Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
don su kamal bazasu iya ba, yanufi gurinsu ganin kamar ya damu yasa itama taje tasa musu hannu don dai ya saki ranshi, sun gyara tsaf ummi ta goge sannan ta rufe dakin. Har magriba bishira bata ji an ce za'a maida taba, sai ta dauki wayar kanwarta ta kira shi wai yazo don Allah yadauketa. Tsakanin mata da miji sai Allah, nan ya tausaya mata yace zaizo, kafin ya isa sai daya sai mata waya irin dai ta hannun ummi. Har cikin gidan ya shiga suka gaisa da babanta, yayi murna sosai yayi tawa Abba godiya, tare da ba shi hakuri yace yasan yanda ta horu zai gata canza da yardar Allah. Yasa aka turo ta yayi mata nasiha, sannan ya gargadeta da cewa inhar ta bari mijinta yakawa kararta zatayi mamakin abinda zai mata. Tace, insha Allahu baza ta kara ba, yakawo kudi yaba Abba, da kyar ya amsa ita kuma ya bata wasu zannuwa acikin leda, yace su raba da abokiya zamanta. Taje tayi wa hajiya zainu sallama suka tafi, tamkar baquwa haka ta koma, sai kace basu taba zaman aure da Abba ba, nauyinsa take ji. Suna tafe ya ciro waya ya miqa mata, tasa hannu ta amsa yace taki ce, tayi ta godiya yace ba komai. Sallamarsu tasa gaban ummi faduwa, ta dake ta fito ta amsa, wani kishi ya tasho mata amma saita danne. Ta kalli bishira tare dayi mata sannu dazuwa, ta amsa tana kallon ummi tayi kyau tagoge daga ka ganta kaga wayayya 'yar gatan miji. Ta dauko makullin dakin ta ba bishira, abba kuma ya nufi dakin ummi. Bishira ta dinga kallon yanda abba ya gyara gidan yaja gini ta gefen ummi yayi mata falo da kicin, sannan tsakar gidan an gyare shi da tiles. Haka bandakin su yagyara shi, nan dai bishira ta shiga dakinta ta zauna bakin gado tana yi wa allah godiya tare dayi wa kanta alkawarin har abada bazata ta kara yin yaji ko ta janyo abinda zaisa mijinta ya sake ta ba. Ummi tana kan gado tana karanta wani littafi yazo ya zauna bakin gadon bata ko kalle shi ba don haushi take ji. Sai take ganin kamar rawar kai yake yi da dawowar bishiran, kuma tuntuni yana zuwa gurin ta ya boye mata. Yace madam ina son in yi magana da ku ne ke da bishira, ummi tace ina jin ka, yace can zaki zo muje. Tace, gsky nagaji, kayi maganar da safe. Yagama gano kishi ne ke damunta, don haka yayi murmushi yace yanda kikace hakan za'ayi. Ya fita kamar minti 30 yasake shigowa ya aje mata leda tare da cewa saida safe aciki tace Allah yabamu alheri. Yana tafiya taje ta banko kofarta, yau kam bacci ya qi idanun ummi sbd tayi sabon bacci a haqarqarin Abba. Dukkan filolinta ta rasa wanda zai maye mata madadin haqarqarin mijinta, ynzun yancan da wata tasan yanda yake wannan rawar jikin ynzun ya manta da batunta. Tarasa me yake mata dadi, littafin datake karantawa kuwa sam bata fahimtar abinda ke ciki. Hka ta dinga zubda hawaye har nisan dare, ganin bata da wata mafita, tashi tayi ta bude kofa lokacin 2 saura taje tayo alwala tazo ta kama nafila. Abba jin bude kofarta ne yasa shi leqowa ta window aranshi yaji tausayinta don yasan bata iya bacci sai ajikinshi, ita bata san ya leqo ba don ko hanyar dakin bata ishe ta kallo ba. Yakalli bishira wadda bacci yayi gaba da ita ya tausaya mata sosai yanda tayi tarawar jiki alokacin auratayyarsu dazun. Yadauko wayarshi yarubuta ma ummi sako. KI KWANTA KIYI BACCI BABY, TARE DA QISIMA CEWA KINA LAFE AMAKWANCINKI (WATO JIKINA) INA CIKE DA KEWAR LEBUNANKI Tana sallah taji shigowar saqo amma bata yi ko marmarin dubawa ba, haka tai sallah har zuwa lokacin da bacci yasoma fizgarta. Tayi adduo'o'i sannan ta kwanta, saida asubahi ne datayi sallah sannan ta karanta, dan tsaki taja tare da cewa, Karya kawai, kishi yasa ta fadin haka don tasan Abba sosai baya boye mata komai ynzun. Sai dai abinda yasake qular da ita da asubahin nan yanda tana fita shi kuma ya fito wanka, duk da tasan dole wani abu yafaru tsakaninshi damatarsa, amma sai taga tamkar da gayya ya tsaya don tafito taganshi. Tna idar da sallah ta dora ruwa akicin dinta, tadafa ruwan tea taje kicin din bishira tadauko flask tazo ta wanke ta zuba musu ruwan zafi taje kofar bishira tayi sallama bishiran ce ta bude ummi tamiqa mata tare da cewa an tashi lpy? Cikin sakin fuska tace, lpy lau, nagode. Ummi ta ce ba komai takoma dakinta ta kulle kofarta don yau bata da darasin safe. Abba ma yau bada wuri zai fita ba, don haka yadan samu baccin safe sai 8 yayi wanka ya karya, sannan yanufi dakin ummi. Kofarta tana rufe, ya kwankwasa ta share sai can dai dataji yaqi tafiya sannan tazo tabude. Takalle shiya yi kyau cikin kananan kaya, ta kauda kai tare da cewa, an tashi lpy? Yace lpy lau, kin karya? Tace, um'um sai anjima, zata rufe kofar yace, makaranta fa? Tace sai karfe 2 nake da darasi. Ta maida kofar ta rufe, yayi dan murmushin takaici sannan yafita. Kwananshi 2 dakin bishira yayi niyyar dawowa dakin ummi, don ya kosa yadawo ya lallasheta bazai iya daukar wannan shariyar da take mishiba. Tsakaninta da bishira lpy lau amma shi sai tana wani share shi. Ya shigo da zumudi zai nufi dakinta, tamiqe cikin fara'a daga wanke-wanken da take yi ta amshi ledar hannunsa da jakar laptop ta nufi dakin bishira. Shida bishira suka bita da kallo, ganin zata shiga bishira tace ummi yau ai dakinki yake. Ummi tace injiwa? Anty bishara ai kullum ke ce dashi har sai kin rama duk kwanakin da kika dauka agida. Kinga kenan kusan wata goma sha daya kenan. Abba cikin sauri yace ke mahaukaciya ce? Ina ki kasamo wannan fatawar? Ta kalle shi, sannan tashiga dakin ta ajiye ta fito taqara kallonshi gurin malamai, yace to ban yarda ba, don haka zanci gaba dayi muku kwana bibbiyunku, ummi tace to ni na yafe mata nawa kwanakin bishira tace nagode ummi. Haushi ya cika Abba, amma shi bazai dauki wannan horon da ummi take shirin yi masa ba. Yadawo dakin bishira a fili yafurta kema saina baki haushi zakiyi dakin sanin wannan furucin. Sharewa yayi yaci gaba da kwana dakin bishira tare da nuna kulawa ga bishiran. Ummi ta jure duk da duk daren Allah sai taci kuka ta gode Allah, sannan tashiga zargin cewa shi ma ya Abban dama can yana son tarewa dakin bishira, inba haka bame zaisa yayi saurin yarda kuma yayi ta nuna mata soyayya? Ganin ummi tana yi tamkar bata damu ba yasa shi qa rajin haushi, yadawo da yamma suna zaune kowa A qofarshi. Ummi tayi kwalliya cikin qananan kaya, bishira kuma tana sanye da leshi, karatun littafi bishiran keyi ita kuma ummi tana yin gyaran qumbunanta. Bawai suna wata hira bane amma suna kula juna sosai musamman bishira tana son su saba da ummi. Ummin ce. bata cika son fitowa ba, bishira ta tashi ta masa sannu dazuwa tare da amsar kayan hannunsa don yanzun tana koyi da ummi gurin kyautatawa, ummi ta kalle shi sannu dazuwa, ya amsa da yauwa baby. Yakalli bishira sweety zanyi wanka, tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai tazo tace masa takai nan k sweety zanyi wanka, tace to, takai masa ruwa yashiga dakinta, sai tazo tace masa takai nan kuma yajanyo bishira jikinshi. Ba wai yana da bukata bane, amma don ya shaqar da ummi sai ya banko kofar, qaran kofar ne yasa ummi kallon gurin dakin. Ta duqar dakai taci gaba da abinda take yi, kusan minti arba'in suka fito, Abba ya matsawa bishira wai suyi wanka tare, tace ni bazan iya ba akwai ummi dama da dare ne inajin kunya. Kuma kada taga kamar cin fuska ne, yace kenan don kada ki bata mata rai ni mijinki bazaki faranta min ba ko? Dole ta bishi suka shiga bayi. Baqin ciki yasa ummi tashi tashige daki, kuka sosai tayi daga nan bata fito ba sai magriba, tanayin alwala tarufo kofa, washegari ma qin bude qofar tayi daga alwalar asubahi. Abba yayi ta raba ido ya ganta amma bata fito ba, yasan fushi take, ya kira wayarta taqi dagowa yayi mata saqo cewa in zata makaranta tafito inkuma sai darana ta bude ta amshi kudin mota. Tana gama karantawa tayi wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka ya tafi. Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy? Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije makaranta bane? Ummi tace, zanje sai sha biyu. Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi masa zancen karatun amma ya share ni, ummi tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa min baki? Ummi ta riqe baki, ni a wa? Ke da yake hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki zage ni. Bishira tace wane irin zagi? Ni dama ki amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai agurina, amma ruhinsa yana gurinki. Ummi ta ce, ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba wani zagi. Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage walwala don wanda yasan kan kula da shi kamarta. Yayi missing din abincinta. Amma ya gaji bazai jure ba. Ya tuna bishira tace masa zata ta yini gidan ummanshi. Don haka yana gama muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin yanufi gida. Ummi tana shirin tafiya makaranta ta dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an jeho shi. Ta daure fuska tamkar bata taba dariya ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan horon naki. Laifin me nayi miki? In don na dawo da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika takura min sai na dawo da ita ba? Ummi tace, ni karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki matarka sbd ni? Ba ruwana. Yace, to ki dawo yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin haqura dani, niban haqura ba. Ke ma kuma nasan dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba, ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame? Ya canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna. Ya lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani abu. Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don lokaci yayi nisa. Ya ficiko ta ta dawo ba zaki makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi ni. Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje. Bishira tana dakin umma tana sallah yabi umma kicin, umma gurinki nazo, ta dube shi lafiya Abba? Ya turo baki, alamun ranshi bace baki, yace umma ki sallami bishira, tace kamar yaya? Yace taje can gidan ko muyi maganar agabanta? Tace, kyale ta muje dakin babanku. Abba ya fada ma umma komai da ummi ke masa, tun dawowar bishira ran umma ya baci tace ka barni da ita. Banda shashancin ta da ita kadai take son azauna? Baga bishirar nan ba gidan nan ta gane kuskurenta ko yau yarinyar nan sai da tace in yafe ta nace ni dama ban riqe ta da wani abu ba. Shine ita zata qirqiro fitina? Yace, umma ai ba da bishira take yi ba dani take yi, tace to zata gane kurenta da dare kuzo kai da ita. Umma ce ta kira ta awaya tace tazo ita da abba, jikinta ya mutu don tasan qararta aka kai, tana idar da sallar isha'i taje gidan. Can tasamu abba, nan ko umma ta rufe tada fada, koda tsohuwa ta jiyo tazo umma tafada mata komai sai ta shiga fada. Wai ai kishi halas ne, ke suwaiba tsakani ga Allah ko ke bazaki so kishiya ba, bare ita yarinya. Abba yace to gata nan ita ce fata dame ne nida batun in dawo da bishirar, yanzun na dawo da ita kuma ni abin ya qare akaina? Nan fa umma tayi mata tatas, ta kuma sata anan ta ba Abba Haquri, aka kira shi awaya ya fita. Umma ta samu dama taqara yi mata nasiha da cewa, in bnda shirmenki yaushe zaki bar ladanki, hanyar aljannarki kice kinyi fushi da ita kin barwa kishiya? To kada in sake jin haka, ki riqe darajarki da mijinki, ke ganinki da ita. Ta jima tana bata shawara kafin Abba yadawo suka nufi gida. Ya shiga gurin Bishira ya fada mata cewa yau gurin ummi zai kwana, nan ya bar ta da kewa yanufi gurin ummi, tamkar yaune daren farkonsu hara sukai rayuwa s / ZURFIN CIKI book 4 part 21 ZURFIN CIKI book 4 part 21 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:19 Kwanci tashi asarar mai rai, shekara ta zagayo lokacin bishira da tsohon ciki, Abba nason yara don muhibba taqi dawowa tafi son umma dole suka haqura suka bar mata. Ta haifi 'yarta budurwa tubarkalla ranar suna ta ci sunan sahura inda suka sa mata walida. Ummi nason yara, don haka in tana gida to tana manne da walida, Abba yana damuwa da rashin samun cikin ummi, wanda ita ummin ta barma Allah komai. Shekaru uku sun sake biyo baya, lokacin Bishira ta sake haihuwar habiba takwara Abba yayi wa ummi. Tsohuwa an qara tsufa, 'yan rigingimu sun qaru tace ita Abba yama takwara amma bata son ya duke ta irin yanda yayi wa ummi. Abba kullum qara son ummi yake, umma ta matsa masa sai da yayi qoqari ya sai fili rabin filoti tace kuma a rage ciye ciyen dadin nan agina shì. Haka kuwa ya gina flat mai daki hudu, daya ummi daya bishira, sai nashi sannan na yara. Yayi qoqari gurin gyaran falon ita kuma ummi ya canza mata kayan daki don bishira an canza mata daza su tashi agidan su. Yace tabishi bashi in ya samu zai bata kudi amadadin kayan daya saima ummi, tace ta yafe. Ummi dake karantar (BUSSINESS) har ta hada (H.N.D) dinta kuma tayi bautar qasa. Abba dai yace baza'ayi aiki ba amma ya yarda tayi kasuwanci, Alhaji babba ne ya bata jari inda take saro kaya zannuwa, lesuna, takalma zuwa jakunkuna. Abin ya amsheta don har kayan aure tana hadawa, tana yin saqo irin su kwatano da chaina, india, pakistan ko dubai, ta hanyar wani wan kawarta. Haka kawai ummi ta samu kanta da zaban abinci, yawan bacci kasala da dai sauransu, sam bata san takamaiman lokacin al'adarta ba. Don bata wani lissafi in yazo shi kenan in bai zo ba bata damu ba tama cire ranta daga batun ciki. Abba ya kalli nonuwanta, baby kwanan nan kirjinki ya cika sosai, gashi kinyi haske ko kin canza mai ne? Tace yaya yaushe kazama likita? Yace, ummi kin fa canza shirya muje asibiti, ta ce ya Abba don Allah ka bar ni nagaji dazuwa asibiti. Yace, to ni zan je inya tambaya game da yanda ki ka canza. Cikin jin haushi tace sai ka dawo. Ga yara atsakar gida sun ishe mu, yace ni naki nake qawar in gani nasan addu'ar da nike yi bazata fadi kara banza ba, sannan ga qoqarin danake yi, shiru ta masa. Dagaske yake yi yaje yayi wa likita bayani, yace yadai kawo fitsarinta. Sai da suka yi tsiya da qyar bishira ta lallasheta ta yarda ta bada fitsarinURFIN CIKI book 4 part 23 ZURFIN CIKI book 4 part 23 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:22 Sam bishira bata damu da barin mijinta da zatayi gurin ummi ba, tunda ta jima da sanin cewa ummi bata da wani ammafni. Wannan ne ma yasa tasha alwashin in taje zatayi addu'a Allah yakara toshe ummin kada ta warke sam, tunda umma Bashir ta fada mata duk addu'ar da tayo kafin ta dawo an karba mata. Ta kuma kara bata shawara ta roko musu rigima suyi tayi har su rabu, Bishira tace duk zata roko. Ko ranar da zasu tafi sai da ta yi wa ummi habaici, kawyenta sun shigo wato makotansu a tsakar gida take fada musu cewa mijinta kurum take tunani. Wai zai sha wahala kafin ta dawo. Wata cikin su tace, wahalar me ga shi da amarya? Ta ce amaryar da ta ke a toshe, ai bata da ammfani. Ummi duk tana ji, takaicin duniya ya isheta sai dai ita zata so ace bishiran take ta roko ma kanta shiriya ko Allah zai sa ta dawo ta kama sallah. Dayar tace, to Bishira ki roko mata sauki mana, cikin zolaya tayi zancen, Bishira tace ba abinda zai kaini makka in roko ma kishiya abin arziki. Ummi ta fito ta ce Anty Bishira zai fi kyau ki roko ma kanki shirya ko in kin dawo kya fara sallah da tsafta. To ban san ma yanda zaki kwashe da ibadar ba ko za a karba tunda ba yin sallah ki ke ba. Ta taso fuuu, kawayen suka reketa suka ce kyaleta bakin ciki ne. Abba ya fito wanka yana cewa, Ok, za kuyi na bankwana ko? Yana da kyau hakan. Ummi ta koma dakinta. Tun bayan tafiyar Bishira Abba ya shiga takura musamman irin wannan lkc na sanyi. Ya dawo da yiwa ummi 'yan wasanni da ya daina, sai hakan yakara sa shi damuwa don haka ya shiga lallashin ummi ta fadawa umma....... Kuyi hkr da typing din banda lafia sstr dita nake sawa tana maku.els / ZURFIN CIKI book 4 part 24 ZURFIN CIKI book 4 part 24 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:24 Tace ita kam ba zata iya ba ranar wata juma'a suka tafi da nufun su fadama umma matsalarsu, sai dai har zuwa bayan isha'i da abban yazo don su tafi sun kssa sanar da umman komai, har sunyi sallama abba yayi kunar bakin wake yace umma ta fada maki matsalarta? Umma tace wa? Yace ummi tace a'a suka koma suka zauna. Abba kanshi na kasa Yace umma dama bata da lafiya ne? Umma tace mike damunta kuma? Yace ummi fada mata. Ummi ta sunne kai cikin cinya tare da cewa shiya fada. Cikin sa'a aka kira wayarshi, nan yayi waje ya barsu, umma tasa ummi saita fada. Ummi ta rasa ta inda zata dauki zancen, umma ta soma yi mata fada har tsohuwa ta leko tambaya take lafiya ba sunyi sallama dama basu tafi bane? Umma tace wai bata da lafiya ne, kuma ita da abban sun kasa fadaman shi yayi waje, ita kuma ta kunshe kai cikin cinya wai injira ya dawo ya fadaman. Tsohuwa taja hannun ummi zuwa dakinta, suka zauna bakin gado ta riko hannunta. Takwara fadaman abunda ke damunki. Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa magana. Tsohuwa tace inda baki fadaman ba akwai wanda zai taimaka maki ne? Tunda naga duk yarda mijinki yake da umman ku ya kasa fadamata to abun mai girma ne. Ummi ta daure tace "Gabana ne fa a toshe....." tsohuwa ta rafka salati, sannan tace yannan badai angurya ba? Cikin tsoro ummi Tace, ni ma ban sani ba ko shine. Salati tsohuwa ne ta jawo hankalin umma tazo dakin da sauri. Tsohuwa Tace ina ga yarinyar nan angurya ne a gabanta. Umma Tace shine don wauta daga ke har abban kukayi shiru, dubi tsawon watanin da kuka dauka, tsohuwa Tace yanzun yaya za'ayi umma tace ni ina nasan yanda za'ayi, ai ni na zata yanzun babu masu irin wannan ciwon. Rabon da inji labarinshi tun muna yan mata. Tsohuwa Tace kai nima na jima banji ba, amman kinsan dama wanzamai ke aikin. Alhaji ya dawo daga sallar isha'i yaga abba tsaye a waje, Yace a'a babana dama baku tafi ba, Abba yace eh yanzun zamu wuce, ya biyo bayan Alhaji suka shigo suka riski zancen dasu dasu umma keyi. Alhaji Yace lafiya? Umma Tace yaran nan ashe zaune suka da lalura, tame inji Alhaji, umma Tace angurya ce ashe ta fito ma Ummi wai suka zaune. Alhaji yace meye kuma angurya Tace wani abu ne dake toshe mace. Nan fa suka shiga tattauna yanda za'a shawo kan abin, tsohuwa Tace wanzami za a kira ya yanka mata. Alhaji yace to gobe zai kira wanzami. ZURFIN CIKI book 4 part 25 ZURFIN CIKI book 4 part 25 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:26 Abba da jin haka sai ya fito, kishi fal da zuciyarshi, ya ce umma wanzami kuma? Ta ce eh, aikin sune. Yace gsky umma ba za a kai ta gurin wani wanzami ba , bagara muje asibiti ba. Tsohuwa ta ce, kaci gdanku da asibiti komai ku ce asibiti to wannan ba aikinsu ba ne. Abba ya ce, Nifa gsky ba xa a kai min mata gurin wani wanzami ba, umma asibiti zamu. Yanzu kai ya waye wanzamai ba duka suke dafa kayan aikinsu ba, haka kawai taje ta hadu da wata cutar? Alhaji yayi murmushi yasan kishi ne ke damun Abba, ya ce Babana kada ka damu, goben sai kuje asibitin, in sun ce ba su san shi ba to sai a zo a yi na wanzam ko ? Kunya ta kama Abba, Sam ya manta Alhaji yana gurin ya ce to Tsohuwa ta ce kuje in kun je ma dawowa za Ku yi dan me taurin kan tsiya. Abba ya ce naji kin ji ummi taso muje gda Tsohuwa ta ce oho dai, kuyi ta tafiya in dai akayi mata aikin ai dole ka barta ta warke . Alhaji da umma dai dariya sukayi ta yi musu, shi kuma yayi musu sallama, ummi kam kasa magana tayi don duk ta tsorata. Suna fita ta rike hannun Abba gam tana cewa. Don Allah ya Abba kada kabari wanzam yayi mini aikin nan, zan ji zafi. Ya rungumota, Ba zan amince ba wani ya ganmin al'aurar mata, likita ma mace zan nema ko nawa zan kashe . Ummi ta ce, to zan ji zafi ya Abba? Ya ce, made ki damu, in asibiti ne kila suyi miki allurar kashe zafi amma in wanzami ne ina za ya ga wata allura yayi mini. Ummi sarkin tsoro ranar kwana tayi cikin damuwa, washegari kuwa tun bakwai suna asibiti. Babban asibiti suka je sun yanki kati likita me kula da fannin mata aka tura su. Mata dayawa suna ta kallon su ummi musamman yanda Abba ke nan-nan da ita, sannan wasu sungane shi kasan cewar shi dan jarida mai farin mini. Wasu mazan kuwa sai zuwa suke suna gaida shi. An kirata dakin ganin likitan, ta mike zata Shiga Abba shima ya mike, wata Nurse ta ce, malam jira mana, ya ce ai duk Mu biyu ne bamu da lfy, ya shige likitan namiji ne ba yanda ya iya dole ya yi masa bayani likitan yayi ma ummi tambayoyi in da duk ta bashi amsa/ ZURFIN CIKI book 4 part 26 ZURFIN CIKI book 4 part 26 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:27 Sannan ya bukaci ta kwanta kan gado ya saka safar hannu, juya kai abba yayi don gaskia ranshi ya baci, lallai ya kamata mata musulmai su dage suyi karatun likitanci don su taimaki yan uwansu mata. Sai da likita ya gama dubata sannan ya iya dubansa, likita yayi wani rubutu ya mika abba tare da cewa, an baku gado zayi mata aiki gobe ko jibi. Abba yace likita zan iya sanin wane ciwo ne wannan? Likita yace tsirone dake fitoma mata dai daiku. Sam abba bai fahimta ba don haka yayi mashi sallama. Umma ce a wurin ummi tana shan magani kafin ranar aiki inda abba hankalinshi ya rabu biyu rabi gurin aiki rabi garin ummi. Don ma umma ta koreshi da so yayi ya rika kwana, addu'a kam yana yinta. Ranar da za'ayi aiki abba hankalinshi duk tashe. Yana zaune bakin gadon da take kwance ita kuma tana can ana aikin. Wayar umma ce a hannunshi yana ta danne danne, ba don nishadi ba don kawai ya rasa me zaiyi. Dript ya shiga yana ta bin abinda ke ciki, mamaki ya cikashi lokacin da yaga irin text din da ummi tasha rubuta mashi don ta tura ma abba, sai kuma ta fasa. Tamkar cikin mafarki abba ya rika karanta sakwanin dama ummi tana sonshi zurfin ciki ne tayi? Ya sake bude wani rubutu cewa, Ya Abba ina sonka, ina kaunarka duk wani motsi na numfashina kara sonka nake, ka tausaya mun sonka zai zama ajalina, duk ciwon da nakeyi na sonka ne. Ko na rantse ba zanyi kaffara ba, in kaji haushin kalamaina ka yafeni, nasan ni ba ajinka bace, amman ka daure kace kana sona koda bada gaske bane. Gama karanta sakon yayi dai dai da dawowa da ummi dakin, da sauri suka nufeta idonta biyu saidai daga gani tasha azaba. Tayi wujiga wujiga. Abba ya kama hannunta cikin matsanancin sonta da tausayi. Sannu suka dinga yimata, nurse tabasu magungunan da za'a rika bata, umma kuma ta dauki wayarta don sanar da alhaji an gama aikin. Abba yasa bakinshi dai dai kunnenta yace ina sonki ummi, ina matukar sonki. Duk da tana cikin wani hali taji kalaman nasa har a tafin kafarta. Ta bude jajayen idonta ta dubeshi, ya sakale hannunshi cikin tafin hannunta ya hade su. Ta girgiza kai dai dai lokacin da nurse din ta sake shigowa tace ga kayanta, ya amsa zaninta ne da siket da sauransu. Tace ka barta tayi bacci kafin ta tashi zafin gurin ya ragu, kila zuwa dare a sallame ku. Umma tace to mungode. Nurse tace yarinyarki nada dauriya, anyi mata allurar kashe zafi bata kama jikinta ba amman bata yimuna ihu ba. Likita ma ya yabata da kokarie ta, Abba ya kalli ummi cikin tausayi. Sai gurin karfe ukku ta farka wurin kam ya dan lafa da radadin, abba ne yaje gida ya dafo masu abinci sannan ya nufi wurin aikin shi. Don ranar bada wuri zashi ba. Tunda ummi ta farka take ta kokarie tunowa shin kalaman da taji cikin mafarki ne ko kuwa ido biyu ne? Bakwai na dare likita ya shigo ya kara duba ummi sannan yace suna iya tafia gida. Ya basu maganin sha sannan yace ta rika shiga ruwan zafi da dettol. Umma ta kira abba ta fada masu batun sallama. Yace su jirashi yana zuwa. Ummi tace da ummansu su alhaji pha? Tace sunxo kina bacci harda ummanku sahura.els / ZURFIN CIKI book 4 part 28 ZURFIN CIKI book 4 part 28 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:30 Bansan lokacin dana dauka ina rigimniya da sonki danqare a zuciyata.Ummi da ban sameki ba da tuni bana garin Kano domin lokacin yanke shawara nayi in nemi canjin aiki zuwa wata jihar har yau ban daina yiwa Salisu addua ba wanda shine mutum na farko da ya soma tsegunta min kin zama

Chapter 21 of 24