Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce kun dawo? Ummin ta hadiye 6acin ranta."Eh, mun dawo Abba a ya shiga gaida Umma sannan ya mika ma Ummi ledar, gashi kin manta Ummi ta amsa tare da cewa, an gode. Umma ta ce, "Me ku ka siyo in ce dai ka sai ma Bishira? Ya ce, "Eh na sai mata, kaza ce fa Umma ba wani abu ba". Ta ce, "To shi ke nan maza ka koma gurin su, yace "To. Tana fita ya kalli Ummi akwai waya a cikin zan kira ki, kuma bana bukatar ki kashe min waya. Ummi ta ciro wayar da sauri, ta dibe shi ba wayar matarka ba ce? Ya ce, "Eh tata ce, ta mika mishi cike da kunan rai, ga abinku ka kira ni da layin Umma. Ya ce, "Ke ce za ki cigaba da rike ma mata tawayarta, ba tare da ya jira jin me za ta ce ba yana murmushi, Ummi ta kasa gane cewa ita ce matarta shi. Ko kallon kazar bata yi ba illa dai tayi duk wasu abubuwan da ta saba yi kafin ta kwanta, sannan ta kunna wayar tana tsammanin kira. 73..... Shi ko Abba koda yazo Bishira tana ta mitar don tsohon wulakanci an zo da ita an shanya ta, bai ce mata kala ba illa dai motar da ya tada suka nufi gida. Gidan duk kaya saboda bai maida ba da a ka gama fentin, ya dauki tsintsiya ya share dakin, sannan ya shimfida katifa ya fito inda take zaune bakin Rijiya. Muhibba tayi bacci tana rungume a jikinta, ya ce kawo ta, ta mike a fusace ta nufi dakin ba tare data bashi 'yar ba. Ya bi bayanta, so kurum yake ya lallasheta ba wai don tsoronta ba sai don tausayinta, yasan mata kan kishi za su iya yin 'yar karamar hauka. Wasu ma sai sun yi babbar kuma bai dace ana nuna kishinsa ba, shi kuma yana nuna ko 'in kula a gare ta, gefen katifar ya zauna ya lalubo hannunta ya rike cikin nashi."Bishira!" ya ambaci sunanta cikin sanyin murya, bata amsa ba kuma bata dube shi ba, ya ci gabada cewa, "Bishira ban ga abin damuwa ba. Ko damata uku a ka daura min aure da su bare daya, inkin yi la'akari da irin son da nake miki ke kin san Bishira ba kiyayya ta hada mu ba. Kina manta wannan ne? Ta dago ta dube shi ta dan soma saukowa, yayi murmushi har yau ban daina sonki ba, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta turo baki sai kace 'yar yarinya. To ai na sha jin a ana cewa so daya ne tak, ya cehaka ne, ta ce "To tsakanin ni da Ummi wa ke keyi wa? Da sauri ya ce ke, ta ce Allah?Ya sake tausasa murya, haba Bishira ya ki ke wannan zancen kema kin sani, kuma don Allah na roki ki in muna tare ki daina min zancen Ummi, ke kadai ce za6i na. Bishira taji dadin wannan kalamai, don haka sukaci namansu suka kwanta, ya bukace ta a nan masai da ta ce kaje gurin Ummin mana. Ya ce, "Na ce in muna tare bana son kina min zancenta. Sai dai in kina son ci gaba da horon daki ke min ne. Haba Bishira, ko tausayina bakya yi?An fi wata uku kina haramta min halas dina. Kullum sai dai ina azumi sai ka ce gwauro? Yajawota jikinshi, ya rungume da kyar dai ya samu yadan rage matsala, sai dai ita ma ya lura tayi missing dinsa. Suna kwance har kusan sha daya saura tuni ita tayi bacci, shi kam daman so yake tayi bacci yakira Ummi. Ya mike yaje yayo wanka sannan ya nufi dakinshi. Yaja katifarshi ya kai dakin, sannan ya kwanta akai, ya kira Ummi lokacin bacci ya soma figarta. Ringing din ne ya farkar da ita, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga, kafin ta amsa sallamarshi sai da tayi wata doguwar hamma.Ya ce, "Ke baccin ki ma ki ke alhalin na ce zan kira ko? Ta ce, "Amma ka san bacci ba ya jira in ya zo,ni kuma ba zan iya yiwa bacci gardama ba". Ya ceto sarkin iya zance, yayi nufin zolayar ta. Yanzun dai na soma tunanin kin soma sona, gabanta ya fafi, sam bata son ya gano hakan yanzu. Tafi son sai lokacin da shima ya soma sonta. Ya katse mata tunani, hasashe na haka ne? Ta ce, ko kusa, mene hujjarka da fadin haka? Ya gyara kwanciya. Na farko naga ana ta kishina, sannan tun da a kadaura aure da ni sai ciwo ya kame kansa, kuma nalura kina ta zumdin tarewa a gidana.Ya saki 'yar dariya, yasan ya cika mata ciki da takaici, shiru tayi nazari take wacce amsa zata bashi, ko dai wayar zata kashe? Tamkar ya shiga zuciyarta, sai ya ce.... 41 Tamkar ya shiga zuciyarta sai ya ce, "Koda wasakada a kashe waya. Ranta ya sake 6aci, ta ce Ya Abba ka tafka kuskure da kayi zaton ina sonka,sam ni bana wani kishinka. In don ka ce wayar matarka ce na ce ka rike abinka, sanin kanka ne ba ma shiri da matarka, kuma duk abinda ka ce nata ne dole na guje shidon ba zan dauki wulakanci ba. Batun ciwo kuma daka ce tunda aka daura mana aure ka neme shi ka rasa dama bani na dora makaina ba, kaima ina naka hawan jinin ya tafi? Sannann kuma wane zumudi na nuna na tarewa a gidanka, Ya Abba ka sani yanda a ka tilasta maka aurena, to ni ma fa dole tasa na hakura. Amma ka rike a ranka bana wani sonka bani kamarina ina sonka, kalaman nata na karshe sun burgeshi har sun sa shi yin da ya sanin tsokale zancen. Sai kuma ya canza salo da cewa, haka dai ki ka ce amma ina da ja mu dai bar zancen, shin dazun kafin ki soma wannan tunanin me ki ke yi? Ta danyi shiru tana tambayar kanta. Dama mutumin nan haka ya ke? Oh yanzun dabara zai min sai ya gano ko ina sonshi dole, to kuwa bazai ji ba, ya katse ta da cewa ban san ki da karya ba. Ta ce, ina tunanin irin ukubar da zan sha a gidanka ne ta wulakancin da zaka min, ya yi shiru zuciyarshi tana cewa yarinyar nan ba ta san irinson da ka ke mata ba ai ta ma dauke ka mugu kenan. A fili sai ya ce, "Kuma fa kin yi tunani, Allah yabaki ikon daukar ukubar da zaki sha tare kuma dajure wulakancin da na tanadar miki goben Ummi. "Ya fadi, wai dama da gaske wulakancin zai mata. Gyara kwanciya kawai tayi bata kara cewa komai ba, kuma bata da nufin cewa wani abu, yasa taji haushi sosai, don haka sai ya tausasa muryarshi. "Ummi kina ji na?" Uhm" Kurum ta ce, don ya gane tana jin shi. Alkawari ta dauka ba zata sake cewakala ba, tunda ya hanata kashe wayar. "Ba ni da nufin miki..." Sai layin ya yanke daga gefanshi, ta ce, "Gara ma haka". Tana kokarin kashe wayar gaba daya kiranshi ya sake shigowa. Tsaki taja kafin ta daga, kuma a ciki ta amsa sallamarshi, sannan cikin murya mai kamar zata rushe da kuka ta ce "Ya Abba ni fa bacci nake son in yi". Ya ce, "Sam ba wani bacci da za ki iya yoa sai tunani". Ta ce "To na ji, ina son yin tunanin please".Ya ce, "Tunanin me za ki yi". Cikin gundira ta ce,"Dole in yi tunanin yanda zan kare kaina daga wulakancinka, don bana tsammanin zan dauka" .Ya ce, "Wasa nake miki fa." Ta ce, "Uhum, ban amince da cewa wasa ka ke min ba, don na tabbata mu ba abokan wasa ba ne".Ya ce, "To shi ke nan bari in bar ki kiyi tunanin, amma tunanin yanda za ki faranta min za ki yi". Muryar Bishira ce ta katse shi. "Oho! Ai tun da na farka ban ganka ba na san ana nan ana cin amanata". Ya kashe wayar da sauri, duk da dai Ummi ta riga ta jiyo muryar Bishiran. Sai dai bata fahimci me Bishirar take cewa ba, ringingine tayi tare da dora filo a kirjinta, tunani take yi wane irin zama za su yi? Koda bata da amsa ta kudurce har abada ba za ta dauki wulakanci ba, a shi ko a matar shi. Sai dai alkawari ta dauka ba za ta musu raini ba, matsawar ba su suka 6ullo da hakan ba. * ************************************** Shi ko Abba rigima suka dinga yi da Bishira cikin tsohon daren wai ya cuce ta ya kwanta da ita yazo yana hira da wata banza. Kila ma ya saba kwanciya da Ummin ne yau bai samu dama ba, Abba ya ce kin so kanki in ki ka yimin wannan zaton, don ban ta6a nemanki ba, kafinki shigo gidana, ko na ta6a?"Ta ce, "Don ka san dai ni ba fuska". Da ya gaji da iya korata ya rufe kofar ya koma can dakin. 40. 74... Washegarin ranar, ga mamakin Ummi tun misalin karfe goma jama'asuka cika gidansu, a ka dora abinci. Can kuma saiga yaran shagon Abba da dinkunan zannuwan daAlhaji Babba ya sai mata.Ranar Abba bai shigo gidan ba a waya ya kiraUmma suka yi magana, zuwa karfe uku angama yiwa Ummi jeren dakin da yake yana da girma yacinye komai tsaf.Fitar 'yan jere babu jimawa sai ga Anty Farida dakannasu motar tana da kaya tana biye da su, gadoda kujeru a ka canzo mata.Suka jera mata sannan suka lodawa motar na dasuka dauki hanya suka koma, Abba kam yana gurinaiki amma zuciyarshi tana gida.Fatanshi Allah yasa yana zuwa ya tarar an kaimishi Umminshi, kawayen Bishira da makotansu'yan jam'iyyarta duk sun shigo gidan sun hadu saizugata suke yi tare da nuna mata koda wasa kadata sakar ma Ummi fuska, kuma in ta mata takamata ta duki 'yan kayanta.Suna gidan a ka kawo Ummi, 'yan kawo Amaeyakam suna jiyo habaici da zagin da su Bishira ke yi,don haka suka ce kada a kai musu yarinyar.Inna Saratu da Inna Harira suka ce ai kuwa sai ankaita.Ba ko kunya Bishira ta zabga musu harara lokacinda suka fada mata cewa ga kanwarta sun kawomata, don Allah su zauna lafiya tare da Aminci.In yarinyar tayi ba daidai ba ta sata a hanya... takatse su cikin tsawa da mikewa tsaye. "Don Allahku fice min daga daki amanar kishiya? Har wai muzauna da aminci ku ke cewa?Tayi 'yar dariyar yake "Kun yi kuskure, ai batacanza daga sunan ta na kishiya ba, kuma kowa yasan kishiya abokiyar gaba ce."Inna Saratu ta ce, "Baiwar Allah jahilan mata sunesuke yin irin wannan tunanin, amma ga masu ilimisuna koyi da gidan mai tsira da Aminci (S.A.W)ne".Bishira ta ce, "To kawai dai ki ce min jahila ki huta,bari ku ji ba za n ba ku a 6oye ba, zama ne za muyi shi na rashin mutunci, na kowa ya iya allonshi. Don ina kishin mijina, kuma zan nuna". Tirkashi! Lallai akwai daru kenan. To masu karatu ku biyo ni cikin littafi na 4, kumana karshe domin jin yadda za ta kasance atsakanin Bishira da Ummi da kuma Oga kwata-kwata wato IKI book 4 part 1 ZURFIN CIKI book 4 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:42 Inna harira tace, Allah ya kyauta ku tashi mu tafi. Suka mike Suka nufi dakin ummi. Duk da ummi a da bata tunanin tana da lokacin bishira, yanxu kam dole tasan zaman da zasuyi. Su inna saratu suka ce ma ummi duk abinda zatayi don allah kada ki kulata. Suka ce tayi harkokin gabanta tayi biyayya wa mijinta shine abunda zai fisheta. Ummi tace To amma a zuciyarta bata tunanin zata zuba ido a rainata. Suna tafiya fatima ta shigo yiman sallama, ummi tace don allah fati ki dan tsaya ni kadai fa zan zauna a dakin nan. fati tace wayace kada kisan kawaye? Ummi ta ce wane kawaye, auren da a ka daura cikin yan mintina? Fati tace, Yau zakiji abinda mata kaji. Ummi ta damko mayafin fati, ni fa inajin turo, wai da gaske da wahala ko kina tsokanata ne? Fati ta kamo kunnen ummi tayi mata rada. Ummi ta zaro ido tare da cewa, Da gaske? Fati ta sheke da dariya tace sai nazo jin batun. Ummi tace sirrine ya za'ayi in fada miki sirrina? Fati tace au ni shine na fadamaki nawa ko? Ummi tace kinyi haram da kika fada fati tace, "ke kuma kinji haram ko? Suka sa dariya. Duk yanda ummi taso fati ta tsaya amman taki, don haka sukayi sallama. Fati ta shige dakin bishira don yi mata sallama. Bishira tace, fati fitar min daga daki bana wasa dake, tunda kema naga kin koma jam'iyar waccan yar iskar, fati ta fita, cikin ranta tana cewa ba zanki yar uwata ba don kishinki na banza tayi tafiyata. Ummi tsuru tayi tanaji tsoron abinda fati ta fadamata, amman sai wata zucia tace keda ba sonki yake ba kila ma bazaibi ta kanki ba, sannan ta samu yar natsuwa. Abba ya fito zai nufi gida sai kuma ya fasa ya nufi super market, ya siyo audugar mata yana tsammanin gobe ne zata tashi da al'ada a lissafinsa. Tun sanda ta soma bai taba mance ranar ba, haka in ya chanza mata lokaci duk yana lissafe. Ya sai masu yan kayan masarufi sannan ya fito, gida ya nufa amman gabansa yana faduwa kila har yanxun ba a kai ummi ba. Da yayi fakin sai kuma ya nufi gidan su umma duk kowa ya watse. Yayi sallama tsohuwa tana alwala ta amsa. Umma daga kicin ta amsa, tsohuwa tace "wane kinibibin kuma ya kawoka mai sunan malam? Bayan an kai maka ita? Yace kaji tsohuwa da wata magana da gurin ummi nake zuwa? Ni gidan mu ne. Tace kadaiji shi, takwara dai kada inji kada in gani, don nace mata duk abunda kuka mata tazo ta fadamin. Yarinyar nan tana kuka wiwi tabar gidan nan. Umma cikin dariya tace "toh ai tsohuwa in don Abba baza ayi fada ba, ummin ce dai abin jama kunnen. Tsohuwa tace 'a' a daina zancen nan suwaiba kada ma ya samu nayi. Abba yace" Toh bari in zo in hada maki kayanki mu tafi can don kada wani ya zafin cewa. Kinga kyafi tare mata. Tace ina gana nan din ma zanji. Yace Alhaji sun shigo kuwa umma? Tace A'a basu shigo ba. Yace toh bari in isa gida. Tace toh Abba ummi ma dazun aka rakata. Don allah Abba ka kara hankuri a kan na da, sannan matarka kuma kada kace zaka nuna mata bambanci a kan ummi yar uwarka ce. Ka kwantar mata da hankali ka mata adalci, sannan kada ka bawa ummi kofar da zata raina bishira. Yace zan kiyaye insha allah, kuma don allah umma ki kara mika godiata gurin alhaji. Tace haba Abba yaya kake fadin haka? Alhaji ai mahaifinka ne karka dinga kallon alakarka da ummi. Yace haka ne duk da haka dai a min godia, tsohuwa tace yaki godia ya samu mata a sama don rashin imani mai sunan malam ko gyauto bai sa mata ba, toh kasani tana binka bashin lefe. Abba Yace umma ni dai na wuce. Umma cikin dariya tace "Toh Abba. Yace tsohuwa ni nayi gaba, don in na cika tsayuwa a nan kila mu dambace, Tsohuwa tace kai dai jeka na baka amana ya tafi yana dariya. Koda ya kai kofar gidan sai ya bude mota ya dauki kayan masarufinshi ya nufi cikin gidan salam dai duk da jarumta irin tashi gabansa ne ke faduwa. Bai san wace irin masifar bishira ta tanada ba. Ya shiga da sallama. Bishira tana zaune akofar daki tana goye da muhibba, amman bata amsa ba. Duhun magriba ya soma dan daf da a kira sallah a ke, yace bishira ya ba a tada inajin ba? Tace tunda kazo yanxun ai sai ka tada kai. Da kafin wata tazo ai baka taba zuwa kace a tada inji ba. "Abba ya kalleta a zuciyarshi Yace" mata kenan masu manta alhaji. Ya aje ledodin hannunshi ya nufi injin. Bishira ta mike ta nufi ledodin tana fadin Tun yanxu a aka shigo mata da kazar, alamun ba za'ayi ada ba kenan. Ni lokaci na sa wuraren tara ya shigo ina lissafe da komai, ta bude ledodin sai taga kayan masarufi d kuma audugar mata. Tsaki taja tare da dangwarar dasu yana kallonta da ya kara mai ya tada injin sa yazo ya kwashe ledodin ya shiga falonta.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 2 ZURFIN CIKI book 4 part 2 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:44 Kujerun da aka chanza mata masu kyau, amman a ran abba yace ya basu sati biyu. Ya cire riga ya fito yana son yayi wanka ne kafin a kira sallar magana,yaja ruwa da sauri da sauri yayi ban daki ya fito ya shiga falo ya kwalama bishira kira. Tace minene kake damuna? Yace ina aka kai min akwatuna na? Tace tace ina kuwa gasu can a kicin da sauri ya fito, kicin din lafia? Ya tsaya yana kallonta bani da mutuncin da za'a sa min kayana a daki? Tace ni da aka guji dakina da kayan a kace ni kazama ce, me zaisa in sake kaine? Daga baice komai ba ya nufi kicin ya kwaso akwatuna shi da takalmin shi ya kai falonta. Bai tsaya chanza kaya ba, ya nufi masallaci don zai rasa sallah. Bai baro masallaci ba sai bayan isha'i amman bishira tana zauna. Ummi kam ta kasa fitowa don tana kyankyamin ban dakin, gashi al ada ta sameta da yamman nan, sannan duk tanajin abin da sukeyi da matarshi. Ya shigo gidan ya chanza kaya sabi fil, ya feshe jikinsa da turarukkanshi wayar shi ta soma ringing ya daga salis ne. Yace aboki in ba sallama akwai daga hannu ko? Kace an kai maka rabin ranka koda ba zamu rakaka ba ai kayi mana sallama. Cikin dariya Abba yace na yafe salis yace To Allah ya bada zaman lafia. Suka yi sallama zai aje wayar kenan sako ya shigo. Ya duba ummi ce da wayar nan da ya bata ajiya cewa tayi, ina da matsala, ina bukatar taimako. Gabanshi ya fadi, sai kuma ya tuna kila al'adar ce, don haka sai ya saka hularshi ya dauki ledar audugar ya nufi dakinta. Har lokacin bishira nan zaune inda take, tace au tun daga yanxu za'a soma rashin adalcin? An dauki leda an nufi dakinta? Sam baiko waiwayo ba, yayi sallama ta amsa tare da gyara mayafinta, ya shiga suka kalli juna Cikin ido zukatansu sukayi fari kal. Cikin taushin murya yace, wane taimako kike bukatar? Ta lumshe ido sannan ta juya masa baya domin kunya ta rufeta. Yace To karba ya mike mata ledar ta waiwayo ta ansa da hannu biyu. Mamaki ya cikata ganin audugar, ya yayi har ya san tana bukatar audugar kuma a ina yake sanin lokacin al'adarta har idan ya chanza? Tace nagode yayi dan murmushi nima ina godia. Ya juya har ya daga labule tace "Em na ce....." ya waiwayo yace kika ce mi? Tace don allah inason maganin wanke bayi ne, tayi maganar Cikin kyankyami, sakamakon irin dattin da tagani a bandaki tare da gamsa kuka. Yayi murmushi wane iri kikeso? (IZAL) yace ai akwai amman yanxu Bai kamata ki shiga wankin bayi ba. Tace zan wanke in dai akwai. Yace bari in wanke maki, da sa tace a'a yaya Abba zan wanke. Falon ya koma ya cire rigarshi ya shiga jan ruwa. Bishira tana zaune ta mike ina badai abokitaina ba, in zaka kwashe mata rijiyar kwashe, amman a juye ko in baras kuma in dai ruwan da za'ayi amfani dashi ne kakeja, To kesani nima duk lokacin da zanyi amfani da ruwa saika dibar min, ehee. Ummi ta fito da bokitai don duk tana jinsu, tazo wurin Cikin sanyin murya tace, Ya Abba don allah ka bari in ja ruwan nan. Ya kalleta, take ya manta da duk bakin Cikin da bishira ta kunsa mashi. Yanxun daga zuwa saiki fara jan ruwa? Ummi tazo ta kama igiyar gugar, ai ba zama nazoyi ba, Ya Abba bauta nazo yi, Aljanna sai an dage. Ya saki dariya bishira ta dakatar dashi da ce wa "Karuwanci za'a gwadaman? Ta daga ruwan da ya zuba a bukati zata watsama ummi, yace kina watsa mata zan baki Mamaki. Cikin tsawa yayi maganar ta tsaya cak da bokitin yace, Sakarya mai kishin hauka. Yaci gaba da jan ruwan yana zubawa abokitan da ummi ta fito dashi. Bishira ta aje ruwan sannan ta hankadar dashi a kasa, Bai ko kalleta ba. Ya zuba ruwan sannan ya fito da izal da omo. Daki ummi ta koma ta dauko tsinsiyar da aka sai mata don wankin bayi, kin tafiya Abba yayi tana wankewa yana zuba mata ruwa har sai da taga bayin yayi yanda take bukatar sannan ta hankura. kyankyami jikinta takeji don haka taje ta hada kayan wanka har lokacinzurfin Ya Abba yana wurin rijiyar. So take ya matsa taja ruwan amman yaki, don ya lura bishira shi kadai take shakka zata iya zartar da komai kan ummi. Shine ya sake zuba mah ummi ruwan wanka, sannan ya coge har ta gama ta fito rufe da hijabi tayi dakinta, sannan ya dauraye jikinsa yaje ya maida kayanshi ya nufi wane. Bishira tana nan wurin kofarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, bakinta kuma Bai fasa sambatu ba sai kace sabon kamun hauka. Fadi take kuma a zo a biyani duk basisikan da nike, ehee. Kuma in yarinya tamin in murji bukina. Ummi kam ta gyara jikinta tsab ta saka sabbin kaya ta feshe jikinta da turarokan da umma ta sai mata. Tunda ba lefe aka mata ba bare ta samu kayan shiga. Kan doguwar kujera ta mike, salam yanzu taji yinwa tana tsammanin rabonta da abinci tun karin safe. Ta shafa Cikin ta ina ma umma na aiko man da abinci. Ta furta a fili WAYA nan ta jawo tana tunanin sanar da Abba cewa tana jin yunwa. Sai wata zucia ta hanata wannan ba girman amarya bane. don haka ta share ta bude shafin game tana ta bugawa. Sai sha daya Abba ya shigo gidan, ya rufe gidan. Nufinshi ya wuce kai tsaye dakin ummi, amma sai ya tuna da kazar da ita bishira ya sawo mata. Duk da baya tunanin ta karba ga mamakinsa tana tsaye a tsakar daki har yanxu da daurin kirji take. Wannan ya nuna batayi sallah ba, bare wanka. Ya mike mata wata harara ta zabga masa banaci, ya juya batare da yace mata kala ba, ta biyo bayan shi, A bani basussukana da nike bi malam. Ya nufi dakin ummi taba biye dashi, ummi ta turo kofa dama yana kokarin tura kofa dama yana kokarin tura kofar bishira tana rike masa riga ta baya. Ya waiwayo Cikin zafin nama zai wanka mata mari sai taci sa'a ta tsugunna, Cikin azama ta yunkura tayi baya da gudu. Banda tsaki da yaja Bai ce komai ba. Ya shige dakin ummi da sallama, ummi bacci ya dan dauketa saboda gajiya. A kan kujera take da waya a hannunta. 4rm Shamsy bello balarabe.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 3 ZURFIN CIKI book 4 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:48 Niyyarta yau sai taji komai, don haka ta kai yarta ta kwantar, dai dai lokacin ne abba ya fito don kashe injin. Sake fitowar da tayi ne taganshi zai koma. Wayan cewa tayi da daukar buta ta shiga bandaki, shi kuma ya shiga daki ya kulle kofa, tazo ta manne jikin kofar. Fitar abba shine yaba ummi damar saka kayan baccinta, don bata iya bacci da kaya masu nauyi. Fargabarta yaya kwanciyar tasu zata kasance? Kan kujera ta zauna tare da kwantar da kanta a hannun kujera. Shima abba yana da jin zafi don baya iya bacci da kaya sai da gajeran wando kurum, idanu ummi ta kulle lokacin da taga ya abba ya soma cire tufafinsa ga hasken cocilar da ya kunna. Filo ya dauka ya jefa Kan doguwar kujera ya kwanta rigingine, ganin haka sai ummi ta mike ta nufi gado addu'a tayi sannan ta lumshe ido har bacci ya dauketa. Fuskarta cike da murmushi zuciyarta cike da godia allah yau gata dakin ya abba a matsayin matarsa. Abu daya ya rage mata shine ta koya masa yarda zaya sota. shima farin ciki ne a ranshi yayi da idanuwanshi sukayi kuri a Kan gado yana hango ummi ya ta zama halalinsa Abu daya ya rage shine ya koya mata sonsa. Bishira data labe bata jiyo komai amman kunnuwanta suna jiyo mata magana kasa kasa,,hawaye na zuba a idonta batasan iya adadin awanin data dauka a kai ba. Koda ta koma daki juyi kawai take a gado. Abbanta abun sonta yana can kwance da wata, watar ma makiyiyarta wadda ta tsana. Wata zuciya tace kije ki watsa masu man petur wata tace ki bari da safe ki caka masu wuka babu abinda bata rayaba har asubahin farko. Labule ta daga ta shiga leke taga ko zasu fito, lokacin ne kuwa abba ya fito yaja ruwa a bokitai yayi wanka da alwala. Ba zata gane ko wani Abu ya faru tsakaninsa da ummi ba don wanka al'adarshi ce Koda bai dauki najasa ba. Nafila ya shiga yi da rokon allah yasa ummi ta so shi, ya kuma hada masa kansu. Koda zai tafi masallaci bai tashi ummi ba tunda yasan ba sallah zatayi ba. Bishira ta fito tasa kujera kofar daki ta zauna, saboda tashi bai bar ummi bacci ba, don haka ta tashi in tana al'ada yini take wanka gaba daya sai ta tah ktankyamin jikin ta. Ta fito da bokitai duk ta cika d ruwa, Bishira tana kallonta sai da ta wanke bayi tas, sannan tayi wanka. Sauri take tayi kwalliya don a cikin nasihohin da umma tayi mata a safiyar da za'a kawota gidan miji tace kada ta sake mijinta ya ganta cikin kazamin yanayi. Kuma kada ta bari ya shaki wari daga gareta, tayi shafe shafenta. Atamfa ta saka riga da siket mai ruwan hoda hoda da ruwan kwai. Daurin dan kwali ta kafa sannan ta feshe jikinta da turaruka masu kamshin gaske, sannan ta shiga gyaran dakin duk da ba datti yayi ba. kayan da abba ya cire ta ninke don da jallabiya yake zuwa masallaci, sannan ta dau kujera ta kishingida saida gari yayi haske sannan ya nufo gida. Tsaki bishira ta jamashi maimakon amsa sallamar ta kara da cewa an girma ba'a san an girma ba, an kwana da yar ciki abin kunya. Ai wallahi baka cika dan halas ba da ka auri yarinyar datayi sanadin kulleka kaci duka har aka ballaka ba. Ya kalleta dalilin kenan da ban cika dan halas ba? Tace eh baka cika ba, yace toh jeka naji ni shege ne, in don dai na auri ummi ne, tace munafuki dama can kana sonta. Ya sake wai wayoowa yace so kuwa mai tsanani. Takaici ya cikata ta daga murya allah ya isa

Chapter 17 of 24