Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suka shafe awa uku cur suna dauki back dadi dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar daya ba. A daidai lokacin ne Sarki Sahibul Hairi, Bawa Haluf, Gwaggwan birin da Alfila suka gama kashe gaba dayan halittun. Koda suka hango mugun artabu da akeyi tsakanin Humaira da Sarki Barusa sai hankalinsu ya dugunzuma ainun. Nan take sai Sarki Sahibul Hairi ya ce "ya kamata mukaiwa Humaira dauki domin Ina ganin cewa bazata iya hallaka Sarki Barusa back". Koda jin haka sai Bawa Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi cikin damuwa ya ce, "ya shugabana shin kamanta Humaira ta gargademu da cewar Kada mukuskura mutari sarki Barusa idan ana wannan gagarunin yaki? Ai kawai muci gaba da zuba ido domin muga abin da zai faru". Koda jin haka sai sarki Sahibul Hairi ya zauna kasa durshan ya city gaba da ganin artabun Humaira da sarki Barusa. Alfila kuwa sai ta ci gaba da zamanta akan wannan doguwar bishiya. Ya yin da sarki Barusa da Humaira suka ga sun shafe wannan lokaci suna kaiwa juna sara da suka ba tare da samun nasarar komai ba sai suka ja da baya suka yi carko-carko kamar zakaru sun haki da kallon juna. Tsawon 'yan dakika suna tsaye a haka sai sarki Barusa ya fara amfani da karfin tsafi ya watsowa Humaira garwashin wuta mai yawa. Kafin garwashin wutar ya zuba a jikinta tuni ta kama karanta wadansu addu'o'i na musamman na neman tsari. Duo garwashin da ya ta6a jikinta sai ka ga Kamar a cikin ruwa ya fada. Nan take garwashin wutar zai mutu ya fado kasa a jike. koda ganin haka sai ya sake yin wani tsafin ya watsa ma ta 6angorin kankara mai tsananin sanyi. Duka kankarar da ta ta6a jikinta sai ta narke ta zama ruwa mai dumi. Haka dai sarki Barusa ya yi ta jefawa Humaira mugayan abubuwa iri-iri har kala Dari ba daya amma bai sami nasar komai ba. Al'amarin da ya mutukar fusatashi Kenyan ya kara kwarara uban ihu a karo na uku sannan ya yi jifa da takobin hannunsa ya gyara tsayuwarsa gami da dunkule hannayansa yana mai nuni da su. Koda ganin haka sai itama Humaira ta gyara tsayuwarta Kumar ta dunkule hannayanta. Sarki Barusa ya dubi Humaira ya yi murmushi ya ce, "idan ina son na tabbatar da ce wa za ki yi wan an gumurzu ne zallan karfin dantsenki said dai ki cire wannan damara da me kugunki saboda na San cewa darajarta ne kika iya samun Laguna". Koda jin haka sai Humaira ta sa hannu zata kwance damarar da ke kugunta. Cikin tsawa sarki Sahibul Hairi yace da ita, "kada kiyi hakan. Lallai sarki Barusa yana son ya yaudareki ne ya sami nasara akanki. Idan har yana ganin damarar ce abin dogaranki me yasa shima bai mallaki damarar ba? ai kar6ar wannan damara a hannun mai ita sai cikakken jarumi mai sadaukantaka ta ban al'ajabi". Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta ce, "kaji abin da sarki Sahibul Hairi ya fadi, me zaka iya cawa?" Sarki Barusa ya bushe da dariya sannan ya ce, "ai bada tsagwaran karfin damtsanki kika kar6i damarar ba a hannun Shamzabul Azwas face kin yi amfani da Marfin sihiri irin naku na ma'abota addinin musulinci. Humaira ta ce, "ai mu bama da wani sihiri face taimakon Ubangijimmu." Barusa ya ce, "haka dai kika ce, amma ban yarda ba. idan Ubangijin naki ne yake baki sa'a ki cire damarar mana na gain". Kafin sarki Barusa ya gama rufe bakinsa tuni Humaira ta kwance damarar daga kugunta ta ajiyeta gefe daya. Nan take ta shiga kiran sunayan Allah tsarkaka a cikin zuciyarta tana mai Neman taimakon Ubangiji". Koda sarki Barusa ya ga Humaira ta kwance wannan damarar ta ajiye a gefe daya sai ya bushe da dariyar farin ciki, sannan ya ruga gareta da dukkan karfinsa cikin mugun nufi. Ita Kuwa ta tsaya cak tana jiran karasowarsa harya iso kusa da ita ko gezau ba ta yi ba. Sarki Barusa ya kawo mata wawan naushi a fuska da dukkan karfinsa. Ko kaucewa bata yi ba, Hannun nasa na naushin fuskarta sai yaji kamar dutse ya nausa, kuma yaji kamar 'yan yatsun hannunsa sun karye. Basan sa'adda yayi kara ba gami da yarfar da hannu ya ja da baya cikin tsananin mamaki da firgici. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf , Alfiya da ke can gefe daya suma kallo suma sai da suka cika da tsananin mamaki bisa ganin abin da ya faru. Jaruma Humaira ta kalli Sarki Barusa cikin murmushi ta ce, "yanzu gashi na ajiye damarar da kake tunanin da ita nake dogaro kuma na sami sama da karfin da nake da shi. Sirrin shi ne, na karanta addu'ar da keep jikin wannan damara ne na naimi taimakon Ubangijina. Ita kuwa wannan addu'a ba komai bace face wadansu ke6antattun sunaye tsarkaka na Ubangiji wadan da bakowa ne ya san su ba. Idan kayi imani da abin da name fada yanzu ka tuba ka daina shirka da tsafi ka kar6i addinina kuma mukoma kasarka ka kaddamar da addinin nawa ga jama'arka Idan kuwa ka ki ni da kai babu sauran sulhu sai dai mu ci gaba da yaki har dayammu ya ga bayan daya. Koda jaruma Humaira tazo nan a zancenta sai sarki Barusa ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya tur6ne fuska ya ce, "Ai ni tsakanina da ma'abota addinin musulunci sai yaki. Ina son kisani cewa iyaye na da kakannina duk sun shude bisa tafarkin tsafi don haka babu wani dan zamani da ya isa ya gusar dani daga kanwannan tafarki na iyayena wanda nai imani da shi dari bisa dari. Dan haka ga maza nan bisa kanki yarinya komai shaidancinki sai naga bayanki". Koda gama fadin haka sai sarki Barusa ya durkusa ya dauki takobinsa ya tafi izuwa kan jaruma Humaira yana wani irin ihuda ruri mai firgitarwa. Hatta kasar wajan sai da ta kama motsi kamar zata rufta. Tsuntsaye da ke sama kan bishiyoyin kuwa suka kama yin hijira. Wannan abu kuwa ya daurewa such sarki Sahibul Hairi kai shi ne, Jaruma Humaira dai ko motsi ma batayiba bare ma ta Naomi takobinta ta dauka amma bakinta na ta motsi alamar cewa tana karanta addu'ointa. Ai kuwa sarki Barusa na isowa daf da ita sai ya kai mata wawan sara a weya da nufin ya tsage mata kai, cikin zafin nama ta kare saran da hannunta. Take takobin ta 6alle gida biyu, al'amarin da ya mutukar razana sarki Barbuda ke nan ya juya da baya da sauri domin ya ruga da gudu, amma sai Jaruma Humaira ta shako wiyansa ta baya da hannu biyu tayi hajijiya da shi sannan ta dagashi sama tayi filfilwa da shi ta kwala da kasa. Sarki Barusa ya baje a kasa a lokacin da yaga taurarin wuya a idanunsa kuma jiri ya kwashe shi ya yunkura da nufin ya mike tsaye amma sai ya Ji ya kasa. Humaira ta kafarta guda ta take wuyan sarki Barusa. Nan take ya fara kakarin mutuwa, wani irin jini ya fara fitowa ta cikin kofofin hancinsa. Koda ganin halin da sarki Barusa ya shiga sai Humaira ta fara jin tausayinsa ya dan darsu a zuciyarta, dan haka sai ta dan durkusar da kanta kasa dai-dai fuskarsa ta ce, "ya kai wannan sarki, idan har za ka yi imani da Ubangijina a yanzu zan Dauke kafata data kan wuyanka domin ka ray. Koda jin wannan batu sai sarki Barusa ya tofawa Humaira jinin bakinsa ya dubeta cikin tsananin kiyayya da fushi ya ce, "Had abada ba zan kaunaci addininki ba domin na tsaneshi fiye da yarda na tsani mutuwata. Kawai ki kashe ni shi ne abin da zai fiye miki alheri domin ba zan ta6a daina adawa da Ku ba har na mutu zan kasance a cikin tunanin kawar da addininku". Koda jin wannan batu sai zuciyar Humaira ta kama tafarfasa kamar zata kone ta dubi sarki Barusa taga ya yi mata muni tamkar dodo, kawai sai ta kama kansa da hannayanta biyu ta murde masa wuya. Sai da karar karyawar ta cika dajin gaba daya. Nan take sarki Barusa ya zama gawa ko motsi bai kara yi ba. Humaira ta mike ta nufi inda sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suke tsaye a lokacin da suka kura mata idanu suna yi mata jinjina bisa ganin gagarumar bajinta da tayi ta ban al'ajabi. A dai-dai wannan lokacine yarinya Alfila ta sakko daga kan wannan doguwar bishiyar da ta hau. Humaira na isowa daf da su sai ta tsaya ta dubi sarki Sahibul Hairi ta ce, "yanzu mun rage daya daga cikin manyan abokan gabarmu saura guda daya wanda yafi kowanne hadari" Cikin mutukar mamaki sarki Sahibul Haiti ya dubi Jaruma Humaira ya ce, "wanene Kuwa wanda ya fi sarki Barusa a garemu?" Humaira tayi murmushi ta ce, " ba wani bane face matarsa Gimbiya Shukura. Ka sani cewa ita mace ce Kuma bata da burin da ya fi a yanzu ta illa ta mallaki yarinya Alfila domin ta hada sihirin da za ta iya mallakar duniya. Tabbas sai munyi da gaske wajan kula da Alfila domin nasan cewa a ko yaushe Gimbiya Shukura zata iya shammatarmu, ta zo ta saceta. yanzu dai babu abin da ya kamacemu face mu hanzarta kai Alfila wajen mahaifinta domain na kawo karshen tafiyata da ku. Koda gama jin haka sai Jaruma Humaira taji sarki Sahibul Hairi ya kirawo sunanta. Cikin mamaki itama ta juyo ta dubeshi, sarki Sahibul Hairi ya ce, "kin manta da waccan Damarar". Koda jin haka sai Humaira ta dubi can inda Damarar take sannan ta dubi Alfila ta ce, "ya ke 'year uwata maza ki ruga inda Damarar take ki daukota muci gaba da tafiya". Cikin hanzari kuwa Alfila ta ruga da gudu taje ta dauko wannan Damara ta kawowa Humaira tana mai mika mata. Humaira bata kar6i damarar ba sai ta dubi Alfila ta ce, "daura a kugunki tunda kema yanzu kina da ikon daurawata tun da kema musulmace". Ba tare da gardamar komai ba kuwa Alfila ta daura Damarar a jikinta. Faruwar haka ke da wuya sai Alfila taji wani irin gagarumin karfi ya shigeta kamar zata iya daga gammo tayi dakon duniyar gaba daya amma sai tayi shiru da bakinta bata fadawa kowa sauyin yanayin da taji ba. Nan fa aka ci gaba da tafiya ba sassauci, domin tun kafin a fara tafiyar Humaira ta gayawa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf cewa su tabbatar da cewa sun bita sahu da sahu, duk inda ta dauke kafarta to su sa ta su. Ai kuwa ba su yi sanya ba said suka dinga binta sau da Kafa. Humaira ta ci gaba da tafiya tana mai karanta wadansu addu'o'i na musamman, nan da nan su sarki Sahibul Hairi suka ga tafiyar ta su tana mutukar sauri tamkar a sama suke yinta bisa aljani saboda gani suke suna ta gifta dazuzzuka Tamar walkiya. Nan da nan suka sun shafe tafiyar sa'a bakyai a rabin sa'a. Tun safe suka fara tafiya, amma basa tsayawa face idan lokacin sallah ya yi. Sannan Humaira da Alfila suka yi Alwala suka gabatar da sallah sai suka ci gaba da tafiya. Bisa mamaki sai suka ga har sun gifta ta manyan garuruwa guda biyu. Daf sallar magariba suka isa birnin su Alfila. Koda Alfila ta fara hango gine-ginen garunsu sai farin ciki mara misaltuwa kuma ta cika da mamaki yadda aka yi suka shafe wannan doguwar tafiya. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf kuwa dama tun sa'adda suka ga yadda Humaira ta sami nasara akan sarki Barusa sai suka tsinke da al'amarinta kuma suka Jim zuciyoyinsu sun fara gamsuwa da gaskiyar addininta gamma saboda burin da ke zuciyarsu bass son su yi saurin nuna yardarsu don Kara burin nasu ya tarwatse. Da isowar su Humaira kofar garin sai suka iske kofar a kulle, masu gadi kimanin dakaru arba'in na tsaitsaye a bakin kofar birnin sun yi shirin yaki kowannansu na rike da makami sai muzurai suke kamar za su ci babu. Da yake Humaira ce a kangaba sai ta dubi masu gadin ta ce, da su "ku bude mana kofa mu shiga birnin ku, mu bakine na salama kuma mun zo muku da alheri". Koda jin haka sai shugaban dakarun wani narkeken kato mai kirar mutanan farko ya dubi Humaira ya ce, "Sarkin mu bamamu umarni kada mubudewa bako kofa ya shigo. Wannan karamar yarinya da Luke tare da ita kadai zamu iya budewa ta shiga domin itace 'yar gari". Sa'adda Humaira taji wannan batu sai ranta ya 6aci, kawai sai ta juya ta kalli Alfila ta ce, "ya ke 'yar uwata jeki ciki ki sadu da mahaifinki, ki bashi labarinmu in ya so shi yazo ya shigar damu cikin birnin naku idan sarkin naku ya bashi izini". Alfila ta yi murmushi ta ce, "angama ya 'yer uwata". Koda fadin haka said masu gadin kofar suka bude kofar, Alfila ta shiga ciki tana ta waigen Humaira kamar zata yi kuka, kai da gani kasan ba a son ranta aka yi haka ba, taso a ce anbar such Humaira sun shigo cikin garin gaba daya. Alfila na shiga cikin birnin sai masu gadi suka mai da kofa suka rude. A lokacin Humaira da sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka raka6e a gefe daya suka zauna domin su huta a lokacin ne hira ta fara wakana tsakanin sarki Sahibul Hairi da Humaira inda ta dubeshi ta ce, "Amma fa nayi mamakin irin wannan doka. Akan wana dalili sarkin wannan gari zai kafa dokar cewar baki baza su shiga garinsa ba. sarki Sahibul Hairi ya yi ajiyar zuciya ya ce, "ni kaina na yi mamakin wannan al'amari, amma babu mamaki akwai mugun abu da wani bakon ya zo ya yi, kin san ance wake daya 6ata gari, babu mamaki wani bakon ne ya shafa mana kashin kaji."SARKIN SARAKAI Littafi Na Biyar (5) Part B. . Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa.. HUMAIRA TA YI AJIYAR ZUCIYA SANNAN TAYI SHIRU NA DAN WASU DAKIKOKI KADAN SANNAN TA CE, " YA KAI WANNAN SARKI SHIN HARYANZU BAKA YANKE SHAWARA BANE a zuciyarka bisa kar6ar addinina? Ka sani cewa nifa na gaji yin wannan tafiya tare da ku, in da back don ina kwadayin in ga ka kar6i musulinci ba da tuni mun rabu. Ba komai ne yasa kaga ina so ka sami wannan babban rabo ba face saboda naga cewa kai adalin mutunne mai tausayi da jin kan talakawa Kuma kasar ka ta kunshi muliyoyin al'umma. Idan ka kar6i addinin musulinci tamkar muliyoyin jama'a sun kar6i addinin ne. Sa'adda Humaira ta zo nan a zancenta sai sarki Sahibul Hairi yai ajiyar zuciya gami da Sunkui da kansa kai sannan ya dago ya dubeta cikin alamun tsananin dimuwa ya ce, "ya ke wannan jaruma mai karamci da ban al'ajabi kiyi sani cewa na sha bakar wahala tun daga lokacin da na baro kasata har name gamu da ke kawo i yanzu kuma gashi har yanzu abin da na fito dominsa ban samu ba Zuciyata ta kwadaitu da son ganin 'yammata ukun da aka ce sai na auresu sannan burina zai cika. Yanzu gashi har nazo garin su sadauki Awaisu wanda shine kadai mutumin da zai iya kai ni inda wadannan 'yan mata uku suke. Yanzu fa idan na kar6i addininki shi ke nan ba zan ta6a ganin wadannan 'yan mata ba har abada. Saboda me zan bar wannan dama ta wuceni alhali aski ya zo gaban goshi saura kiris ya kammalu". Sa'adda jaruma Humaira taji wannan batu sai takaici ya kamata, zuciyarta ta yi bakikkirin nan take taji tayi nadamar biyo sarki Sahibul Hairi tun daga kasarta domin Jan hankalinsa izuwa addinin musulinci tun da gashi har yanzu ya ki kar6ar addinin duk da cewar ya ga abubuwan al'ajabi na gas gata Allah". Cikin tsananin fushi Humaira ta kalli sarki Sahibul Hairi ta ce, "Ai shi ke nan ni dai na gama cika nawa aikin kuma lallai a yau ne zan rabu da Ku. Abin da ya tsai dani kawai a nan shi ne, na tabbatar cewa Alfila ta sadu da mahaifinta kuma ina kwadayin na ga mahaifin Alfila shima ya kar6i addinin musulinci kamar yadda 'yar sa ta kar6a. Lallai zan so na gana da shi domain naga inda ra'ayinsa ya karkata. Idan har sadauki Awaisu ya kar6i addinin musulinci, sarki garin nan ma zai iya kar6a, idan kuwa sarki ya kar6a tamkar mutanan birnin ne gaba daya ne suka kar6a. Wannan shi ne iyakar Burina". Koda jin wannan batu sai hankalin sarki Sahibul Hairi ya dugunzuma yai shiru ya rasa abinda zai ce da Humaira, ya sunkwi da kansa kasa yana tunani. Babban abin da yasa hankalinsa ya tashi shi ne, jin cewar a yau ne Humaira zata rabu da shi. Nan take sarki Sahibul Hairi ya ji kamar ya fashe da kuka domin kauna da bergen Humaira ne ya taso masa ya cika masa zuciya, kuma ya rasa abin da ke masa dadi. Shima Bawa Haluf sai ya ji ya kamu da tsananin damuwa kamar roki Humaira akan ta ci gaba da zama tare da su har izuwa lokacin da maigidansa zai cika burinsa, amma sai ya kura ma ta idanu kawai ya kasa cewa komai. Ya yin da Humaira taga Bawa Haluf ya kura mata idanu sai ta daka masa harara ta ce, "kai kuma fa lafiya ka kura mini ido haka? ko kuwa baka ta6a ganina bane sai yau". Koda jin wannan tambaya sai Bawa Haluf ya yi murmushi ya ce, "ki gafarcene ya shugabata wani Abu na tuno wanda me da sarkina kuka manta da shi." Cikin mutukar mamaki Humaira ta ce, "wana abu ke nan"? Bawa Haluf ya ce, batun goggon birin da ya taimaka mana a yakin da mukayi da sarki Barusa. Tun sa'adda muka gama yakin bamu sake ganinsa ba, kuma dayanmu baiyi zancensa ba. shin an kasheshine a wajan yakin ko kuwa sulalewa ya yi yayi tafiyarsa bamu sani ba ko ya ya?" Koda jin wannan batu sai Humaira da sarki Sahibil Hairi suka kalli junansu cikin tsananin mamaki sannan sarki Sahibul Hairi ya ce, "Hakika Haluf maganarka gaskiyace, domin duk mun sha'afa mun manta da batun wannan biri, amma ni a tunanina wannan birin ya mutu domin kuwa inda yana raye bazai daina biyomu ba, said dai idan ya koma wajan 'yan uwan sa inda ya fito". Humaira tayi ajiyar zuciya ta ce, "ai wannan biri bazai koma inda ya fito ba, domin idan ya koma wajansu kasheshi zasuyi tunda sun san cewa ya za6imu a Kansu. Ni dai abinda nake zargi shine, lallai an kasheshi a lokacin da Mike wannan yaki amma Kuma abin mamakin shi ne bamu ga gawarsa ba a wajan". Koda gama fadin haka sai Humaira ta kashingida saboda gajiya tayi shiru bata kara cewa komai ba. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka yi shiru basu kara cewa uffan ba. WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU GA SU SARKI SAHIBUL HAIRI BAYAN DA JARUMA HUMAIRA TA KAWOSU GARIN SU ALFILA A CIKIN KANKANIN LOKACI BISA TAIMAKON ALLAH. Al'amarin yarinya Alfila kuwa, lokacin da aka bude mata kofar garinsu ta shiga sai ta nufi izuwa hanyar gidan mahaifinta sadauki Awaisu cikin farin ciki tana dokin ta isa ta sadu da shi. A sanin Alfila daga bakin kofar garin zuwa gidansu tafiyace ta a kalla sa'a uku, amma bisa mamaki sai taga ta share tafiyar a cikin abin da wuce wadansu 'yan dakiku ba. Al'amarin da ya matukar ba ta mamaki ke nan. Abin da ta manta shine, wannan damara ta Shamzabul Azwas tana nan a daure a kugunta. Sa'adda Alfila ta isa kofar gidan mahaifinta sai ta iske gidan a kulle kuma dakarun sarki sama da mutum dubu sun kewaye gidan sai muzurai Duke. Al'amarin da ya mutukar bata mamaki ke nan, jikinta ya yi sanyi, kuma hankalinta ya duguzuma ainun. Alfila ta karasa da sauri zawa ga dakarun ta Dubi daya daga cikinsu ta ce, "mene ne yake faruwa ne, ina mahaifina?" Koda jin wannan tambaya sai badakaren nan ya dubeta cikin tsananin tausayi ya ce, "ya ke Alfila ai tunda aka saceki mahaifinki ya kamu da rashin lafiya saboda bakin cikin rabuwa da me da sanin cewa bazai iya zuwa inda kike ba ya Kar6oki. Bisa wannan dalili ne ya kwanta rashin lafiya kullum sai dai a kwantar a tayar. Babu irin kokarin da 'yan uwansa basu yi ba na nema masa magani amma abun sai ya ci tura. Kinsan cewa mahaifinki shine sarkin ya ki a garin nan kuma sarki na mutukar kaunarsa bisa hakanne sarki yasa aka daukeshi aka kaishi can gidan sarauta domin ya yi jinyarsa da kansa kuma ya umarcemu da muyi gadin gidan naku saboda kin san cewa akwai tarin sirrikan tsafinsa a cikin gidan Wanda duk duniya babu kamarsu. an ce ke kadai kike da irin sirrikan tsafin a jikinki" Lokacin wannan badakare ya so nan a zancansa sai hankalin hankalin alfila ya dugunzuma fiye da ko yaushe, nan take hawaye ya zubo mata, tai shiru tana tunani. Babban abinda ya tayar mata da hankali shi ne, a iya saninta da mahaifinta bai ta6a zuwa gidan sarki ba. Koda yaki za'a fita sai dai a tura a gaya masa ya shirya ya taho a hadu da shi a filin daga. Asalin sadauki Awaisu shima dan gidan sarauta ne kuma ubansu daya da sarkin garin, amma ko kadan shi baya sha'awar harkokin sarauta. A rayuwar sadauki Awaisu shi ba shi da wani buri wanda yafi ya gawurta a harkokin tsafi da jarumta a duniya, amma ko kadan dukiya da mulki basa gabansa. Sarkin garin da sadauki Awaisu su kadai ne 'ya 'ya a wajan mahaifinsu, amma awaisu ne babba tun mahaifinsu yana da rai Awaisu ta ce shi bazaiyi sarauta ba ya barwa dan uwansa kuma tun daga sannan ya hada nasa i nasa ya bar gidan sarautar ya gina nasa a can bayan gari ya tare. A wannan lokaci mahaifiyar Alfila na dauke da cikin Alfila. A ranar da ta haifi Alfila ne ta mutu. Alfila ta taso bata San kowa ba sai mahaifinta da kuma hadimansa. Sa'adda ta fara girma ne ya bata labarin mahaifiyarta da kuma labarin dangantakarsa da gidan sarauta. Koda sau daya bai ta6a daukarta ya kaita gidan sarautar kuma shi sarki ba a garin bai ta6a zuwa gadansu ba a matsayin ya kawo ziyara ga dan uwansa Wata rana Alfila ta dubi mahaifinta Sadauki Awaisu ta ce, "ya abbana ka gaya mini cewa sarkin garin nan dan uwanka ne to me yasa baka zuwa wajansa shi ma baya zuwa wajanka?" Lokacin da yaji wannan tambaya sai ya sunkwi da kansa kasa ya yi shiru kamar banzai ce komai ba, sannan ya yi ajiyar zuciya ya dago ya dubi Alfila ya ce, "ya ke 'yata abar soyuwa a cikin raina kiyi sani duk ranar da naje gidan sarki ko kuma shi yazo gidana to daga wannan rana sai daya data cikinmu ya rasa matsayinsa. ko dai ni na rasa dukkan sihirin tsafina ko kuma shi sarki ya rasa mulkinsa. Sa'adda Alfil ta zo dai-dai nan a tunaninta said zuciyarta ta buga da karfi, domin tasan dolane cikin biyu dolene ayi daya. Ko dai mahaifinta ya rasa dukkani. sihirin tsafinsa ko Kuma sarki ya rasa karagarasa. Nan take taji bata gamsu da bayanin da wannan badarakare ya yi ma ta ba sabo da haka sai ta juya da gudu ta nufi hanyar da za ta kai ta gidan sarautar garin. Nan da nan kuwa Alfila ta isa kofar gidan sarautar. Da zuwa sai ta iske mahaifin ta tsaye a kofar gidan idanun sa sharkaf da hawaye ya kura mata idanu. Al'amarin da ya mutukar girgizata Ke nan ta cika da tsananin mamaki ta tsaya cak! daga nesa suna kallan juna tace a ranta, "ya ya mutunin da aka ce da ita yana kwance magashiyan bashi da lafiya kuma gashi yanzu a tsaye a gabanta bisa duga-dugansa. Kuma ina dalilin zubar da wannan hawayen a idanunsa ko kuwa name farin cikin ganinta ne? Alfila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta kuma ta kasa baiwa kanta amsa. Koda Sadauki Awaisu yaga Alfila ta tsaya a nesa ta ki karasowa gareshi sai ya durkusa bisa gwiwoyinsa ya bude hanyansa ya ce, "Rugo gareni ya ke 'yata na ji ki a kirjina ashe zamu sake saduwa a wannan duniya?. Rugo gareni ya ke rabin jikina, rabin ruhina Kuma cikamakin Burkina". Koda jin haka sai Alfila ta ruga da gudu saboda ta San cewa mahaifinta ne kadai yake mata irin wannan furuci. Sai da ya rage saura kiris ta isa gareshi sai taga ya 6ace daga inda yake durkushe ya bayyana a bayanta yana mai kyalkyala dariya. Al'amarin da ya mutukar firgita Alfila ke nan ta juya a tsorace ta dubi Awaisu ta ce, "wanene kai ina mahaifina take?" Koda jin wannan tambaya sai Awaisu ya rikide koma gimbiya Shukura matar sarki Barusa tana kyalkyala dariya. Daga can kuma sai ta murtuke fuska ta dakawa Alfila tsawa ta ce, "ke yarinya kiyi sani cewa rayuwar mahaifinki da ta dan uwnsa duk suna hannuna Idan kina so su tsira da rayuwarsu to ki big dukkanin umarnina. Ki sani cewa a halin yanzu mulkin wannan gari a hannuna yake domin nazo na yaki garin nan gaba daya ni kadai na ci su da yaki". koda jin wannan batu sai Alfila ta tsandara ihu ta ce, "ya ke wannan hatsabibiya ki sani cewa karyarki ta sha karya domin baki isa kiya yaki da mahaifina ba har ki cishi da yaki domain duk abinda kike takama da shi ya Fiji." Shukura ta bushe da dariya sannan ta hade fuska ta ce, "Ai ba fito na fito mukayi da shi ba, kamar yadda na yaudareki a yanzu haka na yaudari Kowa a garin nan na ci su da yaki. Yanzun nan zan nuna miki halin da mahaifinki yake ciki. Idan kika bi umarnina ya ku6uta, Idan kuwa kika bijire mini ya hallaka. Koda gama fadin haka sai sukura wuce izuwa cikin gidan sarautar, Dakaru suka rinka ratsewa suna bata hanya cikin dari-dari. Alfila ta bita a baya har suka shiga cikin turakar sarki. Babu abinda ya daurewa Alfila kai face yadda daya Dakarun gidan hadimai ki ta ratsewa shukura cikin girmamawa tamkar itace sarkin birnin. Alfila ta tambayi kanta cikin zuciyarta ta ce, "wai shin gimbiya shukura da karfin tsiya ta kar6i birnin ne ko kuwa da karfin sihiri?" Amsar da ta kasa baiwa kanta ke nan. Da shigarsu cikin turakar sai Alfiya tayi arba da mahaifinta sadauki Awaisu kwance akan gado an daureshi tamau da wata irin sarkar tsafi wacce ta kanannade jikin gaba daya tana ta zagayeshi. A 6angaren kudancin dagon da yake wani gadon ne daban sarkin garin na kwance shima an daureshi tamau da irin wannan sarka. Koda shukura tayi nuni da hannunta izuwa kan sadauki Awaisu sai sarkar tsafin ta daureshi tamau ya kwalla ihu sakamakon zafin da yaji tamkar kasusuwan jikinsa za su kakkarye. Gimbiya shukura ta bushe da dariyar mugunta ita kuwa Alfila ta ruga da gudu izuwa kan mahaifinta ta rungumeshi kuma ta fashe da kuka tana mai duban shukura ta ce, "ya ke

Chapter 16 of 19