Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gwammace bai zo duniya ba yanzu a gaban idanunki zan yiwa wannan sarki da bawansa kisan wulakanci irin wanda baki taba gani ba. . Duk wannan bayani da sarki barusa ke yi sarki sahibul hairi na zaune akan aljani dabarus ya zuba musu idanu kawai ko gyara zaama baiyi ba maganganun da yake yma jinsu yake kamar tatsuniya ( kunji fa yarda da kai wajan sarki sahibul hairi) ita kuwa gimbiya shukura sa adda taji barusa ya gama jawabinsa sai ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma ta murtuke fuska tace kai barusa dakata kaji ka yi sake dan zaki ya girma ina tabbatar maka da cewa baka isa kayi mini komai ba domin dama na dade ina yin tanadinka. . Nima kuma a yanzu ban isa nayi maka komai ba tunda ban mallaki sihirin tsafin da zan iya ganin bayanka ba kafin na tareka mu gwabza yanzu ga dan uwanka nan sarki SAHIBUL HAIRI GAGARA BADAU saiku fara karawa mu gani ko zaka iya dashi '' koda jin wannan batu sai sarki barusa ya juya ya dubi sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan kuma ya murtuke fuska kawai sai yaga wata irin walkiya ta fito daga cikin idanun barusa ta bugi jikin sahibul hairi take rigar karfen da yake jikin sahibul hairi ta bace bat barusa ya bushe da dariya a karo na biyu yace yanzu saimu gwabza gaskiya da gaskiya. . Kafin sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni barusa yayi tsafi saiga wani narkeken aljani nan ya bayyana a gabansa wanda a girma da kwarjini ya ninka Aljani dabarus sau uku.a lokacinne kuma wata katuwar takobi ta bayyana a hannun sarki barusa. Cikin abinda baifi kiftawar ido ba sarki barusa ya haye kan narkeken aljanin suka afkawa sahibul hairi. Nanfa aka fara azababben yaki ya zamana cewa sahibul hairi na kaiwa sarki barusa sara da gatarin sihiri shi kuma yana karewa da wannan katuwar takobin yana maida martani wannan fada dai a sama suke yinsa bisa aljanun biyu cikin isa gimbiya shukura da bawa haluf kuwa sai suka daga kawunansu sama suna kallon abindake faruwa a cikin sararin samaniya. Al amin ne sunana. Sa adda takobin sarki barusa ta hadu da gatarin sihiri sai kaji wata irin kara mai firgitarwa tamkar saukar aradu sannan kuma sai tartsatsin wuya gami da hayaki sun tashi al amarin da ya janyo girgizar gidan sarautar kenan gaba daya jama ar dake cikin gidan sai da hankalinsu ya dugunzuma saida aka shafe sa a uku ana wannan gumurzu dayansu bai sami nasarar taba jikin daya ba amma tuni sun rugurguza ginin fadar domin a duk sa adda dayansu ya kaiwa daya sara ya goce duk abinda ya sama sai wannan abu ya rabe gida biyu koda kuwa dirkar gini ce shi kansa tartsatsin wutar da ke zuba daga jikin makaman fadan nasu sai da ya haddasa gobara in ba don gimbiya shukura na kashe wutar ba da karfin sihiri da tuni fadar ta kone gaba dayanta. .... LOKACIN DA SAURAN JAMA'A DAKE CIKIN FADAR SUKAJI FADAR NATA GIRGIZA KAMAR, zata rufta cikin kasa sannan karar haduwar makaman su sarki sahibul hairi, ta cika musu dodon kunne sai suka rude suka firgice aka kama iface iface, da guje guje domin ba a taba ganin tashin hankali ba irin wannan, kafin a jima wannan tashin hankali ya isa har cikin gari ko ina da ina, don haka sai gaba daya birnin ya hargitse kai bama mutane ba hatta, dabbobin gida da na daji saida suka firgice suka kama koke koke da, guje guje tsuntsaye kuwa tashi suka rinkayi suna barin shekarsu suna kaara nausawa cikin daji, domin neman maboya manyan dabbobi irinsu kura zaki damisa da sauransu, cikin ramuka da koguna suka ringa shigewa suna boye kansu, kai a wannan rana duk dabbar dake cikin ruwa bata yarda ta leko saman ruwa ba, tun sa adda aka fara azababben yakin tsakanin sarki barusa da sarki sahibul hairi, sai bawa haluf ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme saboda tsananin razana, ko kadan gimbiya shukura bata lura da halin da haluf ya shiga ba domin, gaba daya hankalinta na kansu sarki sahibul hairi sa adda sarki barusa, ya ga an shafe kusan sa a uku ana wannan dauki ba dadi amma ko sau daya, bai sami nasarar taba jikin sahibul hairi ba sai ransa ya baci zuciyarsa tayi bakikirin, kawai sai yai jifa da takobin hannunsa yai nuni da hannunsa guda, izuwa ga sahibul hairi take wadansu masun tsafi suka fito daga cikin, hannun nasa kimanin guda dari suka tafi da gudu kamar an cillosu daga cikin kasa zasu cake a cikin jikin sarki sahibul hairi kawai sai shukura ta nuna masun da yatsantsa guda take suka tsaya kyam a cikin isa kuma suka kone kurmus suka ruburbushe, koda ganin haka sai sarki barusa ya kara fusata ya juyo kan shukura suka fara musayar tsafi a tsakaninsu kowa na jefawa kowa mugayen abubuwa shi kuwa sahibul hairi sai ya zama dan kallo . Sai da barusa da shukura suka jefi junansu da muggan makamai sama da guda dari amma dayansu bai sami nasarar lahanta dan uwansa ba daga nan kuma sai suka jefawa juna wata irin iksa mai karfin tsiya sai gashi suna wujijjiga juna a sama suna ta katantanwa a cikin iska a wannan lokaci iskar sarki barusa tafi ta shukura karfi don haka sai tayi ta wulwulata da karfin tsiya cikin kankanin lokaci shukura ta fita daga cikin hayyacinta kawai sai iskar ta makata a jikin gini sannan ta saketa sai ga jini yana zuba a goshin shukura ta fado kasa magashiyan babu alamar tana numfashi koda ganin abinda ya faru sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma shi kuma sarki barusa sai ya tuntsure da dariyar farin ciki yace yanzu na gama da wannan munafukar maci amana saura kai karamin alhaki ina mai shawartarka daka bani wannan gatarin sihirin dake hannunka kuma ka durkusa bisa gwiwoyinka ka tuba gareni muddin kana son kaci gaba da rayuwa a doron kasa in ba haka ba kuwa yanzun na zan yi daga daga da sassan jikinka na batar dakai yadda har abada babu mai iya shaida barin jikinka guda yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai yayi murmushi irin na manyan mazaje wadanda basa karayar zuci yace yakai tsohon azzalumi kayi sani cewa babu wani da mai jini a jiki wanda ya isa ya firgitani walau mutum ko aljan domin ban san tsoro ba kuma ban san jada baya ba ina tabbatar maka da cewa babu wani bala'i ko wata masifa da ta isa ta rabani da wannan gatarin sihirin dake hannuna don haka ina mai shawartarka daka kauce ka bani hanya na fice daga cikin fadarka salin alin in ba haka ba kuwa zaka riski ajalinsa koda jin wannan batu sai sarki barusa ya bushe da dariya kawai sai ya watsawa sahibul hairi kibiyoyin tsafi da nufin su cake dukkan jikinsa koda kibiyoyin suka diro a kan jikin sahibul hairi sai duk suka narke suka zama jini shikuwa jikin nasa ko kwarzanewa baiyi ba ko da ganin haka sai ran sarki barusa ya baci ya dubi sahibul hairi yace amma kayi farar dabara daka sha jinin dodannina a dakin azaba na karkashin kasa ba don haka ba da tuni yanzu kibiyoyin tsafina sun nutse a cikin gangar jikinka tabbas yanzu ba zan iya hallaka ka ba da karfin sihiri amma idan ka ci maganin kaifi da tsini ai bakaci na karfin damtse ba koda gama fadin haka sai sarki barusa ya daka tsalle daga kan aljaninsa ya dira akan aljani dabarus ya gwabzawa sahibul hairi naushi a baki saboda karfin naushin saida sahibul hairi ya baje a kan aljani dabarus wani irin gudan jini yai tsartuwa daga cikin bakinsa sai yai shame shame kamar ya suma sarki barusa ya raba kafafunsa akan sahibul hairi kuma ya dunkule daya hannun nasa da nufin ya yiwa sahibul hairi fashin albasa aka bazato ba tsammani sai yaji sahibul hairi ya gwabza masa naushi a fuskarsa sarki barusa ya tafi da baya taga taga kamar zai rikito kasa daga kan aljani dabarus take idonsa guda ya kumburo saboda karfin naushin da sahibul hairi yayi masa amma sai ya sake rugowa kan sahibul hairi yaci gaba da tumurmusashi yana naushinsa hannu da kafa. Cikin zafin nama ba kakkautawa tun da sarki sahibul hairi yake fada da sadaukai bai taba haduwa da sadaukin daya yi masa mahaukacin duka ba irin wannan har saida ta kusa cewa sahibul hairi baya iya mai da martani sai dai kokarin kare duka kai da dukan ma yayi masa yawa saiya kasa karewar yanaji yana gani sarki barusa yayi laga laga dashi ya hada masa jini da majina sahibul hairi ya sake yin wanwar akan aljani dabarus ya zamo tamkar gawa sai numfashi yake yi dakyar hakika barusa ya fi karfin sahibul hairi nesa ba kusa ba domin ko tsaywa sukayi mutum ya dubi girmansu da kirar sadaukantakarsu yasan cewa banbancin a bayyane yake lokacin da sarki barusa ya ga ya sumar da sahibul hairi a karo na biyu sai ya sake zuwa kansa ya tsaya ya sunkuyya da nufin ya kamo kansa ya karya masa wuya koda ya kai hannunsa zai kamo kansa sai yaga sahibul hairi ya goce cikin zafin nama yayi dungure ta karkashin kafafunsa ya bulla bayansa kafin dabarus ya juya tuni sahibul hairi ya naushi bayan barusa da dukkan karfinsa nan take sarki barusa ya fado kasa daga kan aljani dabarus fadowar da zaiyi kuwa sai ya fado kan wata rusashshiyar dirkar gini koda buguwar kansa sai ya sume a wannan lokacine sahibul hairi ya mike tsaye da kyar ai kuwa sai ya hango bawa haluf da gimbiya shukura kwance a sume cikin tsawa sahibul hairi ya umarci aljani dabarus daya dauko gimbiya da bawa haluf ya fitar dasu daga cikin wannan fada kafin dakika biyu tuni aljani dabarus ya cika wannan umarni tuni sun luluka sama cikin gajimare bayan kaamar dakika dari da ashirin da bacewar su sahibul hairi sai sarki barusa ya farfado daga suman da yayi cikin razana ya mike tsaye zumbur ya kama dube dube baiga kowa ba a wajan face wadannan narkeken aljani nasa zaune waje daya yai tagumi sarki barusa ya dakawa aljanin tsawa yace ya kai shumakaru ina abokan gabata shumakaru ya risina yace ai tuni wannan aljani nasu ya kwashesu yayi sama dasu sun bace a cikin gajimare cikin tsananin fushi sarki barusa ya sake dakawa shumakaru tsawa yace me yasa ka kyalesu suka gudu shumakaru ya ce ya shugabana ai bana zartar da aiki face da umarninka koda jin wannan batu sai sarki barusa ya takarkare ya kwarara uban ihi mai tsananin firgitawa cikin nuna takaici tamkar ya fashe da kuka sannan ya sunkwi da kansa kasa yace yanzu yau ni aka zo har fadata aka cini da yaki hakika mata shaidanu ne in ba don shukura taci amanata ba da babu yadda za ayi sarki sahibul hairi ya sami ikon satar gatarin sihirina na sani cewa yanzu babu inda zasu nufa face gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya Alfila abinda zanyi kawai shine nayi gagarumin shiri nabi bayansu in yaso sai na labe a kusa da gidan shamzubul azwas sai bayan sun gama shan wahalarsu sun dauko alfila ni kuma na taresu na kwaceta na hallakasu koda gama wannan zance sai sarki barusa ya kama kyalkyala dariyar mugunta yaci gaba da yin dariyar kamar ba zai daina ba nima kuma saina ci gaba da tayashi wannan dariyar ni guyson muje zuwa wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki barusa da sarki sahibul hairi bayan sahibul hairi ya sami nasarar dauko gatarin sihiri Al amarin sarki sahibul hairi da aljani dabarus kuwa.... AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI DA ALJANI DABARUS KUWA SAI DA SUKA SHAFE SA A HUDU SUNA TAFIYA A CAN KOLOLUWAR SAMA SANNAN sahibul hairi ya umarci dabarus daya sauko kasa ba tare da wata gardamar komai ba kuwa sai aljani dabarus ya cika umarni har suka sauko kasa suka dira a cikin wani tafkeken jeji mai dogayen bishiyoyi da manyan tsaunika da fadamomi da koramai gimbiya shukura da bawa haluf basu farfado daga dogon suman da sukayi ba koda ganin haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma ya fara jijjigasu don tsammaninsa sun mutu ne aljani dabarus ne ya dubi sahibul hairi yace ya shugabana ka kwantar da hankalinka ba mutuwa sukayi ba dogon suma sukayi kaje ka samo ruwa ka yayyafa musu ni kuma sai nayi musu fifita da fuka fukaina in muka yi haka zasu farfado koda jin wannan shawarar sai sarki sahibul hairi ya ruga izuwa cikin wata korama ya tsoma wani mayafi nasa a ciki sannan ya daw a guje ya daddana mayafin akan fuskokin su shi kuwa dabarus sai ya kamayi musu fifita da fuka fukansa bayan dakika biyar da faruwar hakan sai duk su biyun suka farfado suna masu yin tari da atishawa koda ganin haka sai farin ciki ya lullube sarki sahibul hairi shukura da haluf suka kama kalle kalle da waige waige suna masu mamakin yadda aka yi suka tsinci kansu a cikin wannan daji koda sarki sahibul hairi ya fahimci halin da suke ciki sai ya bushe da dariya yace kuna mamakin ne bisa yadda kukazo nan? Shukura ta dubeshi tayi masa murmushi tace bana mamaki da al amarinka ya kai jarumi uban jarumai amma ina so ka gaya mini abinda ya faru tsakaninka da mijina shinka kashe shine?? Koda jin wannan tambaya sai sarki sahibul hairi yayi ajiyar zuciya sannan yace ai a rayuwata ban taba haduwa da sadauki mai tsananin karfi ba kamar mijinki tabbas in ba don ina da nisan kwana ba da tuni ya hallakani ina sanar dake lambo nayi masa kamar na suma sannan na shammaceshi na dokeshi daga kan. Daga kan aljani dabarus ni dai naga sa adda ya fado kasa kansa ya bugu da wani rusashshen tubalin gini harma goshinsa ya fashe jini ya zuba abinda ban sani ba shine shin suma yayi ko kuwa mutuwa yayi sa dda gimbiya shukura taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya cikin takaici tace yakai wannan sarki kayi sani cewa kayi babban kuskure da baka tabbatar da mutuwar mijina ba ai kaima kasan cewa manyan mazaje basa saurin mutuwa ina tabbatar maka da cewa sarki barusa na nan a raye kuma zaiyi gagarumin shiri ya biyomu duk inda zamu je ko shakka babu duk sa adda muka sake yin arba da shi sai ya sami nasarar hallakamu yayinda sahibul hairi yaji wannan batu sai yayi murmushi yace yake shukura kiyi sani cewa a rayuwata ni ,utum ne mai tsananin sa a bisa duk abinda nasa a gabana don haka ina tabbatar miki da cewa komai RINTSI DA TSANANI sai na cika burina na zama SARKIN SARAKAI na duniya lallai sai mun dauko yarinya alfila a cikin gidan boka shamzubul azwas kuma sai na sadu da sadauki Awaisu ya taimaka mini mun nemo wadannan yan mata guda uku wadanda zan auresu na sami daukakar dana ke nema Koda jin wannan batu sai gimbiya shukura ta jin jinakai tace tabdijam ashe kuwa kana da gagarumin aiki agabanka ina tabbatar maka da cewa wahalar da kasha a baya tamkar kaso daya ce daga dubun wacce zaka sha a nan gaba yakai wannan sarki kayi sani cewa nemo wadannan yan mata uku dai dai yake da nemo jaki mai kaho domin babu wanda yasan inda suk ) saboda sun boye kansu da karfin sihiri irin na sadauki awaisu tabbas in ba sadauki awaisu ba babu wanda zai iya laluben inda suke shi kansa babu tabbacin cewa zai iya gano inda suke a cikin karamin lokaci yakai wannan sarki idan har dukiya kake bukata da kuma daukaka aiko a yanzu ka samesu domin wannan gatarin sihirin kadai daka mallaka ya isa ya baka duk abinda kake bukata ina tabbatar maka da cewa idan kaje ka ajiye wannan gatarin a cikin gidan sarautarka saika sami dukiya mai yawan da tafi cikin RIJIYA GABA DUBU arba'in kasancewar kayi babbar bajinta wacce babu wanda ya yi ta a wannan zamani don haka dole ne labarinka ya bazu ko ina a cikin duniya mai zai hana yanzu ka koma kasarka kaci gaba da sabuwar rayuwa? Amma ina mai rokonka alfarma guda daya Alfarmar kuwa itace ka daure muje gidan boka shamzubul azwas mu dauko yarinya Alfila ka mallaka min ita koda jin wannan batu sai sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan ya dubi gimbiya shukura yace kai duniya ba gaskiya wato dai kina nufin duk wahalar da nasha a baya ta zamo ke nayi wa kenan idan na hakura da gatarin sihirin kadai ke kuma na baki yarinya Alfila ne zaki sami wadannan sirrikan tsafi guda dari idan kuka samesu kuwa sai kinfi kowa arziki da daukaka a duniya shin kin manta ne cewa nima matsayin da nake nema kenan? Ai so nake nafi dukkan sarakunan duniya dukiya mata da daukaka ya kasance ana kirana da suna SARKIN SARAKAI Hakika ba zan taba samun wannan matsayi ba face na auri wadannan yan mata uku kamar yadda boka hadimul Asur ya yi mini bayani ke yanzu na san so kike nayi miki wahalar banza ki samu abinda kike nema kin taimakeni a cikin gidan sarautar sarki barusa na sami nasarar dauko gatarin sihiri nima na ceci rayuwarki dana daukoki daga can domin inda na baroki a can din sarki barusa ya farfado ya ganki da tuni kin zama gawa guyson naci gaba da cewa ina mai shawartarki da mu rabu anan ki tafi can wani bangare daban na duniya kici gaba da bina har mu dauko yarinya Alfila ki iya rabani da ita muje zuwa mahaukaci ya hau kura' ai wanda baiji bari ba shine yake jin hoho !!! Sa adda sarki uban sadaukai sarki sahibul hairi yazo nan a zancensa sai hankalin gimbiya shukura ya dugunzuma nan take idanunta suka ciko da kwalla taji gaba daya ta tsani kanta kuma ta tsani rayuwar duniya gaba daya domin ta fuskanci cewa zatayi biyu babu ma ana bata ga tsuntsu kuma bata ga tarko... !!!!!!! . SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI SAMI NASARAR SHIGA CIKIN GIDAN BOKA SHAMZUBUL AZWAS HAR YA DAUKO YARINYA ALFILA?? . YAUSHE NE SAHIBUL HAIRI ZAI HADU DA SADAUKI AWAISU?? . SHIN IDAN SUN HADU SADAUKI AWAISU ZAI YARDA SU TAFI NEMAN YAN MATAN UKU? . SHIN SU WAZIRI AKIYANU ZASU SAMI NASARAR SATO WANNAN DOKI NA SARKI AMINUL HAS SU KAIWA BOKA SHUBURUL UZUB? . IDAN SUN KAI MASA DOKIN ZAI CIKA ALKAWARIN YAGAYA MUSU HANYAR DA ZASU BI SU SAMI NASARAR HALLAKA AMINUL HAS? . YAUSHE NE BURIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI CIKA YA ZAMA SARKIN SARAKAI? . SHIN SARKI AMINUL HAS DA MATARSA SHULAIBA ZASU SAMI IKON YIN KWANA SITTIN AKAN GADON SARAUTAR BIRNIN MISRA DON SU SAMI HAIHUWA? SARKIN SARAKAI Littafina Uku 3 complet Na Abdulaziz Sani madakin gini Typing by Al'amin Ahmed misau Post And Ebook creator by Shuraih Usman 99% You can download more Hausaebooks at http://shuraih.waphall.com LOKACIN DA SARKI SAHIBUL HAIRI YA GAMAwannan jawabi ga gimbiya Shukura, sai kawai ya dauki Bawa Haluf ya daurashi a bayan aljani Dabarus din ya zauna yana rike da gatarinsa da wannan garkuwa. Take ya yiwa aljani Dabarus umarni da ya tashi sama da su. Cikin alamun tsoro aljani Dabarusa ya dubi sarki Sahibul Hairi sannan ya dubi gimbiya Shukura ya sake duban sarki Sahibul Hairi ya ce, "ya shugabana yanzu ayi haka kuwa? Ai bai kamata mu bar gimbiya anan ba. Ka tuna fa cewa in ba don itaba da baka sami nasarar dauko wannan Gatarin ba." Sarki Sahibul Hairi ya dakawa Dabarus tsawa ya ce, "maza ka bi umarnina ko kuma yanzun nan mu gwabza ni da kai". Koda jin haka sai Dabarus yai sauri ya bude fuka-fukansa yai sama jikinsa na kyarma. Ita ko gimbiya Shukura wadda ke zaune a kas dirshan, sai ta daga kai sama ta bisu da kallo kawai cikin alamun takaici da nadama har hawaye na zuba a idanunta. Al'amarin da ya sa sarki Sahibul Hairi yaji ya kamu da matsainaicin tausayinta ke nan. Amma da ya tuna irin cin amanar da ta yiwa mijinta sarki Barusa, sai ya tsaneta fiye da komai a duniya. Har ya aiyana a ransa cewa hakika mata abin tsoro ne, kuma abin shakka ga duk da namiji komai karfin mulkinsa. Haka dai Gimbiya shukura ta ci gaba da kallon su sarki Sahibul Hairi suma suna kallonta har suka kule a cikin sararin samaniya suka daina ganin juna. Bayan bacewarsu da kimanin dakika dari da ashirin, sai gimbiya shukura ta tuntsure da dariyar farin ciki ta ce, "ai idan ka san wata baka san wata ba. Zamu hadu ne a can gidan Boka shamzabul Azwas tsakanin ni da kai da Barusa na ga wanda zai mallaki Alfila". Koda gama wannan jawabi sai gimbiya shukura ta yi girgiza, take ta rikida ta zama farin hayaki, shi kuwa hayakin sai yai sama ya bace bat a cikin gajimare. Al'amarin sarki Sahibul hairi Bawa Haluf kuwa,lokacin da suka ci gaba da tafiya bisa aljani Dabarus a can kokolowar sama, sai da suka shafe rabin sa'a dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi ya ga ya yi jugum al'amarin da ya shiga tunani mai zurfi. Cikin biyayya Haluf yai gyaran murya sannan ya ce, "ya shugabana, kai kuwa tunanin mai kake yi haka. Shin kana nazarin gagarumin aikin da ke gabanka ne ko kuwa kana tuno irin wahalar da ka sha a bayane?". Koda jin wadannan tambayoyi sai sarki Sahibul Hairi ya yi murmushi ya ce, "ya kai Bawa Haluf, kayi sani cewa bana tunani bisa duk abubuwa biyu da kake zato. Abin da na ke tunani shi ne gida. Hakika ina cikin fargaba, zullumi bisa halin da Aminul Has zai shiga bisa jagorancin da bashi na rike min kasata kafin na dawo. Na san halin su waziri Akiyanu, su a tunaninsu wannan tafiya da na yi na tattare da mugun hadari, dom haka suna ganin cewa ba zan taba komawa gida a raye ba. Bisa wannan tunani dole na su yi shawarar kawar da Amirul Has gada kan karagar mulkin zalunci. Babu mamaki ma a ahalin yanzu tuni sun kawar da shi kuma sun fara azabtar da jama'ata." Lokacin da sarki Sahibul Hairi ya zo nan a zancensa sai jikin Bawa Haluf ya yi sanyi, kuma shima hankalinsa ya dugunzuma, ya ce, "ya shugabana hakika abin da kake zargi zai iya faruwa. Amma me zai hana ka bincka mana a cikin madubin tsafika don mu ga zahiri?". Sarki Sahibul Hairi ya gyada kai ya ce "tun da muka baro gida ka ga na duba madubin tsafina ko sau daya?". Bawa Haluf ya ce, "A a ban taba gani ba". Sarki Sahibul Hairi ya ce, "ni a tsarin rayuwata in nai gaba bana baya koda kuwa zan hadu da ajalina a gabana. A rayuwata ban taba sa bukata a gabana ta gagareni ba. Ao idan na ga abin da ya faru a madubin tsafina zuciyata za ta iya karaya nayi tunanin komawa da baya. Bisa wannan dalili ne na ki duba madubin tsafi. Ina mai tabbatar maka da cewa ba zan taba waiwayan gida ba face na mallaki abin da na fito nema. Idan kuwa ban sami biyan bukat ba, to har abada ba zan koma gida ba sai dai ajalina ya riskeni a wani wuri daban". Gama fadin hakan ke da wuya sai aljani Dabarus ya sauka kasa yana shirin dira bisa turba. Cikin fishi sarki Sahibul Hairi ya daka masa tsawa ya ce, "kai kuma wane ne ya yi maka umarnin saukowa kasa?". Koda jin wannan tambaya sai jikin aljani Dabarus ya kama kyarma, ya ce, "ka yafeni ya shugabana, ai ba laifina bane. Dubi gabanmu da kyau, ina kyutata zato mun fada tarkon wasu manyan bokayen ne". Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka leko kasa da sauri, sai suka ga tarin wadansu mutane a cikin wani kayataccen birni a tsatsaye cikin shigar kamala, mazansu da matansu, yara da manya sun daga kawunansu sama suna kallon aljani Dabarus. Wani dattijon mutun mai dogon farin gemu, kuma roke da sanda sanye da fariren tufafi na tsaye a gaban dukkan jama'ar, yana rike da wata goguwar cazbaha yana ta motsa bakinsa. Ga dukkan alamu yana karanta wadansu kalmomi ne. Abin da ya daurewa sarki Sahibul Hairi kai shi ne, yadda aljani Dabarus ke ta kokarin kada fuka-fukansa domin ya yi sama ya ci gaba da tafiya amma ya kasa. Koda sarki Sahibul Hairi ya fuskanci abin da ke faruwa, sai ya dubi aljani Dabarus ya ce, "saki jikinka ka sauka kasn mu abin da wadannan mutane ke nufi damu. Tabbas sune suka hanamu ci gaba da tafiya". Take aljani Dabarus ya bi umarni ya sauko kasa a cikin kayataccen birnin. Ai kuwa yana sauka sai sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka kama kalle-kallen gine-ginen birnin suna masu al'ajabi domin basu taba ganin irinsa ba. Dattijon mutumin mai farin gemu ya taho ga su sarki Sahobul Hairi fuskarsa cike da murmushi ya ce, "ale marhabun da jarumi uban jarumai, sarki Sahibul Hairi na birnin Misra. Ina ui maka barka da zuwa birnin Hairin Nur! Sunana Imam Sadiku Ibni Harais. Ni ne shugaba a wannan birni, kuma gaba dayanmu mun kasance ma'abota addinin Musulumci. Ya kai wannan sarki, kayi sani cewa ubangijina ya yi mini nuni sa zuwanka a cikin mafarkina, kuma ya sanar da ni gaba dayan labarinka da duk abin da ka ke son ja cimma buri. In da ka ba da gaskiya da addinina da Ubangijina ya baka duk abin sa kake nema a saukake ba tare da ka ci gaba da shan wahalar da kake sha ba". Ya yin da sarki Sahibul Hairi yaji wannan batu, sai jikinsa ya yi sanyi, ai shiru ya rasa abin da zai fadi. Daga can sai ya gana da Bawa Haluf suka yia kus-kus, bayan nan sai ya dubi imam Sadik sai ya ce, "ina bukatar kabani lokaci, in yi shawara da zuciytz da kuma wannan dan uwan nawa." Imam sadik ya ce, "na baka kwana uku ka yanke shawara. Kuma ina tabbatar maka da cewa zamu baka masauki da kulawa mai kyau a tsawan wadannan kwana uku. Yanzu sai ku taho a kai ku izuwa masaukinku, amma ku baiwa wannan hadimin aljani naku shawara da kada ya kuskura ya taba daya daga cikin jama'ata, domin zai iya konewa kurmus ya zama toka. Koda jin haka sai Sarki Sahibul Hairi ya dubi aljani Dabarus ya yi shiru bai ce da shi komai ba. Shi kuwa aljani Dabarus ya sunkuyar da kai kasa ya sake rabewa a waje guda kamar dan almajiri cikin alamun tsoro tamkar ka ce kyat! Ya zura da gudu. Ba tare da bata lokaciba Imam sadik ya umarci wani hadimi da ya kai su sarki sahibul Hairi izuwa masukinsu. Nan take kuwa wannan hadimi ya wuce gaba suka bishi a baya har izuwa wani gida a gefan garin. Bayan sarki Sahibul Hairia da Bawa Haluf sun ci abinci sun huta, sai suka fara sabuwar hira inda sika shiga tattaunawa bisa wannan sabon al'amari da ya samesu na tsintar kansu a wannan birni na ma'abota addinin musulinci. Sarki Sahibul Hairi ya dubi Bawa Haluf yana cikin yanayin damuwa ya ce, "ya kai Hauf kai sani cewa hakika na tsorata da ak'amarin wadannan mutane, yanzu kai a tunaninka mene ne ya dace nayi? Shin zan yar da na karbi addinin nasu ne na duk abinda na fito nema a saukake kamar yadda suka fada kokuwa na yi kokari murabu lafiya mu ci gaba da tafiya harbukatarmu tabiya? No dai banda tabbacin cewa abin da suka fadi zai yiwu, amma na yi imani cewa da karfin jarumtaka da kuma juriyata komai rintsi komai tsanani sai na cimma burina". Ya yin da Sarki Sahibul Hairi ya zo nan a zancansa, sai Bawa Haluf ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "ya kai shugabana kayia sani cewa hakika muna cikin tsaka mai wuya, domin idan mula ce zamu bujirewa wadannan mutane zasu iya wargaza mana duk shirinmu ya zamana dul wahalar damuka sha a baya ta zama ta banza. Haka kuma ina tsoran kada mu saki reshe mufada kan ganye. Ko kuma muyi biyu babu, ni aganona abin da za ka yi shi ne ka raba kafa. Kana neman taimalon wadwnnan mutane bisa gagarumin aikin da ke gabanka na shiga gidan Boka Shamzabul Azwas don dakko yarinya Alfila, da kuma batun zuwa naiman Sadauko Awaisu, da wadannan 'yn mata

Chapter 8 of 19