Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
takira katon gardin nan a waya tace yazo zata bude mishi hanyar baya yashigo Haka kuwa akayi tsaf yashigo ba Wanda yaganshi yashi harcan bedroom anty na taimakon Hajiya zabbau Itakuwa anty tana bathroom dinta tana aikin kuka tagama wankan har ta zura doguwar Riga amma tana ta aikin kukan rashin iyaye Daddy suna zaune a compound din gidan sa shida su alhaji dan asabe suna tattauwa Sai yaga motar da yabayar aje a dauko su matan maigari sabada anty tadan ji dadi Cikin farinci ya musu iso har part dinta Yanuna musu kujera suka zauna yace yace bara nakira muku ita tana ciki ne Kafin daddy yakarasa dakin anty sa shegen gardin nan yafara magana kamar haka Kai amma Gaskiya maryam kinsan kan duniya wato dan kinga bakowa a ashashinki shine kika zamu inzo gidako Shifa wannan tsohon mijin naki yana dauka kedin wata ta Allah ce ko Dan Allah kiyi sauri kufito daga wankan nan nima na watsa nace kibari muyi tare kince na tsaya kifara saboda kifita da farko anty dake durkushe bandaki taji kaman magana a bedroom dinta sai tayi saurin budewa dai dai lokacin da daddy yabanko kofar yashigo Jiri ne kefaman diban daddy saboda abinda yaji kuma yagani Maryam dinsa takawo mai kwarto daki Matar dayake so fiye dakomai ya yarda da ita Ai kuwa wannan katon yafara shikenan kinja mana maryam yau asirinmu ya tuno anty ta daga hanu tasa akai tace nashiga uku Waye kai dan Allah kafadi gaskiya cewan bansan ka ba Wallahi alhaji bansanshi ba tana kuka daddy kuma da idonsa suka canja kala zuwa ja yace kincuceni maryam kinci amanata maryam Duk hallacin Dana miki ace da wannan Abu zaki saka min Ya bar dakin dasauri anty tabi bayanshi tana kuka tana wallahi alhaji bansanshi ba sharri aka kulla min Daddy bai saurareta gashi duk inda suka wuce sai abinsu kafin wani lokacin gida yadauka ai kwarto adakin amaryar alhaji Maryam suna daki bata San meke faruwaba ganin su nazeefa sukayi sunbanko kofar dakin Nazeefa tace to kina ga uwarki can an kama ta dabkwarto yau dai asiri ya tuno Cikin zafin nama maryam ta tsinke na nazeefa da kyawawan marika har uku Tace har kin isa kidan ganta uwata wanann kazamin aikin ban dau mataki ba Tana gama fadin yahaka tayi waje falo ta nufa ganin taron mutane a falon yasa gaban maryam faduwa ta karso taga antynta a tsugune tana kuka Muryar daddy taji yanacewa nasakeki saki uku maryam Iya Kalmar dataji kenan ta yanke jiki tafadi kasa sumammiya anty tayi kan maryam tana maryam kitashi dan Allah karki mutu kibarni kedai kika rage min yanzu Anty asiya ta zo aguje itama ta tallafo maryam din sai suka ga jini na zuba yana bin kafar maryam Anty shukura tayi salati ta dauki waya takira doctor nabila ba afi minti biyarba ta karaso tana ganin maryam tace ai bari tayi tasamu miscarriage ai kuwa anty kukan ma yakasa zuwa saboda tashin hankali Kasa kawai take kallo takasa motsi Falon yadauki magana Hajiya zabbau tace Allah mungode maka da maka da tuni asirin munafukan agidan nan Mummyn Dagash tace nice da godiyar Allah ashe an yi rufarufa za a aura wa Dana yarinyar datagama yawon taxubar dinta to ta Allah bataku Kowa da abinda yake fada Mara dadi akan su anty Daddy king da alhaji dan asabe jikinsu duk yayi sanyi ballantana uban gayya daddy Shigiwar Dagash da alhaji imam da abokin shi alhaji sudais ne yasa kallo yakoma Kansu Dagash yace mekefuruwa haka agidan Mummy cikin jin dadi tace Allah yasoka my Son da ka rainin dan shege agidanka Kan dagash yadaure kafin yayi magana Alhaji imam yace mekike fada Aisha tace ai yaya bazaka gane ba mushiga kawai kuhuta kwaji komai Kaman daga sama yaji muryar da bazai taba mantawa dashiba a rayuwarsa anty tadago kai tana kuka tace Allah meyasa baka kashe ni ba kafin zuwan wannan rana Caraf idonsu cikin najuna cikin tsanin firgici anty tazuba razanannar kara tana nuna Alhaji imam da hanunta tayi bayan tafafi anty asiya tayi saurin tareta Alhaji imam kuwa salati yake ta na natawa yazube shima dagash ne yayi saurin taroshi Mummy tace wai me kefaruwane bangane ba na shiga uku na Next page Your comment is needed *Signed by ummu afan*πŸ’» [15/07, 1:12 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑 πŸŽ€ *BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM* *Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI* 🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟 G.W.F🌟 *Home of gorgeous, intelligent and expert writers* Dedicate this page to duk wani wanda page 41 to 45 yatabashi to nabashi kyautar wannan page keep it up keep smiling keep pushing don't ever think to ignore my novel saboda zai muku anfani zai nishadantar daku 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 Gaskiya masoya Al'amin ba abinda zance akan wannan touching hearts page din sai godiya saboda yanuna tabbas ana tare so I choose page 41 to 45 to be my best page much love to this page 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH* *PAGE* 4⃣6⃣to5⃣0⃣ Al'amin zaune a gidanshi dakusan two weeks kenan yana cikin ta kuma ba abinda yakeyi sai ibada kuma alhamdullila yana jin saukin zuciyarsa Ya dauko wayarsa ya kunna Kaman jira akeyi yaga kira yashigo yana dubawa yaga Vicky ce wani sabon tsanarta yaji tsaki yayi ya rejecting call Sai kuma Ga kiran zayyad yana dagawa zayyad to mutumin tunda naga number din Nigeria nasan kasauka kenan Dagash yace ai tunjiya nayi landing ina gidana na GRA Zayyad yace ok ganin zuwa nima ina kusa da GRA din dagash yace ok saika karaso Mummy zaune falonta suna waya da yayanta Alhaji imam yace next months zai shigo Nigeria tace to Allah yakawoka lafiya amma dan Allah ka kawantar da hanklinka yaya Wallahi damuwarka yana affecting dinmu sosai ni anyama yaya ba aljanabace kuwa Alhaji imam yayi murmushi yace Aisha kenan bazaki fahimta bane Maryam yarinya ce sosai dan I was think ko Dana Al'amin ma yagirmeta Kuma mutumce kaman ke mummy taja numfashi tace to Allah yasa adace yace amin Aisha kiringa sani a adduarki tace insha Allah yaya Kaine mutum nafarko a adduata Sukayi sallama ta ajiye wayar cike da tausayin dan uwan nata Zayyad yayi sallama a falon dagash Yaganshi kwance kan doguwar kujera Zayyad yace subhanalla Dagash kaga yadda karame kuwa Murmushi yayi yace ai dole na rame zayyad ace mutum ba 'abincin kirki sai snacks ai dole Zayyad yace dan iska ashema laifinkane wai kai yaushe zakadena wannan akidar kyamar taka Abincin mutum biyu kawai kakeci a rayuwarka To aidakasani sai kayi tafiyar da ita maryam din Jin zayyad ya ambaci sunan maryam yasa gabanshi yafadi Zayyad bailura da hakan ba yacigaba da maganarsa Yace amma dai yakamata ka koma gida yau ko tunda kace tunjiya kana gidan nan Dagash yace yanzu kuwa bara nayi wanka nafito mutafi Dagash yayi parking a parking space na compound dinsa yafito cikin kasaita kamar yadda yasaba Maikatan gidan suna ta gaisuwa yana daga musu hanu Yana shiga falon tunda yaga baiga su suhaila a falonba toyasan basa nan To ina maryam ya tambayi kanshi yatura kofar dakinta Yaganta kan abin sallah tana ta tunani da alamu ta Dade a haka Karasowa yayi yasa hanu yacire tagumin datayi frgit maryam ta zabura ganin dagash ne gabanta ya mugun faduwa Gani take zaigane abinda yafaru da ita Yace lafiyanki kuwa tayi murmushi tace lafiya kalau yaya kawai dai banji shigowarka bane shiyasa naji tsoro amma yaya karame kasake haske lafiya kuwa Murmushi dagash yayi yace nayi kanwata da abincinta Kinga kuwa ai dole na rame beside ma kema kinrame baby meyasameki kinyi rashin lafiyane Maryam tace a nayi kuma anty shafa ta kuladani dagash yazaro ido yace shine baki fada minba baby Wani hospital kukaje maryam tace bamuje asibiti magunguna ta karbo min yace no banyardaba zansake dubaki da kaina bayan nahuta banason musu Me kika dafa ne kitemiki dan al'amajiri Maryam murmushin dan almajirin dayace takeyi ta tuna rabonta da shiga kitchen ma ta manta shafa'atu tace me dafa musu abinda yasauwaka Ta tafi school ne duna da lectures Ta kalleshi tayi murmushi tace to kaje kahuta zan dafa maka Abu maisauki yanzu insha Allah Yaja hancinta yauwa good girl yamata murmushi yafita daga dakin maryam ta bishi da kallo Tashi tayi tashiga kitchen din tafara shirin girka mashi abinda zaici Shafa'atu tayi sallama ganin Maryam bata daki saitayi nocking din toilet Bata ciki sai tafito falo ganin kofar yayanta a bude yasa tashiga harsama ta haura tasameshi har yayi wanka yashirya cikin wata lallausar farin yadi half jamfa ya balain mishi kyau shafa'atu tayi sallama tagaida yayan nata yace a a shafa'atu kindawo tace a yaya Yace ya lectures kina karatunko baki bari soyayya ya rinjayi karatunkibako ta sunkuyar kanta tace ina yi yaya Shigowar maryam cikin doguwar hijabinta da tiren abinci yasa shafa'atu mamaki Tace au dama ciwon duk na rashin ganin yayane Kafin maryam tayi magana dagash yayi yace ai ba itakadai bane tayi missing din nima bakiganni ba kwana biyu babu nice food dinta Shafa'atu tayi murmushi tace gaskiya kam karame sosai amma itama maryam yaya harda rashin cin abincin Ya kure maryam da ido sosai yace hakane baby bakyason cin abinci ko Maryam cikin salon muryarta tace inacifa yace banyardaba Zonan muci abinci tace yaya nakoshi yace banason musu Ba yadda zatayi haka tadauki spoon tana ta jujjuya abinci batayi tsammani ba taga yakawo abinci bakinta Shafa'atu ganin kaman ma sun manta da ita agun tace barinje na watsa ruwa Tace maryam Allah yasa da wannan abinci ba yaya kadai kikawa ba maryam dai murmushi tayi abinta Tace yaya zanci dakaina yace banyardaba haka yasauko kasa shima yana bata shima yana ci Tundaga wannan ranar kulawa ta musaman take samu daga yayan nata Abin yana mugun daga hankalin mummy sosai tarasa yadda zatayi *** Bayan wata biyu maryam hankalinta ya Dan kwanta sakamakon kulawa datake samu wajen yayan nata Duk yadda su Aymana da suhaila suka kaiga ganin sun takura wa maryam basu samu damaba Maryam tana zaune a dakinta tana zaune kan resting chair fruit salad tayi takesha Dagash yafado dakin murmushi suka sakarwa juna murmushi karasowa yadauki fruit salad din yafarasha Yace kinsan meye ta girgiza kai alamun a a yace to daddy yakirani anty ta aihu 'Dana miji yau dasafe Maryam cikin tsananin farinciki tace Alhamdullilah lalle ma anty shine bata fada minba cikin murna tafara kokarin kiran anty a waya Hajiya zabbau bakarakaramin hauka taso tayiba jincewar anty ta haifi yaro namiji Sosai tashiga bakincikin abin har yakaita ga takasa zama ta samu mummyn Aymana dazancen nan da nan kuwa tabata shawarar da zuwa gurin boka Mummyn al'amin kuwa ba abinda yadameta ita damuwar daman akan uwarce karta jamusu tsiya saboda ance idan talaka ya rabi mekudi zai iya talaucewa Takira daddy dakanta tamishi barka yaji dadi sosai Dan baiyi tsamanin hakan ba Sai dai yayi yayi sugaisa da anty taki acewarta itafa ba abinda zai hadata da amaryar daddy Kwanansu anty shida acan bayan ta haihu suka dawo Nigeria saboda so yake ayi suna sosai Ranar suna daddy yawa yaro huduba da AL'AMIN wato dai yawa dagash takwara kenan saboda tsananin soyayyar dake tsakanin daddy da dagash yasa yawa dagash takwara Sosai dagash yaji dadi dama gashi tunda yadaura idonshi kan yaro yaji yashiga ranshi Yaron sosai suke kama da daddynsa komai nasu daya Dagash yayi rawar gani sossai yasaki kudi wa takwararsa Har ya mallakawa lil al'amin jirgi guda daya Wanda yake mallakin dagash yabashi kyauta sosai daddy yaji dadi sosai Harda gida abin dai ya daddy dadi sosai yayin da mummy ma bata damu da kyautar da danta yayi ba saboda itama taji dadin yadda daddy ya karrama danta nata kwallidaya Hajiya zabbau dai mutuwane kawai batayiba Anty asiya kuwa yau take hanyar zuwa shiyasa aketa murnar zuwanta Sosai dangin su daddy suka zo suka taya shi murna anci ansha sosai Maryam kuwa taki rabuwa da jaririn Antynta tayi kyau sosai tasake dawowa yarinya shakaf kowa yaganta bazaice tana da kaman maryam ba gaskiya daddy ya iya kiwo sosai Maryam ta kalli anty tace anty na kinga yadda kika dawo kuwa ai bawanda zaiyarda cewar wannan uwatace sai dai ace yayata ce Anty tayi murmushi tace kinci gidanku Kebakiga inda kika komaba ko Maryam kinyi kyau sosai lalle a gaida wannan yayan naki Lokacin da muka barki wajenshi hankalina baikawanta ba kwatata amma Dana ganki a yanzu na tabbatar da ya rike minke yadda yakamata Allah yasaka da alkairi Shigowar anty asiya ne yasa Maryam shiru daga maganar datakeson yi Anty asiya da murmushi ta karasa wajen anty tana murmushi tace koda bansani ba kece small mama dinmu ko anty tayi murmushi tace asiya ko anty asiya tayi murmushi tace la ashe nima zakiganeni Anty tace haba asiya ai tunda naji kince small mama nagane wacece duk da banganki a fuska ba ainasan muryar ki Anty asiya tayi murmushi tace toyanzu dai ina kanwarmu Maryam ita nakeson gani Anty tayi murmushi tace to ga Maryam a bayanki tana nane da jarari kamar bazata ajiyeba Anty asiya suka hada ido da Maryam tayi saurin cewa anty sannu da zuwa Anty asiya takasa magana ta kalli anty tace small mama yanzu kina da budurwa kaman Maryam what's a surprise Anty batace komaiba Maryam tayi murmushi tace kema kema dai kya fada anty asiya saboda haka daga anty kinkoma yayata Dan nasan kona fada bazasu yadda ba Anty asiya tace gaskiya kam ba mai yadda Tace amma gaskiya Small mama Maryam ta dabance ai tafiki kyau ma sosai duk da kema din batayan baya bace wajen kyau Anty tace ina zaki hadani da Maryam asiya baruwana duk sukayi dariya gaba dayansu Anty asiya takarbi lil al'amin Tace kai masha Allah gaskiya baby maikyau duk tunranda aka haifeshi naganshi ta watspp Anty asiya tace anty saura kihaifo mana mace maikama da sis Maryam kyakykyawa Anty tayi murmushi tace rufa asiri asiya wani haiuwa kuma wannan ma Allah yaraya Anty asiya tayi murmushi tace ai insha Allah yanzu kifara Nan dai sukayi ta hirarsu Bayan sati uku Maryam na zaune a falon antynta tana kallo Sai taga wayarta nakara tayi kaman bazata dauka ba Sai kawai ta daga abinta aikuwa al'amin yazo gidan yace futo kisameni a falo Yakashe wayar shi Maryam ta tadauki hijibinta tasaka tayi hanyar falon Shikadai tasamu agurin nan tazauna yace wato kinbar gidana shine harni kinbari ko baby Maryam tayi murmushi dayake sata takara kyau sosai Tace bahabane yaya yace oya jeki kawo min lil al'amin kizo muyi hira Ta tashi tana murmushi tana dawowa da lil al'amin dagash yakarbeshi yaji dadin ganin yaron Dan indai yazo gidan to yakan sa adauko mishi yaron Duk da bawani iya rike jararai ya iya ba sosai Maryam tayi ta mishi dariya Mummy ce ta fito ganin dagash da Maryam bakinciki yakamata Takaraso gurinsu tace son wai yaushe zakafara jin maganata agidan nan Meyasa kullum kake Abu kaman karamin yaro ne Bana hanaka mu'amala da wannan matsiyaciyar yarinyar bane jinin matsiyata mayu matsafa dabbobi Wanda ba abinda suka sani sai zuwa gidan boka da malamai Duk abinda ake was Maryam agidan baitaba damunta ba sai wannan zagin mummyn nayau din Ashe kuwa duk a kunnen antynta Dagash yace haba mummy why meyasa zakiyi haka for God sake wannan kalmomin naki sunyi yawa akansu Kafin dagash yacigaba anty ta matso kusa dasu tasamu fuskar maryam cikin zafin rai ta zabbaga mata mari tace kukan mezakiyi maryam tunda muke a rayuwar mu babu inda aka taba cimanata mutunci irin wannan Kinsan meyasa namareki sosanake kiji zafin aranki sannan kuma kisan maganar dazan fada miki kidauke da muhimmanci Su hajiya zabbau ana jin hayaniya dukansu suka taru a falon Dinjin wainar da aketoya wa sosai taji dadin cin mutuncin su maryam da mummy tayi anty asiya kuwa cikin bakin ciki takoma daki takira daddy a waya Su naxeefa kuwa da afnan abin nema yasamu Anty tacigaba da magana Maryam banyarda ko hanya yasake hadaku da Al'amin ba wallahi idan kikasake nasake ganinku tare sai tsine miki maryam Cikin tsananin kuka maryam tadago ido haba wannan wani irin masifane antynta bata taba zaginta ba bare ta sa hanu ta taba lafiyar ta Sai gashi yau har tana ikirarin tsine mata da gudu takarasa dakin su tabar falon Anty ta kalli mummy tace hajiya mungode da cin mutuncin dakike mana nida yata acikin gidan nan amma inason kisani bazan baki amsaba saboda sanin darajar manya Dan koba komai ba maryam nima kin haifi Wanda yafini bare maryam Dan haka Allah ya huci zuciyarka ta kalli dagash Tamika mishi hanu yabata danta yabata takuwa juya tayi cikin part dinta Dagash ya kalli mummy yace mummy yaushe kika dawo haka nasan bakyason talakawa amma bata tunanin zaki iya cin mutuncin mutum har haka ba Tace au yanzu duk abin dayafaru agabanka son baimaka ciwo ba abinda akamin Mena maka haka ina soyayyar da kake nunamin son akan wadan nan matsiyatan mutanen Yace haba mummy enough please Daddy ne yashigo shida daddy king wato memartaba kenan dama suna tare asiya takira daddy tace mishi gida balafiya wai me ke faruwane Haka mummy tace wai daga na yanke alakar dake tsakanin shi da wadan nan matsiyatar mutanen Daddy ya mata wani mugun kallo yace suwaye matsiyatar tace akwai wasune ne bayan matarka da yarta Ran daddy yayi dubu yabaci Yace haka kikace tace to na nawakuma alhaji Shikenan to ina mai tabbatar miki al'amin bashida mata sai matsiyaciyar dabakyaso kinga sai a Haifa maki matsiyatar jikoki kenan kinga daga nan sainaga nazagin matsiyata Cikin da tashin hankali mummy tace wallahi alhaji baka isaba Dan kwalli daya kace zaka bashi wadan nan marasa asalin Wanda tunda suka zo gidan nan ba Wanda yabata zuwa Yace yau gashi Dan uwansune yazo Karkamanta sunkai kusan shekaru hudu agidan nan saboda wallahi idan sama da kasa zata hade bazan yarda ba Cikin dacin rai daddy yakalleta Kafinta yayi magana maryam ta zo da gudu tarike kafan daddy tace daddy Dan Allah karkayi haka wallahi bazan auri yaya ba Koba Dan komai ba kodan bamu da gata shi maigatane Hakan baifaruba ma mummy batason mu bare kace haka daddy Dan Allah karkiyi min haka Daddy yadagota Yace maryam tunda nake daku nataba banbantaki tsakaninki da yarana Maryam ta girgiza kai yace ok to indai hakane ninake da iko da Ku acikin gidan dama duk wani Abu me numfashi saboda babu Wanda ya isa yasake saku kuka agidan nan kuma hukunci na Riga nayanke shi Cikin meban tausayi tace daddy Kaduba Dan Allah koda ba Dan komai ba shima yayan baice yanasona ba taya za a mishi dole daddy abin zai min yawa kayi hakuri takarasa maganar Tana kuna kuka Kaman daga sama dagash yace wayafada miki bana sonki maryam inason ki kuma nashirya auranki kaman yadda daddy yabukata Abin yadaki zuciyar mummy dama su hajiya zabbau sun rikice shikenan gida zai koma na wadan nan matsiyatar Hajiya zabbau tace gaskiya alhaji wannan ba adalcibane yaza a yi daga zuwan mata gida duk sun asirceka kaida danka Kuma badama muyi magana wannan ma ai zalincine komai an mallaka musu ko uwarsa bai wa kyautar jirgi ba sai wannan yaron Dan matsiyaciya Daddy yace ke kuma wayasa bakinki aciki shasha kawai wato nine matsiyacin tunda danane kince matsiyaci ko Maganar anty ta fito daga part dinta daman duk abinda kefaruwa Tana jinsu Tace kayi hakuri alhaji bazan taba bari maryam ta auri duk wani abunda yashafi hajiya ba saboda tadade tana cimana mutunci agidan nan Kuma bazata hakuraba zatacigaba da ciwa maryam mutunci saboda tunfarko ta nuna bata kaunar mu Dan Allah kayi hakuri bazan iya ba Daddy ya kalli anty yace maryam wato kinason nuna min in ban isa da maryam ba kenan da har zanzartar da hukunci kice be mikiba Cikin kuka anty tace kayi hakuri alhaji Dan Allah banufina kenan ba duk duniya maryam bata da uba da yawuce ka Kasamo mata koda megadin gidan nan akan kabata al'amin Hajiya zabbau tayi shewa tace to mungaji da garafa sa bamuga kahoba Wai idan yarinyar tana da uba kimaida ita gurin ubanta mana kodayake anshigo daula ai baza aso afitaba towa yasani ma ko yar gaba dafatiha ne Batayi tsamaniba taji saukar mari a fuskarta daddy ne yazabga mata zai karamata daddy king yayi saurin rike hanunshi Cikin zafin rai yace zauna yaya Ya kalli hajiya zabbau yace ashe haka kike hajiya wallahi kunbani mamaki bantaba tunanin haka daga gareku ba Kuma ina mai tabbatar muku nan da sati biyu zan daura auren al'amin da maryam Bawanda ya isa ya hana sai Allah Mummy al'amin cikin zafin rai ta wuce dakinta anty kuwa takasa tashi jin wannan tonan sililin da aka musu agaban jama'a akaci mutuncin su Da kyar daddy da daddy king suka bata hakuri suka mata nasiha daddy dakanshi yaraka anty daki yadawo suka fita da daddy king Dagash yakalli maryam da inbanda kuka ba abinda takeyi Yace baby bazakiyi shiruba Cikin kuka tace yaya meyasa kace kansona bayan nasan bahakabane kawai kafadane Dan kana cikin haushin abinda mummy tayimana Dagash yace maryam waya fada miki bana sonki Tunda nake bantaba jin son wata maceba sai akanki bansan soba sai akanki Maryam bansan yadda zan lissafa miki yadda kike acikin rainaba Inason ki ina kaunarki zan aureki zan baki gatan dabaki taba tunain samuba a rayuwa in fact maryam kece rayuwata I can't do without you Maryam tadaga kai takalleshi shima yadaga mata gira Next page Your comment is needed fan Much love to your nice comments *Signed by ummu afan* πŸ’» [15/07, 1:13 PM] SIS UMMY: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑🎑🎑 πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ 🎑🎑 πŸŽ€ *BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM* *Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI* 🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟 🌟 G.W.F🌟 *Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest* *Dedicated to gorgeous writers forum* _🎑AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ 🎑 Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai Comment harda read more πŸ€”much love to your love and care πŸŽ€ *AL'AMIN DAGASH* *PAGE* 5⃣6⃣to 6⃣0⃣ Cikin tsananin tashin hankali dagash yazaunar da Alhaji imam dake kokarin faduwa Dagash yace asiya kudauko to mutafi hospital acan zan fidubata dakyau Cikin sauri yaga maryam wacce ke kwance cinyar shafa'atu jini nazuba mata ai baisan sanda yaisa waje yaduketa cak yayi motaba Anty asiya da doctor nabila su kama anty zuwa mota Shafa'atu kuma ta je tadauki lil al'amin ta goyashi suka nufi hospital Alhaji imam yatashi yayi hanyar waje duk da jirin dake dibansa Dasauri alhaji sudais yakamashi yace haba imam kanutsu hankalinka yadawo jikinka kafin katashi Alhaji imam yakalli alhaji sudais yace maryam ce fa itace fa akafita daita bata numfashi sannan kace nazauna annan nutsuwa tazomin ai bazaiyuwuba ma nitsuwata yana tare da maryam Cikin rashin fahimta mummy ta karaso tace wai yaya mekefaruwa ne kasanar dani Dan Allah kasani a duhu Kafin yabata amsa daddy king yace duk wannan maganar agida bazai mana ba kutashi mubisu hospital din kawai Dakyar alhaji Dan asabe suka rike daddy yashiga mota Mummy da hajiya zabbau da dai sauransu masu son jin gulma haka aka nufi dagash memorial hospital Yanazuwa zuwa yakira zayyad a waya shiya duba anty a inda aka shigar da ita imagency shikuma dagash yasamu yaduba maryam Mutane damkam a acikin tafkeken reception din hospital din dagash Dagash ne yafito cikin sauri yayi hanyar waje megadi yakira yabashi watafarar takarda yace Dan Allah malam Abdul kaje ka karbo wadan nan magungunan please Yanzu yanzu Dan Allah kayi sauri Wanda dagash yakira da malam Abdul yayi saurin karba Matashine shima Wanda bazai wuce dagash din a haifeba Kawai dai saboda talauci da rashin wayewa yasa yake aikin gadi a hospital din dagash Yaji mamakin ubangidan nasa sosai yau shizaiyi aika harda Dan Allah da rokonsa Gaskiya wannan Mara lafiyar tana matukar

Chapter 14 of 18