Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana fafatawa da cikin garin haluf ya san irinsu sarki sahibul hairi basa faduwa da wuri sai dubunnan mazaje sun fadi abin tambayar a nan shine shin har yanzu ana nan ana fafatawar ko kuwa an gama? Haluf ya tuna cewa idan fa yace zai bi sahun maigidansa kuma aka gane cewa tafiyarsu daya shima sunansa gawa nan fa hankalinsaya kara dugunzuma musamman da ya tuna cewa shifa bakin fata ne duk inda ya shiga a cikin birnin Askandariyya ansan cewa shi bawa ne donhaka kamashi za ayi kawai acigaba da bautar dashi haluf na nan zaune cikin tunanin mafita kawai sai ya hango wadansu dakaru bisa dawakai kimanin su dari uku bisa dawakai a tafe suna kewaye wani keken doki cikin firgici bawa haluf ya mike tsaye zumbur jikinsa na karkarwa yana tunanin ya gudu ko ya tsaya shidai yasan cewa wancan ayari sun hangoshi don haka ma inyace zai gudu ai bashi da mafita don zasu iya kure masa gudu bisa wannan daliline haluf ya rungumi kaddara ya tsaya cak a waje daya yana jiran karasowar ayarin inyaso kome zai faru ya faru lokacinda ayarin ya iso daf da haluf sai sukaja tunga suka tsaya cak a gabansa kawai saiyaga an bude labulen keken dokin nan take wata kyakkyawar mace ta leko da fuskarta waje sukayi arba kallo daya haluf yayiwa matar yasan cewa mai sarautace saboda irin tufafin dake jikinta da kuma sarka, da awarwaron dake jikinta matar ta kurawa bawa haluf idanu tana mai murmushi a gareshi tace yakai wannan bakin fata yaya akayi kazo wannan gari namu kuma menene dalilin da yasa ka tsaya a nan baka shiga garin ba ka sani cewa a cikin birninmu gaba daya babu bakin fata koda guda daya kasancewar mijina ya tsaneku ni kuma a duniya babu abinda nake sha awa sama da na ajiye bawa baki ina kallonsa yana min hidima sa adda bawa haluf yaji wannan tambaya saiya risina cikin biyayya yace yake wannan ma abociyar kyau kiyi sani cewa a shirye nake na baki amsar tambayoyin da kikamin amma sai idan kin yi alkawari cewa zaki shigar dani cikin birninku a boye kuma cikin sirri ba tare da sarkinku ya sani ba kuma zaki boyeni har izuwa lokacinda zan kammala abinda ya kawoni kasarku yayin da taji wannan batu saita bushe da dariya tace karka damu duk zanyi maka yadda kake so yanzu saika sanar dani sunanka bawa haluf yayi murmushi yace sunana haluf ibn bilal' kyakkyawar ta maida masa da murmushi tace nikuma sunana gimbiya SHUKURA ni ce matar sarki barusa guda daya jal a duniya koda gama fadin haka saita kira shugaban dakarun dake jagorantar wannan tafiya wani zabgegen kato mai kirar sadaukai wai shi jamhas tace dashi yakai jamhas kasan bukatata wadda na dade a kan nemanta don cikar burin rayuwata wannan bakin bawa shine zai zamo sanadin cikar burina abinda nake so dakai shine ka sanar da gaba daya jama ar dake cikin wannan ayari namu cewa duk abinda suka gani ya faru a yanzu tsakanina da wannan bawa suyi shiru da bakinsu su bar komai a cikin sirri idan kuwa sirrina ya fasu gaba dayansu zasu zama gawa jamhas yayi murmushi yace an gama ya shugabata nan take yabi dakarun gaba daya ya sanar dasu sakon gimbiya sannan ya koma izuwa wajen barorinta mata suma ya sanar dasu sa adda ya komo ga gimbiya saita sake dubansa tace kuje da haluf izuwa keken dokin barorina mata ka umarcesu da suyi masa shiga irin tamu ta mata kuma su sa masa suturar mata koda haluf yaji haka sai hankalinsa ya tashi yace a ransa yanzu shi za a mayar mace aikuwa ba za a iya batar da kamanninsa ba koda anyi masa siffar mata mutum mai natsuwa da kula zai iya ganeshi har haluf yayi nufin yaki yarda da wannan sirri sai kuma ya hakura domin bashi da wani zabi wanda yafi yabi umarnin shukura ba tare da wani bata lokaci ba jamhas yakai haluf izuwa cikin keken dokin nan ya sanar dasu bukatar gimbiya nan take sukabi umarni suka kama aiki lokacinda barori mata suka kammala aikinsu sai suka dauko babban madubi suka sa a gaban haluf ya kalli kansa a ciki nanfa haluf ya cika da tsananin mamaki domin shi kansa bai gane kansa ba dukda kasancewarsa bakin fata saiya zamo farar fata kuma ya juye.. Please Ku dinga daurewa kuna comments ko kun fara gajiya da littafinne?????? DUK DA kasancewarsa bakin fata saiyaga ya zamo farar fata kuma ya juye zuwa kyakkyawar budurwa hatta gashin kansa anmaidashi dogo kuma baki sidik mai kyalli kirjinsa ya cika fam irin na mata ita kanta rigar da aka sanya masa irinta sarakaice abar a tsaya a kalla haluf ya dubi kansa da kyau sai yace a ransa lallai ashe inda mace aka yoni da na kasance daya daga cikin kyawawan duniya koda kuwa an barni a matsayin bakar fata koda aka kammala sauyawa haluf kamanni daga da namiji izuwa ya mace sai jamhas ya tafi dashi izuwa keken dokin gimbiye shukura tunkafin su karasa gareta ta zubo musu idanu tana murmushi gami da yiwa haluf wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya bisa dole ya tsargu cewa lallai wannan mace nada wata babbar manufa a kansa ba tare da ya bata lokaci ba gimbiya shukura ta umarci haluf daya shiga cikin keken dokinta haluf ya waiga gaba da baya yaga gaba daya jama ar ayarin shi suke kallo cikin tsananin mamaki kawai saiya shiga cikin keken dokin ya zauna a gefe daya suna fuskantar juna shida shukura koda isowarsu bakin kofa sai suka iske kofar a balle a kasa makera na ta aikin kokarin gyarata don mayar da ita inda take koda ganin haka sai gimbiya tabada umarnin a tsaya a gaban sarkin kofa A lokacin da sarkin kofa da wadansu sababbin abokan aikinsa suka risina ga gimbiya suna masu yi mata barka da zuwa gimbiya shukura ta dubi sarkin kofa tace menene kuma ya faru naga kofar birnin nan a balle shin giwace tayi mana wannan barnar? Sarkin kofa ya risina yace ranki ya dade ai wannan ba aikin giwa bane wani shahararren mayakine waishi sarki sahibul hairi yazo don ya rabamu da gatarin mu na sihiri yanzu haka ya zama gawa domin sarki ya jefashi cikin gidan masifa na karkashin kasa dake fada koda jin wannan batu sai hankalin bawa haluf ya tashi bai san sa adda gumi ya tsatstsafo masa ba nan da nan fuskarsa ta cika da alamomin tashin hankali yayinda gimbiya shukura ta dubi fuskar haluf ta lura da sabon yanayin daya shiga sai kawai tayi murmushi tayi umarnin aci gaba da tafiya nan take kuwa aka kara nausawa cikin birnin askandariyya lokacinda su gimbiya shukura suka iso fada sai suka iske an gama walimar da ake yi har sarki ya mike ya shiga gida jama a sun fara watsewa kowa na kama gabansa koda aka ga zuwan gimbiya sai aka rabe aka bata hanya kuma ana kwasar gaisuwa gaba daya dawakai suka iso wajen tsayuwarsu aka tsaida su sannan su gimbiya da bakuwarta suka fara gitowa daga cikin keken doki amma bakuwar tasha lullubi ba a iya gane ko wacece nan dai su gimbiya suka shige izuwa cikin gidan sarautar kuyanginta da barorinta na take mata baya su kuwa su jamhas sai suka watse koya ya tafi izuwa nasa gidan A ka ida duk sa adda gimbiya shukura tayi tafiya ta dawo saita aikawa da sarki cewar ta dawo yana jin haka zai tako da kafarsa yazo har turakarta su zauna ta bashi labarin abubuwan da suka faru yayin tafiyarta da dawowarta in banda irin wannan lokaci sarki barusa baya zuwa bangaren gimbiya shukura A wannan karon kuwa sai al amarin ya sauya domin tana shiga cikin turakarta bata zauna hutawa ba sai kawai ta tafi izuwa bangaren da kanta amma kafin ta tafi ta umarci kuyangi dasu yiwa bawa haluf wanka su cire masa tufafin da aka sa masa na mata a takaice dai adawo masa da siffarsa ta dai dai kamar yadda yake a matsayinsa na da namiji sarki barusa ya kishingide a cikin turakarsa cikin nishadi yana hutawa kawai sai yaga gimbiya shukura ta taho gareshi cikin tsananin mamaki ya mike tsaye ya tareta cikin tsananin farin ciki suna annashawa gaba dayansu A duniya babu abinda sarki barusa keso sama da gimbiya shukura don haka ko kadan baya son abinda zai bata mata rai komai kankantarsa sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin murmushi yace yake abarkaunata yau kuma menene dalilinda ta hanaki turo a sanar dani dawowarki domin na taho turakarki mu zauna kamar yadda muka saba? Koda jin wannan tambaya saita maida masa martanin murmushin tace yakai rabin raina rabin jikina kayi sani cewa ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsabar farin ciki domin wannan karon nazo ma ka da labari mai dadi ka sani cewa a wannan tafiya da nayi na ziyarci wani mashahurin boka wanda ya bani magani yace indai na sha wannan magani lallai zan samu ciki dakai na haihu a cikin shekara guda koda barusa yaji haka saiya cika da farin ciki ya sake kankame shukura a kirjinsa yana dariyar murna yau shekara goma sha biyar kenan da yin auran gmbiya shukura da sarki barusa amma basu taba samun haihuwa ba bayan shekara daya da yin auransu sukaga basu samu juna biyu ba sai hankalinsu ya dugunzuma suka bazama neman magani amma ba a dace ba saboda ganin yadda barusa ya damu matuka da neman haihuwa saita bashi shawarar ya sake yin wani auren ya gani domin babu mamaki matsalar daga gareta ne da farko da barusa yaki yarda da wannan shawara sbd sonda yake mata amma data matsa saiya amince saida sarki barusa ya auri mata goma sha daya lokaci guda amma da aka shekara yaga babu haihuwa duk ya koresu ya rungumi kaddara 017. SARKIN SARAKAI BOOK1 . TUN daga wannan rana shukura ta cigaba da yin tafiye tafiye izuwa kasa kasa da ziyarar manyan bokayen duniya akan neman masalaha ranar da taje wajen wani mashahurin boka waishi KUMATU saiya yi bincike ya gano cewa matsalar haihuwarna tare da sarki barusa har abada bazai taba haihuwa ba ita kuma gimbiya shukura bazaata taba samun juna biyu ba face ta kwanta da namiji saurayi wanda shekarunsa basu kai talatinba wanda bai taba tarawa da ya mace ba kuma doleneya kasance bakin fata lokacinda gimbiya shukura taji wannan batu saita kamu da tsananin bakin ciki ta fashe da kuka saida ta dade tana kuka sannan tayi shiru ta dago kai tana mai duban boka kumatu hawaye na zuba a idonta.yace yakai wannan boka ina sonka sanar dani yadda zan gane saurayi mai wadannan suffofi duk sa ar da na hadu dashi boka kumatu yace duk ranar da kika hadu da wannan saurayi kina yin arba dashi zakiji ya kwanta miki a rai ma ana nan take zakiji sonsa to lallai in kikaji haka sine kadai saurayinda zaki tara dashi ki samu haihuwa in kuwa ba hakaba harki mutu ba ke ba samun da gimbiya shukura bata da wani buri wanda yafi ta haifi danda zai gaji mijinta wato sarki barusa domin ta san cewa duk ranar da sarki barusa ya fadi ya mutu dolene ta bar gidan sarautar domin wanine daban daga cikin fadawansa zai karbi mulkin bayan gimbiya shukura da sarki barusa sun gama murnar wanann labari datazo dashi sai tayi masa sallama akan cewa zata tafi dakinta ta kwanta domin ta huta gajiyar tafiya ba tare da gardamar komaiba yayi mata izinin tafiya, lokacinda gimbiya shukura ta iso cikin falon turakarta ta iske bawa haluf a zaune an caba masa ado kyawunsa yakara baiyana kururu a baiyane saita kamu da matukar sha awarsa kai tsaye ta nufo inda yake da zuwa saita yunkura da nufin ta rungumeshi cikin tsananin tsoro ya zame jikinsa ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya dubeta cikin biyayya yace haba ya shugabata shin kin mantane cewar ke matar sarki ce sokike a tsireni idan aka kamani da laifin yin wani abu dake? Sa adda taji wannan batu saita kyalkyale da dariya sannan tace yakai wannan ma abocin kyau da kwarjini ka saki jikinka ka sani cewa duk abinda zamuyi a nan babu mai ganinmu yanzu dai kafin wani abu ya wakana a tsakaninmu ina son ka amsa min tambayoyin nan guda biyu da nayi maka tun farkon haduwarmu' kodajin haka sai haluf ya kirkiri karya ya shara mata yace ai shi bawane ya gudo daga hannun ubangidansa da ga can wata kasa da ake kira SHUBUR kuma ba komai bane ya sa ya gudo ba sai don tsananin aikin wahalar da ake sa shiyi kullum lokacinda ya gama wannan jawabi sai gimbiya shukura ta dubeshi ta kyallkyale da dariya tace haba dan samari ka dubeni da kyau kai kasan cewa ni ba yarinya bace karama kuma ina da kaifin tunani da lura ai fatar jikinta mutum ya duba ya san cewa a dduk inda kake baka shan waahala tun da dai ba zaka gaya min gaskiya ba ni yanzu zan sanar dakai ko kai waye . Yakai haluf ka sani cewa tundazu da muka dawo gida kafin naje ga mijina saida na shiga cikin wani daki na na sihiri inda nake tafiyar da harkokin sihirina yi bincikena na gano cewa kazo wannan birni namu ne tare da maigidanka sarki sahibul hairi na birnin misra domin ya rabamu da gatarinmu na sihiri sbd da wannan gatari ne kadai zai iya balle kofar gidan boka SHAMZUBUL AZWAS wanda ke can tsuburin tekun bahar zallus domin ya dauko karamar yarinya Alfila wadda ta kasance yace ga wani gagarumin sadauki waishi Awaisu yakai haluf kayi sani cewa nima na dade ina neman wannan yarinya alfila na rasa yadda zanyi na sameta saboda na kwashe sirrikan tsafin dake jikinta na dawo dasu jikina don cika burina na biyu a duniya burina na farko shine na haifi da wanda zai gaji sarautar birnin Askandariyya bincike ya nuna mini cewa kaine kadai namijin da zan kwanta dashi na samu haihuwa don haka ina bukatar hadin kanka ayanzu sa adda shukura tazo nan a zancenta saitaga hawaye na zuba a idanun bawa haluf al amarinda ya matukar bata mamaki kenan ta dubeshi tace kai kuwa menene dalilin zubarda wannan hawaye a idanunka? Haluf yace aini yanzu bani da sauran buri a duniya face mutuwa tunda babban masoyina mutumin da nafi shakuwa dashi fiye da kowa babu shi wato sahibul hairi naji dazu sarkin kofa yana bayanin cewa an jefa shi cikin dakin masifa na karkashin kasa ya hallaka bisa wannan dalili nake ganin cewa rayuwata bata da sauran amfani don haka kashe kaina zanyi koda gama fadin haka sai bawa haluf ya sa hannu cikin rigarsa ya dauko wata zuka ya daga sama da nufin ya caka a cikinsa aman sai gimbiya shukura tadubi hannunsa da kwayar idanta take wata irin iska mai karfi ta rike hannun haluf ya kasa cakawa kawai saiji yayi an fisge waukar daga hannunsa anyi jifa da ita can gefe cikin tsananin firgici da mamaki haluf ya zauna kasa dirshan yana mai kallon gimbiya shukura ita kuwa saitayi murmushi ta tako kafafunta tazo daf dashi ta tsugunna suka fuskanci juna tace GIMBIYA SHUKURA tacigaba da cewa aibazan bari ka mutu ba face na cika burina dakai ka kwantar da hankalinka ka sani cewa maigidanka sarki sahibul hairii na nan a raye bai mutuba. Yanzun nan zan nuna maka zahiri ka gani, gama fadin haka keda wuya saitayi nuni da dan yatsanta guda izuwa jikin bango take wani irin haske ya fito daga cikin dan yatsanta ya dira a jikin bangon saiga hoton sahibul hairi kwance a sume cikin dakin nan na maridai a tsakiyar gawarwakin maridan A lokacinne ya farfado daga dogon suman da yayi ya mike ya zauna da kyar yana ta faman haki kamar zai mutu. Ko ina a jikinsa rauni ne yai kaca kaca da jini gimbiya shukura ta dubi bawa haluf tace kaga halin da maigidanka ke ciki akwai dakuna goma sha biyu kowanne dakina dauke da masifa iri iri masifunda suke dakunan gaba sun ninka na baya yanzu ya wuce dakuna biyu saura goma a gabansa. Idan har ya wuce ta cikin ragowar dakunan goma yana raye yaci jarrabawata, donhaka zan taimaka masa mu sace gatarin sihiri tare mu tafi izuwa gidan boka shamzubul Azwas dan dauko yarinya Alfila. Abinda nake soka gane shine zamu hada karfi da karfe ne domin nida shi kowa ya biya bukatarsa amma duk wannan zata farune idan ka bani hadin kai ka sadu dani yanzu' 'lokacinda haluf yaji wannan batu sai hankalinsa ya tashi fiye da ko yaushe ya rasa abinda zaice kawai saiya kurawa gimbiya shukura idanu yana mai al ajabin al amarinta . Wannan shine abinda ya faru tsakanin gimbiya shukura da bawa haluf bayan ta sa an sauya masa kamanni an shigar dashi ckin birnin askandariyya ba tareda sanin sarki barusaba ++ ++ Al'amarin jarumi uban jarumai kuwa wato sahibul hairi lokacinda ya farfado daga suman da yayi ya tsinci kansa cikin tsakiyar gawarwakin maridannan guda dubu yaga har yanzu gashi yana numfashi bai mutuba sai ya cika da mamaki kuma ya shiga tunanin zuci yace a ransa. '' wannan fa shine mataki na fardo da zanbi don biyan burina Amma gashi bani da tabbacin zan kai gaci yaushene zan samu nasarar daukar gatarin sihiri a cikin wannan gidan sarautar sannan na tafi gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya alfila na tabbata cewa masifar dake can fadar boka shamzubul azwas ta ninka wacce ke nan sau dubu idan ma na sami nasarar dauko Alfila yay tafiyarmu zata kasance nida sadauki Awaisu don neman wadannan 'yan matan uku wadanda zan Aura na cika burina na duniya. Shin zamu sami nasarar ganin yan matan kuwa Alhalin babu wanda yasan a inda suke? Koda sarki sahibul hairi yazonan a tunaninsa sai yaji nadama tazo masa bisa gagarumin aikin daya daukowa kansa nan take zuciyarsa ta karaya ya fara aiyanawa a ransa cewa lallai a cikin wannan tafarki zai rasa rayuwarsa, gwarama ace ya rungumi kaddara ya zauna da talaucinsa har ajalinsa ya riskeshi... ¤+++++++¤ SHIN BAWA HALUF ZAI AMINCE YA BIYAWA GIMBIYA SHUKURA BUKATARTA? . SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI IYA SHALLAKE MASIFUN DAKE CIKIN RAGOWAR WADANNAN DAKUNA GUDA GOMA? . INA LABARIN GALADIMA AMINUL HAS WANDA SARKI SAHIBUL HAIRI YABAR MASA RIKON KASA, KUMA YA KASANCE A CIKIN TASHIN HANKALIN MAHASSADA . marubucin yace mu hadu a SARKIN SARAKAI kashi na biyu donjin ci gaban wannan kasaitaccen labari. anan Nake cewa mu hadu a cikin littafi na biyu domin jin yadda zata kasance a wannan kasaitaccen labari na ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KANO. SARKIN SARAKAI Littafi na biyu 2 Abdulaziz Sani m gini Shuraih Usman A.KA 99% Daga:- www.hausaebooks.cf http://keffiansonline.cf . BAYAN SARKI sahibul hairi ya sami karayar zuci bisa burin dake gabansa na zama sarkin sarakai a cikin dakin maridai saiya sake bajewa a kasa yana mai cigaba da tunanin rayuwar daya tsinci kansa a ciki. Sahibul hairi ya tuno da irin bakaken maganganun da sauran sarakuna abokansa suke aiko masa dasu gamida habaici da gori akan cewa' ya talauce bashi da cin yau bare na gobe kuma bashi da lafiya tunda ya kasa aure. Ya sake tunowa da yadda ya baro kasarsa bayan ya baiyana sirrin abinda ya fito nema kuma kowa ya sani haka kuma ya tuno da irin wahalar da ya sha a cikin wadannan dakuna biyu dake karkashin kasa a cikin masarautar sarki barusa koda yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa nan take yaji wani irin kwarin gwiwa ya shigeshi dukkan tsoro da fargaba suka yaye daga cikin zuciyarsa kawai saiya mike tsaye ya tunkari kofar da zata shigar dashi izuwa daki na uku. Cikin zafin nama ya banke kofar da karfin tsiya take kofar ta rufta ciki ta fadi kasa koda yayi arba da abindake cikin dakin saiya kame tamkar gunki saboda tsananin firgita ba wani abu bane sarki sahibul hairi yayi arba dashi a cikin wannan daki na uku ba face wata murtukekiyar macijiya mai kawuna dari da daya idan macijiyar ta bude bakunanta duka babu abinda mutum ke gani a ciki face kibiyoyin wuta haka kuma a cikin kowanne baki akwai wani irin zarkalelen harshe mai tsananin karfi tamkar zabira kowanne kai guda daya na macijiyar yakai kamu dari haka shima wannan haske dake cikin bakin. Sa adda macijiyar mai kawuna dari da dayataga sahibul hairi ya kame a gabanta tamkar gunki sai itama ta tsaya cak tana kallonsa kawai jira take yayi kyakkyawan motsi ta kaddamar dashi tsawon dakiku sittin dayansu bai motsa ba sarki sahibul hairi ya san cewa bai isa ya koma da baya ba haka kuma bai isa ya wuce gaba ba don haka ya tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA domin gabansa tsinine bayansa kuma siyaki daga can sai wata zuciyar tace dashi'' Kai jarumi uban jarumai ita fa masifa kafin tazo ne ake gudunta amma idan ta riga tazo saidai a rungumeta ayi daya daga cikin biyu wato ko kai ko ita' koda gama wannan tunani sai sahibul hairi yayi kukan kura ya afkawa macijiyar da nufin ya dankara mata sara nan take ta mako masa kanta guda ya makashi da jikin bango saboda karfin dukan saida bangon dakin ya burma ya fitar da shatar gaba daya surar jikinsa ya manne a cikin ginin tsananin zafi da zugin da yaji kuwa sai da jiri ya debeshi yaga taurarin wuya a idonsa koda macijiyar taga ya manne a cikin garu saita jefa jelarta a karo na biyu ta fincikoshi da karfin tsiya sannan ta fara kanannade shi saita matse shita ragargaza kasusuwan jikinsa. Tun a farkon lokacinda macijiyar ta fara kanannadeshi sai yaji ya matsu ainun tamkar an daureshi da sarkar karfe murtukekiya nan fa hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da cewa idan fa macijiyar nan ta gama kanannade shi mutuwa zaiyi don kashin dake jikinsa saiya karye hakika wata masifar na iya sa mutum ya yi abinda bai taba tsammanin cewa zai iya ba a dai dai lokacinda macijiyar ke daf da gama kanannade wuyan sahibul hairi ne kawai saiya takarkare iya karfinsa ya buda jikin macijiyar da karfin tsiya a wannan lokaci inda mutum na nan yaga yanda kwanjin sahibul hairi ya ciko da yadda jijiyoyin jikinsa suka tattashi sukayi burdin burdin sai yayi tsammanin cewa jikin dutse gareshi karfin buda jikin macijiyar ne yasa macijiyar taji kamar za a yagata ba shiri ta warware jikinta daga nasa ta sake shi amma kafin yayi wani yunkuri ta bude bakunanta duk ta fara watso masa kibiyoyin wuta bisa mamaki sai yaga duk kibiyar data sauka a jikinsa saita kasa hudashi ta fadi kasa kawai abinda bai sani ba shine wannan naman zakin da yaci a wancan dakin na farko shine ya bashi wannan kariya amma ba karfin sihirinsa ba lokacinda macijiyar taga cewa kibiyoyinta na wuta sun kasa yin tasiri a kan sahibul hairi saita kara fito da harsunanta guda dari da daya duka ta watso masa su da nufin ta daddatsashi gunduwa gunduwa duk harshein da ya bugi jikinsa sai kaji kal kamar karfe da karfe ne suka hadu amma ko kwarzane jikinsa baiyi ba nan fa aka ci gaba da masifaffen fada ya zamana cewa macijiyar na dukan jikin sahibul hairi da harsunanta shi kuma yana saran harsunan da takobin hannunsa sai da aka shafe sa'a guda ana wannan artabu amma dayansu bai sami nasara ba da kanta macijiyar taja da baya ta tsaya cak aka ci gaba da kallon kallo ita tana huci shikuma yana haki hakika wannan macijiyar tasan cewa yau ta hadu da iblishin bil adama domin a tarihin rayuwarta tunda aka ajiyeta acikin wannan daki fiye da shekaru talatin baya ko mutum dubu aka watso mata a cikin dakika guda take hallaka su gaba daya amma yau ga bil adama daya kwal ya gagareta lokaci guda suka sake afkowa juna wannan karon dai kokarin da macijiyar takeyi shine ta hadiye sarki sahibul hairi da daya daga cikin kawunan nata koda ya fuskanci manufarta saiyayi ta zulle da gocewa yana kai mata duka hannu da kafa gami da kai mata sara....... Yauba yawa amma Ku Tara gobe idan Allah yakaimu Koda sarki sahibul hairi ya fuskanci manufar wannan macijiyar sai yayi ta zulle da goce goce yana kaimata duka da hannu da kafa gami da kai ma ta sara ita kuwa ta dinga fyada masa jelarta kafin wani lokaci duk su biyun sunji jiki haka dai aka cigaba da wannan gumurzun har izuwa tsawon wata sa'a gudan Ana cikin hakane sarki sahibul hairi ya shammaci macijiyar nan ya soki idonta guda da tsinin takobinsa faruwar hakan keda wuya sai ruwan idon ya fashe yace tus! Kamar an fasa kwan jimina saiko ruwan jini yata kwarara tamkar teku ta balle ammam saboda naci saida macijiyar taci gaba da kokarin hadiye shi Abinda sahibul hairi ya lura dashi shine kanda wannan ido ke jiki bashi da kuzari kamar sauran kawunan koda ya lura da haka sai yaci gaba da fas a sauran kawunan na jikin sauran kawunan dama a jikin kowanne kan idanuwa biyune idan sarki sahibul hairi ya sami nasarar fasa idanuwa biyu saikaga wannan kai ya daina tasiri ya fadi kasa ya jabe tamkar jikakken tsumma yayinda sarki sahibul hairi yaga ya samo lagon macijiyar saiyaci gaba da fasa mata idanu har saida yafasa gaba daya idanun nan take macijiyar ta baje kasa matacciya jini kuwa ya rinka fita a jikinta saida ya kusan shanye sahibul hairi yazo masa iya kirji kaikace a cikin kogi aka tsomashi A sannanne shima ya langabe a jikin garu ya kama nishin gajiya koda ya dubi jikinsa sai yaga ko ina yai burdin burdin wato jini ya taru masa sakamakon dukan da macijiyar nan ta ringa yi masa tana fyada shi da kasa da kawunanta da jelarta saida sarki sahibul hairi ya kwana ya yini yana jinyar jikinsa a cikin wannan daki na muguwar macijiyar sannan ya sami kwarin jikinsa naman macijiyar ne ya zamo abincinsa a iya tsawon wannan lokaci bayan ya dawo cikin hayyacinsa sosai kuma ya gama jinyar jikinsa sai ya tunkari kofa ta gaba wato daki na hudu kamar yadda ya banke kofa ta uku haka ya banke kofa ta hudu kawai ya kunna kai ciki shi dai wannan daki na hudu ya sha ban ban da sauran dakunan uku da ya wuce domin shi ya kasance mai tsananin tsawo da babu alamar karshe sannan kuma babu wada taccen haske a cikinsa daga shigar sahibul hairi cikin wannan daki sai ya dinga jiyo wani irin gurnani mai ban tsoro irin wanda bai taba ji ba a rayuwarsa koda jin wannan gurnani sai sarki sahibul hairi ya tsaya chak yana waige waige da nazarin gurnanin kawai sai sahibul hairi ya daga takobinsa sama ya riketa da hannu biyu yaci gaba da tafiya abinsa a hankali yana mai ci gaba da waige waige da dube dubensa kwatsam sai ya tsinci kansa a tsakiyar wani makeken fili wanda bashi da duhu ko kadan kuma babu alamar wata kofa da za a fita isowarsa wannan

Chapter 4 of 19