Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
guda uku bisa alkawa da cewa indai bukatarka ta biya zaka karbi addininsu. Ni dai azatona zasu yarda da wannan sharadi, kaga kenan koda karfin addinin su bai yi aiki ba na jarumtkarka zai yi, baza kayi biyu babu ba". Sa'adda Sarki Sahibul Hairi yaji wannan batu na Bawa Haluf sai ya cika da tsananin farin ciki, bao san sa'adda ya rungnmeshi a kirjin sa ya na cewa, " Gaishe ka ya babban Bawana, hakika ina mutukar kaunarka sabo da hikimarka da kaifin kwakwalwarka. Na yi maka alkawari indai na cika burina zan 'yntaka, kuma na maisheka waziri na mu cigaba da tafiyar da mulki tarw a birnin Misra". Koda Bawa Haluf yaji wannan batu, sai shima ya cika da tsananin farin ciki ya kama godiya Kashe gari da safe aka kawowa su sarki Sahibul Hairi mai mai kyau da na garta. Bayan sun kimtsa cikinsu sai Imam Sadik ya Shigo cikin dakin da aka saukesu tare da wani badakore a bayansa cikin shigar fararen kayan yaki na sulke. Badakaren ya nade kansa da rawani idansa kadai ake gani. Duk da cewar gashin kansa a daure yake a gadon bayansa, kuma a rufe cikin rawani kasan cewa Allah yayi masa baiwar gashi mai tsawo. Badakaren ya rataya zabgegiyar takobi a bayansa, kuma kafafunsa a sanye suke da dogwayan takalma na farin kirgi masu madaurai. Kai hakiki shigar Badakaran ta yi kyau, amma ko kadan babu wata alamar kirar sadaukantaka a jikinsa. Koda sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf sukayi arba da idanun Badakaren sai kirjin su ya kama sabo da kwarjini kyawawn idanun Badakaren. Duk su biyun sai suka aiyana a zuciyarsu cewa ina ma ace wannan Badakaren mace ne hakika da anyi kyawu irin wanda babu kamarsa a duniya. Ya yin da Imam Sadik ya shigo sai ya zauna daf da su Sarki Sahibul Hairi.shi kuwa wannan bada karen sai ya koma gefe guda ya tsaya kikam kamar gunki ko kyakkyawan motsi baya yi. Imam Sadik ya dubi sarki Sahibul Hairi cikin fara'a da murmushi ya ce, "ya kai wannan sarki babban namiji, kayi sani cewa yau nea zanyi bankwana da ku,domin ku cigaba da yin tafiyarku, amma bayan mun warware matsalar da ke dake tsakaninmu, shin yanzu ka amince zaka karbi addininmu ko kuwa a'a?". Sarki Sahibul Hairi ya yi gyaran murya, sannan ya ce, " mun amince zamu karbi addininku, amma bisa sharadi gida. Sharadin shi ne, ina so kununa min cewa zaku iya taimakamin naje Boka Shamzabul Azwas na dakko yarinya Alfila 'yar uajan sadauki Awaisu na fito daga ciki a raye kuma lafiya da karfin Ubangijinku, sannan ku kaini inda sadauki Awaisu yake ku tolastashi koda zaiki ko ya yaudareni bayan na bashi 'yarsa akan mutafi neman 'an mata uku wadanda zan aura na zamo Sarkin Sarakai, nayi alkawari in dai kuka yi mini haka zan karbi addininku bil- hakki" .SA'ADDA SARKI SAHIBUL HAIRI YA ZO NAN A ZANCENSA SAI IMAM Sadik ya yi murmushi mai nuna yarda sannan ya ce, "ya kai wannan sarki, ka sani cewa Ubangijina ya sanar dani duk abin da zaaifaru tsakaninmu tun ka fin ku zo wannan birni namu mai Albarka, sabo da haka na amince da dukkan sharadanku bisa dalilin hakan ne ma nazo da wannan Badakeran nawa domin na gabatar da shi a garwku sabo da shine zai zamo wakilinmu, wato shine abokin tafiyarku. Da izinin Ubangijin gaskiya zai iya yi muku duk abin da ya gagareku ya yin wannan gagarumar tafiya. Amma ku sani cewa wannan Badakaren nawz baya magana, amma duk abin da zaku fada yana ji kuma zai iya mzgana da kai kamar yadda bebaye ke magana da hannu. Duk abin da zai faru a tsakanin ku kada ku matsashi, kuma kada kuce zakuyi masa dole, domin zaku sha mamaki. Tabbas dan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. A yanzu haka wannan Badakaren nawa ya futo sa shirinsa na yin wannan tafiya tare da ku, kuma na sa an tanadar muku guzuri. Shawarata a gareku ko kuma ina ce dokar da zan kafa muku ita ce, kada ku kuskura ku yi wani abu da jibanci tsafi a cikin wannan tafiya taku muddin kuna tate da wannan Badakaren nawa, idan kuwa kuka yi din zaku iya halaka ko ku shiga mugun hali. Idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira. Daga wannan furci nake muku bankwana sai kun dawo wannan birni namu mai albarka bayan cikar burinka". Lokacin da Imam Sadik ya zo nan a jawa binsa sai sarki Sahibul Hairu da Bawa Haluf suka ji kamar tatsuniya ya ke musu amma a zahiri basu nuna hakan ba. Nan take suka fito gabaki daya daga cikin wannan gida na masaukinsu sarki Sahibul Hairi.fitowarsu ke da wuya sai suka ga gaba daya mutanan birnin sun taru a waje guda. Koda fitowar sarki sai jama'a suka taho da yawansu suna yi wa Badakaren murna tankar wanda ya sami mulkin duniya. Koda ganin abin da ke faruwa sai mamaki ya kama sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf. Sarki Sahibul Hairi ya dubi Imam Sadij ya ce, "me yasa mutanan ka suke taya wannan Badakaren murna"? Sa'adda Imam Sadik ya ji wannan tambaya sai ya yi murmushi sannan ya ce, "Abin da yasa kaga jama'ata suna wa abokin tafiyarku murna shi ne,sun san cewa zai tafi JAHADI ne, wato daukaka kalmar Ubangijin Musulumci. A ka idar addininmu duk wanda ya mutu a cikin wannan tafarki sai ya sami babban rabo a wajan ubangijin musulumci, don haka gaba dayanmu muna kwadayi da sha'awar ina ma ace mune wannan badakaren". Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf cika da tsananin mamaki irin imanin wadannan mutane a bisa Ubangijinsu. Bayan su sarki Sahibul Hairi sun yi bankwana da su Imam Sadik sai abokin tafiyarsu, wato Badakaren ya zo gaban Imam Sadik ya tsaya daf da shi suka kurawa juna ido. Kawai sai hawaye ya zubowa jowanne daga cilin su a lokaci guda. Nan take suka rungume juna suna kukan zuci, kai da gani kasan cewa akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu. Daga can sai suka saki juna. Badakaren ya nufi inda su sarki Sahibul Hairi ke tsaye daf da Aljani Dabarus yana waigyen Imam Sadik cikin alamun damuwa kamar ya fasa tafiyar. Sauran jama'ar gari sai suka kurawa Badakaren isanu gaba dayansu daga mai zubar da hawaye sai mai kwalla. Ai'amarin da ya kara jefa su sarki Sahibul Hairicikin tsananin mamaki kea nan, suka tambayi kansu a cikin zuciyarsu. wai shin wana irun matsayi wannan Badakaren yake da shi ne a wannan birni harda kowa zai shiga damuwa da bakin ciki sabo da kawai zai yi wannan tafiya? A kan wanne dalili Imam Sadik zai zubar da hawayansa a lokacin da suke bankwana? Wadannan tambayoyi ne wadanda basu san amsar su ba. Amma sai sarki Sahibul Hairi ya kudurce a ransa cewa nan gaba sai ya san amsoshinsu Ba tare da bata lokaciba su sarki Sahibul Hairi,Bawa Haluf da Badakaren suka hau bayan aljani Dabarus suka zauna. Shi dai Badakaren a can gefe daya ya zauna, bai kusanci su sarki Sahibul Hairi ba, har Aljani Dabarus ya yun kura zai bude fuka-fukansa, sai Imam Sadik ya tsaidashi ya dubi sarki Sahibul Hairi ya ce, "in mai yi muku tuni da kada ku manta kuyi tsafi muddin kuna tare da Badakarena, yin hakan zai iya kaiku ga halaka ju shiga mugun hali." Sarki Sahibul Hairi ya ce, "lallai zamu kiyaye da wannan umarni naka." Take aljano Dabarus ya sake yunkurawa bude fuka- fukansa yai sama, kafin kiftawar ido ya luluka a can kokoliyar sama. Koda Badakaren ya leko kasa ya hango birninsu da jama'arsu sun zamo 'yan mini-mini kamar kiyasai, sai hankalinsa ya dugunzuma, baisan sa'adda hawaye ya subuto masa ba, domin gani yake kamar har abada ba zai sake dawowa birninsu ba bare yaga jama'arsu. Sai da sa'a uku ta shide suna tafiya a sararin samaniya sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suna ta hirarsu amma shi Badakaren ko kallansu bai ba bare ya nuna ra'ayinsa bisa abin da suke tattaunawa, kuma tunda aka fara tafiyar ba abinda ya ke yi face jan wata tasbaha yana ta lazumi abinsa. Da yake a wannan lokaci ana zabga rana su sarki Sahibul Hairi sun sha ruwa a kalla ya kai sau bakwai, amma shi Badalaren ko sau daya bai bukaci ruwa ba. Wannan al'amari ba karamin mamaki ya baiwa sarki Sahibul Hairi ba, har ma sai da suka yi tseguminsa suna cewa, "wai shi wannan Badakaren wana irin mutun ne shi? Anya kuwa mutin ne? Babu mamali aljani ne ya yi badda bani" Lokacin da Dabarus yaji tsegumi nasu Sarki Sahibul Hairi sai ya bushe da dariya sai ya ce, "ya shugabana ai tabbas wannan Badakaren mutun ne dan uwanku,domin inda aljani ne yana kusantata zan gane, amma a cikin mutanan ma shi daban ne." Haka dai suka ci gaba da surutansu har suka sake shafe sa'o'i ukun. A tsawan wannan tafiya Badakaren bai yi wata bukata ba facelazumi, sallah sa nafulfuli kuma a duk sa'adda zai yi sallah ko nafula sai ya kwance farin mayafi a kugunsa ya shimfida shi a kan aljani Danarus sannan ya hau kan mayafin sannan ya yi ibadarsa, kuma ko yaushe alkibla yake fuslanta. Bayan cikar sa'a shida da fara tafiyar sai sarki Sahibul Hairi ya yi wa aljani Dabarus umarni da ya sauka su ya da zango. Ba tare da bata lokaci ba aljani Dabarus ya bi uamarni ya sau ka kasa ya dure a cikin wani tafkeken daji mai tarin bishiyoyi, koramai da kwzazzabai iri-iri. Nan take sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka kafa tanti,shi kuwa Badakaren ko kallansu bai yiba bare ma ya tayasu aikin kafa tantin. kafa tantin ke da wuya sai Bawa Haluf ya je ya samo itatuwa ya hada su waje daya ya kunna wuta, suka zauna a ganwutar suna jin dimi kasancewa a wannan lokaci ana muku-mukun sanyi a wannan nahiyar da suke. Shi wannan Badakaren nan sai ya koma gefe daya ya yo zaman sa a kas y dakko casbaha ya kama lazumi. A dai-dai wannan lokaci ne sarki Sahibul Hairi ya fuskanci cewa wannan guri da suka yada zango, sansani ne na wadansu mucizai iri-iri barkatai, gasu nan a kwance ko ina babu adadi. Wasu manya wasu kananu, kafin kace me tuni mucizan sun kewa ye harabar wajen gaba daya. Ba shiri Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka dakatsalle suka haye kan bishiya, sai da suka kure can karshan bishiyar sannan suka sami nutsuwa. Dama bishiyar masu irin santsin nan ne, macizan ba za su iya tafiya a kan su ba. Shi kuwa Badakaren nan ko kadan bai yi gezau ba da ganin mucizan, sai kawai ya cigaba da karanta 'yar addu'o'insa, mucizan kuwa sukai ta kewa ye shi aka rasa guda daya wanda zai kawo masa hari. Bayan Badakaren ya gama lazuminsa, sai kawai ya kwanta bisa buzunsa, ya kama barci tamkar ma babu ko mai a kusa da shi. Mucizan suka kare zaryarsu a gefan Badakaren sannan duk suka watse suka bar wajan. Dyk abinda ke faruwa su sarki Sahibul Hairi suna makale a kan bishiyar suna kallo, dan haka suka cigaba da tsananin mamakin yadda akayi wadannan mugan mucizai suka kasa yiwa wannan Badakaren komai. Bayan tafiyar mucizan ne sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka sakko daga kan bshiyar suka tsaya a kan Badakaren suna masu mamakinsa. Bawa Haluf ya bubi sarki Sahibul Hairi Sai ya ce, " ya shugabanani ko zan so naga fuskar wannan takafarin barde mai ban al'ajabi. Wai shin ma sabo da me ya rufe fuskar tasa garemu? Sarki Sahibul Hairi ya ce, " ni kaina na kagu naga irin fuskarsa, amma tunda barci yake yanzu mai zai hana ka ya ye rawanin da ke fuskar tasa?". Koda jin haka sai Bawa Haluf ya ce, "kwarai kuwa, adin da ya kamata ke nan ayi". Kai tsaye ya kai hannu da nufin ya ye rawanin. Caraf! Sai yaji Badakareb ya cafke hannunsa ya matse da karfi. Sai da tsananin jin zafin rukon da ya yi masa bai sa'adda ya kwallara ihu, kuma ya saki fitsari a wando. Badakaren ya bude idanunsa yana mai nuna Haluf da daya hannun nasa cikian nuna alamun yi masa kashedi. Cikin rawar murya Bawa Haluf ya shiga wana yanayi yana bada hakuri Shi kauwa sarki Sahibul Hairi sai ya tuntsure da dariya da yaga Bawa Haluf ya saki futsari a wando. Ya yi kyakayatawa da dariya kamar ba zai daina ba. Koda Badakaren ya saki hannun Bawa Halufa sai Haluf ya rugo da gudu izuwa bayan sarki Sahibul Hairi ya boye tamkar zomo ya ga kare yana yiwa sarki Sahibul Hairi rada a kunne ya ce, " ya shugabana tabbas wannan ba mutun bane, domin da danke hannuna ji nayi kamar zai rugurguza min kashi. Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya sake bushewa da dariya a karo na biyu ya ce, " kai tabbas wannan Badakaren mutun ne, amma sadauki ne na gaske. Kar ka damu, wata rana zamu kara ni da shi domin na jarraba iyakar sadaukantakarsa." A wannan daji su sarki Sahibul Hairi suka kwana sannan kashe gari suka sake hawa kan aljani Dabarus ya tashi da su sama aka ci gaba da tafiya. Sai da suka shafe kwana arba'in da daya suna tafiya, su sauka nan su tashi can. Duk tsawan wadannan kwanaki su sarki Sahibul Hairi basu taba ganin fuskar wannan Badakaren ba, kuma ko wanka ya so yi baya yi a inda zasu ganshi. Koda sun bi yansa suna labewa sai su nai meshi sama ko kasa su rasa shi. Shi kansa sarki Sahibul Hairi ya tsorata da al'a,arin wannan Badakaren, burinsa kawai shi ne wani abin ya haddasa ya takaleshi da fada su gwabza domin ya gwada jarumta karsa da tasa. A ranar kwana arba'in ne cif suka iso dajin da gidan Boka Shamzabul Azwas yake. Tun daga nesa suka hango tafkeken gidan wanda girmansa ya kai na wani garin. Nan fa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka bude baki suna kallon gidan cikain tsananin mamaki da al'ajabi tamkar dan kauye ya shigo burni. Shi dau wannnan gida an gina shi ne a kan wani tafkeken tsauni mai tsawo da fadin gaske. Kuma gabaki daya gidan da wani irin murtokeken kaife aka yi shi tam kara naekakkiyar dalma. Kai inda mutun zai iya huda ginin da gatari da sai ya kwana dari yana haka a jikin ginin bai hudo karshansa ba sabo da kauri. Da saukar aljani Dabarus kan tsaunin sai ya ja da baya ya tsaya a can nesa da gidan jikin sa ya kama karkarwa, sabo da tsananin razana. Shima Bawa Haluf jikin sa ya kama kyarma, idanun sa suka zazzaro kamar ace kyat! Ya ski futsari a wando. Shi ma sarki Sahibul Hairi duk da kasancewarsa mai da kakakkiyar zuciya bai yi yun kurin komai ba, koda sauka daga kan aljani Dabarus bai yi ba sai da yaga Badakaren ya sauka ya nufi gidan Gadan- Gadan sannan ya bi bayansa rike da Gatarin Sihiri wanda ya dauko a fadar sarki Barusa. Sa'adda Badakaren ya iso daf da gaban gidan Boka Shamzabul Azwas sai ya tsaya cak ya waiga baya yana mai dubam su sarki Sahibul Hairi. Sarki Sahibul Hairi ya karasa gare shi da suri ya dube shi cikin alamun rauni ya ce, " dakata a nan indai ba so ka ke ka halaja ba. Bayan na bude mana kofar shiga gidan nan sai ku biyo bayana". Sa'adda Badakaren ya ji wannan batu sai kawai ya yi murmushi ya tsaya cak a waje daya. Sarki Sahibul hairi ya je jikin kofar da Bokan sa ya yi masa bayaninta tun kafin ya zo ya daga Gatarin Sihiri ya sara mata. Karfin saran ya cika jejin gaba ki daya yana mai amsa kuwa da firgitar da dukkan tsuntsayen dake kan bishiyoyi da duwatsu suka tashi sama farr! Ba shiri. Sa'adda kaifin Gatarin ya hadu da jikin kofar kuwa sai da tartsatsin wuta ya tashi game da gagarumin hayaki kamar ana bulbulawa wuta mai. Bayan hayaki ya tashi sai Sarki Sahibul Hairi ya ga ashe inda ya sara a jikin kofar ko kwarzane bai yi ba bare ya fashe. Al'amarin da ya mutukar razana sarki Sahibul Hairi ke nan kuma zuciyarsa ta karaya, ya dawo daga rakiyar Bokaye. A cikin zuciyarsa ya ce, "Hakika makaryaci sama da boka. Kuma duk mutumin da ya sallama imaninsa a kansu a karshe ingiza mai kantu ruwa za su yi masa ya fada cikin halaka. Yanzu gashi Bokana ya tabbayar mini da cewa da wannan gatari ne kadai zan iya sara kofar gidan nan na shiga. Akan hakan na sallamar da rayuwata dan dakko gatarin. Na sha bakar wahala da kyar na tsira da rayuwat a kokarin dakko wannan gatarin, yanzu gashi wahala duk ta zamo a banza, tun da ga gatarin ba zai iya cika mini burina ba". Wata zuciyar kuma sai ta ce da shi, "haba jarumi uban jarumai, kai kuwa daga yin sara sau daya sai ka karaya? Ai ka cigaba da jarraba balle kofar wata kila kasa mi nasara". Koda sarli Sahibul Hairi ya ci gaba da saran kofar nan babu sassautawa, tun yana yi da kuzarinsa har ya sare. A karshe ma ya fadi kasa yana haki sabo da tsananin gajiya. Koda ya dago kai ya dubi kofar da yake sara sai takai ci ya lullubeshi tamkar ya fashe da kuka. Ba wani abu bane yasa shi takaici ba face ganin cewa har yanzu ko alamar kwarzanewa kofar bat yi ba. Ba zato ba tsammani sai suka ji an bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mara dadin sauti wadda ta cika dajin gaba daya, sannan aka ce. "ya kai wannan makahon sarki wanda ya haukaceakan bukatarsa, kayi sani cewa bokan ka ya yaudareka har da yace maka Gatarin Sihirin sarki Barusa zai fasa kofar gidannan har ka shiga ka iya rabani da Alfila. Taka sani cewa duk duniyar nan babu wani mahaluki wanda ya isa ya shigo cikon wannan gidanawa, walau mutun ko aljanba tare da izinina ba. Ina mai shawartar ka da karungumi kaddara, idan ko ka ci gaba da damummu da saran kofar gidan nan zan gallakaka na hallaka abokan tafiyarka, ya kasan ce kunyi wahalar banza da tafiyar banza daga birninku. Don ko a tarihi baza a iya binciko yadda karshenku ya kasance ba". Ya yin da kakkaurar muryar ta gama wannan jawabi, sai sarki Sahibul Hairi yaji babban nadama razo masa, nan take hawayan bakin ciki ya subuto masa. Kawai sai ya sako gatarinsa a kafada ya jiyo da baya da nufin ya rungumi kaddara. Kawai sai yaga Badakaren ya sha gabansa yana yi masa nuni da ya koma da ya koma da baya shi zai bude masa kofar gidan su shiga. Kai tsaye Badakaren ya nufi wannan kofa. Shi kuwa sarki Sahibul Hairi sai ya tsaya daga baya dan yaga iyakar karyar Badakaren. Da zuwan Badakaren sai ya dafa kofar sai ya karanta wata addu'a, sannan ya dafa kofar da hannunsa na dama. Kamar a bude littafi haka kofar gidan ta bude wanwar, sai ga hanya zururu izuwa cikin gidan Boka Shamzabul Azwas. cikin tsananin mamaki sarki Sahibul Hairi ya rugo da gudu izuwa gaban Badalaren, shima Bawa Haluf ya rugo gareshi, suduka su biyun sai suka yiwa Badakaren jinjina. A sannan Sarki Sahibul Hairi ya wuce kan gaba izuwa cijin gidan. Badakaren shi kuma ya biyo bayansa, shi kuma Haluf ya take masa baya. Suna gama shiga ciki sai kofar ta rufe kanta ta mai bayar da gagarumin sautin rufewar tamkar an saki katan dutse daga sama ya fada kan dan uwansa Ko mai jarumtakar mutun da dakewar zuciyarsa in dai ya shigo wannan gida na Baka Shamzabul Azwas sai ya ji tsoro sabo da irin mugwayan halittun da aka tanada a cikinsa. Da farko sai da su sarki Sahibul Hairi suka yi tafaiya ta rabin sa'a a cikin gidan basu hadu sa qani abin tsoro ba. kwatsam sai suka ga wani jibgegen kare ya duro daga sama ya sha gabansu. Karar dirar tasa ma sai da ta firgitasu. Ya yin da ya yi haushi kuwa, sai da hantar kowanne a cikin su ta kada banda Badakaren nan. Shi dai wannan kare girmansa ya kai na katuwar giwa, yana da kawuna uku. Na daya kan batoyi nae, yana fesar da wuta kai na biyu irin na mesa ne, yan fesar da dafi. Shi kuwa kai na uku irin na zalbe ne, yana zazzago wani irin dogon harshe mai kai fin tsiya kamar zabira. da ya ke sarki Sahibul Hairi nea a kan gaba, yana ganin wannan kare mai kawuna uku, sai ya yi wuf! Sai ya daga garkuwarsa sama, sannan ya daga gataren sihiri da daya hannun nasa, nan take karan ya fesowa sarki sahibul hairi wuta da kansa na farko. .CIKIN ZAFIN NAMA YA KARE WUTAR DA GARKUWARSA. KARFIN IKAR WUTAR CE TA BANGAJE SARKI SAHIBUL HAIRI ya fadi kasa can gefe daya. Ka fin ya yunkura ya tashi kan karen na biyu ya kawo masa sara. Koda ya kare saran da garkuwarsa sai hakoran karan suka gutsire garkuwar, duk da cewar ta karfe ce, sai ga shi an wawake tsakiyar garkuwar an yi mata rami wawakeke. Cikin dimauta sarki Sahibul Hairi ya yi jifa da garkuwar. A dai-dai wannan lokaci ne daya kan karan ya zazzago wannan harshe mai kaifi mai kaifin tsiya ya kawo wa sarki Sahibul Hairi sara. Sarki Sahibul Gairi ya dada karewa da gatarin sihiri. Take gatarin ya rabe gida biyu tamkar an yanka katako da zarto. kuma duk da haka sai da haishin sai da ya laftawa sarki sahibul Hairi sara a kafada, ta ke wajan ya dare, jini ya yi tsartuwa. Sarki Sahibul Hairi ya kwarara uban ihu sabo da tsananin zugin da yaji. A lokaci guda ya sulale kasa a sume. Bawa Haluf da ke can baya da ya hango abin da yake faruwa, sai shima ya sulalea kasa a sume sabo da tsananin razana ya rage saura badakaren kadai a tsaye a gaban wannan jibgegen kare. Nan fa suka fara kallon- kallo. Sai dai Badakaren ya na tsaye a inda yake ko motsi bai yiba, kuma bai yi yunkurin komai ba. Shima karen sai ya tsaya cak! Yana jiran yaga irin yunkurin da Badakaren zai yi. Kai da ganin yadda suka kurawa juna ido kasan cewa ana shayin juna Daga can sai Bzdakaren ya far karanta addu'o'i a ransa. Shi kuwa karen sai ya fara gurnani mai ban tsoro. Ko kadan zuciyar Badakaren bata yi rawa ba, bare ya ji wani tsoro. Cikin shammace karen ya kawowa Badakaren wawan farmaki da dukkan kawunansa uku. Wato kai na farko ya feso wuta,na biyu ya kawo sara mai dafi. Shi kuwa kai na uku ya harbo harshe mai kaifi. cikin tsananin zafin nama Badakaren ya daka tsalle sama tamkar anjanye shi da kugiya, ya kau cewa duka harin guda ukun. Duk wajan da karen ya kawo hari sai kaga ya fashe kamar ansa diga an hake, kuma gagarumar wuta ta kama wajan. Durowar da Badakaren zai yi sai ya sauka akan wuyan karen, ya hau sukarsa da takobinsa ba kakkautawa amma sai ya ji kamar dutse yake suka, ko kadan tako bin bata tasiri a jikinsa. Karen ya yi ta tsalle dan ya jeho Badakaren kasa daga kansa, amma sai abin ya gagara, domin ya makakkale radau da kafafunsa. Koda ganin haka sai karen ya fita da gudu yana karo da gini domin ya watsar da Badakaren. Kai wani lokacin ma ta cikin gini yake shigewa, sai dai kaga ya fasa katanga komai kaurinta ya wuce, amma duk da haka duk da haka Badakaren na makakkale da shi ya ki fadowa Sai da karen ya shafe sa'a guda yana guje-guje da bangazar katanga suna rushewa su fado musu a jiki shi da Badakaren, amma duk a banza. Koda ganin haka sai karen ya tsaya cak ya kama a dungure a kas da murgin-murgin yana danne Badakaren da nufin ya galabaitar dashi a haka ya kakkarya masa kasusuwan jikinsa. Amma sai hakan ya zamo a banza tamkar karawa Badakaren karfi yake domin ji yake yana kara rukunkumeshi tamkar matsattsaku tamkar ta dafe a jikin mutun. Inda mutun na nan a tsaye yana kallon wannan gumurzu da ya bada labarin cewa bai taba ganin mutun mai juriya,naci,jaruntaka kamar Badakaren. Lokacin da kare mai kai uku yaga har yanzu fa bai samu nasara ba, sai ya tsaya cak a waje daya ya shiga wurkila kawunansa izuwa Badakaren domin ya kai masa farmaki. Shi kuwa Badakaren sai ya dinga naushin kawunan da dukkan karfin dantsansa cikin zafin nama. Karfin naushin ne ya haukata karen ya yi ta haushi mara dadin ji. Kafin a jima Badakaren ya kumbura fuskokin karen sun duri jini. Ba shiri karen ya daina gani sosai, idanuwansa duka sun junbura sun yi luhu-luhu. Take jikin karen ya yi tsami ya sulale kasa. A sannan Badakaren ya sauka daga kan karen domin a tsammaninsa ya samo lagwan karen, ashe karen lambo ya yi. Koda jin Badakaren ya yunkura, cikin zafin nama ya daka tsalle sama da nufin ya yi dirar mikiya akan Badakaren. Hucin iskar karen ce ta doko dodan kunnnan Badakaren ya farga da farmakinsa, don haka sai shima ya juya cikin zafin nama ya sunkuya kasa. Kafin karen ya shallakeshi sai ya ruko kafafuwansa na baya da hannayaensa biyu. Take ya wujijjiga karen sama cikin iskakai ka ce mage yake wulwulawa, duj da cewar girman karen ya kai na giwa. Tabbasa sadaukantakar Baiwa ce, ba girman jiki ba. Idam mutun ya dubi girman karen kyma ya dubi kankantar Badakaren sai ya rantse cewar idan karen ya danneshi jo shurawa bazai yi ba zai zamo gawa. Amma sai gashi Badakaren yana hajijiya da karen a sama. Sai da Badakaren ya wulwula karen sau arba'in sannan ya damfara shi a kan dirkar ginin. Take kawunan karen duka ukun suka dagwargwaje, jini ya kama malala yana gudu tamkar an bude ruwan fanfo. A sannan Badakaren ya koma da baya a guje izuwa inda ya baro su sarki Sahibul Hairi a sume. Da zuwa sai ya iske sarki sahibul Hairi a kwance yana nunfashi sama-sama, kuma har yanzu jini yana zuba a kafadarsa. Cikin hanzari Badakaren ya daure masa kafadarsa tamau da wani mayafi, sannnan ya karkata jarkarsa ta ruwa ya yayyafawa sarki Sahibul Hairi ruwan. Take sarki Sahibul Hairi ya farfado. Koda ya bude idanunsa yaga Badakaren a tsaye a kansa kuma a raye sai ya cika da tsananin mamaki ya ce, "in wannan shirgegen karen yake?". Maimakon Badakaren ya bude baki ya amsa wannan tambaya sai ya tashi sarki Sahibul Hairi tsaye ya jashi suka tafi izuwa inda gawar karen take, yana nuna masa ita. Ya yin da sarki Sahibul Hairi ya ga irin motsuwar da karen ya yi, sai ya kurawa Badakaren idanu cikin matukar al'ajabi. Nan take sarki Sahibul Hairi ya raina kansa, kuma ya raina duk

Chapter 9 of 19