Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taso zuwa amma suka ce ba wuri ta bar shi kawai. Asibitin kudi ne kuma likita guda ne ya duba su. Ummi dai hawan jini ne don ita a ka fara dubawa. Gado likitan ya bata,sannan Abba ya shiga shima likitan ya ce jininsa ya hau,amma ba kamar nata ba. Nan ya roki likitan cewa kada ya fada ma iyayensu abnda ke damunsa,ya rubuta mishi magunguna kawai. Likitan ya ce Ba komai. Amma me ya ke damunku kai da sister dinka ciwonku iri daya kuma ya kama ku a lkc daya? Abba ya ce Ba komai lalura ce kawai a ka kaddara ta same su lkc daya.Da Abba ya fito sai ya ce ma su Alhj Zazza6i ne. sai dai shi kanshi ya ji mmkn ciwonsu iri daya. Yana jingine da bango a dakin da a ka ba Ummi gado,yayin da Bashir ya tsaya a gabn gadon Umma tana zaune a kan kujera. Alhj krm d Bbba suka shigo tare da Likitan ya kalli Abba Yarona kana bukatar bacci ga. Abba ya ce To yanzun zan tafi gida. Ya iso kan Ummi wadda a ka daura ma ruwa,ya ce ku barta ta huta bata bukatar hayaniya,don haka ku rage daga cikin dakin. Alhji ya ce, To mun gode. Suka tafi suka bar Umma. A mota Alhj ya ce da Abba,ka fada a wurin ainkan? ya ce, Eh abokin aikina ya kira ni kuma na fada masa. Alhj ya ce,To shi kenan,yanzun sai muje can gidanmu zaka fi hutawa... .Yanayin aikinku ne ba ka samun bacci ko? eh kurum Abba ya ce,amma shi yasan tunanin Ummi ne ya ke hana shi bacci da matsalolin da yake hangowa. Yinin ranar yasha bacci,sai kusan 4 ya tashi ya yi Sallah,ya ji dadin jikinshi. Bishira tana gidan Umman Bashir wai ita da tazo jinyar miji,tana bata lbrn wai Abba bai fada mata ba shi da lfy ba,ya kira Alhj yazo yana ta min surutai wai mijina ya fita ban sani ba,meye- meye? Umman Bashir ta ce, Da Allah kyale su,don wani sabon iskanci ma wai Bashi ne ke son Ummi. Bishira ta mike zumbur tare da cewa, Bashir fa ki ka ce Umma? Hu'um,lallai da wani abu. Bashi da ya tsani Ummi shi ne zai ce yana sonta? Umma ta ce, Sannu 'yar albarja,ashe kin fahimta,? Tabbas nasan ke za ki fahimta,to in gaya miki Bashir ko yau da safe fa sai da muka yi ta dashi. Dubi yadda Bashir ke min biyayya amma yau ina fada yana fada. wai hr da ce min shi bai ga wani mugun halin Suwaiba da nike fada ba,tana min alkairi amma ni kullum ina binta da sharri. Kai dai jin wannan zancan ka san ba yin Bashir ba ne,don haka na ce masa ba komai nasan ba yin ka ba ne. Bishira ta ce,Tabdi,Umma sai kin tashi tsaye. Ta ce ke dai bari ai ina cikin wani hali shi kanshi miji naki sai na nema masa taimako. Don wannan ciwon nashi ban yarda shi ba, kuma lkcn daya. Fati ta shigo gidan da sallama,ta shiga dakinsu ta canza kaya. Umma ta ce,sai ina? ta ce Ya Abba ne ya ce in zo in canza kaya zamu je asibiti wurin Ummi. Bishira ta mike ya farka ne? Ta ce Eh hr ya yi wanka da sallah Umma ta ce Bari in same shi bai gama jin sauki ba zai tafi wurin wata can kema banza mara kishi kin taho jiki Na 6ari,Fati ta ce,Umma don Allah ki daina irin wannan abubuwan,wlh Umman su Ummi bata yin haka Bishira ta fita tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3 Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta ce, Ni a wa zan shiga maka ga . Bishira ta fita tana fadin Ai Ummi yanzun ita ce uwar Fati, don bata jin mgnr kowa sai ta Ummi,tunda ta dawo mkrnt. Sun samu Tsohuwa ma hr ta shiga mota,shi kuma Abba yana jingine a jikin Motar yana sanye da shadda (Sky blue) Rigar 'yar 3 Quarter kanshi da hula. Bishira ta ce,Babn Walid hr ka tashi? ya dube ta,sannan ya kai idanunshi kan fati Shiga muje. Bishira taja baya Ina ba in da za ni. Ya kalleta ke Kuma ke da wa? Wa ya fada miki da ke nake? yaja tsaki. Ta iso Ummar tasu Abba ka hakura mana da wannan tafiyar. Ta ce Naji sauki Umma. Tsohuwa ta ce, Mai sunan Malam ka shiga don Allah mu tafi. cikin sauri ya fada mota suka wuce. Yana yi wa Umman nuni da Hannu wai yana zuwa. Tsohuwa ta ce,Kinibibin banza ne da wannan matar taka mai sunan Malam kana bukata kara aure,me a ke da kazamar mace? Abba ya ce, Tsohuwa sha kuruminki zan sake aure,ke ce ma za ki bani, Ta ce, Ni a wa zan shiga maka gaba a baka ku taru kai da matarka ku halakata?Duk da Abba yana jin jikinshi gim, sai da ya dar dara,sannan ya ce, Sai ka ce ma su yankan kai? Tsohuwa kuma da za ki ce na cika zcy yanzun ba ga mata nan ina da ita ba tana kawo miki karan ina dukanta ne? Tsohuwa ta ce Tabdi,ni yaushe ma wannan guzumar matar taka zata zo guna da sunan kawo min kara? Ban da ma haka ni bani shi da mara kunya. Ya ce, sai Ummi ko? koda yake ita ai takwararki ce shi yasa lkcn da tayi tata rashin kunya ta zama 'yar lelanki. Tsohuwa ta ce ai wannan ba kuciya ba ce? Yanzun ko kai ba ka fi ta hankali ba.Abba da fati suka sa dry. suna isa dakin suka samu Umma suna waya da Alhj,Ummi kowa hr lkcn bacci take yi. Abba ya jingina da bango yayin da Tsohuwa da Fati suka je suka tsaya a gabn gadon. Sunyi Sallama da Alhj shi ma ya kira ne ya ji ko Ummi ta farka. Ta ce masa ba ta farka ba,kuma Likitan ya ce an fi son tayi baccin. Nan suka gaisa tare da tambayar mai jiki,Abba kallon Ummi yake,yau daya duk ta fyade kmr ta yi sati,sonta da tsananin kaunarta ne suka sake mamaye ko'ina na jikinshi. Ya kalli Umma wadda ke tambayar nashi jikin, ya ce da sauki. Sannan ya kalli Ummi tare da cewa Umma wai dame Ummi ta fara? Umma ta ce kamar ya ya? Ya ce mmkn ciwon Ummi nake,wai hawan jini?Dama can bata da lfy ne? Tsohuwa ta amshe da cewa, ko kai ai kasa mata hawan jini,irin tsanar da ka mata Mai sunan Malam ai ta isa. Abba ya ce Don Allah Tsohuwa ki daina mgnr nan. Ya dubi Umma yana me kara maimaita tambayarshi. Ta ce ko kusa ai kasan Ummi bata cika laulayi ba ma,lalura ce dai yanzun bata ga babba ba ta ga yaro,amma mafari daga yi mata zancen aure shi kenan take ta kuka. Abba ya ce to don Allah Umma ku barta da zancen nan,ina krtn take so tayi kayanta,don gudun hawan jinin nan kada yakw tashi akai-akai. Tsohuwa ta ce Don kawai kada jinita ya hau sai a zura mata ido kada tayi aure?ai ko lallai sai dai kada jininta ya sauka. in ya hau,aure ya haifeta dole tayi shi,in a kasarmu ce ta Zamfara wane ita. . Abba ya ce Muje in kai ki gidan Tsohuwa. Ta ce ban tafiya, sai naga dama Umma da fati suna ta musu dry. Nan dai Abba ya fita yaje wurin likitan ya amshi takardn maganin,dn da farko bai rubuta ba magaungunan ba. Kwanan Ummi 3 a asibiti a ka sallem ta. Abba ya kwashe su zuwa gida. Saurayinta Sahabi zuwanshi 2, kuma sun je da mahaifiyarshi. sai lkcn ne ma ta mishi kallon tsaff,sam ita ba sonshi take yi ba,sai dai gara shi da Bashir. Kuma ta lura Bashir din da gaske yake yi. Domin kullum zai zo safe da yamma,haka nan yakan dan tsaya hr yafi Abba wanda ke zuwa sau daya hr tana cewa ina ma yadda Bashir ke nuna tausayinshi a gare ta Abba ne. An shuri sati 2 da sallamo ta kuma ta warke sarai,sai dai fa hr yanzun Alhj yana nan kan bakanshi,ganin Bashir na son takura mata sai ta daina fita. Abba ya kira Basshir shagonshi wani yammaci,ya sake fada masa ya rabu da Ummi sai dai yau da lallashi yazo masa,. Ya ce Bashir ka ga mahaifiyarmu bata sonka da ummi,dn haka ka hkr ka nemi wata,na maka alwashin kashe ko nawa ne dn yin hakan zai faranta ran Umma. Bashir ya yi 'yar dry,sannan ya mike tsaye Ya Abba kenan! kana tsammanin ni wawa ne?nasan ba don Umma ka ke fafutukar in bar Ummi ba kana yi ne don kana sonta. Gaban Abba ya fadi,cikin saurin baki Abba ya ce,In ji wa ya fada maka? Allah ya kiyaye. kai ka san Ummi kanwa na dauke ta. Bashir ya kakki cikin idon Abba,sannan ya ce,"Haba Malam,fadan da ka ke da kalaman da ka ke furtawa suna nuna kishinka ne karara. Dubi cikin idanunka,kishinUmmi ka ke yi. don haka sai ka hkr ka bar min ita,domin ka san ba wanda zai fi girgiza Umma tsakanina da kai irin ka. Ya nuna Abba da yatsa, Za tafi bakin ciki ka zama mijin Ummi fiye da ni. Abba ya daga hannu ya falla mishi mari Bashir ya dafe wurin sannan ya kalli sau 'yan shagon wadanda marin ya janyo hankalinsu. Don farko ba su san abn da a ke tattaunawa ba.Bashir ya ce, ka mare ni? Abba ya ce, Zan kara maka,ko za ka rama ne? Bashir ya ce, Ba zan rama ba,amma zan fada ma su Alhj yau dinnan ina son Ummi. ya fita fuu. Abba ya zauna ya rike kai yana huci. shi kam Bashir ya kudurci niyyar fada wa iyayensu yau dinnan. Abba ya kira wayar Umma ta daga suka gaisa lkcn karfe 6 na yamma ya ce, Ummi fa? ta ce Gata can kwance. Ya ce Ba dai jikin ba? ta ce A" aikin karance-karancenta take. Ya ce, Ba ni ita Umma. Umma ta kwala ma Ummi kira,ta mika mata wayar tare da cewa "Yanyanki ne ke son magana da ke. Yau ce rana ta farko da suka yi waya a matsayin shi na Abba,ita kuma Ummi, in an debe lkcn da suka yi waya a matsayin shi na Abba ita kuma Suhailat. Tayi sallama cikin sanyi murya can kasan makoshinta ya amsa tare da runtse ido sakamakon tsigar jikinshi da ta tashi. Ya ce "Ummi ta ce Na'am yaya. Ya ce "Kina son Bashir? ta raunana murya. Yaya am sorry to say bana son shin gsky. Ya ce To yau kam zai sanar da su Alhj cewa yana sonki,in kina san kida wanda ki ke so to ki gabatar da shi kafin shi ya rigaki. Takaici ya kama ta, kamar ta ce, Ni kai na ke so.......ya ce kina jina? ta ce,To Ya ce, kin san in su Alhj suka ji ba ki da mafita,Ummi ta ce To ni fa bani da wanda nake so shi ne ban san yadda zan yi ba. Ya ce, shi kenan matsalarki ce., ya kashe wayar. Ummi tayi shiru tana tunanin mafita,ko dai ta hkr ne ta aure Bashir din? kai a'a to kuma gashi wanda take so ya ce matsalarta ce. Can dai ta yanke yadda zata yi,don haka ta kosa Alhj ya dawo. Tun kafin suje wurin cin abnci ta same su a dakinshi su da Umma,ya yii wanka yana kokarin fita sallar magriba. Ta ce Alhj dama wanda ya ke zuwa gurina ne ya ce in fada muku iyayenshi za su zo. Dadi ya kashe Alhj ya ce To to dan nan unguwar ne? ta ce Eh ya ce To madallah dama wannan yaron na sabon titi din nan Suwaiba wanda kwanaki nake fada miki nasan ubansa a kasuwarmu ya ke? Ta ce Naji wanda ya soma zuwa wurin Ummi? ya ce Shifa, Uban danai masa zancen naga dansa wurin 'yata sai cewa ya yi auran gida za su yi masa,ko ni na so hadin nan sai dai Allah bai so ba. Ya kalli Ummi Yaushe za su zo? ta ce Ya dai ce in tambaya ne. Alhj ya ce To Allah ya kawo su. Da dare Sahabi yazo ta ce Sahabi an ce in maka mgn ka turo ya ce Alhamdulillah, dama ina son in miki mgn sai ina tsoron kada ki ce ya yi wuri don haka gabe zan turo. Bashir yazo ya zauna gabn Alhj suna cin abnci ya gaishe su. Suka amsa ya yi shiru yana tunanin ta ina zai fara? Alhj Babba ya ce ya ya Bashir akwai wata matsala ne?Ya ce Am dama ina son in ce ni dai ina son Ummi ne. Ummi kuma?Alhj karami?Ya ce Eh Alhj Babba ya ce Ta amma ya aka yi kayi nauyin baki hr a ka ba wani dama? Bashir ya ce Alhj Wanene? Alhj karami ya ce Sai ka san shi? koda ba a tambaya ba, ba zan ba da goyon baya a baka Ummii ba, tashi ka bamu wuri. Abba ya ce, Bashir je ka ci gaba da addu'a Allah yasa Ummi ta zam rabinka,zan so haka dn na jima ina son zumuncin nan. Iyayen Sahabi sun zo kuma an basu hr ma an tsaida ranar daya fa ta Fati. Tun daga ranar Ummi kullum cikin kuka take wanda iyayenta suka kasa gane nufinta. Bashir bai daina cin alwashin sai ya auri Ummi ba, dn haka kullum cikin aiken kiranta yake. Ban da haka ma ya maida hnkl kan sana'arshi tunda ubansa ya mishi gorin wa zai ba shi mata ya ki tsayawa sana'a nashi ganin in ya rike sana'a r za a ba shi. Abba kuwa ya ji ya yi ma gidan wai don ya goge Ummi a ranshi. Anya "ZURFIN CIKIN nan zai kai su? . Sai mu hadu a littafi na Uku don jin yadda za a kare. ZURFIN CIKI book 3 part 1 ZURFIN CIKI book 3 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:21 Na Halima Abdullahi K/Mashi 1... Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je gaisheta." Ahankali yake tukin, kira'ar Ahmed Suleiman ce ke tashi wadda ya yi murya biyu cikin sanyin murya. Wayarshi d ake gefe ta soma ruri. Ya kali fuskar wayar, Hajiya Nina ce, don haka ya ci gaba da tukinshi, kusan kira na bakwai sannan ya daga. Ta ce, "Lokacinka ne za ka iya yin duk yanda kaso, amma kafin kazo hannuna wacce shawara ka yanke?" ya ce, "Ta me?" Ta ce, "Au, ka manta kenan? To ba damuwa za ka zo yau ne ko sai an dauko ka?" 2.... 'Yar dariya ta kufce masa, "Ki sa a dauko ni sai ka ce wani karamin yaro? In kin ci gaba da bibiyata za kiyi nadamar hakan." Ta ce, "Ko kuma kai kayi ba, na baka awa goma ka kawo kanka in ko ka 'ki, hum! Za a kawo ka." Abba yaja tsaki "Yanda ki ke zatona na wuce haka". Ta ce, "Idris Aminu Idris raina ya biya da kai, kuma dole sai na cimma hakan, jarumtarka din nan ta sake bige ni, kasan dalilin da yasa na ce nan da awa goma? In ka lissafa zai baka bakwai na yamma. Daidai lokacin da ake watso mana labarai ina kwadayin ina tare da kai, lokaci guda kuma ina kallonka cikin TV kana feso turanci, kasan ina son muryarka ga shi ka gwanance da iya tsara turanci, sai ka ce yarenka. Kada in cika ka da surutu sai mun hadu anjiman". Ta kashe wayarta. Abba yayi kokari ya tsaida motar shi a gefen titi a hankali ya furta "Allahumma ajir ni fi musibati..." ya kifa kansa a jikin sitiyarin motar, yana tunanin wai shin ba za ta sauya masa a halin da yake ciki ba? Wata zuciyar ta ce in tasan kana cikin wani halin ko? A haka ya isa gurin aikinsa, tunda suka shiga dakin daukar labarai, abokanshi suka gane yana cikin wani hali duk da bai kasance mai yawan magana ba, amma yau ba kamar kullum ba. Salis ne ya kasa hakuri, don haka bayan an gama daukar labarai da kyar sun je su yi sallar Azahar suna zaune wata Bafulatana da ke kawo musu fura ta kawo. 3..... Dama shi Abba bai cika shan fura da rana ba, yafi shanta da dare, don haka siyan kurum yake yi. Bayan yaje gida sai yasha, amma ranar ya ce mata ta bar shi kawai, ta jiya ma tana nan bai sha ba. Da ta tafi Salis ya dube shi, "Idris ba ka da lafiya ne?" Ya ce, "A'a me ka gani?" Ya ce "Ba yanda ka saba ba, duk kwanakin nan na lura kana cikin damuwa". Abba ya dube shi amma ai kasan nayi rashin lafiya ko? Salis ya ce dakata Idris kada kaga kamar na matsa maka sai na ji cikinka, ko kusa ba haka ba ne. Ni mutum ne mai saurin karantar duk dan Adam din dana zauna kusa da shi na awa daya bare kai da na zauna da kai tsawon lokaci, muna kuma ci gaba da zama. Idris na fahimci kana da matukar 'ZURFIN CIKI' dalili kenan da yasa ban ta6a damuwa da in tambaye ka matsalarka ba. Sannan dalilin 'ZURFIN CIKIN' da naga kana da shi ne yasa har kwanakin baya na kawo maka matsalata da iyalina. Alhamdulillahi ka bani shawara kuma nayi amfani da ita, kuma naga ci gaba, matsalolina sun ragu". Abba yayi dan murmushi. "Wai kana nufin saboda ina da 'ZURFIN CIKI' ne kaga ya dace ka sanar da ni sirrinka?" Salis ya ce "Kusan haka ne, don me Zurfin Ciki ya iya hadiye magana, sai dai a ganina zurfin ciki wataran zai iya fadawa halaka, ko wata gagarumar matsala". Abba ya dube shi, "Wace irin halaka? Salis ya ce, "Me zurfin ciki sai ciwon zuciya ya kama shi yana muku-muku da matsalarshi, wani ma har ya mutu da ita ba wanda ya sani. Amma in abu na cinka ka samu wanda ka yarda da shi mai amana ka fada masa zaka ji dan dadi". Abba ya ce, "To kai tunda baka da zurfin ciki, kenan bai dace ka ji matsalar ba?" 4....Salis ya tuntsire da dariya, "Ta nan ka 6ullo? Ai dama ka sani ba ina son yabon kaina ba ne, a'a duk surutuna nasan abinda nake fadi". Abba ya ce, "Salis na gode da kulawarka, matsalata ko ka ji ta nasan shawarar da za ka bani bata wuce ka ce in yi hakuri ba, ni kuma ba wannan ni ke son ji ba. Salis ba komai nake yiwa 'ZURFIN CIKI' ba, yawanci in ina da matsala nakan tunkari Ummata ne kuma ta warware min komai. Saboda na taso da wannan koyin da ta min, yanda na shaku da ita ko su Alhajina ba mu shaku haka ba". Salis ya ce, "To me ya hana ka fada mata wannan karon?" Abba ya ce, "Ba zan iya ba, sai dai in za ka samo min mafita ban da hakuri, to in fada maka". Salis ya ce "In sha Allah ba za arasa mafita ba". Nan Abba ya bai wa Salis labarinshi da Ummi tun farko har zuwa yau. Salis ya numfasa, sannan ya ce "Kaga illar 'ZURFIN CIKI' ko? Ummin ma taka ce amma kana nema ka rasata, ai ba mafitar da ta wuce ka samu Ummarka ko Alhajinka ka fada musu muradinka". Abba ya ce, "Tabbas haka ce mafita, sai dai idan na aikata haka abu biyu za su faru, na farko na zubar da mutuncin Alhajina, domin babu girma, sun ba da 'ya ba tare da wani dalili ba ya ce ya fasa. Sannan haramun ne neman aure cikin aure". Salis ya ce, "Haka ne, to hakurin kawai zaka yi". Abba ya ce "Ai mun yi ban da bada hakuri ko?" Salis ya saki dariya, sannan ya ce "To kayi addu'a". Abba ya mike tare da fadin "Ka tayani da addu'a". Daga nan ya shiga dakin, Filin Don Matasa na Hausa, don likkafar shirin tayi gaba yanzu har na Hausa yana gabatarwa. Kullum sake kar6uwa shirin yake a gurin Jama'a. 5......UMMI Tana kwance kan doguwar kujera, yau kwana hudu kenan bata saka Abba a idonta ba. Tamkar Umma ta san abinda ke ranta, sai ta tsinkayi Umma na cewa "Yau kwana uku ne ko hudu rabon Abba da gidan nan, sai dai ya kira mu a waya. Alhaji dai ya ce, yana zuwa gunsa kasuwa". Ummi ta ce, "Nima yanzun nake tunanin haka". Ta miko ma Ummi wayarta da ke gefenta. "Lalubo min shi in ji". Da ta soma /ringing/ sai ta mika mata. Ya dauka suka gaisa ta ce "Abba ko dai na maka laifi ne?" Ya ce, "Umma me a ka yi?" Ta ce, "Tsaf, ka dauke min kafa, wanda kullum komai saurinka sai ka biyo". Ya ce, "Ina nan zuwa Ummata, kina raina duk inda nabi, harkoki ne suka taru suka sa ni gaba". Ta ce, "Ni kuma sai na ke ganin kamar don ba mu dauki shawararka ba ne ta game da karatun Ummi shi yasa ka". Ya ce, "Umma ba haka ba ne, zan shigo da zarar na dawo". Ta ce. "To". Sam shi batun shi yayi ba, sai dai baya son yazo ya ga Ummi domin da ya ganta yake neman kwanciyar hankalinsa ya rasa na tsawon lokaci. Amma yanzun kalmar Salis ta karshe daya fafa masa da za su rabu a gurin aiki ita yake tunawa. Dafa shi ya yi tare da cewa "Miste Man shawara ta karshe, ka nunawa kanwarka kana sonta a fili". Ya ce "Tab, wannan shi ne me wahalar ai, furtawa Ummi kalmar so. Zubar da kai kenan". Ga shi ba sonsa take ba, duk yanda mace ke girmamaka da zaran ka ce kana sonta shi kenan ka zube a idonta. Musamman in kai ke sonta ita ba ta sonka, wata ma har da rashin kunya zata tsula maka, a fili ya ce, "Ina, ai ba zan ta6a gigin bari ta san ina sonta ba". Daga kasan zuciyarshi yaji an ce za ko ka sarata. Sai da ya yi sallar Isha'i sannan ya yi wanka ya saka kananan kaya, ya fito da nufin gidan su Ummarshi. Bishira ta bishi da kallo, daga ganin fita zai yi ta fito da saurinta tana cewa "Baban Walid! Baban Walid!!." Ya tsaya, ta dube shi "Ina za ka?" Ya ce "Gidan su Umma". Ta ce, "Ba wani gidansu Umma, kai dai kurum tadi za ka je". 6.... Dariya ta su6uce masa, sai da ya dara sannan ya ce "To in ma tadin zan je ya za ki yi dani?". Ta ce, "Tab!, ai na rantse maka kayi kadan. Kullum kuma ina 'kara fada maka kai mijin mace daya ne rak!" Ya ce, "In ji ki ko?" ta ce, "Eh." Ya ture ta gefe tare da cewa "Da sauki tunda ba fadin Allah ba ne". Yayi ficewarsa ya barta nan tana ta masifarta. Kan dakalin kofar gidan, Ummi ce zaune da Sahabi suna hira, duk da cewa Sahabin shi kadai ke ta surutanshi Ummi na can duniyar tunanin abinda zuciyarta ke so. Tun daga nesa ta shaki kamshin turaransa, zaraf ta mike tsaye. So take ta kalli fuskarshi amma ya dauke kanshi daga gare su. Haka nan ya share sannun da zuwan da ta ke mishi tare da shigewa cikin gida abinsa. Sahabi ya ce, "Ya Abba na nan kuwa kwana biyu na rabu da ganinshi?" Ta dauke kai sannan ta ce "Zan tafi gida". Ya ce, "Haba Ummi, zuwana fa kenan?" Ta dube shi. Ji take tamkar ta sheka mishi mari, ta ce "To kaina ciwo yake yi, sannan kuma ga Ya Abba yazo baya son ina dadewa a waje". Ya ce, "To shi kenan sai gobe?" Ta ce, "Don Allah kada kazo gobe, ka bari sai jibi". Ya ce "Za ki azabtar da ni, ba zan iya kwana biyu ban gan ki ba." Maimaikon taji dadin kalmar, sai taji takaici ya mamayeta. A ranta ta ce,, "Tunda ga gyatumarka ba". Ya ce, "In zo goben don Allah?" Cikin muryar tausayi yake maganar, ta ce "To shi kenan". Ta soma tafiya, ya dan tako ya biyo ta tare da cewa "Sahibata mu kwana lafiya" A kagare ta ce "Uhum". Ta samu Abba suna hira da Umma, ta tura mishi kular birabisko tana lallashinshi ya ci, tayi sallama Umma ce ta amsa. Ta shiga idanunta kan Abba, ta zauna a kujerar da ke fuskantarshi. Umma ta ce "Har Sahabin ya tafi?" Ummi ta ce "Eh". Ta tsura ma Abba ido tare da cewa, "Ina kwana Ya Abba?" Umma ta ce "Wane irin kwana kuma Ummi da wannan daren?" Ta ce, "Au, zan ce ina yini?" Ya amsa tare da kallonta, "Lafiya". Ya mayar da dubanshi ga Umma. "Umma Matar Ahmad fa ta haihu". Ta ce, "Eh, ba jiya ka fada min ba a waya? Me ta samu ne?" Ya ce, "Mace ta haifa, gashi ta sha wuya". Umma ta ce, "Allah Sarki, to Allah ya raya mata, zan je in dubota in mata barka gobe". Ya ce, "Allah

Chapter 11 of 24