Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dai bata san inda ta saka sim din ba sai wanda ta tsinto ne a ciki.ummi dai tayi shiru ta miqa ma umma waya. kusan qarfe goma sha daya wayar abba da umma ta taho da ita ta soma qara,umma ta dauka.alhj ne ya ce ina wayarki ina ta kira ana cemin a kashe?una tace, a ku6e take gata ma a hannuna.yace to inata kira.tace qila faduwan da tayi daxu ne ta samu matsala.yace to dama zance ne ki dafa masa ruwan xafi a xuba a flask dan uwan matansa xai kawo mu yanxun a mota xai amsa ya kai.ta ce to alhj wayn xai kwana gunsa?yace bashir na nan kuma matarsa anyi anyi ta qi tafiya shi yasa na haqura xan dawo dan ba na xauna gun su ba ko? umma tace amma yaya jikin nashi?ya ce da sauqi yanxu ma yana son shan tea ne.tace to xan hada harda wayar tasa inya so ma dunga kiran shi kafin gari ya waye.ya ce yauwa ki bada.Alhamdulillah abba jiki ba matsala. Don hk a ka sallamo shi zuwa gd.kai tsaye gdn su umma a ka wuce d shi. A salin dakinsa a ka gyara a cikin kwana nan 3 ya yi ras sannan ya koma shago. Bishira kuwa lkcn mahaifinta ya ce maza ta koma dakinta,tunda ga abn d ya samu mijinta.Sun dawo hr da tafkeken injin Janareto wai yaron ba ya son duhu. Sannan ga kayan kallo d saraunsu.TabbasAbba ya ji dadin dawowar iyalanshi,dn dama yana cike d bukatarsu. Ranar yini suka yi gyaran gd ita da 'yan uwanta,sai byn magrib sannan ya shigo d tsarabobi.madara tatacciya da kaji. Ya dauki dansa cikin jin dadi yana kallonta cike da so da kauna,Nayi missing din ku da yawa.URFIN CIKI book 2 part 3 ZURFIN CIKI book 2 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:08 Ai bama shiri. shi ne fa ya kawo ni mkrntr kwana dn kawai baya son ganina. Suka yi ta mamaki. Can jimawa ya dawo, sun fito rakiyar 'yan uwansu Safiyya da na Khadija, suka ganshi tsaye yana danne- dannen waya. Ya taho ya gaida iyayensu duka,sannan suka koma gefe d ummi, ya ce Ni ma zan tafi. Ta ce, Ya Abba ko fa gaisawa ba mu yi ba. Ta karkatar da kai,Cikin raunin murya tamkar mai shawagaba,ta ci ga ba da cewa Ya Abba su Umma ba wanda ya ce a gaishe ni? Sai hawaye suka soma zuba. Hankicinshi da ke hannunta tasa tana sharar kwalla.Abba yana da matukar tausayin mace. Don haka duk da tsanar da ya yi wa Ummi sai da ya tausaya mata.Ya tausasa Murya. Sun ce in gaishe ki sosai, za ki ga gyada mai gishiri, Tsohuwa ta ce a ba ki.Umma ta miki miya, ta kuma daka miki yaji. Ta ce Na gode, Alhj me yasai min?ya ce kayan tea ne da lemun kwali. Ta ce Na gode. Tana ci gaba da share hawaye. Ya mike Zan tafi. yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi ya mika mata, ta ce A'a ya Abba ka bar kudinka. Ya ce Ba ni ne na baki ba,Alhj Karami ne ya ce in ba ki. Ta sa hannu 2 ta amsa tare d godiya.Sun raka shi kusa da Gate ita da su khadija,sai kuka Ummi ke yi. Bayan sun dawo dakinsu ne ta zauna tana duba kayan da ya lissafo mata,duk ta gani. Sai kuma saitin sabulun wanka da manshi da turaransa da hodarsa duk na (Aloe vera.) Shi kuma bai fada mata ko daga wa ba,ko ba komai ta dai yi murna sobada tana da 'yan kuraje a fuska,tasan kuma za su mutu. Sai kuma audagar mata,tayi dan murmushi. . Tunda Umma taji sallamar Abba ya shigo dakin ta bar komai tazo ta zauna tana son jin lbrn Ummi. Abba ya fahimci Haka,dn haka sai ya boye mata cewa, Ummi na kuka hr yanzun. Ya nuna mata ai Ummi ta kwantar da Hankalinta,km tayi hnkl dn ya bincika ya ji ana ta yabonta. Umma taji dadi Sosai,Sai da ya fara zuwa gurin Ummu,sannan ya je gida.Ya samu Bishira tana zaune tana aikin nata,wato Kallo. Tun da ta dawo daga wankan gida tazo da janareto da kayan kallo,shi kenan ta sanu abn yi.Kullum tana gabn (TV)da ta shi da safe in ta kokarta shi ne ta dafa ruwan tea ko wanka ba za ta yi wa dan ba,sai lkcn d man injin ya kare. Ya nufi gurin injin ya kashe,dif din da ta ji komai ya tsaya shi ne yasa ta zabura ta mike tana fadin Ba dai har man nan ya kare ba? Ta fito da niyar dubawa.Abba ta gani tsaye gabn injin yana bn tsakar gidan da kallo cikin takaici. Ta ce Baban Walid kashe min injin kayi??Ya ce Eh na kashe dn Allah dubi gidanki?kalli wanke-wanke kuda na bi dubi tulin wankin kayan Fitsarin yaronki. Dubi kicin dinki,kuma ko da bn shiga dakinki da wannan falon da ki ke kallo ba.na tabbata da wanda ki ka dauke ko tsinkw a cikin sa.Kila ma ba ki yi Sallah ba. Ta ce Dan karashe ne fa ya rage min in gama kallon in zo in yi aikin.Haushi ya sake kana shi,Sai kurum ya shige daki. Tsakuwar da ya dora kafa a kai tasa tsigar jikinshi tashi,sam ya tsani ya shiga daki ya dora kafa kan datti. Ya dawo yasa takalmanshi ya shiga da su,Walid yana kwance tun kayan da ya bar shi da su da safe sune a jikinshi yana ta bacci cikin fitsarin da ya shafka wanda ba wata leda da zata hana katifar ta jike. Ko wankan safe ma ba a mishi ba kenan.A fili ya ce,",Inna lillahi wa'inna ilaihinr raji'un. ya juya ya nufi shagi. Ita kam sai ta kunna injinta ta karasa kallonta, sannanta tashi ta dora girki.sai lkcn ta ma Walid wanka. Ta dan dauraye kwanukan da za su ci abnci,wai ta gaji sauran wanke-wanken sai gobe. Fati ta shigo,Bishira ta ce Yauwa Fatima naji dadin zuwanki.shuga dakina ki gyara min gado,ki dan yo min shara. Fati ta ce To. Ta shiga ita ma duk shegiyar darin ce gurin kuiyar aikin,dn haka ta dan birbira ta fito ta ce ta gama. Bishira ta ce Yauwa dan dauraye min kaya can na Walid. Nan ma tasan sama ta shanya. Bishira ta ce Yauwa ta ga abnci nan kici.sai ki dauki na Ummarku ki kai mata. Har Fati ta kai waje,Bishira ta kwala mata kira. ta ce,Zo ki tafi da wannan galan din na man fetir kije shagon Babn Walid kice ya taho mana da shi,dn man ya kare. Koda Fati ta same shi da galan ta fada mishi sako ya ce Ba zan siya ba,Maida mata galan din. Ta tafi,Shi kuma ya ci gaba da mita a zcyrshi. Yana fadin Na daina sayan man tunda ba za a bari sai dare a kunnan ba.Gidan Ummanshi yaje,ba ta nan ma taje barkar Haihuwa. Ko dakin Tsohuwa bai shiga ba,ya zauna nan falonta.Ya za kula ya zuba abncinshi ya ci.sannan ya dan huta sai ya fita zuwa gidan su Ahmad. Cam ya samu wasu daga cikin abokanshi suka shiga hira. Ranar dai Abba bai je gida ba sai misalin sha daya ko daya shiga bai nemi matar gidan ba,ya dibi ruwa ya yi wanka sannan ya shiga dakin. Ya lalibo makunnan wuta ya kunna,dn Nefa sun kawo wuta. Tana kwance irn banzan kwanciyarta da ta iya,dakin sai tashin wani irin wari yake kamar na ruma,kamar na fitsari ko na datti.Ya kalli ko'ina kullin kaya ne na wanki ne,na gaga ne ciki da guri.Ranshi ya baci,Ya kuma dubanta ga wata kiba da ta tafka. Tun da ta haihu ta zama rusheshiya,gashi bata son kama jikinta.Tsaki yaja,sannan ya dauki fiko ya fita. kan doguwar kujera ya jefa filo,ya kwanta a gajiye.Amma me?sai ya ji dora gadon bayansa acikin lema.Da sauri ya mike ya kunna wuta.Duk fitsarin yaron ne a kan kujerun dakin,dn haka sai ya nufi dakin da takw aje tarkace ya kunna wuta,shi ma dai duk shirgi. . Ya share Ya shimfida ta barma ya kwanta,a ranar ya dauri aniyar maida dakin ya zama nashi din-din-dn. Don haka washegari yasa a ka zo a kayi masa fenti,ya siyo kati fa ya yar da zanin gado,dk wani abu nashi sai da ya kwashe su. Kafin wata guda ya maida dakinshi cikakken daki,ya zuba dk wani abu da yake bukata. kafin ya fita kullum sai ya gyara dakinsa fes. ita kuma sam bata zuwa dakin,sai dai in yana da lalura yaje can ya sauke ya dawo. kazantarta kam ta kai in da ta kai,tunda hr kayan kashi tana zube su a cikin daki. Ya gaji yaje ya samu Anty ya fada mata,hr gidan Anty tazo ta zazzageta,ta tasata suka gyara gidan, amma ko a jikinta.Washegari ta ci gaba da in da ta tsaya. Sam babu wanda zai ganta ya ce haihuwarta daya. ¤¤¤¤¤¤ ¤¤¤¤¤¤ UMMI yau ba wanda ya kaita murna,domin yau dai an basu hutu..Sai dai tunaninta zata ko iya kai kanta gida? Sunyi ban kwana bata da kudin mota, dan duk tayi taba su safiya kudin gurinta, amma ta ce yau ko da qafa ne xata gida.sun fito wajan mkrt wata maryam tana cema,ki tsaya mota xato da xata kaimu cikin kn.ummi tace baxan jira ba.sai ga abba kamar daga sama,tsoro ya kamata karya ce ta xauna gidan abokin sa da yace.hanka linta ya tashi cikin in ina ta gaida shi ya amsa.ya shiga mkrtn jim kadan ya dawo.hakan ta sha alwashin yau ko da shiya saita je gida.shi kam ma ya manta yai mata wannan maganan ma.ya sabi akwatinta suka je suka shiga mota. abba mamakin natsuwan ummi yake yi, ko da yake baxai ce ta natsu ba, qila lafawa tayi.tundaga soro ta saki jakanta da bokin tayi ciki da gudu,cikin kuka tana kiran ummanta.umma ta share do min tsohuwa tana cikin gida,kada tace tayi rashin kara,sai tsohuwa ne ta tashi da sauri tana fadin oyoyo takwara.suka qungume juna tace to menene kuma na kuka?umma ta fito nan fa ummi taje ta rungume ta.sai umma ta doje tace bubi shirme,sakar ni ni.tsohuwa tace haba suwaiba yarinya tana dokin, . Tsohuwa tace haba suwaiba yarinya tana dokin ganinki amma ki gwasale ta? abba ya ce daman nasan ba natsuwan da yarinyan nan tayi,har ina yabonta.dubi yanda ta xubarda kayan a soro.to xaki debo su.tsohuwa tace bari ni in debo mata tunda kai baka da tausayi.laile umma taga canji,do min ummi dai tunda ta dawo ko qofar gida bata fita ba,sai ko in an aike ta.sannan yanxu ba gudu da tsalle tsalle bare tsokana.ga aiki har girki ita kema umma komai.alhj yana shan shayi da safe,ummi ta yi sallama ta shiga. can gefen su umma ta xauna,sannan ta gaida alhj ta gaida umma wanda ta saka alhj agaba tana masa fira.wannan qa'idan umma ne bata barin mijinta shi kadai,in har yana gida.alhj yace suwaiba kinga ummina ko?laile abba yayi namijin qoqari. yarinya ta natsu.umma tace Allah ya amsa addu'an mu ka duba tsayuwan daran da muka dunga yi bayan tafiyan ta kan cewa Allah ya kintsa mana ita.alhj yace hakane,ummi dai na jinsu tana murmushi.can tace alhj anjima xanje gidan inna saratu in gaishe ta. qanwan sahura ce da ke aure a kabuga.ya ce to ummi, xanba umman ki kudin mota ko? ummi ta ce,to na gode.ta miqe ta fita ta bar mahaifanta cikin farin ciki jin dadin natsuwarta, suna godiya ga Allah mai shirya bayinsa.lkcn da ta shirya dan xuwa kabuga.sai umma tace ki kwana dan bana san ta fiyan yamma,kabuga da nisa.tace to sannan ta dauki kayanta kala guda, sannan ta fito.har xata wuce sai ta shiga gidan alhj qarami,sahura na ganinta ta hade rai,daman daqar take amsa gaisuwan ummi tunda ta dawo.ummi ta gaisheta a ciki ta amsa,sam ummi bata damu ba,tace umma ina fati?ta yatsine baki tace tana gidan abba,tace to inta xo ki ce mata naje kabuga sai gobe xan dawo.umman bashir tayi tsaki,tare da cewa ni yar aiken ki ne?ita dai ta wuce.tun dawowan ummi suke shiri da fati kamar me,ko yaushe suna tare suna fira.ummi tana mata labarin mkrtn su.ita kuma fati tana bata lbrn saurayin da tayi fahad,da irin son da take masa.ummi tace tab,ni ko xanyi saurayi nafi san irin ya abba...... . fati ta dubeta da al'ajabi kina nufin ya abba kike so?ummi ta xabura tana fadin tir, ko a mafarki Allah ya kyauta.ina nufin mai irin hirarsa da tsafta.fati ta qyalqyale da dariya tare da cewa ai na xaci shi kike cewa,inko ya ji kici duka ummi ta ce,ai ni ba ma da shi nake ba tab,shi da yayi auran so?kusan ko yaushe yanayin hiran tasu kenan.ummi tana tafe wadansu samari suka yi ta binta, sun shawo kanta ta tsaya da kyar,kuma har ta masu kwatancen gidansu. kwanaki uku bayan haka tana ki shingide kan kujeran dakin umma,misalin takwas saura ma dare.krtn wani littafi take yi na hausa da fati ta ara mata,sam ita bata taba krnt irin littafin ba,amma fati ta ce mata ta karanta da dadi sunan littafin NAGA TA KAINA na (sodangi).kasance wan wannan ne karo na farko da ta taba krnt lbrn soyayya,sai abin ya birgeta.amma nata ganin gwarxon sojan nan xai fi dacewa a ce abba ne, jefi jefi takan kalli abba da ke xaune kan kujera kusa da umma suna wani xance da bata jiyo su. 'Amma tasan ko me suke tattaunawa mai mahimmanci ne a gare su.sallamar wani yaro ne ya katse su,umma da abba suka amsa mishi a lkc gudu.yace wai ana kiran ummi a waje inji wadansu.da sauri abba ya kalla yaron,sam ba xai ce me yasa xance yaran ya fadar masa da gaba ba.sai ya lumshe ido sannan ya kalli ummi wadda kunya ta rufe kasancewar yau ce rana ta farko da aka soma yin sallama da ita.umma wadda kullum fatanta ummi ta samu miji,sai tayi murmushi,sannanta ce da yaron kace tana xuwa.abba ya dube ta da sauri, umma kin san ko su waye?ta ce, a'a.yace ya kamata a san ko su wanene dan kin san bata da kan gado,kowa ma sai ta jajibo kuma ma duk nawa ummin take da har xata soma tsayawa da samari?umma tace,to abba ai gara ta kama dahir, tana qare sakan dire ba sai ayi mata aure ba?yace gaskiya umma gara ta dan taba krt,dan yanxu xamani ne na krt.umma tace,tayi acan a dakinta.ta dubi ummi tasgi kije.ummi ta miqe ta fita.abba ya miqe shi ma,umma bari dai in gani ma su kamun kai ne? umma tace to.., . Sun gama gaisawa kenan sai ga abba ya fito.ganinsu tsaye da ummi sai ya tsinci kanshi cikin wani bacin rai.ya isa gun ya musu sallama, suka amsa, sannan suka gaisa.yace daga ina kuke? suka dube shi dayan ya ce lfy dai ko? ummi tayi karaf ta ce yayana ne.anan suka sake gaida abba.bai amsa ba, sai ma cewa yayi na tambeye ku kai ma kana tambayana,wai lfy? suka ce,kayi haquri,nan suka gabatar da sunansu.mai san ummi shine nazir, abokinsa kuma sagir. sun 3a masa cewa dukkansu daga kabuga suke.yace krt kuke ko kasuwanci? sagir yace,eh krt muke,amma muna taba kasuwanci a shagon mahaifinsa da ke kwari.abba ya dan yi jim,sannan yace to kai ka shirya aure ne?nazir yace eh to, nasan dai kafin a tashi yi mata aure na shirya.abba ya ce, to ita kam krt xata yi, kuma c ma buqatan ta hada krt da soyayya. ya dubi ummi da fatan xaki sallame su.ya juya gida.sagir ya ce, wannan wanki ne da gaske? ummi tace qwarai kuwa. nazir ya ce to yanxu ya kenan? kin ji abin da ya ce.ummi yayi shiru tana tunani, ita fa basu kwanta mata rai, tun randa ta hadu dasu,sam basu iya saka kaya kalar yadda ya abba ke sawa ba.dan haka sai tace, ina ganin xai fi mu haqura kada yaxo ni yayi ta mun fada.nazir ya ce yanxun haka xaki ce? ummi tace, um,sai da safenku.kada ku ja min duka.sagir cikin jin haushi ya ce,ki xama mangofak qarewan krt.sannan in kin gama wan naki ya aure ki. ita dai ta shige gida.kusa da soro ta iske umma da ya abba ta yo masa rakiya, tana kuma ba shi aaki kan cewa yayi ta haquri,tace ina fada maka ko yaushe ba fa fushi ko fada ne xai saka matarka a hanya ba.lallashi da nashiha,ka dunga koya mata giqki daka nutsu ka koya mata ba gashi ka ce ta iya daidai gwargwado ba?abba yace,hum lamarin yarinyan nan yayi nisa fa umma,wankan jikinta ni xan koya mata? sallah fa daga nake da ita.amma abin yaci tura.antynta sau nawa tana xuwa tai mata fada duk a cnxa,mkrtn ma ta qi xuwa.ni kuma da ce ruwanta.umma cikin al'ajabi tace, sallah! sallai ma bata san yi abba?abba yace umma baxan mata sharri ba... Ta ce Tabdi,to kuwa ba kuwa kazantarta ta wuce jiki hr d zcy. wannan ita ce kazanta mafi muni. Don haka dole ne ka zage damtse don ganin ta kama sallah,to menene marabar arne d Muslmi in ba Sallah ba?Abba ya ce Umma na mata nasiha na gaji. Ta ce To kasa ta a mkrntr Islamiyya,kila ta ji tsoran Allah in tana jin Wa'azi. Sannan ka dainga siyo mata kasasuwan wa'azi.Abba ya ce Umma kaset nawa na kawo mata bata sakawa,Kullum sai indiya da Hausa fim,in naki sayan man fetur in tana da kudi ta saya. In kuma ba a ta da shi sai ta dauki ittafin Hausa ta dukufa.umma ta ce Allah ya kyauta,kaje kayi ta hkr tare da addu'a. Ya kalli Ummi,sannan ya ce ma umma,kada ta sake fita gurin wadanan kananan yaran,sannan ya fita. A daki umma take tambayar Ummi daga ina suke? Ta ce um,Umma kyale su ni sam ma ba su min ba. Umma ta ce to Allah dai ya miki za6i nagari. Abba yana kwance a dakinsa ya yi lamo cikin bargo,ya kasa amsa ma kanshi tarin tambayoyin da ke yawo cikin kanshi. Haka tambayoyi suke zuwa masa daya-bayan-daya ,me yasa ya damu da lamarin Ummi??me yasa da a ka yi sallama da ita ya samu kanshi cikin wani tashin Hankali? Me ya sa ranar da zai je mata ziyara ya za6i ya sai mata kayan kwalliya? A fili ya ce,don tana kanwata.Zuciyarshi ta ki amincewa da haka. Me yake shirin faruwa da ni ne? ya fada a fili. Ya yi juyi zuwa rigingine,sannan ya dauki filo ya manna a kirjinshi, ya ci gaba da magana shi daya. Bana zaton cewa Son Ummi nake yi.don lkcn da na yi tsananin Son Bishira bn ta6a samun kaina cikin wannan yanayin ba. Kai Allah ya tsare ni da Son ummi,wannan mahaukaciyar yarinyar..........bugun kofarshi da a ke yi ne ya katse shi. Murayar Bishira ce ta na cewa Babn Walid!Babn Walid!! Ya bude kofar da sauri,ta ce Walid ne ke ta amai. Ya fita ya dauki yaron daga hannunta yana fadin Me zai hana shi amai,in ba a ci sa'a ba har zawo sai ya yi,Saboda kazantarki.Sam ba ki lura da me zai wawuro ya tura bakinsa. Ta ce Yau fa bai ci komai ba,tun da safe yake wannan aman.Ya ce shi ne ba ki sanar da ni ba?Ya cire masa kayan jikinsa wadanda ya ji suna ta doka karni.. . Ya isa igiyar shanya ya ciri wasu yasa masa,sannan ya fita dashi.Wani babban kyamis ya tafi da shi,mai kyamis din likita ne,sai dai ba na yara ba ne,amma kowa yazo sai ya duba shi.Nan dai ya masa bayani ya ba su magunguna. Sha biyu dai dai ya dawo,tana zaune tana kallo ya ce "A'uzubillahi,wai ke kallon nan masifa ya zamarmiki ne?to ki sani na kusan fita da kayan kallon nan. Ta ce,Tab,ka kaisu ina? dadinta dai dafa gidan ubana a ka kawo su. Ya ce ta za su koma gidan uban naki. Ta dafe kirji "Zagina ka ke yi?ya dora mata dan a jiki "An zage ki,ke din banza,kazama!yazube mata maganguna ya fita. Ya jima zaune a kofar gidanshi dafe da kai,yana tunanin shin wai shi kadai ne bai yi sa'ar mata ba,ko kuwa duk maza ne.Ya tuna abokanshi 2 da suka yi aure. Muktar d Jamilu,sam ba su da wannan matsalar,duk lkcn da yaje gidansu tsaf matansu,ga mutunci da mutanta mutane. Shi kuma a cikin abokanshi babu mai zuwa gidan sbd bata gainin kowa da gashi. 'Yan uwanshi sai wanda ta za6a sannan zata yi hulda da su. 'Yan garinsu kuwa can ¤ZAMFARA¤In suka zo kiri- kiri take nuna musu kyama ga rowa,sam bata hulda da matan abokanshi. Ya numfasa zai bi shawarar Umma ya gani, amma gaskiya Bishira ba matar zama ba ce. Tun da ya dawo sallarAsubahi dakinta ya shiga tana ta shirga bacci. Walid kuma ya yi faca-faca cikin kashi ya tausasa zuciyarshi ya ce "Bishira! . Bishira!!Ya dan duki kafarta,sannan ta tashi. Ya ce Ki tashi ki gyara masa jiki kiyi sallah.Ta ce,Tab, me ya yi?ya ce, "kashi ya yi.kurum sai ya ji ta ce Tab,wannan akwai dan iskan yaro.Yanzun dan ubanka kashi ka min? Sam bai san lkcn da ya watsa mata mari a baki ba,cikin murya mai karfi ya ce "kada ki kuskura ki sake ce ma dana dan iska!kar ki sake zagar min yaro kada ki yi wa dana baki.Ba zan dauki wannan ba. . Ta mike daga kan gadon tana kuka Ni ka daka? wlh sai na rama. Kasancewar lebe baya raina duka,sai jini.Nan da nan sai kumburi. Ta cakumo shi,wlh sai na rama.Ya hankadata kan gado ya bar gidan.cikin zcyrshi yana fadin ,"Wannan fitina da me tayi kama? Ita kam ruwa ta dafa sannan ta wa yaron wanka, cukuikuiye zanin gadon ta saka shi cikin baho,sannan tayi kwaskwarima ta sabi danta baki suntum ta nufi gida tana kuka. Mahaifinta bai nan yana Abuja,Hjy Zainu ta kalle ta bayan ta gama kero karyarta. Wai don yaro ya yi kashi ta ce yaron bai kyauta ba shine ya hau ta da duka da zagi. Hjy Zainu ta ce Amma wannan da muciya ya dake ki ko?ta ce, Da hannu ne,nushina fa ya dinga yi. Hjy Zainu ta ce Ai kin gani ba yadda ba a yi ba ki tsaya kiyi karatunki kin ki,kin kafe sai kin aure shi,wannan matsiyacin? Dama talaka yana da wannan tsiyar.Yanzun za ki zauna mu jiraZuwan Alhj,ba za ki koma ba.Ya dai baki takardarki in yaso ki koma mkrnt.Su kuma su dauki dan nasu. Bishira dai tayi shiru,zcyrta tana jinjina rabuwa da Abba d kuma danata. Abba kam gidansu ya nufa.Ummi ya soma cin karo da ita tana sanye da doguwar rigar bacci,ta dora rigar sanyu ta sakar ulu, a kai tana wanke baki da busushi. Ta dube shi,mmkn ganinshi tayi a wannan lkcn.Sai da ta dauraye baki sannan ta ce masa sannu da zuwa,ya amsa a hnkl bai san mai yasa ya kasa dauke idanunshi daga kanta ba,hr ta gama alwala tayi addu a ta mike. Ta dube shi da niyar yin magana,amma sai ta fasa don tana tsoron kada ya daka mata tsawa. Ta daga labulan dakin Umma zata shiga. Ya ce, "Ke!' ta waiwayo cikin hada rai,domin ta tsani kiranta da yake da ke!Ya ce Ummana fa?ta kalli dakin Alhj Ba ta fito ba,,Ta shige ta zura hijabi ta tada Sallah. Ya shiga dakin ya zauna,yana kallonta tana Sallah zcyrshi tana nazarin Rayuwar Ummarshi. Tun tasowarshi ya ke ganin kulawa da kyautatawa da take yiwa Alhj Babba ga biyya, sam bata wasa da dk wani abu nashi daga lkcn da ya shigo gida ta gama sauraron kowa sai lkcn da ya fita. Bai ta6a jin sunyi sa'in-sa ba bare ta daga murya sama da tasa.Shin sauran matan ba su fahimci irin wannan ladabi ba ne?Ummi tana addu'a zcyrta cike da tunanin shi kuma ya Abba me ya kawo shi da wannan sassafen? Muryar Umma suka ji daga waje tana cewa,"Ummi in kin idae ki fito ki share gidannan,ki wanke bayi,Ummi ta ce To''. Sam Umma ba ta san Abba ya shigo ba,dmn da ta ba Ummi umurni sai ta sake komawa dakin mijinta, Ummi ta wanke bayi kansu,sannan ta share ko ina na gidan, ta kunna risho ta dora ruwan karyawa, sannan ta shiga firar doya. Gyangyadi yake daga zaunw, Muryar Ummanshi ce ta farkar da shi tana cewa, "A'aha! ya bude ido cike da bacci.ZURFIN CIKI book 2 part 4 ZURFIN CIKI book 2 part 4 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 22:10 "A'aha! ya bude ido cike da bacci. Ya kalle ta tare da yin mika,ta ce "Lafiya"? Ya ce,Umma lfyr kenan.Ta zauna da sauri Me ya faru Kuma? Yayi dan tsaki,umma na gaji da auran nan ina ga wannan karan xan yar da qwallon mangwaro in huta ta quda. umma ta ce abba! abba!! me yasa baka da haquri? ban xace ka haka ba abba,ina ce jiyannan ka min alqawarin kawo qarshen duk wata matsala tsakaninka da matanka?shin ban fada maka hanyoyin da xaka bi ka xauna da matarka lfy ba?ya kamo hannun ta,umma ba na san bata ranki, ban san yadda xanyi da halin yarinyan nan ba ne. jiya fa ina kwance taxo tace min yarona amai naje kai shi kyamis,ina dawowa na samu ta xauna tana kallon,ina mata magana ta hayayyaqo min da asuba na tashe ta sallah,wai dan yayi kashi shine ta hau xagin yaron nan,wai dan iska. ni ko na bige mata baki har da cukume ni da dambe fa.umma tace kaine harda duka abba? dukan mace?ta xuba tagumi tana kallon shi,ya ce umma xaginshi fa tayi,kuma kin san dai ba kyau uwa ta dinga xagin danta.dan ba haka kikai min tarbiyya ba.kalli rashin ji irin na ummi, amma ban taba jin kin ce mata yar iska ba.tace to ba sai ka xaunar da ita cikin tsanaki ba?? . Yayi shiru a xuciyarshi fadi yake umma ba xata fahinta ba.tace, tashi kaje ka bata haquri, ka lallasheta.matafa sai haquri,kasan da qashin haqarqari aka yi su,dole ka ganta a karka ce.saidai nasiha da lallashi,da xaran ka ce kan dole xaka miqar da ita,sai ta karye.nan dai ta yi ta ma abba fada, har sai da shi kanshi yaga cewa eh,yayi saurin fushi.dan haka ya miqe ya nufi gida da nufin bata baki.sai dai kuma kash! lkcn da yaxo tuni tana gidansu.ya dawo ya sanar da umma, tace to dole sai alhj yaji kenan.ta shiga gun alhj yana shirin fita. yace yau dai suwaiba akwai abin da ya dauke miki hankali daga kaina ko? tace, me kagani? yace tunda kika fita ban kuma jin duriyarki ba, hatta karin kumallo yau uwata ce ta kawo min.ko taya ni shafa mai yau ban samu ba, tace uhum, abba ne in gaya maka na gani hankalinshi a duk tashe, matsala ce suka samu da matarshi,wai ta yi yaji.alhj yace,yaji? umma tace eh wai a ce kamar abba bai san yadda xai yi haquri da mace ba, alhj yace ina abban?ta ce yana daki yana karya wa. Ya ce kira min shi.abba ya xauna ya xayyane ma alhj komai duk abubuwan da ke faruwa wanda take masa,hatta batun sallah da bata san yi duk ya fadia.alhj yayi shiru,can ya ce in ko haka ne ba qaramin haquri kake yi ba, amma kaje xamu je gidan.abba ya ce, ni dama xa a baita can dana huta.alhj yace ba xa

Chapter 8 of 24