Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ce, "ya ke wannan kuyanga mai zai hana ki zauna ki bamu wannan labari yadda akayi har matar Baruzul Damsus ta yaudareshi ta sace rabin dukiyarsa alhalin yana kan matsayin sarkin 6arayi na duniya mai karfin sihirin tsafi?" Kuyangar ta sake murmushi a karo na biyu ta ce, "hakika kuna wasa da kaidi irin namu na mata, domin inda ka ji kaidin da matar Baruzul Damsus ta kulla ta sami nasarar sace dukiyar kuma ta tsira da ita da kun sallamawa mata. Ku yi sani cewa dokace babba akan duk hadiman gidan nan na baku wannan labari, domin labarin ya kunshi sirrin Baruzul Damsus. Wata kila nan gana bayan bukatarku ta biya shi da kansa ya iya baku labarin da bakinsa. Da wannan furuci nake yi muku sallama, ku huta lafiya". Koda fadin haka sai kuyangar ta juya ta fita daga cikin dakin, ta janyo musu kofa ta rufe. Nan da nan kuwannansu ya hau kan gado guda suka bararraje suna more lahinsa da ni'imarsa domin su yi barci. Amma sai barcin ya gagara, domin hirace ta sarke a tsakaninsu. Da farko dai Waziri ne ya dubesu ya ce, "hakoka duniyar nan da fadi take, kuma abin cikinta yawa gareshi. Ni kam na fuskanci cewa in dai da rai da nuntashi to har abada buri ba zai yi karshe ba. Ku tsaya kuyi tunanin irin dukiyar da wannan 6arawo ya tara ku dubi irin daular da yake ciki, amma duk basu ishe shi ba yana hankoran ya sami wata. Wai shin me zai yi da dukiya ne? Gashi dai bashi da mata a yanzu, kuma bashi da 'ya'ya, shin baya tunanin cewa komai dadewa sai mutuwa ta riskeshi. A yau idan ya fadi ya mutu waye zai gaji gidan da dukiyar da ke cikinsa?". Sa'adda Waziri ya zo nan a zancensa sai ya ran nasa biyu guda biya sai suka yi ajiyar zuciya. Daya daga ciki mai suna shumar ya ce, "ya shugabana ai baka san sirrin da ke zuciyarsa ba, sabo da haka bai kamata kayi mana wannan tambaya ba. Tabbas akwai wani abun da yake shiryawa rayuwarsa da dukiyarsa. Itkanta wannan rabin dukiya ta birninmu da yake son ya mallaka akwai wani burin da yake son ya cika da ita. Ni dai kawai abinda ya daure min i kai da al'amarinsa shi ne batun matarsa wadda ta shammaceshi ta gudu da rabin dukiyarsa". Koda jin wannan batu sai Waziri ya yi murmushi ya ce, "ai inda ka san matsayin kaidin mata a duniya da baka fadi haka ba. Ina tabbatr maka da cewa duk wani tashin hankali da ke faruwa a duniya babu mai haddasa shi face mata. Idan mata suka so za ai zaman lafiya, idan kuma basu so ba sai dai ayi ta tashin hankali. Shin ka ta6a jin labarin sarkin Rum shi ne mutumin da yake kaunar 'yarsa fiye da kansa, wanda a sabo da haka ya shiga duniya neman wadansu gagaruman abubuwa don ta daukaka a duniya, ya yin da matansa suka dauki aniyar ruguza wannan shiri nasa tare da kawar da yarinyar daga doron kasa?". Waziri ya ce, "ai kuwa ban ta6a jin wannan labarin ba, kuma zan so in ji shi". Sumar yai murmushi ya ce, "ai kuwa labarin yana rubuce a cikin wani littafi wai shi DAKAKKIYAR ZUCIYA amma zan datsi labarin ne na ci maka gaba soda yawansa. "Sarkin Rum ya co gaba da keta gudu a cikin daji tamkar bazai tsaya ba har duhun dare ya fara shigowa. Bisa sole ya ja linzamin dokinsa ya tsaya, ba don ya gajo ba, kuma ba don ya so ba face sai domin dokinsa ya dan huta ya yi kiwo, shima ya ci daga guzurinsa, ya sha ruwa, ya dan kishingida yana hutawa. Bayan kimanin sa'a data ya tashi ya ci gaba da tafiya. Bayan ya shafe tsawon sati guda yana tafiya a cikin mugwayan dazuzzukan da ke nahiyar ba tare da ya sake haduwa da wani mugun abu ba tun daga muyagun arnan dajin nan masu karfin sihiri da suka kwabza azababban yaki da su, face namun daji wadanda ko damuwa da su baiyi ba, domin ya raina jarumtakarsu. Amma a zuciyarsa yana fata ya sake haduwa da wani mugun abun wanda yafi arnan dajin, domin shi yana ganin a haka zai ci gaba da baiwa kansa horon yaki da miyagun abubuwan da suke cikin wadannan dazuzzuka. Yana tsaka da tafiya sai ya zo bakin wata sahara mai tsananin zafi da nisan tsiya, ko ina ka kai dubawarka saharace, ba za ka ta6a hango karshenta ba. Kuma sau tari zazzafar iska kan buso daga cikin saharar ta yanyame sagarar sai ka daina ganin komai, wanda ko wacce halitta indai tana wajen. Sa'adda ya zo dai-dai bakin saharar ne, ba tare da wata shawara ba, ko kuma tunanin abin da zai biyo baya ba, ya banna kansa kawai cikin saharar ya fara tafiya tinkis-tinkis bisa dokinsa yana kallon gefe da gefensa. Bai yi nisa da fara tafiya ba wata kishirwa mai tsanani ta soma addabassa, dan haka ya dakko silkassa ta ruwa ya kafa a bakinsa ya shanye ruwan cikinta. Koda ya sake ci gaba da tafiya sai ya sake jin wata kishirwar wadda ta fi ta farko a karo na biyu. Ya sake dakko silkar ruwan nasa ya sha ruwa. A takaice dai bai yi nisa da tafiya a cikin saharar ba ya shanye gaba daya ruwan guzurinsa. Haka ma dokinsa ya gaza tafiya a cikin saharar. A fusace ya tsaya cak, ya dire daga kan dokin, kafarsa ta nutse a cikin saharar, wata kura ta tashi. A dai-dai lokacin ya ji wata kakkarfar iska a saman kansa. A nutse ya daga kansa ba tare da fargaba ba. Wani jibgegen mummunan aljani ya gani mai suffar mikiya ya yi masa rumfa. Fuskar aljanin irin ta biri ce, wadda take dauke da wani ta6a66an hanci, tare da katon baki masu dauke da manya-manyan hakora kamar kashin guiwa. Haka idanunsa jajawur kamar wuta ce ke ruri a cikinsu. Haka kuma fuskar duk a dabai baye take da wani bakin gashi. Kan aljanin dan karami ne kamar na karamin biri, sai dai akwau wadansu kahuhhuna guda hudu a jere akai. Yana da manya-manyan fuka-fukai guda takwas. Aljanin ya tsuke fuka-fukansa ya dire kasa. Wani tsamurraran dattijo wanda a kalla ya yi rubda ciki akan shekaru dari biyu da 'yan kai ya sauko daga kan tsauntsun tamkar ya sauka daga kan doki, yana fadada mummunar fuskarsa da wani kodaddan murmushi wanda shi a ganinsa shi ne murmushin kure adaka, murmushin da ba kowa zai iya yiwa irinsa ba. Abin da bai sani ba da ya yi irin wannan murmushin gwara ya fashe da kuka, domin da kuka da murmushin basu da maraba, musamman ganin yadda fatar kumatunsa ta tatta6e tamkar ana nannade Tabarmar karauni. Jarumin sarkin baiyi wani yunkurin komai ba balle ta kai da ya yi shirin ko ta kwana, ya dai kurawa halattar tsamurarran tsohon yana dubansa, yana jiran ya karaso gareshi dan jin da wacce ya zo. Ya yin da tsohon ya kusanto gareshi, sai ya ce da shi da muryarsa da take satar kwaikwayo da kukan dan marakin saniya. " An gai da mai shirin zama gwarzo. Na zo na taimaka maka a wajen cimma burin rayuwar ka." "bana bukatar temakonka. ! Ka yi gaggawar 6ace mini da gano!!" ya yi mai tsawa a fusace yana da karkarfar murya yana nunashi da dan yatsa. "Ba a sannu dan samari. Ba'a yi min tsawa kuma ba'a nunani da hannu. Idan na fadi magana ta zauna, dole a amince da ita. Kuma kaima dole ka kar6i taimakona." Tsohon ya ce dashi da karkarfar murya. "karyarka tasha karya gafalallan banza! Baka isa ba, ba ka kai matsayin da zaka tai maka min bz. Kai! Ba ai wani da namiji ba, akan burin rayuwata. Zan iya sada zai iya sada kuntuwar rayuwarka da ajalinta mutukar baka 6ace mini da gano ba." A fusace yake gaya masa maganar cikin kunfar baki. Ya tuntsure da wata karkarfar tsawa. "Lallai yaro baia san wuta ba sai ya taka! Na san baka san koni waye ba shi yasa kake gaya min gafalallun maganganunka kai tsaye ba tare da fargaba ko sha yi ba. Dan haka zan yi maka afuwa, na san kayi ne bisa kuskure." "Bana bukatar a tarihina ace wani ya yi min afuwa bisa wani kuskure da na yi masa, zan bukaci ya dauki fansa mutukar zai iya. Ka sani cewa na girmi in yaki karkarfan sadauki shi kadai, balle gafalallan tsoho da jikinsa ya gama kasalantuwa, babu kuzari da karfin jiki a tare da shi. Sadaukantakata ta girmi in kai hannu jikinka da nufin yaki. Dan haka kaje ga wani sarki ka nemi alfarmagareshi ya ara maka gayyar rundunonin yaki a kalla mutum sama da dubu daya ku taho gareni tare da gyara a kai, anan ne na san zan iya sauraronka da nufin yaki. Yana gama maganganunsa ya haye dokinsa, ya yi gaba ba tare da ya dubi tsohon ba. Taku daya, biyu uku, ya yi ya ga tsohon a gabansa yana masa murmushin mugunta ya ce, "Dan samari na girmi tunaninkagigin yarinta ya daina dibanka ga furta gafalallun furci ga maigidanka. Koda ka ganni tsoho ka yi tunani ka fini tsagwaran sadaukantaka ko jarumtaka. Ka daina tunanin kana karar da adadin ragwaye har kana tutiya da alfahariba maza a gabanka, ba za ka yaki mutun daya ba sai mutun dubu. Da sannu zan nuna maka yadda tsoho yake dakawa karamin sadauki gumba a hannu, ya sanya shi yin dana sanin zuwa duniya, ya sanya shi yin ihun azaba. Ko kallonsa bai yi ba, ya kada kan dokinsa ya ratse shi zai wuce. Ya ce da shi, "Ba zan yarda da ka cika kai cikakaen ne ba sai kazo da adadin runduna da na gaya maka, su doraka a matsayin gyara, in ya so a nan sai ka nina min ko kai waye". Kai yaro ne. Ban zo gareka da nufin na yake ka ko na hallakar da kai ba, na zo ne domin na taimaka maka bisa abinda ba zaka iya ta6awa iyawa ba mutukar ban taimaka maka ba. Domin miliyoyonka sun gaza. Amma kafin nan zan nuna maka matsyina da na kai. Na shallake tunaninka da hangenka. Idan ka saduda zan baiyana gareka na sanar da kai sunana da irin taimakon da zan yi maka." Ba tare da ya ko kalleshi ba ya kada ya yi gaba tsohon ya bishi da kallo cikin murmushin mugunta yana girgiza kai. Sarki Jurhama ya ci gaba da tafiya ba tare da waigo ba. Ya ma manta da batun wannan tsoho. Saharar da yake tafiya a kanta ta dau zafi sosai, kishirwa ta dameshi daga shi har dokinsa, babu ruwa, kuma babu wani tsiro a kan saharar. Dan haka ya sauka daga kan dokin ya rike linzamin dokin suka kama tafiya a hankali-a hankali. Can bai ankara ba sai ji ya yi an fincike linzamin dokin daga hannunsa. Ya jiyo bayansa a fusace dan ganin wane mai tsautsayin ne ya aikata wannan babban lefi a gareshi? Wadansu irin halittu ya ga ni kimanin goma sha biyu masu mutukar girma tamkar tsauni. Sai gani ya yi guda ya jefa dokinsa a baki ya yi masa tauna daya ya hadiye, tamkar dan adama ya sa tsokar nama guda ya lunkuma a bakinsa, haka halittar nan ta dauki dokin ta lamushe. A dai-dai lokacin ne ya jiyo dariyar wannan tsohon nan da ya bayyana a gareshi dazu. Bayan daukewar dariyar tasa sai ya ce da shi, "ga wani dan abu daga cikin matsayina sai ka zuba ka gani, su kansu nafi karfinsu shiyasa nake sarrafasu, wabda ina da tabbacin kaima sun fi karfinka. Ba ma kai ba, daya daga cikinsu zai iya kifar da kasa a cikin sa'a daya. Don haka a bada homma mai burin zama gwarzo". Ya kima budlshe da dariya, saharar ta kuma amsa amon sautin muryar daryarsa. Daukewar tasa ta yi dai-dai da surarsa da akai aka gwarashi a jikon wani abu mai kama da tsini. Aka gara gwarashi da tsauni a karo na biyu. Anan yaji numfashinsa ya dauke, bai kuma sanin halin da yake cikin ba.". Shumar ya bakata a dai-dai nan sakamakon kwankwasa kofar da yaji ana yi. Nan take shumar ya mike yaje ya bude kofar sai ga saikon Harayi Baruzul Damsus ya shigo fuskarsa cike da annuri yana murmushi. Al'amarin da ya mutukar basu mamaki ke nan gaba dayansu. Baruzul Damsus ya ce, "kuyi hukuri na katse muku hanzari, amma naga kun manta da abin da ya kamata ku fara yi mafi mahimmanci a gareku. Bawani abu bane face yanke shawara bisa sharadin da na gindaya muku akan bukatar da kuke son na biya muku. Ku rabu da baiwa junanku labari ko kuma son jin labarin yadda matata ta ci amanata. Lallai ina son ku yanke wannan shawara a tsakanin yau zuwa gobe domin 6ata lokaci a tsakaninmu na da hadari, saboda nayi bincike na gano cewa saura kwanaki kadan Sarki Sahibul Hairi ya sami nasarar abin da ya tafi nema ya dawo gida. Kun ga kuwa idan kuka yi sakaki har ya dawo baku kawar da Aminul Has ba har abada burinku ba zai cika ba". Koda gama fadin haka sai Baruzul Damsus ya nufi jikin bango ya shafa shi da hannunsa na hagu. Take bangon ya tsage ya wuce kamar yadda danshi ke tsatstsafowa daga cikin kasa, ya fice fit daga cikin dakin. Koda ganin haka sai su Waziri suka sake tsorata da al'amarin Baruzul Damsus suka shiga sabon tunani domin sun san cewa abin da ya fada musu gaskiya ne. Bisa wannan dalili ne daya daga cikinsu cikin tsananin damuwa ya ce, "Ya kai shugabana mene ne abin yi, shi zamu aminta da sharadin Baruzul Damsus ne ko kuwa zamu hakura da bukatar tamu ne gaba daya?." koda jin wannan tambaya sai Waziri ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ai tun da muka kawo izuwa wannan matsayi ina ganin cewa bamu da wani za6i na Baruzul Damsus Ku tuna cewa matsoraci baya zama gwani har abada. Haka kuma ita duniya ba'a samunta a banza, shi kuwa nema kugiya ne ba'a san abin da zai janyo ba sai an jarraba. Kawai mu karfafi zukatammu mu mika wuya mu jira muga abin da zai faru". Gama fadin haka ke da wuya sai farin ciki ya lullu6esu suka ce, "Tabbas mun gamsu da wannan jawabi naka bamu da wani haufi a kansa. Kashe gari da sassafe bayan su Waziri sun yi kalaci sai Baruzul Damsus ya sa ala sake kai su fadarsa. Da zuwa sai suka iskeshi cikin mutukar farin ciki tamkar wanda ya gama cika burinsa na duniya. Ko zama su Waziri ba su yi ba sai ya dubesu cikin murmushi ya ce, "Na yi murna da naji kun yanke shawara akan cewa kun amince da sharadina sabo da haka na urmarceku da ku kama hanya ku koma birninku na Misra ni kuma zan biyo bayanku zuwa gobe, ina mai tabbatar muku da cewa a cikin kwana uku rak! Zan sato Takalmi, Alkyabba da Sandar Aminul Has na kawo muku. Lallai ku kasance masu cika alkawari a gareni, odan kuwa ku ka sa6a, ina tabbatar muku da cewa dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba. Yanzu sai ku tashi ku yi haramar tafiya na sallameku". Dajin wannan sai su Waziri suka yi sallama da Baruzul Damsus cikin murna suka fice daga fadar sannan suka hau dawakansu suka durfafi birnin Misra. ¤¤¤¤¤¤ A can birnin Misra kuwa, a ranar da wannan al'amari ya faru ne Aminul Has ya yi wani mummunan mafarki mai ban tsoro. A cikin mafarkin nasa an nuna masa wani bakin jaki ya take mutum ya kashe shi. Faruwar haka ke da wuya sai jini ya kama zuba daga jikin mutumin ya yi ta kwarara yana jika gonakai. Nan take duk shukar garin ta kone kurmus, sakamakon wannan jinin da ya jika kasa. Cikin rusa ihu da firgicewa Aminul Has ya farka daga wannan mafarki ya mike zaune zumbur! Karar da ya yi ne yasa matarsa ta farka, dama tare suke kwance bisa gado a wannan lokaci. Cikin firgici itama ta farka. Koda ta fahimci cewa Aminul Hasa ne ya yi mafarki na ban tsoro sai ta rungumeshi tana shafarsa ta ce, "Ya kai mijina bani labarin irin mafarkin da kayi". Ba tare da 6oye komai ba Aminul Has ya zaiyane mata duk abin da ya gani a cikon mafarkin nasa. Koda jin haka sai hankalinta ya dugunzuma ainun, tayi shiru tana tunani da nazari. Daga can sai tai ajiyar zuciya ta daga kai ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina kayi sani cewa kakana ya sanar da ni ilimon fassarar mafarki, tabbas wannan mafarki naka yana nuni da cewa makiyanka suna nan suna dana maka tarkon yadda za su sami nasarar hallakaka. Wannan bakin jaki da ka gani a cikin mafarkin shi ne makiyinka. Mutumin da ya danne kuma kaine. Wannan jini da ka gani ya malala gonakai ba komai bane face zaluncin makiyanka akan jama'ar gari. Shukoki da ka ga sun kone yana nuna cewa makiyanka za su kwashe duk arzikin wannan birni su tsiyatar da kowa". Lokacin da matar Aminul Has ta zo nan a jawabinta sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da ko yaushe har tausayin jama'a yasa idanunsa suka ciko da kwalla. Cikin alamun karayar zuciya ya dubeta ya ce, "Ya ke matata kin sani cewa nayi imani da ke dari bisa dari domin in ba don taimakon da kika bani ba da tuni yanzu na dade da mutuwa. Yanzu wacce shawara za ki bani domin na tsira daga muggan tarkon da wadannan makiya nawa suka dana mini, ko don sabo da na ceci rayuwar jama'a da dukiyoyinsu?". Koda jin wannan magana sai matar Aminul Has tayi shiru tana tunani har izuwa lokaci mai dan tsaho, sannan ta ce da shi, "abin da za a yi shi ne, duk abin da ka ga na yi kada ka tambayeni dalili. Kuma abin da na umarceka da yi ka yi shi kawai koda kuwa cewa na ce ka shiga cikin wuta Aminul Has ya kyada kai ya ce, "ai ko cewa za ki yi na cakawa kaina wuka a ciki ba zan ki ba". Daga wannan rana Aminul Has ya zuba ido kuma ya kasa kunne yaji ko matarsa za ta umarceshi da yin wani abu sa6anin wanda ya saba yi kullum ko kuma ita da kanta za ta yi wani abun wanda bata saba yi ba, amma shiru, kamar maye ya ci shirwa har izuwa tsawon kwana uku. A safiyar kwana na uku ne bayan sarki Aminul Has ya gama shiri tsaf zai tafi fada sai matarsa ta zo gareshi rike da wata katuwar jakar fata. Kawai sai ta mika masa jakar fatar ya kar6i, sannan ta ce da shi, "ya kai mijina kayi sani cewa ba komai bane a cikin wannan jaka ba face takalmi, alkyabba da sanda iri daya sak da wanda ke jikinka yanzu tamkar an tsaga kara babu digon bambanci. Ina son ka tafi da wannan jaka a sirrince, kafin ka isa fada ka sami ka6a66en waje ka 6oye jakar inda babu wanda zai gani. Kada ka taso daga fada sai dare ya soma sannan ka biyo ta inda ka 6oye wannan jaka ka sauya takalminka, alkyabbarka da andarka, ma'ana ka sanya na gaskiyar a jakar ka 6oyesu ka dawo gida sanye da na karyar ka kwana da su a jikinka". Koda jon wannan umarni sai Aminul Has ya cika da mamaki. Har ya bude baki zai tambayi dalilin bashi wannan umarni sai ya tuno da sharadin da ta kafa masa, sabo da haka sai yai shiru bai ce komai ba ya kar6i jakar kawai ya juya ya tafi. Kamar yadda matar tasa ta umarceshi ya yi hakan ya yi bai karya ka'ida ba. Wato sarki Aminul Has bai baro fada ba sai da dare ya yi, kuma ya 6oye ta inda ya 6oye wannan jaka ya sauya takalminsa, alkyabbarsa da sandarsa ya nufi gida kai tsaye cikin tsananin tsoro da fargaba. Gani yake a ko yaushe za a iya hallakashi tun da baya tare da abubuwa uku da ya gamsu cewa su ne suka kareshi daga dukkan masifa. Lokacin da Aminul Has ya shigo cikin turakarsa ya iske matarsa a zaune akan gado tana jiransa, hankalinta a tashe sakamakon ganin cewa ya dade da yawa bai dawo ba. Koda ta hangoshi sai ta ruga gareshi ta rungumeshi cikim matukar farin ciki, sannan ya sa bakinta dai-dai kunnensa tayi masa magana cikin rada ta ce, "idan mun kwanta muna barci karufe idanun ka kamar kana barcin, amma kada kayi barcin, kuma kanutsu kaji abinda zai faru a jikinka. Kai za ma ka iya byde idanunnka kadan domin ka ga abin da zai faru, amma kada ka kuskura kayi ido biyu da abin da ya shigo". Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa kan gado suka kwanta. Dama kafin su kwanta din ta kashe fitilun turakar, turakar ya yi duhu dumdum! Ko tafin hannu mutun ba zai iya gani ba. Nan fa suka yi lamo tamkar suna barci har ma jan munsharin karya auke yi. Bayan kamar rabin sa'a da kwanciyarsu sai suka ji wata irin iska mai sanyi ta buso cikin cikin turakar. Al'amarin da jefa matukar tsoro ke nan a cikin zukatansa. Amma sai sukadaure suka ki su motsa jikinsu. Cikin mutukar karfin hali sarki Aminul Has ya bude idonsa guda kadan kawai sai ya ga wani abu kamar inuwa ya ratso bango ya shigo cikin turakar ya tsaya dai-dai kansa. Koda abin ya dafa kafarsa sai yaji takalminsa ya cire, abin ya sake dafa jikinsa da hunnunsa, sai alkyabbarsa ta 6ace, sandarma da yake ruke da ita sai ta 6ace 6at. Faruwar haka ke da wuya sai itama inuwar ta 6ace 6at! Bayan kamar dakika dari da ashirin sai Aminul Has ya ga matarsa ta mike zumbur! Taje ta kaunna fitilun turakar haske ya gauraye turakar. Sai gashi kuwa Aminul Has bayatare da abubuwa uku a jikinsa. SARKIN SARAKAI Littafi Na Hudu (4) Part C. . Marubucin littafin Abdul Aziz sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa NAN TAKE MATAR TASA TA BUSHE DA DARIYA SANNAN TA RUNGUMESHI TA CE, "YA KAImijina, kayi sani cewa gobe kana da gagarumin yaki a fada, domin a gobe ne za ka ga makiyinka a fili wadanda suke son su yi maka juyin mulki su hallakaka. Abin da na ke so da kai shi ne, ka tashi da duku-dukun safiya ka tafi izuwa inda ka boye wannan jaka ka sanya alkyabbar da takalmin, sandar ka wuce kai tsaye izuwa fada. Duk irin sauyin da za ka gani kada ka ji tsoron komai, kaje ka zauna a kan karagar mulkinka." Koda gama jin wannan batu sai Aminul Has ya sumbaci goshin matarsa ya ce, "madallah da matar da take kaunar mijinta fiye da uwa take son danta. Hakika kina bina bashin da ban san yadda zan iya saka miki ba." Nan take suka sake kashe fitilun tirakar kamar yadda suka saba kwanciya a kullum, har barci ya kwashe su basu sani ba. Da asubar fari zakara ya baiwa Aminul Has sa'a ya tashi ya yi wanka ya kintsa, ya sanya tufafinsa wanda ya saba sawaa kullum, sannan ya sulale ya fice daga cikin gidan sarautar ba tare da kowa ya shaida shi ba. Kai tsaye ya wuce can cikin wani lambu mai yawan dogayan bishiyoyi da dogayan ciyayi masu duhuwam inda ya hoye jakar. Da shigar Aminul Has lambun sai ya wuce izuwa cikin wata duhuwa ya bankada ya dauko ajiyarsa. Cikim hanzari ya bide jakar ya fiddo da sandarsa, takalminsa da alkyabbarsa. Nan take ya sanya takalminsa da alkyabbarsa sannan ya dogara sandar ya fice da sauri ya nufi fada. Da zuwan Aminul Has fada sai ya cika da mamaki, domin ya iske kofar cike makil da dakaru, dukkaninsu sun yi shigar yaki ta musamman, sunyi sahu-sahu biyu. Aka'ida wadannan dakaru basa fitowa sai bayan sarki ya iso, amma yau gashi sun riga sarki fitowa. Nan fa Aminul Has yaji a jikinsa cewa lallai akwai makarkashiyar da ka killawa amma sai ya dake ya ratsa ta tsakiyar dakarun ya wuce izuwa cikin fadar. Koda ya yi nazzarin fiskokin dakarun sai ya gane cewa basu bane wadanda suka saba tsayawa ba a bakin kofar, lallai an sauyasu. Da shigar Aminul Has cikin fadar kuma sai ya ga abin mamaki. Ba komai ya gani ba face Waziri da dukkanin mukarrabansa a tsaitsaye cikin shigar yaki sun yiwa fadar kawanya kimunin su dari daya. Gaba daya sauran fadawa da barori wadanda suka saba hidima a fadar babu ko mutum daya daga cikinsu. Da shigar Aminul Has sai aka yi sauri aka rufe gaba daya kofofin fadar ya zamana cewa babu ta inda mutun zai iya fita. Faruwar hakan ke da wuya sai Waziri da mukarrabansa suka bushe da dariya gaba dayansu suka yi ta kyalkyalawa kamar ba za su daina ba. A wannan lokaci Aminul Has ya tsaya cak! A tsakiyar fadar yana kallonsu kawai. Daga can sai suka ga shima ya 6arke da dariyar yana tayasu. Al'amarin da ya sa suka tsuke nasu bakin ke nan suka kura masa idanu, domin da farko sun yi tsammanin ko ya sami ta6in kwakwalwane. Aminul Has ya daina dariyar sannan ya dubi Waziri cikin murmushi ya ce, "me kuke nufi dani?". Koda jin wannan tambaya sai Waziro ya sake bushewa da dariya a karo na biyu domin ya gane cewa Aminul Has ba zautuwa ya yi ba Waziri ya hada fuska sannan ya nuna Aminul Has da hannu ya ce, "Ya kaia wannan shashashan sarki kayi sani cewa mun gaji da walakancinka na banza da wofi, wanda mataccen sarkinmu ya bar maka domin ka takuremu ka hanamu walwala da jin dadi a cikin mulkinmu. Sabo da haka yanzun za mu yi maka kisan wulakanci na haye karagar mulkinka. Kayi sani cewa tuntuni mun dade muna ta kokarin halaka ka amma mun kasa sabo da kana tare da abubuwan sihiri guda uku wadanda suke kareka. To ka sani cewa a jiya mun sa sarkin 6arayi Baruzul Damsus ya shiga har cikin turakarka ya sace wadannan abubuwa guda uku a jikinka kana barci baka sani ba har ma mun konasu a daren jiya. Yanzu ta ya za ka iya kare kanka daga mugun kisan da zamu yi maka?". Sa'adda Aminul Has yaji wannan batu sai yai murmushi, sannan dubi Waziri ya ce, "Shin kai makaho ne ko kuwa mai idanu? Ka dubeni da kyau ka gani, abubuwa ukun nawa da kuka sa aka sace irin su ne sak a tare da ni yanzu ko basu bane? Ga sandar a hannuna, da alkyabbata a jikina, kuma ga takalmina a kafata! Ina mai sanar da kai cewa kayan da sarkin 6rayi ya sace mini a jiya da daddare ba su bane na gaskiya ba. Tun a jiya na cire na gaskiyar na 6oyesu

Chapter 13 of 19