Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da hankalinki ya ke Alfila kiyi sani cewa ni da maigidana mun san komao bisa al'amarinki, kuma akan hakan ne ma muka zo nan fadar Shmzabul Azwas domin mu sace ki mu kaiki gida ga abbanki domin muma munada muhimmiyar bukata wacce muka son ya biya mana". Koda jin wannan batu sai Alfila tayi murmushi ta ce, "shin maigidanaka shi ne sarki Sahibul Hairu na Birnin Misra?". Cikin mamaki Bawa Haluf ya ce, "kwarai kuwa shi ne, ya ya aki yi kika sani?". Alfila ta ce, "Ai tuntuni mahaifina ya bani labarinsa da irin matsalar da ta addabi rayuwarsa cewa bashi da wani buri wanda yafi ya ga yafi gaba dayan sarakunan duniya arzuki, daukaka da yawan mata sabo da gorin da sauran sarakina suke yi masa akan cewa shine mafi talauci da kaskanci a cikin sarakuna. Lallai yanzu na aminta da kai don haka sai ka fito da wadannan kwalabe na nuna maka wadda za kayi amfani da shi." Cikin murna da hanzari Bawa Haluf ya fito da sauran kwalaban daga cikin aljihunsa. Nan take Alfila ta dauki kwalba da ke dauke da shudin ruwa ta karasa in da su sarki Sahibul Hairi suke a tsaye jikam cikin suffar gumaka. Da zuwan ta sai ta bude kwalbar sai ta digawa kowannensu. Faruwar haka ke da wuya sai Sarki Sahibul Hairi ya fara motsawa. Idanunsa ne suka fara budewa, sannan 'yan yatsunsa na hannu da na kafafunsa, sannan ragowar jikinsa. Faruwar haka ke da wuya sai jikin gimbiya Humaira ya motsa gaba daya. Koda Humaira ta bude idanun ta sai ta rafka salati. Al'amarin da ya janyo gaba daya gidan ya kama girgiza yana rugurgujewa ke nan. Kwatsam! Sai ga aljani Shamzabul Azwas ya kara bayyana a gabansu cikin firgici da tsananin mamaki. Ita kuwa gimbiya Humaira sai ta lazamci karanta wadansu addu'o'i na musammam bata yadda ta daina ambatonsu. Ya yin da Shamzabul Azwas ya yi arba da Bawa Haluf sai ya ciji yatsa cikin tsananin takaici domin ya san cewa mantuwar da ya yi da shi ita ce babban kuskurensa. Ita kuwa Alfila sai ta ruga bayan sarki Sahibul Hairi ta 6uya tana mau cewa da shi, "ya kai wannan sadaukin sarki kada ka bari azzalumi Shamzabul Azwas ya maidani cikin kwalbarsa ta tsafi, domin kuwa idan hakan ta faru kaima har abada burinka ba zai ta6a ciki ba." Koda wannan batu sai Sarki Sahibul Hairi dada kankame Alfila a bayansa sannan ya zare takobinsa yana mai fuskantar Shamzabul Azwas. Shamzabul Azwas ya dubi sarki Sahibul Hairi ya dubi gimbiya Humaira kawai sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan kuma ya murtuke fuskarsa tamkar wnda aka aikowa da sakon mutuwa ya daka musu tsawa wadda ta sa suka ji hantar cikinsu ta kada kamar zata fito waje. Ya ce, "ku kananan sadaukai ku yi sani cewa hakika ku tsokano tsuliyar dodo, dan haka yau zakuga bala'i da masifa irin wadda baku ta6a gani ba a rayuwarku. Kun katse mini aikina a karo na farko alhali na kusa idashi, nakamaku na sanyaku a cikin tarkona wanda babu wani mahaluki da ya isa ya ketareshi ya kai labari amma sai gashi ku yanzu kun tarwatsa tarkon nawa, har ma kun katse mini aikin nawa a karo na biyu. To ku sani cewa wannan karon ba wai zan sanyaku a cikin tarko bane sai dai na zaremuku ruhin numfashinku gaba daya tunda kun zamo dan hakin da ka raina maitsokane mini ido". Kafin Shamzabul Azwas ya gama rufe bakinsa sai gimbiya Humaira ta daka masa tsawa ta ce, "ya kai tsohon munafikin Allah wanda ya gaji cin amanar Allah da bayinsa, ka sani cewa kai kana kan hanyar 6ata mabayyani, ni kuwa ina kanhanyar shiriya kuma a ko yaushe Allah na tare da bayinsa masu tsoransa da bin dokokinsa, don haka nasan cewa komai wuya, komai gumu sai na sami nasara akan ka, don haka sai ka shirya ga MACE MAI KAMAR MAZA nan bisa kan ka". Kafin Shamzabul Azwas ya kara mai da martani tuni Humaira ta falfala da azababban gudu izuwa gareshe, kawai sai gani ya yi ta daka tsalle guda daya tayi sama ta dure a gabansa tana mai kawo masa mummunan sara da nufin ta zarga masa kafada gida biyu. Shamzabul Azwas ya goce cikin zafin nama, amma duk da haka sai da takobinta ta zabtare rabin gashin kansa, shi kuwa ya hantsila gefe daya. Koda Sha,zabul Azwas ya g rabin gashin kansa a kas, sai hankalins ya dugunzuma domin tunda ya mallaki wannan damara ta kugunsa bai ta6a haduwa da wani jarumi ba wanda ya iya kai masa wannan mugun hari ba face Humaira. Cikin tsananin rudewa ya daga rigarsa ya shafa damarar kugun nasa don yaji wai shin yana tare da ita kuwa. Ai kuwa sai yaga damarar na nan. Al'amarin da ya kara furgitardashi kenan ya mie tsaye zumbur! Ya ja da baya ya gyara tsayiwa sannan ya zare takobinsa sannan ya fuskanci Humaira. Koda ganin haka sau Humaira tayi murmushi ta ce, "ya kai tsohon munafikin Allah kai sani cewa komai na da lokacinsa. Tabbas Allah ya ara maka lokaci a baya kayi budurinka ta hanyar amfani da wannan damara da ke kugunka wacce ke dauke da sunayansa tsarkaka, to ka sani cewa lokaci ya kare a yanzu. A yau sai na hallakaka na rabaka da wannan damara ta zama tawa domin shi kansa Ubangiji yana kishin Addininsa da bayinsa, don haka nayi imani cewa sai ya bani nasara a kanka. Lallai zai bani karfin da ya fi wanda kake amfani da shi wajan zaluntar bayinsa, burinka na son ka mallaki duniyar nan gaba dayanta ba zai taba cika ba." Koda gama fadin haka sai Humaira ta sake daka taalle irin na baya ta dire gaban Shamzabul Azwas suka sake ruguntsimewa da azababban yaki suna masu kaiwa juna sara da suka cikin mutukar zafin nama, juriya da bajinta gami da nuna kwarewa. A duk sa'adda takobin suka sai kaga tartsatsin wuta na tashi gami da tsawa da walkiya. Duk wanda aka kaiwa sara ya goce, to fa duk abin da takobin ta sara sai abin ya dare gida biyu kuma ya kama da wuta. Nan da nan suka hargitsa fadar gaba daya suka dugunzuma hankalin duk wani abu mai rai da ke cikinta. Su kansu su sarki Sahibul Hairi daka tsaye suna kallon artabun da ake sai da kallon ya gagresu suka kama gujeguje suna neman ma6uya domin ginin ya ci gaba da rushewa yana fadowa kasa zai dannesu. Sai da Shanzabul Azwas da Humaira suka shafe sa'a uku cur! Suna wannan gumurzu ya zamana cewa gini fadar fadar ya ruguje ya zama fili fetal har ma 6angorin sun danne sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf da yarinya Alfila sun kasa tashi, kuma suna ihu suna kiran sunan Humaira ta kawo musu dauki domin rayuwarsu tana cikin tsaka mai wuya. A wannan lokaci Huamaira da Shamzabul Azwas babu wanda ya sami rauni ko daya a jikinsu, kuma babu mai nuna almar gajiya a tare da shi, tamkar ma a sannan suka fara gumurzun. Koda Humaira ta hango hali da su sarki Sahibul Hairi suke ciki sai ta fusata ainun ta ci gaba da karanta addu'o'i da ta fara yi a dazu, sannan ta afkawa Shamzabul Azwas da dukkan karfinta tana mai kai masa mugun sara da suka. Wannan karon sai labari yasha banbandomin karfin saran nata da nauyinsa sai ya ninka na Shamzabul Azwas sau uku har ta kai cewa baya iya mai da martani kuma da kyar yake iya kare harin. Ana cikin haka ne da ta kawo masa wannan sara a ka ya kare da takobinsa sai da ya durkuahe kasa bisa gwiwoyinsa. Take takobinsa da tata suka rabe gida bibiyu. Karfin saran ya sa Shamzabul Azwas ya fadi kasa ya mirgina baya sau uku, sannan ya mike zaune zumbur! A lokaci guda duk su biyun suka dubi gutsiran takobin da ke hannunsu suka yi jifa da su. Kawai sai Shamzabul Azwas ya mike tsaye yana murmushin mugunta sannan ya dunkule yatsun hannunsa yana shirin a fara gumurzuwa da hannu. A tunaninsa ya tabbatar da cewa ya fi Humaira karfin dantse, don haka dolene wannan karan ya gama da ita. Koda Humaira ta gane nufin Shamzabul Azwas sai ita ma ta dunkule yatsun hannunta ta daga hannayen sama tayi shirin fara dambe, kuma ta ci gaba da karanta Addu'o'i a cikin zuciyarta. Shamzabul Azwas ya falfalo da gudun tsiya irin nasu na aljanu tamkar walkiya izuwa gareta ya kawo mata wawan naushi a fuska kawai sai yaga ta kare naushin da hannunta. Koda hannunsa da nata suka hadu sai yaji kamar nasa hannayan za su rugurguje, ba shiri ya juya da baya zai kare amma sai ta damko wuyansa da hannun daya ta daga shi sama tamkar ta dau jariri ta fyada da kasa sannan ta kuma dau kansa da hannu biyu ta cillashi sama kamar takarada. Shamzabul Azwas ya fado kan rusassun tubalin gini a galabaice. Kafin ya sami damar mikewa Humaira ta bayyana tsulum a gabansa ta tallafo kansa da hannunta na hagu sannan ta dinga gabza masa lugude naushi a fuskarsa da hannunta na dama. Nan da nan ta hada masa jini da majina ta sauyawa fuakarsa kamanni. Nan take Shamzabul Azwas ya sume, Humaira ta sakeshi sai ya baje a kas tamkar gawa. Kawai sai ta sunkuya tana mai karanta Bismillah, ta kwance wannan damara daga kugunsa mai dauke da sunayen Allah tsarkaka ta daura a kugunta. Gama hakan ke da wuya sai ta ruga wajan su Sarki Sahibul Hairi domin ta ceci rayuwarsu. Gunguma-gunguman tobalin dutse ne ya danne su sarki Sahibul Hairi wanda inda karti goma za su taru baza su iya dagashi ba, amma sai ga Humaira tana dauke tubalan duwatsun tana wurgi da su can gefe daya. Cikin dakika kadan ta zaro sarki Sahibul Hairi, Alfila da Bawa Haluf sai suka tsandara ihu sabo da abin da suka hango a bayanta. Kafin Humaira ta juya taga abin da yake tahowa tuni Shamzabul Azwas ya soka mata wani dogon mashi a gadon bayanta. Mashin ya faso ta cikinta. Bisa mamaki sai Humaira ta ga babu ko digon jini da ya zuba daga jikinta sakamakon wannan mashin da ya tsira ma ta. Humaira ta juya tafuskanci Shamzabul Azwas ta ga ya tsaya cak! Yana kallonta cikin tsananin mamaki, nan take Humaira ta sa hannunta ta zare mashin daga cikinta sai gashi sai gashi ramin da mashin ya yi a jikinta sai gashi ya 6ace 6at! Ko alamar rauni babu a wajan. Humaira tasa hannunta biyu ta lankwasa mashin duk da cewa an yishi da karfe mai kwari da kauri, amma sai gashi ta kanannadeshi ta cureshi waje daya tamkar an daka fura a turmi, sannan tayi jifa da shi. Koda ganin wannan abin al'ajabi sai Shamzabul Azwas ya juya da sauri da nufin ya gudu amma sai Humaira ta sake cafo wuyansa. Wannan karon da ta daga shi sama sai da ta yi filfilwa da shi sannan ta fyadashi da kasa ta sa kafarta guda ta take wuyansa sai gashi yana kakarin mutuwa, jini na zuba ta hancinsa da bakinsa. Allah sarkin iko, yanzu in ba Allah ba wazai iya bawa Bil'adama irin wannan gagarumin karfi wanda zai iya yin fada da aljani har ya sami nasara akansa. Lokacin da aljani Shamzabul Azwas ya fara wannan kakarin mutuwa sai ya dubi humaira cikin karfin hali sannan ya bushe da dariya. Al'amarin da ya mutukar bata mamaki ke nan ta daga kafarta daga kan wuyansa sabo da tasan bashi da wani kuzarin da zai iya yin komai. Koda Shamzabul Azwas ya yi tari sai ga gudan jini ya fado daga bakinsa mai kauri tamkar hantar cikinsa ce ta fado. A wannan lokaci idanunsa sunyi jawaur babu kyan gani tamkar wutace ke ruri a cikinsa. Shamzabul Azwas ya bude baki dakar ya dubi Humaira ya ce, ya ke wannan 'yar sarki, ki sani cewa koda kin sami nasarar hallakani to fa baku isa ku fita daga cikin gidan nan ba a raye, idan ma kum fita har abada burin dayanku ba zai ta6a cika ba. Ke na sani cewa so kike addinin musulinci ya bazu ko ina a duniya ya danne sauran addinai? To ki sani cewa munyi mummunar 6arna a boron kasa, kadan ne daga cikin mutane da aljanu za su baka goyan baya. Kai kuma sarki Sahibul Hairi kayi sani cewa burinka bazai ta6a cika ba na shahara da daukaka feye da sauran sarakunan duniya face ka auri wadannan 'yan mata uku da aka yi maka da aka yi mka bayanin su tun da farko. Idan kuwa kana tare da wannan ma 'abociyar addinin musulincin har abada bazaka ta6a haduwa da wadannan 'yammata ba koda kuwa ka kai Alfila wajan mahaifinta ya tai maka maka ku tafi neman 'yan matan. Shawarar da zan baka ita ce duk yadda zakai kayi ka rabu da ita domin burinka ya cika, ina ba haka ba kuqa duk wahalar da ka sha a baya zata zamo ta banza. Koda gama fadin haka sai Humaira ta fusata ta sake take wuyan Shamzabul Azwas ya ci gada da kakarin mutuwa. Kafin cikar dakika dari ya daina motse, komai na jikinsa ya sandare. Faruwar hakan ke da wuya sai gidan gaba daya ya fara nutsewa izuwa karkashin kasa. Cikin tsananin zafin nama Humaira ta goya Alfila ta kama hannun Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf tana mai kiran sunayan Allah tsarkaka. Kawai sai ji tayi an yi sama da ita, a lokacin da gidan ya ci gaba da nutsewa izuwa cikin kasa. Hakika abin al'ajabi baya karewa a duniya. Humaira na dauke da su Sarki Sahibul Hairi a cikin iska sai su kaji an tsai da su cak! Don haka sai suka kallo kas suna ganin yadda fadar Shamzabul Azwas ke ci gaba da nutsewa izuwa cikin kasa. sai da fadar ta gama nutsewa kaf sannan kasar wajen ta koma ta hade tayi lebur tamkkar wani abu bai ta6a faruwa ba a wajen. A sannan ne su Humaira suka ji an sakko da su kas a hankali sun dire bisa turba. Nan take Humaira ta yi wa Allah godiya bisa wannan tai mako da ya bata ta sami nasara akan azzalumi Shamzabul Azwas wanda ya dade yana cutar da musulmi a doran kasa. Bayan ta kammala wannan godiya ga Allah sai ta juya ta dubi Sarki Sahibul Hairi, da Bawa Haluf da yarinya Alfila ta ce, "to yanzu ku ganau ne ba hiyau ba, hakika kunga iko da isa irin na Ubangijina bisa yadda ya bani gagarumin karfi na hallaka boka Shamzabul Azwas, kuma sannan ya tserar da rayuwarmu daga cikin fadarsa. Wannan ya isa hujja a gareku wacce za ta sa kuyi imani cewa babu wani sarki da ya cann canta a bauta masa face Ubangijin Musulinci kuma shi ne kadai mai yin dud abin da ya so. Arziki da Talauci duk nasa ne. Rayuwa da mutuwa na hannunsa, shi ne mai mayar da sarki ya zama bawa, kuma ya daukaka bawa ya zama sarki. Idan har kun gamsu da bayanina ina son a yanzu take ku kar6i addinina mai daraja. Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Sahibul Hairi ya dugunzuma ainun yana tunowa da wasiyar da Boka Shamzabul Azwas ya yi masa kafin Humaira ta hallakashi cewar muddin yana tare da Humaira har adaba burinsa ba zai cika ba. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf da Yarinya Alfila suka kurawa Humaira idanu aka rasa wanda zai ce da ita kala. Koda ganin haka sai Humaira tayi murmushi sannan ta dubi Sarki Sahibul Hairi ta ce, "ya kai wannan sarki mai babban buri, kayi sani cewa musannan sabo da kai na baro kasata na yia wannan tafiya bisa umarnin mahaifina dan na sanyaka bisa tafarkin gaskiya, don ha lallai sai ka ce wani abu a yanzu in a haka ba kuwa zan datse maka dukkan shirinka bisa neman biyana bukatarka". Lokacin da Humaira tazo nan a zancenta sai sarki Sahibul Hairi ya yi ajiyar zuciya gami da gyaran murya sannan ya dubeta ya ce, "ya ke wannan jaruma mai abin mamaki, kiyi sani cewa hakika akwai dumbin abin al'ajabi a cikin lamarun Ubangijinki, to amma duk da haka ina bukatar dan lokaci ka domin na yanke hukunci a cikin zuciyata. Ina son son ki bani dama mu isa birnin su Alfila domin in dankata a hannun mahaifinta. Na yi miki alkawari lallai a sannan ne zan kar6i addininki. To amma wane alkawari za ki yi mini cewa nima nawa burin zai ciki?. Sa'adda Gimbya Humaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi ta ce, "ya kai wannan sarki kayi sani cewa, duniya, mulki da mata da kake son ka mallaka fiye da kowa ba komai bane a wajen Ubangijin musulinci, domin da ya so zai iya baka kamarsu cikin duniya sau ba adadi domin da duniyar da duk abin da ke cikinta da wanda ke wajanta shi ke da ikonsa. Na yarda na amince da duk sharadin da ka zo dashi, kuma kuma zan yi hakuri mu isa har garin su Alfila. Ina mai sanar maka da cewa ko a yanzu ka kar6i addini musulinci to zamu roki Ubangijin musulunci da ya cika maka birinka cikin gaggawa ba tare da ka sha wata wahala ba. Ina gargadarka da kada ka dauki Shawarar wannan fandararran Boka Shamzabul Azwas gafalalle, domin bazata kai ka ko ina ba face izuwa ga halaka. Lallai kayi tunani kuma kayi hattara. Ka sani cewa tsalle daya mutun yake ya fada rijiya."koda gama wannan jawabi sai Gimbiya Humaira ta juya baya ta ci gaba da tafiya tana mai cewa, "ku biyoni mu tafi, domin akwai dogon zango a gabanmu". Ba tare da gardamar ko mai ba kuwa su ukun suka bita a baya suka nufi inda suke tsammanin cewa za su ga aljanin da yya kawosu wannan wuri. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Sarki Sahibul Hairi bayan san sami nasarar shiga fadar Boka Shamzabul Azwas sun hallakashu kuma sun dauko yarinya Alfila. .SARKIN SARAKAIA Littafi Na Huɗu (4) Part B. . Marubucin Littafin Abdul Aziz sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa A CAN BIRNIN MISRA KUWA, LOKACIN DA SU WAZIRI SUKA ISA WAJAN ABINDOGARONSU kuwa, wato boka suka sanar da shi duk irin abin da ya faru tsakaninsu da dokin Aminul Has sai ya cika da tsananin mamaki yai shiru ya shiga tunani. Daga can kawai sai ya runtse idanunsa ya shiga karanta wadansu dalasiman tsafi. Yana cikin haka ne awani irin turaren hayaki ya fara fitowa ta ckin kunnuwansa, nana take ya kwala ihu ya daina karanta dalasiman tsafin. Al'amarin da ya mutukar furgita su Waziri ke nan su kaji kamar su tashi su ruga da gudu amma sai suka yi ta maza. A sannan ne bokan ya dubi Waziri ya ce, "ya shugabana ai babu yadda za a yi ka sami nasarar hallaka Aminul Has face anyi abu guda. Dole ne ka tura a sato awannan takalmi da yake sanyawa kullum a kafarsa wanda ko barci zai yi baya cireshi, sannan a sato tsohuwar Alkebbassa wadda ya ke sawa kullum a jikinsa da kuma sanda da yake dogarawa kullum. Ku sani cewa irin sihirin da yake jikin wannan Doki nasa da ya gagareku kamuwa shi ne a jokin wadannan abubuwan uku nasa. Da zarar kun sani nasarar rabashi da wadannan abubuwa uku tolallai zaku iya hallakashi a kowane lokaci". Sa'adda su Waziri suka gama jin wannan jawabi sai Hanlalinsu ya dugunzuma suka rasa abin da ke musu dadi domin sun san cewa sato wadannan abubuwa uku daidai yake da tafiya ne man jiki mai kaho tun da de dare da rana sarki Aminul Has na tare da su sannan kuma akwai kyakkyawan tsaro na dakaru a cikin gidan sarautar don haka basu san yadda za a yi ba a shiga har cikin turakar Aminul Has a sato abubuwan uku. Bayan su Waziri sun yi nazarin maganar boka sun yi tunani akan al'amarin sai dukkaninsu suka rasa abin cewa. Daga can sai Waziri ya dubi bola ya ce, "ya kai abin dogaranmu kayi sani cewa mu kammu ba mu ga mahalukin da zai iya sato wadannan abubuwa uku ba sabo da haka wannnan bukata tafi karfimmu sai dai mu hakura gaba daya, in ya so mu yi hijira mu bar garin domin ba zamu iya ci gaba da zama ba muna ganin abin takaici". Ya yin da boka yaji wannan batu sai ya bushe da dariya. Al'amarin da ya baiwa su Waziri mamaki ke nan. Daga can kuma sai bokan ya hada rai ya ce, "ya ku wadannan sarakai kuyi sani cewa akwai mani shahararran kungurmin 6arawo a birnin kisra wanda zai iya wannan aiki ana kiransa da suna Baruzul Damsus. Ina tabbatar muku da cewa wannan 6arawon yana da karfin Sihiri mutuka kuma a halin yanzu duk duniya babu wani 6arawo da da ya fishi kwarewa da sa'a kan sata, domin yafi shekaru arba'in yana sata amma ko sau daya bai ta6a haduwa ba da 6acin rana ko rashin sa'a. Ina mai shawartarku da ku gaggauta zuwa can Birnin Kisra ku gana da wannan 6arawo. Amma ku tabbata kun tafi da Durhami mai ya wan gaske, domin aikinsa na da mutukar tsada, idan attajiri bai bunkasa ba farat! Daya yake talautashi. Asalin Baruzul Damsus baya harka da kananan Attajirai da kananan sarakai sai wandanda suka gawurta a duniya". Lokacin da Boka ya zo nan a zancensa sai Waziri ya bushe da dariyar farin ciki ya ce, "ai wannan abu ne mai sauki, domin idan so yake na shimfida Durhami a ko ina a cikin 8irni Kisra ya zamo abin takawar jama'a zan iya yin hakan". Nan take Waziri ya yiwa boka sallama sannan ya kawo zinare guda dari ya bashi suka tafi suka barshi. Kashegari kuwa tun da duku-dukun safiya Waziri tare da magoya bayansa mutum biyu suka ya shirin kama hanya suka nufi birnin Kisra Lokacin da suka isa birnin suna tambayar gidan 6arawo Baruzul Damsus aka sa su akan hanya domin gidan ba 6oyayye bane amma a karshen gari yake. Tafiyar rabin sa'a suka yi kacal suka isa kofar gidan. Da zuwa sai suka iske gaba daya kofofin gidan a bude suke kuma babu masu gadi a kofar gidan, sannan duk inda suka duba basa ganin komai face buhunhuna cike da lu'u-lu'u, da zinare, jahurma da sauransu. Kai har a kasa ma an zubar da wannan dukiya ga ta nan birjik! Ga ta nan birjik ba adadi sai mutun ya takata da kafafuwansa sannan zai iya shiga gidan. Al'amarin da ya baiwa su Waziri mamaki ke nan suka tambayi kansu a cikin zuciyoyinsu cewa Baruzul Damsus ba ya tsoran wasu 6arayin su zo su yashe shi ne? Amsar da suka baiwa kansu ita ce, "ai kura ta san gidan mai babbar sanda." Nan dai su Waziri suka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak! A kofar gidan kamar masu jiran a basu umarni. Kwatsam! Sai suka ji an bushe da mahaukaciyar dariya amma kuma ba su ga mai yin dariyar ba. Daga can kuma sai aka daina yin dariyar aka ce, "lale marhaban da manyan sarakai daga birnin Misra, ku yi sani cewa na dade ina jiran wannan rana da zaku kawo mini wannan babbar ziyara sabo da haka ku manyan baki ne masu mutukar mahimmanci a gareni. Na umarceku da ku shiga gidan nawa, domin mu gana". Koda ji wannan batu sai farin ciki ya lullube su Waziri suka sauko daga kan dawakansu suka dauresu, sanna suka kunna kai izuwa cikin gidan. Sai da suka yi 'yar doguwar tafiya sannan suka isa wata kasaitacciyar fada ta gaban kwatance wadda ko fadar sarkin birnin Kisran bata kai ta ba a kyau da tsaruwa. Kuyangi da barori na tai kawo a cikin fadar suna ta hidima. Can kuma ga wani mutunnan zaune akan wata kasaitacciyar karagar mulki ta kasita 6arawo Baruzul Damsus ne fuskarsa cike da annuri, a gabansa an ajiye wani tebur cikie da kayan abinci da na sha iri-iri. Koda shi gowar su Waziri sai Baruzul Damsus ya mike tsaye da kansa ya tarbesu yana mai rungume Waziri cikin mutukar farin ciki kamar wanda ya ga babban amininsa, bayan dan lokaci sai ya janye jikinsa daga cikin na Waziri, sannan ya jasu inda karagar mulkin tasa take ya zaunar da su kuma ya yi musu tayi abincin da ke gabansu. Ba tare da gardamar komai ba suka hau kintsawa har sai da suka ji sun gamsu amma basu cinye kaso daya ba cikin kaso goma na abincin da ke gabansu. Lokacin da 6arawo Baruzul Damsus ya ga su Waziri sun sami nutsuwa sai yai gyaran murya sannan ya dubi Waziri ya ce, "na san cewa baku zo gareni domin komai ba sai domin na yi muku gagarumin aiki na sato takalmi da Alkebba da sanda na Sarki Aminul Has, ko ba haka bane? Cikin tsananin mamaki duk su ukun suka bude baki suka ce, "tabbas maganarka dutse ce". Damsus ya yi murmushi sannan ya ce, "hakika wannan aiki da kuka zo min dashi na san dashi fiye da shekara goma baya kuma na san cewa duk ranar da Sarki Sahibul Hairi ya bar ksarsa za ku zo gareni, domin aikin, inaso ku sani cewa wannan aikin yana da mutukar hadari, dole ne cikin biyu ayi daya. Ko dai ayi nasara ko dai na rasa rayuwata. Lallai zanyu wannan aiki, amma bisa sharadi guda. Shadin kuwa shi ne, idan har na sami nasara kammala aikin da zarar kun hau kan karagar mulki zaku raba dukiyar birnin Misra kaf biyu ku bani kaso guda. Wannan shi ne babban burina a duniya." Koda jin haka sai su Waziri suka yi tsuru-tsuru da idanu suka cika da tsananin mamaki. Daga can sai waziri yayi ajiyar zuciya ya ce, "ya kai wannan kungurmin 6arawo, kayi sani cewa kazo mana da babban al'amari sabo da haka akwai bukatar muyi shawara." Koda jin haka sai Baruzul Damsus ya yi murmushi ya ce, "na baku kwana biyu kuyi shawara. Yanzu zan sa a kaiku masaukinku dan ku huta sosai". Gama fadin haka ke da wuya sai Damsus ya kira wata kuyanga ya umarceta da ta kai su Waziri masauki. Nan take su Waziri suka mike tsaye suka wanke hannayansu da ruwa sakamakon abincin da suka ci. Sannan suka bi bayan kuyangar izuwa masauki. Da shigarsu cikin wannan katon daki wanda aka kawatashi da gadaje da shinfidu na alfarma sai suka cika da tsananin mamaki, suka tabbatar da cewa ba a cikin karamar daula suke ba. Cikin su6utar baki daya daga cikin su ya ce, "hakika kai gidannan ba karamin attajiri bane. Ai ko a gidan sarautar birnin Hindu bana jin akwai dakin da yakawatu kamar wannan". Koda jin wannan batu sai kuyangar tai murmushi ta ce, "ai in ba dan matarsa ta ci amanarsa ba ta gudu da rabin dukiyarsa da sai in ce da ku bana tsammaninza a sami wani mutun guda daya mai karfin arziki tamkarsa a duniya". Koda jin wannan batu sai Waziri ya dubi kuyangar cikin kaduwa

Chapter 12 of 19