Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan matsafiya ki gayamin abin da ki ke so na yi domin ki kyale mahaifina kada ki salwantar da rayuwarsa". Koda jin haka sai sadauki Awaisu ya yi farat ya ce,"ya ke 'yata kada kibi uamarnin wannan azzaluma domin ko kinyi abin da take so ba zata fasa hallakamu ba. ki sani cewa ta cika mayaudariya kuma maci amana, kuma a halin yanzu tafi kowa karfin sihiri a duniya. sihiri daya ne ya rage mata wato wanda ke cikin jikinki". Alfila ta kalli Awaisu cikin mamaki ta ce, "ya kai abbana yaya akayi wannan mata ta samu nasara a kanka alhalin kafi karfin dantse da na sihiri?" Awaisu ya kwada kai cikin takaici ya ce, "Ai kamar yadda na gaya miki ta zo garinnan a siffar 'yar uwar mahaifiyarki wacce ke zaune a birnin kisra wadda rabona da ita tun da aka yi rashin mahaifiyarki tun da ta tafi bata sake dawowa garin nan ba. kwatsam sai na ganta ta zo. Bayan na sauketa a gidana sai ta gaya mini cewa anyi yakine a birnin kisra an kashe mijinta da 'ya 'yanta biyu don haka yanzu bata da kowa a duniya shi yasa ta dawo garemu. A lokacin ne ta tambayi labarinki na gaya ma ta cewa ai boka shamzabul Azwas ya sace ki tsawan shekaru. Koda jin haka sai ta fashe da matsanaicin kuka na bakin ciki. Da kyar da sidin goshi na shawo kanta ta daina kukan. Ina mai rarrashinta ta na cewa shi ke nan yanzu babu wanda za ta kalla ta gani a matsayi. tsatson jininta. Daga wannan rana ta ci gaba da zama a gidana ya zamana cewa tanayin ayyukan gida kamar yadda mahaifiyarki ke yi mini sa'adda tana raye. Hatta abinci itace take girkawa tana bani ina ci. Kin sani cewa da ma ita 'yar uwar mahaifiyar taki kamrsu daya da mahaifiyar taki don haka sai soyayya ta shiga tsakaninmu. Cikin kankanin lokaci magaar aure ta wakana. A daren da na shiga dakin Amarya ne na tsinci kaina a cikin wani irin mugun hali domin nan take na daina Jin kwarin jikina na yan ke jiki na fado kasa daga kan gado kuma naji ko danyatsan hannuna bazan iya dagawa ba. Haka kuma sai na ji gaba daya sirrikan tsafina sun daina aiki. A wannan lokacin Amaryata tana zaune a gefan gado kawai ta Kura mini ido tana murmushin mugunta. Da kyar na juyar da kaina na kalleta kuma na bude baki na ce, "ya ke matata ina dalilin faruwar wannan al'amari a gareni?. Koda jin wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan tayi girgiza ta rikide izuwa kamannin Shukura matar sarki Barusa. Nan take ta gabatar da kanta a gareni sannan ta ce,"ya kai wannan Sadauki kayi Sani cewa 'yar uwar matarka tana can birnin kisra tare da mijinta da 'ya 'yanta lafiya kalau, Kawai na juya izuwa kwmannin ta ne na zo nan kasar domin na Kama garin naku Karin su sarki Sahibul Hairi su iso tare da 'yarka Alfila". Koda jin haka sai na cika da farin ciki duk da cewa ina cikin wannan hali name ce yanzu kina nufin cewa su sarki Sahibul Hairi sun sami nasarar dauko Alfila daga fadar sarki Shamzabul Azwas?" Shukura tayi murmushi ta ce, "kwarai kuwa kuma suna nan akan hanyarsu ta zuwa nan domin su mika Alfila a gareka. Bukatar Sarki Sahibul Hairi itace ka daukeshi ka kaishi gurin 'yam mata uku wadanda idan ya sure su sai yafi kowa na sarki daukaka, mulki da karfin arzuki. Ni kuwa bazan ta6a bari ya samu wannan matsayin ba, idan ya sameshi burina na son mulkar duniyar nan gaba daya ba zai cika back. Lallai nice nake son na hau wannan matsayi wanda sarki Sahibul Hairi ke bukata. Abu na farko da zanyi shi ne, na sake rabaka da 'yarka Alfila na tafi da ita izuwa can birninmu na cire sirrikan tsafin jikinta wanda ka sa Mata na Mai da shi jikina domin na samu irin karfi da boka Shamzabul Azwas ya Samu. Kai kanka ka sani cewa Alfila ce kawai mai irin wannan karfin. Bayin na cire sirrin daga jikinta na sa shi a jikina sannan sai ka rakani inda wadannan mata uku suke domin na kamasu suma na cire sihirin da ke jikinsu ya zamana cewa nafi kowa arziki da daukaka a duniya tunda na fi kowa karfin sihiri". Koda gama wannan jawabi sai Shukura ta bushe da dariyar mugunta. Tana cikin dariyane ta dafani, nan take muka 6ace tare ni da ita. Bamu bayyana a ko ina ba sai a tsakiyar turakar nan inda muka iske a kwance kan gadonsa yana ta shara barci. Nan take tayi nuni da hannunta sarkar tsafi ta daureshi. Nima sai ta nunoni da hannu na tsinci kaina a kan gadon daure da sarkar sihiri kamar yadda sarki ya kasance. Tun daga wannan rana Shukura ta rinka wanzuwa a cikin siffar sarkinmu shi yasa kika ga kowa yana biyayya a gareta sai abin da ta ce shi ake yi. Yanzu ke kadai ce kika ganinta a cikin ainihin siffarta.... Hatta ni da sarki a cikin siffar sarkin muke ganinta". Koda jin wannan batu sai Alfila ta juya ta kalli Shukura ta ce, "yanzu me kike son na yi miki ki kyale mahaifina baza ki kashe shi ba?". Sa'adda gimbiya Shukura ta ji wannan batu daga bakin Alfila sai ta tuntsure da dariyar farin ciki sannan ta murtuke fuska tamkar wadda aka aikowa mata da sakon mutuwa ta ce, " abu na farko da nake so ki yi shi ne, ina so ki cire damarar da ke jikinki ki ajiyeta a gefe daya sannan na baki wuta ki kona damarar da hannunki Abu na biyu da za kiyi shi ne, zaki koma can kofar garin tare da ni, kuma zan je ne a siffar mahaifinki domin mutarbu su sarki Sahibul Hairi mu shigo da su har nan cikin fadar domin na hallakasu cikin salim alim sannan na dauke ki na tafi da ke". Koda jin wannan batu sai Alfila ta mike tsaye daga kan mahaifinta ta dubi shukura ta ce, "yanzu mene ne tabbaci idan na aikata duk abin da ki ka umarceni baza ki ta6a lafiyar mahaifina ba.?" Da jin wannan tambaya sai shukura ta yi murmushi ta ce, zaki sameni mai cika alkawari idan har ki ka aikata abin da na umarceki". Alfila ta ce, "ai ke ba mai cika alkawari bace. Idan da mai cika alkawari ce baza ki ta6a cin amanar mijinki ba sarki Barusa tunda bai rageki da komai ba a rayuwarsa, sannan ya nuna miki tsananin kauna kamar yadda uwa ko uba yake son dan da suka Haifa". Kada jin wannan batu sai Shukura ta fusata ta sake nuni da hannunta izuwa kan sadauki Awaisu kawai sai wannan sarka ta sihiri ta kara matse sadauki Awaisu tamau fiye da karon farko. Awaisu ya kurma uban ihu, wannan karon har sai da kashin kafarsa ya karye yai kara kal! Alfila ta rusa ihu Kuma ta zare takobinta tai kan Shukura da nufin ta sareta, sai Shikura ta daka mata tsawa ta ce, "idan ki ka karaso inda nake zan karasa mahaifinki. Kawai ki yi abin da na umarceki baki da wani za6i". Cikin karfin hali Awaisu ya dubi Alfila a lokacin da gaba dayan fuskarsa ta cika da gumin wahala ya ce, "Na gaya miki kada ki bi umarninta. Da dai ta umarceki ki ci amanar su sarki Sahibul Hairi wadanda suka sha wahala suka daukoki daga cikin fadar Shamzabul Azwas kuma suka kawoki har nan domain ki sadu da ni ai gwara ki bari ta kasheni Fatana shi ne burina kada ya cika tunda ta kasance azzaluma wadda zata haddasa zalunci da bakin mulki a doran kasa. ya ke 'yata na gani a cikin madubin tsafina cewa kin kar6i addinin musulinci a gurin gimbiya Humaira tun kafin Shukura tazo garin nan, kuma ko kadan bana bakin ciki da hakan. Dama shirina shi ne, da zarar kin dawo gareni ni ma na kar6i wannan addinin kuma nasa sarkin mu shi ma ya kar6a domin gaba daya al'umar kasan nan su ma su kar6eshi. ya ke 'yata in kika ka bi umarnin shukura duk wannan shirin ya wargatse ke nan. Ina tabbatar miki da cewa ni da sarki duk mutuwa zamu yi". Lokacin da sadauki Awaisu ya zo nan a zancensa sai hankalin Alfila ya dugunzuma ta rasa abinda zata yankewa kanta hukunci. kawai sai ta Kama kallon fuskar sarki da ta sadauki Awisu a sannan kuma sai ta dubi shikura wacceke tsaye tana ta murmushi mugunta. Alfila ta kama duru-duru da sake-saken zuciya. Bayan ta danyi nazari a cikin zuciyarta sai kawai ta kwance wannan damara dake jikinta ta ajiye a gefe daya. Koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar mugunta da farin ciki. Nan take shukura tai tsafi sai ga wutar ice ta bayyana a hannunta. Kawai sai ta mikawa Alfila wutar sai ta kar6a sannan tace da ita, "maza ki kona wannan damara". Alfila ta nufi inda ta jefar da damarar tana waigen shukura da su sadauki Awaisu hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, kai da gani kasan ba a san ranta zata kona damarar ba sai bisa dole tunda ba yadda za ta yi. Shi kuwa sadauki Awaisu sai takaici ya rufeshi bai san sa'adda ya matso kwallar bakin ciki ba. Shi kuwa sarki dama ya dade yanata kukan zuci da zahiri bisa halin da ya tsinci kansa karkashin ikon gimbiya shukura a matsayinsa na sarkin guda mai cikakken iko amma sai yadda aka sarrafashi tun da gashi an kwace masa karagasa da jama'arsa. Tun daga ranar da ya bude ido daga bacci yaga shukura tsaye a kansa bai kara mikewa zaune ba yana kwance kan gado a daure, shukurace ta ci gaba da zartar da komai na sarautar Kasar. Haka Alfila ta dosana wannan wuta a kan wannan damara tana ji tana gani. Nan take damarar ta kama cin wuta, cikin dakika kadan ta kone kurmus ta zama toka. Koda ganin haka sai gimbiya shukura ta bushe da dariyar farin ciki, ta ce, ‘’yanzu kin bi umarnina na daya da na biyu saura na uku kawai. Sai ki biyoni a baya muje can kofar gari inda kika baro su sarki Sahibul Hairi. Kafin mu tafi ina mai gargadinki da kada ki kuskura ki ce za wani abu ba dai-dai ba a gareni domin kina yin dan kuskureko kika ce zaki tona min asiri a wajan su gimbiya Humaira a bakin ran mahaifinki.’’ Gama fadin haka ki da wuya sa gimbiya Shukura ta juya ta fice daga cikin turakar, Alfila ta bita da sauri a lokacin da sadauki Awaisu ya bisu da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki hawaye na kwarara bisa kumatunsa. Gimbiya Shukura da Alfila suka jera suna tafiya a cikin harabar gidan sarautar tamkar babu wata damuwa a tsakaninsu. Abin da idanun jama’ar gidan ke gani shi ne, Sarkinsu tare da Alfila ‘yar sarkin yaki don haka duk inda suka wuce sai ayi ta kallonsu cikin mutukar mamaki domin an san cewa Alfila ta 6ace tsawon shekaru amma yanzu gashi ta dawo, alhalin an ce sarkin bokayan aljanun duniya ne ya saceta kuma babu mahalukin da zai iya shiga fadarsa ya kar6ota. SARKIN SARAKAI Littafi Na Biyar (5) Part C. . Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini Admin AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa.. . ALHALIN ANCE SARKIN BOKAYEN ALJANUN DUNIYA NE YA SACETA KUMA BABU MAHALUKIN DA ZAI IYA ZUWA FADARSA YA KARBOTA To wai shin yanzu yaya aka yi ta dawo gida ? Amsar da babu wanda ya san ta ke nan, sarki sahibul hairi, bawa haluf, da gimbiya humaira suna zaune a kofar birnin sun gaji ainun da jiran dawowar yarinya alfila, sun kagu sosai, har humaira ta fara zargin anya kuwa lafiya? Bai kamata suci gaba da jiran gawar shanu ba cikin matukar damuwa sarki sahibul hairi ya dubi humaira yace yake wannan jaruma mai abin mamaki, yanzu me ya kamata muyi? Humaira tace ai tun da dai yarinyar nan ta dade bata dawo ba lallai akwai abin da ya faru ba dai dai ba saboda haka ina ganin cewa kawai mu shiga cikin garin nan ta kowanne hali koda salama ko da tsiya tsiya nan take humaira ta mike tsaye ta zare takobinta ta nufi bakin kofar cikin sauri sarki sauri sarki sahibul hairi da bawa haluf ma suka zare nasu takubban suka take mata baya koda masu tsaron kofar suka hangosu sai suma suka zazzare nasu makaman suka tsaya suna jiran isowarsu a ruguntsume ba zato ba tsammani sai masu tsaron kofar sukaji an daka musu tsawa daga bayansu cikin sauri suka waiga sai suka ga ashe sarkinsu ne tare da yarinya alfila cikin gaggawa suka dare suka basu hanya suka wuce ta tsakiyarsu suka nufi inda su humaira suke humaira sarki sahibul hairi da bawa haluf sai suka cika da tsanannin mamaki lokacin da suka hango yarinya alfila tare da mahaifinta sadauki awaisu a tafe cikin nishadi awaisu rike da hannun alfila, da isowarsu sai awaisu ya dubi sarki sahibul hairi cikin tsananin farin ciki ya ruguntsumeshi yana mai cewa, lale marhaban da sarki mai daraja wanda ya share mini hawayen bakin ciki na tsawon shekaru lallai zan kasance mai taimakonka har izuwa lokacin da bukatarka zata biya koda kuwa zan rasa rayuwata koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya cika da matukar farin ciki ya janye jikinsa daga cikin nasa awaisu, sannan ya bashi hannu suka gaisa koda gaisuwar tasu sai jikin sarki sahibul hairi yayi sanyi, ba komai ne ya janyo hakan ba face irin yanayin da yaji hannun awaisu mai tsananin taushi tamkar na mata awaisu ya dubi sarki sahibul hairi ya ce yanaga jikinka ya yi sanyi ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace, babu komai, kawai na tuno da irin halin da kake ciki ne a yanzu na farin ciki bisa sake saduwa da yarka alfila tabbas na san cewa a yanzu babu wanda ya fika murna da kwanciyar hankali a wannan birni koda jin wannan batu sai awaisu ya bushe da dariya yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne kuma babu wanda ya fini bakin ciki a lokacin da aka rabani da alfila inda baku je kun daukota kun dawo mini da ita ba, tabbas zan iya kamuwa da cutar ajali a ko yaushe koda gama fadin haka sai awaisu ya dubi gimbiya humaira da bawa haluf da kyau sannan yayi murmushi yace an gaisheku manyan jarumai hakika kun sha gwagwarmaya tsakaninku da sarki shamzubulu azwas da sarki barusa, na gamsu cewar kun cika manyan sadaukai a duniya wadanda har abada ba za a manta da tarihin sadaukantakar suba cikin matukar mamaki humaira ta dubi awaisu tace yaya akayi ka san irin gwagwarmayar da muka yi dasu shamzubul azwas alhalin tsafinsu yafi naka tasiri ba za ka iya ganin al amarinsu ba a cikin tsafinka koda jin wannan tambaya sai sadauki awaisu ya dan rikice ya kasa bada amsa da wuri amma sai ya dan wayance yace ai alfila ce ta bani labarin duk abinda ya faru a gareku koda jin haka sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi dan murmushi ita kuwa sai ta tsuke fuska domin ko kadan bata ji ta aminta da awaisu ba awaisu ya dubesu gaba daya cikin fara a yace yanzu saiku zo mu shiga cikin gari domin muje gidana ku zauna ku huta kuci abinci ba tare da gardamar komai ba kuwa su humaira suka bi sadauki awaisu da alfila izuwa cikin garin sai da suka yi yar tafiya mai dan tsawo sannan suka iso gidan sadauki awaisu da zuwa masu gadi suka bude musu kofa suka shiga ciki shigarsu keda wuya sai ga kuyangi maza da mata sun tarbesu da lale marhaban, sukayi musu rakiya har izuwa babbar turakar gidan daga nan kuma sai awaisu ya umarci wani hadimi da yaje ya nunawa humaira nata dakin daban sarki sahibul hairi da bawa haluf ma sai aka kaisu nasu dakin daban kuma aka umarci kuyangi da su shirya abinci na musamman ga baki lokacin da aka kai humaira dakinta aka tafi aka barta ita kadai sai ta rufe kofar dakin sannan ta shiga kewaye taje taayi alwala ta gabatar da sallah, a lokacinne ta tuno da alfila da tace a ranta 'Allah ya sa dai alfila bata shagala ba ga barin yin sallah bisa farin cikin saduwa da mahaifinta koda aiyana hakan sai humaira taji zuciyarta ta buga da karfi nan take hankalinta ya dugunzuma ta tuno da tambayar da ta yiwa awaisu dazu ya dabarbarce ya kasa bata amsa da wuri nan take taji bata amince da awaisu ba a cikin ranta ta fara wasi wasi a zuciyarta tana mai cewa 'Anya kuwa wannan awaisun ne ainihin mahaifin alfila? Nikam ba zan saki jiki dashi ba har izuwa lokacin rabuwarmu AA Misau Nake Magana, Gama aiyana hakan keda wuya sai humaira taji an kwankwasa mata kofa Al amarin da ya fusata ta kenan tace a ranta, Me za ayi da irin wannan al adar banza ta kafirai, sai dai a kwankwasa maka kofa ba za ayi maka sallama irin ta addinin musulunci ba ? Kawai sai ta bude baki tace shigo koda kofar ta bude tayi arba da wani kyakkyawan saurayi mai tsananin kyau tun da humaira tazo duniya bata taba ganin da namiji mai kyansa ba saurayin yaci ado na gaban kwatance cikin sutura mai tsadar gaske wacce tafi karfin karamin sarki hakika babu wata ya mace lafiyayyiya da zataga wannan saurayi bataji sha awarsa ba saurayin na dauke da farantin abinci na kasaita iri iri gami da ababan sha danginsu ruwan inibi da ruwan hadaddan tataccen sauran yayan itatuwa kamshinsu ya cika dakin gaba daya, koda humaira tayi arba da wannan saurayi sai zuciyarta ta buga da karfi a karo na biyu nan take tayi hailala a cikin zuciyarta ta nemi tsarin Allah daga shaidan, nan take kuwa taji ta tsani saurayin kuma ta tsani abincin da ya kawo yayin da saurayin ya ajiyea farantin abincin bisa wani tebur dake daf da humaira sai ya tsugunna ya dauki tambulan na ruwan inibi zai zuba a kofi da nufin ya mika mata domin ya birgeta ko kallonsa batayi ba ta daka masa tsawa tace bana bukatar kayi mini komai kuma kayi sauri ka bace mini da gani, cikin rawar jiki saurayin ya mike zumbur ya fice daga cikin dakin bai zame ko ina ba sai wannan babbar turaka ta gidan inda ya iske alfila da awaisu zaune sunyi jugun jugun babu mai cewa uffan cikin girmamawa saurayin ya durkusa a gaban awaisu sai ya rikide ya zama wani bakin aljani mai matukar muni da ban tsoro awaisu ya dubi aljanin yace menene labari yakai zarmalu? Aljani zarmulu ya dukar da kansa cikin alamun tsoro da fargaba yace ya shugabana aiko kadan humaira bata saurareni ba, koroni ma tayi kuma sa adda na matsa daf da ita sai naji kamar an tsamoni a cikin tafasashshen ruwa ba shiri na fito daga cikin dakin koda jin haka sai bakin ciki ya lullube awaisu ita kuwa alfila sai ta cika da farin ciki , awaisu ya sake duban aljani zarmalu yace ya ya batun sarki sahibul hairi da bawansa haluf kuma? Koda jin wannan tambaya sai zarmalu yayi murmushi yace ai wadannan tuni mun fara samun nasara akansu domin tuni sunci abincin da muka basu har sun bingire da barci awaisu yayi murmushi yace da kyau zarmalu, aikinka na kyau AA Misau Ke Magana, Lallai a daren yau zan hallaka sarki sahibul hairi da bawansa haluf ita kuwa humaira kafin daren yayi lallai zamu sake jarraba wani tuggun akanta domin mu sami lagonta Ka sani cewa ita musulma ce tana da karfin tsari irin nasu a jikinta sai munyi da gaske, zarmalu yayi ajiyar zuciya yace ai ni dai kam tafi karfina ya shugabana ba zan iya sake tunkararta ba sai dai ke da kanki ki san hanyar da zaki bullo mata Dajin haka sai awaisu ya bushe da dariya yace ai babu mai tarar zaki sai dan uwansa zaki ka barni da ita, lallai a daren yau zanga karshenta kafin wayewar gari tashi ka tafi na sallameka, koda gama fadin haka sai aljani zarmalu ya daidaice tamkar yayan kwayar zarra sannan ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajen ba bacewarsa keda wuya sai awaisu ya dubi alfila ya tuntsire da dariya sannan ya hade fuska yace na gama da abokan tafiyarki biyu saura guda daya jal ina mai dada yi miki tuni da cewar idan kika kuskura kikayi wani abu ba dai dai ba lallai zakiyi arba da gawar mahaifinki a ko yaushe koda jin wannan batu sai idanun alfila suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye hawayen takaici da bakin ciki AL AMARIN gimbiya humaira kuwa bayan ta kori wannan kyakkyawan saurayi daga cikin dakinta sai taki cin wannan abinci da ya kawo mata na alfarma duk da cewa kuwa tana jin yunwa da kishirwa kawai sai ta bude jakarta ta dauko ragowar wani gasashshen nama daga cikin guzurinta na tafiyar taci kuma ta daga battar ruwanta ta sha sannan tayi godiya ga Allah kammala cin abincin keda wuya sai taji babu abin da take so sama da ganin abokan tafiyarta, gashi bata san dakin da aka kaisu ba kawai sai ta mike tsaye ta fara tafiya ba tare da fargabar komai ba ta bude kofar dakinta ta fita ta janyo kofar ta rufe sannan taci gaba da tafiya a cikin gidan tana shiga wannan lungu, ta fada wancan sako tana leka kowanne daki bisa mamaki sai humaira taga Allah ya makantar da dukkanin barorin gidan da hadimai sam basa ganinta kuma gashi ta gabansu take wucewa, wani lokacin ma ta tsakiyarsu take ratsewa har tana bangazar kafadunsu amma ko alamun ta basa ji bare su ganta AA Misau Sunana haka dai humaira taci gaba da leka cikin dakuna daban daban har ta shiga dakin dasu sarki sahibul hairi suke da shigarta cikin dakin sai ta iskesu a kwance tamkar gawarwaki ko numfashin kirki basa yi cikim rudewa da tashin hankali ta ruga kansu ta tsugunna kawai sai ta fara karanta addu oi na musamman tana tofa musu, cikin dakiku kadan suka farka a tare suna masu jan dogon numfashi a lokaci guda kuma a firgice suka mike zaune zumbur suna zare idanu Al amarin da ya baiwa humaira dariya kenan Bata san sa adda ta dan dara Ba cikin rudewa sarki sahibul hairi ya dubeta yace, yake ma abociyar kyau da jarumta menene ya faru garemu nida bawana haluf? Sa adda humaira taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya sannan tace nidai ina zaune a can dakina ni kadai sai ga wani saurayi mai tsananin kyau irin wanda ban taba gani ba ko a mafarki da labarai ya shigo mini dauke da abinci na alfarma ina ganinsa sai tsigar jikina ta tashi naji ban aminta dashi ba don haka sai na daka masa tsawa na koreshi daga cikin dakin yana fita sai naji bani da sauran sukuni face na ganku domin nasan halin da kuke ciki saboda haka sai na kama karanta wadansu adduo i a cikin zuciyata sannan na fito daga cikin dakina nayi ta dube dube da leke leke har na shigo nan ubangijina bai baiwa kowa ikon ganina ba ina shigowa ana iskeku a kwance tamkar gawarwaki ko numfashin kirki bakwa yi, cikin hanzari na karanta wata addu ar daban na tofa muku, faruwar hakan keda wuya sai naga kun farka firgigit a cikin dimauce tamkar wadanda sukayi dogon suma, lallai abincin da aka baku kuka ci an sa banju mai karfi, a cikinsa saboda haka ni dai ko kadan ban aminta da wannan awaisun ba a matsayin mahaifin alfila AA Misau Ke Magana, Sa adda humaira tazo nan a zancenta sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suka yi ajiyar zuciya a tare suka jinjina al amarin, sannan sarki sahibul hairi ya dubi humaira cikin alamun karayar zuciya yace yake ma abociyar kyawu da jarumta hakika kin ceci rayuwata har sau uku kenan, lallai kina bina bashin da ba na zaton zan iya biya amma ina fatan na samu damar biyanki wannan bashi koda sau daya ne kafin mu rabu, yanzu dai menene abin da ya kamacemu dayi? Humaira taja numfashi tace ya zama dole muyi bincike mu tabbatar da cewa wannan awaisun shine ainihin mahaifin Alfila? Idan kuwa muka gane cewa bashi bane, to fa dole ne ya bamu alfila mu nemi mahaifin na gaskiya mu dankata a hannunsa, nifa abin da ya zaunar dani kenan, kawai a garin nan saboda haka yanzu yanzun nan nake son mu tura a kirawo alfila da mahaifin nata domin mu tantance komai, kafin humaira ta gama rufe bakinta sai sukaji an kwankwasa kofar dakin cikin hadin baki sukace shigo, nan take aka turo kofar saiga bakin bawa ya shigo fuskarsa cike da annuri bawan ya risina a garesu gaba daya yace, yaku wadannan manyan baki masu daraja kuyi sani cewa mai girma sarkin yakine ya turoni nayi muku jagora izuwa can filin shakatawa domin yayi ganawa ta musamman daku koda jin wannan batu sai humaira tayi farat ta fara mikewa tsaye tana mai gyara takobinta dake daure a kugunta tace mu je zuwa ya babban hadimi, koda ganin haka sai sarki sahibul hairi da bawa haluf suma suka mike tsaye da hanzari nan take kuwa bakin bawan ya juya ya fita daga cikin dakin ya nufi wani bangare daban na gidan su humaira na biye dashi haka dai suka ci gaba da tafiya cikin harabar gidan su kutsa nan su fita can kamar tafiyar ba zata kare ba babu abin da ya daurewa su humaira kai face ganin yadda suke ta shiga sako sako, lungu lungu, tafiyar nata kara tsawo kamar ba zasuje inda suka nufa ba, kwatsam ba zato ba tsammani sai suka tsinci kansu a cikin ainihin gidan sarautar birnin kuma a tsakiyar fada, zaune akan karagar mulki sarkin yaki awaisu ne yayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da bam sha awa da isowar su humaira cikin fadar suka ga dakarun yaki na aljanu da na bil adama masu yawan tsiya ba adadi sunyi musu kawanya tun da sarki sahibul hairi yake gumurzu da gwagwarmaya bai taba ganin dakaru masu matukar ban tsoro ba irin wadannan, domin girmansu ya wuce misali, makaman yakin da suke rike dasu kuwa wani kalarma ko a tunani kwakwalwa bazata taba kawoshi ba, koda su humaira sukaga wadannan dakaru sunyi musu kawanya sai duk su ukun suka zare takubbansu suka hada bayansu a tsakiya, ma ana kowannansu ya dubi fuska guda ya zamana cewa sun hade jikinsu a tsakiya suna nazari ta bangaren da za a fara kawo musu farmaki kawai sai humaira taji jikin sarki sahibul hairi dana bawa haluf ya kama karkarwa kai da gani ka san cewa a tsorace suke ainun koda fahimtar hakan sai humaira ta daka musu tsawa tace yaku abokan tafiya ku saki jikinku, ku daina shakkar komai, da izinin ubangijina babu abinda zai sami dayanku tabbas mun fado cikin tarkon abokan gaba kuma ta kowanne hali sai mun fita yakai sarki sahibul hairi ka mantane da duk irin hadarurrukan da aka shiga a baya ka sha bakar wahala tamkar ranka zai salwanta, amma sai gashi duka ka tsira? Ai mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya gani kafin humaira ta gama rufe bakinta sai sukaji sarkin yaki awaisu

Chapter 17 of 19