Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kama labe labe yana tunanin hanyar da ya kamata yabi yaje inda aka ajiye gatarin sihirin inda matsalar take shi bai san a ina aka ajiye gatarin sihirin ba haka dai ya ci gaba da labewa a cikin wani sako mai duhu yana tunani a lokacin da hadimai da dakarun gidan sarautar ke kai komo wasu mata gabansa suke wucewa amma basu ganshi ba. ** wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi bayan ya sha bakar wahala a cikin gidan halaka wanda ke karkashin kasa a masarautar sarki barusa ++ ++ ++ ++ ++ ACAN BIRNIN MISRA KUWA kashe gari da sassafe fada ta cika makil da jama a tare da dukkan fadawan sarki kowa ya zuba idanu yana jiran fitowar sabon sarki wato mai rikon karaga AMINUL HAS. don aga yadda zai tafiyar da nasa tsarin mulkin ana cikin wannan haline aka hango shi a tafe shi kadai a bayansa kafarsa sanye da wadansu tsofaffin takalma wadanda saboda tsufa har sun fara lalacewa sannan kuma yana rike da wata tsohuwar sanda itama duk ta fara farfashewa rigar dake jikinsa ma ba wata mai kyau bace rigace irin wadda kowanne irin talaka zai iya sawa . Koda ganain Aminul has a cikin wannan shiga sai su waziri suka shiga duban junansu suka fara dariyar farin ciki jama ar gari kuwa sai suka cika da dumbin mamaki suka kurawa aminul has idanu a lokacin da jama a suka dare suka bashi hanya ya nufi kan karagar mulki dama a wannan lokaci kowa a tsaitsaye yake har saida aminul has ya zauna a kan karaga sannan fadawa suka zazzauna a mazaunansu suma mutanan gari sai kowa ya nemi wuri ya zauna take fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta . Cikin nutsuwa sarki aminul has ya mike tsaye ya dubi jama arsa cikin fara a da walwala yace yaku jama ar birnin misra kuyi sani cewa adalin sarkinku wato sarki sahibul hairi wanda yai tafiya bai tafi ba yana nan . Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa da kowa fadar ta sake rude wa da hayaniyar jama ah koda ganin haka sai Aminul has ya daga hannu aka yi tsit sannan yace nasan kun shiga rudani bisa jin abinda na fada yanzu to amma abin da na ke nufi anan shine sarki ya tafi amma ni wakilinsa ne duk irin mulkin da yasaba yi akansa zanci gaba ba zan sauya komai ba . Ban yarda mai mulki ko wani attajiri ya zalunci talaka ba duk mutumin da yayi laifi za a hukuntashi kamar yadda za a hukunta kowa da kowa. Sa adda jama a sukaji wannan batu sai suka barke da shewa suna tafi kowa ka dubi fuskarsa sai kaga ta cika da annuri amma ban da ragowar fadawa su waziri Akiyanu wadanda suka murtuke fuskokinsa sai muzurai suke kamar zasu fashe da kuka don bakin ciki musamman waziri Akiyanu ji yayi kamar ya tashi yaje ya soke aminul has da takobi yayi juyin mulki nan take . Sarki aminul has yaci gaba da bayani yana mai tabbatar da cewa za aci gaba da yiwa jama a adalci da kuma taimakon marasa shi haka dai yayi ta bayanai har ma yana kirkiro sababbin abubuwa don farantawa talakawa haka dai taro ya watse kowa yana farin ciki aminul has ya mike tsaye ya shiga cikin gidan sarauta inda ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar sarki sahibul hairi. Da shigarsa cikin turakar sai ya iske matarsa shulaiba zaune a gefen gadon taci ado fuskarta cike da annuri ya yinda ta dago kai suka dubi juna sai kowannansu ya Kama murmushi saboda tsananin farin ciki aminul has ya matsa gareta ya zauna daf da ita sannan ya ajiye sandarsa akan gadon a gefe daya koda ya sunkuya da nufin ya cire takalman kafarsa sai tayi wuf ta tare hannayansa tace A kul ka cire wadannan takalma lallai dasu zaka yi barci akan wannan gado mai Albarka. Yayinda Aminul has yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ki gafarceni yake abar kaunata hakika na sha afa da dokokin da kika shimfida mini bisa wadannan takalma da kuma wannan sandar amma ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsananin farin ciki kasancewar yau ne zamu shafe dare daya daga cikin dare sittin na farin ciki akan wannan gado na sarauta . Yayinda shulaiba taji wannan batu sai tayi dariya sannan ta mike tsaye taje ta rufe kofar turakar ta kuma kashe gaba dayan fitilun dake cikin turakar dakin yayi duhu matuka yadda ko tafin hannu mutum ya daga ba zai iya ganiba. ++ ++ ++ Al amarin waziri Akiyanu kuwa sai suka kasa tashi daga filin fadar saboda tsabar bakin ciki ya zamana cewa kowa ya watse an barsu a zaune su kadai a cikin fadar har dare ya raba basu koma gidajensu ba sai da suka tabbatar da cewa babu kowa a cikin fadar sai su kadai a lokacin ma masu gadin kofar fadar sunrufe kofa sannan suka fara tattaunawa akan yadda zasu ga bayan sarki Aminul has. Waziri akiyanu ne ya fara magana yace yaku yan uwana yan majalisa kun gani kuma kunji abubuwan da babban makiyinmu ya fada lallai ya zama wajibi muyi saurin kawai dashi in ba haka ba kuwa gaba dayanmu zamu wulakanta sai mun kaskanta a idon talakawa saimun talauce mun zama abin tausayi . Yayinda yan majalisa sukaji wannan batu na Akiyanu sai duk sukayi shiri aka rasa wanda zai ce kala daga can sai tsoho kilzam yayi gyaran murya yace yakai waziri Akiyanu kayi sani cewa dolene a dawo kan maganata ta farko wato dolene mu yiwa aminul has juyin mulki a dare daya idan ba hali kawai muje mu kashe shi yanzu yanzu a cikin wannan dare . Waziri Akiyanu yayi murmushi yace kai kuwa dadina dakai kenan ka cika gaggawa na yarda da shawararka cewa mu sa a kashe shi a cikin darennan amma ba mu da kanmu za muyi wannan aiki ba domin aikin ne mai hadari manufa ta anan inda bamuci nasara ba asirinmu zai tonu a hallaka mu amma idan wasu muka sa sukayi wannan aiki kome za ayi musu ba zasu fadi cewa mune muka sasu ba . Abinda za ayi kawai shine yanzu idan muka bar nan zan tura a kirawo mini manyan yarana amintattu bakwai wadanda zasuyi wannan aiki a gobe da daddare ina tabbatar muku da cewar sai dai a wayi gari sarki ya mutu kun san kuwa yana mutuwa nine zan hau karaga kasa ta zama tamu . Koda jin wannan batu sai gaba dayansu suka bushe da dariyar mugunta dariyar da suke ce masu gadin kofar fadar suka jiyo suka fahimci cewa akwai mutane a ciki dan haka sai suka rugo da gudu suka bude kofar suka haska fitilu koda sukayi arba dasu waziri akiyanu sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa nan dai su waziri Akiyanu suka tarwatse kowa ya tafi gidansa cikin farin cikin muguntar da suka kulla. . Lokacin da waziri Akiyanu ya isa gida sai ya tsaya cikin wani babban falonsa inda ya saba ganawa da jama arsa ya zauna nan take ya kira wani bawanda mai suna JAMASI ya umarceshi daya hau doki a cikin wannan dare ya tafi izuwa gidajen wadansu barade su uku musabu, Akaifu da samar yace ya gaya musu cewa suzo yanzu yanzu yana son ganinsu a gidansa cikin rawar jiki jamusi ya fita daga cikin falon ya tafi cika umarni . waziri akiyanu na nan zaune a falonsa har tsawon kusan rabin sa a sai ga musabu da akaifu da samar sun bayyana kamar wadanda aka jefosu daga sama cikin biyayya su duka suka zube kasa gaban waziri Akiyanu suka kwashi gaisuwa. Su dai wadannan barade uku sune manyan mayakan birnin misra wadanda sarki sahibul hairi ke takama dasu domin duk sa adda zai bita yaki sune suke take masa baya kasancewar waziri akiyanu mai dukiyane saiya dinga siye zuciyoyinsu da abin duniya ya zamana cewa yana yi musu kyauta da alheri mai yawa fiye da tunaninsu su kansu sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake musu wannan alheri bisa dalilin haka ne suke matukar yi masa biyayya duk abinda ya umarcesu dayi ba zasu ketara ba A zahirin gaskiya ba wani abu bane yasa yake musu alheri ba face tanadin irin wannan rana wacce ya san cewa ko ba dade ko bajima zatazo amfaninsu zai taso. . Bayan su barde musabu sun gama kwasar gaisuwa ga waziri akiyanu sai ya dubesu cikin murmushi da girmamawa ya yi musu izinin zama akan kujeru na alfarma ba tare da gardamar komai ba kuwa suka zauna cikin nutsuwa ya sake dubansu yace yaku wadannan zaratan jarumai kuma dirkokin misra ina mai mika godiyata gareku da kuka amsa wannan gayyata tawa ta bazata kuma a cikin wannan dare na san zakuyi mamaki matuka to amma idan kuka dubi sabon yanayin da muka shiga na mulkin kasar nan bai kamata kuyi mamaki ba ku duka kun sani cewa sarkinmu yayi gagarumar tafiya mai tsananin hadari da kowa ya san ba zai taba dawowa ba hakane ko ba hakaba!? . Gaba dayansu ukun suka amsa da cewa wannan haka ne gaskiya kam Waziri Akiyanu yayi murmushi sannan yaci gaba da cewa a halin yanzu galadima Aminul has ne sarkinmu maimakon ace nine na hau karagar mulkin. Ina tabbatar muku da cewa idan yaci gaba da mulkinmu ba zan iya ci gaba da muku alherin da na saba yi muku ba domin kuwa zan talauce na zama fakiri.. Abinda nake so daku shine ku bani hadin kai mu kawar da gwamnatin Aminul has mu kafa tamu idan har mukayi nasarar hakan nayi muku alkawarin zan sanyaku a cikin manyan yan majalisata kuma na baku dukiya mai yawa irin wacce baku taba mallaka ba a rayuwarku idan aka sami akasi akan wannan aiki to kada ku kuskura ku fada sunana domin kun san illar da hakan zata iya haifarwa ina mai dada tabbatar muku da cewa dani da sauran yan majalisa duk bakinmu daya muna da goyon bayansu dari bisa dari . Lokacinda su barde musabu suka ji wannan jawabi daga bakin waziri sai duk suka bushe da dariya a lokaci guda kamar hadin baki Al amarin da ya bashi mamaki kenan musabu ya dubi Akiyanu cikin nutsuwa yace ya shugabana kayi sani cewa yadda muka yarda da kanmu ko sarki sahibul hairi kace mu yiwa juyin mulki zamu iya bare galadima Aminul has wanda bashi da jarumtaka kuma bashi da karfin sihiri na kare kansa muna tabbatar maka da cewa cire silin gashi daga cikin tandun mai yafi wannan aiki wuya a daren gobe zamu je har cikin turakar sarki mu kashe shi salin alin ba tare da kowa ya ganmu ba hatta iyalansa kuwa . Cikin mamaki waziri akiyanu ya dubi musabu yace tayaya zaku iya wannan aiki alhalin ciki da wajen gidan sarautar a zagaye yake da dakaru masu tsaro dare da rana musabu ya sake yin dariya shi kadai a karo na biyu yace ai kowa akan aikinsa sarki ne wannan aikinmu ne ba naka ba. Don haka ka kyalemu muyi aikinmu kawai sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba' waziri akiyanu ya zazzaro ido yace wanne hanzari ne daku? Musabu yace duk da cewa wannan aiki mai sauki ne a wajanmu amma hadarinsa na da matukar yawa dalilina anan shine koda bayan ka zama sarki ne idan bisa tsautsayi wani ya ganmu a sa adda muke wannan aiki tofa sai sirrinmu ya tonu har abada jama aba zasuga kimarmu ba da mutuncinmu ba sbd haka ba zamu fara wannan aiki ba face ka bamu dukiya mai yawan gaske ta kimanin rakuma dari dari da shanu hamsin hamsin da kuma gonakai goma goma . Koda jin wannan batu sai waziri ya bushe da dariyar farin ciki har da tafa hannaye sannan yace gobe da safe zan dankawa kowannenku wannan dukiya a hannunsa idan aka wayi gari na samu labari cewa galadima ya mutu zam kara muku rubi uku na wannan dukiya yayinda su barde musabu sukaji wannan lafazi sai suka cika da murna nan take suka yiwa waziri sallama suka tafi. Kamar yadda waziri akiyanu ya yi alkawari haka al amarin ya kasance wato kashe gari da safe ya sake turawa aka kirasu baradan uku ya basu wannan dukiya su kuwa suka tafi suka zauna suna ta shirye shiryen yadda zasu sami nasara bisa wannan gagarumin aiki dake gabansu . Lokacin da dare ya fara rabawa sai musabu Akaifu da samar sukayi wata irin shiga ta bad da kama gaba dayansu bakaken kaya suka sa sama da kasa suka fufe fuskokinsu da babaken rawani ya zamana cewa idanunsu kadai ake gani hatta kufen takubbansu da kakalminsu bakake ne bayan sun gama wannan kimtsi sai suka nufi gidan sarautar yayinda suka isa daf da gidan sai suka hada hannayansu waje guda sukayi kawanya faruwar hakan keda wuya sai ga wata guguwa ta zagayesu guguwar ta suresu a sama ta rika yin katantanwa dasu nan take suka rikide suka zama guguwar ta bace dasu bat !! A can cikin gidan sarauta kuwa yaune dare na biyu ga sarki Aminul has tare da matarsa da samun wannan kwanciya yin barci a gadon sarauta tun a farkon darensuka yi barci suna ta shara mafarkai masu dadin gaske shulaiba na cikin yin mafarki ne ta farka daga bacci kawai sai taji bawali ya kamata don haka saita sauko daga kan gadon ta shiga kewaye ta bar Aminul has a kwance bisa gadon yana ta shara barci abinsa . Shigarta cikin kewayen keda wuya sai ga guguwa ta bayyana tana mai kewaye gadon karfin guguwar yasa gashin kan Aminul has ya kama tashi sama maimakon ya farka daga barci sai ya kara gyara kwanciya saboda jin dadin iskar guguwar da ke kadawa nan take kuma sai guguwar ta rikide ta zama su musabu suna zagaye da gadon kowannansu na rike da takobi ya dagata sama tsininta na kallon kasa . Lokaci guda suka dubu juna kawai sai suka yunkura da nufin su tsire cikin sarki aminul has da takubbansu bisa mamaki sai sukaji an ruke hannayansu tamau a sama sun kasa saukesu kasa nan fa suka ci gaba da kokarin sauke hannayen amma sai abu ya gagara sai da suka jarraba soke cikin shi sau uku amma suka kasa bisa dole suka hakura suka rikide izuwa guguwa suka bace bat faruwar hakan keda wuya saiga shulaiba ta fito daga cikin kewayen duk abinda ya faru bata sani ba koda ta hau gadon da nufin ta kwanta sai taga gashin kan Aminul has duk ya tarwatse kuma matashin kai ya fado masa mamaki ya kama ta amma dataga cewa Aminul has ya sauya wuri daga inda ya ke kwance saita yi tsammanin cewa garin mirgin murgin Ne ya jeho matashin kan kasa har gashin kansa ya barbaje kawai saitayi kwanciyarta taci gaba da barcinta Al amarinsu barade kuwa lokacinda suka zama guguwa suka bace bat sai suka bayyana a can nesa da gidan sarautar su ukun suka dubi juna cikin matukar mamaki da razani masabu yace yaya akayi aminul has ya sami tsari da sihiri. Akaifu yai ajiyar numfashi yace ni dai a tunanina kafin sarki sahibul hairi ya bar gida ya taimaka masa samar yace sam sam ba haka bane shin kun mantane cewa sarki sahibul hairi ya taba gaya mana cewa babu wani mahaluki da zai taba yin amfani da irin sirrikan tsafinsa ai duk yadda akayi ya sami wannan tsari ne daga wajan wani mutum daban kun san cewa tun da ya zama sarki dole ne shima ya mike tsaye ya nemi tsari musabu yace to yanzu menene abin da zai fishshemu? . Akaifu yace bamu da abinyi face muje mu sanar da waziri akiyanu duk abinda ya faru kuma mu bukaci ya bamu dama ta biyu in ba haka ba kuwa kun san cewa duk dukiyar da ya bamu karbeta zaiyi. Ai kan wannan shawara baradan suka rabu kow aya tafi izuwa gidansa Kashe gari da safe tun kafin alfijir ya keto su musabu sukaje wajan waziri akiyanu suka zayyane masa duk abinda ya faru sa adda sukaje hallahaka aminul Has koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Akiyanu zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone har saida kallar takaici ta fado masa cikin tsananin fishi ya dubi su musabu yace ku tashi kuje na bamu dama ta biyu lallai kuyi tunanin duk hanyar da zaku bi kuga bayan wannan mutum kafin nan kafin kwana bakwai in ba haka ba kuwa duk dukiyar da na baku sai kun dawo mun da ita. Cikin sanyin jiki da tsananin damuwa su musabu suka mike tsaye suka tafi sai da su musabu suka shafe kwana uku suna tunanin hanyar da zasu bi su hallaka sarki Aminul has amma basu sami mafita ba a rana ta ukuce da yammaci suka tsinci dami a kala a wannan lokaci suna zaune su ukun a can bayan gari suna tattauna wa matsalar kawai sai suka hango sarki Aminul has tare da mai dakinsa da kuma dakaru kimanin mutum dari kacal sun fito ran gadi. Da yake suna labe ne a bayan wani dutse babu wanda ya hangosu har tawagar sarki ta wuce bayan wucewar sune musabu ya dubesu yace. Yauwa ga tsuntsu daga sama gasashshe yanzu menen abinyi Akaifu yai ajiyar zuciya yace ai ba hawan ba saukar kun sani dai cewa koda munyi gaba da gaba da sarki ba zamu iya hallakashi ba tunda mun jarraba mun gani duk su ukun sukayi shiru suka shiga tunani mai zurfi daga can sai dabara ta fadowa samar yace ku bani dama na san abinda zanyi Ni kadai zanje na aiwatar da wannan aiki bana bukatar taimakonku. . Hm cikin matukar mamaki musabu ya dubesu yace haba samar tayaya zaka iya yin aikin da mu uku ya gagaremu samar yace ai ka san ance kowanne mutum da irin tasa hikimar kuma ai ita hikima baiwace don haka saiku kyaleni na jarraba sa ata musabu ya dubi Akaifu yace yaka gani Akaifu yace aiba a kwacewa yaro garma mu bashi dama mu gani koda jin wannan batu sai samar yayi girgiza ya bace bat su kuwa sai suka ci gaba da labewa a bayan dutsen suna jiran dawowar samar. . Lokacin da tawagar sarki aminul has sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa da bayan gari sukayi nisa a cikindaji sai suka yada zango a bakin wata koramar koramar mai kyawun ruwa garai garai nan take aka kafawa sarki tanki aka sauke kayansa aka zuba a ciki . A rayuwar Aminul has babu abinda yake sha awa sama da harbin tsuntsaye dan haka ana sauka a bakin wannan korama sai yaga tsuntsaye iri iri suna ta shawagi a cikin dajin nan take yasa aka dauko masa kwari da baka ya fara kaiwa tsuntsaye hari bisa sa a kuwa sai yaga yana harbo tsuntsayen suna fadowa kasa ana debewa ana tarawa a cikin wani babban kwando Al amarin da ya jefashi cikin farin ciki kenan yaji zuciyarsa tayi fari ana cikin wannan hali ne samar ya baiyana a wajan ba tare da kowa ya ganshi ba cikin sanda ya isa inda dokin sarki ke daure. Ba tare da kowa ya ganshi ba sai ya fiddo bakar ciyawa ya baiwa dokin ya cinye koda fruwar haka sai samar ya bace . Sarki aminul has yaci gaba da harbo tsuntsaye cikin farin ciki da nishadi har sai da ya harbo guda dari a sannan gajiya ta riskeshi ya bada umarnin a tashi a tafi gida nan da nan kowa ya haye kan dokinsa aka juya da baya don a koma cikin gari koda fara tafiyar sai kawai aka ga dokin sarki yai turjiya yana mai dag kafafuwansa sama yana haniniya tamkar ya ga wani abin tsoro da ya firgitashi. . Kafin a yi wani yunkuri tuni dokin ya juya da baya sarki na kansa ya zabura da gudu ya nausa cikin dawa cikin tsananin tashin hankali dakaru sukabi bayansa a sukwane don su tsayar da dokin. Ita kuwa gimbiya shulaiba kida taga abinda ya faru da mijinta sai ta sulale ta fado daga kan dokinta a sume saboda tsananin razana. Guyson ke magana dakaru da dokin sarki aka kasa tsere suna ta kokarin cimmasa amma abu ya gagara domin na gaba yai gaba na baya sai labari. Aminul has yayi ta jan linzamin dokin don ya tsaya amma kamar ma kara masa gudu yake yi don haka sai ya rungumi kaddara ya zuba ido yaga inda...Ya zuba ido yaga inda dokin zai kaishi dokin yaci gaba da azababben gudu ya zamana cewa ya baiwa dakarun tazara mai yawan gaske babu yadda za ayi su cimmasa babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda dokin yake ratsawa ta cikin kwazazzabai da kayoyi ba tare da wata damuwa ba rami kuwa komai girmansa yana yin tsalle ya haye shi . A iya sanin Aminul has bai taba ganin doki mai tsananin karfin gudu ba kamar wannan doki amma abin da ya bashi mamaki shne ya mallaki wannan doki fiye da shekaru ashirin kuma babu wanda ya taba hawansa face shi kadai yaya akayi wannan doki ya zama maguji haka alhalin bai taba yin tseren gudu da shi ba dokin yaci gaba da gudu irin gudun da idan aminul has yace zaiyi gangancin dira daga kansa sai iya hallaka kansa. . Haka dai dokin yai ta tsala gudu har ya iso bakin teku suka lume a cikinsa su biyun a dai dai wannan lokacin dakarun suka iso wajan bakin tekun sukaja tunga cikin thanzari wadanda suka iya ninkaya suka sauka kasa daga kan dawakansu suka fada cikin tekun suka hau lalube. Saida aka shafe sa a uku suna lalube a cikin tekun amma ba a ga sarki da dokinsa ba bisa dole aka hakura aka fito daga cikin tekun aka juya da baya, . Lokacin da labari ya riski gimbiya shulaiba cewa da sarki da dokinsa sun lume a cikin teku an nemesu sama da kasa an rasa sai ta fashe da kuka da kyar kuyanginta suka dauketa suka dorata akan doki aka tafi da ita gida, . Nan da nan labari ya cika gari cewa sarki da dokinsa sun hallaka a can bayan gari cikin teku nan fa hankalin jama a ya dugunzuma aka kama kuka cikin kankanin lokaci fada ta cika makil da jama a ana ta koke koke da zullumi cikin tsananin bakin ciki ba komai ne yasa jama ar gari suke wannan bakin ciki ba face sanin cewa yanzu fa mulkine zai koma hannun waziri akiyanu idan kuwa mulkin ya koma hannunsa talakawa sun shiga uku babu wadanda zasuji dadi face masu mulki da tajirai. Lokacin da labari ya riski waziri akiyanu da mukarrabansa cewa sarki ya hallaka a cikin teku sai farin ciki ya lullubesu sukaji kamar su zuba ruwa akasa su sha tun kafin su iso fada suka fara rabawa makada da mawaka dukiya suka shiga aikinsu kafin a jima kuwa tuni su waziri Akiyanu sun hallara a fadar don kaddamar da bakin nadin sarautarsa kafin ya hau karagar ne makada da mawaka wuka yi ta cashewa bayan nan sai waziri akiyanu ya mike yayi bayanin tsautsayin da ya sami sarki Aminul has har ma ya matso hawayan karya yana mai nuna bakin cikinsa duk da ya san cewa jama a sun san cewa murna yake da faruwar tsautsayin . Bayan ya gama jawabin sai ya tafi izuwa kan karagar mulkin don ya zauna ba zato ba tsammani sai aka jiyo sukuwar doki gaba daya jama ar dake fadar suka waigo suka dubi bakin kofa saiga sarki Aminul has bisa wannan dokin a sukwane . Da shi da dokin duk a jike suke sharkaf da ruwa Al amarin da ya jefa kowa a cikin mamaki kenan shi kuwa waziri akiyanu sai ya kasa zama a kan karagar mulkin ya kame kamar gunki sbd tsananin mamaki da jin kunya, Da shi da mukarraban nasa duk sai ido ya raina fata sarki Aminul has yazo har gaban karagar mulkin fuskarsa cike da annuri da zuwa sai yaja tunga ya sauko daga kan dokinsa ya nufi kan karagar . Waziri akiyanu ya matsa gefe daya ya bashi hanya a wannan lokaci gimbiya shulaiba na can cikin turakarta tana shara kukan bakin ciki tana cikin hakanne wata kuyanga tazo ta tabbatar mata da cewa ai ga sarki can ya dawo a cikin koshin lafiya koda jin wannan batu sai ta mike zumbur ta ruga izuwa fada da zuwanta bakin kofar fada saita hango Aminul has a zaune bisa karagar mulki jama a na kewaye da shi suna tayashi murnan tsira da rayuwarsa . Kawai sai ta tsaya a bakin kofar ta na ta kyalkyala dariyar farin ciki bayan sarki Aminul has ya gama karbar jajen murna sai ya mike tsaye ya fuskanci jama a yace' yaku jamar wannan birni na misra na fuskanci cewa kunyi matukar mamaki da kuka ga na dawo gareku a raye? Hakika akwai alajabi a cikin wannan al amari don haka akwai bukatar nayi muku bayanin yadda akai na kubuta da rayuwata da farko lokacin da dokina ya zabura dani ya kama gudun tsiya dani sai hankalina ya dugunzuma ainun domin nine nayi kiwon dokin tun yana karami kuma ko sau daya ban taba jarraba yin gudu dashi ba haka kuma babu wanda ya taba hawa dokin in baniba . Ko da naga na kasa sarrafa wannan dokin don na tsai dashi sai na rungumi kaddara na zuba ido kawai naga inda zai kaini ban ankara ba sai gani nayi ya afak dani cikin teku kafin nayi wani yunkuri dani dashi mun lume izuwa karkashin tekun ba zato ba tsammani kuma sai naga munci gaba da tafiya a karkashin ruwa tamkar akan doron kasa muke ba a ruwa ba nan ne fa na dada cika da mamaki ainun. Haka dai dokin nawa yayi ta tafiya dani a karkashin teku har tsawon sa a biyar kawai sai naga ya juyo da baya cikin tsananin gudu fiye da na farko tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya nan da nan muka iso bakin gabar tekun muka fito waje fitarmu keda wuya ..Sai dokin ya tsugunna kasa ya kama kumallo nan take ya amayar da wata irin bakar ciyawa duk wannan abu da ya faru hannu na na rike da wannan sanda ta hannuna shi kuwa takalmin nan dake kafata bai bar jikina ba kwatsam sai naga wani danguntun Aljani ya bayyana a gabana wanda baifi na kifeshi da kwando ba. Aljanin yayi sujjada a gareni yace an gaisheka ya wakilin adalin sarki ka kwantar da hankalin ka ka sani cewa indai kana tare da wannan sanda ta hannunka da kuma wannan takalmi na kafarka babu wani tsautsayi da zai sameka . Koda naji wannan batu sai na cika da mamaki nace kai kuma waye yaya akayi kasan wannan al amari? Koda jin wannan tambaya sai aljanin ya bushe da dariya yace ni sunana MAKANUL URUD kuma na kasance mai tsaron wanda duk yake tare da wannan sanda da takalmin in baka mance ba asalin wadannan abubuwa biyu na mahaifin matarka ne wato Abu hakim a wajansa ta gajesu . Labarin wadannan sanda da

Chapter 6 of 19