sosai haka maryam tace jiyane nazame a bandaki
Shafa'atu tace or sorry kinji daure kitashi dakyar shafa'atu ta kamata zuwa bathroom din kafin tadawo ta shimfida mata bedsheet
Ta dafa mata indomie da ruwan tea
Maryam tashirya cikin doguwar Riga amma fa saida shafa'atu tayi ta matsa mata sannan tadansha tea din da abincin
Tabata maganin zazzabi data aiki driver yasiyo
Tasha itakanta tadanji dadin jikin ta sosai
Sai dai kuma hakan baisa maryam tadaina zubda hawaye ba
Shafa'atu tace wai maryam bazaki daina kukan nan ba ko
*
Aymana kuwa bayan tadawo bata tarar dagash agidan ba tadauki waya takirashi
Yadaga yace mata yana airport ne
Cikin rudewa aymana tace kakoma kuma
Yace daman ai Abu kawai zandauka already nayi buking fly daman so sai nan da two weeks zan dawo yakashe wayarshi rana tafarko da al'amin ya dauro alwala yaraya wannan dare da salloli da istigifari
Aymana haukane kawai batayiba saboda tariga tayi wankan maganin tun agidansu
Yanzu shikenan sunyi asarar kudinsu kudi sosai suka narka kafin akabasu maganin
Shikuwa dagash wayoyinsa yakashe gaba daya saboda bayason adameshi
Haka shafa'atu tazauna da maryam tana jinyarta sosai maryam taji dadin zaman shafa'atu da ita
Sati biyu da faruwar hakan maryam ta warke sosai sai dai damuwa da rashin sakewa Ga wani uban rama datayi tasake haske sosai tayi kara kyau saidai rashin walwala
Su rahama da fareeda ne sukazo tunsafe ana hira amma banda maryam daga murmushi sai kallo take binsu dashi fareeda tace maryam duk kinyi sanyi ina bakin ne
Rahama tayi murmushi tace daman nasan za arina tu da yayanta yayi tafiya takoma kurma
Shafa'atu dake jinsu tace nima nalura da maryam anya baciwon son yayana bane
Rahama tace yauwa anty shafa'atu Ashe kingane
Fareeda ta kalli maryam kallon tuhuma
Tace menakeji maryam Allah yasadai badagaske ba ne abinda nakeji
Maryam batasan lokacin data fashe kuka meciwo tayi dakinta
Suka kalli juna gabadayansu
Next page
Your comments is needed fan's
*Signed by ummu afan*π»
[15/07, 1:12 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO MAMAN IBTISAN GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
Comment harda read more π€much love to your love and care
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 5β£1β£to5β£5β£
hajiya zabbau cikin tashin hankali ta nufi dakinta ta dau waya takira mummyn Aymana tace kunsan kuwa abinda kefaruwa
Mummyn Aymana tace a a saikin fada
Nan hajiya zabbau takwashe duk abinda yafaru tafada mata
ai kuwa mummyn Aymana tayi wani wawan ihu tace karya sukeyi wallahi
Auren nan bazai taba yuwuwa ba yaranmu suzama shara kenan agidan mijinsu to bazaiyi yuwuba
Mummyn Aymana tace hajiya zabbau dan kizo kisameni muwuce gidan malam yanzu nan
Hajiya zabbau tace ganinan zuwa yanzu kuwa wallahi nima ina bayanku
**
Maryam ce durkushe kan gwiwarta tana kuka tace anty dan Allah kiyi hakuri
Nabata miki rai
Anty tayi murmushin dole ta taso dago maryam suka zauna kan bed tace maryam baki min laifi
Marin Dana miki ma nayi ne saboda raina yabaci amma bawai dan kinmin komai ba
Maryam tace anty dan Allah karkibari a aura min yaya wallahi bana sonshi bazan iya auranshiba
Anty tace to maryam yazanyi kinga yadda alhaji yamana hallaci ba yadda za ayi nayi jayayya dashi
Nima ba ason raina hakan zata faruba kodan mummynshi yadda take nuna tsanarta akanmu bazanso hada jini da ita ba
Cikin kuka maryam tace yanzu anty kema kin amince kenan anty tace kema yakamata kiduba girman hallacin da alhaji yamana karkibashi kunya
Cikin kuka maryam ta tashi tayi dakinta
Tafada gado ita babban damuwarta ma
Yadda yayan nata zai sameta ba cikakkiyar maceba
Ansha fada musu a islamiya akan budurci yadda maza suke matukar daraja mace saboda shi
To ita yazatayi ta iya auran yayan mezatace mishi
Zai dauka ma asali ita yar iskace kukanta ya tsananta sosai
Ta ga dai kukan bazai fishshetaba tadauro auwala tafara nafilfili
***
Mummyn dagash zaune kan sallaya abin duniya yabi duk yadameta
Wayartace yafara ringing tana dauka taga alhaji imam ne cikin sanyi jiki ta amsa wayar
Yace a a Aisha yanaji muryarki haka mummy zuciyarta takasa rike damuwarta kawai sai ta fashe da kuka
Nan hankalin alhaji imam yatashi yace tayi shiru tamishi bayani
Tama rasa mezatace mishi
Kawai sai tace ba wani abubane yasata kuka illa halin dayakeciki
Alhaji imam yasauke ajiyar zuciya yace Aisha kicigaba datayani da adduarki insha Allah inajin nasara ajiki na
Mummy tace addua ai kullum cikin yimaka nake saboda yanzu hakama kan abinsallah nake inata muku addua
Yace kanwata Allah yamiki albarka kema ya kareki daga sharrin makiya
Tace amin yaya tace yaya kace zakazo bakazoba
Kuma naga lokaci nafiya saikasa lokaci kuma kaki zuwa
Yace zanzo insha Allah nan sati biyu Aisha daga yanzu bazan sake dagawaba da izinin Allah inaji ajikina nakusa haduwa da farincikina
Mummy tace Allah yasa yaya wallahi Dana fi kowa farinciki
Nan dai sukayi sallama
Mummy ta sauke ajiyar zuciya itadai tasan koda yayanta zaisamu yarinyar dayake fada to tayi aure kuma tabbas zaishiga matsalar datafi nayanzu
To wai mashin meya hadasu da har yake nemanta haka Allah dai yasaukaka al'amarin
*****
Aymana durkushe kan gwiwarta tana kuka kaman Allah ya aiko ta tana dan Allah mummy karbari yaya ya auri wannan aljanar yarinyar wallahi zai iya korummu agidan saboda ita
Mummyn Aymana hankalinta yatashi ganin yarlelenta nakuka haka
Tace kwantar da hankalinki basu isaba yanzu zamuje wurin malam musake mishi kudi yamana aiki kawai akansu gaba daya
Suhaila ma haka ta yita tayar wa mummynsu da hankali sosai mummyn tashiga damuwa sai dai ita bata iya zuwa wurin malamaiba
Kawai dai ta iya kirsa da munafurci kalala dan haka ta zaunar da suhaila suka shiga kulla wa da kwancewa
Dagash zaune a office dinsa yana ta kiran wayar maryam taki picking
Zayyad ne ya kura mishi ido
Dagash yace kaikuma lafiya da kallo haka
Zayyad yace ai kallo dole a kalleka saboda you are totally change yau Kaine da mace kana kira tana rejecting kanasake kiranta gaskiya maryam tayi a rayuwa
Dagash yamaka mishi harara yace ai saitafada min dalilin dayasa take rejecting call dina
Zayyad yafashe da dariya yace daga baya kenan
Faisal yashigo yakalli zayyad yace kaikuma wannan dariya haka saikace rahama tayi kira
Zayyad yace mutuminkane kawai yake raina mana hankali yafada soyayya kuma yanaso yayi mata iko
Faisal ya kalli Dagash yace wayafada maka zaka mata yadda kakeso
Dagash yace duk da ina son ta bazan dauki raini bazan canja daga Al'amin da kukasaniba
Faisal yace na nawa kuma ai tafaru takare wai anyi wa me dami daya sata
Dagash yace zanbaku mamaki zayyad nawa kuma kaidai ai sha'ani kaji
Faisal yace nima fa ma antambayo min kuma anbani shafa'atu nan da two weeks din dady na yaroka a hada dana Dagash
Zayyad yace a haba dai nizakubari a baya ai kuwa nima yau zankai maganata gurin daddy zakusha mamaki
Dagash ya kalli Faisal yace kaikuma saboda raini shine zaku hada kanku dani ko
Faisal yace afuwan babban yaya amma fa da anason girma kaman ka zayyad ma Yakama ta yafara Jan girmanshi a gurinka
Dagash yace kuma fa hakane babban wa ko to babban yaya aje akai maganar gaban manya saboda asamu ashiga daga ciki
Zayyad da Faisal suka kwashe da dariya
Zayyad yace dayake basabawa kayi da biyayyar ba ma bata dace dakaiba
Dagash yayi murmushi yana juyi kan kujerar shi
****
Mummyn Aymana da hajiya zabbau zaune gaban boka ne ko malam suke ce mishi su sukasani
Dariya yayi aikinsu amma sai an aiki aljanu birinin sin
Za atura wa alhaji aljanar dazata shiga jikinsa yaji bayason duk wani Wanda yashafi amaryarsa bare kuma har yasake tunanin aurawa Dagash maryam
Murna sosai sukayi suka zuba makudan kudade sukayi gaba
Hajiya zabbau tace zata dawo kuma amata aiki kan mummyn Al'amin a tsaneta agidan
***
Antyn maryam tana zaune itada Lil Al'amin a falo yana cinyarta
Maryam kuma na kitchen tana daura abinci daddy yakira wayar anty tasameshi a dakinsa
Anty tana zuwa daddy yataso yakarbi lil Al'amin itakuma ya riko hanunta suka karasa ciki
Yace daman maganar bikin nan angama da maganar kayan daki companyn mu dake Singapore nabasu order na komai
Nakiraki ne muyi maganar abinda kike bukata keda yarinyata maryam nagame da hidiman biki
Tunfitowar anty hajiya zabbau ke labe a bayan ta tana musu labe
Taso taji sabanin abinda kunnuwanta sukeji a yanzu
ai kuwa takado dakin irin hidaman da Daddy ya anty da Maryam sosai kishi yakamata
Itama ai auran yarinya zatayi meyasa baimata hakan ba
Sun shiga uku idan dai maganin nan baici alhajiba dasake
**
Bayan fitan anty zuwadakin daddy Maryam tana kitchen tana hada milkshake dinta dan kullum tagama abinci saita hada tasha tanason abin sosai
Haka kawai jikin yabata da mutum a kitchen din nan sakama kon kamshin turaren daya daki hancinta yasa ta saurin juyowa
Tarazana fuskar nashi dan yau kam a Prince Al'amin yazo mata
Cikin in ina tace sannu da shigowa yaya yamaka mata banzan kallo yace meye dalilin dayasa nake kiranki kike rejecting call dina
Maryam ta turo baki Cikin shagwaba tace bakomai yaya kainane yake ciwo yace oh really zo naji naga bakin karyar
Ya matso tamatsa yakamo kunnenta yace nizakiyiwa karya ko cikin kukan shagwabar dayake rikita dagash tace yaya dazafi fa yace ai zafin nakeson kiji
Dakyar tasamu yasaketa yace kikawo min abinci ina falon anty
Yana fita maryam tace kai wannan mutum akwai issa saikace dashi tadafa abincin
Ya zauna kan kujerun falonsu maryam rana ta farko kenan daya taba zama a falon yanayin tsabtar gurin a burgeshi sosai
Mummyn shi tana da tsabta sosai sai dai ita yan aiki take sawa sugyra mata koina bata son datti kokadan shiyasa ma yayi gadonta
To yaga wadanda dakansu ma suke komai kaman basu San wahalar jikinsu ba
Shidai gaskiya idan ya auri maryam girki kawai za ta mishi aiki kuwa zai sa adebo mata yan aiki ta huta kawai bayason ta wahala
Maryam ce ta kawo abincin a tiren ta ajiye
Yadaga ido ya kalleta yaga tazaro wani katon hijabi
Dafe kai yayi yace oh my God
Baby bana ce miki banason kidinga sakamin hijabi bane baikisan nan da kwana bakwai kina gidana bane
Tobanso tashi kicire kizo serving dina abinci am hungry
Maryam zatayi magana yadaga mata hanu
Ta turo baki tacire hijabin ai kuwa yatsareta da kallo tsaf
Ta tsargu hartasa abincin baisaniba tace ga abincin
Yace kefa tace niba yanzu ba yace nikuma nace yanzu zakici tace dan Allah karka sank dole yaya milkshake kawai zansha
Yace nima kinzuba min tace zakashane ka iya sha kuwa
Yace mezaihana idan dai kema kinsha tace shikenan tacika mishi cup
Bissimilla yayi yafara cikin hadaddiyar jalouf rice Wanda yasha kayan lambu da nama sosai acikinta
Sosai yake jin dadin abincin
Tace baka tambayi lil dinkaba yace ai nasan inda yake
Maryam tace au Ashe kaganshi kenan yace yana gurin daddy
Maryam tayi murmushi tace haba ai shiyasa naga kasake mana ashe kasan anty bata nan
Dagash yayi murmushi metsada yace waya fada miki inajin kunyar anty
Maryam yayi murmushi tace hummmm
Yace baki yaddaba ko zanbaki mamaki to
Yakurbi milkshake din yaji dadi har kunnenshi yace wai dame dame ake wannan abun da har kike son yimin rowarsa
Maryam tayi murmushi kawai batare datace komai ba tadauko pillow daya tasa a bayanshi
Dagash yayi murmushi yana enjoying moment din sosai jiyake kaman karsu rabu inama da aransu da zai kasance da Maryam a haka bazai gaji ba
Yace baby maganar lefenki ba
Sai yaga tabata rai sosai ta turo baki
Dagash yace wai mekike nufine idan namiki maganar aure sai kibata rai tace yaya nifa wallahi tsoro nakeji gabana yana faduwa
Ba lalle ka iya zama daniba idan har Kasan abinda kedamuna
Dagash ya kura mata ido yasan abunda take nufi zurfi cikin yahanata tayi magana yaso tayi magana ne yanuna mata shi zai aureta a yanasonta a haka
Amma taki fada mishi komai sai dai kawai tayi ta kaucewa
****
Abu ya gagara fa wa manyan mata da sunki saka mummyn zayyad aciki saboda kartasan abinda suke ciki
Ita mummyn Aymana tana son su kwace gidan ne itakuma hajiya zabbau tana son anty tabar musu gidan
amma abin yaki ci yaki cinyewa
Sai kawai suka nufi gidan alhaji dan asabe suka mummyn suhaila suka zauna suna mayar matada komai
Mummyn suhaila tace au kuda kuna ta kona ta kona kudinku gurin malaman karyar nan ne aikin banza
Tace ai wannan aiki sai kirsa da hada tuggu
Hajiya zabbau tace kaman yaya kenan hajiya
Nan mummyn zayyad tashiga tsara musu yadda zasuyi kuma hajiya zabbau ita zata musu wannan hadin da suka kulla
Akan wai tasamu wani katon tabiyashi yaje dakin anty idan dai daici daddy zaishiga
Sai yayi kaman shi kwarton antyne yasaba zuwa ma
Hajiya zabbau da mummyn Aymana suka yi shewa sukace lalle hajiya kinsan kan duniya
Tace a to mudun wasane
Nagidana ma tarata nakeyi rana daya alhaji zaiyi waje da ita wallahi
Daga ita har agolarta mummyn alyamana tace mutane sunzo duk suna son hana mu jin dadi rayuwa
Mummyn zayyad tace ai barni dasu shi wannan dan ma kallonshi nakeyi wallahi indai ina raye bazai taba auran yarinyar nan rahama take kowa ba
Itama inan ina Neman hanyar dazan kulla musu kulleliya subar min gidan kowa ya tsanesu
Nan dai suka rabu cikin farinci kaman sun samu biyan bukata
***
LIBIYA
ALHAJI IMAM zaune a katafaren office dinsa yayin da abokinshi alhaji sudaise yake ta faman yimashi nasiha akan ya hakura kawai yayi aurenshi ya tabbatar idan yayi aure zai rage mishi radadin abinda ke damunsa
Alhaji imam yadago da kanshi yakalli yakalli aminin nasa yace sudais bazaka gane abinda zuciya ta yakeciki ba
Tunda nake bantaba fadawa wa wani wannan sirrin ba sai kai yau zanfada maka koda zuciya ta zai dan damama
Alhaji sudais yace ina sauraronka
Alhaji imam yace idan bazaka mataba nataba tafiya Nigeria wani aiki na tsawan shekara biyu ko
Yace kwarai kuwa
Nan da nan alhaji imam yakwashe labarin komai yafada mishi
Alhaji sudais yace innalillahi wainnanirirairaju'un ya mai mauta sau uku
Alhaji imam yace abinda yasa sauran bandamu dasuba su dasaninsu hakan tafaru sakamakon kwadayin kudi dasuke yi
Kuma dukansu ba budurwa acikinsu kaga sunsaba da rayuwar ma kenan
Amma ita wannan yarinyar maryam yarinyace sosai dan bazata wuce shekaru shatakwas ba aduniya kuma kamila ce sosai dan ganin danayi mata cikin hijabinta naganta
Nasa yarana suka dauko min ita na aureta da karfi naso a washagarin auran nasaketa ta tafi sai dai ina naji ba irin mace da ake saka lokaci dayabane
Sai nabarta tare dani harna sati
Sakamakon kiran da akamin jikin hajiyarmu yatashi shine nasaketa nasa suka maida ita garinsu
Tunda daga kan yarinyar nan har yau bani da nutsuwa bani da kwanciyar hankali
Allah ya jarrabeni da matsanancin sonta a raina kuma a yadda nake gani idan har bansamu maryam bazan taba aureba har abada a rayuwata kuma haka zan mutu da son maryam a zuciyata
Alhaji sudais yarasa bakin maganane yayi shiru yace na tausaya yarinyar nan sosai
To yanzu baka sake komawa ba tunda kasan garinsu
Alhaji imam yace naje garin nami labarin ance ai mahaifinta yabar garin gabadaya da iyalansa sunko cikin garin medugiri
Alhaji sudais yace ya ilahi Allah ka kawo mana taimako
Hawaye ne suka karasa saukowa daga idon alhaji imam yace kataimaka min sudais narasa yadda zanyi wallahi kwalwata yatoshe
Gashi hajiyarmu da yaya nura suna tunanin wai ko bani da lafiyar yin aure ne dasunsan abinda na aikata da sunyi Allah wadai da halina
Alhaji sudais yace ya isa haka abokina kayi shiru kayarda da kaddara kacigaba da istgifari da neman gafarar Allah
Abinda zamuyi yanzu shine duk inda yarinyar nan take a Nigeria dole mu aje komai muje munemota
Kanemi gafararta batun wai kayi tunin samun ta matsayin mata wannan kacire azuciyarka tariga tayi aure
Kukan alhaji imam ya tsananta yace kana nufin narasa maryam kenan har abada
alhaji sudais yace kayi hakuri mana imam kazama namiji bansan ka hakaba kayarda da kaddara mana wannan Abu tabbas jarabawa ubangiji ya jarrabeka dashi saboda ba halinkabane no shaida ne akan ka imam
Sosoi alhaji imam yake kuka kaman karamin yaro saboda azaban tausayin kanshi idan baisamu maryam a matsayin mata ba
Nan suka yanke shawarar zuwa Nigeria Neman maryam da danginta
****
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya yau Allah yakawo mu auren AL'AMIN ZAYYAD FAISAL Wanda za a daura karfe hudu na yamma
Gida yacika makil da mutane dangin su daddy da abokan arziki Hajiya zabbau ma da yan uwan ta
Mummyn Dagash ma kannanta da matar babban yayansu duk sunzo
Sai kawayenta manyan hajiyoyi sai matar shugaban kasa da mata gommonini duk suna bangaren mummy
Ana tayata Murna yayin da ita kuma zuciyar fal da bakin cikin wannan Abu sai ganin mutane ta boye komai a ranta
Allah sarki anty ita ba fita ko ina suke ba batasan kowa dan haka dakinta bakowa sai kawayen maryam kuma suna can dakinta ma
Matan megari ne daman zasuzo to suna hanya basu isoba
Sai a yau anty tayi kukan dangi sosai daga karshe ta goge hawayen ta tashiga wanka
Dai dai likacin da Hajiya zabbau
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 18