Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fada musu ai kwa6ar su za ki yi, sannan kada kije a kan lokaci, kije ana gobe daurin auren". Ta ce, "Saboda me?" Ya ce, "Saboda su Alhaji Babban suji haushin rashin fada musu da wuri". Ta ce, "Haka za a yi, kuma in an fasa Malamai zan shiga don a hanata auran ma kwata-kwata". Ya ce, "Kada kije wurin Malamai yanzun tukun". Ta ce. "Ai dama sai an natsa". * Abba ya fito cikin suit bakake, yayi kyau matuka hatta takalminshi sawu ciki baki ne, tamkar wani black America. Igiyar wuyan ta zauna tsam, sai kamshi yake. Dakin Bishira ya nufa ya daga labule, ta dago ta kalle shi yayi matukar birgeta. Tana alfahari da shi matsayin mijinta, ya ce "Kin shirya?" ta ce,, "Zuwa ina?' Ya ce, "A'a, jiya fa na sanar da ke ki shirya da wuri zamu je asibiti ki gaida Ummi". Ta watso mishi wani kallo uku saura kwata, tare da cewa "Ko garin nan ba a sanyi ba zan fita gaida wata can Ummi ba bare da sanyin nan." Ya ce, "Dalili ta mike tsaye "Ciwo bai kai mutuwa ba, da mutuwa ya yi tazo ta min gaisuwa?" Takaici ya turnu'ke Abba, da yake sarkin dankara magana ne, sai ya ce "To ita ta kashe shi da zata miki gaisuwa?" Ta kule da bakin ciki ta zabga mishi harara "To ai kasan ni na dora mata ciwon, don haka dole in je gaisheta." Ya ja tsaki tare da cewa, ballahaza wadda bata san mutuncin mijin auranta ba". Ya yakice labulen ya wuce yana jiyo ta tana cewa, "Ba dai za ni ba ko me za ka ce". Ranshi a 6ace ya isa asibitin, Ummi na zaune kan gado ta kosa Abbanta yazo, ko karyawa ta kasa yi, yana sallama suka hada ido. Nan ta ke ya ji ya manta da duk wani bakin ciki da ya taho da shi, ya isa bakin gadon fuskarshi dauke da murmushi. Itama murmushin take yi, ya ce. "Ummi ya ya jikin?" Ta ce "da sauki". Ya Abba kayi kyau sai ka ce Manajan Banki". Umma ta saka dariya, shi ma ya yi 'yar dariya, "To ko bankin zan koma?" Ta ce, "A'a kafi kyau da dan jaridanka Ya Abba, balle in kana turancinn nan a labarai". Ya lakuci kumatunta "Ko kwanwata?" Ya juya ya gaida Umma, Umma ta ce "Ka zo katafi gurin aikinka fa". Ya ce, "Umma sai sha daya yau zanje gurin aiki". Ta ce, "Ni na ma kosa a sallame mu". Abba ya ce "Ai kila a sallame ku yau. Likitan ya shigo ne?" Suka ce "A'a. Suna cikin karyawa Likita ya shigo ya same su, ya kuma kafa mata dokokin daina tunani, daina shiga duk wani abu da zai sa ta cikin damuwa. Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 6 ZURFIN CIKI book 3 part 6 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:31 Rage shan gishiri tare da samun isassen bacci, ya kuma gargadi su Umma su dinga nisantar 6acin ranta. 26. 43... ABBA Ya kwaso su ya maida su gida, cikin satin Ummi ta murmure. Sahabi na zuwa sai dai da sun gaisa yake tafiya. Mahaifiyyarshi ma tazo, amma Bishira da Sahura ko le'ke, Bashir ma yana ta sintirin zuwa. Ganin haka Alhaji ya ci gaba da shirin biki, mutan kauye dai dama an ce kada su dawo, Ummi dai bata maida hankali ga komai ba. Ta ce ma Umma zata je gidan Fati, Umma ta ce To sai ki je gurin Sahura ta kwatanta miki. Abba ya same su suna zancen, don haka ya ce ta shirya zai kaita ya ajiyeta in ya tashi aiki sai yaje ya daukota. Yanda ta samu Fati da Angonta ana ta ji da juna abin ya tsokanota, sai dai ta kasa ganin dacewar soyayyar da Sahabi. Da mijin Fati ya fita Ummi ta ce, "Oh, Fati cikin kwana takwas dubi yanda ki ka yi kyau". Fati ta ce, "Amma ban rame ba?" Ummi ta ce "Eh to, kin dan rairaye". Fati ta ce, "Kai ai dole, gaskiya ina koduwa, wallahi ba ya barina in huta". Ummi ta ce, "Da me?" Fati ta ce, "Dallacan ki gane mana". Ummi ta ce, "Wai da me? Allah ban gane ba". Fati ta ce, "Ai ke sokuwa ce, gurin kwanciya mana. Ummarmu ta samu ta dirka min kayan sha na mata, gashi nan nazo ina ta shan wuya". Ummi ta zaro ido, "Da wahala ne?" Fati ta ce, "Tab, ai kin kusa kema za ki ji". Tsoro ya cika Ummi. Ta ce, "Zan ce ma Umma ni dai kada ta bani wannan kayan matan". Fati ta yi ta dariya tare da cewa, "Ke yanzun sai ki iya wa Ummanku wannan zance?" Ummi ta ce, "Sosai ma". Fati ta ce, "Ko ba ki sha ba yarinya sai kin sha zafi, ana kawo ni ko dan kwana daya bai raga min ba". Ummi dai ido ya raina fata. Koda Abba ya zo daukarta duk ta damu. ** ** 44..... Tasalla ta samu uwar Sahabi ta fada mata cewa, in dole ne sai danta ya auri Ummi, to ta amso mishi karya tambaya. Don kuwa wata rana sai ta taso ta ganshi ko da a hanya ne ta rasa samun hakan. Inna ta tsure ta ce, sai a fasa babu dole, ita dama tuni abin ya sire mata. Ana gobe daurin aure gidan su Ummi suna ta shiri Ummi na ta kuka, wannan karon ba Umma ba har Alhaji da Tsohuwa sun kule da wannan iskancin da Ummi ke yi. Alhaji ya ce "Ki sani uwata, wannan karon ko kin tsokalo ciwon nan naki auren nan dole ne babu fashi. Idan yaso jinin naki ya tashi ya ta6o sama ba zan kuma daga auran nan ba". Lokacin da Alhaji ke wannan fadan Abba yana gidan yana zaune dakin Umma yayin da Ummi ke gefanshi tana rusa kuka. Umma ta shigo ya ce "Umma don Allah ki lallashi Alhaji a dan daga bikin nan mana". Abba bai ta6a ganin ranar da Umma tayi mishi irin wannan kallon da ta masa yanzu ba tun tasowarshi. Sannan bata ta6a daka masa irin wannan tsawar ba ta ce "Kai! Abba shiga taitayinka, me yasa yanzun ka canza, ko kai ba za ka hukunta Ummi ba da irin wannan yaro da hankalin da take mana? Don gidansu kanta a ka soma aure? To wannan karon ba za a daga bikin ba, in yaso ta mutu, ke ko mutuwa ki ka yi gawarki can gidan mijinki za a je a miki sutura". Tsohuwa ma daga can tana yo nata fadan tare da dauko tarihe-tarihen da tana cewa, "Lokacinsu kaza-kaza". Abba ya sake kallon Ummi, matsanancin kukan da take yi yana daga mishi hankali, ya mike tare da kama hannunta, "Zo muje". Ya bude mazaunin direba ya ce ta shiga, shi ma ya koma ya shiga motar ya tasheta, tafiya kawai suke ba tare da ya san in da suka dosa ba. Kukan Ummi na tsikararshi, sun yi tafiya mai nisa sannan ya tsaya a hankali cikin wata irin murya, ya ce "Ummi ki fada min gaskiya kina son Sahabi?" Ta dago ta dube shi, "Ni bana son shi". "To me yasa ki ka fito da shi?" cikin dasasshiyar murya ta ce, "Ba ni da yanda zan yi ne, saboda in ban za6i Sahabi ba za a bani Bashir". Ya ce, "To ke yanzun fada min wa ki ke so?" Gabanshi ya shiga faduwa don tsoron kada kunnenshi ya ji mishi ta ce wani ba shi ba. Ta kuro shi da ido tamkar ta ce kai, amma sai take ganin in ta fada mishi haka dan shirin da suka soma yanzun zai wargaje, kila ma sai ya hada mata da duka. Wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatunta, daidai lokacin da yake cewa "Ko dan digo ki ka ji son ko waye a ranki kada ki rufe min". 45... Ta girgiza kai "Ba na son kowa Ya Abba". Cikin wani irin yanayi ya dubeta, "Shi kenan, sai ki je ki hakura da Sahabin a sannun kin so shi". Cikin kuka ta ce, "Ya Abba Allah ni bana son shi, kai to ka hada ni da ko waye mana". Ranshi 6ace ya dubeta cikin tsawa ya ce, "Ki rufa min baki tunda ba ki ta6a son kowa ba ki zauna da wanda ki ka za6i zama da shi. In da kina son wani ne to da sai in cije in tunkari su Alhaji, tunda kuwa babu sai in ce musu me?" Ya fada mota, ya koma kofar gidan. Koda ya tsaya tafi minti uku sannan ta fito, yana kallonta maimakon ya wuce gida sai kawai ya nufi gidan Maman Iman makociyarsu da suke shiri da ita. Shima kanshi na kan sitiyarin motar har ttsawon shudewar wasu dakiku, sannan ya nufi gida. 27. Misalin karfe tara Umman Bashir ta rangada sallama a tsakar gidan, Innar su Sahabi ta amsa tare da fadin "Shigo". Sahura ta shiga tana tambayar "Ba kowa dai ko?" Inna ta ce "Shigo mu kadai ne". Bayan sun gaisa ta ce "Ba ki sanni ba ko?" Inna ta ce, "Eh." Sahura ta ce, "To ni dai tsakani ga Allah zuwa nayi in ba ki shawara bisa ga yarinyar da danki zai aura. Tsakani ga Allah yarinyar ba ta da mutunci, sannan iyayenta za su mallake miki da, don ni kaina ya faru da ni". Sahura don makirci ta soma rishin kuka. "Dana maigidana ya ba su riko, ina sheda miki wannan zance 'yar uwa yanzun tsakanina da shi sai ido, sun makkale shi komai shi yake musu, ni ko da nayi wahalar ciki da nakuda sai na tashi a banza. To da yake an ce ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, shi ne nazo in sanar da ke. Amma in kin ji haushi kiyi hakuri". Ta yunkura zata mike. 46... Inna ta ce, "Zauna 'yar uwa, na gode. Nima fa tuni auran nan ya fice min a rai, dama da naga shi Sahabin ya dage ne sai kuma suka aiko gobe azo za a daura aure sai na hakura". Kafiin Sahura tayi magana sai Sahabi ya doka sallama, Inna ta ce "Yauwa zo nan". Ya nufo ta "Zauna kaji ma kunnenka". Ya rage tsawo, Inna ta ce "Baiwar Allah ya ki ka ce?" Nan Sahura ta soma zuga sharri, ta kara da cewa "Yaro ina ga ma za ka san dan nawa da suke riko Abba a ke ce masa". Cikin saurin baki ya ce, "Na san shi". Ta ce, "To dana ne da asiri suka amshe min shi, sai dai Allah ya isa". Ya tuna irin halayen da Abban ke nuna mishi. Yaa jinjina kai, sannan ya dubi mahaifiyarshi "Inna to da Kawu yayo binciken halayan iyayenta ai ana ta yabon halinsu". Inna ta ce, "Kin ji shi ko? To bari kaji, kwanaki ma Tasalla da ke bayan layin nan tazo ta fadan irin wannan matsalar ban kama ba ne don na asanta da shegiyar karya. To kuwa an yi biyu ba zan bari ai na uku ba, don haka a daran ta tabbatar ma da danta an fasa gobe ya wuce gurin Badariyya a daura, su kuma in sun ji shiru sa ba wani can". Cike da murna Sahura ta koma gida. * Maman Iman tayi lallashin duniya amma Ummi ta ki yin shiru, ga zazza6i tamkar wuta a jikinta. Sai kusan sha dayan dare sannan Maman Iman ta rako ta gida, lokacin Umma tana ta neman layin Abba a kashe. Ta ce, "A'a sun dawo ne yanzun ni ke neman Abba in ji suna ina ne?" Maman Iman ta ce, "Tun dazu tana gidanmu zazza6i da ya rufe Ummin, na bata magani ta 'ki sha". 47... Umma ta ce "Rabu da ita kar Allah yasa tasha, aure dai gobe babu fashim dubi irin yanda a ka sa gidan su yaron nan wancan karon suka kashe kudi gurin yin girki da sauransu ba a yi bikin nan ba. Yanzun a kuma dagawa daga lokacin da muka samu?" Maman Iman ta ce, "Ai ba zai yiwu ba, sai dai a bi ta da lallashi". Umma ta ce, "Mun daina lallashinta tunda ko mun lallasheta aikin banza ne". Maman Iman ta ce, "To Allah ya kaimu gobem bari in shiga gida sai mun shigo aiki da safe". Umma ta ce, "To sai da safe". Ummi tana shiga dakin Umma taga baki kwakkwance, ta ce a ranta "Mayu, don kalata sai da wasu suka dada zuwa". Tana fushi da tsohuwa amma duk da haka dakin ta nufa, ta kwanta a bayanta don ita tuni tayi bacci. Nishin kukanta ya farkar da Tsohuwar, kala bata ce mata ba, sai sauka tayi ta shimfida a kasa ta kwanta, sannan ta ce "Aniyarki ta biki Takwara". Wannan dare gurin Ummi da Abba wani dare ne mai cike da bakin ciki da tashin hankali, ko Sarkin sata bacci ranar bai samu galaba gare su ba. Dukkan su a kan kunnansu aka kira sallar farko, Abba ya mike cikin rangaji, jin jikinshi yake yi tamkar iska ta dauke shi saboda rashin karfi. Ruwa ya diba ya watsa, wanka sannan yayo alwala don yin nafila, addu'a yake Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi a gare shi. Da ya dawo Masallaci kwanciya yayi amma baccin ya ki bai fita ba sai kusan takwas. Koda yaga Bishira zaune a tsakar gida tana karatun littafin sam bai ji haushin rashin zuwanta gidan su Umma ba. Nashi ganin duk wanda yaje tamkar yana murna ne da rasa Umminshi da yayi, ita kuwa da gadara ta fito don ya ji haushi, bata je ba yana son sanin halin da Ummi take ciki amma ba ya ra'ayin zuwa gidan su Umma. Shagonshi ya bude ya shiga ya dan zauna har zuwa tara, yana kallon lokacin da Jama'a suka yi ta dafifin shiga layinsu don halartar daurin auran. Kurum sai ya samu kansa da tare dan Aca6a ya hau ba tare da ya shaida masa inda za su ba. Koda dan Aca6an ya tambaye shi ce masa ya yi mu je. 48.... Ita ko Ummi ranar zaune tayi sallah ta koma ta kwanta, duk kaikawon ai da 'yan shewe-shewen da jama'a dangi da makota tana jin su. Sai dai makoshinta ya bushe ga zufa da ta rufeta, duk da yanayin ba na zafi ba ne. Karfe goma daidai shi ne lokacin daurin auran, layin ya dinke da jama'a, Alhaji ranshi a dame don bai ga Abba ba. Ya kalli Alhaji Karami, "Ina Abba ne?" Alhaji Karami ya ce, "Abokan aikinshi ga su can sun zo ba a ganshi ba son daukan daurin auran". Alhaji ya ce, "Su dauka mana nasan yana nan tafe". Har sha daya ana ta jiran 'yan gidan Ango shiru, su Alhaji suka tashi dan aike gidan don a ce ana jiran wakilan ango. Amma sai a ka dawo musu da sako wai sun fasa, kalmar da ta rikita Alhaji ta tashi hankalinsa. Ga jama'a an tara, Alhaji Karami ya ce wadannan akwai kananan mutane." Daidai lokacin da muryar wani Maroki ta ratso dodon kunnuwansu da cewa, "Alhaji ku hanzarta Jama'a sun gaji da jira". Alhaji ya dubi Alhaji Karami, "Aminu a daura da Bashir". Alhaji Karami yayi shiru, can ya ce "A daura da Abba". Alhaji Babba ya ce, "Ina zuwa". Ya fito daga dakin Abba na da inda suke yin shawarar, ya ratsa mutane ya ce a yi masa magana da Suwaiba. Umma ta fito daga kicin ta same shi a dakinsa yana tsaye yana kai-kawo ta ce lafia? Ya ce Gidan ango ne shiru, an bisu sun ce sun fasa. To shi ne na ce me zai hana a daura da da Bashir? 49... Umma ta ce a daura da Abba. Ya ce, "Haka ma Aminu ya ce. To ni ban ga Abban ba ma, amma bari muje Allah yasa hakan shi ne mafi alkairi". Take a nan a ka daura auren, Habiba da Idris Alhaji Babba ya kirgo sadaki ya mika. Alhaji Karami Waliyinta ya amsa, mutane na ta al'ajabin yanda lamarin ya sauya. Umman Bashir kuwa Bashir din ne ya shiga gidan hankali a tashe yana fada mata cewa da Abba a ka daura. Nan ko ta hau bala'i da zage- zage. Ummi ko tunda ta jiyo guda na alamta mata an daura aure, sai ta birkice ta shiga kowa da numfashinta. Fati da ke kusa da ita tana lallaminta ita ce ta kwala ihu, ba shiri aka yi asibiti da Amarya. Fati ta shiga gidansu da kuka, nan ta taras Ummansu tana bala'i sai lokacin ta ji da Abba a ka daura. Ta ce da Ummar su to menen ba shi ke nan ba? Umma ta hau zaginta tare da cewa, kar ki ga kin yi aure sai in miki shegen duka, Fati dai ta fice ta bar gidan. Sam Umma bata ji dar da ciwon Ummi ba, wannan karon don haka ma bata bi su Asibiti ba, da kanwarta Saratu a ka tafi. Likitan yayi ta fada lokacin da yake yi mata allurai, a kuma bata gado Umma ci gaba tayi da kula da bakinta. Yayin da zuciyarta take fara kar, ta sani kuma tayi Imani Allah ba ya tozarta addu'ar bawansa, matsawar bawan yayi hakuri tare da dogewa. Haka nan in baka samu biyan bukatarka nan duniya ba lallai gobe kiyama zaka tarar da abinka. Ta jima tana rokon Allah yasa 'ya'yan nata biyu su zam miji da mata su haifa mata jikoki masu albarka. Suma su Alhaji suna ta sallamar baki sai dai yanzun ba wanda ya damu ya gani irin Abba. Fatanshi Allah yasa Abban yayi farin ciki da wannan hukunci da suka yanke. Salis kuwa burinshi ya zama shi ne mutum na farko da zai wa Abba wannan albishir sai dai ya kira layin Abba sama da sau hamsim bai daga ba. Abinda bai sani ba shi Abba ma gida ya bar wayar, haka suka gama dauke-daukensu yayi hira da Jama'a da kuma iyayen Ango da Amarya don jin ta bakinsu a kan yanda auren ya juye zuwa na zumunci. Haka nan suka tafi ya samu abin sawa a Taskar labarai, burinshi yanzu shi ne ya je ya nemo angon. 28 50.....Abba kam kofar dan Agundi ya yada zango gidan su Mansir abokinsu, shi ne kurum cikin abokan Abba da bai yi aure ba. Yana isa kofar gidan Mansur na fitowa za shi daurin auren, wani dan layinsu a Gwammaja suka gaisa. Abba ya ce "Bari in dan kwanta a dakinka". Mansur cikin mamaki ya ce, Lafiya? Abba ya ce lafiya lau. Yana kwance dakin Mansur idanunshi suna kallon agogo, zuciyarshi tana raya yanzun abar sonshi ta zama matar Sahabi. Sai dai bai san dalilin da bugawar agogon karfe sha daya daidai tazo gwame da bugawar zuciyarshi ba. Zuciyarshi ta fada mishi cewa wannan alamu ne na an kammala daurin auren. Wasu hawaye ne suka biyo ta gefen idanunshi suna sauka a kan filon. Yini zur yana dakin in lokacin sallah yayi sai ya fito kofar dakin yayi alwala har duhun Magriba ya gabato. Ya fito tare da kulle dakin, don Mansur bai dawo ba, kuma dama ya ce ba zai dawo da wuri ba. Gidan nashi ba kowa lokacin da ya shiga, kai tsaye dakinshi ya wuce, ban da idanunshi da suka kai kan wayarshi ya manta ma yana mallakinta. Ya kai hannu ya dauka, bai ji mamakin yawan missed calls din da ya gani ba, kiran Salis ya sake shigowa. A kasale ya daga, muryar Salis ta ratsa dodon kunnanshi, fadi yake yana maimaitawa Ango- Ango. Abba cikin sanyin murya ya ce "Salis ya haramta a gare ka ka zolaye ni a halin da nake ciki. Sanin kanka kai kadai ne kasan yanayin da nake ciki". Salis cikin zumudi ya ce, "Kana nufin ba ka sani ba?" Abba ya ce, "Me?" Salis ya ce "To bani goron albishir in sanar da kai". Abba ya ce, "Don Allah Salis kada ka min karya". Salis ya ce, "Ina rantsuwa da wanda ya yi mu Ummi matarka ce, da kai a ka daura. Ina ka shige lokacin da al'amarin ya canza salo?" Abba ya mike zumbur. "Ka fa rantse Salis!" cikin dariya Salis ya ce, "Wai har yanzun ba ka sani ba? To ka aje min goron albishir dina". Abba yasa hannunshi a baki ya gatsa, zafin da ya ji ne ya tabbatar da mishi da ba mafarki yake ba. 51... Ai sai ya katse wayar ya zube yayi sujjada ya fita tsakar gida yana furta "Alhamdulillah." Ruwa yaja ya watsa ma jikinshim sannan ya yi alwala. Sabuwar shadda ya saka kalar kunkumadi, ya fesa turare sama da kala hudu. Hula da takalmin bakake, ya nufi Masallaci, daga can za shi gidan su Umma don jin karin bayani. Bayan sun idar da Sallah, mutane suka yi ta masa murna, nan ya hadu da su Alhaji kawai yau sai ya samu kansa da kunyar Alhajin. Alhaji ya ce, "Ubana ina ka shige duk yau?" Ya rasa me zai ce, sai in-ina "Am...na kwanta ne bana jin dadi". Alhaji yayi 'yar dariya, "Kai dai ka ce kana taya kanwarka fushi don mun ce ba zamu daga aure ba, to ba mu daga ba amma Allah cikin ikonsa ya sauya lamarin". Abba tamkar bai san komai ba, ya ce "Alhaji me kuma ya faru?" Alhaji Karami ya karaso gurin su yana cewa, "Kai Abba ina ka shige ne?" Abba ya dube shi "Nan dan Agundi na shiga". Alhaji ya ce, "Oho, shi yasa aka yi ta nemanka. To ka ji kuma yadda lamari ya sauya ko?" Alhaji Babba ya amsa tare da cewa, "Shi ne nake massa bayani, wato Abba iyayen yaron nan Sahabi muka yi ta jiransu su zo gurin daurin aure, wai ashe su sun fasa. Amma ba su shaida mana ba har bin su fa nasa aka yi, gashi mun tara jama'a kawai sai Aminu da Ummanka suka ce a daura da kai, da ni na ce a daura da Bashir". Dadi ya lullu6e Abba irin wanda bai ta6a ji ba, Alhaji ya ci gaba da cewa, kayi hakuri mun kara maka nauyi ba tare da mun ji ra'ayinka ba". Abba cikin matukar murna ya ce, "Haba, ai ko ba 'yar uwata ba ku ka daura min aure da ita zan aminta bare jinina. Nagode". Sun ji mamakin yanda Abba yayi murna, duk da sun san biyayya irin tashi ba zai 'ki ba, tare suka rankaya gidan su Umman, so kurum yake yaga Ummi. Ba mutane sosai, don haka har ciki ya kutsa, sai dai suna hada ido da Umma sai ya ji nauyinta, ta fada da fara'a. "Ina ka shige Abba?" Yayi dan murmushi, ta ci gaba "Sai kuma ka ji yanda abu ya kasance?" Ya ce, "Na ji Umma, Allah yasa haka shi ne alkairi". Ta ce, "Amin, Insha Allahu". Tamkar ya tambayi ina Ummin, amma ya kasa. Umma ta ce "A baka abinci ko?" sai lokacin ya tuna da batun abinci, amma baya gabanshi, ya ce "Na koshi Umma". Ta ce, "To ga na 'yan asibiti can in kayi isha'i". Da sauri ya ce "Wa ke asibiti kuma?" Ta ce, "Ummi ce, ko 'yan daurin auran ba su watse ba don ka ji yarintar nan ta hau farin suma don haushi ko leka su ban yi ba. Tana can it da Saratu sai Tsohuwa da ta matsa yanzun Alhaji Karami ya kai ta". Jikin Abba ya yi sanyi, kenan tsabar rashin sonshi ne ya saka Ummi suma? Ya ce Umma bani abincin asibitin. Sai da yaje gidanshi ya dauko dan mukullin motar, a zuciyarshi yana tambayar kanshi ina kuma Bishira tayi ne? Zai bude motar kenan muryar Bashir ta dakar da shi, "Kaci nasarar samun furen zuciyata, amma ka sani ka kulla abota da rashin zaman lafiya a novels / ZURFIN CIKI book 3 part 7 ZURFIN CIKI book 3 part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:33 kulla abota da rashin zaman lafiya a gidanka". * 52..A fusace abba ya dubeshi"xansa yan sanda su rufe min kai inhar zaka cigaba da kiran matata da furen zuciyarka,rashin zaman lfy kake cewa? An dade ba'ayi yaki abgdn ba kullum,bashir yace oho dai ni zanta zuga umma abba yaja tsaki tareda shigewa motarshi. Bashir yashiga gdnsu inda su ummanshi dasu bishirabke zaune jugum jugum tamkar masu zaman makoki,bishira tabi bashir da kallo lkcn dayace ga ya abba ya can a waje yashiga mota ya kure wanka,kila ma asibiti zaije ana fada maku yanaso kuna wani tilasta shi akayi,bishira cikin dasahhshiyar murya tace aiko da bala'i don ko bazan yarda ba,umman bashir tace sha kutuminki bishira,barni dasu zan maganinsu, bishira tafita fuu,amma saidai. Kafin ta isa gurin motar tuni ya, Cilla yabar mata hayaki. Da innna saratu kanwar umma ya soma cin karo a asibitun suka gaisa,tace ashe kuma haka abu ya zama? Yace eh"nima dana dawo dazu nasamu lbrin,tace Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,abba yace ameen inna,ya mai jikin? Tace dasauki,yace bacci take? Tace a'a ta farka tun kusan karfe uku,koda fatima ta fada mata yanda abubuwa zuka zama,tayita yan koke kokenta,gaban abba yafadi****tabbas ummi ba son shi take ba inba hka ba meye na kuka? Ya kalli inna bari in karasa,tace to kaje tshuwa na ciki,a ranshi yace jaraba road,yasan dai ko yane sai tshuwa tayi mishi surutu,yana tura kofar tareda salama suka hada ido da ummi,sun kure juna da kallo,kowanne nason ya fahimci ya dan uwansa yadauki abin"tshuwa ta katse su dacewa to zakin fama sai ynz kaga daman zuwa? Ya dubeta eh" ai eh ace? To me kikeso ince,tace to madalla ai na dade da sanin halinka,kuma da ace iyayenku sunyi shawara dani lallai da baza suyi wanna hadin ba Domin na tabbata kai zaka karasa takwara don baka kaunarta, haushi ya cika abba abba yana kallon tsohuwa yana tuna amsar data dace da ita, ummi kuwa tsura mishi ido tayi tana son jin me zaice,yace kamar kin sani,tace ahaf shiyasa tausan yar nan kebani tausayi, ta soma matsar ido,yace nima yakamata. ki tausayamin tnda cusa min ita akayi,ummi takoma ta kwanta lakwas tareda hakikancewabl kalaman abba sako ne zuwa gareta,matar cushe kuma bata daraja,to inaso kasan wani abu guda,duk randa naji wani abu daidai da wulakanci, toba kaiba har iyayenka saisun san naje makura. 52..Dazun nake gaya masu basun hada kai sun kulla auren nan ba,duk randa suka kuskura sukazo min da batun warwareshi saina basu mamaki,abba ya tabe baki tareda kallon ummi wadda takasa jurewa tashiga rera kuka,ya isa gaban gadon,"jikin ne ummi? Tayi shuru,kinci abinci? Nan ma ta share,sai kurum ya nufi wurin likitan zuciyarshi na kuna bako shakka kukan kin shi ummi keyi,sun zo da likita ya shiga yimata fadan kukan da takeyi,a cewar likitan kukan illa ne ga lafiyarta,tshuwa ta kalli likita dan nan dole ta koka a dauke ka ahadaka da wanda baya kaunarka"abba cikin takaici yace subhanallla! Don Allah tshuwa kibarni inji da abinda

Chapter 14 of 24