Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bwata matsala, ummi tamike dazumudi bari a karasa. Tun daga soro take kwala ma umma kira. Umma tce, A'a muryar wa nake ji haka? Ummi tashigo da gudu ta cakume umma, tsohuwa tafito tana fadin lale. Dakin tsohuwa tasoma shiga suka gaisa sannan tadawo dakin umma, sun gaisa umma tasake mata nasiha, ummi tace umma ni matsalata daya matarsa. Kullum saitayi min habaici tana zagina wata rana r harda kawayentaRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 9 ZURFIN CIKI book 4 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:54 Ita ko bishira gidan su umman bashir ta tafi dakuka wiwi, tace Abba yamata duka takan sun taka hakkinta sun fita ranar girkinta. Tayi magana ummi ta mata tsaki shi kuma yazo yazo yahauta da duka, umman bashir tace duka! Duka akan ummi? Tabdi, tashi muje gurin wadanda suka daure masu gindi. Umma na kokarin shiga daukin alhaji taji sallamarsu sama-sama, gabanta yafadi ta amsa tare da dawowa baya. Sahura tace to suwaiba, abinda kuka shiirya yasoma tasiri. Abba yayi wa bishira shegen duka saboda 'yarku, umma tace haba sahura, yaya ki ke irin wannan maganar? Mu ne zamu sa Abba ya cutar da iyalinsa? Sahura kiyi nazari. Alhaji yafito, me yafaru ne ni kejin hayaniya suwaiba? Umma tace, oho. Sahura tace, bishira fada musu. Nan bishira ta shaida masu yanda ta tsara ma umman bashir, alhaji yadaga waya yakira Abba, Abba yana dagawa alhaji cikin zafi yace Abba maza kazo yanzun duk in da kake. Abba yace to alhaji, ummi ta mike zan bika tsoro nake ji ni daya, cikin zafin rai yace abin daki ke tsoro ya cinye ki, ya fita fuuu. Cirko-cirko ya same su a tsakar gida, sai muryar sahura kake ji tana rashin mutunci. Alhaji karami yadawo gidan shi sai ya jiyo muryar sahura a can gidan, ya nufi gidan don haka kusan tare suka shiga gidan da Abba. Alhaji cikin bacin rai yafada Abba da fada, abba bai katse shi ba har sai daya kai ga tambayarshi cewa me yasa yayi mata duka? Yace, banyi mata duka ba alhaji marinta kawai nayi, umma ta ce mari kawai ne Abba? Alhaji karami yace, to kan wane dalili ma zaka mare ta? Abba ya koro musu komai, ya kara da cewa, wannan har zata ce an mata tsaki, zata yi duka ni wane irin zagi ne bata min ina hakura darajar iyayenta? Ya nuna ta, wallahi in kika kai ni bango zaki koma gidanku don bazan iya ba na gaji, nan kuma su alhaji suka shiga bashi hakuri. Ita kuma suka bata rashin gaskiya, sai dai duk da haka umma tai masa fadan kada ya sake daukan ummi ranar girkin bishira ya fita da ita, yace to. Umman bashir taja bishira zo muje ai dama nasan baza suga laifin 'yar su ba. To wllh marin da yamiki ki tabbata bashine. Ko nan da yaushe ne ki rama shi kan ummin, in ba haka ba duk da banice uwar data haife kiba sai na tsine miki. Alhaji karami yace, to katuwa mara lissafi, ke dai kinji haushin rayuwarki, to ki sani duk randa ta rama duka akan ummi ni kuma akan ki zan rama wa ummin inga ta tsiya. Alhaji babba yace, kada kai ma kazama su mana aminu. Tsohuwa tace, gskiya ne, in har tazama silar dukan ummi itama sai ya mata taji. Umma tace, a'a duk abin ba zai kai haka ba insha Allahu, kai dai abba kayi ta hakuri sannan kadaina sa hannu kana dukan mace. Yace, umma dukana fa tayi, sai kace wani soko zan tsaya mce tna dukana, umma tace, to ai tace ummi taje duka, yace ummin 'yarta ce? Alhaji yace, tafi gidan kahadasu kayi masu nasiha, Abba yace ai baza ta tsaya ba, wannan yarinyar fa sai dai addu'a ni in nagaji kawai hakura za ayi, umma tace bana son jin wannan zancan, alhaji karami yace ai gskiyarshi ne, shi yasan irin zaman dayake da ita. Alhaji babba yace, ai kuma darajar mahaifinta za aduba, da mutuncinsa, Abba yace ai dama alhaji ni banda mahaifinta da tuni nayar da kwallon mangwaro na huta da kuda. Umman tace je ka gida Allah ya kyauta. Nan dai ya musu sallama yanufi gida. Ummi da gske tsoro ne da ita, da rana in ba kowa bta damuwa, amma da dare tfi son tdinga jiyo motsin bishira koda habaicin dta sabayi mata. Soro taje ta tsaya tana yi tana leka waje, can ta hango bishira, don haka takoma daki ta kullo kofa aranta ta ce kada tazo tayi min duka. Ummi tna jiyota lokacin data shigo tana cewa wllh kan yarinya zan rama marina, wannan dole ne koba dade saina ramashi. Abba kan bai nufo gida ba, shagonsa ya wuce lokacin goma ta gota, yaran sunyi shirin tafiya, don haka ya amshi makullin ya shiga shagon saman teburin da suke yin yanka da guga ya hau ya zauna. Tagumi ya zuba hummu biyu tare da sauke wata ajiyar zuciya mai karfi, me yasa ummi ta furta kalmar data tuna mishi cewa bata sonshi? Sakankancewa dayanda ummin kenuna mishi yasa shi jin kamar sonsa take ashe dai shi yake shermenshi. Ya tuno wani labari yaya tabaji na wani mutum da aka ara masa mata wadda bata sonsa, tazo tazauna dashi tsawon shekaru kuma tayi masa biyayya matuka. Ga 'ya'ya sun haifa yaran sun yi girma sosai, suma sun zama magidanta, sai wata rana mutumin nan suna hira da matar, yace oh, wance dafa ba kya sona, yanzun gashi harmun tsufa kin manta dawata kiyayyah. Tadubeshi, inji wa yace maka na manta? Biyayya kurum nake maka amma har gobe bana sonka. Abba yajinjina kai, lallai dole ne ya nutso, yadaina tunanin ummi tana sonshi kokuma zata soshi, shidai da kaddarar sonta tafada mishi sai yayi ta addu'a Allah ya bashi hakurin jure zama da ita ahaka. Bai san adadin lokacin daya dauka awaje ba kuma baisan adadin tunanin dayayi ba. Daga karshe yarufe shagon yanufi gida. Ganin yanda garin yayi tsit shine yasa shi kallon agogon hannunshi, daya da minti shabakwai, lallai lokaci yatafi. ZURFIN CIKI book 4 part 10 ZURFIN CIKI book 4 part 10 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:55 Yanufi dakin bishira aranshi yce da wanda yake kinka gara mai sonka ko mahaukaci ne. Gdon yahau tagefe ya kwanta suka saka muhibba atsakiya, ummi kuwa duk tsawon lokacin nan tkasa bacci domin bata ga shigowarshi ba. Idonta biyu har sai daya shigo ta leka ta windo tana kalloshi har yashiga dakin bishira ya rufo kofa, sannan ta kwanta tare dayin ajiyar zuciya. A fili tace ina ga fa har dani alaifin nan, amma bari gari yawaye inba shi hakuri durkusa ma wada ai ba gajiyawa bane. Bishira tafarka cikin dare taga Abba kwance hannunsa na dama dore kan jikin 'yarsu, ta tsura mishi idanu tana son mijinta sosai. Ban dahaka data kaishi koto ya bata takardarta koda mahaifinta xaimata baki sanadiyar haka, amma shi yanzun yadaina sonta. Takai hannu tadora a kumatunshi, ahankali yabude idanu, suka kura majuna ido yace bishira me yasa kike yin abinda zai samu mu samu sabani bayan kinsan sone ya hadamu? Idanuwanta suka kawo ruwa, Abba dane ka soni kaji dani har alokacin ina ganin ba Wata mace data kai ni dacen gwanin iya soyayya. Amma yanzun duk ka zuba ni a kwandon shara har kana marina saboda ummi. Ya ce, a'a ba sbd ummi na mare kiba, saboda kin dukeni ne amma kiyi hakuri. Banason kina zubar da kanki a gurinta, yawan fadanku zai sa raini ya shiga tsakaninku, ni kuma ba zan so ta rainaki ba. Kuma da kin kwantar da hankalin ki ummi fa ba wai tana sona bane, ita fa an matsa ma tane, kuma su umma da kike zagi na rantse miki masoyan kine. Ta ce tokai kana son ummi ne ? Ya dan yi jim, sannan ya ce ai dai kin san yanda auran namu da ita yakasance bagatatan bai dace ace kinma tsaya yin wannan tambayar ma. Tadan yi shiru, zancen nan ya shige ta bakamar yanda ta zata da farko ba, ko dadin baki zaimata? Sannan ta tuno da ranar da fati tazo. Ta labe taji koza suyi zancenta sai taji suna ta hirarsu, acikin harar fati ke cewa wai kuwa ya kuka kaya ne ummi? Nasan yanzun ai kin warke, kema kin goge. Ta ce damefa? Fati tace, a'a ki gane mana, batun kwanciya. Ummi tace, kin san cewa yaya Abba ko gadona bai taba kwana ba? Fati tace kai haba? Ummi tadinga yimata rantsuwa, tuno da wannan sai bishira ta yarda mijinta ma baya son ummi, don haka sai ta saki murmushi. Yace, tunanin me ki ke yi? Tace da ina ga kamar dadin baki kake min, amma dana tuno naji ummi tana fadama fati wai baka taba ko kwanciya a gadonta ba, bare ka hada jiki da ita sai na yarda. Abba ya zaro ido, a ina kika ji suna zancan? Ta ce, a'a tazo mata rakiyane naji suna maganar a soro. Abba ya girgiza kai. Bishira tace, kuma da gske hakane, yakai hannu yakama nata tafin hannun, wannan wani sirri ne tsakanina da ummin. Ynda ba zan fada mata komai tsakanina dake ba, haka itama zan sakaya nata sirrin, tadai fahimci hakane, don haka sai ranta yayi mata dadi har ma ta baiwa Abban kanta a daran. Ynda taga yna rawar jiki ya tabbatar ma ta ba wani angwanci da yayi, don haka zuciyarta fes ta wayi gari. Duk da cewa abba ya tashe ta cewa taje tayi wanka harda Allah yahadata amma tayi niyar baza tayi hakan ba sai gari yayi haske. Ummi ta fito don tanuna mata cewa Abba ya kwana da ita. Bishira an dafa ruwan tea an kai falo sai wannan rawan kai ake yi. Sai data lura ummi ta dauko tsintsiya tasoma sharar gidan kamar yanda tasaba, sannan tafito da buta aka nufi bandaki, kai ko dankwali babu aka yiwanka aka fito. Gashi yna ta digar ruwa, ummi ta fahimta kuma tagane cewa tayi hakan don ta nuna mata ne. Kuma taji zafi aranta kamar ynda bishiran taso, ta amma azuciyar ta sai tace na banza jiya nan yakora miki mari. Lokacin da abba ya shigo gidan tagama shara tana kwashewa, bai ko dubeta baya shige falon bishira, kan ummi yasake daurewa, me yake faruwane haka da zafi? Ta tambayi kanta. Data koma daki tagumi ta zabga tana tunani ita da suka yi kaca-kaca ma sun shirya bare ni? Kamar tabi shi har falon bishiran ta gaida shi, amma sai tafasa. Tazuba ido taga zai bar gidanne ba tare daya leko dakinta ba? Sun gama karin kumallonsu tsaf yayo wanka don tafiya gurin aiki, sai dai kayan dazai saka suna dakin ummi. Ya fito yanufi dakin. Ciki- ciki yayi sallama ita kam tsoro ne ya tsirga mata, tasake tambayar kanta mekuma yafaru? Ta amsa tare da gaida shi. Nan ma a ciki ya amsa, yadauki kayan sai dazai fita sannan yace ba kya bukatar komai ko? Tayi karfin halin cewa sugata ceta kare. Ya dube ta furka tsuke me yasa baki fada minba? Ta ce, na manta ne, yace to sai kije gurin bishira da dibar miki inzan dawo na siyo. Ba kya neman komai da rana ko? Tace a'a sai nama kawai ya daga murya, kullum ne ya zama dole a saka nama a abinci? Jikinta har bari yake don tsoro, ta ce a'a yaja tsaki ya fita. Ummi tasaka kanta cikin cinya tana furta 'inna lillahi wa inna ilaihir raji'un.' hawaye suka soma yi mata sintiri.KI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 11 ZURFIN CIKI book 4 part 11 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:57 Dadi tamkar yakashe bishira don tna labe tana jinsu afalon ya saka kya yashirya tsaf, sannan ya nufo dakinta don dauka jakar laptop dinshi. Jin sallamarshi tayi mza tashare hawaye sannan ta amsa, yshigo ya dauko dari biyu ya aje mata akan gdo, ga kudin maman nan kura, kada fati tzo kifada mata baki kudin nama kullum tunda har kin iya shaida mta cewa ban tba kwana agadonkiba. Kin kosa inkwanta dakene? Yadauki jakar yarataya sannan yayi mata wani kallo sama dakasa, to banga gurin kwana agadon naki ba. Hakanan banga abin kwanciya ajikinki ba, yafice yabar ummi tsaye tazaro idanunta cikin matukar al'ajabi da kunya. Ina ya Abba yaji zancen nan? Kodai fati ceta fada masa? Wata zuciyar tace fati baza ta iyayi masa zancan nanba saidai in ummarsu tafada mawa ita kuma tafada masa. Inko hakane fati batayi mata adalci ba, ai hira ce irinta aminta tsakaninsu, gashi ta bata kunya har tasa ya Abba naganin tazaku. Tokuwa tasha alwashin nuna mishi bahaka take nufi ba, afili tace Allah yabamu rai da lpy. Sai kuma tasoma kuka. Bishira tafadi kan dadi ashe gara data fada masa zancen dataji suna yida fati, gashi yanzun yayi mata rana. Lallai labe yayi mata amfani sai kawai tasabi 'yarta tazari mayafi tafice makota, yau kan tana da labari mai dadi sai yawon raba shi take bata manta ko kalma daya. Sannan darana tazo tahau kici-kicin dora girki, lokacin ummi tafito don yin alwala, ita ko karyawa batayi ba don tawuni da takaici ya Abba. Tana kallon yanda bishira tazubu kayan miya tana jajjagawa batare data wanke ba hancin kawai ta cire. Ummi tayi alwala tashige daki, ranar har dare ummi bataci komai ba, duk da tanajin yunwa. Zantukan abba kawai kemata yawo a kwanya. Tayi kuka harta gaji fuska ta kumbura. Tun uku yadawo baiga ummi ba, bishira tagabatar masa da abinci dakyar yayi cokali uku. Dama yazo dafura, yasha sannan yanufi shago, yini yayi yana tunanin kamar bai kyauta ma ummi ba, amma yana mamakin yanda ummi ta iya cewa bai hau gadonta ba. Kenan inyahau din dakuma abinda yabiyo bayan hawa gadon duk zata ringa fesarwa ne? Kai yafaji haushin abu biyun nan dacewa bada sonta aka daura masu auran suba dakuma fada ma fati sirrinsu. Saidai duk dahaka zuciya da idanunshi suna matukar kewar ganin ummi, sai shida yadawo gidan. Ruwan wanka ya diba yanufi bandaki, man shafawarshi dasauran su suna dakin ummi, don haka yakalli bishira. Bari in dauko kayana can dakin ummi kozaki dauko min? Tace, bazan jeba kaje da kanka. Tana kwance kan doguwar kujera lokacin kanta yana matukar sarawa, don kuwa yanda yayi sallamar da kyar itama dinda kyar ta amsa. Saidai ita badon wulakanci tayiba, saidai don yanda take jin jikinta. Yashafa mai tare da feshe jikinsa da turaruka. Idanunshi suka sauka kan darinshi biyu daya aje mata. Yakalleta, ke ina abincin da kika dafa? Batare data dubeshiba tace, bandafa ba. Yace sbd me? Tace banjin yunwa, kaikuma naga ba anan kake ba, baki ya taba yasa kaya yafice. Har tayi sallar isha'i lokacin tasoma jin jiri, amma bata da niyar shan ko tea tanajin ya shigo ya aje mata ledar ta kusan minta 30 kafin tataso tazo tatura kofarta. Sannan taduba ledar, nama ne balango yaji albasa da tumatiri, sai sugar da madara, nan ta aje su tayi kwanciyarta afili tace natabbata kurar kenan indai naci maman nan. Bacci yadauketa can kusan ukun dare fa yunwa fatakai yunwa, kowa yasan yunwar dare yanda take jigata bawa, a gigice ummi ta tashi tahada tea tahau sha da gaggawa. Tagama kamar taci naman sai kuma tafasa ( tamiko min ninkuma nayi fuska nacinye au namanta madawani azumi lolx) ta kauda kayan ta koma ta kwanta, aikonan fa cikinta yahau hautsinawa. Dagudu tatashi tanufi fita tana bude kofa kafin takai bandaki tasoma sheka amai, tun bude kofarta abba yafarka dasauri yafito. Riketa yayi ganin yanda take sheka amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, sai sannu yake mata. Data gama yajanyo ruwa ya wanke mata fuska ta kuskure baki. Yawanke gurin gurin tana gefe tsugunne, cikinta da kanta sai ciwo sukeyi tana mikewa sai jiri. Nan tafadi ragwaf, shine yadauketa tamkar ya dau jaririya don rashin nauyi yace duk kece kikayi makanki sanadin wannan matsalar. Don kina fushi saiki yiwa abinci yaji, ai gashi nan kema kina ji ajikinki, kan kujer yadorata ya cire mata siket din atamfar dake jikinta, don duk sun jike sai na ciki. Yajuyata zai zage mata zif din rigar tana son ta hana amma bata dawani karfin hanawa. Tanaji tana gani abba yacire mata riga, gashi ko best bata saka ba sai breziya. Takai hannuwanta tarufe kirjinta. Shikam ganinta ahaka yasa tsigar jikinsa tashi, tun daga karamin yatsansa har tsakiyan kansa ruf da ciki ta juya tayi, shi kuma ya kunna mata fanka yafita. Zaune ya samu bishira atsakiyar gado, ta kalle shi da tuhuma, me kaje yi dakinta? Yce amai naji tanayi shiyasa nafita, bta dlpy ne, tsaki taja sannan ta kwanta. Shi kam bai runtsa ba, kunnanshi da hankalinshi suna can, dga bisani madayaga baccin yaki sai yatashi yayi alwala yasomayin nafila. Dazai tafi masallaci yske lekawa yaga IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 13 ZURFIN CIKI book 4 part 13 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:05 shikenan yanyun bata dawani aji agurin Abba ummi da tsoron allura sam taqi tsayawa jiya ma don agalabaice take Nurse din tace ke dai shagwaba ta miki yawa A ce allura ma kin kasa tsayawa kefa mace ce Wata rana ma haihuwa zakiyi ummi fa taki tsayawa nurse tazo tace ma Abba taki tsayawa abba yaleka dakin allura menene haka ummi tsoron alluran ki yayi yawa kitsaya mana Tadube shi fuska a shagwabe ya Abba dazafi nikam na hakura da allurar nan Abba ya shiga dakin ya kalli nurse din zo kimata ba zanyi asarar kudina ba Ummi bata ankara basai jinta tayi atsakiyar kirjin Abba shi kanshi sai jin wani abu yayi yataso daga tafin kafarshi zuwa tsakiyar kanshi Har yayi baya dasu tamkar zasu fadi to bare ummi wadda jikin nata ya dauki rawa Ya kalli nurse dinda idanuwanshi wadanda suka canza kala nan da nan zo kiyi mata Yadaga hajabinta tare dazame zanin daidai inda za ayi mata allurar shigar allurar ta saka ummi cewa wash tare da sake makalewa jikin Abba Don kuka tasaka wanda daga jinshi kasan shagwaba ce zalla ya lumshe ido lokaci daya ya kuma budesu nurse din tace kai ke kam kin cika shagwaba Abba ya dora yatsunshi guda adaidai gurin da akayi allurar yana murza mata tare da rada mata 'sannu' akunnenta Rekicewa tayi sannan ta kwace jikinta daga gare shi wani yanayi ta tsinci kanta mai girgiza bawa Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace mu tafi suna cikin mota dukkansu sunyi shiru Abba kasala ce da muradin matar shi yasa shizama hakan Ita ko ummi mamakinta ba yau Abba yasoma taba jikinta ba can baya yasha rike ta yazane ta, yasha rungumeta ayi mata allura, bata taba jin irin abinda taji yanzun ba Ta jingina da kujera tare da lumshe ido sai take ta tuno yanayin dataji lokacin daya mannata ajikinshi. Tsayawar motar ne ya sata bude idanunta, azatonta gida suka zo,sai taga ashe gurin kayan kwalama ne Ya kalleta, ina zuwa Ya fita ya nufi zuwa ciki jim kadan ya fito da ledoji, kaji ya siyo da madara mai tsafta, har da kankarar dayaji tana tambayar umma yasai musu. Tace, gama fa kankarar umma tasai mana. Bishira ta cika fam don takaici, kamal kaninsu Abba yaduba mata ko ummi tana gidan umma, ya fada mata bata nan. Ta tabbatar suna tare, ta cema umman bashir tunfa safe suka fita tare umma tace tun safe wane iri? Tace wai bta da lpy yaje kaita asibiti Umman bashir tace Allah ya tashe mu lpy Goben nan zan tafi kauye dama gobe ta ce indawo gaje 'yar bori, ina fada miki ummi dakanta zata bar gidan basai ance mata ba. Bishira tace dahaka zata faru zanfi kowa farin ciki, umman bashir tace kece aida shegen kyamar 'yan kauye bakison mutane Matsalarki kenan da ace zaki jure muje tare kiyi kwana 2 'yar bori da bokan tsauni zasu cika miki aiki Bishira tace zanje umma. Biyan bukata ai yafi dogon buri umma tace taki turo minshi ince masa sha'ani zamu don kada yace zai hana, bishira tace to. Sun sameta agidan ummi tayi dakinta da ledar ta shikuma yashiga gurin bishira. Ranar daya dawo dakin ta kuwa tayi kyau cikin doguwar rigar shadda ruwan kunkumadi, tun yana kallon ummi asace harya kasa dauke idonsa Ummi talura ta birgeshi sosai don haka tazauna bakin gado tana fuskantarshi hira ce suke yi jifa- jifa itace ma tasoma sako zancen Ya Abba zance ma alhaji yasai min TV nagaji dazama shiru Abba yace a'a banason haka ina sane zansai miki, tace to Bishira dake labe ta girgiza kai aranta tace ashe za ayi bala'i duk randa yakawo TV ai itama ai iyayenta suka sai mata. Tace to yaya abba inason makaranta ya aje laptop din daya soma budewa yamaimaita kalmar makaranta? Ta ce eh, yace sai nayi tunani Ummi ta marairaice tunani ya Abba? Kai dakake son inyi karatu? Yace shikenan haka sukayi ta hira har lokacin kwanciya ummi tayi shafa'i da wuturi tayi shirin baccinta takwanta Abba yau yakasa nutsuwa tamkar yaje ga ummi, amma girman kai ya hanashi. Ranar sama-sama yayi bacci sau biyu yna fita yana watsa majikinshi ruwan sanyi kozai dan samu nutsuwa. Har lokacin daya tafi gurin aiki bashi da wani kuzari. Ranar fati tazo lokacin bishira ta tafi badadinta, ummi tahau fati damasifa tare da fada mata yanda sukayi da ya Abba. Fati ta rantse tamaya kan cewa ba wanda yasan zancen nan don bata fada ma kowa ba, sukayi ta tunanin ta ina ne zancan nan yafita? Fati tace to ko kiyi hankali koda Anty bishira tana miki labe? Ummi tayi shiru tna nazari, can tadubi fati Bazan zargeta ba, domin ban taba ganinta ba amma zansa ido fati tace gara kisa kam yanzun harzuwa yau baku sasanta ba? Ummi tace aini bana bukatar sasantawa dashi tunda yace baiga gurin kwanciya agadona ba Fati tasaka dariya ke dai kada kicika baki,ummi tace kedai mu bar wannan zancen inbaki kudin kayan don Allah? Tati tace kibani dan bnida matsala mijina she ne yakaini nasai nawa zance yakaini insai miki kinason wanduna Ummi tace kinjiki da siket zaki debo min Ai har gajerun wanduna ki kwaso min, wulakanci zanyi a gidan nan.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 15 ZURFIN CIKI book 4 part 15 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:12 Saidatayi sallah sannan tazauna gaban madubi duk da shirin bacci take yi Saida tashafa manta da hoda sannan tadan goga jan baki. Tafesa turarenta ta isa gurin kayan baccinta dake cikin dirowar dora akwati, ta dauko duguwa tazira sannan takama karshen kitsonta tahada su guri daya ta tufke. Zata ha gado yace, ga nama kizo muci. Ta fada gado tare da jan filo ta dora kanta da kirjinta sannan tace nama saikace wata kura? Dazun fana danci amiyar danayi. Yace nida na siyo shine nazama kuran ko? Tace, a'a ya Abba kaine ranar nan naji kace kura. Kullum ake cin nama? Yayi murmushi aranshi yace, ok nan na rama ne kenan, sannan yace toshi kenan bari in ajiye miki naki. Nan tayi kwanciyarta. To 'yar gidan tsohuwa, yafada danufin zolaya, tace kai kuma dan gidan ummanka. Cigaba yayi dashiga yanar gizonsa, ita kam a gajiye take bacci yasoma fizgarta. Lokacin dayazo shima ya kwanta akan gado, ta bude ido lpy Yaya Abba? Ya dubeta tsakaninsu mutum daya zai iya kwanciya. Wace irin tambayace wannan mutum da dakin matarsa da gadonta atambaye shi lpy? Tatashi zaune, gani nayi ba guri agadona, yayi shiru, wato ummi bata barin bashi, ta tsura mishi ido tana jira jin mezaice. Yatashi zaune, idanunshi akan lebunanta, toni dai ga guri na samu, ta sulale itama takwanta rigingine tare dajan bargo tarufe rabin jikinta. Shima hakan yayi, ummi fargaba ce tasa tanemi bacci tarasa, shikam addu'ar bacci yakaranta sannan yashafa yalumshe idanu. Duk su biyun bacci sama- sama sukayi koda Abba baisamu nasarar kama kayan ummi ba amma aranshi yace wannan sharar fage ce. Dasannu za'a kai ga muradi, ko washegari daya kwana adakin dai bawani cigaba sai sake- sake Abban yayi tayi azuciyarshi, na cewa yakauda wata kunya ya fito mata amutum, amma yakasa hakan. Musamman yanda yaga ummin tana da shegen wayo, ba kamar yan yazata ba. Sannan gashi ta iya yin ado irin na tsokana. Hakan yasa duk ranakun girkinta Abba yana zumudi amma yakanyi kwanan rashin sukuni. Wata jumma'a tsohuwa ta riski ummi da irn wannan shiga tariga da gajeren wando, ta kawo mata ziyarar data saba inta dawo masallaci. Salati tasaka tare da cewa, yarinyar nan kece haka kinzamo sai kace arniya? Ummi ta tashi tsaye tayi juyi tare da cewa. Ynzun tsohuwa ban birge kiba? Ta ce kitson naki ne kurum yamin kyau, amma wannan shiga dame tai kama? Kuma shimai sunan malam yakasa hanaki koke ma yasoma tsoron nakine? Ummi ta tuntsure da dariya, ba tsorona yake jiba, shine ma yake son kayan don shine ma yasai minsu. Tsohuwa tace, oho! Eh lallai ta mike Allah ya taimaka, duk abin ku dai baza ki koma baturiya ba, ummi tace oho dai ke dai kuma baza ki iya wannan ba. Tace, Allah ya tsare nida wannan shiga, ummi ta dauko dari biyu ganin tsohuwa ta mike, nizan tafi in dan zazzaga in ziyarci jama'a. Ummi ta kama hannunta ta saka dari biyun, gana goron jumma'a, Allah ya hadamu aladan ziyarar. Suka fito tana cewa. Ke kullum nazo sai kin bani kudi ummi, to Allah ya shi muku albarka, Allah kuma yasa ki sauko lpy. Murmushi ummi tayi duk 'yan gidan su kallon mai cike suke mata. Duk hirar nan tasu bishira najinsu, ta cika tayi fam. Dama Abba yana kwana da ummi? Ashe shine yake sai mata kananan kaya? Ashe har tana da ciki shine yamata karyar cewa baya sonta? Tana dawowa raka tsohuwa, bishira ta kalleta, karamar yarinya ta iya karuwanci, dube ki. Ummi ta kalleta babba fa ya rike girmanshi inba haka ba inhau in taka, kuma niba karuwa bace, kema kalle ki. Ta taso zan zane kifa? Ummi ma tadaga murya. Sai kace wata 'yarki? Ba ki isa ba. Bishira tazo zata shakota, ummi ta daka tsalle taja baya. Karki sake ki taba ni. Nan fa gidan ya kacame, bishira sai ashar take zugama ummi, tana kiranta 'yar matsiyata. Ummi tace, banga kamannin masu arziki ba a jikinki, nan makota suka shigo yin rabo. Ummi ko tana fada mata take ramawa, abin da yafi yiwa ummi ciwo datace ummanki matsafiya, nasan

Chapter 19 of 24