Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a can lambuna na wajan gari, yau da duku-dukun safiya naje na daukosu na sanyasu a jikina, sannan na taho fada. Ina mai tabbatar maka da cewa duk yawan nan naku na banza ne, domin ba za ku oya hallakni ba. Yanzu kun rufe kofofin fadae gaba daya babu wanda zai kawi mini dauki, kuma babu wanda zai kawo muku. Ni da ku kowa karfinsa da sihirinsa ya kwaceshi." Koda gana fadin haka sai Aminul Has ya gyara tsayuwa ya ruke sandarsa da hannu biyu. Cikin tsananin firgita da taurin rai Waziri ya dakawa dakarunsa tsawa ya ce, "Su afkawa Aminul Has su yi gutsun-gutsun da sassan jikinsa". Nan take kuwa dakarun suka yi ca! A kansa tamkar an ajiye kwayar dawa a tsakiyar gidan tururuwa. Nan fa fadar ta hargitse da ihu mazaje, karafkiyar karafa, domin Aminul Has ya zamo tamkar shaidani a cikinsu. Duk inda ya kai duka da sandar hannunsa sai ka ga ya bazar da sama da dakaru biyar. Kuma take suke zama gawa ko shurawa basa yi. Shi kuwa idan suka sari jikinsa sai kaji kara kal! Tamkar sun sari dutse. Wani lokacin idan suka yi masa rubdugu suka lullu6eshi suka danneshi kasa da ya yunkura sai ka ga ya taso sama ya tarwatsasu tamjar an jenyesu da kugiyoyi. Koda dakarun suka ga Aminul Has baya jin sara da suka kuma sai bankesu yake tayi suna ta mutuwa, sai suka fara rugawa da gudu izuwa bakin kofofin fadar da nufin su bude su gudu. Koda Aminul Has ya fahimci hakan sai ya kwaci kwari da baka a hannun wani Badakare ya rinka harbo wadanda suka ruga jikin kofofin suna fadowa kasa matattu. Babu abinda zai baiwa mutun mamaki face irin tsananin zafin naman da Aminul Has ke amfani da shi wajen harbo dakarun, domin a cikin dakika biyu yana iya dana kibiyoyi arba'in cikin bakansa ya harbe mutum arba'in din. Kafin a jima Aminul Has ya kashe sama da rabin Dakarun da ke cikin fadar. Koda ganin wannan al'amari, sai cikin Waziri ya duri ruwa suka fara tunanin hanyar da za su bi su tsira da rayuwarsu. Abin da ya fara fado musu a rai shi ne suma su shmmaci Aminul Has su ruga su bude kofa su fita. Amma kuma samun nasarar yin hakan abu ne mai hadari, domin zafin naman Aminul Has ya wuce tunaninsu. A wannan lokaci Waziri da manyan mukarrabansa sun 6oye ne a bayan karagar mulkin. Nan fa suka fara tattaunawa a tsakaninsu. Waziri ya dubi mukarraban nasa ya ce, "Hakika bokanmu ya yaudaremu kuma ya cucemu, ashe bai samu ikon sato ababan dogaron Aminul Has ba?". Koda jin haka sai galadima ya ce, "ai ba yauda rarmu ya yi ba, shima an shammace shi ne. Ni kam a tawa shawarar kada mu ce zamu yi yunkurin gudu, kawai mu fito mu yakeshi da iyakar karfimmu da dai mu mutu ragwaye ai gwara mu mutu mazaje. Ina tabbatar muku da cewa a yau dai dayanmu ba zai tsira da rayuwarsa ba. Don haka dukkamu burinmu da shirinmu ya rushe, kawai mu fita mu yi kundumbala mu tari kaddararmu". Koda jin wannan batu sai hawayen takaici da bakin ciki ya su6uto daga cikin idanun Waziri, kawai sai ya kurma ihu ya mike tsaye sannan ya zare takobinsa ya ruga izuwa kan Aminul Has. Koda Aminul Has ya hango Waziri ya durfafoshi gadan-gadan da mugun nufi, sai Aminul Has ya daka tsalle sama ya kai masa wawan duka da sandar aka. Take kan Waziri ya rabe goda biyu tamkar an 6are gyada, ya sulale kasa matacce. Koda ragowr mukarrabansa suka ga abin da ya faru akan shugabansu, sai suka kara firgicewa, suka kasa fitowa dga bayan karagar har dai Aminul Has ya gama kashe dukkunin dakarun dake cikin fadar. Lokacin da ake ta wannan gumurzu a cikin fadar, jara'ar gari sun yi cincirindo a kofar fada suna ta jiyo ihun daharu a ciki, gashikuma kofa a rufe take an ki budewa. Al'amarin da ya tabbatar da cewa lallai akwai makarkashiyar da ake shiryawa a kan harkokin mulki. Da yawa daga cikin jama'ar gari sai suka yi tsammmanin cewa ana ta kashe dakarun sarki Aminul Has ne makusanta a gareshi da kuma shi kansa Aminul Has din. Abin da basu sani ba shi ne, kishiyar hakan ce take faruwa. Bayan Aminul Has ya gama kashe dukkanin dakarun da ke cikin fadar ya zamana cewa duk inda ka duba ba abin da za ka gani face gawarwakin dakarun da kuma jinimalemale a kasa sai ya dubi 6angaren da kargar milki take ya ce, "ya ku makarraban Waziri, ku fito daga ma6oyarku ku yi mubaya'a gareni ku nemi gafara, idan har kuka yi alkawarin cewa ba za ku sake ha'intata ba ni kuwa zan yi muku rai, kuma na barku a cikin majalisata." Koda jin wannan batu sai mukarraban Waziri sukai tsurutsuru suka kasa fitowa sabo da tsoro. Tunaninsu shi ne, suma zargin cewa Aminul Has so yake ya yaudaresu. Cikim rada daya daga cikinsu ya ce, "mu amince da tayin Aminul Has, akwai abin da na shirya a zuciyata". Koda jin haka sai gaba dayansu suka fito daga ma6oyar tasu suka nufi inda Aminul Has yake suka durkusa a gabansa. Kawai sai suka kama tuba suna neaman gafara, harma suna kuka suna cewa, "ai Waziri ne ya yi musu dole suka bashi hadin kai". Ya yin da Aminul yaga yadda suka marairaice sai tausayinsu ya kamashi ya ce da su, "su mike tsaye ya yafe musu." Su duka suka mike tsaye suka kama murna da godiya. Aminul Has ya juya da baya ya nufi babbar kofa ta shigowa fadar da nufin ya budeta. Cikin shammata daya daga cikinsu ya dauki mashi a kasa ya duge sandar da ke hannun Aminul Has ta fadi kasa can gefe daya. Koda ganin haka sai su duka suka afkawa Aminul Has da nufin su hallakashi, domin a zatansu idan daya tare da wannan sanda ta hannunsa ba zai iya tsinana komai ba. Nan fa suka rufeshi da rubdugun sara da suka, har suka saishi kasa. Sai dai ko kadan makaman nasu basu yi tasiri a jikinsa ba, don fatar jikinsa ko kwarzanewa bata yi ba bare ya sami babban rauni. Cikin tsananin fusata Aminul Has ya yunkura ya taso sama ya watsar da su su duka suka zube kasa, kafin su yunkura su sake afka masa tuni ya hausu da naushi da bugi hannu da kafa. Duk wanda ya yiwa naushi daya a fuska sai ka ga jini na tsartuwa a hancinsa da bakinsa, kuma nan take ya fadi kasa matacce, sabo da karfin naushin ya wuce misali. Kafin cikin dakika dari da ashirin babu dayansu a tsaye ko a zaune rayayye. Sarki Aminul Has ya tsaya cak! Ya dubi dukkanin gawarwakin da ke kwance a cikin fadar, ya ga cewa shi kadai ne fa ya kashe su sai takaici da bakin ciki ya lullu6eshi. Nan take idanunsa suka ciko da kwalla, ya fara zubar da hawaye. Cikin sanyin jiki ya karasa bakin kofar fadar ya budeta da hannu daya alhalin sai karti Arba'in sun taru suke iya budeta. Koda kofar ta wangame mutanan gari suka yi arba da sarki Aminul Has suka ga shi kadai ne a raye a cikin fadar si suka rude da shewa da jinjina. Suka hau yi masa kirari. Aminul Has ya gadawa jama'a hannu suka yi tsit! Sannan ya ce, "ya ku jama'ar birnin Misra, ku yi sani cewa wadannan da na salwantar bada son raina ba ne, domin su ne wadanda suke son su kawar da mulkin Adalcin da ake yi muku su shimfida na zalumci. Ni kuwa na yiwa sarki Sahibul Hairi Alkawari cewa zan ci gaba da tafiyar da mulki kamar yadda ya saba tafiyar da shi, kuma zan tsare rayukan talakawa da dukiyoyinsu. Ina fata za ku gafarcene bisa wannan rayuka da na salwantar, domin da yawansu suna da nasaba da wasunku." Koda jin wannan sai wani dattijo mafi tsuma a birnin ya matso daf! Da Aminul Has ya ce, "ya shugabana kayi sani cewa wadanda ka kashe ina farin ciki da hakan, domin mutun baya cika na gari face yana kaunar ci gaban Al'umarsa. Hakika muna Alfahari da mutane irinka da irin su sarki Sahibul hairi wadanda suke son talakawa kamar yadda suke son kansu." Koda tsohon ya zo nan a jawabinsa sai mutane gari suka sake rudewa da shewa suka daga sarki Aminul Has sama suna masu ci gaba da yi masa kirari da jinjina. Duk wannan abu da ke faruwa Bokan su Waziri na la6e a can gefe daya yana cizon yatsa cikin tsananin takaici da bakin ciki, domin yaga samu yaga rashi. wannan shine abin da ya faru a birnin Misra bayan Sarki Aminul Has mai ruke da karagar mulki ya sami nasarar kawar da makiyansa. ¤¤¤¤¤¤¤¤ SARKI SAHIBUL HAIRI Al'amarin su sarki Sahibul Hairi kuwa, lokacin da suka kama tafiya suka iso inda suka bar aljanin da ya kawo su fadar Boka Shamzabul Azwas sai suka iske wajan wayam babu wata haliita mai rai guda daya. Al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalinsu ke nan suka yi cirko-cirko suna tunanin abin da ya kamata su ya. Daga can sai sarki Sahibul Hairi ya dubi gimbiya Humaira ya ce, "ya ke wannan Basadaukiya, yanzu ina dabara? Ta ya ya zamu yi wannan doguwar tafiya a kasa mu isa can garin su sadauki Awaisu mu kai masa 'yarsa Alfila domin ya yi mana jagora izuwa inda 'yan mata uku suke wadanda zan aura?" ya yin da gimbiya Humaira taji wannan batu sai tayi murmushi sannan ta sami wuri ta dubi sarki Sahibul Hairi cikin untsuwa ta ce, "ni zan iya rokon Ubangijima ya kaimu can a cikin kwanaki kadan, ti amma yin hajan ba shi da wani amfani". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf da yarinya Alfila, har ma suka kurawa Humaira idanu. Sarki Sahibul Hairi ya tambayeta ya ce, "mene ne dalilin da ya sa kika ce bashi da amfani yin hakan?" Humaira ta sake yin murmushi a karo na biyu ta ce, "ya kai wannan jarumin sarki, ka ga dai da farko da muka zo nan kayi amfani da duk karfin damtsenka da kuma karfin sohirinka wajen shoga gidan nan amma ka kasa. Ni kuwa sai gashi na bide maka kofa da taimakon Ubangijina mun shiga. Wannan abu da ya faru ya isa ishara a gareka kayi imani da Ubangijina ko ka rabauta, amma baka yi ba. Bayan mun fafata kazamin yaki da Boka Shamzabul Azwas ya sami nasra a kammu ya tsafancemu muka zama gumaka daga baya kuma muka sake tashi, ni ce na sake yin gumurzu da Shamzabul Azwas har na sami nasarar hallakshi da taimakon Ubangijina. Gashi har na mallaki wannan damara da ke kugunsa. Wannan abu da ya faru ahima ya isa ishara a gareka akan ka kar6i addinin musulinci, amma har yanzu baja kar6a ba. Shin akan wanne dalili zan ci gaba da yin tafiyata tare da kai tun da na biyoka ne dama domin na ja hankalinka izuwa mikakkiyar hanyar da babu karkata a cikinta, hasken da babu duhu a cikinsa, tafarkin gaskiya, tafarkin da kau da karya, wato tafarkin addinin musulinci! Ina tabbatar maka da cewa ni yanzu a nan zan rabu da ku na kama gabana, in ya so kowa tashi ta fishsheshi". Koda jin wannan batu sai hankalin yarinya Alfila ya dugunzuma ainun, ta faka kuka. Al'amarin da ya mutukar bawa Humaira da su sarki Sahibul Hairi mamaki ke nan. Humaira ta durkusa gaban Alfila ta ruke kafunfunta ta shiga rarrashinta tayi shiru, sannan ta tambayeta ta ce, "ya ke Alfila mene ne dalilin da ya sa kike wannankuku?" Alfila tayi ajiyar zauciya ta ce, "ba wani abu bane yasa kika ga ina wannan kuka ba face na san cewa idan kika tafi kika barni a nan su sarki Sahibul Hairi ba za su iya mayar dani kasarmu ba na sadu da mahaifina ba, domin daha nan zuwa kaarmu tafiya ce ta a kalla wata bakwai basa rakumi ko doki. Kuma akwai muggan abubuwan hadari a hanya wadanda ba za mu iya shallake hasarin su ba. Ina rokonki da ki taimaka ki ci gaba da tafiyar nan tare da mu domin nawa burin ya cika". Sa'adda gimbiya Humaira taji wannan batu, sai tai ajiyar zuciya sannan ta ce, "ya ke Alfila yanzu idan na kaiki kasarku kika sadu da mahaofinki za ki yi imani da addinina?" koda jin wannan tambaya sai Alfila ta yi murmushi ta ce, "Ai tun da na ga ma kin sami nasara akan Shamzabul Azwas na ji na gamsu cewa tsafi karyane, addininki shi ne addinin gaskiya, yanzu take ina son ki shigar dani cikin addinin naki". Da jin haka sai farin ciki ya lullu6e gimbiya humaira. Nan take ta biyawa Alfila kalmar shahada ta maimaita. Humaira ta mike tsaye sannan ta dauki Alfila ta goyata a bayanta. Humaira ta dubi yarinya Alfila da ke bayanta ta ce, "ya ke Alfila ki sani cewa daga yau kin zama 'yar uwata, duk rintsin da za ki shiga sai dai mu shiga tare". Gimbiya Humaira ta sake juyowa ta dubi su Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf ta ce, "ku kuma kun ci albarkacin wannan yarinya, sabo da haka ku zo mu ci gaba da tafiya". Gama fadin haka ke da wuya, sai gimbiya Humaira ta ci gaba da tafiya dauke da yarinya Alfila, su sarki Sahibul Hairi suka biyo bayanta cikin jin kunya. Gimbiya Humaira ta ci gaba da tafiya tana mai karanta wata addu'a ta musamman. Sarki Sahibul da Bawa Haluf kuwa suka rinka bin bayanta da sauri ba sa yarda ta basu sata. Nan fa suja rinka ganin abin Al'ajabi, domin gani suka yi suna wuce dazuzzuka tamkar walkiya na giftawa. Tafiyar da ya kamata su yi ta a cikin sa'a guda sai gashi sun shafeta a cikin dakika sittin. Haka dai suka ci gaba da wannan tafiya har suka shafe tafiyar kwana arba'in a cikin sa'o'i kadan A sannan ne dare ya riskesu a cikin wani dajo mai yawan manyan tsaunuka da duwatsu. Kuma a dai-dai lokacin ne hadari ya gangamo, gari yai duhu, iska ta soma kadawa mai karfi alamar ruwa na shirin sauka. Kafin dakika goma karkarfan ruwa ya kece kamar da bakin kwarya. Cikin gaggawa suka ruga izuwa cikin wani kogon dutse suka zauna. Zamansu ke da wuya sai Humaira ta dau wata karamar butar duma cike da ruwa tayi alwala sannan ta nunawa Alfila yadda itama za ta yi alwalar, sannan suka yi sallah tare. Duk abin da ke faruwa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf na daga can nesa kadan a zaune suna kallonsu. Sarki Sahibul Hairi ya dubi Bawa Haluf ya ce, "ya kai Haluf kayi sani cewa ina ji a jikina cewa wannan addini na Humaira gaskiya ne, kuma kaima kanka shaidane bisa abubuwan da muka gani a zahiri na ban al'ajabi. To amma inda matsalar take shi ne, ina jin tsoron cewa idan na kar6i addinin shi ke nan har abada burina bazai cika ba". Sa'adda Haluf ya ji wannan batu sai yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "ya shugabana, amma ai idan baka manta ba Humaira ta gaya maka cewa idan har kayi imani da Ubangijinta dukkan burin ka zai cika, sabo da me ba za ka yi imani da shi ba idan har jikinka ya baka cewa addini ne na gaskiya?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Sahibul Hairi yai shiru yana sake-sake. Zuwa wani lokaci ya dago kai ya dubi Bawa Haluf ya kura masa ido na tsawan dakiku, sannan ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da tunani ba tare da ya ce da Bawa Haluf komai ba. Tabbas komai na duniya rabone, kuma komai yana da lokacinsa. Gashi dai sarki Sahibul Hairi ya gamsu da cewa addinin Musulinci gaskiya ne, amma kuma ya kasa tankwara zuciyar tasa ta yarda ta kar6i addinin sabo da tsoron kada ya yi asarar abin da ya fito nema. Lolacin da ruwan sama ya ci gaba da tsugewa, sai wata irin iska mai sanyi ta rinka busowa har cikin kogon da su Humaira ke ciki ta addabesu. Ba shiri su sarki Sahibul Hairo suka mike suka kama karyo tsurarrun itatuwan da ke cikin kogon suka hada makamashi. Bayan sun tare ice mai yawa sai suka fara kokarin kunna wuta ta hanyar goga dutse da dutse, amma sai wuta ta ki kamawa. Lokacin da Humaira ta ga sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf sun jima suna fama amma sun kasa kuma wutar sai ta dubi Alfila cikin murmushi ta ce, "je ki ki kar6i duwatsun a hannunsu kiyi bisimilla ki ambaci sunan Ubangijin musulinci, da izininsa wutar za ta kama." Ba tare da fargabar komai ba yarinya Alfila ta mike tsaye taje ta kar6i duwatsun biyu da ke hannun sarki Sahibul Hairi tare da yin bisimilla kamar yadda Humaira ta koyar da ita, ta ambaci sunan Ubangijin musulinci. Gogawa daya tayi akan makamashin sai wuta ta tashi kamar an zuba mai. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka cika da tsananin mamaki, jikinsu yao sanyi. Nan dai suka gewaye wutar su hudun suna jin dumi. Alfila na zaune daf da Humaira, sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf na daga can 6angare guda suna fuskantar juna. A duk sa'adda Humaira ta dago kai sai ta ga sarki Sahibul Hairi na satar kallonta, kawai sai ta mike tsaye tsam! Ta bar gaban wutar ta koma can gefe daya taa shimfida buzu ta zauna tana mai fuskantar gabas, sannan ta dauki casbaha ta kama lazumi. Ba wani abu bane yasa sarki Sahibul Hairi ke satar kallon Gimbiya Humaira ba face tsananin kyawunta da ya ribaci zuciyarsa. Tun ranar farko da ya fara ganinta yaji zuciyarsa ta buga da karfi, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan. Abin da sarki Sahibul Hairi bai sani ba ya kamu da tsananin kaunarta da begenta. Haka dai su sarki Sahibul Hairi suka ci gaba da zama a cikin wannan kogon dutsen har dare ya yi sosai suka kama barci. A duk sa'adda sarki Sahibul Hairi ya farka sai ya ga Alfila da Bawa Haluf na ta sharar barci abinsu. Ita kuma Humaira na nan a zaune bisa buzu tana ta lazumi. Wani lokacin kuma sai ya ga ta mike tsaye ta kama nafilfiloli. Kai a takai ce dai Humaira bata gushe ba tana ibada har sai da ta gabatar da sallar Asuba ta jira Alfijir ya keto sannan ta kwanta ta lullu6e jikinta gaba daya tayi barci. Lokacin da gari ya waye sosai sai sarki Sahibul Hairi da bawa Haluf suka farka daga barci suka ga Humaira da Alfila na ta barci abinsu. Kawai sai sarki Sahibul Hairi ya dauki kwari da bakansa ya rataya sannan ya soke takobinsa a cikin gidanta da ke daure a kugunsa ya dubi Haluf ya ce, "zo mu tafo neman abin kalaci. Koda jin haka sai shima Haluf yai sauri ya dauki nasa kayan yakin suka face daga cikin kogon dutsen suka nausa cikin daji. Ba su yi wata doguwar tafiya ba suka hango wata barewa a can saman wani dogon tsauni da ke nesa da su. Sarki Sahibul Hairi yai sauri ya dana kwari a cikin bakansa ya saita barewar, amma sai ya auna ya ga cewa ba zai sami nasara ba domin akwai tazara sosai a tsakaninsu da barewar, don haka sai ya yiwa Haluf inkiyar cewa su lalla6a ta bayan barewar su kusanci tsaunin da take kai. Cikin sanda suka rinka taku dai-dai a hankali har suka isa kan tsaunin suka hau a durkushe yadda za su iya hango barewar ta baya, amma ita ba ta hangosu ba. Cikin hanzari sarki Sahibul Hairi ya sake dana kwari a cikin bakansa ya ta6eshi iya karfinsa ya saita barewar a ciki, sai ya saki harbi. Kibiyar ta tafi cikin azababban gudu. Koda taje daf da barewar sai ta tsaya cak! A cikin iska ta kasa huda cikin barewar. Ita kuwa barewar sai ta juyo tayi arba da su sarki Sahibul Hairi, ta kura musu ido kawai. Al'amarin da ya matukar baiwa su sarki Sahibul Hairi mamaki ke nan, suka mike tsaye jikinsu a sanyaye suka kasa juyawa da baya, kuma suka kasa karasawa inda barewar take. Cikin tsananin tsoro Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi a lokacin da jikinsa ya kama karkarwa, ya ce, "ya shugabana waccan dabbar ba barewz bace aljanai ce, zai fi kyau mu hakura mu koma da baya domin na fuskanci cewa akwai muggan abubuwa a cikin wannan daji". Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya dakawa Bawa Haluf tsawa ya ce, "ai ni idan nayi gaba bana baya. Idan na za ka iya biyoni ba ka tsaya a nan ka ga abin da zai faru tsakanina da waccan barewar, idan kuma ba za ka iya tsayawa ba kayi kallo ba to ka koma inda muka fito". Koda gama fadin haka sai sarki Sahibul Hairi ya zare takobinsa ya ci gaba da hawa kan tsaunin ya dufafi inda barewar take kai tsaye ba tare da shakkar komai ba. Shi kuwa Bawa Haluf sai yaji kamar ya juya da baya a guje amma sai ya daure ya tsaya domin ya ga abin da zai faru. Har sarki Sahibul Hairi ya isa daf da barewar wannan kibiyar ba ya harba mata tana nan a tsaye a cikin iska daf da barewar. Da zuwan sarki Sahibul Hairi gaban barewar sai ya daga takobinsa sama ya kai ma ta wawan sara da nufin ya tsarge jikinta gida biyu. Ba zato ba tsammani sai ya ga barewar ta rikida ta zama sarki Barusa rike da takobi yana mai kare saran. A sannan ne wannan kibiya ta fadi kasa. Koda sarki Sahibul Hairi ya ga sarki Barusa a gabansa sai ya ja da baya a tsorace cikin mutukar mamaki ya kasa ci gaba da kai masa hari. Sarki Barusa ya bushe da dariyar mugunta ya ce, "shin kana tsammanin na mutu ne? To ka sani cewa kashe na mijin kwarai ba karamin aiki bane, duk abin da ke faruwa ina bie da ku baku sani ba. Yanzu gashi kun je kun sha bakar wahala kun dauko yarinya Alfila a cikin fadar Shamzabul Azwas ni kuma zan kwaceta a salim-alim a hannunku ba tare da na sha wahalar komai ba". Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi shima ya bushe da dariya ya ce, "ya akai wannan sarki kayi sani cewa wannnan mafarkin naka ba zai ta6a tabbata ba don haka ina mai baka shawara da ka janye wannan manufa taka ka koma kasarka ka ci gaba da mulki, ka hakura da iyakar abin da ka mallaka. Idan kuwa ka zake ina tabbatar maka da cewa za ka iya rasa rayuwarka". Ya yin da sarki Barusa yaji wannan batu sai ya sake kyakyatawa da Dariya a karo na biyu ya ce, "hakika iska na yawo da mai kayan kara. Tsaya kaji na gaya maka gaskiyar abin da duk yasa na kasa mallakar yarinya Alfila, shi ne zai sa kaima ka kasa mallakarta. Yanzu zan kamaku nayi garkuwa da ku, domin gimbiya Humaira ta kawo yarinya Alfila, idan kuwa taki sai na hallaka ku. Sannan na bi sawunta itama na hallakata na dauke Alfila." Sa'adda sarki Sahibul Hairi yaji hakan sai abin ya bashi dariya ya ce, "ya naji kana cewa za ka kama mu kayi garkuwa damu kamar wanda zai kama 'yan tsaki? Shin kana tsammanin kamani a hannunka abu ne mai sauki?". Koda jin wannan tambaya sai Barusa yai murmushin mugunta ya ce, "yanzun nan kuwa za ka sha mamaki, domin sanin da ka yi mini na da ne, amma wannan karon na zama MURUCIN KAN DUTSU, ban tashi fitowa ba sai na shirya" . SARKIN SARAKAI Littafi Na Huɗu (4) Part D. . Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa KAFIN BARUSA YA GAMA RUFE BAKINSA TUNI SARKI SAHIBUL HAIRI YA KURMAihu ya kara afka masa da nufin su ci gaba da gumurzu. Kawai sai Barusa ya nunashi da hannu, take wata irin murtukekiyar sarja ta karfe ta nannade sarki Sahibul Hairi tun daga sama har kasa, ta daure shi tamau ya zamana cewa ko motsi baya iyawa. Nan fa sarki Sahibul Hairi ya shiga kokarin kwace kansa ta hanyar amfani da karkin sihiri, amma sai sihirin nasa ya ki ya yi tasiri. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan ya tabbatar da cewa ya kamu. Bawa Haluf dake can kasan tsaunin kuwa koda ya ga abin da ya faru da shugabansa sai ya juya ya falfala da gudu da nufin ya tsere. Amma sai ya ga wani katon tsuntsu ya sauko kasa ya sureshi da 'yan yatsunsa ya mai da shi kan tsaunin inda sarki Sahibul Hairi ke tsaye a daure. Koda tsuntsun ya sakoshi kasa ya fado kusa da Barusa sai shima sarkar sihirin ta kanannadeshi ta daureshi tamau. Koda faruwar hakan sai sarki Barusa ya bushe da dariyar mugunta sannan ya rubuta wasika ya mikawa wannan katon tsuntsun da ya dauko Bawa Haluf. Shi kuwa tsuntsun sai ya bude bakinsa ya kar6i wasikar sannan ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka a cikin gajimare. Bacewar tsuntsun ke da wuya sai sarki Barusa ya tafa hannayensa biyu, take gidan dutse ya bayyana akan tsaunin, sai ga wadansu irin halittu masu kama da dodanni ba adadi suna fitowa daga cikin gidan dutse. Sai da suka shafe mintina masu yawa suna fitowa da jeruwa sahu-sahu sannan suka kare. Lokaci guda su duka suka yi sujjada ga sarki Barusa. Barusa ya dubi halittun ya ce, "ku kama wadannan fursunonin ku shigar da su cikin gidan nan ku jefasu cikin kurkuku ku kulle. Shugaban halittun ya ce, "an gama ya shugabana, shin akwai wani abun bayan wannan?" Sarki Barusa ya ce, "eh, ina son kuyi gagarumin shirin yaki, domin nan da wadansu 'yan sa'o'e kadan gimbiya Humaira za ta zo tare da Alfila, kuma nasan idan tazo za ta yi kokarin hanani Alfila. Lallai tsakaninmu da ita yaki ne mai tsanani sai mun yi da gaske zamu sami nasara a kanta. Koda jin wannan batu sai shugaban halittun ya kada baki ya ce, "ya shigabana lallai zamu yi shiri irin wanda bamu ta6a yin kamarsa ba. Ina tabbatar maka da cewa ko gaba dayan dakarun duniya ne za su zo su yakemu ba za su sami nasara a kanmu ba." Gama fadin haka ke da wuya sai shugaban halittun ya juya ya dubi wasu daga cikin yaransa su kuma sai suka kama sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka shiga da su izuwa cikin gadan. Ragowar kuwa sai suka koma cikin gidan suka yi ta fitowa da makaman yaki. Suka ci gaba da shirye-shiryen yaki. Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf bayan sun fita farauta sarki Barusa ya sake baiyana a garesu tare da sabon hatsabibanci. A can kogon dutse kuwa, lokacin da Humaira da Alfila suka farka daga barci, sai suka nemi sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka rasa. Alfila ta dubi Humaira ta ce, "ya ke 'yar uwata yanzu kuwa ina kike

Chapter 14 of 19