Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
komai saboda bakin asirinta ne sahabi yafasa aurenki aka mannawa mijina. Don shima ya fada min ba ya sonki, har yanzun bai taba kwanciya dake ba. Ummi tace, kazama mara sallah me labe, kina labe min akofan don bakin kishi, kuma insha Allahu sai Allah yasakawa ummata tunda kika ce tana asiri. Maman amir kawar bishira tuni taruga takira umman bashir, sai dai cikin sa'a tanazuwa Abba nayin parking. Ganin yanda mahaifiyarshi tashiga gidan cikin hanzari haka shima agurguje yafada gidan, ranshi yayi mugun baci yanda yaga gidan cike da jama'a. Ga bishira mutum biyu sun rike ta tana zambarmar asake ta ta lallasa ummi, ga ita kuma ummi tsaye akofarta kanta babu ko dan kwali ta sha gajeren wando ya dan gota gwuiwarta da 'yar riga tana maida martani. Yace ma matan dasuka rike bishira, ku saketa suka sake ta ya daka mata tsawa da karfi, duk ku fice min daga gida, magulmata tunda duk yawanku kun kasa sasanta su. Sum-sum suka wucesuna tabe baki, duk dahaka bishira bata daina magana ba.ZURFIN CIKI book 4 part 16 ZURFIN CIKI book 4 part 16 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:14 Haka umman bashar batasan yarda komai ya faru ba. Amman ta shiga zagi da tsine ma ummi har da ce mata karuwancin ne ya motsa, ai dama nasan tun kafin kixo gidan nan kinsan maza. Bishira ta ce umma wllhi ga babban mai laifin nan, muna funtata sukeyi duk ire ire wadannan kayan na jikinta shiya sai mata su, ni bai siyo min ba. Na gaji da hakuri ana cutata gwara yaban takarda ta. Umma tace daina fadin ya baki takarda insha allahu saidai ita ya bata, Abba yayima bishira wani kallo tare da cewa ki tafi mana sai me? Yarda kika gaji da ni nima Haka na gaji da ke, ya kalli ummi yace ke kuma mi nake fada maki kullum? Itama cikin fushi tayi magana toh shikenan saita ta zagina tana ma ummata sheri don ita kake so? Bishira ta cafke dama ai ya fadaman baya sonki. Ummi ta kalleshi ko zai kare kanshi, amman baya kokarin Haka saima kara zaro mata ido da yayi yana cewa. Ni kike ma ihu ummi? Zuciya tazo mata wuya nata ganin an daketa ne kuma an hanata kuka. Shi kanshi ya tozarta ta da ya fadama kishiyarta baya sonta. Duk da tasan da haka ta kalli bishira cikin daga murya tace, an fada maki na damune don baya sona bana son ya soni don nima bana son Shi.... Mari Abba ya sakar ma ummi da bayan hannu, kalmar da ya tsana kenan, zafi yakeji a Zuciyarshi ko tunowa yayi da ummi bata sonshi. Daki ummi ta fada, ta fada kan gado tana kuka, ya kalli bishira kije gidan ku sai nazo, umman bashar tace ba inda zataje kuma in ka sake na samu labarin ta tafi saina debe maka albarka. Tasa kai fuuuu ta fice, tunda ka dauki hukunki mai kyau ka duki marar kunya ai naji dadi. Bishira ma taji dadin haka, Shi kuwa ba don su yayi ba zafin furta bata sonshi ne yasa ya daketa. Yana shiga dakin ummi lokacin ta mike tana kuka, ta dauko zane ta daura tana kuka sosai. Ta zari hijabi ta zura zata fita, yace ina zaki? Taki sauraronshi zata fita ya rikota, ina zaki nake? Tayi magana cikin daga murya cikin muryar kuka tace gidan ubana kai kuma ka zauna da warda kakeso, tunda ya mareta nan ya gane bai kyauta mata ba, don yasan ba dole bane ta fahimce Shi, sai ya samu kanshi da jawota ya rungume. Duk da suna cikin bacin rai Duk kansu saida sukaji wani irin yanayi. Yace kada kiyi yaji ummi kinsan dai koh kinje su umma fada zasu maki. Cikin sanyin murya yayi maganar, kan ummi ya sara, ta kwace daga jikinshi ta sake fadawa kan gado. Sabon kuka ta saki, ya zauna bakin gado ya kamo hannunta ta sarke ya tsunshi da nata ya dan matsa, ummi! Ummi!! Tashi kiji, cikin kuka tace mi zanji yaya Abba, kawai ka rabu dani, ni baka man adalci ba. Ya za'a yi kaje kana fada mata ni baka sona kasa tana man gori, umman bashar harda ceman wai ni nabi maza. Ya sake kwantar da murya yace ki yarda ni ban fadama bishira cewa bana sonki ba, kuma batun umma kisashi a gefe kawai don ni nafi kowa sanin halinki. Nafi kowa sanin tarbiyar umma na... Duk da haka ai baka kare kanka ba lokacin da take fada ba, ummi ta katse kiran da yake mata, yasan ummi sarai yanzu kam bazata saurari komai ba, koma ta saurara zata ta kalubatanshi ne, don haka sai yace to Tashi ki bani abinci. Kin Tashi tayi don kanta jinsa take kamar ya fado, mi kewa yayi ya fita, ya rasa sukuni, koda yaje shago kasa yin komai yayi, sai murza hannunsa da ya mari ummi yake. Ya ciro wayarsa ya kira ummin tayi ta ringing kusan sau 3 kafin ummi ta daga yace haba ummi, inata kira kayi banza dani? Shiru dai tayi bata tanka ba, ummi cikin disashiyar murya tace, dama haka ne, sai an kwance ma mutum zane kasuwa azo gida ace za'a daura masa. Sai ta kashe wayar. Daga nan gidan umma ya nufa, tace anya Abba lafiyarka kuwa? Naga Duk ka ya mutse. Ya zauna suka gaisa yace umma ina fa lafia, dazun bayan sallar jumma'a ina iso wa gida da yunwa sai kurum na samu gidan tam d jama'a. Ummi da bishira na tarar suna ta zage zage har aka samu wata shedaniya taje ta kira umman bashar. Umma tace subhanallah! To ya akayi yanzu? Yace tarwatsa taron nayi, nasan koda ban tsaya bin bahasi ba ummi ce mai gaskiya. Domin bata kula bishira, Duk yarda akayi ta kure ta ne. Tsohuwa daga can gefe tace, wai bayan zuwa na gidan sukayi fadan? Abba yace oho ni ban masan mafarin fadan ba. Umma tace kai wannan abu allah ya dai dai ta maka su. Amman kyanshi kana zuwa ummin ya kamata kayi wa fada, koma ka zane ta, don itace karama. Abba har suna hada baki da Tsohuwa gurin fadin "Haba dai". Abba yace umma in itace da gaskiya kuma ai na zalinceta, yanzun da haka fushi take, Duk na tsorata bana son fushinta, sai taki cin abinci. Don allah umma bari in kira maki ita ki bata hnkr, umma tace ba zan bata hnkr ba, abinci kuwa kada allah yasa taci. Sai dai ayi tunanin abinda ke cikin ta, Tsohuwa tace, wannan sakaryar matar taka dama na lura fada takeji. Sanda nayi sallama tana zaune amman amsawa ta gagareta, don haka ma ko gaisheta banyi ba na wuce. Ita kuma takwara ka hanata saka wadannan kayan na arna. Abba yace, su ake yayi Tsohuwa, Tsohuwa tace, tafdi lallai yayi ya zama banza. Abba yake cewa Don allah umma ga nmbr bari in saka maki a waya, ya dauki wayar umma ya saka mata lambar wayar da ke hannun ummin, yace umma na roke ki lallasheta ba wai fada zaki mata ZURFIN CIKI book 4 part 17 ZURFIN CIKI book 4 part 17 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:17 Duk jumma'a abba yana dawowa gida musamman in ranar girkin ummi ne don cin abinci na musamman. Jumma'a biyu kenan bata fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin tsohuwa tazo. Don haka suna gaisawa da umma tace gurin tsohuwa nazo. Suka shige daki tace da tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin. Tsohuwa tace, name ummi? Ta ce na gyaran jiki mana. Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu abubuwa. Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari? Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana, bada ina fada miki kina sharewa ba? Ummi tace haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja hankalin mijina. Ta ce, toda farko ki dinga kula da jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar iska. Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi. Sannan ki amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga matsa farin miski a ehem dinki. Sannan ki samu saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari, mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi biyu safe da yamma. Sannan ki aya garinta, kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa, sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale, citta, lemun tsami, ki markada su kisha. In anan maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban da dukkan sauran mata. Ki hada da biyayya tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi. Ummi tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin nan? Tace, bari zanba matar ado dake yawan zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu. Amma su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan. Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi tasan duk wadannan hadin matan? Tun ranar alhamis din ta soma aiwatar da darussan da ta debo daga tsohuwa, safiyar jumma'a ranar zai bar dakin bishira. Ya fito tana sharar tsakar gida ta gaidashi, ya amsa da fara'a, tare dawani kallo mai fassarar in ba keba. Cikin muryar data adana don shi kadai tace, ya abba ina son in je ayi min zanen fulawa. Yace jiya kin fita yau kam a'a. amma ki aika akira mai zanen tazo ta miki. Ta marairaice, towa zan aika yaya abba? Yace aike ni, ina ne gidan? Tace layin su umma ne yace to za'azo ai miki. Bishira tafito daga daki tazabga ma ummi harara, Tare dacewa kisisina. Abba yakalleta, kema sai tayi miki. Tace bana bukata, aikin banza, shikam yafice. Ummi kuwa tace gaba da aikinta, ita ko sai tasa kujera tazauna tana sakin zantuka, eh don kwalliyar tabanzanta tunda ba a iya biyawa miji bukata. Allah dai yasa ya fada min komai, to ni me zai dame ni don 'yar aiki kawai na dauki yarinya. Tashare min gida, tayi wa mijina abinci, daga nan fa? Saita saki shewa, ummi ta ce aranta yau zan bambance miki. Birabiskon shinkafa tayi da miya, ta wadata birabiskon da kayan lambu, miyar ta dauki nama da bushasshen kifi. Sannan ta hada musu kunun aya yaji dabino da madara, ta aikawa ummanta lokacin da kamal yazo daukar na ummarsu. Tasheka wanka taci doguwar rigar shadda koriya mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau ne daurin aurensu. Ga fulawar da yaje ya biya akazo aka zana mata. Tanajin rigimar muhibba tafito tazuba mata adan kwano tazaunar da ita akofar falon mamanta. bishira tafito kicin baki tasaki tana kallon ummi da tazo wucewa harda bangazar ummi, nan ko kamshi ya bude ta na turarukan da ummi ta fesa. Abba yana yin sallama ummi tafito da sauri, oyoyo yayana, bishira tana daga kicin dinta tana kallon su. Ummi ta rungume shi, sannu dazuwa sahibina. Ta amshi ledar hannunshi dajakar, yace yauwa sannu babyna tace inazan kai ledar? Yace akwai ta bishira aciki ki ciro. Ta mika mishi ledar ta wuce dajakar dakinta. Ya mika wa bishira lemo da abarba da yayo musu tsaraba sannan ya wuce danasu, awulakance ta aje. Yana shiga ummi tadan karo kofar yanda bishiran zata iya lekensu sosai ta gefen kofan. Ta cire masa hula ta aje akan madubi sannan ta kunna fanka. Ta shirya masa abinci, yauni zan baka har ka qoshi. Haka suka yita baiwa juna abaki har suka qoshi. Yakamo hannunta mai qunshi yana ta sumbata, wai kamar kada su goge. Kumatun shi ta shafa nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me kyaune, ina sonka ya abba sosai. Cikin jin dadi ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada wata rana ka juya min baya. Ya saqalo hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin lokacin. Ummi tasomayi masa wasu irin darussa wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama surutai. Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi duniyar ma'aurata. Bishira tamkar tayi hauka sai kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana, har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba munafiki. Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka, ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu? Da taga ya sauko da zafin rai saita gudu dakinta. Yabita yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai komane yaci gaba daga inda ya tsaya. Tayi ta kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir dole ta tafi gidansu. Shi kam abba shareta ya yi kosu umma bai fadawa ba. Sabuwar soyayya ma ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su fita yawonsu a qafa ko amota. In yana gurin aiki bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman dazata fada masa take.ZURFIN CIKI book 4 part 18 ZURFIN CIKI book 4 part 18 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:19 Ummi tayi alalar gwangwani ta sauke kenan sai ga aunty farida da yake tunda akayi auren ummi batazo gidan ba. Har daki ummi ta shiga suka gaisa tayi masu addu'a zama lafia, tayi mata nasihar zama da miji. Umman taji dadi tare da kwadayin ina ma bishira take da halin yayarta, ta zuba alala ta kaima aunty falon bishira. Ta isko su tana mata fadan kaxanta, cikin murna aunty ta anshi alalar taci bishira ta cika fam. Tun tana jurewa har tace aunty ai kin zubar min da kima, ya ya za'a yi ki anshi abun kishiya kici. Aunty ta kalli bishira fuska daure tace ke da ita akwai bambamci ne? Bishira tace aunty bambamci ma nifa jininki ce ita fa? Aunty tace a musulunci fa? Bishira ta hade rai tana kallon aunty, taci gaba da cewa, A musulunci tama fiki don tana sallah, Haka nima ina sallah, kefa kin faru? In kin soma sallar to kin shigo cikin mu ni da ita. Domin addinin mu ya nuna muna dukkan musulmi dan uwan musulmi ne. Inji mai tsira da aminci. Haka zan iya cin abincinta banci naki ba don bakida tsafta. Ta daka mata tsawa tashi don allah malama kije kiyi wanka, ki wanke duk jirwayen nan naki kafin In daukeki da motata. Da zasu tafi har kudi aunty farida taba ummi, ummi kam godiya ta dinga yi. Haka nan da abba ya shigo ta nuna masa tace ai abba ya ciri tuta a zuri'arsu, halin mahaifinsu ne da ita. Wata rana aunty ta bugo ma abba waya cewa aisharsu ta haihu don allah ya fadama bishira koda ya iso gida ya fada mata nan ta shiga murna. Washe gari tace zata gida tama mahaifiyarsu barka. Sannan taji randa zasu abuja wurin aisha. Yace ta shirya ya sauketa, ta samu aunty tazo nan dai sukeyi wa juna barka, mahaifiyarsu tace dubi yar uwarki sai yanxu ta haihu gwanin shawa. Amman kinje kin gwarje miji ma yayi maki kishiya, dubeki kamar ba yar gidan nan ba. Aunty tace mummy ai ita taso ta zama Haka, tunda kaxanta ce sana'arta. Hajiya zainu tace ni wani lokacin bana ganin laifinta a kaxanta, don a gida bata saba aiki ba. Laifinta daya a gurina wannan abba data nace ta aura, data tsaya ta gama karatunta ta auri wanda zai dobo mata yan aiki komai saidai ayi mata tana daga zaune, amman ta likema talakan tela wanda bashida ko sisi. Aunty ta katse mamarsu da cewa In tana da yan aiki shine har wanka zasuyi? Ta cire dan kwalin dake kan bishira kalli fa mummy har kanta zasu wanke mata. Mummy tace aiki gida ya mata yawa, yaushe har ta gyara jikinta? Aunty tace kawai mummy kina goyon bayanta ne. Bishira tace aunty mummy ta fahimta kece baki fahimta ba saboda kina da yan aiki. Mummy tace duk ba kece kika yima kanki ba, ga kishiya an maki, bishira ta tabe baki nima duk nadama ta isheni. Kuma shi da matar duk bana raga masu. Don ban damu ya sakeni ba, yaji ne dai nace na daina, daddy ko nazo cin mutuncina yake gabansu. Mummy tace kin man dai dai. Haka yake bishira kullum cikin tsokanan hayaniya da ita da miji ko kishiya. Amman ummi yamxun bata kulata Domin umma ta gargadeta. Bishira bata bar gidan ba saida mummy ta zugata Sannan tace mata jibi kizo za a kai su innarku yin barka abuja kije ki dan huta kafin suna. Bishira tace daman ban taba zuwa ba, ko anyi suna sai na huta. Aunty tace kada ku yanke hukunci ba tare da sanin mijinki ba kije kiji ta bakinsa. Bishira ta ce ina ruwana da yardarsa aunty. Haka kuwa data dawo ta shiga tattaro kayan ta dake jibge a gefen gadonta, don ita zane ko yau a aka dinka shi In tasa ta cire duk In da tayar kafin ta dauke shi yaji jiki. Wani ma saita goge ruwa ne, kamu ne, duk kyan zani saita goge tsakar daki dashi. Ranar dama abba dakinta yake, tace mashi jibi zamu abuja Inji mummy. Taso ya dan sai mata zani sabo wanda zata danci suna ya dinka mata. Yace akwai wani leshi dan sai maku yana shago, Tun wancan satin naso In zauna In dinkashi da kaina don mai tsada ne. Tace nawa ka siyeshi, yace dubu biyar ko wane daya, bishira ta tabe baki. Na zaci zakace sha biyar wai dubu biyar, yace matsalata da ke rainuwa yace bari zansa a dinka maku gobe ashe sunan har yazo? Tace a'a jiya pha ta haihu, ya sake kallonta jiya? Shine zaku tafi jibi? Tace eh mummy ce tace mu tafi jibi. Yace a'a kibari sai ana gobe suna kije. Kafin lokacin ma na samu wasu kudi da nike sa rai. Sai na sai maki kayan barka zanen maman da kayan baby. Bishira ta ce gaskia gobe zamu tafi, In ka sayi kayan barkar ka aika dasu can wurin mummy yan tafiya Ranar suna su kai mata. Abba yace nifa ban amince da tafiyar nan gobe ba. Ban yarda ba. Bishira ta ce ba wai ina neman yardarka bane, ina fada maka umurnin da mummy ta bani ne, ko ka mance mahaifiyata ce? Mamakinta ya cika abba, yace mahaifiyarki ita zata baki izinin tafiya ko ni? Umurnina da nata yanzu wanene...? Bishira ta katseshi kada kayi ganganci hada kanka da mahaifiyata, ita ta haifeni ta raineni har ka ganni kace kana sona Sannan ka dinga kokarin kwatanta kanka da ita? An fada maka kowa baisan darajar mahaifiyarsa ba irinka? Abba ya mike ni ne bansan darajar mahaifiyata ba? Tayi shiru yace nagode Kuma suna na hanashi ma gaba daya. Zan gani Kuma Bishira ta ce zako ka gani.ls / ZURFIN CIKI book 4 part 19 ZURFIN CIKI book 4 part 19 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:14 Duk ummi tana jiyo su amman bata fito ba, tana ta mamakin yarda bishira batasan darajar aurenta ba, bare tasan girman miji. Ranar da zasu tafi kuwa ko a jikinta ta dibi tsummanta ta nufi gidan su, Duk ta fadama mummy yarda sukayi. Mummy tace kinman dai dai talakan banza shine zai hada kanshi dani, tafiya zakiyi in yaso in kika dawo ya ce baya auren. Abba ya dawo ya samu dakinta a rufe, ummi na daka sakwara a kofar dakinta yace ina bishira? Ummi tace ina ga ta fita, don ina daki bansan fitarta ba. Ya daga waya ya kira aunty yace bishira tazo? Aunty tace bata fada maka zasu tafi abuja bane, Abba yace ta fadaman amman nace a'a sai ana gobe suna zataje, ya kwashe komai ya fadama aunty. Aunty tace kayi hnkr don allah idan ta dawo da kaina zan hadata da daddyn mu, Abba yace kiyi hnkr aunty na gaji da halin bishira inga wannan karo gwara kowa ya huta ni da ita. Aunty tace kayi hnkr Abba yace sai anjima ya kashe wayarsa. Zama yayi kan kujera dakin ummi yace gaskia wannan karo bazai fadawa kowa ba ya gama auren bishira. In bai nuna mata kurenta ba nan gaba zata masa abunda yafi wannan don Haka yabar komai sai ta dawo. Ummi kam batason ya rabu da matarsa, amman kam saida taga tarairaya cikin kwanu kan nan matsalarsu daya, Abba yace ummi kodai asibiti zamuje ne, ummi tace muce masu mi? Yace muyi masu bayani mana, ummi tace a'a. Yace to muje mu fadawa umma, ummi ta zare ido yanxu sai kama umma wannan zancen? Yayi murmushi. Ai da zan iya mata wannan maganar da tuni na mata, asibiti ma abunda yasa banson zuwa sai likita ya bukaci ganin wurin. Ni kuma ina kishin wani namiji ya kallan mi al'aurarki, ummi tace nima ai shine, ya sake janyota jikinshi. Yanzun Haka zamu zauna? Shine nakeson in fada maka naji kana ka gaji da aunty bishira kila zaka saketa ne. Toh don allah ka rabu da ita tunda ko ka saketa sai ka auri wata. Tunda nasan zama Haka bazai yiwu ba. Ta soma hawaye ya shiga lallashinta yace Allah zai yaye masu. Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kwanakin da bishira bata nan, ummi tanason kalolin wasanin da Abba ke mata, amman da yaso kwatantawa ko allah ya amshi addu'a su ta warke saita kwace jikinta ya hau bari tayi ta kuka. Don Haka sai ya hnkr da bukatarsa amman ya takura sosai, kuma yana ganin dole yabar batun bishira yanxu don Haka ya jaye batun saki amman sai dole ya nuna mata kurenta. Ranar data dawo kwananta takwas Ranar ma bata da niyar dawowa sai da aunty ta kira mahaifinsu ta sanar dashi, ya kirasu a waya ya zagesu tas gaban mahaifiyarsu harda mai jego. Tace bishira ta dawo shine ya kira Abba da waya ya bashi hnkr yace Duk irin wannan ta faru ya kirashi ya sanar dashi. Abba ya shigo da T. V guda 2 daya ya kai dakin ummi, daya ya kai falon bishira wanda ya yanke kwadon. Ummi tayi ta murna bishira kuma ta daki Duk rashin kunyarta gabanta sai faduwa yake, batasan ya zasu kwashe ba. Sai da taga baiko kalleta ba daga ita har yar sannan ta dan saki jikinta, tasan ba zai tsaya a fushi ne in taci sa'a. An dauki sati guda Abba baya ko kallon inda bishira ta ke ko Ranar girkinta sai dai yayi kwanciyarsa a falonta. Duk da yana bukatarta Haka kuma ya janye yan wasanin da yake da ummi don wahalce yake bacci, ita kuma sai ta damu don ya saba mata sai tayi tunanin ko laifin tayi masa ne. Ita kam bishira ganin zura ido ba zai kaita ba, don Haka ta sauke zafin kai ta iske Abba a falonta wani dare harda kukanta take bashi hnkr. Wai sherin shedan ne ba zata sake ba, Abba ya dubeta mi kikayi? Tace nidai ka yafeman, yace ashe kinsan kinyi ba dai dai ba? Ai inda ke ce saikin kara, amman bari kiji na rantse maki duk kika kara zuwa wani wurin bada izinina ba wllhi sai kinsha mamaki. Tace na yarda, abun mata da miji nan dai suka sasanta, hakan nan dakin ta ya kwana, suna shiri cikin satin don bishira ta fahimci mijnta ita kadai a matarsa, yarda yake rawar jiki lokacin kwanciyarsu. ***ummi na zaune idonta kan tv Abba take kallo yarda yake watso turanci cikin kwarewa. Kullum kara sonshi take, ta kwantar da kanta a hannun kujera, kusan sati guda kenan tana lura da Abba. Baya son ko taba hannunta sannan ga wani shiri da yake da matarsa, sai dai yazo yaci abinci ya dauki laptop dinsa ya raba dare. Inko yazo kwanciya saidai ya juya mata baya sabanin kwanaki da yake mata makwanci da hakarkarinsa, lokacin tasan babu inda keda dadin kwanciya ga matar aure irin hakarkarin mijinta, sam bata iya bacci sai tunanin abunda tayi masa, amman yau din nan zata tmbysa ko laifi tayi masa, Bayan yaci abinci yayi wanka ta dauko mai zata shafa masa ya amsa da murmushi yace barshi kawai nagode, ta dawo ta zauna, zaya fita tace ina zaka ya Abba, yace aski zani, ko zaki rakkani tace eh yace taso muje. Suna tafe suna hirar aikin shi, yace An koma kirkirar wani filin kuma An saka shi ciki, yanxu abubuwa zasu kara mashi yawa. Sun isa babu layi An suma mashi ya mika mata wayoyinsa guda biyu tana danne danne kira ya shigo. Nan take ta hade rai ganin sunan dake jiki zainab dina, ya tmbyta da ido waya kira ta sake hade rai, sannan ta mika masa. Ya kalli sunan zainab sannan ya daga cike da son ya zolayi ummi yace zainabuna. Can bangaren Duk da kallaman Sun mata dadi tace da ba amman yanxu ta wani ce. Yaya salis ya kawo maka katin aurena? Yace eh yabani tace ya amarya? Yace gata bari in bata ku gaisa, ummi ta kauda kai tare da jan tsaki, yayi dan murmushi yanason yanda ummi ke nuna kishinsa, salon da take wurin kishinta daban ne. Yace zainab Wai tana gaisheki, zainab tace to ina amsawa. Ka gaida umma sannan ka sai masu anko kalla biyu ne. Abba ya naji ko kalla goma ne zan saya tace to gobe kazo gidan mu nan ake sai dawa. Ya kalli ummi yasan kadan ya rage ya kaita bango. Ya danne dariyar da ta taso masa yace gobe kikeso nazo gidanku zainab? Tace eh don gobe za'a kawo wasu kayan, yace to zanzo, ummi ta zaro ido ta mika tsaye dai dai lokacin da aka gama askin. Yayi sallama da zainab din sannan ya shiga karkabe jikinsa. Ummi kam tuni ta kai bakin kofa. Ya sallami mai askin ya isketa Sun jera yanxu ba kamar daxun da suke fira ba. Sun kusa layinsu yace muje mu gaida su umma tace ni bacci nakeji baice komai ba, Sun iso hijabi kawai ta cire ta kwanta, yace Wai lafia don zainab ta kirani tun dazun kin kasa sukuni?URFIN CIKI book 4 part 20 ZURFIN CIKI book 4 part 20 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:17 Ummi ta taba baki, Allah yakawo ta lpy. Ya ce ni ban soba gsky. Sbd ke ummi tadafa kirji, sbd ni? Ni ya abba, kada kasa duniya ta zage ni, Tare fa nasameku? Yace to ni dai kada kiga kamar da son raina, tace don Allah ya Abba kabar zancen nan. Kaje kagyar mata dakunanta

Chapter 20 of 24