Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ranar da ummi takira ummansu tafada mata cewa bishirafa tuntuni tayi yaji amma Abba yaqi zuwa, umma ta kira shi tace inya dawo gurin aiki tana son ganinshi. To kafin yadawo ma saiga hajiya zainu da direba tazo gidan su umma tadire musu 'yar, sannan tashiga gidan umman bashir tace, in kin haifi danki na halas ne ba shege ba to kisa shi ya aiko wa 'yata saki. Umman tace zoko kiga dan halas ne in yaso kuje ku nemi arne mara sallah dan uwanta kazami kubashi. Nan fa zage- zage ya tashi har su umma dasauran makota suka shigo. Dakyar aka tura hajiya ta tafi, tace kuma saita kira 'yan sanda anzo antafi da umman bashir. Alhji qarami ma cewa yayi maza abba Abba yarubuta takarda ya aika ma bishira.ZURFIN CIKI book 4 part 32 ZURFIN CIKI book 4 part 32 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:37 Shiko alhji babba da umma suka ce a'a abari qura ta lafa sannan aje. Koda aka kwana 2 abba kin bin alhaji yayi sai wani abokinshi alhaji yasamu suka tafi tare. Mahaifin bishira yaji mamaki cewa ba sakinta abba yayi ba. Kuma bai san sun maida 'ya ba, tadai ce mishi kunzo kun amshi 'yarku, to yanzun tunda haka ne kunga kenan bishira da uwarta basa son takoma gidan mijinta ko? Su alhaji suka ce eh, yace to ku sa shi ya rubuto takardarta ku kawo min, su alhaji sukace ba za'ayi haka ba. Yace, to kuje ku barta zata gane gidan ubanta bananne yadace tazauna ba. Sukai godiya suka tafi. Harta koma gidan anty farida mahaifinsu yace tadawo nan gidanshi badashi take takama ba? Wato ta kashe auranta zata je ta kashe na yarta dole ta dawo, tsohuwar dake musu aiki yace ta koma gida tahuta amma duk wata tazo ta amshi albashinta. Sannan yace bishira itace zata dinga wannan aikin duka ita kadai, lamarin yayi wa bishira tsauri da yawa, gashi ba fita duk ta rame ta lalace ga tunanin 'yarta. Muhibba kuwa tana gurin umma, ummi ma takan daukota sannan ummi tasamu nasarar rufe bakin umman bashir, ta hanyar yi mata kyautuka ko me sukace sai ta aika mata. Tasa Abba ya canja mata gado don nata ya lallace, sannan da fati ta haihu tasa Abba ya sai mata garar abinci, ita kuma tasa zani da rigunan yara. Nan fa sai ga sahura babu ko kunya tana shima ummi albarka, ko bashir ne yakawo gulmarsu ummi sai tace ai ita bata yo halin uwarta ba. Tafi-tafi ma in ya kawo sai tace ai su umma da ummi sun gane kuransu. Haba sahura kodai ki gane kuranki? Abba yasoma damun ummi da batun ciki, wai shifa yana tsoro kada su gaji su umma, ummi tace su dai yi addu'a sunje asibiti ba wata matsala, likita yace in rabonsu yazo zasu haihu. Da kyar ummi ta shawo kan Abba ya amince ta zana (JAMB) don ci gaba da karatu, sannan ta shiga islamiya. Abba yayi kyau yayi kiba ya kara gogewa, haka nan ummi duk wanda yaganta saita birge shi, daka ganta kaga wayayya wadda mijinta yasan da ita. Taci nasarar samun (POLY) saboda bata samu abinda take so don zuwa (UNIVERSITY) ba, sai dai ba tasha dokoki kafin ta fara zuwa. Bayason kawaye baya son abokai, irin wanda wasu matan keyi sannan yadinka mata manyan hijabai, kuma banda hawa acaba, inya samu sarari zai dinga zuwa da kansa yana daukarta. Sai kuma gargadi na karshe kuma da babbar murya, in har ya daina samun kular datake bashi ta kowane fanni wai saboda karatu, to kuwa za adaina karatun gaba daya. Tace, insha Allah sai abinda yai gaba. Ya canja mota, umma tayi ta fada wai tafi son yasai fili yayi dan gidanshi irin na zamani yace za'azo gurin ahankali kada ki damu umma. Bishira ta sulale ta tafi na'ibawa gidan anty da kukanta wiwi don Allah ta taimaka mata taba Abba hakuri ya maida ta, wlh tagane kuskurenta. Anty tace, nifa bazan iya kiran Abba ba don kin riga kin bmu kunya, sai dai in ke ce zaki kira shi ga waya can. Ta dauko ta kira, shikuma ganin kiran anty sai yayi parking yadauko ummi daga makaranta, ya daga sai yaji muryar bishira. Cikin kuka tana cewa, don Allah abba nice, kayi hakuri indawo dakina, wallh zan canza, yace ok baki riga kin canza din ba, to bari inkin canza din sai muyi magana. Yakashe haka tayi ta kuka tagama anty tabata wasu kayan sawanta sannan ta tafi. In lokacin labarai yayi haka take zuwa ta tasa TV tayi ta kallonshi tana kuka, kullum kara sonshi take gashi yayi kyau idanunshi sun qara haske. Wata ranar jumma'a wuraran karfe sha daya ta saci jiki tanufi gurin aikin Abba, yana fitowa dakin daukar labarai akace wata tana nemanshi. Baiji wani mamaki ba don mata kanzo neman shi wasu suce suna sonshi wasu suce ganinshi kurum zasuyi don yana birge su. Yana zuwa sai yaga bishira, nan take ya daure fuska tamkar bai taba dariya ba, duk da cewa acan kasan zuciyarshi yatausaya mata. Ta tsugunna gwuiwa 2 tana rokonsa, yace ke tashi kada ki janyo min mutane, jeki zanzo. Koda ta tafi cikin murna shi ko harkokinsa yakama. Shiru-shiru tana saka rai bashi ba alamarsa. Nan kuma tashiga daukar waya kannanta tana kiranshi, harma yadaina dagawa. Wataran taje tasamu ahmad tana kuka, ahmad yace taje zai ganshi. Rannan kuwa har gida ahmad yiyi sallama da abba yashiga rokon Abba ya maidota. Abba yace taje taroqi mahaifiyarsa dasu umma insun yarda shikenan. Har gida ahmad yaje ya fada mata, bata yi sanyi ba tanufi gurin umman bashir. Umman tana zaune da 'ya'yanta suna shan farfesun kifin da ummi ta aiko musu dashi, tana ganin bishira ta hade rai. Tace, lapiya? Bishira tace lpy lau umma zuwa nayi in roqi gafararki. Tace nime kika min? Tace don Allah dai ki yafe ni, ina son indawo dakina Abba yace sai kin hakura, tace oho, yanzun kin yarda ina da kima agurinsa? To bari kiji bazaki dawo ba, mai baqar rowa kince nimai kwadayi ke kuma mai rowa ko? To kin gani wannan ummi ce ta dafo mana ta nuna mata kular kifi, sanda kinanan bana cin komai bansan dana yana samu ko baya samu ba. Yanzun abin arziki iri-iri kidawo ki toshemana kofar samu? Tace, wlh bazan toshe ba, umman bashir tace dukda haka dai bazaki dawo ba. Tayi takuka sannan tafita, har zata wuce gidan su ummanshi sai ta tuna kada suyi mata dariya sai tace baridai ta shiga. Kyakkyawar karba umma tayi mata suka gaisa, tazauna umma ta kawo mata ruwa ta amsa tasha. Muhibba tana ta tsalle tsallenta kan kujera zuwa jikin umma, umma tace ji hibba ki gaida mamanki, ga mamakin bishira sai yarinyar ta kalleta tace. Umma niba wannan bace ba momina, momina sun tafi da babana zaya kaita makaranta. Umma tace, wannan ma ummarki ce yarinyar taruga dakin tsohuwa tana cewa, ita ba ummarta bace. Bishira ta bita dakallo, yarinyar tayi bulbul gata cikin shiga mai kyau da tsafta kanta yaji kitso da 'yan duwatsu. Saita soma kuka tana fadin mahaifiyata ta cuce ni, umma tace a'a kece kika cuci kanki, inbaki dauki damuwarki kin kai mata ba yaushe zatasan anyi? To ynzun dai dubi 'yarki tana gudunki sbd bata sanki ba, ina amfanin wannan? Tsohuwa tace kukan wanikeji ta shigo tana kallon bishira cikin mamaki tace. 'yar nan kece haka? Ciwo kikayi ko ko duniya ce ta juya miki baya? Kai jama'a dubi yanda kika kare kikayi bikinkirin. Ita da tadukar dakai tare da cewa bnyi ciwo ba nidai nazo ku yafe ni, sannan ku roqa min abba ya yafe min in dawo dakina. Yace, bazan dawo ba har sai kun yafe min, amma naje gurin umman bashir ta kore ni tace bazata bari in dawo ba. Kuma gidanmu wuya nake sha, kusan rabin aikin gidan nikeyi ga qannaina duk sun raina ni. Umma tace, yi shiru share hawayenki bari zaki koma. Tsohuwa tace, ke dai kin cika sa kai a uku suwaiba, gashi abin kirki bai karbe kiba. Kina yi ana zaginki ana zagin 'yarki, bishira ta ce wlh duk na daina, yanzu na gane kune masu sona, umma tace ba komai. Tadaga waya ta kira alhaji ta fada masa komai yace to yana zuwa donshi ya qosa asulhunta yarinyar ta koma dakinta saboda darajar tsohonta. Yana zuwa yaji komai nan ya daga waya yakira Abba, yace yana zuwa yana hanya ne yace to ya same su gida. Abba yana shigowa ganin bishira yahade rai ya zauna nan dai alhaji ya hada su yayi musu fada da nasiha, sannan yace baya son abba yace komai komai kuma ko sun koma gida banda tashin tashina. Bishira tayi ta godiya alhaji babba yace su tashi ashiga gurin umman bashir din tana ganinsu tahau cewa alhaji dakanka? Maimakon ace in zo? Umma tace, a'a keda zamu zo baki hakuri ai mu ya dace mu shigo. Nai dai alhaji yayi bata hakuri tace taci albarkacinta na hakura, amma da sharadi inta sake maimaita halin da tayi abaya ko taje ta takurawa ummi tofa saita tabar gidan. Bishira cikin kuka tace ta daina insha Allahu, nan itama umman bashir din tace dasu umma su yafe mata sharrin shaidan ne da qaryar barayin imani wato bokaye da 'yan tsibbu suka ce ba komai. Nan alhaji yace da abba yakai bishira gida, ba don son ranshi ba yadauke tazuwa gida, sam bata damu da daure fuskarshi ba, dadi da murna fal ranta. Yana sauke tazai wuce tace, don Allah ka yafe min sannan ka gaida min ummi, yace zataji. Tace to yaushe zan dawo? Yace, duk lokacin dasu alhaji suka zo gurin dadynku. Nan yatafi, ita kuma ta shiga gida, hajiya zainu ta tsareta wai sai ta fadi inda taje, tunda ta kira anty tace, bata can. Bishira tace naje ba mijina da surukaina hakuri ne, hajiya zainu tace ni dazai maida ki ai sai nafi kowa murna. Na gaji da zamanki da qazantarki, tunda babanku yaqi ki koma makaranta yakashe miki kudi ki goge ko kya samu mai kudin dazai aure ki, to gara kin koma can kin qarata. Abba kam shi tunaninshi ta ina zai soma sanar da ummi dawowar bishira? Don baya son ko kusa hankalinta yatashi, baya son wani abu yayi musu katsalandan a cikin daddadan zamansu, don haka ya share bai fada mata ba. Da dare alhaji da umma suka je, an sasanta sannan suka taho da alkawarin cewa gobe zata dawo dakinta. Washegari umma ta kira Abba tace ya share ma bishira daki yau zata dawo, yace umma nifa gsky dabata hankalina yafi kwanciya. Sannan ina ta tunanin yanda zan tunkari ummi da wannan zancen, umma ta riqe baki tare da rafka salati, yace ynzun tsoron ummin ka koma ne? Yace, a'a umma kin gata sakankance ynzun hankalinta yakwanta sai kuma taji nazo mata da zance dawowar bishira? Tace, shi kenan nina fada mata. Awaya ta kira ummi tafada mata cewa bishira zata dawo, duk datasan cewa matar mijinta ce dama, amma sai da gabanta yafadi. Umma taja mata kunne da cewa kada taji kada tagani, abba ranar sai kusan sha biyu zaije gurin aiki. Don haka yace kannanshi suje su soma fito da kayan kafin yazo sunzo sun fada ma ummi, ita ce ta bude musu dakunan don abba ya canza makulli bayan tafiyar bishira. Abba ya shigo tana zaune kan kujera sai tunani take yi na irin zaman dazasu yi in bishira tadawo. Yazauna tare dariko hannunta, tunanin me ki ke yi? Takalle shi, halin rayuwa nake tunani, yace yanzun umma ta kira ni jiya sun je gidan su bishira wai yau zata dawo. Ummi ta taba baki, Allah yakawo ta lpy. Ya ce ni ban soba gsky. Sbd ke ummi tadafa kirji, sbd ni? Ni ya abba, kada kasa duniya ta zage ni, Tare fa nasameku? Yace to ni dai kada kiga kamar da son raina, tace don Allah ya Abba kabar zancen nan. Kaje kagyar mata dakunanta don su kamal bazasu iya ba, yanufi gurinsu ganin kamar ya damu yasa itama taje tasa musu hannu don dai ya saki ranshi, sun gyara tsaf ummi ta goge sannan ta rufe dakin. Har magriba bishira bata ji an ce za'a maida taba, sai ta dauki wayar kanwarta ta kira shi wai yazo don Allah yadauketa. Tsakanin mata da miji sai Allah, nan ya tausaya mata yace zaizo, kafin ya isa sai daya sai mata waya irin dai ta hannun ummi. Har cikin gidan ya shiga suka gaisa da babanta, yayi murna sosai yayi tawa Abba godiya, tare da ba shi hakuri yace yasan yanda ta horu zai gata canza da yardar Allah. Yasa aka turo ta yayi mata nasiha, sannan ya gargadeta da cewa inhar ta bari mijinta yakawa kararta zatayi mamakin abinda zai mata. Tace, insha Allahu baza ta kara ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar ya amsa ita kuma ya bata wasu zannuwa acikin leda, yace su raba da abokiya zamanta. Taje tayi wa hajiya zainu sallama suka tafi, tamkar baquwa haka ta koma, sai kace basu taba zaman aure da Abba ba, nauyinsa take ji. Suna tafe ya ciro waya ya miqa mata, tasa hannu ta amsa yace taki ce, tayi ta godiya yace ba komai. Sallamarsu tasa gaban ummi faduwa, ta dake ta fito ta amsa, wani kishi ya tasho mata amma saita danne. Ta kalli bishira tare dayi mata sannu dazuwa, ta amsa tana kallon ummi tayi kyau tagoge daga ka ganta kaga wayayya 'yar gatan miji. Ta dauko makullin dakin ta ba bishira, abba kuma ya nufi dakin ummi. Bishira ta dinga kallon yanda abba ya gyara gidan yaja gini ta gefen ummi yayi mata falo da kicin, sannan tsakar gidan an gyare shi da tiles. Haka bandakin su yagyara shi, nan dai bishira ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana yi wa allah godiya tare dayi wa kanta alkawarin har abada bazata ta kara yin yaji ko ta janyo abinda zaisa mijinta ya sake ta ba. Ummi tana kan gado tana karanta wani littafi yazo ya zauna bakin gadon bata ko kalle shi ba don haushi take ji. Sai take ganin kamar rawar kai yake yi da dawowar bishiran, kuma tuntuni yana zuwa gurin ta ya boye mata. Yace madam ina son in yi magana da ku ne ke da bishira, ummi tace ina jin ka, yace can zaki zo muje. Tace, gsky nagaji, kayi maganar da safe. Yagama gano kishi ne ke damunta, don haka yayi murmushi yace yanda kikace hakan za'ayi. Ya fita kamar minti 30 yasake shigowa ya aje mata leda tare da cewa saida safe aciki tace Allah yabamu alheri. Yana tafiya taje ta banko kofarta, yau kam bacci ya qi idanun ummi sbd tayi sabon bacci a haqarqarin Abba. Dukkan filolinta ta rasa wanda zai maye mata madadin haqarqarin mijinta, ynzun yancan da wata tasan yanda yake wannan rawar jikin ynzun ya manta da batunta. Tarasa me yake mata dadi, littafin datake karantawa kuwa sam bata fahimtar abinda ke ciki. Hka ta dinga zubda hawaye har nisan dare, ganin bata da wata mafita, tashi tayi ta bude kofa lokacin 2 saura taje tayo alwala tazo ta kama nafila. Abba jin bude kofarta ne yasa shi leqowa ta window aranshi yaji tausayinta don yasan bata iya bacci sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba don ko hanyar dakin bata ishe ta kallo ba. Yakalli bishira wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya mata sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin auratayyarsu dazun. Yadauko wayarshi yarubuta ma ummi sako. KI KWANTA KIYI BACCI BABY, TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA KEWAR LEBUNANKI. Tana sallah taji shigowar saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma fizgarta. Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye mata komai ynzun. Sai dai abinda yasake qular da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da gayya ya tsaya don tafito taganshi. Tna idar da sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata tare da cewa an tashi lpy? Cikin sakin fuska tace, lpy lau, nagode. Ummi ta ce ba komai takoma dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin safe. Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka ya karya, sannan yanufi dakin ummi. Kofarta tana rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji yaqi tafiya sannan tazo tabude. Takalle shiya yi kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da cewa, an tashi lpy? Yace lpy lau, kin karya? Tace, um'um sai anjima, zata rufe kofar yace, makaranta fa? Tace sai karfe 2 nake da darasi. Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin takaici sannan yafita. Kwananshi 2 dakin bishira yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan shariyar da take mishiba. Tsakaninta da bishira lpy lau amma shi sai tana wani share shi. part 33 the end Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:45 Ya shigo da zumudi zai nufi dakinta, tamiqe cikin fara'a daga wanke-wanken da take yi ta amshi ledar hannunsa da jakar laptop ta nufi dakin bishira. Shida bishira suka bita da kallo, ganin zata shiga bishira tace ummi yau ai dakinki yake. Ummi tace injiwa? Anty bishara ai kullum ke ce dashi har sai kin rama duk kwanakin da kika dauka agida. Kinga kenan kusan wata goma sha daya kenan. Abba cikin sauri yace ke mahaukaciya ce? Ina ki kasamo wannan fatawar? Ta kalle shi, sannan tashiga dakin ta ajiye ta fito taqara kallonshi gurin malamai, yace to ban yarda ba, don haka zanci gaba dayi muku kwana bibbiyunku, ummi tace to ni na yafe mata nawa kwanakin bishira tace nagode ummi. Haushi ya cika Abba, amma shi bazai dauki wannan horon da ummi take shirin yi masa ba. Yadawo dakin bishira a fili yafurta kema saina baki haushi zakiyi dakin sanin wannan furucin. Sharewa yayi yaci gaba da kwana dakin bishira tare da nuna kulawa ga bishiran. Ummi ta jure duk da duk daren Allah sai taci kuka ta gode Allah, sannan tashiga zargin cewa shi ma ya Abban dama can yana son tarewa dakin bishira, inba haka bame zaisa yayi saurin yarda kuma yayi ta nuna mata soyayya? Ganin ummi tana yi tamkar bata damu ba yasa shi qa rajin haushi, yadawo da yamma suna zaune kowa A qofarshi. Ummi tayi kwalliya cikin qananan kaya, bishira kuma tana sanye da leshi, karatun littafi bishiran keyi ita kuma ummi tana yin gyaran qumbunanta. Bawai suna wata hira bane amma suna kula juna sosai musamman bishira tana son su saba da ummi. Ummin ce bata cika son fitowa ba, bishira ta tashi ta masa sannu dazuwa tare da amsar kayan hannunsa don yanzun tana koyi da ummi gurin kyautatawa, ummi ta kalle shi sannu dazuwa, ya amsa da yauwa baby. Yakalli bishira sweety zanyi wanka, tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai tazo tace masa takai nan kuma yajanyo bishira jikinshi. Ba wai yana da bukata bane, amma don ya shaqar da ummi sai ya banko kofar, qaran kofar ne yasa ummi kallon gurin dakin. Ta duqar dakai taci gaba da abinda take yi, kusan minti arba'in suka fito, Abba ya matsawa bishira wai suyi wanka tare, tace ni bazan iya ba akwai ummi dama da dare ne inajin kunya. Kuma kada taga kamar cin fuska ne, yace kenan don kada ki bata mata rai ni mijinki bazaki faranta min ba ko? Dole ta bishi suka shiga bayi. Baqin ciki yasa ummi tashi tashige daki, kuka sosai tayi daga nan bata fito ba sai magriba, tanayin alwala tarufo kofa, washegari ma qin bude qofar tayi daga alwalar asubahi. Abba yayi ta raba ido ya ganta amma bata fito ba, yasan fushi take, ya kira wayarta taqi dagowa yayi mata saqo cewa in zata makaranta tafito inkuma sai darana ta bude ta amshi kudin mota. Tana gama karantawa tayi wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka ya tafi. Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy? Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije makaranta bane? Ummi tace, zanje sai sha biyu. Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi masa zancen karatun amma ya share ni, ummi tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa min baki? Ummi ta riqe baki, ni a wa? Ke da yake hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki zage ni. Bishira tace wane irin zagi? Ni dama ki amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai agurina, amma ruhinsa yana gurinki. Ummi ta ce, ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba wani zagi. Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage walwala don wanda yasan kan kula da shi kamarta. Yayi missing din abincinta. Amma ya gaji bazai jure ba. Ya tuna bishira tace masa zata ta yini gidan ummanshi. Don haka yana gama muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin yanufi gida. Ummi tana shirin tafiya makaranta ta dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an jeho shi. Ta daure fuska tamkar bata taba dariya ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan horon naki. Laifin me nayi miki? In don na dawo da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika takura min sai na dawo da ita ba? Ummi tace, ni karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki matarka sbd ni? Ba ruwana. Yace, to ki dawo yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin haqura dani, niban haqura ba. Ke ma kuma nasan dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba, ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame? Ya canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna. Ya lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani abu. Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don lokaci yayi nisa. Ya ficiko ta ta dawo ba zaki makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi ni. Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje. Bishira tana dakin umma tana sallah yabi umma kicin, umma gurinki nazo, ta dube shi lafiya Abba? Ya turo baki, alamun ranshi bace baki, yace umma ki sallami bishira, tace kamar yaya? Yace taje can gidan ko muyi maganar agabanta? Tace, kyale ta muje dakin babanku. Abba ya fada ma umma komai da ummi ke masa, tun dawowar bishira ran umma ya baci tace ka barni da ita. Banda shashancin ta da ita kadai take son azauna? Baga bishirar nan ba gidan nan ta gane kuskurenta ko yau yarinyar nan sai da tace in yafe ta nace ni dama ban riqe ta da wani abu ba. Shine ita zata qirqiro fitina? Yace, umma ai ba da bishira take yi ba dani take yi, tace to zata gane kurenta da dare kuzo kai da ita. Umma ce ta kira ta awaya tace tazo ita da abba, jikinta ya mutu don tasan qararta aka kai, tana idar da sallar isha'i taje gidan. Can tasamu abba, nan ko umma ta rufe tada fada, koda tsohuwa ta jiyo tazo umma tafada mata komai sai ta shiga fada. Wai ai kishi halas ne, ke suwaiba tsakani ga Allah ko ke bazaki so kishiya ba, bare ita yarinya. Abba yace to gata nan ita ce fata dame ne nida batun in dawo da bishirar, yanzun na dawo da ita kuma ni abin ya qare akaina? Nan fa umma tayi mata tatas, ta kuma sata anan ta ba Abba Haquri, aka kira shi awaya ya fita. Umma ta samu dama taqara yi mata nasiha da cewa, in bnda shirmenki yaushe zaki bar ladanki, hanyar aljannarki kice kinyi fushi da ita kin barwa kishiya? To kada in sake jin haka, ki riqe darajarki da mijinki, ke ganinki da ita. Ta jima tana bata shawara kafin Abba yadawo suka nufi gida. Ya shiga gurin Bishira ya fada mata cewa yau gurin ummi zai kwana, nan ya bar ta da kewa yanufi gurin ummi, tamkar yaune daren farkonsu hara sukai rayuwa aranar. ** ** ** ** Kwanci tashi asarar mai rai, shekara ta zagayo lokacin bishira da tsohon ciki, Abba nason yara don muhibba taqi dawowa tafi son umma dole suka haqura suka bar mata. Ta haifi 'yarta budurwa tubarkalla ranar suna ta ci sunan sahura inda suka sa mata walida. Ummi nason yara, don haka in tana gida to tana manne da walida, Abba yana damuwa da rashin samun cikin ummi, wanda ita ummin ta barma Allah komai. Shekaru uku sun sake biyo baya, lokacin Bishira ta sake haihuwar habiba takwara Abba yayi wa ummi. Tsohuwa an qara tsufa, 'yan rigingimu sun qaru tace ita Abba yama takwara amma bata son ya duke ta irin yanda yayi wa ummi. Abba kullum qara son ummi yake, umma ta matsa masa sai da yayi qoqari ya sai fili rabin filoti tace kuma a rage ciye ciyen dadin nan agina shì. Haka kuwa ya gina flat mai daki hudu, daya ummi daya bishira, sai nashi sannan na yara. Yayi qoqari gurin gyaran falon ita kuma ummi ya canza mata kayan daki don bishira an canza mata daza su tashi agidan su. Yace tabishi bashi in ya samu zai bata kudi amadadin kayan daya saima ummi, tace ta yafe. Ummi dake karantar (BUSSINESS) har ta hada (H.N.D) dinta kuma tayi bautar qasa. Abba dai yace baza'ayi aiki ba amma ya yarda tayi kasuwanci, Alhaji babba ne ya bata jari inda take saro kaya zannuwa, lesuna, takalma zuwa jakunkuna. Abin ya amsheta don har kayan aure tana hadawa, tana yin saqo irin su kwatano da chaina, india, pakistan ko dubai, ta hanyar wani wan kawarta. Haka kawai ummi ta samu kanta da zaban abinci, yawan bacci kasala da dai sauransu, sam bata san takamaiman lokacin al'adarta ba. Don bata wani lissafi in yazo shi kenan in bai zo ba bata damu ba tama cire ranta daga batun ciki. Abba ya kalli nonuwanta, baby kwanan nan kirjinki ya cika sosai, gashi kinyi haske ko kin canza mai ne? Tace yaya yaushe kazama likita? Yace, ummi kin fa canza shirya muje asibiti, ta ce ya Abba don Allah ka bar ni nagaji dazuwa asibiti. Yace, to ni zan je inya tambaya game da yanda

Chapter 23 of 24