Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Ina tunanin yanda abubuwan za su kasance gobe. Yanda har za'a yi fenti, sannan a jire kuma in tare duk a gobe". Ya ce "Duk mai sauki ne, ni kuma kin san tunanin da nake yi yanzun? Ta ce, "A'a, ya ce gobe kamar yanzun muna tare... da sauri ta katse wayar, me Ya Abba ke son fada? Ta kashe wayar sannan ta kudundune. Ita ma yanzun ya jona mata wannan tunanin, a fili ta furta gobe kamar yanzun me ya ke faruwa? Shi kuwa sai ya ji haushin kansa sakamakon furucin da ya yi har ta yanke wayar, wani gefen kuma sai ya ga kila don bata sonshi ne shi yasa har ta ji haushin furucin nashi. Kila ma yanzun tana can tana kuka in ta tuna gobe tana gidansa, dare ya tsala amma ya kasa bacci, don haka sai ya mike yayo alwala. Sallah ya shiga don kara nuna godiyarsa ga Allah da ya bashi Ummi tare da rokon Allah ya kimsa mata sonshi, daga karshe ya roki hadin kan matansa. 34 63..Yana wanka da safe ya jiyo muryar mum dinsa harta zo gdn, a zuciyarshi yace innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yana fitowa tace wurinka nazo, Bashir yazo ya fada min cewa yau za'a kawo fitsararriyar yarinyar nan ko? Abba cikin damuwa yace umma nima bansani ba, tace munafiki kasani, bari kaji ko an kawota ko magana bance ta hadaku da ita ba, kai in ma kaje girin munafukan iyayen nan nata su ka ce yau zata tare kace saika shirya. Bishira tace umma bazan yarda ta tare ba, bai sai min komai ba, ya kalli Bishira to itama na sai mata wani abun ne? Sahura tace to ina ruwan wani da baka sai mata ba? Abba yace toni bani da kudi ma, Bishira tace to kudin jiya da babana ya baka fa? Umma tace fito dasu, yace umma dama fa kudin sadaki ne ya biya min, kuma naba alhji karami waliyyinta sai dai ki je gun shi ki amsa, tace don kasan bazan tunkareshi bane shi yasa to tana binka bashi, zaka chanza mata kayan daki, ka sai mata zannuwa sannan ka bata jari, yace umma banyi alkawari ba, in dai na samu kudi kuma ta kwantar da hankalinta to xan mata, ya nufi daki yabar su nan sunata zantukan su. Lkcn daya shiga gdn su umman shi, ummi tana linke kaya tana sakawa cikin jaka, yana daga bakin kofa ta dago ta amsa sallamar shi ta kalle shi, ya kalli kayan sam zuciyarshi bata mishi dadi, ya nufi wurin umma don yana son neman alfarma abar ummi zuwa dan wasu kwanaki don yana so ya dan gyara gidan, rashin galihun zai yi yawa, ba lefe kuma gida ba gyara? Yayi sallama suka amsa, bayan ya gaishe su, ya dukar da kai yace alhji dama nazo ne neman alfarma, suka ce alfarman me? Yace inaso ne kudan bar ummi zuwa nan da sati daya, sannan na gyara gdn, kuma nayi mata sabbin dinki, alhji yace ba kana da fentin ba? Kaje kasa a goga, sai ka biyo ta kasuwarmu ka amshi zannuwa, abba yayi shuru umma tace koda wani abu bayan nan? Yace a'a, umma tace to an daga maka zuwa gobe, yace to umma da alhji nagode, ya mike ya zai fita, yace am umma ummi tace zata je gyaran gashi, suka yi dariya su kace ai wannan ikon kane, yace to na tafi alhji sainazo kasuwar, ummi ta jera masa kayan karin kumallo koda ya leka dakin sai tace ya abba ka shigo ga break, yace ummi zanyi latti, tace to da yunwa zaka tafi? Yace akwai shayi a can, tace come on ya abba zoka karya, ya kalli agogo minti biyar gareni, ta dau copi ta tsiyayo kunu ta mika masa, ya fara kurbar kunun, ta zubo kosai a plate tarike a hannunta dauka kaci, ji take tamkar ta bashi a baki, tsohuwa ta dago labulen dakin, tace zura masa a baki za kiyi? Ummi tace kada ya kware tsohuwa, an hana yin magana in ana cin abinci, toshuwa tace tafi can da cusa kai ba kwarjini, abba ya dire kofi tareda mikewa yace ummi saina dawo, ki bari da dare zan kai ki gyaran gashi, yasa hannu a aljihu ya zaro yan dari binbiyu guda biyar ya bata, tayi godiya ya ciro dari yaba tshuwa yace yar sa ido kema kiyi kotso da wannan, ta rike baki tana fadin wannan yara da munafunci suke, ya fita yana murmushi ummi tace a dawo lfy, ya sake waiwayo wa ya kalli ummi, suka saki murmushi, 35. 64.... Tsohuwa da ke bin su da ido ta ce, "Kai ban yarda da ku ba Takwara, dama can ke da me sunan Malam soyayya ku ke? ---- Umma da ta tsinci zancen bayan fitowarta daga dakin Alhaji, ta ce "Ya a ka yi?" Ta ce, "Suwaiba ina ga yarannan tuni kallonmu kawai suke. Sai wannan salo suke wa juna, sannan ga Takwara ciwon barin gida shiru, ina ga dama ciwon nan na mai sunan Malam ne." Umma ta saki dariya tare da cewa "Allah yasa haka ne. Ummi kam cikin daki ta kule zuciyarta zallah dadi. Misalin karfe biyu Umma ta dan kishingide baya, ta idar da sallah, tsuwar wayar da da Abba ya ba Ummi ajiya ce ta farkar da ita. Ta ce, Ummi me ke tsuwa a dakin nan? Wannan dai ba wayata ba ce. Ummi da ke tsakar gida ana mata zanan fulawa ta ce, Lah, Umma Ya Abba ne ya bani ajiya. Kila ma shi ne ya kirata, ta dubi wadda ta yi mata zanen fulawar ta ce Sabira don Allah shiga ki dauko min a kan gado. 2missed call ta gani, ta ce kash! Sai gashi ya sake kira, kafin ta daga sai da ta leka dakin tsohuwa ta hango ta kwance a gadonta. Dama a kofar dakin Tsohuwar take ta biyo inuwa ta daga wayar tare da sallama, ya amsa cikin dokin jin muryarta. Ina ki ka shiga ne? Ta amsa a can cikin makoshinta, ana min fulawa a tsakar gida wayar kuma tana daki. Ya ce, Ok ana miki zanen fulawar ne? Ta ce an ma ganin har ya fara bushewa ya saki murmushi tamkar yana gabanta. Ana yi miki me kyau? Ta ce, Eh yayi kyau sosai, ya ce Good, zan dawo kamar karfe uku saboda zan kwashe kaya za a yi fenti a daki, so kin ga ba zan samu kai ki gurin gyaran gashin da wuri ba. 65... Don haka sai mu bar shi zuwa dare ko? Ta ce, "To Ya Abba, ehm za a dafa maka wani abu ne? Dadi ya lullu6e shi amma saboda burinshi na kimanta Bishira a idonta sai ya a'ah. Na hutar da ke zan ci na Antynki Bishira, maganar ta soki ran Ummi har ta kasa magana, ya fahimci hakan don haka sai ya kawo zancen da cewa sai nazo. Ta tura baki tare da cewa uhm, tana kashe wayar ta shiga kunkunan cewa in yaso kaci abinci gidansu bana ta ba. Tsohuwa da ke sauraronta ta sheka dariya tare da cewa, ba dai ke kin ce me sunan Malam ba? Sai ma kin je gidanshi yarinya ban miki baki ba amma za ki raina kanki. Ummi ta cafke cikin jin haushi ta ce, wai to Tsohuwa da za ki ce na ce Ya Abba cewa nayi ina sonshi? Kuma da su Alhaji suka jona ni da shi da naki har da ke za a dinga cewa ban yi biyayya ba. Tsohuwa ta ce, Raba ni da gulmarki, kina sonshi ai ni ba yarinyar goye ba ce, kina waya kina kashe murya, san nan ciwoce- ciwancanki duk sun lafa. Sai wannnan rawar kai ki ke, to ki sani me sunan Malam dai ya aure ki ne don dole, matar cushe kuwa ba daraja take ba. Ummi ta ce, "To nima dai ai ba sonshi ni ke ba, ni dai tsohuwa don Allah ki daina samin ido. Ta mike, Na ma bar miki kofarki. Ta nufi kofar dakin Alhaji tana kunkunai. 36. 66... Sai dai duk da haka kalaman tsohuwa sun tsaya a ranta, matar cushe bata daraja, Ya Abba kan dole ya aureta, lallai zancen tsohuwa abin dubawa ne. Abba ya shigo gidan uku da doriya, tare yake da yara guda biyu, dayan zai mishi dan face-face, dayan kuma zai masa fenti. Sune suka taya shi kwasar kaya, bai samu Bishira a gidan ba, kila tana gidan Ummanshi, ko makota. Sun kama aikinsu shi kuma ya shiga kicin don ya dan dafa abinda zai ci. Bishira gidan Anty ta tafi kuka take wiwi wai ita fa ba za ta iya zaman gidan nan ba, ta ce "Aunty Farida tunda kuna shiri da Baban Walid ki ce masaya sawake min". Anty Farida ta tsura ma kanwarta ido, tausayin Bishiran ya cikata. Tabbas kishiya bata da dadi koda mahaukaciya ce bare mai hankali. Sai dai ita bata da ikon da zata hana ayi kishiyar koda kuwa mijinta ne ke son yi, don sunna ce ta mai tsira da Aminci. Bishira ta katse mata tunani da cewa, dubi fa Anty hatta Dady yanzu yafi son Baban Walid fiye da ni. A gabana ya dauki kudi yaba baban Walid, a halinni kara na kai a kar6ar min 'yancina, kuma Momy zata yi magana ya hanata cikin tozartawa. Hakan da Daddy yayi ba zubar min da kima yayi ba, har da ita Momy? Yaushe Baban Walid zai sake ganin darajarta? Anty Farida ta sauke ajiyar zuciya, ta ce "Bishira Dady bai zubar miki da mutunci ba, illa kara tarairayo miki mutunci da yayi daga ke har Momy. Kuma ni ba zan ce mijinki ya sake ki ba, haka nan ba zan ga laifinshi ba, domin aure sunna ce ta Manzon Allah (S.A.W), sam ba zan yi fushi da wanda ya raya Sunna ba, koda mijina ne. Kiyi hakuri kanwata koda bani da kishiya nasan akwai zafi, amma kema kina da laifi, dube ki fa. Yanzu Bishira wa zai gan ki ya amince ke kanwata ce ta hudu? Zato za a yi ke yayata ce, kin saki kin yi ragwaf, nonuwa har ciki haihuwa biyu jal, dubi yanda tsabar datti yasa fuskarki da dokin wuyanki zuwa bayanki duk kyasbi ya miki riga. Da kin zauna kusa da mutum wari ki ke tashi, hakora sun miki yalo, kai mijinki fa ya yi kokarin ba kowane zai dauki hakan ba. Duk ba ki kalli laifinki ba sai don ya kara aure yanzun? Ina ce kwanaki garin shegen gantalinki ne ki ka bar danki a gida ya fada rijiya ya mutu? To hatta Abban Nasir ce min ya yi da shi ne ba zai yarda ba, saboda haka ki dawo hankalinki ki zubar da kazantar nan ki kama Ibadarki. Bishira ba kya jin kunya a ce ba kya sallah? Kuma a tare da haka kina da wannan kazantar ki ke kaurace ma shimfidar mijinki. Kwanan baya ya kira ni a waya ya sanar da nicewa kin ce min ina wari, don haka ni kuma na ceya tafi gurin mai tsafta mai kamshi. Shima fa Anty magana yake dankara min don ba kisan halinshi ba ne. Anty ta ce, "Bishira kina cikin hadari, ga kin sallah sannan ga kauracewa miji ki kwana Mala'iku suna tsine miki. To daidaita sahunki, ga mijinki dan kwallisan dan Jarida mai farin jini, ki kalli yanda in yana gabatar da shirinsa yanda 'yammata kan kira su ce suna son lambarsa. Amma ke kina sakaci da shi, ki dubi yanda wata mata ta kawo masa hari kwanaki da a ce ya yarda ke ba za ki san kina da kishiyar waje ba. Ki shiga taitayinki zan dai miki taimako daya in kinamince za ki natsu. 67.... Bishira ta ce, Anty taimakon me? Ta ce, "Zan samu Momy su taimaka su canza miki kayan daki, sannan Dady ya ba mu kujerar Makka ni da ke da Aisha. To sai ya ce tunda ke kin ki kwantar da hankalinki ki kwantar da na mijinki to ya fasa naki, mu harmun yi passport. Bishira ta zaro ido, da gaske Anty? Anty ta ce, Allah da gaske. To yanzun shi ne ni ke son in ce muje mu ba shi hakuri kila ya amince. Bishira ta ce, Tashi muje Anty don Allah, Anty ta ce kin tambayo zuwa can ne? Bishira ta ta6a baki, nifa ko nan din ban wani tambaya ba, wallahi gidan ne bakikkirin nake ganinshi. Anty ta ce, "Ki dinga addu'a, kishi yayi miki yawa. Sannan ki daina fita ba tare da izinin mijinki ba, duk in da ki ka je har ki dawo Mala'iku suna tsine miki. Don haka yanzun tashi ki tafi gidanki, ni zan samu Hajiya da Dady yau din nan kuma in sha Allah za amiki gyaran dakin, sannan tafiyar za ta kasance tare da ke. Bishira ta ce, Na gode Anty, amma don Allah ki barni na dan huta a nan gidan duhunsa nake gani, don ba ki ji yanda ni ke ji ba ne Anty ko da dana Walid ya rasu ban ji kunci irin wannan ba. Ta sake rushewa da sabon kuka wiwi, Anty kallonta kawai take ta ma rasa me zata ce. Wayarta ta ciro daga chaji ta shiga kiran layin Abba, lokacin ya kira kananan kannanshi su Kamal suna ta fito da kayan dakin Bishira saboda ayi fenti har an gama nashi dakin. Wayarshi da ya ajiye a kan windown dakinshi ta shiga ruri, ya duba, Anty ce. Ya daga tare da sallama, ta amsa ya gaida ta cikin girmamawa da mutuntuwa, ta amsa da fara'a sannan ta ce, "Abba ga Bishira nan tazo tana kuka, kuma ta ce min ba ka san ta fito ba". Ya ce, "Eh haka ne, ta ce don Allah in baka wani abu ina son ganinka. Ya ce To zan zo Anty, amma yanzu ina aiki ne kayan dakin ta muke fita da shi za a yi mata fenti ne, ta ce To ko da dare ne haka, ya ce to zan zo. * 68.... Ummi tana ta zuba ido ganin Abba amma shiru har a ka yi Magriba tayi wanka tayi sallah. Tana zaune har Isha'i tayi daga Masallaci shima ya nufo gidan su Ummi, lokacin Ummi tana bakin gado tana 'yan shafe- shafenta.Ta juyo Abba suna gaisawa da su Umma, ta shirya cikin leshi mai ruwan lemun tsami, da dan mayafinta fari haka takalminta. Ta fito tana zaune kan kujera, ta ce "Sannu da zuwa. Za ka ci abinci?" ya ce, "Da sauri haka ba muko gaisa ba?" Ta zauna ina yini? Ya ce, lafiya lau. To na kawo abinci? Ya ce, daga gida fa nake, ina da kuma mata. Ummi ta ta6a baki, oh, haka ne ashe kana da mata, gani nayi da matar taka ka ke zuwa cin abincin daga nan ta lafe a kujera tare da hada rai. Ya mike muje ko? itama ta mike, ya kalle ta da wannan mayafin za ki? Ta ce, eh, ya ce a'a dauko hijabi ba zan lamunci yafa wannan dan mayafin ba. Ta kalle shi kamar ta ce ai matarka tana yafa irin shi sai kuma tayi shiru ta nufi uwar daki don dauko hijabi. Shi kuma ya nufi waje, ta yi wa su Umma sallama sannan ta fito. Yana tsaye jikin mota ya ce, ina wayar nan? Ta ce, "Gata nan a hannuna ya yi dan murmushi yace mayyar waya dama nasan sai kin dauko har yanzun cikin haushin maganar shi ta dazun take yi. Don haka bata kula shi ba, ya shiga motar ya bude mata gefen kusa da direba ta zauna cikin fushi. Lura ya yi da hakan, don haka sai ya ce ba ni tamata ta ce so nake in loda mata kudi. Ya guntse baki don kada yayi dariya, ganin yanda tamiko mishi wayar cikin hanzari gata Allah yasa bacewa nayi a bani ba. Ta juyar da kai tana kallon titi, shima bai sake cewa kala ba har suka shiga cikin gari. Ya dube ta, wane shagon zamu? Ta ce, duk wanda kaje, ni sanin wani saloon nayi? Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar Maiduguri.Shamsy belloRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 9 ZURFIN CIKI book 3 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:40 nayi? Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar Maiduguri. 69.... Abba ya ce mata ga Amaryata a gyara mata kai duk da ba wai gashi ne da ita ba ya yi kyau sosai ko nawa ne zan biya. Mai shagon tayi 'yar dariya, zan mata yanda ka keso ya dubi Ummi wadda ta samu kujera ta zauna fuska daure. Ya ce, "Kanwata zan tafi nayi aski nima, daga nan sai na dauki matata daga unguwa na kaita gida, sannan ta san in har ta bude baki to kuka ne zai kwace mata, don haka sai ta yi shiru. Ya fita yana 'yar dariya, mai shagon Yagana saloon ta ce, "Kai kanwata kun dace fa, kuma da alamayana sonki sosai.Ta kalli mai shagon hawayen da take makalewasuka zubo, ta ce "Anty ina so a nan, dubi fa abinda yake min.Komai sai ya ce min matarsa, matarsa, ko inaruwana da matarsa? Yagana ta ce, "Yana da matane? Sam bai yi kama da mai mata ba.Ummi ta ta6a baki ta ce, "Yana da mata da yakeso ni bana sonshi, baya sona, iyayenmu ne sukahada mu.Yagana ta ce, in ma ke ba kya sonshi shi kam yanadauke da tsantsar sonki a idanunshi n fuskancihakan. Ummi ta ce, "Anya kuwa? Bana zaton yanasona ne, in kin ce yabi iyayenmu ne zan fi yardadon shi din mai biyayya ne.Yagana ta tura mata kujera, zauna in soma miki,sai da ta fara gyara mata kai sannan ta ce, "In mamijinki ba ya sonki to kuwa ba za a yi wuyarshawo kai ba.Ummi tayi murmushi tare da kallon fuskarta tamadubin da suke fuskanta, ki ke gani Anty? Ta cesosai kuwa, ki tarairaye shi da kyau, kin san shinamiji dai dan shauki ne da son nishadi. (((KWARAI KUWWA!!!)))Ga kuma son tarairaya kamar jaririn yaro, ummi tace, "To zan yi hakan in har yin hakan zai sa ya soni.Yagana ta ce, "Zai so ki, zan so kiyi gyaran jiki dafata, Umi ta ce, kamar ya ya? Yagana ta ce, kayanmata zuwa gyaran fata, wanda za ki sha don 'karinni'ima. Ummi tayi shiru, don bata son irin wannanzantukan.Ta ce, "Kin yi shiru, Ummi ta ce Ummana ta ce bata son in sha komai, tunda ni budurwa ce, in je wamijina da ainihin halittata.In yaso daga baya sanin saboda 'yan garinmu sunzo da shi daga Zamfara. Yagana ta ce, Hakan mayana da kyau, domin Amare da yawa suna shanwahala sosai kasancewar ba su saba ba.Sannan mazajen ba su bambance ainihin yandamatan suke. Ummi cikin gundira ta ce, Gara ma nagyara fatar.Yagana ta ce, "Wancan ma za ki neme shi, ko nangaba Ummi ta ta6a baki, ni dai fada min na gayarnfatar.Ta ce, "Ina sai dawa in kina so zan baki kije gida kihada kiyi zan hada ma angon lissafi da shi Ummita ce, ba ni sai da suka gama a ka gyara matagashi fes, sannan ta dauko kayan ta shiga lissafamata kamar haka:-1. Man Zaitun2. Lalle3. Kurkur4. Madara ta ruwaZa ki hada su guri daya ki kwa6a, sannan ki shafejikinki da su kafin shiga wanka, in ya bushe idan zaki shiga wankan sai ki murje shi tas, dukwadannan 'yan kurajen na fuskarki za su mutu,jikinki ya yi laushi da sheki.Ga kuma wani.1. Sabulun Ghana2. Dettol3. Zogale4. Farar AlbasaZa ki hada Sabulun Ghanada da Dettol da garinzogale, da farar albasa, ki hada su ki kir6a kimurmule shima a jikin za ki ringa shafawa.Da fuska kafin ki shiga wanka, zan bar ki da biyunin sun amshe ki ma sun ishe ki. Yanzun ko inwanke miki kafa? 39. 70.... Ummita ce, "Ina tsoron kada yazo kuma kudin shi ba su kai ba, Yagana tayi 'yar dariya, kina tausayinsa ne? Ki daina tausayin mijinki shi ne zai amfana da gyaran da duk za ki yi. Ummi ta ce, "To wanke mini".Ta hada kayan wankin kafa ta ce yarana ke yi amma zan miki da kaina. Sai kuma taga zanen fulawa. Ta ce, "Au, an riga an yi zanen fulawa ma ba dama ayi, Ummi ta ce, Ohi ni na manta ma, to ki fada min yanda zan dinga gyara kafar, ta ce To bari in ba ki mai sauki ma. 1. Man kwaka 2. Man shanu 3. Man Zaitun Ki samu man kwakwa da man shanu da man zaitun ki hada man kwakwa da man shanu guri daya, ki shafa da dare da safe. Ki dan gasa kafar sannan ki wanke ki shafa man zaitun, za ki ga yanda kafafunki za su yi tamkar ta jariri. Ko ki yi na ruwan ko kumba, lalle ki hada su guri daya ki shafa a kafafunki da dare. Da safe ki wanke ki shafa man ridi, wadan nan kurum in kin rike su za ki ba wani labari, Ummi tace zan kiyaye in sha Allah. Shi kuma Abba yana fitowa daga shagon aski kai tsaye gidan Anty ya nufa, ya samu Bishira Anty ta matsa mata tayi wanka ta bata kaya ta saka. Ta kira mai kitso tazo tayi mata ta sata ta shafa turaruka. Tunda Abba ya shigo yake kallon Bishira, sun gaisa da Anty, sannan ta ce dama dai na ce kazo ne don Bishira ta baka hakuri. Sannan in maka tuni da yin adalci a tsakanin matanka, kuma na yi wa Bishira fada sosai. Ta dubi Bishira, ki ba shi hakuri, Bishira ta hada rai tare da turo baki, ta kalle shi cike da tsananin jin haushin shi. Kayi hakuri ya ce ba komai dama ni ban yi fushi dake ba, a zuciyarta ta ce, ba ka isa in baka hakuriba, albarkacin ina son zuwa Makka ne da kuma canjin kayan dakin. Ya yi wa Anty godiya ta ce ma Bishira gobe da wuri kiyi parking din duk kayan ki a waje da mun zo sai mu shirya miki. Bishira ta ce, Allah dai yasa su yarda, Anty ta ce,"Za mu su yarda in Allah ya yarda. Ta dauko wasu kayan sawa da sabbin kuloli ta ce ma Bishiran je kisa a motarku. Abba ya ce, "Kawo in kai, Anty na gode sai anjima, ta ce To Abba ayi ta hakuri". Ya ce, Ba komai, Insha Allahu. Suka biyo shi a baya tana kara jawa Bishira kunne kan cewa in har ta kuskura ta ji wata magana ta 6ullo ta rashin mutunci sai ta fasa tsaya mata a kan maganar aikin Hajji ko Dady ya amince sai tasa ya janye. 71.... Sun shigo mata Muhibba tana baya tana 'yanwutsil-wutsil dinta tamkar kurame, haka suke tafiyar. Ta zaci su nufi gida sai taga sun nufi cikin gari. Bata tambaye shi ina za su ba, har suka isa inda yayi parking ya dubeta, Madam ina zuwa, hum kawai ta ce. Ya bude baya ya dauko Muhibba ya sa6a a kafada ya nufi shagon saloon din. Daidai lokacin sun kammala komai, Ummi ta zari hijabinta da niyyar rufe kanta, Yagana ta ce a'a kanwata bari ya gani don ya biya ni 'yan kudina. Abba bai zaci Ummi tana da gashi ba, domin dai acikin Hausawa 'yan Arewa za a iya saka Ummi acikin ma su gashi. Yayi laya-laya a dokin wuyanta baki sidik. Yayi murmushi, lallai kin gyara da kyau. Nawa ne kudinki? Ta fada ya ciro ya bata, sannan Ummi tazari hijabinta. Mamaki take, Gida ya koma ya dauko Muhibba? Yamiko mata ita, Ga 'yarki. Ta amsheta. Yagana tace, yarinyar tana kama da ku. Abba ya ce, "Ai 'yarmu ce, suka yi mata sallama suka fito. Ummi da Bishira a tare gabansu ya fadi lokacin da suka ga juna. Bishira ta kauda kai yayin da Ummi taja baya daga mazaunin kusa da direban da ta nufa, ya bude mata baya ta zauna tana rike da yarinyar. Ya tada motar suka dauki hanyar tafiya kowanne zuciyarshi da abinda take karantowa. Ummi tunaninta Abba ya je ya zo da matarshi ne don yanuna mata shi fa matarshi yake so. Ita ko Bishira nata ganin wulakanci ne na karshe da ya dauko ta yazo da ita gurin wannan karamar yarinyar. Shi ko Abba addu'a ce a zuciyarshi Allah ya hada masa kan matansa, sai kuma ya soma tunanin ina zai soma zuwa? Nashi ganin in ya kai Bishira gida ya sauke ya tafi kai Ummi bai mata adalci ba. Amma ya kula Ummi tana fushi kuma yaso ya lallasheta, yana cikin wannan tunanin ya tuna dawayar nan. Ya kalli wayar a gefanshi. Dan murmushi yayi da ya tuna lokacin da ta dangwarar masa da wayar don ya ce ta matarsa ce. Yanayin yanda Ummin ke nuna kishinta yana birge shi, koda bata sonshi tana kishinshi sannan bata masa raini ko rashin kunya. Kofar wani gidan saida gasassun kaji da ire-iren kayan kwalam ya tsaya. Ya kalli Bishira Madam mu shiga ko? Ta ce, "A'a ni fa ba zan fita ba, ya ce To bari in dawo, ya nufi ciki. 72.. Ta waiwayo ta dubi Ummi, ta ce "Ba ni 'yata fitsararriya. Ummi ta mika mata tare da cewa nima ai ba cewa nayi a bani ba, ta ce "Kar dai ki min rashin kunyaki bar ganin an jona ki da mijina ki zata za ki hada sahu da ni. Ummi ta ce, "Sai dai kada a kuma in dai batun hada sahu ne, kuma ban damu don mijinki ba bai sona ba, tunda ni ina sonshi. Bishira cikin daga murya ta ce, oho? Dama sonshiki ke yi? Yanzun na gane da nufi aka yi. To ki sani kin sai ma kanki masifa da bala'i. Ummita ce, "Kin ga bala'inki can, daga nan batakara magana ba ta bar Bishira na ta masifa. Tundaki ka za6i ki auri mijina zan shayar da ke ruwan dana sani. Sai kin gwammace zama a kurkuku fiye da gidan mijina, daidai lokacin Abba ya dawo da ledoji guda biyu. Bishira bata yi shiru ba sai zagin Ummi take yi,"'Yar iska, 'yar daba... tsawa Abba ya daka ma Bishira, tare da cewa ba ki ji kunya ba da ki ke zaginta amma bata kula ki ba? "Ta ce, "To ka ji abin da ta ce min ne? Tsaki yaja tare da daukar wayar da ta aje yasa a ledar Ummi, sannan ya tada motar. Kofar gidan su Umma ya tsaya, Ummi wadda dama ta kosa tazo gida, ta bude motar ta fada gida cike da takaici. Ya kashe motar sannan ya dauki ledarta ya kalli Bishira, Ina zuwa. Kala bata ce ba. Illa baki da ta cije, kirjinta na yin wata irin suya. Ban da tana tsoron Anty kada ta fasa zuwa gurin Dadynsu da tuni ta shago Ummi ta nadi 'yan kayanta. Dakin Umma ta shige, Ummar tana shirin fitowa Ummi na shiga, ta

Chapter 16 of 24