Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daji na kwana nan na tashi can sannan na koma gida wato birnin misra. Sa adda sarki sahibul hairi yazo nan a labarinsa tuni sun gama cinye abincin dake gabansu haluf ya jinjina kai yace hakika ya shugabana ka cika jarumi uban jarumai ina ba don wasu dalilai ba da sainace idan akwai irinka goma a birnin misra da munci duniya da yaki. Koda jin haka sai sarki ya bushe da dariya ba tare da yace komaiba ya mike ya fita wajen tantin koda ganin haka sai bawa haluf ya mike da sauri ya harhada kayansu gaba daya sannan suka hau ababan hawansu suka nausa daji. Kamar yadda sarki sahibul hairi ya fada haka lamarin yakasance wato basu isa birnin askandariyya ba sai kwana talatin da bakwai har suka isa can din kuwa basu sake haduwa da yan fashi ba saidai muggan dabbobin dawa wadanda nan take sarki sahibul hairi keyi musu kisan farat daya. Lokacinda suka iso kofar birnin Askandariyya dare yayi tsaka har bawa haluf ya nufi kofar birnin da nufin yaje ya kwankwasa a bude masa sai sarki ya dakatar dashi yace saurara yakai haluf aini kadai zan shiga cikin birnin nan kuma indai na shiga ba zan tsaya ko ina ba har saina dangana da fadar sarki barusa naje har inda aka ajiye gatarin nan na lu'u lu'u na daukoshi ka sani yaki da daddare na matsoraci ne lallai gobe da safe ido na ganin ido zan shiga cikin wannan birni na nufi gidan sarautar gadan gadan duk wanda ya tsaya a gabana sai dai gawarsa abinda nake so dakai mu kwana nan kofar gari kuma idan gari ya waye ka jirani a nan har naje na dawo bayan cikar burina idan kuwa kayi kuskure ka biyoni lallai zaka rasa rayuwarka. Koda gama wannan jawabi sai bawa haluf ya sauko daga kan dokinsa sannan yarike taguwar sarki shima ya sauka cikin hanzari ya daure ababan hawansu a jikin wani dutse ya kafa musu tanti suka shiga ciki suka kwanta suka kama aikin rago. Da Asubar fari sarki ya farka daga barci koda bude idansa yaga bawa haluf yanata barci har da munshari saiya mike ya kama yin damarar yaki ya kwaso makamansa ya shiryasu a jikinsa da ya gama wannan shiri sai ya rufe fuskarsa da wani rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake iya gani ba tare da ya tashi bawa haluf daga barci ba sai ya fita daga tantin yaje ya kwance taguwarsa ya haye kanta ya durfafi kofar birnin Askandariyya a lokacinda gari ya waye sosai rana ta fito. Koda ya iso daf da kofar birnin wacce akayita da bakin karfe sai yaja dunga ba tare da ya sauko daga kan taguwar ba ya zare takobinsa ya kwankwasa kofar da ita faruwar hakankeda wuya sai yaji an tambayeshi da kakkausar murya wanene nan yake kwankwasa mana kofa da sassafe haka? Hala kai bakone baka san ka'idar shigowa birnin mu ba. . 011. SARKIN SARAKAI BOOK1 . Koda budar bakin sarki sahibul hairi sai yace Ubankane yake kwankwasa kofar tun muna shaida juna ka bude kofar nan in kuwa ka kuskura na banke kofar na shigo sai mataccen dake kabari yafika kwanciyar hankali maimakon abi umarni a bude kofar sai aka kyalkyale da dariya Al amarinda ya fusata sarki kenan kawai ya sauko daga kan taguwar tasa yaja da baya kimanin taku Ashirin sannan ya rugo da gudu ya hada karfinsa gaba daya ya doki kofar garin da kwanjinsa take kofar ta fita fit! Shi da ita suka burma ciki kai kace giwace ta rugo ta bangaji kofar .wOHoHO nikain Cikin hanzari sarki sahibul hairi ya mike tsaye sai yayi arba da wani murjejen kato a gabansa katon sanye da suulken yaki kuma ga wani shafcecen gatari a hannunsa amma duk jikinsa karkarwa yake ya kurawa sarki sahibul hairi idanu kawai cikin firgici kamar ace kyat ya fita da gudu sbd razana shidai wannan kato ba kowa bane face sarkin kofa sahibul hairi ya dubi katon yace, kai kuma waye kuma me kake jira dani ba tare da ka afko mini ba tunda ga makami a hannunka' cikin murma mai rawa katon yace nine sarkin kofar birnin Askandariyya yau shekarata arba'in ina gadin wannan kofa amma a tsawon wadannan shekaru ban taba ganin sadaukin mutum tamkarka ba ka sani cewa an taba kokarin balle wannan kofa da karfin giwaye biyu amma abu ya faskara yau gashi kai bil adama kai daya ka banketa anya kuwa kaiba aljan bane? Idan kai mutum ne wanene kai kuma menene yazo dakai wannan birni namu' sarki sahibul hairi yace nine sarki sahibul hairi na birnin misa kuma nazo wannan birni nakune don biyan wata bukata tawa, kayi mini jagora izuwa fadar sarkinku inba haka ba kuwa yanzun nan zaka bakunci barzahu, lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai sarkin kofa yai ajiyar zuciya yace hakika biri yayi kama da mutum ni kam nasan cewa duk duniya babu wani sadauki da zai iya bangaje wannan kofa ta fadi face sarkin misra tuni labarinka yazo mana nan to amma ina mai shawartarka da ka janye duk irin bukatar dakazo da ita domin na tabbata cewa sarkinmu bazai yarda da ita ba na sani cewa kai jarumine uban jarumai amma kada ka manta cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi kodajin haka sai sarki sahibul hairi ya dakawa sarkin kofa tsawa yace ai ragon maza shike tsoron yawan maza kabi umarnina ko kuma na tabbatar da alkawarina akanka sarkin kofa yace nikam bazanbi umarninkaba saidai nabi na sarkina domin idan na saba masa masifarda zan shiga saina gwammace Ajalina kafin sarki yace wani abu tuni sarkin kofa ya zare wani kaho ya busa faruwar hakan keda wuya saiga dakaru suna ta bullowa a guje tako ina duk sun zare makamai ashe tun dazu ma a lallabe suke suna ganin abinda ke faruwa tsakaninsu lokacinda sarki ya balla kofar birnin saida karar kofar ta cika birnin gaba daya amma da yawan jama a basuyi tsammanin cewa kofar birnin bace wasuma sun zata fashewar dutsen wuta ne kafin sarki ya ankara tuni sama da mutum dari uku sun kewaye shi rike da makamai tsirara sahibul hairi ya dubesu yai murmushi kawai saiya yunkura da nufin ya ratsa ta cikinsu yai gaba aikuwa sai suka rufar masa gaba daya da nufinsu daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakaru sunsan abinda zai biyo baya da basuyi gangancin afkawa sarki sahibul hairi ba domin a cikin dakika dari da ashirin ya rugurguzasu tamkar an kwankwasa gilashi ya zamana cewa sarkin kofa ne kawai a tsaye kikam kamar gunki idanunsa sun zazzaro kamar zasu fado kasa gaba daya jikinsa rawa yake ya firgita fiye da dazu sa adda ya gaya balla kofar birnin ya fado ciki sahibul hairi ya dubi sarkin kofa yace maza ka gayawa sarkinku abinda ya faru yanzu kuma kace dashi idan ya bani abinda nazo nema zamu rabu lafiya idan kuma ya ki a yau dinnan zan baje wannan birni yadda ko a tarihi baza a tuna dakuba. Koda gama fadin haka sai sarkin kofa ya ruga inda dokinsa yake ya kwance ya haye sannan ya sukwaneshi izuwa cikin birnin Askandariyya shikuwa sarki sahibul hairi sai ya koma inda yabaro taguwarsa yahau sanna ya shigo cikin birnin ya kara gaba ++ A can fadar sarki barusa kuwa fadar ta cika makil da fadawa da talakawan gari domin a yaune sarki barusa ke walimar cikar shekaru talatin akan karagar mulki banda shagali babu abinda akeyi a fadar masu kida nayi masu rawa nayi abinci kuwa da abin shaye shaye gasu nan birjik babu adadi kowa abinda yake so shi yakeci kallo daya mutum zaiyiwa sarki barusa ya gane cewa a cikin tsananin farin ciki yake A wannan lokaci Barusa na zaune shirim kamar giwa a kan karagar mulki yanata kwankwadar giya sai rusa dariya yake yana kallon wadansu yan mata dake ta tikar rawa a gabansa yana annashawa. Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yanata faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kowa kuma ya kame kamar babu mai rai a wajen ++ . Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yana ta faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit kamar mutuwa ta gifta kowa ya kame kamar babu mai rai a wajen Da zuwan sarkin kofa saiya fadi gaban sarki yayi gaisuwa sannan yace ya shugabana kayi sani cewa yanzu haka jarumi uban jarumai ya shigo kasar nan ya banke kofar gari da karfin sadaukantakarsa kuma ya kashe dukkanin abokan aikina yana nan tafe izuwa nan fadarka don biyan wata bukata tasa ni kaina ya kyaleni ne kawai don nazo na isar da sako' cikin tsananin fushi sarki BARUSA ya dakawa sarkin fada tsawa wacce tasa dukkanin jamar wajan suka fadi kasa suka kwanta da ruf da ciki don tsananin razana sarki barusa ya kasance lafcecen katon mutum mai surar mutanen farko gashi dogo kuma gashi kakkaura duk jikinsa a murde yake ya tara jijiya da kwanji komai tsawon mutum sarki barusa na iya dora abinci a kansa yaci yana da jajayen idanuwa ababan tsoro yanada wawakeken hanci da katon baki a takaice dai idan ana batun muni to sarki BARUSA kurunkus ne! Sarki barusa ya nuna sarkin kofa da yatsa yace wai shin wanene jarumi uban jarumai harda ya isa ya banke kofar birnina ya kashe min dakaru har yace lallai sai ya shigo fadata bidar wani abu? Sarkin kofa yace Aiba wani fane face SARKI SAHIBUL HAIRI na birnin misra kodajin wannan batu sai sarki barusa ya mike tsaye ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ita kanta dariyar abar tsoroce domin zata iya firgita mai ciki tayi bari zata iya sa mutum gudawa kuma zata iya zamo sanadin yin hijirar dukkanin tsuntsayen daji bayan sarki barusa yai dariya ya gaji saiya koma kan kujerarsa ya zauna su kuwa fadawanda gaba daya sun tsure sun dimauce tunda sukaji ance sarki sahibul hairine yazo wazirin sarki barusa wanda ake kira YARKUS ya matso daf da sarki yace ranka ya dade yanzu menene abinyi? Ka sani cewa sarki sahibul hairi ya shahara fagen jarumtaka da samun nasarar yaki shinefa mutuminda ya gagari rumawa da hindu shine wanda ya shiga har birnin farisa ya sare kan sarkinsu kuma shine sarkinda ba a taba cin kasarsa da yaki ba sai sau daya a yakin da suka gwaza da rumawa amma dukda cewa an kashe gaba daya dakarunsa saura shi kadai saida yayi musu mummunar barna kuma ya tsira da rayuwarsa lokacinda waziri yarkus yazo nan a zancensa sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga can kuma ya murtuke fuskarsa yace ya kai yarkus kayi sani cewa baka fini sanin ko waye sahibul hairi ba na sanshi kamar yadda na san kaina abinda nake so daku shine kowa ya nutsu ya koma mazauninsa idan sahibul hairi ya shigo nan ya iskemu muna harkokinmu kamar yadda muke yi dazu tamkar labarinsa bai riskemu ba ina son naji abinda ya zo nema a kasata sannan na san hukuncin da zan dauka akansa koda gama fadin haka saigaba daya jama ar dake fadar suka dawo cikin hayyacinsu aka ci gaba da sharholiya tamkar babu abinda ya faru jim kadan da faruwar haka saiga sarki sahibul hairi bisa taguwarsa ya shigo da ita har cikin fadar babu abinda zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda ita kanta taguwar take tafiyar kasaita tamkar akan sahara shi kuwa sarki sahibul hairi na zaune a kanta cikin wannan shigata bakaken kaya fuskarsa arufe idanunsa kadai ake gani sbd tsabar kwarjinin sahibul hairi saida masu rawa da kida suka kasa cigaba da aikinsa fadawa da sauran jama ar gari kuwa saida kowa ya natsu ya kurawa sarki sahibul hairi idanu duk wanda ka duba saikaga bakinsa a bude tamkar shashasha. Taguwa taci gaba da tafiya har ta iso daf da karagar sarki barusa sannan ta tsaya cak aka fara kallon kallo a tsakanin sarakan biyu sarki barusa ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa dama tuniya kule saboda ganin jama arsa sun firgita da ganin sarki sahibul hairi. Tsawon yan dakiku fadar tayi shiru kamar ba mai rai a cikinta daga can sai sarki sahibul hairi ya risina kadan ga sarki barusa yace tsakanin sarki da sarki akwai girmamawa yakai mai birnin Askandariyya kayi sani cewa ban shigo kasarka da nufin cin zarafinka ba ko zalunci ba zan la anta kowa ba face wanda yaso la antani ina hadaka da girma da arziki ka bani abu guda daya rak na tafi dashi idan kayi haka nayi alkawarin ba zan cutar da ko kazar garinnan ba idan kuma kaki nayi alkawari saina karar da dukkanin dakarunka na biya bukatata koda kuwa a sanadin hakan zan baje gidajenku su zamo turbaya koda jin wannan batu sai sarki barusa ya bushe da dariya sannan ya hade fuska yace yakai mai birnin misra ka fadi abinda kake bukata daga gareni na baka domin ina da labarin cewa fatara da talauci sun isheka idan na abinci ne zan sa a baka wanda zakaci kaida jama arka na shekara goma idan kuma sutura ce kake so zan baka wacce zata kaika shekara arba in kana sawa kullum sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya murtuke fuskarsa yace ai ba bara nazo yi wajenka ba abinda nake bukata a wajenka ba komai bane face gatarin lu'u lu'u wanda kuke bautawa . 013. SARKIN SARAKAI BOOK1 . Koda jin wannan batu sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na hudu sannan ya mike tsaye ya dubi sahibul hairi cikin murmushi yace ai wannan abune mai sauki kabi waccen hanyar zaka isa dakin da gatarin yake saika dauko cikin salama kazo kayi tafiyarka' ba tare da tsayawa yin wani nazari ko tunani ba kawai sarki sahibul hairi yabi wannan hanya wadda sarki barusa ya nuna masa koda ya kusa isa wata kofa sai kasa ta dare ya rufta cikin wani dakin kasa mai tsananin zurfi yana fadawa sai kasar ta hade ta rufe ruf tamkar bata taba darewa ba sarki barusa ya tuntsure da dariya yace lallai wannan ya cika mahaukaci to inbanda mahaukaci wane ne abokin gabarsa zai nuna masa hanya yabi? Tabbas yakai kansa izuwa mahallakarsa sa adda sauran fadawa da jama ar gari sukaji haka sai suma suka kama kyalkyala dariya suna cewa tabbas sarki sahibul hairi ya cika mahaukaci WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR SARKI BARUSA ++ AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI kuwa lokacinda kasa ta dare ya fada kasanta sai yaji ya fadi cikin wani faffadan daki mai tsananin zurfi fadowarsa keda wuya yaji ana tayin wani irin gurnani mai ban tsoro kasancewar dakin akwai duhun gaske baiga abubuwanda ke gurnanin ba. Bazato ba tsammani sai dakin ya haske fayau yaga abubuwan dake gurnanin ba komai bane face wadansu rikakkun zakuna wadanda a kalla adadinsu yakai guda dubu dukkaninsu a kwance suke sunyi wa dakin kawanya ma ana a tsakiyarsu sarki sahibul hairi yafado koda zakunan nan sukayi arba dashi sai suka fara zazzago harshe suna tamde baki alamar cewa sun jima suna fama da yunwar abinci kawai suke nema tunda sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin zakuna masu girma da tamkar wadannan dukda dakakkiyar zuciya ta mazan jiya saida hankalinsa ya dugunzuma yasan cewa lallai yau ya gamu da gamonsa sai abinda hali yayi kamar hadin baki sai zakuna suka daka tsalle lokaci guda gaba dayansu suka yi kan sarki sahibul hairi suka tumurmusheshi da nufin su cinyeshi sahibul hairi ya yunkura da dukkanin karfinsa ya watsar dasu sai gashi sun tarwatse a sama suna buguwa da garun dakin kafin su sake kawo masa farmaki tuni ya zare takubba biyu a jikinsa hagu da dama ya hausu da sara duk zakin da ya sara sai yaji kamar dutse ne saidai kaji wani irin sauti ya tashi kall. Al amarinda ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa lallai maganar sarki barusa ta tabbata cewa ya kawo kansa izuwa mahallakarsa nanfa zakunan nan suka kara kaimi wajen daka tsalle suna kai masa hari suna kokarin ya kusarsa da kokarin cinyeshi inba don sahibul hairi ya kasance mai tsananin zafin nama da sadaukantaka ba da tuni sun gama dashi amma dukda hakan saida suka fara karkarce jikinsa da faratan hannunsu kafin ya ankara tuni jini ya fara zuba a jikinsa koda ya fuskanci cewa zai hallaka ba da dadewa ba in akaci gaba da wannan gumurzu sai yayi jifa da takkubban hannunsa sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ihune ya sa zakunan sukaja da baya sukayi cirko cirko ihun yaci gaba da amsa kuwwa har sarki barusa da jama arsa dake zaune a can fada saida suka jiyo ihun amma sai sukayi zaton cewa wahala ce tasa sahibul hairi yake wannan ihu don haka sai suka kama kyalkyala dariyar mugunta lokacinda zakunan nan suka firgice da jin wannan ihu na sahibul hairi sai aka fara kallon kallo tsakaninsa dasu tamkar sunji tsoro bazasu sake afka masa ba daga can sai suka sake daka tsalle gaba dayansu sukayi masa rubdugu wohoho! A sannan ne fa tsagwaron karfi da jarumtaka sukayi ranarsu domin sahibul hairi wanzuwa yayi tamkar shaidani a tsakiyar zakunan nan duk wanda ya nausa sai dai kaga yai sama ya fado kasa kafin ya mike sai yasa kafa ya tatsile kansa take zakaga kan zakin ya dagwargwaje tamkar an kwankwatsa shida dutse wani lokacin idan ya naushi zaki a gadon baya saidai kaji bass! Wato ya karya masa kashi nan fa zakunan nan suka ringa bajewa a kasa suna zama gawa koda sahibul hairi yaga ya samo lagon zakunan saiya kara kaimi a kansu yaci gaba da ragargazarsu da karfin damtse cikin zafin nama da juriya da jarumtaka kai saida takai cewa yana kama kawunansu yana murde musu wuya da karfin tsiya saidai kaga yayi jifa da gawar zaki. Hakika karfi jarine domin inda sarki bai kasance sadaukin gaskeba da tuni zakunan sun zamo sanadiyar Ajalinsa duk da cewar ya samo lagon zakunan ba su fasa yi masa rauni ba domin kartar jikinsa suke da farata nan da nan jikin nasa yai fata fata tamkar da kaifin takobi ake saransa saboda zafin yankan da suke masa ne ya dinga kwarara ihu yana ci gaba da kakkarya gabban jikinsu. Saida aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan dauki ba dadi sannan ya samu ya kashe gaba dayan zakunan nan aikuwa yana gamawa dasu ya yanke jiki ya fadi a lokacinda jiri da jini ke dibarsa, dama tun lokacinda aka fara wannan gumurzu su sarki barusa na jiyo ihunsu da gurnanin zakunan amma daga bisani sai sukaji shiru ba ihun sarki bana zakuna . . Dama run lokacin da aka fara wannan gumurzu tsakanin sahibul Haiti da zakunan su sarku barusa Na jiyo ihunsu da gurnaninsu amma daga bisani sukaji shuru ma ana babu ihun sahibul Haiti kuma babu Na zakunan Al,amarinda ya baiwa sarki barusa mamaki kenan kawai sai ya dubi wadansu dakaru dubu uku tace maza kuje cikin wannan dakin Kasan su gano masa abindake faruwa shinn zakunann nan sunn kashee sarki sahibul hairii ko kuwa shine yakarkashesu. Yayinda dakaru sukaji wannan umarni Na sarki barusa sai hankalinsu ya dugunnzuma suka tsaya suka yi charko charko suna kallon junansu aka rasa Wanda zai wuce gaba Ba wani dalili bane yasa wadannann dakaru suka kasa zuwa wqnnan daki ba sai saboda bala,in dake cikinsa Shidai wannan wuri an tanadeshine musamman son hallaka iron mutanan da aka yankewa hukunncin kisa hakika sarrki barusaa karyaa yayiwa sahibull hairi cewaa a wannan bangareen gatarinn sihirinn yakee A cikin wannan gidaan kasa India sarki sahibul hairii ya fadaa akwai dakuna gomaa sha biyuu a cikinn kowanne dakinwl akwaii masifa iri dabann masifar dakina farko ta bata kai wacce take dakii nabiyu baa wadda ke dakin Na uku tafi ta daki nabiyu Wato dai abin bi dabi be har zuwa dakin karshe wato Na gomaa sha biyu Idan mutun ya kuskura ya fada daki Na farkoo toga babu wata hanya da zaibi ya fito dolene sai yabi ta cikin ragowar dakunaa goma sha dayann Lokacinda sarkibarusa yaga dakarunsa sunnoke sun kasa lafiya cikin wannan wuri sai ya tuntsure da dariyar far in ciki yace lallai kun Sani cewa ba a Shigaa wannan wuri a fito a rayee Ko shakka babu wannan makiyi namu tuni yanzu ya hallaka,, Koda fadawa da jama at gari sukaji wannan batu sai suka bushe da dariya nan take aka cigaba da shagali tamkarr babu wata miskila data task ++. +++. ++. ++ Al amarin sarki sahibul haiiri kuwa lokacinda yaga ya kashe zakunan nan gudaa dubu saiya fadii kasa yana haki saboda tsananin gajiyaa Visa dole ya yanke hukuncin ya tsaya yayi jinyar jikinsa kafinnan kafin ya tunkari daki Na gabaa tunda dai baisan masifar dazai iske ba a cikinta nan take ya kwance wata karamar jakaa dake kugunsa ya fiddo wani Baron magani ya shashahafa a jikinsa sannan ya kwanta a cikin gawarwakin zakunan nan son ya huta Faruwar hakan keda wuya sai bacci ya saceshi bai saniba aikuwa bai farka ba sai da rana ta fadi kodaya bude idonsa ya tsinci Kansas cikin gawarwakin zakuna kuma ya fuskancii cewaa ya Dade yana wannan bacci sai ransa ya baci domin yaso ace duk bala inda zaiyi ya dauko Gagarin sihirin a cikin abinda vai wuce ss a biyarba har yabarr kasar Askandariyya Nan take kuma sahibul haiiri yaji yanajin yunwa gashi kuma bai taho da jakar guzuri ba ya barta a can bayan gari wajan bawa haluf nanfa hankalinsa ya tashi SBD yasan cewa Indaii yacigaba da Shiva dakunan wannan gida a haka zai jya rasa rayuwarsa tunda gajiya da yunwa a jikinsa babu kuzarinda zai iya yin yaki Yana cikin wannan haline dabara ta fado masa nan take ya farke cikin zakuna ya fiddo kayan cikinsu yakama cinsu danye bataree da gashiba tunda babu wutarda zaigasa run yana yamutsa fuska SBD rashin jin dadin naman a bakinsa harma yajiyasaba da rashin dadin Bai gusheba yanacin naman harsaida yaji ya koshi sannan ya mike tsaye yasake daukar takubbansa guda biyu nan ya banke kofar dakina biyu da kafarsa ya kunnna kai ciki Da shigarsa sarki sahibul haiiri cikin dakinn Na biyu sai yayi arba da wadansu iron zagba zabgan maridai wadanda girmansu ya wuce kima da tunanin bill adama kowanne daga cikin su ya ninka sarki barusa a tsawo sai biyu hakama fadinsu da kaurinsu Dukda cewa sarki sahibul haiiri Nada dakakkiyar zuciya saida ya tsorata ainun da ganin wadannan maridai Dan ko a labaran dayasha ji baitaba jincewa akwai maridai kalan suba Wadannan maridai dai su dubu ne cif kuma kowannensu Na rike da zabgegiyar makamai guda Inda za a ajiye makamin mutum daga daga cikinsu makamin ba zai dauuku ba face antara karti majiya karfii mutum arba in Sudai wadannan maridai suna da mummunar siffa maiban tsoro tamkar dodanni kallon daga zakayiwa kirar jikinsu kasan cewa karfafane domin duk naman jikinsu a cure take tamkar an shirya mulmulallen diwatsu gashi sun Tara many an damatsa jijiyoyin kwanji hakika idan aka Tara irinsu goma zasu iya yakar babban birni suciahida yaki a cikin Rabin ss a Yayinda sarki sahibul hairi yai arba da wadannan maridai sai zuciyarsa ta karaya ya juya d baya da nufin ya koma wajan da ya fito wato dakina farko aikuwa saidaya daga cikin maridan ya zuro zungureren hannunsa ya cafkoshi yai samaa dashi ya fyada da kasa Saboda tsananon radadi da zugi saida sahibul hairi yatakarkare yaji kamar an karya Massa duk kasusuwan dake bayansaa don haka saiya kasa tashi Maridin ya daga wani faskeken gatari Dame hannunsa ya dankarawa sahibul haiiri Sara a cikii aikuwa koda gatarin ya dira akan cikin sahibul haiiri saiya kakkarye amma karfinn saran yasa cikinsa ya kulle yaji kamar zai suma Kosa faruwar haka sai mamaki ya kama maridannan gaba dayansuu saboda ganin yadda karfin gatarinsu yake yasiri a cikin duk wani .wahaluki amma yau gashi bill adama yaki yayi tasiri a jikinsa harma ya zauna lafiya bayan a tarihin Gagarin ba a taba saran wani abuba Wanda ya kasa rabewa gida biyu Aikuwa sai maridannan suka taso Masa gaba dayansu shikuma yahau maridannan da Sara da suka sukuwa suka dinga kai masaaa cafka yana gocewa Babban abinda yatayarwa da sahibul haiiri hankali shine gashidai yana saransu jikinsu nadarewa yana zubar da jini amma ko kadan basa gezau kai wani lokacima harr caka musu adduna yake a cikinsu amma da ya zaree saikaga sun cigaba sa yaki saboda taurin rai da naci iron nasu Al,amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa indai akaci gaba da wannan gumurzu a haka izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gajiya su sami damar hallakashi Su kansu maridan sunsan cewa yau sun hadu da shahararren bill adama domin tinda suka wanzu a wannan wuri ba a taba jeho musu mutun ya gagaresu hallakawa a cikin dakika sittin yau gashi sun shade kusan Rabin sa a suna artabu da mutum daga kacal alhali sunsha ragargaza mutane dubu cikin kankanin lokaci Ana cikin wannan dauki ba dadi ne sahibul haiiri ya sari daga daga cikin maridan a tsakiyar kai kawai sai yaga wannan maridin ya sulale kasa ya zama gawa koda ganin haka sai murna ta kama sahibul haiiri don yagano lagonsu nan fa ya wanzu yana saransu aka suna faduwa kasa matattu Yayinda .maridan su kaga yanayi musu wannan barna suma sai suka kara kaimi wajen kokarin hallakashi maimakon koka Inda suke su cafkeshi sai suka fara kaimasa Sara da suka da bugu da naushi A wannan lokaci nefa yakin ya sauya salo domin idan suka sameshi da. Naushi saikaga kamar an cillashi daga cikin kibiya Saidai kaga yaje ya manne da jikin garu akwai lokacinda babban cikin maridan yayiwa sarki wawan naushi a ciki saiyaga sahibul haiiri a sama ya manne da rufin dakin yana aman jini amma SBD juriya irin namaza bai yarda sun cafkeahi ba sai yaci gaba da saransu aka sukaci haba da mutuwa . . Hahahaha kaji many an sarakuna sahibul hairi mazajen duniya . 015. SARKIN SARAKAI BOOK1 . YAYINDA maridannan sukaga suna dada cigaba da mutuwa sai suka rude kuma suka firgice suka rinka kaiwa sahibul hairi mummunan sara da suka shikuwa ya wanzu yana mai zilliya da goce goce a tsakaninsu a hakanne fa suka rike kashe kansu basu saniba saida aka shafe sa a uku ana wannan dauki ba dadi sannan gaba daya maridannan suka kare wato dai suka zama gawa shikuwa sahibul hairi saiya bingire kasa a sume saboda tsananin jigata wannan shine abinda ya shiga cikin fadar sarki barusa don daukar gatarin sihiri ++ Al amarin bawa haluf kuwa lokacinda ya farka daga barci sai ya nemi ubangidansa bai ganshiba kuma baiga taguwarsa ba saiya tabbatar da cewa aikin gama ya gama wato tuni sarki sahibul hairi ya shiga cikin birnin Askandariyya nanfa hankalin sahibul hairi ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi kawai saiya zauna yana shawarwari a cikin zuciyarsa abu na farko dai shine bai san halinda sarki sahibul hairi ke ciki ba a yanzu, zata iya yiwuwa ya hallaka kuma ko

Chapter 3 of 19