Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata gareni So, Ummi baya raina abinda yake so da nayi zaton zubar da kima ne in furta maki kalmar so musammam in na tuna ke baki soma, zurfin a so bashida wani amfani don na sha wahala.Ba zan Qara boye dimbin son da nike maki ba Ummi ko gaban wa zan nuna kina jina matsala? Ummi wadda ke zaton mafarki take sai taji bakinta yana furta wayyo dadi Ya Allah kada ka farkar dani in har bacci nike Abba yace ciji yatsanki zakiji zafi Ummi nine Abban ki mai sonki wanda ya reneki tun kina zanen gobe. Hawaye suka soma zubo mata cikin muryar kuka tace Ya Abba da gaske kana sona? Nafi zaton tausayina yasa ka furta haka, Amma koba gaske ba ne na gode kuma naji dadi Amma ka sani Ya Abba ina sonka mai tsanani sai tasa kuka. Yace ummi yi shiru, in kukan takaici ne kukan ya kare. Nima na jima ina sonki jiya naga sakonki a wayar umma da kike rubutawa mai dauke da nuna sonki gareni. Sai zurfin ciki ya hanaki, don allah ummi kada ki koma zurfin ciki a sona, ki zazzage min duk irin sonki gareni. Ummi tace yau kam ji nake kamar a mafarki. Sun nutsa a cikin hirar so suna ta baiwa juna labarin halin da suke shiga a baya, a lokacin daya ganta da wani namiji yace hankalinsa yayi mugun tashi. Sai lokacin daya fuskanci bashir na sonta, ita kuma Tace ta tsani koh mace ta kira layin shi, zainab kuwa data samu labarin ta kamar ta mutu. Tace ko bishira bata kishi kamar yarda take kishin zainab, sunyi nisa basu san sun kwana zance ba, sai da ummi taji kiran sallah. Tace ya abba kaji abunda naji, yace sallah ake kira naji, kin sani kwana zance. Ban gaji dajin muryarki ba amarya tah. Ummi tace gari yayi saurin wayewa kaje kayi muna godia ga allah ta hanyar nafita, yace to matata. Hamdala ta rikayi har bacci ya dauketa, muryar umma taji tana cewa ummi ki tashi kiyi wanka ki gasa jikinki. Tana zaune cikin baho wanda umma ta zuba ruwan dimi da dettol, tsohuwa ta shigo cikin bandakin. Ummi tace don allah tsohuwa fita, tace don allah ja can anki a fita din, ta saka hannu cikin ruwan wankan ummi dake gefe a bokiti. Tace ina suwaiba? Ai karo mata ruwan zafi, wannan ruwa yaushe zata gasa jikinta, idan da dan tawul dauko in danna mata jikin. Ummi tace nidai tsohuwa ki barshi don allah, sai kace wata mai jego? Tsohuwa tace tafi can kuda baku san darajar jikinku ba. Wannan rawar kan da mai sunan malam keyi idan ba'a gyara kiba saiki ba sai zance ya dawo baya, idan anyi magana ku yan zamani kuce bamu waye ba. Alhali ku wayewarku itace kwalliya amman jiki ba'a san a gyara ba, umma tazo ta kara mata ruwan zafi a cikin bokiti. Tsohuwa tace yau a sawo bagaruwa a tafasa ruwan shigar tata da ita don tayi saurin warkewa. Kuma ko ina zai hade, in kin koma gidanki kin kwana biyu ki dinga hada bagaruwa da alim kina tafasa su kina shiga.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 29 ZURFIN CIKI book 4 part 29 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:31 Umma Tace xa'asiyo tafita tabar su ummi nacewa to tsohowa kije mana tace bantafiya sai naga yanda xakiyi ganin ummi tabata lokaci nan tsohuwa ta dauki tawul din tashiga nadar ruwa tana dannama Ummi, Ummi tanacewa itadai abata tayi da kanta. Tsohuwa tace gaddamace daku ya'yan yau kinga duk macce dake rufe jikinta tafita daban damasu tallar jiki. Ita macce anfison a sameta ko yaushe da dumi a jikinta, yawo babu takalmi ko a tsakargidane yana ragewa mace dumi sbd sanyinda ke ratsa tafin kafarta har ni'ima yana ragemata. Sannan zama atantagaryar suminti shima yana rage mace, da a ace zaku gane kunga masu saka hijabinnan da safa? bakaramin wayo suke yimukuba. Inda za'a banbance za a samu sunfiku ni'ima da kyau fata, don haka sai kin dage Ummi dai tayi shiru, amma aranta cewa take wannan tsohowa ko ina tasan wannan duk bayanin? Filo aka ajewa Ummi ta zauna tana karin kumallo, duk takosa taga abbanta, koda ta tsinkayi sallamarsa tamkar tamike ta taroshi. Amma dole yaje yagaida su alhaji, tsohuwa tace aefa mu kuma bana munga takanmu don nan zaka dinga likemana. Yace dadin abundai nima nan gidan ubanane, da uwata. Umma tana kicin tanamasu dariya. Tunda ya zama idanunsu sunsarke da juna sun kasa ko magana Ummi ce tayi karfin halin lumshe ido sannan tabude tace sannu daxuwa. Tasowa yayi ya tsugunna kusa da 'its, yajikin babyna?sunan yamata dadi, naji sauki bari in kawomaka abun karinka. yamika mata tafin hannunsa tasaka nata yahadasu ya yasarke, murya kasa kasa yace barshi na' amso. Ta kula abba mutum ne maison wasa da tafin hannu. Ita kanta tanason hakan da akwai wani sako da tafin hannu ke isarwa acikin duniyar ma'abota so, kila wannan dalilin ne yasa abba ke kashema tafin hannusa kudi da mayukan da ke saka laushin hannu har ita mah ya saimata. Koda umma ta shigo Ummi tayi kokarie amshe hannunta amman abba yaki saki, kuma a hakan ya karya. Umma kasa zaman dakin tayi domin a baki abba yake ba Ummi abinci, umma nafita taceels / ZURFIN CIKI book 4 part 30 ZURFIN CIKI book 4 part 30 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:33 Daren ranar duk suna kan kujera doguwa a dakin umma ya bude mata laptop wai yana koya mata kanta kwance a cinyarsa, umma ta shigo dakin tsohuwa tace tsohuwa zaifi kyau mu sallami yaran nan na gaji da ganin wannan aiki nasu ai tasamu sauki. Tsohuwa tace suwaiba ina laifin ta kwan goma ma, umma tace anya zasu kwan goma nan? Gobe bakwai guda ta koma dakin ta, tsohuwa tace shine nan. Abba yace Ummi kinfa samu sauki ba zakizo mu koma gidan mu ba? Tace su umma ne zasu maidani ai nima ya abba inason in koma yace yau nan zan kwana in sunga haka sun kuramu, Ummi tace ya abba kayi hnkr kada ka kwana, shine yace kin yarda goma inxo mutafi ko ba sanin su umma? Tasa dariya tace taf inajin kunya bazan iya binka ba yace to kuwa zan kwana a nan. Suna cikin haka umma ta leko tace abba bazakaje gida ba yanxo fa sha biyu saura, yace umma nima nan zan kwana. Ta rike haba nan din lafia? Yace to umma nima ba gidan mu bane? Ummi tace dama yafi umma kada yaje wani abu ya rudashi, umma tace a'a abba tashi ka tafi insha allah gobe Ummi zata koma yayi murmushi tare da cewa nagode umma.nan dai ya tattara yanashi yanashi ya tafi gida cike da kewar matarshi, itama Ummi lamo tayi a gado. Bayan umma ta gama yimata fada ta bari ta warke taki ko, sai cewa tayi umma ni fa na warke. Umma ta kalli Ummi cike da mamaki tace yaran yazo saidai a barsu. Shiyasa akace idan macce ta isa aure ayi mata a huta. Ita kam Ummi tana ganin a barta tabi mijinta ta faranta mashi shine abinda yafi dacewa don yanxu ba inda ya kai mata dakinta dadi bacci. Duk da kashedin da tsohuwa tasa abba dakinta tayi mashi na cewa ya bar Ummi sai ta kara sati kafin yace zai kulata da sunan auratayya, bai sa abba jin zai iya ba. Don haka koda ta fada mashi cewa yayi kadai da huruminki da wanda ba naki ba duk sai kin shiga? To nidai ki lafa man haka. Ya fice a dakin. Ita kuma tana ta fadanta tana cewa "Na shiga din dan neman yaro, da kyar ya barta ta kara kwana biyu ya afka mata don shi hkr sa ya kare, ta nuna mashi ita fa tsoro take ji kada ta wahala, ya lallasheta yace ba wani wahala. Ummi tana son faranta ran mijinta. Don haka ta jure duk da yarda yazo mata ba sauki, sai dai tasha albarka kuma ta kara samun wani matsayi na musammam a gunsa. Cikin satin ta zama yar lelenshin kafin sati biyu ta hardace duk wani darasi da abba yake koya mata, abba jinsa yake kamar wannan lokacin ne ya fara rayuwar angoncinsa. Sam ya manta yana da wata mata uwa duniya saida Aunty ta kirashi tace lafia baya kiran matarsa sai ga abba da girman shi ya girba karya. Wai ya kira ya kasa samunsu Aunty ta yanda tunda farkon tafiyarsu yana kiransu sun gaisa da bishira tana tmbyrshi ina hibbarta? Sai lokacin ya tuna kwana biyu bai ganta don tana gidansu umman bashir, amman sai yace tana lafia in yaje zai kirata taji gwarancin yar tata. La'asar sur suka jero ita da abba don su dan zaga kurum. Sun shigo gidan ahmad da muktar duk basu rabu ba saida sukaji sun saba da ummi. Don ita haka take yana da wuya kayi zaman awa guda da ita bakaji ta kwanta maka a rai ba. Abba yaji dadi yarda Ummi ta nuna kauna ga matan abokanin nasa, yasan bada jimawa ba matansu zasu zama kawaye kamar yarda yaso da bishira amman taki. Daga can suka nufi layin su gidan su umman bashir Ummi tace su fara shiga su dauki muhibba abba yace bazata yarda dake ba. Ummi tace zata yarda muje a ran abba tsoro yake gada umman bashir ta gwasaleta Ummi, sun sameta tana shara da sauri Ummi ta amsa ta soma sharewa hakan ya faranta ran abba sai dai da ya kalli umman bashir yaga tana hararar Ummi, saida ta gama taxo ta zauna suka gaisa abba na rike da hibba tayi kaca kaca da kunu gashi duk ya dunkule dama ko lokacin da bishira tana nan haka zakaga yar duk kazanta. Ummi ta bude post dinta ta cire dari biyu guda biyu ta mikawa umman bashir gashi umma kin sai goro saida ta tabe baki ta amsa babu ko godia, sai dai abba cikin jin dadi yace angode, da hibba taki binsu Ummi tace kamal xo ka siyo wa hibba alawa, kinga baba kamal baya nan xo muje in sayo maki. Cikin sa'a sai taxo zasu fita sai ga bashir dauke kai yayi tare da jan tsaki daya shiga gidan sai ya hau umma da fada Wai ta daina barin Ummi da wannan abba suna zuwa in ba haka ba zasu kawo mata wani asiri. Umman bashir tace suta zuwa ma indan ta nine mi jiya tayi bare yau, ka gansu dari hudu yanxu ta bani don haka bazan hana zuwa ba amma fa ina nan yarda nake bazan canza ba, suna shiga gidan su umma kicin ta wuce ruwan zafi ta zubu ta cude muhibba tas, ta wanke mata kai ta chajeshi ta shafeta da mai nan ma basu jima ba suka nufi gida zanen umma ta ansa ta goye muhibba, shine ya bude dakin bishira duk kayan yarinyar sun rine da datti, Ummi dai ta zazzaba yace .ba maidata za'ayi ba, Ummi tace ta dan kwana biyu mana. Yace tana fitsari fa. Ummi tace kasawo muna pampers Yace shikenan duk da ya nuna bayaso yarinyar ta zauna gurinsu amman yaji dadi sai lokacin bacci daya shigo ya shigo da pampers din ta saka mata Sannan ta kwantar da ita can gefe ta azama mata pillo guda haba guda baya, su kuma suka kwanta a nasu makwancin suka cigaba da soyewa. novels / ZURFIN CIKI book 4 part 31 ZURFIN CIKI book 4 part 31 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:36 Ummi tana son yara don haka hibba ta dinga samun gata, satinta guda umman bashir ta dinga jaraba sai an dawo da ita. Wai kwadayi ne don in bishira tadawo ta bata tsaraba, amma koda ta tafi da hibban yarinyar sai taqi sai kuka har dasu amai. Dole aka dawo da ita, don alhaji karami cewa yayi atattara mata kayanta duka inyasake samun an maido da ita sai ya saba ma umman bashir. Hakan da babbar sallah abba yakashe musu kudi ita da hibba, sai dai duk abinda yasai ma ummi to ya aje ma bishira nata. Ita kam tana can duk addu'arta akan ummi ne, kafin ta dawo ummi tafita, don haka data dawo da kwarin gwuiwarta ce wa bazata samu ummi agidan ba. La'asar sakaliya, direban gidansu ya iso da ita gidan kamar yanda mahaifinsu ya umarce shi cewa in ya dauko su kada yaso dasunan, ya dire kowa agidanta. Kasancewar unguwa uku suka soma zuwa sai anty ta taya bishira diban kaya su shiga. Daidai kofar dakin bishiran abba na kwance rigingine, 'yar T-shirt ajikinshi fara kar. Dawandon jeans gajere iyaka gwuiwa. Ummi kuma dogon wando ne irin mai kama jikin nan dariga mai kamar singileti kanta yasha kana nan kitso, tayi filo da kirjinshi yana bata labarin wata mota da yake son yabada tashi yayi ciko. Ita kuma tana ce masa ya dai je ya shawarci umma, muhibba kuwa tana ta faman wasa da sabbin kayan wasanta da ummi tasai mata. Ita ma cikin 'yar shimi mai kyau, kanta kuwa ummi tayi mata kitson (3 in 1). Sororo bishira ta tsaya tana kallonsu, sam bata tsammaci a irin addu'ar datayi zata dawo ta samu ummi agidan ba. Basu ganta ba saida anty tayi sallama tare da cewa, ya naga kin tsaya? da sauri suka waiwayo duk suka mike. Gaban ummi yayi wata muguwar faduwa, amma duk dahaka cikin fara'a ta nufe su, bishira ta hade rai matuqa sannan taqi ko kallon ummi ta nufi 'yarta. Anty kam cikin fara'a suka gaisa da ummi harta zage jakarta dake kafadarta tabawa ummi wani dan agogo mai kyau. Nan dai ummi tayi ta godiya shima abba ya mata godiya. Abban ne ya shigar mata da kayan daki, ummi tana cewa anty kin mana dawowar bazata, dakin fada da an share miki dakin. Nan ma bata tanka ba, ummi dai data gaji dayi mata sannu bata amsa ba sai kurum ta nufi dakinta, zuciyarta babu dadi, tasan yanzun ya Abba zai raba jin da yake da ita zuwa su biyu. Bishira tayi kyam tana ta qamshi don anty baza su barta tazauna masu da qazanta ba, ga haqorin makka an sako ana ta qwambo. Ranar dakinta Abba yakwana, yanda bata ga wata rawar jiki daga gare shi ba tayi zargin ummi tasamu lafiya. Hakan ya qara dagula mata lissafi, tayi rabon tsarabarta daga kawayenta sai maqota, don ko umman bashir daga zam-zam bata qara mata komai ba. Dama tana cike da haushin umman data bari ummi ta daukar mata 'ya gashi nan muhibba ta liqe ma ummi. Hakan ya shaqar da umman bashir har tace amaida mata zam-zam dinta ita bata sha. Wato don taje makka shine zato zo ta canza hali? Ita kuma bishira ta amsa tare da cewa, ai ba ita ta aike ni makkan bada har sai tazabi abinda zan bata. Ummi ko zam zam din ba abata ba, kuma ko ajikinta. Abba kam shita kawo masa dogayen riguna da T-shirt masu kyau, amma su anty ne suka matsa mata sai ta saya. Ranar daya dawo daga dakin bishira ummi tana fashin sallah gashi yanuna yana dalarura alokacin. Sai tace ta yafe masa yau dagobe yaje gurin anty bishira, yace A'a tace ba haramun bane nina amince, yace nasani. Shiba yason sai yatafi tafara damuwa ko tazo tana jin haushinsa, tace ba komai saida yatafin kuwa har kuka tayi don kishi. Amma tabawa zuciyarta hakuri tasan wata rana wannan jarumtar datayi zata zame mata alkhairi. Ita ko bishira koda yazo mata sam bata damu ta bincika ba, tunda taga ba girkinta ba, saima ta hau murna yayo satar kwana ya bata musamman dataga dayayi wanka yakoma dakin ummi, haka washegari. Don haka sai tashiga daga hanci har da 'yan habaice habaice, kafin tadawo tun da dama da namiji dan uwansa yake kwana. Tana nufin ummi bata ba tayi masa amfanin komai wannan yasa ummi ta daura aniyar cusa mata takaici, aranta tace tunda cinikinki labe nikuma zansa miki hawan jini. Kamal yazo daukar abincin da ummi ta saba sawa yau har da kunun gyada tayi. Bishira ta kalle shi, wai kai wannan abincin na waye kullum kake zuwa dauka? Yace na ummarmu ne. Ta taba baki, ummar nan taku kwadayinta yayi yawa, ko kuwa itama asirin ya kamata ne? Kamal kuwa yaje yafada sai ga umman bashir agidan suna zage zage da bishira, tana ce ma bishira dadin abin gidan dana nazo kwadayin ba gidan ubanki ba. Marowaciyar bnza ai dama ina da cikinki, lokacin da Abba yasai maku TV, yace ki bani naki sai ki kace gara kiyar. Bishira tace, Eh na hana TV aiba wani shegen ya sai minba, ubana yasai min, kuma nace mai kwadayin yarinyar daki kace uwarta mai asiri, menene na amsar abincinta kici banda kwadayi? Shiyasa kika bata 'yata ashe don asami abinci ne, umman tasa kuka ni ke ke zagi? Yau ko abba zai zo gidan nan zai zaba ko ni ko ke. Ummi dai tana daki tana jinsu. (aranta tace dadi na da gobe saurin zuwa). Bishira tace dama ya darajaki ne shine za kice haka, yazo din nace mai kwadayi harda rainawa na baki zam zam butulu duk abinda na miki kin manta kece kika aikeni makkan? Umman tace, zuwa makkan naki dashi gara babu, don nasan da kyar ne in za akarbi wannan aikin nani ke da bakya sallah arniyar banza qazama. Ummi harda riqe ciki don dariya, haka dai suka yi tayi wajuna gori har dai 'yan kallon da suka taru suka soma bda haquri, umman bashir tayi gida cikin kuka. Tagayawa 'ya'yanta komai su bashir dasunce sai sunje sun zaneta umman bashir din tace barta ku barta kawai bari abban yadawo. Da dare ta ritsa shi agidan yasha mamakin wai yau mahaifiyarshi da bishira ne suke fada yace hakane dama duk zamantakewar da ba'a kafata don Allha ba wata rana sai ta rushe. Nan yayi tawa bishira fada da cewa uwarshi sa'arta ce dazata tsaya ta dinga gaya mata magana? Nan fa aka sake kacamewa har abba. Yakai ga kwasa wa bishira mari, sakamakon irin rashin kunyar data rike qugu take tsulawa umman bashir din. Ummi ganin abin yana tsawo ta fita taja umman bashir tana bata haquri ta zaci zata hantare ta amma sai taji tana cewa ba komai ummi sakayya ce tunda na nuna ina sonta dole tamin haka. Abba yace ummi tasa mayafi taraka umma gida, hakan ya qara qona ran bishira gashi yanda taga Abba ya bata rai zai iya yin komai, dole ta koma daki tana cizon yatsa tare da tunanin mafita. Ummi kuwa ahanya sai lallashin umman take tare dayi mata alqawarin cewa duk abinda take so ta tambayeta zata mata shi tarakata har gida sannan tadawo. Sabon kuka umman bashir tazauna tanayi, takaicinta yanda bishira ta zage ta taci mata mutunci agaban ummi, tashare ido tare dayin ajiyar zuciya a fili tace dani take magana. Ynzun ummi tasan kishi fiye da baya, don ta hau turbar ma'aurata kuma tasan muhimmancin abinda ake yiwa kishi, don haka zatayi komai na jan hankali don ganin taja mijinta gareta. Kuma inta lura cewa bishira ta maqale mata aqofar daki sai tayi ta jan abba da wasanni, don ta quntata ma me labe. Amma hakan baisa ta daina ba, don haka ta daura aniyai saita mata abinda zata tona kanta ha abba yasani. Duk jumma'a abba yana dawowa gida musamman in ranar girkin ummi ne don cin abinci na musamman. Jumma'a biyu kenan bata fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin tsohuwa tazo. Don haka suna gaisawa da umma tace gurin tsohuwa nazo. Suka shige daki tace da tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin. Tsohuwa tace, name ummi? Ta ce na gyaran jiki mana. Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu abubuwa. Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari? Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana, bada ina fada miki kina sharewa ba? Ummi tace haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja hankalin mijina. Ta ce, toda farko ki dinga kula da jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar iska. Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi. Sannan ki amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga matsa farin miski a ehem dinki. Sannan ki samu saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari, mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi biyu safe da yamma. Sannan ki aya garinta, kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa, sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale, citta, lemun tsami, ki markada su kisha. In anan maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban da dukkan sauran mata. Ki hada da biyayya tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi. Ummi tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin nan? Tace, bari zanba matar ado dake yawan zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu. Amma su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan. Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi tasan duk wadannan hadin matan? Amma data tuna cewa 'yar katsina ce sai tace ba mamaki. Tun ranar alhamis din ta soma aiwatar da darussan da ta debo daga tsohuwa, safiyar jumma'a ranar zai bar dakin bishira. Ya fito tana sharar tsakar gida ta gaidashi, ya amsa da fara'a, tare dawani kallo mai fassarar in ba keba. Cikin muryar data adana don shi kadai tace, ya abba ina son in je ayi min zanen fulawa. Yace jiya kin fita yau kam a'a. amma ki aika akira mai zanen tazo ta miki. Ta marairaice, towa zan aika yaya abba? Yace aike ni, ina ne gidan? Tace layin su umma ne yace to za'azo ai miki. Bishira tafito daga daki tazabga ma ummi harara, Tare dacewa kisisina. Abba yakalleta, kema sai tayi miki. Tace bana bukata, aikin banza, shikam yafice. Ummi kuwa tace gaba da aikinta, ita ko sai tasa kujera tazauna tana sakin zantuka, eh don kwalliyar tabanzanta tunda ba a iya biyawa miji bukata. Allah dai yasa ya fada min komai, to ni me zai dame ni don 'yar aiki kawai na dauki yarinya. Tashare min gida, tayi wa mijina abinci, daga nan fa? Saita saki shewa, ummi ta ce aranta yau zan bambance miki. Birabiskon shinkafa tayi da miya, ta wadata birabiskon da kayan lambu, miyar ta dauki nama da bushasshen kifi. Sannan ta hada musu kunun aya yaji dabino da madara, ta aikawa ummanta lokacin da kamal yazo daukar na ummarsu. Tasheka wanka taci doguwar rigar shadda koriya mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau ne daurin aurensu. Ga fulawar da yaje ya biya akazo aka zana mata. Tanajin rigimar muhibba tafito tazuba mata adan kwano tazaunar da ita akofar falon mamanta.bishira tafito kicin baki tasaki tana kallon ummi da tazo wucewa harda bangazar ummi, nan ko kamshi ya bude ta na turarukan da ummi ta fesa. Abba yana yin sallama ummi tafito da sauri, oyoyo yayana, bishira tana daga kicin dinta tana kallon su. Ummi ta rungume shi, sannu dazuwa sahibina. Ta amshi ledar hannunshi dajakar, yace yauwa sannu babyna tace inazan kai ledar? Yace akwai ta bishira aciki ki ciro. Ta mika mishi ledar ta wuce dajakar dakinta. Ya mika wa bishira lemo da abarba da yayo musu tsaraba sannan ya wuce danasu, awulakance ta aje. Yana shiga ummi tadan karo kofar yanda bishiran zata iya lekensu sosai ta gefen kofan. Ta cire masa hula ta aje akan madubi sannan ta kunna fanka. Ta shirya masa abinci, yauni zan baka har ka qoshi. Haka suka yita baiwa juna abaki har suka qoshi. Yakamo hannunta mai qunshi yana ta sumbata, wai kamar kada su goge. Kumatun shi ta shafa nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me kyaune, ina sonka ya abba sosai. Cikin jin dadi ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada wata rana ka juya min baya. Ya saqalo hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin lokacin. Ummi tasomayi masa wasu irin darussa wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama surutai. Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi duniyar ma'aurata. Bishira tamkar tayi hauka sai kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana, har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba munafiki. Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka, ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu? Da taga ya sauko da zafin rai saita gudu dakinta. Yabita yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai komane yaci gaba daga inda ya tsaya. Tayi ta kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir dole ta tafi gidansu. Shi kam abba shareta ya yi kosu umma bai fadawa ba. Sabuwar soyayya ma ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su fita yawonsu a qafa ko amota. In yana gurin aiki bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman dazata fada masa take. Duk lokacin datayi masa zancen bishira sai ya ce, don Allah ta bar ta ta huta, ummanshi kuwa 'yar bin qwaqqwafi sai da tabi ta gano bishira bata nan. Don haka koda ya shiga gaisheta sai tace kada ya yarda yaje yama bata takardarta. Ita ko tana can uwarta tace ma mahaifinta abba sakinta yayi, shi kuma yace to sai tazauna tunda zaman gidan take so. Amma su sani daga abinci sai ruwan gidanshi ya amince tayi amfani dasu sai ko gurin kwana, amma bnda wannan ko makilin dinshi ta taba bai yafe mata ba, wannan hukunci yayi musu tsauri. Ko wata bata rufa ba taji gidan ya isheta don hajiya zainu taso maidata makaranta amma yace tagama boko. Bishira na zaune ta zuba tagumi hajiya zainu ta shigo dakiki tace tagumin menene kuma? Tace, su sumayyah ne wai nace suyi ma muhibba wanka sukace Allah yakiyaye. Wai tunda nazo dakinsu ya lalace da kazanta, hajiya zainu tace aiba karya suka yiba, don haka ma maida yarinyar nan za ayi ke kuma ki koma gidan antynku ko ki tafi abuja gidan aisha. Tace baxanje gidan aisha ba, don itama bama shiri, gara gidan antyn amma gsky ni abarmin 'yata kuma fakinsan bai sakeni ba. Tace, inda ubanki yasan ba saki bne da tuni bai kora kiba? Don haka mubarshi haka amma batun 'ya nice zan maidata.

Chapter 22 of 24