Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kai mu, ai Ahmad yayi dacen mata ba kamar ni ba. A da Umma bana tunanin sake aure, amma yanzun ina ganin dole sai nayi mata biyu". Umma ta ce, "To ba dai yanzun ba duk nawa ka ke kuma yaushe kayi wancan?" Ya ce, "Umma ke dai ki min addu'a, ban samu irin macen data dace da ni ba". Ta ce, "Ina maka addu'a, Allah ya shirya maka matarka." Abba ya ce, "Ko ta shiryu sai nayi aure insha Allahu". Ta ce, "Abba ni ko gani nake ba ka san wadda za ka aure din ba itama da nata kalar halin zata zo, sai su taru su ruda ka". Ya kalli Ummi wadda ya lura da kallon da ta tsare shi da shi kamar tana son jin abin da yake fada ne. Ya maida idanunshi kan Umma. "Na yarda da tarbiyar wannan yarinyar da nake son aure yanzun, duk da yarinyar bata sona tana girmamani". Umma ta ce, "Har ka samu kenan, 'yar gidan waye? Ummi kuwa tuni makoshinta ya bushe, ta zaro idanu tana son ji wa kuma Abba ke so? 7:....Ya kalli Ummi ganin yadda ta zaro ido ya ce "Ke ni ke fadama wa ki ka zaro ido ki ka tsare ni da su?" A hankali ta lumshe idanu sannan ta maida kanta kan hannun kujera, ya fuskanci Umma "Ba 'yar unguwar nan ba ce", matsalar da yarinyar bata sona". Umma ta ce, "To ka bar ta mana ka samu mai sonka? Yo in haka ne ma ka ce gara matar taka ta gida, don ita tana sonka". Yayi shiru zuwa can ya ce "Umma in dai zan sameta zan aureta a haka". Umma ta ce, "Kayi addu'a, ina ko mamakin mene ne ta gani na 'ki a tare dakai Abba?" Ya ce cikin 'yar dariya "Umma ai ba dole ba ne sai ka birgke kowa". Ummi ta mike jiri na dan dibanta ta shige ciki. Zance ya dada watsewa, ta furta bayan ta fada kan gado, ni ina son shi shi kuma ashe yana can ya zarme da son wata. Ranar ta raba dare tana kuka daga karshe ta soma ba kanta shawarar ta samu Abba ta ce a fili dama shisshigi ne irin na zuciyata Ya Abba ba irina yake so ba. Shi kuwa zuciyarshi ta soma zargin wani abu a kan Ummi, irin yanda ya ga tayi kamar hankalinta ya tashi da batunsa. In ko haka ne zai fi kowa murna, wata zuciyar ta ce ka sani ko tsabar jin gulma ne yasa ta kafa maka ido duk da haka yasha alwashin bibiyarta. Sun taso daga sallar Juma'a shi da su Ahmad gidan budurwar Tukur suka dosa, wayar Salis ta katse shi. Wani aiki ne ya taso dole ya koma gurin aiki. Ya sauke su a unguwar shi kuma ya nufi gurin aikinshi. Karfe biyar ya baro gurin aikin da nufin yada zango gidan Ummanshi. 8.... Yasan yau juma'a duk yanda aka yi zai samu abinci na musamman, don al'adarta ce girkinta na juma'a daban ne, tana girmama ranar da abincin da ta san mijinta zai yi farin ciki da shi. Haka nan ta kan yi kwaliyyar musamman, shi yasa yake kara kwadayin aura Ummi, ya san zata dauki wannan tarbiyyar. Matasa guda uku a tsaye gefen titi cikin fara'a da murna suka tsaida shi, ya saba kusan kullum sai irin haka ta faru. Matasa kan tsaida shi suna ma su nuna jin dadi da ganinshi, a gaisa su wuce. Wasu kuma su amshi lambarshi har da ma su son adireshinsa, yanzun ma sai ya tsaya zai fito, tsum! Yaga sun bude motar sun shigo. Biyu baya daya gaba, ya ba su hannu suka gaisa su duka. Na gaban ya ce. "Mai matasa ai muna jin dadin taimakon da ka ke mana. Ya kamata a baka Sardaunan Matasa". Daya daga baya ya ce "Sarkin Matasa gaba daya zamu ba shi, don yana kokarin gurin binciko matsalolin matasa". Abba ya yi murmushi tare da cewa, "Na Gode". Dayan da bai yi magana ba sai ya ce "Amma mai Matasa ka san da wannan matsalar?" Abba ya waiwaya da nufin jin karin bayani, sai ko ya fesa mishi wata farar hoda a fuska. Take nan atishawa da tari suka tirnike shi. Ya soma mutsuka idanunshi bakinshi na furta "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Kafin 'yar sakwanni kanshi yayi din, kuma ya fita daga hayyacinsa. Suka tuka motar suka tashi dashi. * Farkawa ya yi tamkar wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude ido tangaran a kan silin, irin na masu hali. Kwan lantarki irin na kasaitattun gidaje ya daki hancinshi. Nan take ya shiga tunanin me ya kawo shi nan? ba 6ata lokaci ya tuna duk abinda ya faru, da sauri ya tashi zaune yana fadin "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un". Ya ci gaba da kallon dakin, cikin tangameme ne yana dauke da tafkeken gado da sauran saitin shi. Sai kafet din tsakar daki da kayan kallo, ga kuma kofofi guda biyu. Ya tambayi kanshi da cewa me ya kawo ni nan? me matasan suke nema a gurina?" Take muryar Hajiya Nina ta fado masa, inda take cewa "Za ka zo yau din ne ko sai an dauko ka?" ya girgiza kai tare da cewa, Lallai wannan makirar matar ce tasa aka mi shi haka". 9... Nan take ya soma karanta addu'ar neman tsari. Daya daga cikin kofofin ta bude, ya kure idonsa gurin da kallo, matar ta shigo sanye cikin doguwar riga baka mai ma6allai a gaba. Fara ce kyakkyawa, shekarunta suna tsakanin Talatin da takwas zuwa arba'in da biyar, domin kyawun nata sun 6oye shekarunta, ta baza gashi a kafada. Tsura mata ido yayi yana son tuna inda ya ta6a ganinta, domin tabbas yasan fuskar. Muryarta ce ta katse shi,"Dama nasan zuwa yanzun ka farko, kuma ka gama nazarin yanda aka yi kazo nan. Kila ma tunda kana da kamannin ma su basira ka hararo wadda tasa a ka dauko ka". Ya ce, "Kwarai kuwa". Lokacin ne ya tuno inda ya santa, wato Hajiya Zabba'u ce matar shaharraran Attajirin nan Alhaji Uzairu wadda a ke nuno ta a TV da Jaridu tana taimakon talakawa da Marayu. Wadda ake labarin tsoron Allahnta da gudun duniyarta, wadda ta gina Masallatai da Makarantun Addini ma su dama. Ya girgiza kai cikin matukar mamaki, ta ce "Ka gane ni kenan?" Ya ce (Cikin karfin hali) "Lallai mutum mugun ice. Wannan shi ne Allah a baki shaidan a zuci". Ta ce "Kai ne na biyu da ka furta wannan kalmar, sai dai bana fata ka zama na biyu da ya bakunci inda na farkon ya tafi. 10.... Ta tako a hankali ta dunfaro shi, ya matsa baya cikin zuciyarshi yana korar shaidan, 'yar dariya tayi. "Nutsu Idris ko ince Abba. Ba fyade zan maka ba". Ya dubeta da sauri, "Eh haka nace, in na son hakan zan maka, amma ba hakanne burina ba". Ta zauna bakin gadon, "Ka zo mu daidaita, in kana tsoron ciwo zan baka makari, sai dai ina so ka sani bana dauke da wata cuta". Ya ce, "Karya ki ke, kina dauke da mummunar cuta". Ta ce "In ka tashi daga dan jarida ne, ka koma Likita zan baka dama ka gwada ni". "Ya ce ba ki bukatar gwaji don ga ciwonki nan a fili ciwon zuciya". Ta ce, "Sam ba ni da ciwon a zuciyata, to in ma ina da shi me zai dameka tunda ba dauka za ka yi ba". Ya sake ja da baya ya ce, "Zuciyarki ta kamu da ciwon zina. Ta yi duhu dumdum! har bata iya ganin gaskiya...". "Ta daga mishi hannu, "Dakata min, ban tambayeka labarin wa'azi ba, domin in shi nake son ji ina da kaset-kaset kala-kala zan saka na ji". Ta mike zuwa wata durowa ta bude, dauri uku ta dauko ta aje gaban madubi na 'yan dari biyar-biyar sababbi dal! Ta ce, "Wannan za ka sha mai ne sannan kasa kati, kuma in ka kwantar da hankalinka zan canja maka mota, zaka je Makka. 11.... Sannan idan naga kana bin umarnina zaka yi suna a aikin jarida fiye da duk wani dan jarida da ka sani a kasar nan. Kai zaka taka duk wani matsayi da dan jarida ke takawa". ta sake nufoshi da tausasa murya. "In kabi yanda nace ba kai ba sake kwana a talauci..." Ya katseta da fadin, "In naki fa?" Ta hade rai tare da zuba mishi ido, "Shima kallonta yake, sai a lokacin ya ga tsufanta ya bayyana. Ta juya mishi baya tana 'yar tafiya, sannan ta ce "Am sorry to say". Ta juya ta dube shi "Za ka mutu". Gabanshi ya fadi, amma sai ya yi karfin hali ya ce "In na mutu sai me? Dama can mutuwa zan yi ko ba ki kashe ni ba. Kuma ni na san ba zan wuce iyakar ajalina ba, murnata daya zaki sauke min nauyin zunubaina". Ta matso kusa da shi "Ka san matasa nawa ke shiga malamai kawai don su yi hulda da ni? In ka dade muna hulda shi ne muyi wata biyar, sau daya na rike saurayi har tsawon shekara daya don yana da hankali". A zuciyar Abba ya ce "In fa na daka ta matar nan zan mutu ban auri Ummi ba. Sannan ba Allah a ranta bare taji nasiha, yanzu bari yabi ta hikima". Ya ce, "Saboda me suke shiga malamai don suyi hulda da ke? Sannan daman duniya tasan ki kina haka?" Ta ce, "Ko kusa, sun sanni a Hajiya Nina sai in mutum ya zo ya ganni, in ya sanni to in bai sanni ba duk daya. Sudai burinsu kudin". 12...... Abba ya ce, "Nikam ba zan iya wannan huldar ba". Ta ce, "Kada ka bari taurin kai yaja ka nadama irin wadda waninka ya ta6a yi. In kana da sha'awa in baka labarinsa don ya zamar maka Ishara". Shirun da Abba ya yi shi yasa ta ci gaba, domin alamar yana son ji kenan. Da a ce zan fadi sunanshi zaka sanshi, wani malami daga cikin Malaman garin nan, haka nan yanda na ganka a TV kana labarai na kwadaita da kai, shima haka na ganshi a TV yana wa'azi kuma zuciyata ta yaba. Na neme shi ya zo kuma shi na fada masa ni ce Zabba'u ban 6oye masa ba. Sai dai nuna masa nai aikin rabon zakka zan ba shi, ma'ana kudi ne masu yawa ban san yadda zan fidda musu zakka ba. Da jin haka sai ya taho, nan dakin na kawo shi, sannan na fito mishi da maitata fir! ya shiga jawo min ayoyi na numa masa cewa ba zan hakura da abinda zuciyata ke so ba. Don ban ta6a 'kin cika mata burinta ba, shi kuma ya fir ya ki ya nemi ya gudu na bashi guri ya dan ci abinci na nuna masa mishi kuskure ne ya ce zai gudu. Don gidan nan duk masu tsaro ne har da ma layin gaba daya. Da sauri za a kama ka a matsayin dan fashi, sannan in ka yi kokarin shigo da jami'an tsaro lamarin to, zaka kwana ciki. Domin duk a hannunmu suke, amma Ustazun ya ki shan ko ruwan gidan nan, gashi ya min shame-shame zai mutu don yunwa. Ba arziki na saka aka fita da shi kuma aka kai shi gidan karuwai a ka ba su na sakar musu kudi suka sa shi a daki. Nasa Malamina ya karasa min shi, sannan na sa karuwan suka kira 'yan sanda kan cewa ga wani ya zo gurinsu amma kwananshi ya kare a nan. To dama iyalanshi suna ta nemanshi an sace shi nan fa suka dauke shi, na san yanzu ka gane kowane Malami ne tunda labarin ya yadu a cikin garin nan da ma wajen shi". CIKI book 3 part 3 ZURFIN CIKI book 3 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:24 Abba ya ce "Lokacin da muke cin abinci tare, Umma ta ce, lokacin da ka ke bata dai, Abba shi ne ya fara baki abinci a baki. 20..... Watanki hudu, da kin hango shi za ki soma daga hannu, Abba ya ce Umma na fa goya Ummi a bayana. Lah, goyo? In ji Ummi. Umma ta ce, "Goyo sosai kuwa, suka sa dariya, Umma ta ce, "Shi yasa in naga yanda ku ke rashin shiri a tsakaninku yanzun sai in ta mamaki. Don tun ba ki fita a tsumma ba Abba ke rainonki, tun ba ki fi wata hudu ba, ki ka tantance muryarshi. Haka nan sunan shi ne ki ka fara iya fadi a duniya. Abba yana goya ki kin sha yi masa fitsari da kashi da tumbudi, wanka da wanki duk Abba ya miki Ummi. In ko na aike shi ko zai tafi Makaranta to sai da wayo da dabara. Ke har an kai lokacin da kin yarda in tafi unguwa in bar ki gurin Abba, in ya dawo Makaranta tun daga soro zai soma miki wakar da yake miki. Ummin Abba da Alhaji, Ummin Umma da Tsohuwa, da kin ji haka za ki dibi rarrafe ki nufi gurinshi, kuma duk kudin break dinsa zai debo miki tsaraba. Umma na bada tarihi Ummi ta zuba ma Abba idanu cikin wani irin yanayi da ba zata iya tantance shi ba, shi kuwa lokacin ne ya dawo mishi, ido ya yi dan murmushi tare da cewa "Allah sarki da na tuna ranar da aka yaye Ummi, Umma tayi dariya ta ce, "Ranar tare kuka kwana kuna min kuka wai in yi hakuri in baki nono". Wata sabuwar kauna da so Ummi taji ya rufe ta na Abba, har kwalla ta cika mata ido, ta ce "To Ya Abba me yasa ka daina sona?" Ya ce, "Ummi ban daina sonki ba, kanwata kiriniyarki ce ta hada mu fada dama, yanzun kuma kin daina ko?" Ta daga kai alamar eh, Umma ta ce "Labarin yanda ku ka kaunaci juna mai tsawo ne, kusan kullum sai mun yi labarin da Alhaji". Ummi ta kalli Umma shi ne ba ku ta6a bani labari ba? Ta ce ba gashi kin ji ba, Tsohuwa tayi sallama, suka amsa. Ta ce, "Kai me sunan Malam me ya faru da kai? Nan ya warware musu komai, suka yi ta al'jabi. Umma ta ce "Ni 'yasu, yanzu haka mata suka maida aure ba a bakin komai ba?" Kuma ka ce matar aure ce, Abba ya ce dama z aki san kowa ce ce za ki ji mamaki fiye da haka, don dai kurum na rufa mata asiri ne in taci gaba to can gabanta hadu da mai tona ta. Su Alhaji suka shigo da sallama, nan suma aka ci gaba da jajanta batun, Alhaji Babba ya ce, "Babana ina ga dai rahoto za mu kai gurin 'yansanda". Abba ya ce, "Alhaji tuni manyan shuwagabannin gurin aikinmu suka shigo da hukuma, in Allah ya yarda dolenta ta bar ni, Alhaji Karami ya ce, "Addu'a dai ita ce z aka kara rikewa, Allah ya ja mana gaba". Suka ce Amin. 21... Ranar su Alhaji a tsakar gida suka ci abinci anata hira, Ummi dai kallonsu take yi amma zuciyarta na can duniyar tunanin labarin da aka bata. Ashe har yanzu Ya Abba na sonta, Allah ya sa haka har yanzun. Sai kusan sha daya Alhaji ya matsa wa Abba ya tafi gida. Abba ya ji dadin hirar musamman in ya waiwaya idanunshi suna kallon Ummi ta mai 'kuri da ido, Umma ta ce, "Ka gaida 'yan gidan". Ya ce "Za su ji, har ya kai soro Ummi ta ce Alhaji da an raka shi kada a kara sace shi fa, duk suka sa dariya". Abba ya dawo yana cewa, "Umma kun rage man fetur kuwa? Na san yanzu na gidan ya kare tunda ba shi da yawa, bana son kuma sai na sake daukar galan na fita". Alhaji ya ce, "Na shigo da mai dazu duba nan soro na aje shi, Ummi ta sake cewa Ya Abba ka ce Alhaji su rakaka gida, yayi 'yar dariya kada ki damu Ummi, ina yin addu'a Allah zai kare ni. Yau kam Ummi ta dade bata ga daren da farin ciki ya hanata bacci ba irin yau. Haka nan shima Abba zuciyarshi fes Ummi ta fahimci dama can santa yake, da alamu ba zai sha wuya gurin shawo kanta kuma cikin karammin lokaci. 11 HAJIYA NINA Ta kalli matashin, sannan ta kalli jaridar hannunshi ta ce, "Me ya'ki kai fa ba jakadan azriki ba ne, a duk lokacin da na ganka sai gabana ya fadi, musamman in kazo min da jarida". Yayi 'yar dariya "Hajjaju makatu sallah Makka Sallah Madina, ni dai kin san ba ilimin nan gare ni ba, in da z aki tsare ni in karanta ban iya ba, ni dan sako ne. Muftahu ne mai siyo duk wata jarida da ya ga ta shafe ki, ta amsa ta bude cikin azama, hoton Abba ta gani gabanta ya fadi, ta ce dan jarida shege ne, yaron nan tallatani zai yi? Ta soma karanta labarin zufa tana karyo mata, har ta gama. Kafa kurum take karkadawa tana tunanin abin yi, murna daya tayi da bai tona ma duniya cewa ita ce Hajiya Zabba'u ba. Amma duk da haka ba zata bar shi ba, koda yake ta ga manyan 'yan jarida na kokarin shigowa ciki, ta kai hannu ta dauko daya daga cikin wayoyinta ta danna kira. 22.... Jim kadan aka daga ta ce, "Karamakallu barka da warhaka, ya amsa da Ranki ya dade lafiya dai ko?" Ta ce, "Malam ba lau ba, kana ji? Ina yaron da nake baka labari dan jarida? Ya ce, Naji. Ta ci gaba, Yaron nan kaga yanda ya yayata ni a duniya? Sai na koya mishi hankali, da ni zai ja?" Malam ya ce, ya ma ki ka ce sunanshi? Ta ce Idris, ya ce To zan kira ki anjima, kada ki dauki wani mataki tukunna sai na gama bincikena duka. Ta ce an gama. Sintiri tayi ta yi tsakanin dargajejen falonta zuwa barandar shakatawarta, lokacin da taji rurin wayarta tayi tsammanin Malamin ne, sai data duba taga Aminiyarta ce Haiya Attine. Ta daga da cewa, "Hello Attinen bishasha ya aka yi ne? Ta ce, Zabba haka kwallon dan iskan yaron nan zai miki? Ta ce, Hum! Ke dai bari Aminiyata, yanzun nan na gama karantawa a jarida ban ma san hukuncin da zan yanke ma yaron nan ba. Attine ta ce, sa su Adda su tura shi Jami'ar mi'kakku mana. Hajiya Zabba'u ta ce, "Ai kuma na riga na kira Teacher ya ce in saurare shi". Attine ta ce, "Eh to kin yi dabara ma, kya iya sa Teacher din ma ya tura ba tare da an zargi kowa ba". Hajiya Zabba ta ce, "Kin san jami'an tsaro suna cikin maganar tsundum! Don haka dole in yi taka tsan- tsan, guri daya yaron ya yi min kyan kai, da bai fada ma duniya Zabba'u ita ce Nina ba." Attine ta ce "Eh yayi wannan adalcin, yanzun bari muji ta bakin Teacher". 23.... Shikam Malamin duk lamura sun kasa masa daidai, sai kusan karfe uku saura, sannan ya kira ta da rawar jiki ta dauka. Ya ce, Hajiya? Ta ce, Na'am ya ce ki tattara ta batun yaron nan ki watsar domin yanda naga al'amuran to fa in mun matsa ba zamu kai labari ba. Haka nan allura zata tono garma game da damuwar malamin nan, sannan asirinki zai tonu a gurin maigidanki. Tsaki taja don maigidana Malam nasha fada maka ban 'ki ya ji ba, tunda shi ne sanadin komai, tafiya kullum daga waccan kasa zuwa waccan, kullum cikin bakin yawon neman kudi. Sam baya biya mini bukatata ba dole in nema ba? Yarana biyu cal a duniya duk sun yi aure su ne kawai zan ji kunyar su sani, don haka in zai yiwu ka sa Aljanu su tsotse min jinin matsiyaci. Malam ya ce, "Ba zai yiwu ba, ina ce tun lokacin da ki ka zo min da batunshi kafin ma ki sa a dauko miki shi sai d ana fada miki yaron yana da kariyar da take kare shi daga Ubangiji. Yaron ma'abocin kyautata Sallah ne, tare da yin Azkar, yana da makarin da Aljanu ba za su iya tunkararshi ba... Dakata Malam, ta katse si duk addu'arshi ya kai Malam ne, kuma muka ci nasara a kanshi? Ya ce kila shi Malamin kwananshi ya kare dama ke ce sila shi ko wannan da sauran shan ruwansa. Ta ce, "Kai ne sila dai daina jingina min mutuwarsa, ya ce ko kin ki dole ki dauki nauyin zunubin mutuwar Malam". Yanzun kuma ta wannan sai ki wamu wani don ni ba zan matsa lamba a kan al'amarin da Aljanu suka nuna tsoronsu ba, tsaki taja sannan ta kashe wayar. Har gari ya waye ba ta daina tunani ba, haka nan bata yanke matsaya ba. Gidan Aminiyarta Attine bishsha ta nufa, sun tattauna sosai sannan suka bukaci sukai koken ga wasu Malaman. Sai dai guri uku zancan iri daya ne, wato ta bar shi kawai, yayin da guri biyu suma zancan su iri daya ne, sun ce zata ci sa'ar kashe shi amma asirinta zai tonu zata rasa ran 'yarta daya kuma zai yiwu tayi zaman Jarun. Ta ce, "Wannan akwai shegen yaro, shi yasa da na ce zan sa Aljanu su dauko shi ya ce min yana da makaminsu? Daga karshe ta ce na bar shi mara rabo". Attine ta ce da dai yafi shi yasa tun farko in naga wanda zai ja min aji ni ke watsi da shi in nemi wani. Kai jama'a sai kace aikin Allah menene amfanin zinar ma da har ake shiga Bokaye dominta? Allah ka tsare mana Imaninmu, amin. 12 24.... Ummi tana zaune zata wanke 'yan kayanta na ciki, ta zubo omon cikin ruwa tana faman karkadawa, tana 'yar wakar da ke sata nishadi. Sam ba ta ji sallamar Abba ba, yana jingine yana kallonta, tana fadin, Akwai wanda na ke so, amma kunya naso, ya wanke ni da soso dan Yayana. Ta tsoma sikyat dinta da fant da 'yan bireziyoyinta farare ne ta soma cudawa tana maimaita wannan baitin wakar, shi kadai ta iya. A jikinta taji cewa ana kallonta, ta waiwaya da sauri, idanunta tsaf cikin na Abba, sai ta samu kanta da sunne fuskarta cikin cinyoyi. Ya ce, "Kunyata ki ke ji ne Ummi?" Ta dago da dan murmushi, "Sannu da zuwa Yaya Abba". Ya ce, "Yauwa dama kin iya waka?" Tsohuwa daga daki ta cafke, tun da ta samu wannan wakar sai ka ce me hadda, kullum Abba ya isa kofar Tsohuwa suka gaisa. Ya dawo kofar Umma yana tabayarta. Ummi ta ce, "Taje Hotoro sunan kanwar Umman Bashir da ta haihu, ya manta fa matarshi ma ta na can, Tsohuwa ta fito tana cewa, ai Ummanku ta juri wulakanci. Waccan haihuwar da Zilai kanwar Sahura tayi tas a ka zageta a gidan sunan, amma yau ta koma. Abba ya ce, "Ummata tayi nisa a zumunci, Allah zai bata lada" Tsohuwa ta ce, "Ai sai tayi ta yi, in dai shisshigi ne ba kwarjini". Ta dubi Ummi, wai wankin me ki ke yi ne har yanzun ina nan ina jira ki yanke min farce". Ta hango kayan Ummi na daura ta ce, "Kai ni wannan zamani naku yana bani mamaki, ace 'yammata suna saka rigar mama? Kunya ta cika Ummi saboda Abba da ke gurin. 25.... Abba ya ce, "Kin ji tsohuwa, lokacinku da namu daya ne? Ku lokacinku kai bai waye ba, ta aje 'yar kujerarta ta zauna. Tir da wannan wayewar taku ta zamani, yarinya ta fadi a gaban iyayenta har ta shiga sa tara mama bata kama dakin kanta ba? Mu kuwa da wata ma ba sai tayi haihuwa goma ba ma ta sa ran mama ba. Abba dariya ta ishe shi yayin da Ummi kunya ta hanata shanya kayan ta matse ta aje. Abba ya ce, "Yanzun Ummi har wani girma tayi, shekara sha takwas kurum ce fa, bata ma cika ba. Ta ce "Mu lokacin sha biyu sha daya yarinya ta kama dakinta. Ummi ta zanua ta soma yanke ma Tsohuwa 'kumba, tana cewa To dai nima na kusan tafiya in huta gorinki. Abba ya matso, "Ummi don Allah in tambaye ki mana? Ta tsaya da yanke 'kunbar tana kallonshi, ya maimaita tambayar da gira ta bashi amsa ya ce kina ko son wannan Sahabin? Ta maida kanta ga yankan 'kunbar duk jikinta da hannunta suna dan rawa, a zuciyarta ta ce, "Kai ne kadai zuciyata ke so, amma a fili sai ta ce, Um, ya ce Yaya hausar um?" Tayi kokarin saisaita hawayenta, sannan ta ce Eh, jikinshi yayi lakwas, Tsohuwa ta ce, "Zancan banza, in bata sonshi zaka daga batun auren ne?" Ai ko tana so ko bata so tunda ta kawo shi zance ya kare, ka ji mai sunan Malam da zancen wofi. Ya ce, "Tsohuwa ni fa ba wani abu na ce ba, kin ga ma dai bari in tafi abina. Ummi ina Azimi yau, zan zo in yi buda baki anjima. Ta ce, "To." Tsohuwa ta ce, "Wai kai ba ka da gidan mata ne kullum kana la'ke a nan? Tsoron ta ka ke ji ne da zaka kasa lankwasata ta yi maka girki?" Ya ce, "Na nan nake son ci Ummi kam tana can duniyar tunani tana tambayar kanta shi kenan ta rasa Abbanta? Son da da yayi mata da ca dama ba na aure ba ne, na 'yan uwantaka ne? Kai ko dai ta fito ta ce Abba take so, gaskiya ita fa Sahabi ba sonsa take ba. Kusan wata daya kenan rabon da ya samu biyan bukata daga matarsa, don gaskiya baya iya zuwa dakinta saboda kazanta da kuma datti da wari da zarni da 'karni ba za su bar shi ya samu cikakkiyar biyan bukata ba. In ta zo dakinshi ma jikinta tashi yake, a haka yake maneji, amma in iskancinta ya motsa har yanga take mishi (Mtsw! Allah rabamu da kazaman Mata). Shi kuma yana da wani hali, duk yanda ya matsu in har ya nuna mata bukatarshi ta 'ki sai ya hakura ya roki Allah ya shiryeta, shi kuma ya kare shi da fadawa sharrin zina. 26.... Bai zaginta ko ya ce zai nuna mata karfin shi, ko ya ce zai tsaya rokonta, shi yasa yake yawan yin Azumi. Ummi ta ce, "Umma ki kawo kudi in siyo kwai in soya ma Yaya Abba doya, ya ce zai zo shan ruwa. Ta ce, "To je ki kasan filo ki dauko, amma fa sai kin yi azama don an kusa kiran sallah. Ta ce, "Ai na dafa ruwan shayi, sannan na masa kunun tsamiya, doyar ce kawai, ta ce "To sai da ta gama komai sannan tayi wanka tayi sallah. Riga da siket na leshi tasa fari tas, bata damu da yin fenti da dare ba amma yau tayi ta feshe jikinta da turare wanda shi ne ya sai mata. Sallamarshi ta jiyo suna

Chapter 12 of 24