Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaisawa da su Umma, ta fito ya bita da kallo, kin yi kyau kanwata, Umma ta ce yau za ku hoton ne? Ta ce kila, Abba ya ce shi yasa ki ka yi kwalliya haka? Ba ta ce komai ba sai dai ranta bai so ma maganar da Umman tayi ba. Suna hira da Umma ta shirya misi abinci ta koma kan kujera ta dauki littafi lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. 13 Suna hira da Umma ta shirya mishi abinci ta koma kan kujera ta dauki littafi, lokaci-lokaci idanunta suna kan Abba. Shi ma haka ya ce wai ni littafin nan da ku ke nacin karatunshi dame kuke karuwa? Umma ta ce, Ai fa gara ka tambaye ta, don ban ga abinda ta ba muhimmanci ba irin wannan littafin. Ummi ta cem ina karuwa sosai Umma suna koya mana tarbiyya yyanda zamu tafi da rayuwarmu cikin tsarin Addini da al'adarmu. Abba ya ce amma basa koya tsafta da biyayya, Ummi ta ce suna yi sosai ma, ya ce Umma ni naga jarabar karatu irin na Bishira amma kullum mugayen halayenta bayyana suke yi. Ummi ta ce ni ko har addu'o'i zuwa girki kala- kala ina koyo, Umma ba rannan nayi dafadukan kwakwa ku ka ce ya yi dai ba?" Ta ce, "To ki dai dinga daukan na kwarai kina yarda na banza, Abba ya ce in haka ne d agaske zan samu lokaci in zo ki karanta min in ji, ta ce "To." 27..... Umma ta yi 'yar dariya ta ce, "Sai ka ce ba ka da aikin yi? Ya ce, "Allah Umma da gaske nake yi don in ji wacce irin koyarwa suke yi, marubutan ko ko sai shirme?" Kiran sallar Isha'i ne yasa Abba mikewa, ita kuma Umma ta tafi kicin don shiryawa su Alhaji Abinci. Ummi kam sun bar ta cikin takaicin tafiyar Abba don dai bata gundura da shi. * Alhaji Ya kalli Umma, wai yau bikin yaran nan saura wata nawa? Ta ce, "Wata ko kwana dai?" Yau saura kwana talatin da shida, ban ga kana motsi ba? Alhaji bikin nan zai mamaye mu, ya ce "Yanzun ya za a yi da batun kaya?" Ta ce, "Ni da cewa nayi ga Abba sai yaje ko kuje ku za6a musu kaya masu kyau a siya, kada a ba kafintoci in ba a yi sa'a ba har lokacin yayi ba a gama ba". Ya ce, "To zan sa shi ya tafi da su kawai su za6a". Ta ce, "Sai kayan girki na dai sayi tukwane da risho, sai kuloli". Ya ce, "Duk da haka uwata zan sa ta za6i wasu kayan." Umma tayi dariya tare da cewa, "Allah ya kara budi, nan dai suka yi ta lissafin kudi. Da safe Alhaji ya kira Abba a waya ya sanar da shi cewa ya dauki su Ummi suje su za6i irin kayan da suke so, duk da cewa zancan ya doki zuciyarshi amma ya ce "To." insha Allah zamu je, suka yi sallama. Sam baya son ya ji batun auran su Ummi, baya son rasata, kuma yana ji a jikinshi cewa zai same ta. ** ** 28.....Yammacin ranar Asabar La'asar lis garin yayi dan sanyi Abba ya nufi gidansu don daukan su Ummi zuwa kasuwa. Jikinshi sanye da farin yadi mai shara-shara, har ana iya hango fara kar din singiletin da ke ciki ta manne a jikinshi. Kamshin turarenshi ya cika dakin Umma wanda ba shiga yayi ba daga bakin kofa suka gaisa. Ya ce, "Ummi su fito don Ummi ce ke shiryawa tuni Fati ta fito, ya matsa kofar Tsohuwa suka gaisa, sannan ya ce "Umma sai mun dawo. Ya nufi waje yana fadin su Ummi su mishi sauri. Sun fito za su duru a baya Abba ya ce Ummi ta dawo nan gaba, ta zauna ranta dagule don ita bata bukatar wani za6i tunda ba wanda take so zata aura ba. Haka nan ta fuskanci Abba yau yana cikin wani irin yanayi, kila daga gida aka 6ato masa rai, nata tunanin kenan. Shi kam takaicin zuwa za6on kayan ke damunsa, ya kalli wayarsa da ke ruri ya daga, Salis ya ce kana ina ne? Ya ce ina nan unguwarmu zan kai kannena ne za su za6i kayan daki. Ya ce, "Ta ina zaku bi? Abba ya ce kai kana ina ne? Ya ce ina nan kusa da asibitin Malam, bari in jira ka a jikin gidan man nan, Abba ya ce "To." Salis ya kalli yarinyar da Abba ya ce Ummi koma baya ya ce, "'Yammata sannunku, suka gaishe shi ya yi murmushi ke ce Ummi?" Ta ce, "Eh, ya ce ya su Umma?" Ta ce lafiya lau, ya maida dubansi ga Abba wanda ke tuki cikin nutsuwa ya ce, "Idris akan batun yarinyar nan ne don Allah ka daure muje gidansu yau". Gaban Ummi ya fadi. Abba ya ce, "Don Allah Salis ka bar batun yarinyar nan, kai dai kasan halin da nake ciki game da wata". Salis ya ce, "Me yasa ka amsa kana sonta, kuma har kana daga waya duk lokacin da ta kira ka?" Abba ya ce, "Shike nan za mu je da yamma tunda wancan na rasa madafa". Salis ya ce kuma fa da hakan zai fi maka. Ummi gashin jikinta duk ya mike, suna fitar da zufa lumshi ido tayi luf a kan kujera ta kwantar da kai, Salis ya waiwaya ya dubeta, yaya dai? Ta yi dan yake, "Ba komai." . 29.... Sun je gurin kujeru da gadaje, Fati tayi ta ruwan ido yayin da Ummi ta koma ta jingina a kujerar da ta zauna. Abba ya dube ta. "Ke wanne ki ka za6a? Ita ta ce wancan farin". Ummi ta yatsina fuska, "Nifa bani da za6i, duk wanda ku ka ga yayi". Salis ya ce, " Idris yarinyar nan ina zaton tana sonka, naga tunda muka yi maganar zuwa gurin wata ta canza yanayi. Abba ya ce, "Kyaleta ba wani ya dubeta ba, ke Ummi tashi ki za6a mu ji farashinsu, sauri muke. Ta ce, "Ya Abba cikina ke ciwo, ka za6ar min don Allah". Ya ce, "Salis ita ma a bata farin kawai ko? Salis ya ce, "A daukar mata mai ruwan madaran, mai shagon ya ce sun fi tsada, Abba ya ce ka daukar mata su. Sun koma gefen kujeru nan fa Abba ya ce dole sai ta za6a, nan ma wanda ta za6a a ka ce sun fi na Fati tsada, suka ji farashinsu su sannan ya ba da wani abu suka tafi. Ya sauke su a gida, Fati sai ba Umma labari take yayinda Ummi ta shiga kuka, Umma ta ce ke kuma lafiya ki ke kuka? Ummi ta ce "Umma ni bana son in yi auren nan, bana son in bar gida. Fati ta ce, "Shi yasa naga tun a gurin shagon kina ta 6acin rai? Umma ta ce, "Shirmen banza da wofi, sai ki tayi. Ta fice, Fati ta ce Ummi ke kin cika son damuwa. Menene na damuwa? Kila ma kina nan unguwar.ovels / ZURFIN CIKI book 3 part 5 ZURFIN CIKI book 3 part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:29 ummi sannu da zuwanku, nan sukayi masa gaisuwa yace ummi kaisu ciki. 36.. Zainab tace a ranta wato ma ummi yafara gani, a fallon su umma suke don nan ta fara kai su, tace umma wanan ce zainab, wannan kuma matar abokinshi salis, umma tayi masu sannu da zuwa sanna tace ummi ta kaisu dakin bishira, sun shiga sun yi mata gaisuwa, bishira tace ke ko gaisuwa baki zo min ba koda yake bai dame ki ba, ummi tace nima ana ta zuwa min gaisuwan ne a gd, duk yan dakin suka kalli ummi, sahura tace ke asuwa? Bishira tace ita a mahaifiyar shi, ummi tace zainab kuzo muje, tun daga lkcn zainab tasa a ranta akwai matsala a wanan familyn din, basu jima ba suka yi sallama, inda ummi ta rakasu daga can itama ta wice gd, suna shiga soro shima ya shigo yace badai tafiya zakuyi ba? Ya kalli ummi sun sha ruwa ma kuwa?ummi wadda dama idanunta na kanshi ta amsa mishi da idanu. Yace yama akayi kuka gane gdn zainab tace yaya salis ne yakawo mu, ya kalli matar salis yace madam mun gode fa,tace bakomai Allah ya jianshi, sam ummi batasan lokacin da furucin ya fito mata ba, sai dai taji tace ya abba duk ka rame baka cin abinci ko? Shi kanshi yayi mamaki don haka ya ya tsura mata ido, sai taji kunya ta rufee ta saita kau da kanta daga kanshi,don kada su zargeta. Kayi hkr naji wani malami yace duk wanda yaranshi kananan uku suka rasu to zasu ceceshi ranar gobe. Kaga ynz kafara da daya,matar salis tace ai koma dayane indai kayi hkr kayi tawakkali,ummi ta kalle shi tace to kaji ma,yace ummi nifa tuni na dangana,ta sake tausasa murya to meyasa baka cin abinci? Ya tausasa murya wadda dama take a dusashe yace ummi inaci,tace ya abba baka fa yin karya,yace to yau zanzo inci a gabanki, ya kalli matar salis wadda ke murmushi, in naci a gabanta saita yarda ko? Tace tabbas! 37..Zainab wadda takaici ya cikata tace da matar salis anty nifa natafi, abba ya dubeta zainabu nagode ki gaida su mama sai nazo,batare da ta tsaya ba tace to, ummi ta musu sallama itama ta tafi gd. Zainab ta dubi matar Salis bayan tafiyar Ummi, ta ce, "Duk da son da na ke ma Idris din nan ba zan aure shi ba". Matar Salis ta ce dalili? Zainab ta ce, "Bana zaton ko matarshi ta gida da ya aura ya aje yana sonta irin yanda yake son Umiin nan". Abin nasu yayi yawa. Dubi yanda ya manta da ni, ta ita kawai yake yi. Matar Salis ta ce, kin ji ki da wani shirme, ita da zata yi aure?" Zainab ta ce, "Abinda ke tausar zuciyata ke nan in na tuna cewa zata yi aure, amma kai naga ji ba zan iya ba, haka suka tafi tana ta bai wa yarta labarin yanda Abba ke ji da Ummi. Kamar yadda Abba ya ce zai zo cin abinci da dare yazo, Ummi ta saka shi gaba wai sai ya cinye wake da alayyaho da kifin da ta dafa masa. Da kyar ya cinye plate din farko ya ce "Ummi na koshi kin ji? Ta daure fuska tana kallonshi, shi ma ita yake kallo yana dan murmushi. Ya ce, "Ina ma a ce tun da da haka muka yi sabo, Ummin cikin kwanakin nan kin lura cewa muna shiri". Ta harare shi, "Kana zaton na manta da irin dukan da ka yi ta min ne? Shi ma ya harare ta tare da kwaikwayon muryarta. "Kina tsammanin zan manta da irin tsokanar fadanki ne? Ko zan manta da Suhailar Kaduna...?" Kafin ya rufe baki tuni ta yi uwar daka da gudu, shi kam dariya yayi ta yi yana cewa ki zo mana Ummi, kin fitowa tayi har sai da ya bar gidan. Duk lokacin da suka kasance tare kowannan su yana mantawa yana da wata matsala. Saura kwana uku daurin auransu, lokacin dangi sun soma zuwa, musamman 'yan Zamfara. Ummi da Abba hankalinsu ya kai kololuwa gurin tashi. Ranar ya ziyarci Zainab wai ko zai samu 'yar nutsuwa. Bayan sun gaisa ta sake mishi gaisuwa, shi kuma ya mata bangajiya, dama tun da aka yi rasuwar bai zo ba. Ya ce "Zainab ina ganin da an gama hayaniyar bikin Ummi zan turo". Tayi shiru bata yanke ma kanta shawarar matsawar ya cikata da zancan Ummi yau kam za su yi ta ta kare. Jin tayi shiru ya ce kina jina Ummi... ta katse shi da sauri, "Ba Ummi nake ba Sorry Zainabu. Ya ci gaba bakina ne ya saba da kiran Ummi, da yake daga ni sai ita ne a gidan. Yanzun haka auran nan da zata yi ina cikin tsananin kewarta...Zainab ta ce ina Idris? Don Allah ni na hakura ka je ka auri Ummi, Abba ya dubeta cikin tsananin mamaki. 38.. Me ki ke fada? Me Salis ya sanar da ke? Ta ce Idris duk wanda ya san so, minti biyar in ya zauna da ku zai san kuna tsananin son junanku kuma ni na tambayi Salis cikinku daya? Ya ce min A'a tun daga nan nasan cewa ku masoya ne, ta nufi hanyar gida, da sauri ya sha gabanta. Zainabu kada muyi haka da ke, wallahi auranki zan yi. Ta ce, "Eh ai na san aurena zaka yi, amma ba sona ka ke ba, don Allah ban hanya sonka in zai yi ajalina ba zan aure ka ba, ya kauce ta wuce, ya bita da kallo har ta shige. Jiki ba karfi yake tuka motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don haka ya nufi dakin. 21. Jiki ba karfi yake tuka motar har ya iso gida, kukan Muhibba ya jiyo don haka ya nufi dakin. Bishira na zaune ta zuba tagumi tunanin danta take, ga Abba sam baya sakar mata fuska, ya ce "Lafiya Mamina take kuka?" Ya shiga ya dauketa Bishira ta ce, "Rigima cee kawai, ya nufi kan madubi inda ya hangi pampers ya dauki guda daya ya nufi dakinshi da ita. Bishira ta biyo shi itama ta zauna a gefen katifa kusa da shi, cikin sanyin murya ta ce, "Abban Walid don Allah kayi hakuri, ya ce me a ka yi? Ta ce, "Gani nayi kana ta fushi, ya ce ni bana fushi wannan kadan kenan ki ka gani daga cikin sakacinki, na tabbata kin fini jin bakin cikin mutuwar yaron nan. Musamman da ki ka zama sanadi, amma don batun yawo ni na daina miki fada, kiyi tayi illa dai zan nemo wadda zata dinga lurar min da gida. Ta ce me ka ke nufi? Ya ce aure zan yi". Ta doki kirji tare da fadin, "Aure?" ya ce, "Eh". Ta soma kuka haba Baban Walid, wane laifi na maka da zaka yanke min irin wannan mummunan hukuncin? Ya ce, "Don Allah fita, ta ce sai ka fada min dalilin yin auranka, ba za ka bar ni in ji da rashin dana ba ko? ta mike an zugo ka an ce kayi aure, to bisimilla. Ta fita ta zari mayafi tayi gidan Umman Bashir. Abba ya rungume 'yarshi ya yi laf a kan katifa shawara ya yanke zai tura magabanshi gidan su Zainabu ba tare da ya sake bi ta kan Zainabun ba. * Umma ta leko dakin Tsohuwa, Ummi kin san na ce miki kizo ki kwashe kayanki daga dakina ki adana su ko? Kin san dai yau duk na nesa za su iso, ki cire wadanda za ki bada. Tsohuwa ta ce, "Suwaiba yarinyar nan ina kallonta jiya bata runtsa ba, sannan da Asubahi a zaune tayi sallah. Umma ta shiga dakin warwas take a kan gado, Umma ta tasheta zaune Ummi ciwon kai ta keya ga jiri da ta ke gani daga zaune. 39.. Umma ta ce taso ki dan watsa ruwa ki karya, mikewar da zata yi sai ta sulale a kasa sumammiya, nan suka dau salati, Toshuwa kam kuka ta saka. Alhaji ya fito wanka kenan ya ji Umma na salati, don haka dakki ya shiga ya dauko waya ya kira Abba lokacin yana kokarin shiga wanka. Alhaji ya kira shi, jin cewa Ummi ba lafiya zari mukullin mota ya fito. Sai da suka kai asibiti sannan ya lura da silifas ya fito da jallabiyarshi ta wanka, Lkitan ma bai zo ba lambarshi suka amsa Abba ya kira shi. Ya duba Ummi sosai da kyar suka samu numfashinta ya dawo, sun daura mata ruwa sannan aka kaita wani daki. Likitan ya ce su zo ofishinsa, Ya kalli Alhaji ya ce, "Gaskiyar magana yarinyar nan tana bukatar kulawarku, ciwonta baya son sakaci. Jininta ya hau ya wuce matakin da zata iya samun mutuwar 6arin jiki. Su Alhaji suka dauki salati,, ya ci gaba da cewa yanzun dai addu'a zamu ci gaba da yi. Allah yasa in ta farfado kada wata matsala ta biyo baya. Sannan ya basu takardar magunguna". Alhaji ne ya amsa don Abba fita yayi ya koma dakin da Ummi ke kwance. Idanu ya zub amata, sam bai san cewa kuka yake ba, sai da Alhaji ya shigo ya dafa shi tare da cewa, "Haba Abba ba girmanka ba ne kuka. Addu'a za ka yi Allah ya bata lafiya". Ya share hawaye. Alhaji don Allah kada ka sanar da Umma abinda Likitan ya ce, Alhajin ya ce ai dama ba zan fada mata ba. Bari in je sai tazo ga takardar maganin inta zo sai ka siyo, ya ciro kudi ya mika ma Abba, Abba ya ce a'a da kudi a jikina. Alhaji ya ce ka amsa ka kashe kudi cikin kwanakin nan ina sane da duk lokacin da na ce kazo ka siyo wani abu sai kawai in gan ka da shi ban da kayan dakin da ka siya musu, Abba ya ce ai ina da shi ne. Bayan fitar Alhaji Abba yaja kujera ya zauna ya zabga tagumi tare da tsura ma Ummi ido, a zuciyarshi fadi yake ALLAH ka tashi yarinyar nan lafiya, Allah kasa kar ko ina na jikinta ya nakasa. Alhaji ya fada wa Umma an ba Ummi gado, don haka ta shirya su wuce. Abba ya tashi ya nufi ofishin Likitan, bayan ya kwankwasa Lokitan ya ba shi izinin shiga, ya same shi yana rubuce-rubuce. Ba tare da ya dago kai ba ya ce, "Zauna sai da ya kai aya rubutunshi sannan ya dago kai ya kalli Abba "Ba dai mai jikin ba ce ko?" Abba ya ce, "a'a ina son ne nima agwada nawa jinin, Likitan ya ce kana jin jikinka ba dadi ne?" Abba ya ce, "Eh da har yasa a dauko fayal din Abba kuma ya tasa ya dauki abin gwaji. Bayan ya gama ya zaunar, ya tsare Abba da ido wai kun yi gadon ciwon nan ne? Abba ya ce, "A'a, Likitan ya ce, "Jininka ya hau, sai dai ba sosai ba. Kila don kai namiji ne kana kokarin kauce ma abubuwa. Zan rubuta maka magani na sati daya, kuma ka dinga kokarin yin bacci a kalla na wa shida kada ka dinga yawan tunani. Kaga kanwar nan taka, sai sa'ar gaske zata tashi lafiya. Ku dai cigaba da addu'a, zata yi bacci na tsawon awa tara ko goma. Ina son daidai lokacin da zata farka ya kasance ta soma dora ido a kan wanda suke shiri ko wanda ta fi so a cikin mahaifanta ko danginta, Abba ya ce "To." Lokacin da ya koma dakin su Umma sun zo har da tsohuwa, nan Abba yake fada musu abinda Likitan ya ce game da farkawa in tayi. Koda bude bakin tsohuwa sai cewa ta yi ai ko dai ba a bar mai sunan Malam ba, tunda an ce wanda suke shiri, don in taga mai sunan Malam karasawa zata yi. * 22. Duk da ana cikin wani hali sai da su Alhaji suka murmusa. Abba kam daure fuska yayi yana kallon Tsohuwa, Umma ta ce, "Ai da ne Tsohuwa. Yanzun shiri suke tunda ta daina rashin jinta". Likitan ya shigo ya sake musu bayani kamar yadda ya yi ma Abba, sannan ya ce su bata guri kada zantukansu ya farkar da ita a samu matsala. Suka fito, Umma ta ce da Abba ya tafi gurin aikinsa, su Alhaji ma suka fita tare da Abba. Fati ta je gidansu Sahabi dan uwansa yana kankarar rake a kofar gida, inda yake saidawa ta tambayi Sahabi. Yaron ya ce mata ya ffita, ta ce To in yazo kaa ce masa Ummi tana asibiti ba lafiya, an bata gado. Karfe uku ya iso asibitin hankali a tashe, sun gaisa da Umma ta raka shi dakin, hankalinshi ya tashi da ganin Amaryarshi kwance a gadon. Abba kam yana gurin aikinshi amma hankalinshi na Asibiti, su Alhaji ma duk nan suka nufo, Abba sai da yayi magriba sannan ya shigo asibitin. Jikinshi babu karfi, bai matsa sai yaga farkawar Ummi ba ne saboda yasan da gaske ba shi ne ya dace idanunta su soma arba da shi ba, ya samu su Umma da su Alhaji. Sahabi da abokansa duk suna gurin, ya gaida su tare da tambayar ko ta farka? Umma ta ce har yanzun dai shiru. Ya nufi cikin gurin Likitan suka gaisa, ya ce Likita har yanzu ba ta farka ba. Suka jera zuwa dakin, Likiran yana cewa cikin wannan dan takin zata farka, In sha Allahu. Sun shiga takin tana dan motsi suka nufi gadon Abba ya ce Ummi. Likitan ya daga mishi hannu alamar yayi shiru ita kam daidai lokacin mafarkin Abba take wai suna tafiya ya rike mata hannu sai ga Sahabi. Yana zuwa ya kama hannunta tana tirjrewa, sai janta yake zai fita da ita, Abba yana tsaye yana kallonsu. Ita kuma sai kiran "Ya Abba! Ya Abba!! Take yi. Likitan ya kara kunne gurin bakinta ya dagowa yayi ya dube shi. "Waye Yaya Abba?" Abba ya ce ni ne. Liitan ya ce, matsa kusa, ya kama hannunta. Ummi. A hankali ta bude ido. Ya Abba! Ya abba, zan sha ruwa, ya ce to ya kalli likitan za ta sha ruwa, Likitan ya ce, "A'a bari ta dan kara warwarewa tukunna. Likitan ya kama kafafunta ya dan matsa, sannu ko. Ta kalle shi, kin ji zafi? Bata yi magana ba ya dauki allira ya 6are ya dan soka mata a tafin kafa ta ja kafafunta alamun taji zafi. Ta yunkura zata tashi, Ya abba zan tashi, ya tayar da ita zaune. "Likitan ya ce Alhamdulillah, Abba ya kalli likitan, ba matsala kenan? Ya ce, Ina zaton haka insha Allah, Abba ya ce "Alhamdulillahi, ya jinginata da jikinshi, sannu Ummina. 41.... Alhaji ya shigo yana cewa, "Ina Abba ne?" ya ganta zaune a'a ta farka ne? ya kama hannunta sannu uwata. Ta kalle shi. "Ina Ummata?" ya ce, "Bari in kira miki ita". Yaje ya sanar da su, sun shigo da murna. Sahabi ya iso gaban gadon. "Sannu Ummi". Ta kalle shi sai ta kwantar da kanta a kafadar Abba, "Ya Abba ina son in wanke bakina". Ya ce, "To bari in siyo miki Maclean din". Ta ce, "A'a kada kaje". Ya gyara zama "To shi kenan." Umma ta ce, "Me ta ke so?" Abba ya ce "Baki zata wanke". Umma ta ce "Ai nazo mata da maclean da burushin nata, don nasan ita gwanar wanke baki ce". Nurse ta kawo wani dan kwano na silba Ummi ta wanke baki da taimakon Abba. Likitan ya ce, a bata tea mara zafi sosai, sannan a bata magani. Takaici dan'kam a zuciyar Sahabi, irin wannan shigewa da Abba ke matar da zai aura tayi yawa. Kai shi fa wannan Yaya Abban bai masa ba ma, don yana daure mishi fuska ko gaida shi yayi d kyar yake amsawa. Shi fa tun ranar da a ka ce mishi Ummi ba cikinsu daya da Abba ba ya ji ya tsane shi. Umma ta ce, "Abba an kira Isha'i. Sahabi kaje kai ma ka huta yaran nan tun tuni ya ke nan". Abba ya kalle shi, "Ya kamata ka tafi haka ko?" ya kalli Ummi sannan ya dan rusuna "Sannu Ummi". Ta ce, "Yauwa" "Innata ta ce in gaida ki da jiki, ni zan tafi sai da safe. Me zan kawo miki?" Abba ya dube shi a kule., "Don Allah Malam kaje ba za ta iya cin wani abu yanzun ba". Umma ta ce, "Abba". Ya kale ta, sai ta girgiza mishi kai alamun ya bari. Sahabi jiki a sanyaye ya fice tare da cewa "Umma sai da safe". Ta ce, "To Sahabi, ka gaida Innar taka". Da ya fita ta kalli Abba "Wannan ba halinka ba ne kada in kuma gani". Ya ce "To Umma". 23. Su Alhaji sun yanke shawarar daga auran Ummi a darua na Fati kawai, ita sati biyu masu zuwa sannan ta murmure sai a daura nata. Gidan su Sahabi sun ji haushi musamman Innarshi, sun kashe dan abinda suka tattala don bikin amma gashi an daga, su kam da an daura auren in ta murmure sai a yi bikin. Sahabi ya shigo gidan ranshi a 6ace, ya kalli Mahaifiyarshi, "Inna wai sun ki a dauram?" Ta ce, "Sun ki, dama ai gaddamar dan yau ce. Ban da shegiyar gaddama ga 'ya can da a ka baka a daura ka gaddame, to yanzun ina ranar abin da aka mana? Gida duk dangi sun cika amma wai a daga biki, mu kuma karamin karfi ne da mu, bare mu ce nan da sati biyu zamu sake kashe kudi". Sahabi ya tuna abinda Abba ya masa a asibiti, shi ne dalilin da bai sake zuwa asibitin ba, yaja tsaki. "Kin san Allah Inna ni kaina sai yanzun nake jin haushin kaina da na ki amincewa da Badariyya. Mu zuba musu idanu in za su sake kawo mana cikas sai kawai in koma gurin Badariyya." Inna ta ce, "In da tun jiya kamin zancan nan da tuni yau ba a fasa daura auranka ba an ma da Badariyya". Ya ce, "Kiyi hakuri Inna mu ga nufin su". * 42... An sha shagalin bikin Fati kuma an kaita gidanta. Ummi jiki Alhamdulillah, Abba kullum in zai je aiki sai ya biya. Haka nan in ya dawo gida wanka kawai zai yi ya tafi, wataran sai goma ko sha daya. Abokanshi suna ta zuba duba Ummi, ita kanta da lokacin zuwanshi ya karato ta dinga kallon agogo ke nan tana kallon kofa. A zaman asibitin nan Umma ta gama karantar su tsaf., matukar son juna suke yi, sai dai taji takaicin da sai yanzun sonsu ga juna ya bayyana. Lokacin da ya kasance an riga an bada Ummi ga wani sai dai ta ci gaba da addu'a Allah yayi za6i na alkairi. Bashir yayi murna da fasa auran Ummi, dama a fasa gaba daya. Yana fitowa dakinshi ya ji Ummarsu tana cewa, "Kin san Allah Tasalla, uwar yaron nan da zai auri Ummi zata ga bakin ciki, don mallake mata da za su yi. Tana ji tana gani sai yanda suka yi da shi. Kuma ba yanda zata yi sai Allah ya isa". Tasalla ta ce "Ban da halin mutanan yanzun ba da sai na fada mata ba. Kin san makotanmu ne ta baya, gashi su ba karfi ba. Sahabin ne fa ke rike da gidan, kin san shine Babban a gidan". Sahura ta ce, "Don Allah Tasalla ki taimaka ki fada musu, don ko in har aka yi auran nan in suna cin abinci sau uku ne a rana, to za su koma dau daya". Tasalla ta ce "Ai ko zanje". Tana fita Bashir ya dawo kusa da Ummarsu ya ce, "Umma dama da kanki ki ka je, saboda za su fi yarda tunda sun ga ke kina da danganta da gidan". Ta ce, "To in Babanku ya ji fa?" Ya ce "Umma ai in kin

Chapter 13 of 24