Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke gabana,tace ina ruwana da abinda ke gabanka,likita yayi dariya yace mama yakamata ki koma gd haka,abba yace bari inkaita indawo,tace ban binka da can dani kazo? Abba yace nahuta,likita yayi dariya,da kyar suka lallaba tshuwa ta tafi da inna saratu,abba yaja kujera ya zauna gaban gadon,bayan fitan likita Idanu ya zuba ma ummi,godiya yake ma Allah a zucin shi daya amsa addu'ar shi yabashi abar sonshi,itako kai ta dukar a ynz takasa tantance kukan farin ciki take ko takaicin kalaman ya abbanta? Wani. Dan zare dake jikin hijabinta take wasa dashi,a zuciyarta kuma tambayoyi ne da fuska data jefa masa su,ya katse ta kinci abinci? Ta daga kai alamun eh" yace to yakamata ki dangana da kukan haka kisani ni kaina da ina nan bazan bari su alhji su daura maki aure da wanda bakiso ba. 53..Da sauri ta kalleshi,yace. amma inkin yi hkr zansame su zamu san yadda zamuyi,ta lumshe ido a zuciya tace tab! Ai rabamu sai mutuwa,zan juri duk wani ki dazan gani daga gareka,ya katsxeta kina zance a zuci fadi abnd kikeson cewa,tayi tagumi tareda kallonshi,ya abba yakanfi dacewa sa dan sanda ne ba dan jarida ba,sbd yanada saurin nazartar mutum,to amma meyasa yakasa gane tana son shi? Yayi murmushi,zanso inji abnda kikeb saqawa azuciyarki ko kinn samo mafita ne? 29. Zancan mafitar nan tana bata haushi, don haka saita canza zancen da cewa, tambaya zan maka guda biyu, ya dan yi shiru. Nazari yake, wace irin tambaya zata masa? Kila zata tambaye shi ne ko zai amince ya sahale mata auranshi, ya dubeta amsa daya zan ba ki in kin yarda, ta ce To dama zance ne ya ka ji lokacin da labarin sauyawar lamari ya zo gareka? Ya kura ta da ido, ya tambayi kansa a zuciya, me yasa take son ji@ yayi dan yake, yi tambayarki ta gaba, ta tsura mishi ido. Yanzun yaya za ka yi da maganar Zainab? Ya yi 'yar dariya, wacce amsa ki ke so a ciki? da sauri ta ce ba ni wannan amsar. Ya ce, "Kiin manta ni mijin mace hudu ne? Ta zaro ido kamar ya ya? Ya yi kokarin danne dariyarsa, sakamakon yanda ya ga ta zarana. Ya ce, "Ina nufin bayan Zainab har da wata, Ummi ta hade rai sannan ta zame ta kwanta cike da dana sanin tambayar. Abba ya yi mamakin kishin Ummi gare shi, ita da ba sonshi take ba? Ko da yake an ce mace ko bata son namiji in dai mijinta ne ta tsani ta ganshi da wata. Duk da haka ya ji dadin yanda ta nuna kishinta a kanshi, da ya tuna da Bishira ya ce tab, wata fitinar tana can tana jirana yau. Sam Ummi bata kara magana ba, shi kam Abba waya ma yake tayi Inna Saratu ta dawo, don haka ya mike ya kalli Ummi. Zan tafi ba tare da ta dago ba ta ce, sai anjima. Ya tafi yana waiwayonta bayan ya wa Inna Sallama. Kin shiga gidanshi ya yi sai kusan sha biyu a nufinshi lokacin Bishira tayi bacci, sannan yaje ya sai mata wayar da layi don yasan tana son waya. Kudinshi kenan ma ya kwashe ya sai mata, bai yi wani motsin kirki ba don kada ta farka, ya bude dakinshi ya shiga ya fito yana jan ruwan wanka kenan ta fito daure da zani a kirji. Jikinta ko dan kwali babu, gaban Abba ya fadi ta ce, "Munafukin Allah, annamimi dama ashe abinda kuke shiryawa kenan? To ka sani dole kasa ke ni don ba zan iya zama da Ummi ba, Allah ya kiyaye in hada miji da wannan 'yar yarinyar, tunda kai baka ga ai baya ba". Ya sassauta murya, "Haba Bishira, wannan abin fa Allah ya kaddaro za a yi haka, matar murtum kabarinsa. Ta ce, "To wannan ajalinka ce tunda wancan ya ki shi ne kai a ka cusa maka. Ya bar jan ruwan ya kama hannunta suka nufi dakinta, tana ta masifa. Ya ce, kibar maganar yanzu dare ne duk makota suna ji za su yi, kuma banga bain da zai sa ki daga hankalinki ba. Kin san dai ina sonki ko? Ta yi shiru tana kallonshi, ya ce ina zuwa. Yaje dakinshi wayar ya dauko mata, ga wayarki. Ta ce, "Eh don ka toshe min baki k? to bana so, ita wa ya san abinda ka sai mata? Ya ce, ya ki ke wannan maganar? Ban sai komai ba ko lefe ma tukunna. Ta mike tare da jefa mishi kwalin wayar, Ga tsiyarka nan matsiyaci, dole ka saka min da haka, tuni a ka gaya min tsiyar talaka na tafe. Haushi ya kama Abba ya dauki wayarshi ya tafi ya maida yazo ya dau ruwanshi yayi wanka, yana jiyo kukanta da duk zage-zagen da take yi. Shi kam katifarshi ya fada tare da rungume fito yana tunanin ranar da Ummi zata maye gurbin filon. 30. Har an tada sallah a Masallaci lokacin da ya farka, ya jima bai yi irin wannan baccin ba, da hanzari ya fito ya nufi ban daki don alwala. Abin mamaki Bishira ce zaune kan kujera a kofar dakinta, matar da sai ta kai takwas bata farka ba, amma yau bala'in kishi ya hanata bacci. Ta ce, "Eh na fito a ba ni takardata na gama zama da kai, ko in da take bai kalla ba ya ci gaba da abinda ke gabanshi, ya nufi Masallaci yana jinta tana ina nan ina jira ba zan zauna ba. Haba, gaskiya naji na tsani yarinyar ashe mijina zata aura, tsaki ya yi ya bude gidan ya fice. Har gari ya soma haske yana cikin masallacin, tunanin zuwa gidan yake, daga karshe dai ya fita da niyyar zuwa gidan Ummarshi. Wata zuciyar ta tambaye shi da cewa, tsoron ta ka ke ji ne? Kar ka zama soko dai a gidanka. A fili ya furta cewa, tunda na bita ta lalama ta ki, bari in koma mata ta zafin, ida din me? Sai ya sauya hanya zuwa gida rai 6ace, fuska daure ya shiga gidan, tana ta kai-kawo a tsakar gida. Ta dumfaroshi sai ka ce sabon kamun hauka, daga ganinshi ta dinfaroshi. "Ka ban takardata ba ni ba zama da kai, tafiya zan yi". Ya harareta "Sai da takarda za ki tafi? Lallai ba ki ji tafiyar ba. To ba zan bada takarda ba, don ki sani, sai dai in kotu za ki kai can Alkali ya baki". Ta nufo shi da zummar shako masa kwala, ya ce Kina ta6a ni sai na zane ki, in yaso ki tafi da hujja". Ganin yanda Abba ya bude mata wuta sai taja baya, Ka isa ka zane ni, ai da ka san ka dake ni, don ko sai ka sha dauri. Ya nufi dakinshi, wanka ya fito yayi sannan ya yi shirin tafiya aiki, amma har lokacin tana nan, ga 'yarta ta tashi daga bacci sai kuka take yi. Ta dauke ta ta goya, ta shiga dakinta can kuma ta sauke 'yar tasa kaya ta fito ta dauraye fuska da kafa ta goya 'yar tasa kaya ta fito taja kofar tana fadin." "Tafiya zan yi". Ta fito ta same shi yana goge gilashin motarsa na gaba. Ta ce, Tafiya zan yi sai an kar6ar min hakkina". Murmushi ya saki, sannan ya kalleta, ta ina za ki bi in rage miki hanya? Ta dawo ta duki motar, Ba zan shiga wannan gwanganin motar ba, kai ne bakon mota. Kafi kowa sanin daga gidan da na fito, ko motar zuwa cefanen gidanmu tafi wannan tsarri. Ya ce. "Gurinki ko? Ni ai bani da wadda ta fita tunda bata gidan naku nike hawa ba. Sannan kuma tunda ba za ki zo in rage miki hanya ba shi kenan sai naga sammaci. Ya shiga motar ya tasheta yayi gaba, ba tare da ya saurari abinda take cewa ba. Ta isa gidansu cikin tashin hankali, Hajiya Zainu ta saurare ta tsaf, sannan ta ce "Kin dai ga abinda a ke fada miki, kina ganin ba zai faru ba ke so ya rufe miki ido, to yanzu an zo gurin. Bishira ta ce, "Ai na gane komai yanzun, Momy nayi nadama. Ta ce, "To zan tsaya miki matsalata Babanku, yana nan a gari na kuma san za su zo iyayen Abba. Amma wannan karon shi kanshi Babankun zan iya ja da shi, Bishira taji dadi sosai, don kuwa duk son da ta ke wa Abba yanzun kishi yasa ya koma 'ki. Gidansu Umma yaje a gurguje suka gaisa, ya kwashe su da Alhaji da Alhaji Karami zuwa asibiti, a motar nema ya ke fada musu cewa Bishira ta tafi gidansu Umma ta ce a kan me Abba, me ka mata? Ya ce, "Ban mata komai ba, ya fada musu duk yanda aka yi. Alhaji Karami ya ce, Sahura ke zugata, itama ai kwana tayi bala'in. Don haka kada kaje bikonta, Alhaji Babba ya ce, "Ba za a yi haka ba, da dare kazo muje, Abba ya ce To. Sun isa asibitin tana wanka, sun gaisa da Inna Saratu ta fada musu tana wanka, sannan likitan ya sallame su amma sai sha biyu za su tafi gida, lokacin an karasa mata allura. Abba can baya ya tsaya kusa da kofar shigowa ya jingina da bango idanunshi suna fuskantar kofar bayin, matuka ya kosa yaga Ummi. Sanye da hijabi da zani daurin kirji ta fito, da Abba suka soma hada ido, bai ta6a kallon Ummi da sha'awa ba sai yau. Kamshin turaren Abba ya ratsa ko'ina a dakin, ta zare idanunta daga nashi, ta kalli Ummanta sannunku Umma. Suka ce Yauwa. Ta gaida su sannan ta zauna bakin gado tare da sunkuyar da kai, Alhaji Karami ya ce, "Uwata jiki kuma ya yi sauki ko? Kanta na kasa ta ce, Eh, ta kasa dago kanta, gani take Abba ya cika dakin. Abban ya ce, "To ni zan tafi don lokacin aikina ya kusa, Alhaji zamu je ne in sauke ku? Suka ce To, Umma ta ce In an yi mata Allurar anjima ma nemo mai Taxi. Alhaji ya ce, To shi ke nan. Umma ta dubi Ummi ba za ki gaida Yayan naki ba? Ta saci kallon Abban tare da cewa, Au, ban ganshi ba. Ina yini? Ya ce, Umma me yasa za ki rokar min gaisuwarta? Inna Saratu ta ce, Kai Ummi da iya shege take, ina kallonta shi ta fara kare ma kallo sannan ta kalli kowa amma wai bata ganshi ba. Su Alhaji dai 'yar dariya suka yi sannan suka fita, Abba ya bi su tare da yi wa su Umma sallama. * 31. Bayan fitarsu, Umma ta dubi Ummi fuska daure, ina fatan baki nuna damarar nuna kiyayya ga Abba ba ne? Ummi ta sunkuyar da kai, a ranta ta ce, "Kin ji Umma da wani zance, ai ina zaton nafi Mahaifiyarshi sonshi ma bare ku. "Amma a fili sai ta ce, To Umma shi ma fa Ya Abban bai ce yana sona ba, Umma ta ce Saratu ji ta da wani shirme. Ina ce ita ce zata janyo ra'ayinshi gareta? Inna Saratu ta ce, Kwarai kuwa, ta hanyar ladabi, biyayya da girmamashi, musamman shi da ke da matsalar mata. Ummi ta ce, Kuma ina tsoron masifar matarsa ba dai guri daya zamu zauna ba ko? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa? Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai kama? Umma ta ce ina ruwanki da matarsa? Sannan in ba ku zauna guri daya ba haya zai kama? Kada ma in ji kin kuma zan nan, Ummi dai tayi shiru. Da dare Alhaji ya tasa Abba zuwa gidan su Bishira, zuwan su ne ma Alhajin yasan 'yarshi tayo yaji, cikin 6acin rai ya kira wayar Hajiya Zainu ya ce su zo ita da Bishira. Ba tare da ya jira amsarta ba ya aje wayar, ba tare da yasan abinda ya faru ba ya shiga ba su hakuri. Hajiya Zainau taje dakin su Bishira ta kira, suka nufi sashen Alhajin tana mitar cewa munafukai sun zo kenan, ai za'ayi ta bari muje mu ji. Suna shiga Alhajin ya kalli Bishira, "Me ki ka zo min ki yi a gida? Ta ce, Daddy cin amanata ya yi, aure fa ya yi da yarinyar da suka tsane ni. Alhajin ya daukin da ke gabanshi na plastik ya jefe ta da shi, auren shi ne cin amana don uwaki? Hajiya Zainu ta ce, "A'a Alhaji, zan cen gaskiya a duba hakkinta itama, ya ya za a dau 'yar da bata kaunarta, iyayenta basa kaunarta a ba shi. Sannan ta yi magana ya hauta da zagin iyaye? Ya ce, "Ke yi min shiru ban tambaye ki ba". Ya kalli Abba, Ya abin ya faru? Ban ji ta bakinka ba? Nan dai Abba ya fadi komai har ta taho, daidai da cewa tazo ya rage mata haya da abin da ta ce duka. Alhajin ya yi tsaki ya dubi Alhaji Babba, irin wannan ai ba a biyo su, tayi ta tafiya sai dai nima in ba zata koma gidanta ba, to ba gidana ba. Ya zura hannu cikin aljihu ya ciro rafar 'yan dari bibbiyu, Ga shi Abba, dama nayi maka alkawarin baka sadaki duk lokacin da ka nemo aure. 57..... Abba ya ce, "A'a ka bar su ai an riga an yi. Mahaifin Bishira ya ce, "Ni nayi alkawari. Suka yi godiya. Ya kalli Bishira, Ko ki bi mijinki, ko ki bar gidana. Hajiya Zainu ji take tamkar ta shake Abba. Ta ce, "Haba Alhaji, gaskiya ban yarda da wannann hukuncin..." Ya katse ta da cewa, Ke! Da Allah fita anan. Su Abba suna shiga mota Bishira na fitowa da kukanta, dole ta zo ta shiga motar. Alhaji Babba ke ta bata baki har suka kai gida, shi kam Abba da suke sauke Alhaji ya yi nasu gidan, suna shiga ta soma zantuka. Ba za ka ta6a samun kwanciyar hankali ba a gidan nan har abada, ba dai ka matsa an dawo da ni ba? Abba ya yi murmushin mugunta, ai ni wannan yajin naki naji dadinsa, gashi har na samu gudunmawa, kin ga sai naje kasuwa in soma darzo wa Amarya zannuwan lefe. Ya nufi dakinshi ya barta nan tsaye tana zage- zage, lefen banza, in ma uban lefe ne kai da ita sai na koya musu hankali. Kusan goman dare Ummi tana kan doguwar kujera, addu'a take yi Allah yasa Abba yazo ta ganshi kafin tayi bacci. Can kasan zuciyarta kuma kishi ne don tasan sun je gidansu Bishira ne biko ganin Alhaji ya shigo shi daya sai ta debe tsammani da zuwanshi. A ranta take raya cewa yanzun haka suna can suna cin soyayyarsu, kamshin turaren shi ne ke mata gizo a hanci. Amma sai kunnuwanta suka tsinkayi sallamarshi, a hankali tamkar ba ya son a san ya shigo. Umma tana ciki? Tambayar da ya yi kenan ba tare da ya jira ta amsa sallamar ba, ta tashi zaune da sauri a'a tana gurin Alhaji. Ya shigo ya zauna ta ce, "Sannu da zuwa". Ya amsa yana kalonta, ta sunkuyar da kai, gabanta ke wata irin faduwa. Shi kam ji yake tamkar ya manne ta a jikinshi, sai dai yana jin nauyin hakan tunda ba suyi wannan sabon da ba rin haka zata faru tsakaninsu ba. Dakin yayi shiru, ita tana wasa da yatsunta shi kuma yana kallonta, can ya ce "Ummi". Ta dube shi "Yaushe za ki tare? Ta ce, Nima ban sani ba, sai yanda su Umma suka ce. Ya dauko kwalin wayar da ya sai ma Bishira ta jefe shi da shi ya ciro wayar ya hadata da batir din bayan ya 6are sim din ya saka. Ummi dai tana ta kallonshi, ya manna chajar a jiki, ya mika ma Ummi jona min can, ya nuna mata soke din da ke bayanta. Ta amsa cike da sha'awar wayar duk da bata nuna hakan ba sannan ba ta ce kala ba. Ya ci gaba da cewa, "Karfe nawa a ke kashe inji? Ta ce, har yanzu ba a canza daga yanda ka ke kashewa ba. Ya ce, "Sha daya zuwa sha biyu? Ta ce, "Eh, ya ce in har zuwa wannan lokacin ba kiyi bacci ba to ki cire in an kashe, ki kunna ko da yake in dai ke ce ba sai na ce ki kunna ba. Ta dago ido ta kalle shi, ya ce, Eh kunnawa za ki yi ko za ki musa ne? Don kin fi ni ma sanin kan waya. Ta ce, Wayar Umma kadai na iya kunnawa, sai taka. Ya ce, Oho, cikin dan murmushi, na za ci ba za ki fadi tawa ba in tuna miki lokacin da kika kunna tawa. Haka nan don tsabar iya sarrafa wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin Kaduna. * 58....Haka nan don tsabar iya sarrafa wayarki tun kina 'yar karama ki ka tura ni garin Kaduna. Ta zuba fuskarta cikin tafukan hannayenta, sam bata son Ya Abba yana tada wannan zancen, Umma ta shigo da sallama tana cewa, Yuwa Ummi, ina ki ka sa min 'yar kwalbar turaren nan? Ummi ta dago fuska, "Cikin jakarki ta rataye. Umma ta dubi Abba, "A'a ha, yaushe ka shigo? Ya ce Ban jima sosai ba. Ta zauna ya gaisheta, sannan ta ce masa dama Alhaji yanzu yake ce min zaman me Ummi ke yi a gidan nan? Ya zaci tun daga asibitin zata wuce dakinta, Ummi ta turo baki. Umma Alhaji ya gaji da ni sosai, suka kalle ta, Umma ta ce, Ji wani shirme, me ya yi na gajiya? Ta ce To dubi fa daga cewa an fasa aurena sai da ya matsa ya daura min aure. Sannann kuma yanzun wai ya zaci daga asibiti zan tare? Abba ya ce, Ai yana daki yi hanzari ki same shi don shi ya san amsarki ba Ummata ba. Umma ta ce, "Wallahi daga nan suka share Ummi. Ta kalli Abba ta ce, "To kawai yanda za a yi gobe ka kwashe kayanka daga dakinka sai a kai na Ummi din kawai. In yaso zuwa yamma ko Saratu da sauran makota sai su rakota. Abba ya kalli Umma, ni da so nayi a dan yi kwaskwarima a gidan kafin sannan na dan samu na sai ma Ummin Zannuwa. Umma ta ce, "Zancen wofi, yanzun tsirara take yawo? Kawai in kana da fenti a hannu a goga a kawo ta haka, in babu ma dai goben nan zata tare don ba zan amince ran mijina ya 6aci ba. Abba ya yi murmushi, to shi kenan Umma da safe kafin na fita zan nemo masu aiki ina da fenti da siminti sai ayi 'yar kwaskwarima shi ke nan. Dama ga kudi nan da Mahaifin Bishira ya bani, wai dama ya yi min alkawarin biya min sadaki. . 59... Umma ta ce, "Yanzun Alhaji ya gama bani labari, Mahaifin yarinyar nan mutumin kwarai ne, don Allah Abba ka rike yarinyar nan ko don darajar mahaifinta. Ummi ta ta6a baki, kishi ya motsa. Abba ya ce "In sha Allahu Umma nima abinda nike dubawa kenan, ni ke hakuri da ita. Ta ci gaba da cewa, Sannan kada kaga Ummi yar uwarka ce ka ce zaka fifitata, sam ba zan yarda da haka ba. Kayi adalci a tsakaninsu ka dinga addu'a Allah ya hada maka kansu. Ya ce, "In Allah ya yarda Umma zan kula. Ta ce, "To maza ka tashi ka tafi gurin iyalinka. Sam bai ma dace ka fito ba, kamata ya yi a ce ka zauna gida ka kara ba matarka baki, ya cee To Umma. Ta mike tana cewa, tashi maza. Ya mike yana kallon Ummi, yayin da ita kuma ta juya fuskarta cike da 6acin rai. Ya ce, Ummi ki fa kunna in an kashe injin? Sam ba ta tanka ba don haushi, sai da ya tafi sannan Umma ta dubi Ummi. Ki tashi ki kwanta don gobe ki tashi da wuri, kiyi duk shirin da ya dace saboda babu daga kafa a tarewarki gobe. Ki ta fasha-fishenki ba zamu kuma yarda da kalace-kalacen ciwonki ba, ta tafi abinta. A zaton Umma, Ummi tana fushin ba zata tare ba ne, ita ko haushinta korar mata miji da Umma tayi ya tafi gurin kishiyarta. Koda ta kulle kofar ba ta shiga uwar dakin ba, nan kan doguwar kujeta ta mike abinta. Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya. Abba ko kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai tsafta.I novels / ZURFIN CIKI book 3 part 8 ZURFIN CIKI book 3 part 8 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:37 Jira ta ke a kashe Injin ta kunna waya. Abba ko kafin ya isa gida sai da ya fita titi ya fanshi kaji guda biyu da madara mai tsafta. 60...Sai dai yana shiga gidan ya iske mahaifiyarshi da matar tashi suna ta zage- zage. Ya nufi gurinsu, Sahura ta ce, Sai yanzun suka barka ka taho? Ya ce, "Umma dama ban dade da zuwa ba". Ta ce, "Ina ta aiken kazo ina nemanka shi ne ka 'ki zuwa saboda ka maida ni 'yar iska ko? Ya ce, A'a Umma ba a fada min ba. Sannan aiki ne yasha kaina... Ta ce, "Rufe min baki, ai baka daga kafa da zuwa gun Suwaiba. To saurare ni da kyau ka ji, nazo ne in fada maka cewa ka rubuta saki ka ba wannan 'yar iskar yarinyar. Ya ce, Kiyi hakuri Umma, ki bari sai a hankali. Bishira ta ce, Umma yana sonta fa, jin ku kawai nake. Maganar Bashir gaskiya ce da ya ce da shi a ka shirya hakan. Umman Bashir ta ce, "Dama Abba kaima son Ummi ka ke yi? Ya ce, Umma ba zan ki Ummi ba, in kun yi la'akari da kaunar da iyayenta suke nuna min. Amman wallahi ban san komai game da auranmu ba, ta ce kana nufin kan dole a ka daura muku aure ba don kana sonta ba? Abba ya yi dan jim, ta ce kai nake sauraro, don ta tafi sai ya ce kusan haka dinne, itama kuma ba sona take ba. Umma ta ce, Ina ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai suna so. Ni dai bukatata yanzun kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka. 33. 61... Umma ta ce, "Ina ruwana da bata sonka, in bata so iyayenta ai suna so. Ni dai bukatata yanzu kada ka bari ta tare, sannan ko kusa kada taga fuska a gurinka". Ya dan yi shiru yana tunanin wannan irin lamari a zuciyarshi ya ce, bari kawai in lalla6ata, zan yi yanda ki ka ce sai dai kuma in su Alhaji suka sa kawo ta ni ba zan iya ja da su ba. Sannann ke kanki bana so a ce ke ki ka sa ni in ma Ummi rashin mutunci, amma ki bar ni da ita in har ta yarda ta tare a nan gidan. Bishira ta ce, "Tab, ba ko zata tare a nan gidan ba". Umma ta ce "A'a ki bari in sun matsa ta tare a nan din ta tare, gara suna kusa muna kallon irin zaman da za su yi. Can gefe ba sai su rinjaye shi ba". Bishira ta ce, "Umma na tsani shegiyar yarinyar nan ne, bana son in ganta ko cikin mafarkina, bare a zahiri". Sahura ta ce, "Bishira na ce ki nutsu ki bar komai a hannuna, in ma zan hada da Bokaye ne ba Malamai ba in sha Allahu sai kin dara a gidan nan. Ta ce, "To Umma, Sahura ta ce, Yauwa ke dai ki zuba ido, Abba dai yana tsaye yana kallonsu. Sai lokacin yayi magana, Umma dare fa yayi, ta ce to muga ledar hannunka, ya mika mata. Ta buda ta gani, "A'a kaza? To ku zuba min nawa". Ya mika wa Bishira, Ki dibarwa Umma. Ya nufi dakinsa yana jin sallamarta tana fadin ta wuce, ya fito ya ce "To Umma sai da safe, ya rufe gidan ya koma dakinsa. Da ya shigo gidan ne da niyyar lallashin Bishira, amma yanda abubuwan suka zama sai ya ji ba ma ya son ganin Bishiran. Zantukan Bishiran da na Mahaifiyarshi sun saka shi cikin tunani, lamo ya kwanta a kan katifa yana ta harsaso irin zaman da za a yi a gidan. Anya kuwa ba zai kama wa Ummi haya ba? Cak! Hasken wutar dakin ya dauke tare da tsayawar Injin. A fili ya futa, Mai ya kare kenan, sai da ya yi shirin bacci ya kwanta tare da manne filo a kirjinshi, sannan ya dauko wayarshi ya kira layin da ya hada cikin sabuwar wayar da ya ba Ummi. 62.. Gabanta ne ya fadi, lokacin da taga lambar Ya Abba suna rawa a fuskar wayar, ta haddace lambobinshi tun shekarun baya. A fili ta ce, kenan ma ya hada wayar ba yau ya soma hada ta ba, ta sake yin lamo a kan gado tare da janyo filo ta manna a kirjinta. Ta daga wayar lokacin tana daf da tsinkikewa, can cikin makoshinta tayi sallama. Ya amsa, tsigar jikinsa a tashe sakamon jin muryarta tana ratsa jikinshi, ya ce "Ummi, ta ce Na'am Ya Abba. Ya ce, "Kina son ki tare goben? Ta lumshe ido, ba ni da za6i Ya Abba, duk yanda ku ka ce. Dadi ya cika zuciyarshi. To shi kenan ki tare goben, zan yi parking tun Asubahi sai in sa mai fenti yayi kafin in tafi aiki. Ta ce, "Ba an ce in mutum ya yi aure ana ba shi hutu ba? Ya yi 'yar dariya, "To ni ba ki ga yanda auren nawwa yazo daga sama ba? Amma duk da haka in na nemi hutun za a bani, ta ce kayi aikin kama kawai ba sai ka nemi hutu ba.. Ya katseta, "Don ba a sona shi yasa ba a damu na amshi hutu ba? Ta ce, "Ba nufina kenan ba, naga kana matukar son aikinka ne". Ya yi dan murmushi "Kin dai wayance kawai, to yanzun haka zaki tare babu ko dan kunshi bare gyaran kai irin na Amare? Koda yake ba aure so ba ne. Cikin muryar shagwa6a ta ce, "Ya Abba ka daina, ya ce me zan daina? Kana cewa bana sona, ai kai ma ba ka sona... Ya dan yi shiru, yanda ta ke shagwa6ar ne ta tsuma shi. Ya ce, ok, to goben sai kije ki gyaranki ko? ta ce, "Umma ba za ta bari in fita ba, amma me yin fulawa za ta iya ta mini". Ya ce, "To ina ne a ke gyaran gashin? Ta ce, "Cikin gari ne, ya ce kin san gurin? Ta ce, "Eh, amma ban ta6a yi ba, ya ce to ki bari zan shigo gidan kafin na tafi aiki zan ce Umma ta bar ki, ta ce "To." Suka dan yi shiru. Can ya katse shirun da cewa, "Me ki ke tunani?" "Yaushe?" "Yanzun." Ta dan musukuta,

Chapter 15 of 24