Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bayan dana ga yaata alfila sa adda ta kwanta a kaina tana kuka sai hankalina ya gushe sakamakon azabar da shukura tayi mini ta matse mini jiki da sarkar sihiri har kafata ta karye koda fadin haka sai duk suka dubi kafar awaisu sukaga har ta kumbura nan take sarki ya kwallawa wani hadiminsa kira ya shigo cikin turakar da shigowar hadimin sai sarki ya daaka masa tsawa yace duk ina dakarun gidan nan suke har wata matsafiya ta shigo ta kamani ta daureni basu sabi ba hadimin ya risina yace ya shugabana ai mu bamu ga kowa ya shigo gidan nan ba kuma kullum kai muke gani kana harkokinka kamar yadda ka saba koda jin haka sai sarki ya sake cika da mamaki ya tsinke da al amarin hatsabibancin gimbiya shukura ba tare da bata lokaci ba aka tura aka kirawo likita yazo ya gyara karayar sadauki awaisu sannan likitan yaje ya duba sahibul hairi da bawa haluf suma yayi musu magani aka kaisu masauki mai kyau, sai da su sahibul hairi suka kwana goma sha tara suna jinya sannan suka sami lafiyar jikinsu sosai A wannan rana ne sarki yasa aka yi shela gaba daya jama ar garin suka taru a fada nan take sarki ya baiwa jama alabarin sarki sahibul hairi tun daga lokacinda ya baro kasarsa domin neman matsayi da daukaka har izuwa lokacin da ya hadu da gimbiya humaira a can garinsu suka dunguma suka tafi fadar shamzubul azwas da duk irin fafatawar da sukayi har suka iso wannan gari suka yi bakin gumurzu da gimbiya shukura har ta sake guduwa tare da Alfila lokacin da sarki ya gama bayar da wannan labari sai gaba dayan mutanen garin jikinsu yayi sanyi nan take kowa yayi imani da addinin musulunci sarki sahibul hairi ne ya karanta kalmar shahada sannan gaba dayan jama ar garin suka maimaita farin ciki a wajen gimbiya humaira a wannan rana ba zai misaltuba bayan an kaddamar da addinin musulunci ne a kasar humaira ta shiga koyar da jama a yadda zasu bautawa allah sai da ta shafe kwana bakwai tana wannan hidima sannan aka sami masu basira suka lakanci abin da ta koya musu suma suka dinga koyar da wasu A wannan lokacine sadauki awaisu, sahibul hairi da bawa haluf suka yi zama na musamman suka shiga tattaunawa akan yadda zasu tafi neman yarinya alfila domin suyi gumurzu na karshe da gimbiya shukura suga bayanta a sannan ne sarki sahibul hairi zai sami damar komawa kasarsa ya jaddada addinin musulunci ga jama arsa daga nan kuma sai su tafi izuwa garinsu gimbiya humaira domin ya nemi auranta a wajan iyayanta sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun damuwa yace yake abar kaunata yanzu tayaya kike ganin zamu iya zuwa inda shukura takai alfila harmu yaketa mu karbo alfila? Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya tace babu wanda zai iya yi mana jagora izuwa wannan tafiya face Allah domin don haka zamu rokeshi akan ya taimakemu kuma ya bamu sa'a bisa abindake gabanmu , bawa haluf yai ajiyar zuciya yace a gaskiya ni dai na tsorata da al amarin gimbiya shukura kuma ina tsoron karonmu da ita na biyu domin na tabbatar dacewa shirin da zatayi yanzu kanmu sai ya ninka na baya sau dari AA Misau Kenan Sunana, Sa adda humaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai duk shirin da shukura zaatayi ba zata sami nasara akanmu ba tunda dai mu akan tafarkin gaskiya muke ita kuwa akan tafarkin karya take duk abinda take takama dashi kafin ita anyi manyan kafirai a duniya wadanda sukafita komai da komai, amma a karshe sai da suka wulakanta suka zama mushe ina tabbatar maka da cewa babu wani abu madawwami face Allah Sarki guda daya wanda bashi da abokin tarayya shine wanda ya halicci sammai da kassai da duk abubuwan dake cikinsu kunga kenan shine mai ikon Tafiyar da mutane da aljanu a doron kasa da izininsa ne kowa ke yin abinda ya ga dama idan Allah ya so ya kawar da mutum ko aljan take yake kawar dashi sai dai kawai ayi masa jinkiri izuwa iyakar wa adin da aka diba masa zaiyi a duniya lokacin da humaira tazo nan a zancenta sai taga sarki sahibul hairi da sadauki awaisu sun fara hanmma alamar cewa suna jin barci Don haka sai tayi shiru ga barin zance tace ya kamata mu tsaya a nan sai wani lokaci kuma idan mun sami dama saimu cigaba da wannan labari Kuma ku sani cewa a daren yau zanyi Addu a da rokon Allah Akan yayi mana jagora bisa tafiyar da zamuyi gobe don neman inda fadar gimbiya shukura take domin mu yaketa mu kawar da ita sannan mu karbi Alfila daga Hannunta Koda jin haka sai murna ta kama sadauki Awaisu yace da izinin ubangin musulunci saimun sami nasara kuma lallai dani za ayi wannan tafiya Sarki yace Ai nima dani za ayi wannan tafiya domin na sami irin ladan da ake samu na JAHADI... SARKI YACE AI NIMA DANI ZA AYI WANNAN TAFIYA DOMIN NA SAMI IRIN LADAN DA AKE SAMU A JAHADI humaira ta dubi sarki tace to yanzu idan ka bimu izuwa wannan tafiya wane ne kuma zaici gaba da mulkin jama arka kayi hakuri ka zauna ka jagoranci jama arka har Allah ya dawo da sadauki awaisu lafiya mu kuwa a can zamu rabu dasu awaisu mu tafi birnin Misra domin sarki sahibul hairi ya jaddada addinin musulunci a can, da wannan furuci aka tashi daga taron kowa ya je ya kwanta Kashe gari da sassafe kuwa humaira , sahibul hairi da bawa haluf da sadauki awasiu sukayi gagarumar shigar yaki sannan suka yi bankwana da sarki da sauran jama ar gari kuma suka bukaci jama a da su tayasu da addu a bisa wannan JAHADI da zasu tafi koda jama ar gari suka ga su humaira zasu tafi su barsu sai suka kama kuka saboda sabon da sukayi dasu al amarinda ya karya zuciyar su humaira kenan suma suka kama kuka nI kaina AA Misau Saida na Tausaya Musu, Nan dai suka yi musu sallama sarki ya sa aka kawo dawakai ingarmu guda hudu gami da isashshen guzuri yace ga nawa gudumawar humaira ta dubi sarki tayi murmushi sannan tace mun gode da wannan kyauta taka amma bama bukatar wadannan dawakai kamar yadda Allah ya kawomu birninka a kafafunmu muka shafe tafiyar watanni a cikin kwanaki kadan haka Allah zai kaimu inda Gimbiya shukura take wannan guzuri dai daka bamu na abinci shi muke da bukata koda gama fadin haka sai kowannansu ya karbi jakar guzurin ya rataya a bayansa sannan suka kama hanya suka fice daga cikin garin tun jama a na hangensu har suka kule su humaira suka wanzu suna masu tafiya dare da rana cikin karanta addu l'i na daurin kasa da neman taimakon Allah akan ya kaisu inda fadar Gimbiya shukura take da yake Allah maji rokon bawansa ne nan da nan kuwa su humaira suka shafe tafiyar watanni da dama a cikin kwanaki kadan su shiga nan su fita can wani lokacin ma sai su kera kwale kwale sun shiga sun ratsa ta cikin koguna da koramai wani iko na Allah tunda suka fara tafiyar sai wani kankanin tsuntsu ya zamo tamkar jagoransu duk inda tsuntsun yabi nan suke bi dalili kuwa shine humaira tayi mafarki da wannan tsuntsun tun kafin ya baiyana garesu kuma a cikin mafarkin tsuntsun yayi magana da ita yace duk inda kukaga nabi kuma kubi insha Allahu zan kaiku fadar Shukura Wata rana kwatam sai suka hango wani katon gida akan wani dogon tsauni a tsakiyar dokar daji Girman gidan ya wuce misali domin ya ninka gidan boka shamzubul azwas sau goma tunda ga nesa su humaira suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallon gidan suka sha jinin jikinsu akan cewa lallai wannan shine fadar gimbiya shukura bayan sun gama nazarin gidan sai humaira ta dubi sahibul hairi, bawa haluf da sadauki awaisu tace ku bini a baya duk inda na dauke sawuna ku sa naku da izinin Allah harmu shige cikin gidan can babu wanda zai ganmu, da zarar mun tsinci kanmu a ciki kowa yayi iya kokarinsa wajan kwatar kansa gami da neman tsari daga Allah akan makiya koda gama fadin haka sai humaira ta wuce gaba tana karanta wata addu'a ta musamman, sahibul hairi bawa halu da awaisu, kuwa suka rinka bin sawunta kamar yadda ta umarcesu AA Misau Nake, haka dai suka ci gaba da tafiya har suka hau kan tsaunin da zuwansu gaban katon gidan sai suka ga dakarun Aljanu sama da guda miliyan dubu daya sun yiwa gidan kawanya wasu a sama wasu a kasa kuma gaba dayansu muninsu da kwarjininsu ya ninka na wadancan aljanu da suka fafata dasu a garin su Awaisu bisa mamaki sai su sahibul hairi sukaga sam aljanun basa ganinsu abinda ya basu matsala shine, kwata kwata babu kofa ko taga a jikin gidan gaba daya bare su bude su shiga koda ganin haka sai humaira ta dafa bangon gidan ta karanta wata addu ar daban take bangon ya tsage suka shiga ciki wohoho ! Da shigarsu ciki suka tsinci kansu cikin Aljannar duniya domin irin kayan alatun da suka gani da kuma dukiya iri iri ko a tarihi basu taba jin kamarsu ba domin sai dai a kwatanta yawanta da karuna sai da suka shafe sa a tara suna tafiya a cikin gidan suna wuce fadoji kala kala suka iso fadar karshe inda suka yi arba da yarinya Alfila a cikin wata katuwar kwalba cike da ruwa ko motsi batayi a ciki kamar gawa dakarun aljanu da suka kewaye kwalbar suna tsaronta sun kai su dubu saba'in kuma girmansu da kwarjininsu ma ya ninka na aljanun dake wajan gidan sau goma sannan sai ga karagar mulki a gefe daya wacce aka kerata da zallar lu'u 'u'u babu kowa a kanta koda humaira tayi arba da wannan kwalba wacce alfila ke ciki sai ta zare takobinta karar zare takobince tasa wadannan dakarun aljanu suka juyo sukayi arba dasu ai kuwa sai aljanun suka taso musu gaba daya suna wani irin gurnani da ihu wanda ka iya sa mutum ya zautu ko ya mutu nan take ai kuwa suma su humaira sai suka kwala kabbara suka tari Aljanun aka ruguntsume da azababben yaki sai da aka kwana aka yini ana wannan yaki sannan humaira ta sami nasarar saran wannan kwalbar sihiri cikin kiran Sunan Allah take kwalbar ta fashe ruwan cikin kwalbar ya cika fadar gaba daya tamkar tekuce ta balle koda ruwan ya lullube wadannan dakarun Aljanu sai dukkaninsu suka zagwanye a cikinsu dabansu bai rayu ba humaira ta tsamo Alfila daga cikin ruwan ta tofa mata Addu'a ta farfado daaga dogon suman da tayi sannan ta goyata a bayanta A sanna ne suka ji ihu da kururuwar gimbiya shukura tsulum sai gata ta baiyana a cikin ruwan tana sanye da kayan yaki na bakin sulke kuma ta rike takubba guda biyu humaira da shukura suka kurawa juna ido sannan shukura tace yaune za ayita ta kare koni koke kafin humaira ta budi baki ta maida raddi tunu shukura ta afka musu su ukun da azababben yaki nan fa ta zame musu alakakai suka rasa yadda zasuyi da ita sai da suka sake shafe sa a bakwai ana wannan bakin gumurzu ya zamana cewa shukura ta yiwa dukkaninsu mugayen raunika a jikinsu duk ta bazar dasu a kasa harda ita kanta humairan babu mai iya mikewa tsaye Amma banda Jarumi AA Misau hahaha A sannan ne humaira ta sake yiwa Allah kirari irin wanda tayi masa a wancan karon ai kuwa nan take ta sami wannan gagarumin karfi ta dinga ragargazar shukura har sai da ta daddatsa sassan jikinta filla filla A karshe humaira ta yanke jiki ta fadi kasa sai da suka kwana ashirin a cikin wannan gida suna jinyar jikinsu sannan suka warware suka fita cikin tsananin farin ciki sadauki awaisu ya karbi yarsa Alfila ya koma garinsu Sahibul hairi, bawa haluf da Humaira kuwa sai suka je birnin misa aka kaddamar da addinin musulunci sannan suka tafi garin su humaira aka daura auransu suka sake komawa birnin misra suka ci gaba da rayuwa mai cike da farin ciki, bisa mamaki a wannan lokaci sai arziki mai tarin yawa ya samu ga sarki sahibul hairi da tarin daukaka a tsakanin sarakunan dake nahiyar, ya zamo shine babban Sarki kuma yaci gaba da yake yake na jaddada addinin Islama har zuwa karshen Rayuwarsa !!! ALHAMDULILLAH !!! Bayan nan kuma sai Sadauki AA Misau ma aka daura Auransa Da yarinya Alfila inda suka ci gaba da rayuwarsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali hahahahaha ------------------------------------------------Alhamdulillah Anan ne muka zo karshen Littafin sarkin sarakai 1-5 dafatan littafin ya kayatar daku wanda AA Misau Ya jagoranci typing dinshi, sannankuma nake cewa ku huta lafiya marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini kado typing AA Misau ke Magana Nake cewa saimun hadu daku a cikin wani sabon littafin idan mai duka ya nupemu !!! Signed AA Misau..... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19