Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwantar mata da hankali gami da bata tabbaci cewa Hurbas bazai ci amanarsa ba. Lallai zai dawo masa da damarar bayan ya kawo matar Shaharuz zaman ya kone gidansa. Har su Saif suka gama binne shahidai suka koma gida bai ga dawowar abokinsa Hurbas ba. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ya kama wasu-wasin zuci. Da farko sai ya fara tunani ya hau doki yabi bayan Hurbas, amma sai wata zuciyar ta ce da shi. "Haba sai wai shin shakkar me kake yi? Tun da kasan Hurbas ba zai ha'in ceka ba ai ba sai kabi bayansa ba. Ba shakka bai gama abinda ya je yi bane shi yasa har yanzu bai dawo ba". Haka dai Saif ya yi ta tunani har dare ya yi barci ya sace shi bai sani ba. Da tsakar dare Saif na bacci sai yaji ana luma masa makami a ciki. Take makamin ya burma cikinsa ya burma shimfidar gadon, jini yai tsartuwa. Cikin kiran sunan Allah ya bude idanunsa da kyar, kawai sai yaga Hurbas a tsaye a kansa yana yi masa murmushi mugunta. Cikin tsananin mamaki da takaici Saif ya bude baki ya ce, "ya kai abokina yanzu ashe zaka iya cin amanata?" Koda jin wannan tambaya sai Hurbas ya bushe da dariya, sannan ya ce, "kayi hakuri ya aminina, ka gafarceni bisa wannan cin amana da nayi maka, domin ba zan iya barin daular da na gani ba a gidan Boka shaharuz zaman ba. Tabbas na za6i duniya akan lahira..... Idan baka manta ba ai dama na gaya maka cewa ina tsoran ranar da zan iya cin amanarka, sabo da na san halinmu na aljanu bamu da amana. Da wannan furci nake maka bankwana. Ina fatan zaka yafe min baza ka mutu da kullatata ba?". Koda gama fadin hakan sai Saif ya ce, "ina damarata ta yaki?" Hurbas ya ce, "ai wannan damara ta zama tawa har abada. Gata nan a jikina, da iata zanci gaba da yakar musulmin duniya har sai na karar da su. In kuma ajali ya riskeni kafin na cika burina tabbas dana ne zai gaji wannan damara". Koda Hurbas ya gama wannan jawabi sai ya 6ace 6at! Shi kuwa Saif sai hawaye ya zubo masa ya ce, "tabbas babu amana ga mara amana Allah ka sa amana ta ci abokina kamar yadda ya cita. Gama fadin haka ke da wuya sai Saif ya yi kalmar shahada ya rasu. Duk wannan abu da ya faru a wannan tsakar dare tsakanin Saif da Hurbas babu wanda ya gani ko ya ji sai da gari ya waye sai matar Saif da dansa suka shiga turakarsa suka iske gawarsa. ----<<<<>>>>---- Al'amarin Hurbas kuwa, a wannan dare sai ya koma gurin Harfiza suka ci gaba da sheke ayarsu. Hurbas ya zauna da Harfiza har tsawan shekara goma, sa'adda ta haifi da aka sa masa Shamzabul Azwas. Ranar da aka haifi wannan yaro ne Harfiza ta kashe Hurbas ya yin da suke ta nishadi da murnar wannan haihuwa. Wato sai ta shammace shi ta burma masa wata wuka ta sihiri a cikinsa. Dama a lokacin ya cire damarar nan ta yaki daga kugunsa ya ajiye ta gefe guda. Nan take Hurbas ya sulale kasa yana kakarin mutuwa. Cikin tsananin dauriya ya dago kai ya dubi Harfiza ya ce, "ya ke masoyiyata sabo da me za ki kasheni?" Koda jin wannan tambaya sai Harfiza ta bushe da dariya ta ce, "ai baka da sauran amfani a wajena tunda ka biya min bukatata. Akan wana dalili zan ci gaba da zama dakai na baka amanata alhalin na san cewa mu alajanu bamu da amana? Shin ka manta cewa mahaifiyarka ta ci amanar mahaifinka, ta kashe hsi, kai kuma ka ci amanar abokinka ka kashe shi, nima tabbas nan gaba zaka iya cin tawa amanar shi yasa na yanke hukuncin na kawar da kai kafin ka kawar da ni. Ni kam a yanzu na ci riba biyu, domin ka biya mini bukatata, kuma ga shi na sami gadon wannan damara ta yaki wacce dana zai gada." Koda Harfiza tazo nan a zancenta sai nimfashin Hurbas ya fara sarkewa. Cikin karfin hali ya dubeta ya ce, "tabbas amana bata barin amana. Kema ki kiyayi bibiyar tawa amanar." Yana gama fadin haka sai komai na jikinsa ya sandare ya daina motsi, wato ya zamo gawa. Daga wannan rana Harfiza ta ci gaba da rainon danta har ya fara girma, tama koyar dashi ilimin tsafi har ya iya duk irin saihirin da Shahauz zaman ya iya. Shamzabul Azwas ya taso sadauki, kuma azzalumi mara imani. Nan da nan ya shahara a tsafi, har ma yaso yafi uwarsa Harfiza sanin ilimin tsafi. Tun bayan mutuwar Hurbas sai Harfiza ta 6oye wannan damara ta yaki, kuma bata ta6a bawa Shamzabul Azwas labarin mahaifinsa ba da yadda ya mutu. Wata rana sai Shamzabul Azwas ya shiga binciken tarihin rayuwar mahaifinsa a cikin madubin tsafi. Ai kuwa take yaga duk irin aminantakar da ta kullu a tskaninsa da Saif tun daga farkon haduwarsu har izuwa lokacin da suka yi yaki da Boka Shaharuz zaman da kuma sa'adda da Hurbas ya ci amanar Saif ya rabashi da damararsa ta yaki yaje ya yi zina da Harfiza, sannan ya koma ya kashe Saif. Shamzabul Azwas yaga yadda akai Harfiza ta sami cikinsa har ta haifeshi, da kuma sa'adda ta kashe ubansa Hurbas a daran da aka haifeshi. Koda gama ganin wannan al'amari sai Shamzabul Azwas ya fashe da matsanaicin kuka ya ce, " hakika mahaifiyata ta ci amanata da ta 6oye mini wannan labari, dole ne itama tabi bayan mahaifina". Nan take Shamzabul Azwas ya mike tsaye ya fita daga cikin dakinsa na tsafi ya wuce izuwa dakin mahaifiyarsa Harfiza, inda ya isaketa zaune a kan gado tana kwalliya. Cikin fara'a ya matsa gareta kamar zai rungumeta kawai sai ya caka mata wukar sihiri a ciki. Wannan wuka itace wadda ta kashe mahaifinsa da ita. Cikin kalarin rai ta dubeshi ta ce, "me yasa ka kasheni ya kai dana?" Shamzabul Azwas ya ce, "sabo da kinci amanata, kuma kinci amanar ubana. Lallai amana bata barin amana. Me yasa baki bani labarin ubana ba? Me yasa baki ta6a yin mini batun damararsa ta yaki ba? To ki sani cewa bayan kin mutu zandauko wannan damara a duk inda kika 6oyeta in ci gaba da amfani da ita ina ruguza musulimci da musulmai. Lallai sai na ciki burin Baka Shaharuz zaman domin shi ya kamata ya zamo ubana na kwarai ba Hurbas ba maci amana". Lokacin da Shamzabul Azwas ya zo nan a cikin labarinsa, sai yai shiru ga barin zancen. A lokacin ne ya ga Humaira ta kura masa idanu tana zabga masa harara. Shi kuwa sarki Sahibul Hairi, sabo da tsananin mamakin labarin sai yai shiru yana juya al'amarin a ransa. Shamzabul Azwas ya bushe da dariya ya ce, "ya ke Humairat yanzu kin fahimci cewa ubana ne ya yaudari kakanki ya ci amanarsa har yaga karshensa? To ku sani cewa nima sai naga karshan dukkanin ma'abota addinin musulinci. Kin rigaya kinji nasabata da wannan damara wacca aslinta ta kakanki ce. Idan har zaki iya sai ki kar6i abarki yanzu, idan ba za ki iya ba kuwa shi ke nan. Ina tabbatar miki da ke da Sarki Sahibul Hairi ba za ku ta6a cika burinku ba. Kuna ba za ku ta6a fita daga cikin wannan fada tawa ba a raye. Nikam baku isa ku kasheni ba muddin ina da wannan damarar yaki. Ku sani cewa babu wani sirrin tsafi da bam malka baface na jikin yarinya Alfila, kuma yau saura kwana arba'in nagama dibar sirrin tsafin jikin na ta, don haka baku isa ku tsayar da wannan aiki ba. Koda gama wannan jawabi sai Humairat ta dakawa Shamzabul Azwas tsawa ta ce, "kai tsohon kafuri karyarka ta sha karya. Ka sani cewa babu mai kashewa da rayawa face Ubangijin Musulinci, don haka kai baka isa ka kashe mu ba face kwanan mu ya kare. Ka sani cewa duk abubuwan da kake dogaro da su da izinin Allah suke tasiri, idan babu izini ba za su yi tasiri ba. tabbas faduwar gaba asarar namiji ce, don haka ko kadan bana tsoranka, kuma bana shakkarka. Zan fafata da kai da zuciya daya, idan ka kasheni zanyi shahada, idan na kasheka na rage mugun iri doron kasa, kuma na karawa Musulinci karfi a wannan nahiya tamu." Koda jin wannan batu sai aljani Shamzabul Azwas ya kyalkyale da mahaukaciyar dariya. Sannan ya ce, "ka yarinya tsaya kiji, yadda kikayi imana da Ubangijin Musulinci haka mu ma muka yi imani da shi. Amma fa ba zamu fasa tsafi ba, kuma baza mu fasa morewa rayuwar Duniya ba. Yadda zaki roki Ubangiji Musulinci bukata ya biya miki ita, haka muma zamu rokeshi ya biya mama." tabbas mun san gaskiya amma mun take tane dan kwadayin duniya". Kafin Humairai ta sake bu6e baki ta kara cewa wani abu tuni Shamzabul Azwas ya daka tsalle ya dire a tsakiyarsu ita da Sarki Sahibul Hairi. Nan fa ya fara kaimusu sara da sukacikin tsananin zafin nama irin wanda basu ta6a gani ba. Sabo da karfin saran sai ya zana cewa da kyar suke iya karewa, ko martani basa iya maidawa. Tabbas jarumtakar Shanzabul Azwas ta ninka ta Humairat da Sarki Sahibul Hairi. Bambamcin a bayyane yake. Nan fa ya kuntata su ya hana su sakat har takai cewza ya kadar da makamansu daga hannunsu. Koda yaga babi makamai a hannunsu sai shima ya yarda takobinsa da garkuwarsa. Nan fa ya fara naushinsu yana bugunsu hannu da kafa. Abin ka da naushi irin na aljanu, nan da nan ya lugwe-gwetasu, in ba dan karfin addu'a ba da ma basu isa su tareshi ba, inda matsalar take shi ne, kamar yadda suke addu'a shima haka yake yinta. Hakika Allah ya kasance mai hakuri da bayinsa, shi yasa duk shegantakar da bawa zai yi sai ya ara masa rana ya yi ta yi. Amma idan yaso sai ya kama shi a rana daya ya raina kansa kamar yadda ya yiwa sarki Fir'auna sarkin Misra. A halin yanzu Allah ya arawa Shamzabul Azwas lokaci, shi yasa yake kan sharafinsa, duk abinda yasa gabansa sai ya sami nasara. Lokacin da Shamzabul Azwas ya ci gaba da dukan su Sarki Sahibul Hairi da Humairat, sai ya sumar da su suka zube kasa wanwar babu mai nunfashin kirki a cikinsu. Koda yaga ya sami wannan nasara sai ya kyalkayala dariya mugunta, nan take ya yi tsafi, sai jikin Sarki Sahibul Hairi da jaruma Humairat ya sandare, suka zamo gumaka. Fatuwar hakan ke da wuya sai ya juya da baya ya shiga wani daki na musamman inda yake tafi da harkokin na tsafi. Burinsa shine ya kammala wannan tsafi na cire sirrikan tsafi da ke jikin yarinya Alfila ya mai da su cikin jikinsa. Kash! Duk wannan nasara da aljani Shamzabul Azwas ya samu akan su Sarki Sahibul Hairi ya yi tuya ya manta da albasa. Dalili kuwa shi ne, Allah ya mantar da shi batun Bawa Haluf wanda tun a farkon shigowarsu gadan ya fadi sumamme. A she wannan gumurzu da akayi tsakanin aljani Shamzabul Azwas da su Sarki Sahibul Hairi Bawa Haluf na la6e a wani sako yana kallo jikinsa na makyarkyata sabo da tsananin razana. Bayan Shamzabul Azwas ya tsafance su Humairat sun zama gumaka kuma ya shiga cikin dakin tsafinsa sai Bawa Haluf ya shiga tunanin hanyar da zai ceci su Sarki Sahibul Hairi, amma sai ya kasa yanke hulunci bisa abin da ya kamata ya yi ya sake fadawa kogon tunani. Wannan shi ne abin da ya faru da su Sarki Sahibul Haira ya yin da suka sami damar shiga Fadar Aljni Shamzabul Azwas dan Dauko Yarinya Alfila. . A CAN BIRNIN MISRA KUWA, BAYAN SU WAZIRI AKIYANU SUN DAWO DAGA WAJAN Boka Shiburul Uzab sai suka sake yin zama na musamman a cukin sirri domin su tattauna akan yadda za su sami nasarar sato wannan Doki na Aminul Has ba tare da sirrinsu ya tonu ba. Sao da suka shafe sa'a biyar suna mahawara sannan daga karshe suka tsaya akan shawara guda. Shawarar kuwa ita ce za'a sato Dokin ne da duku-dukun safiya sa'adda mai kula da bargar Dawakan ke baiwa Dawakan Abinci. A ka'ida kullum kafin a baiwa Dawakan Abinci sai an fita da su daga cikin birgarsu an sakesu su dan yawata a harabar sai a mai da su cikin bargar sannan sai a zuba musu Abincinsu. Dabarar da aka shirya shi ne, a kwai wani babban hadimin gidan sarautar wanda babu inda baya shiga a gidan, ana kiransa da suna kumais. Tuni su Waziri sun baiwa Kumai Dukiya mai yawa sun gaya masa bukatarsu cewa suna so a sato wannan Doki na sarki Aminul Has. Koda Kumais yaga an bashi dukiya irin wadda bai ta6a mallaka ba a rayuwarsa, sai ya amince zai sato Dokin. Nan take yasa aka nemo wani dokin daban, wanda kamarsa daya da Dokin sarki. Hatta tswansu, kibarsu da launin jikinsu dyk iri daya ne sak babu banbanci kai kace tagwaye ne. Da sassafe sai ya ja wannan Doki na karya ya shiga dashi cikin gidan sarautar ya nufi bargar Dawakan sarki kai tsaye. A wannan lokaci mai kula da bargar ma bai iso bargar ba dan yin aikin sa na kullum da ya saba. Da yake mutane basa gilmawa a wajan sai kawai ya yi sauri ya shiga bargar dawakan da wannan Doki na karya, sannan ya kamo na gaskiya ya fito da shi. Bisa mamaki sai yaga Dokin bai yi masa gardama ba ko sau daya har ya fita dashi daga cikin gidan sarautar gaba daya. Koda kumais yaga ya smi wannan nasara sai ya cika da tsananin farin ciki, domin ya san cewa indai ya kai dokin nan ga su Waziri Akiyanu za su bashi kada ninkin baninkin abin da suka bashi a baya. Kumais na cikin jan dokin sai yaji dokin ya cije, kumais ya yi iya yinsa dan yaja dokin gaba su ci gaba da tafiya, amma sai yaji ya kasa. Kawai sai ya jiyo a fusace domin ya tursasa dokin. Waigowar da zai yi sai yaga linzamin a jikin wani mumunan gutun aljani mai ban tsoro, bao san sa'adda ya saki futsari a wando ba jikinsa na karkarwa. Aljanin sai ya daka masa tsawa ya ce, "maza kaje ka gayawa wadanda suka turoka satar dokin sarki ka gaya mu su cewa wannan dokin ba zai satu ba. Koda duk duniya zata taru akan yin hakan. Koda gama wannan jawabi sai aljanin ya 6ace 6at! Ya bar kumais tsaye rike da linzamin duki a hannu babu doki. Nan take kumais ya sulale kasa sumamme. Sai da kumais ya kusan shafe rabin sa'a a kwance cikin halin suman sannan ya farfado. Koda ya bude idanu ya dubi gabas da yamma, kudu da arewa yaga babu wannan guntun aljani sai ya mike zumbur ya furgice ya cika wandansa da iska. Bai zami a ko ina ba sai a gaban Waziri Akiyanu. Da zuwa ya wuce kai tsaye zuwa cikin turakar Waziri yana tafiya buguzum-buguzum. Kai da ganinsa kasan a cikin mumunan tashin hankali yake. Yana shiga cikin turakar ya iske Waziri Akiyanu a zaune cikin nishadi suna walimar farin ciki bisa samun tabbacin lallai yau ne za'a kawo musu wannan doki na sarki wanda za su kaiwa boka domin su sami damar kawar da Aminul Has daga kan karagar mulki. Koda ganin kumais sai Waziri Akiyanu da sauran jama'ar tasa suka mike zumbur a firgice. Waziri Akiyanu ya tareshi da sauri ya zaunar da shi gefe daya sannan ya tambayeshi abinda ya faru Nan take kumais ya kwashi labarin duk abin da ya faru gareshi tun daga lokacin da ya sami nasarar dakko dakin sarji daga cikin burgar har izuwz bayan gari sa'adda yaji dokin yaki jawuwa a hannunsa yana waigawa sai ya yi arba da wannan guntun aljani. Koda gama wannan jawabi sai hankalin Waziri Akiyanu ya dugunzuma, haka ma na sauran jama'ar tasa, suka rasa abin da yake musu dadi. Al'amarin da ya janyo fadar tayi tsit kenan kamar mutuwa ta gifta. Waziri Akiyanu ya kama kai komo a cikin fadar yana tinani mai zurfi. daga can sai ya tsaya cak ya dubi jama'ar tasa daya bayan daya ya ce, "ya ku abokanan kuka ku yi sani cewa masu iya magana sun ce ta inda aka hau tanan ake sauka. Ni ina ganin cewa tunda al'amarin nan yafi karfin tunaninmu babu abin da ya kamata muyi face mu koma gurin wanda ya umarcemu da dauko wannan doki, shi ka dai ne zai iya yi mana maganin wannan aljani da ya hana a dauko dokin."koda jin wannan batu sai gaba daya 'yan majalisar suka ce,"tabbas kayi tunani mai kyau, lallai hakan za'a yi, kuma ai da zafi-zafi akan daki karfe ba sai ya huce ba". Koda fadin haka sai 'yan majalisar suka amnice da haka. Ba tare da 6ata lokaci ba Waziri Akiyanu da tsoho Kilzim suka yi shiri suka tafi zuwa gidan abin dogaronsu. Da yake akwai tazara mao tsaho a cikin tafiyar tasu sai hira ta 6arke a tsakanin Waziri Akiyanu da tsoho Kilzim. Inda Kilzim ya dubi Waziri ya ce, "ya kai Waziri yanzu idan ka sami sarkin Misra wana buri ne da kai na farko wanda zaka fara kawar da shi? Ya yin da Waziri yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariyar farin ciji, sannan ya ce, "ya kai Kilzim kayi sani cewa ina da wasu burika uku wadanda suka dade suna yi mini yawo a cikin zuciyata. Burina na farko shi ne, ina so na sauya gaba dayan rayuwar mutanan birnin Misra, ya zamana cewa in ba attahirai ba ko mai mulki babu mai samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Abu na biyu, ina so na tsauwala haraji ga kowa domin na tara dukiya mai dimbin yawan gaske a cikin kankanin lokaci, domin sauran sarakunan da ke mulki a sauran kasashe su jani a jiki su dinga harka tare da ni, sa6anin yadda suke kyamatar sarkinmu a yanzu. Abu na uku shi ne, ina so na shirya gagarumin yaki wanda zan murkushe manyan kasashe da ke wannan nahiya tamu su dawo karkashin mulkina sabo da na tara karfin tattalin arzikin kasar tawa. A sannan ne zamu zauna cikin jin dadi, arziki da kwanciyar hankali". Sa'adda Waziri Akiyanu ya zo nan a zancensa sai tsoho Kilzim ya rage gudun dokinsa ya sassaita tafiyar tazo dai- dai da dokin Waziri Akiyanu, sannan ya ce, " ya shugabana yanzu naji naka burin. Mukuma da muke makusantanka a wane matsayi zaka ajiyemu?". Waziri ya yi murmushi, sannan ya dubi Kilzum ya ce, "ka ga kai yanzu shekarunka sun haura casa'in a duniya, na tabbatar da cewa dukiya da kyakkyawar mace basu dame ka ba, domin babu irin arzikin da baka gani ba, haka ma matan, komai kyan mace babu irin macen da baka gani ba. Bukatarka kawai ita ce ko baka nan kada bayanka ta tozarta. Nayi maka alkawari muddin ina numfashi a doran kasa iyalinka ba za su walakanta ba. Kuma dulk abinda suka bukata nayi alkawarin zan basu har izuwa karshen rayuwata". Lokacin da Waziri Akiyanu ya zo nan a zancensa sai ya ga hawaye ya zubo daga idanun tsoho Kilzim. Al'amarin da ya mutukar bashi mamaki ke nan. Ya dubeshi ya ce, " ya kai Kilzim, kai kuwa menene dalilin zubar da hawayanka?" Tsoho Kilzim yasa hannu ya share hawaye, sannan ya yi ajiyar zuciya ya ce, " ya kai Waziri Akiyanu, kayi sani cewa ba komai ne ya sani zubar da hawaye ba face tunowa da yadda mutuwa take yanke jin dadin rayuwar duniya. Tabbas insa ace akwai maganin mutuwa da komai tsadarsa, ko kuma wahalar nemansa ba zan karaya ba akan nemansa. Gaba daya matsafan duniya sun yi iyakar kokarinsu akan samar da maganin mutuwa da na tsufa amma abu ya gagara tunda daga farkon duniya kawo yanzu. Ni dai yanzu kaga tun ina saurayi nake da burin shiga cikin majalisar kasar nan, amma ban sami wannan dama ba sai da girma ya fara kamani bayan mutuwar ubana. Yanzu gashi dama zata samu wacce mulki gaba daya zai dawo karkashin sarrafawarmu, amma sai yazu mini a lokacin da tsufa ya riskeni. Ba lallai ne ma naji dadin mulki tun da a ko yaushe zan iya barin duniyar duk da cewa ina cikin koshin lafiya". Ya yin da tsoho Kilzim ya zo nan a zancensa sai Waziri Akiyanu ya bushe da dariya, sannan ya ce, "ai shi jin dadi ko nace arziki ko na kwana daya ne yafi talauci na shekara dubu. Ka sani cewa idan muka sami nasara akan abin da muka sa a gabanmu har a bada bayanka bazata wulakanta ba, ka ga ashe ko mutuwa kayi ka san cewa baka tafi ka barsu a cikin takura ba da halin kaka na kayi." tsoho Kilzom yai ajiyar zuciya ya ce, "ai wani baya yiwa wani maganin yunwa, domin ita rayuwa ba ta da tabbas domin komai na iya sauyawa a ko yaushe. Idan kayi tunani za kaga cewa shi dan adam baya daina buri har sai ya bar duniya. Shin ka ta6a zaton cewa sarki zai tunanin barin kasar nan ya tafi neman arziki? To kaima nan gaba ba mamaki ka tafi neman wani abun daban wan da yafi wan da sarki ya tafi nema wahalar samu. Ka tuna cewa sau da yawa sarki yana zama bawa, bawa kuma ya zama sarki". Koda jin wannan batu sai Waziri Akiyanu ya fusata ya dakawatsoho Kilzim tsawa ya ce, "kada ka saki yin furci irin wannan a gareni, domin ni tunda na taso a rayuwata duk abin da nasa a gaba sai na sami nasara, ban ta6a samun mushkila ba. Indai na zama sarki sai dai na mutu akan karaga ba dai wani mahaluki ya iya sauke ni ba. In dai akwai dukiya, kuma akwai boka babu abin da ba zai yiwu ba a wannan zamani". Tsoho Kilzim ya jinjina kai ya ce, "ya kai Waziri kayi sani cewa kamar yadda ka taso da samun sa'a bisa duk abin da kasa a gabanka haka sarki Sahibul Hairi ma ya kasance. Shin baka tsoran cewa zai iya samun nasara a bisa abinda ya tafi nema ya dawo gida cikin koshin lafiya. Idan kuwa ya dawo ya iske kaine akan karagar mulkinsa taka ta kare." Koda jin haka sai Waziri Akiyanu ya bushe da dariya, sannan ya ce, "kai a zatonka zan zauna akan karagar sarki Sahibul Hairi haka kawai ne? Ai duk abin da zanyi sai na yishi don na tabbatar da cewa sarki Sahibul Hairi bai dawo ba, in kuwa ya dawo sai dai gawarsa ta dawo. Yanzu dai babban abu mai muhimmanci shi ne, mu fara samun nasarar kawar da Aminul Has akan karagar mulki". Tsoho kilzim ya yi murmushi ya ce, "nikam na tabbatar da cewa zamu sami nasarar kawar da Aminul Has ta kowana hali. Yanzu idan bulata ta biya ni wana matsayi zaka bani a fada?" Waziri Akiyanu yai dariya ya ce, "abin da kake so shi zan baka". Koda jin haka sai shima kilzim yai murmushi ya ce, "tabbas babu wanda ya san abin da nake so sama da kai, kuma nayi imanai da cewa kai mutunne mai cika alkawari. Lallai idan ka zamo sarki zan zamo Waziri. Amma kai me yasa ka za6i na zama Wazirinka?" Waziri Akiyanu ya ce, "ai mulki ga shekarun da basu haura arba'in ba basa tafiya dai-dai sai da jagorancin manya masu tunani da hangen nesa. Ni nafi kowa sanin muhimmancinka a cikin majalisata. Ko ba komai ka ga jiya kuma ka ga yau, sannan kuma babu wanda ya san sirrin gidan sarautar birnin nan sama da kai". Koda jin wannan batu sai tsho kilzim ya yi dariyar farin ciki ya ce, "hakika duk abin da ka fada gaskiya ne, kuma ba karamar dabara kayi ba da ka za6eni a matsayin Wazirika, domin na san wadansu abubuwa ma wadanda baka ta6a tsammanin na sansu ba. Domin akwai wani sirri guda daya na sarki Sahibul Hairi wanda duk duniya babu wanda ya san shi face ni......... . Hmm AA Misau Ke Magana . SHIN BURIN WAZIRI AKIYANU YANA CIKA KUWA NA GANIN YA KAWAR DA AMINUL HAS DAGA KAN KARAGAR MULKIN BIRNIN MISRA YA HAU?. . SHIN BAWA HALUF ZAI IYA CETON SU SARKI SAHIBUL HAIRI A FADAR ALJANI SHAMZABUL AZWAS WADANDA YA MAYAR DA SU GUMAKA? INA LABARIN SARKI BARUSA? . WANA IRIN SHIRI GIMBIYA SHUKURA ZA TA YI? YAUSHI SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SADU DA SADAUKI AWAISU HAR YA CIKA BURINSA? . Mu hadu a littafin SARKIN SARAKAI na hudu (4) dan jin cigaban wannan kayataccen labarin. SARKIN SARAKAI Littafina Uku 3 complet Na Abdulaziz Sani madakin gini Typing by Al'amin Ahmed misau Post And Ebook creator by Shuraih Usman 99% You can download more Hausaebooks at http://shuraih.waphall.com Date of ebook created: 8/6/2018 Time of ebook created: 8:15 AM Sarkin sarakai Littafi na Hudu 4 Na Abdulaziz Sani m Gini Typing:- Alamin Ahmed Misau Ebook creator:- Shuraih 99% . You can download more Adventure hausaebooks at http://shuraih.waphall.com Domin downloading na wasu littatafanmu amatsayin eboook sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan adireshi www.shuraih.waphall.com SARKIN SARAKAI Littafi Na Huɗu (4) Part A. . Marubucin Littafin Abdul Aziz sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa NAN TAKE BAWA HALUF YA GOYATA A BAYANSA SUKA TAFI INDA AKA KAMAR DA su Sarki Sahibul Hairi. Kafin su karasa gurin sai suka ga wani kare wanda shi ma aka kamar da shi kamar yadda aka kamar da su Sarki Sahibul Hairi. Bawa Haluf ya tsaya a dai-dai kan karen sannan ya sauke Alfila daga bayansa ya fito da wannan kana nan kwalabe masu ruwan sihiri a aljihunsa. Kawai sai ya bude guda ya yunkura zai kwara akan wannan kare. Cikin sauri Alfila ta ruke Hannunsa ta ce da shi a cikin rada. "me kake shirin yi ne?" Haluf ya ce, "so nake na jarraba wannan ruwan sihirin akan wannan karen ko ruhinsa zai dawo domin nayi amfani da shi wajan tashin 'yan uwana da Boka Shamzabul zwas ya mai da su gumaka." Koda jin wannan batu sai Alfila tayi murmushi ta ce, "Ai inda ka zuba wannan shidin ruwa akan wannan karen da nan take zai rugurguje ya zama gari." Cikin mamaki Haluf ya dubeta ya ce, "ya ya akayi ki ka san wannan?". Alfila tayi murmushi ta ce, "Ai mahaifina yana da duk irin wadannan ruwan sihirin guda dari ba daya ne kuma ko wanne na san amfaninsa". Koda jin haka sai murna ta kama Bawa Haluf ya ce, "To yanzu wanne ne zan zubawa 'yan uwana ruhinsu ya dawo?". Alfila ta ce, "ba zan gaya maka ba face kayi mini alkawari guda." Haluf ya ce, "fadi duk irin abinda ki ke son nayi miki, lallai zan zama mai ciki alkawari a gareki". Alfila ta ce, "ina son ka yi mini alkawari cewa zaka mayar da ni kasarmu wajen mahaifina, domin na tabbatar da cewa a halin yanzu yana can cikin tsananin damuwa da taahin hankali bisa rashin ganina. Tabbas inda yana da ikon zuwa nan ya kar6eni da tuni ya zo." Bawa Haluf ya ce, "kwantar

Chapter 11 of 19