Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
irin jarumtakarsa ya tabbatar da cewa Badakaren ya sha gabansa. Sarki Sahibul Hairi ya dubi Badalaren ya ce, "wai shin kai wana irin mutun ne mai karfi kanar na zakuna? Na rantse da darajar burin da ke gabana ban taba ganin sadauki kamarka ba. Kai kuwa ya ya akayi ka sami nasara sadaukantaka?". Koda jin wannan tambaya sai Badakaren ya yi murmushi bai ce komai ba, kuma ya nuna da cewa kawai du ci gaba da tafiya a cikin gidan. Ya yin da sarki sahibul Hairu ya fuskanci nufin Badakaren sai ya ce, "na yar da zamuci gaba da tafiya, amma ina mai rokun alfarma guda daya. Na gamaka da girman Ubangijin da kake bautawa da ka ya ye rawanin fuskarka. Bana so murabu banga fuskarka ba, domin na samu damar bayar da labarinka da cikkakkiyar kwatancen suffarka". Sa'adda Badakaren ya ji bukatar sarki Sahibul Hairi sai ya yi masa nuni da hannu cewa ya yi hakuri sai nan gaba zai ga fuskarsa. Koda gama fadin hakan sai Badakaren ya juya ya ci gaba da tafiya. Bisa dole sarki Sahibul Hairi ya bishi da sauri yana mai dafa kafadarsa inda yaji rauni sabo da zugin da yake masa. A sannan ne tunanin Bawa Haluf ya fadowa sarki sahibul Hairi ya ce a ransa, "tabbasa Haluf tsananin furgita ne ya sashi suma. Amma babu komai, nasan zai farfado kuma zai biyo bayanmu". Badalaren da sarki Sahibul Hairi suka ci gaba da kurdawa acikin gidan Boka Shamzabul Azwas, amma sai da suka sake shafe wata rabin sa'a busu sake haduwa da wani mugun abu ba. Ba zato ba tsammani sai sula ga wadansu irin jibga-jibgan Dodanni munana sun yi musu kawanya ba tare da ganin ta inda suka bello ba. Daga sama ne ko daga kasa ne, Allahu ya alamu. Sudai wadannan dodanni adadinsu ya kaidubu daya. Ko wnnansu na dauke sa mulmulallan sugumi mai kaco- kacon tsini. Fyskar dodannin a rube take har tsutsa na zuba, sai dai kaga suna ciro tsutar suna jefawa a bakinsu suna cinyewa. Idan daya daga cikinsu ya yi tafiya sai kaji karar sawunsa tamkar ana goga karfe a makera da katuwarguduma. Lokacin da sarki Sahibul Hairi yaga wadannan dodanni sunyi nusu kawanya babu ta inda zasu iya ratsewa su wuce, sai hankalinsa ya dugunzuma ya sare, domin ya tabbatar da cewa ajalinsa yazo. Shi kuwa Badakaren sai ya zare takobinsa guda biyu ya gyara tsayuwar cikin cikin yarda da kai yana jiran mai tsautsayin da zai fara dirfafoshi. Koda ya fuskanci cewa sarki Sahibul Hairi ya tsorata da ganin wadannan dodanni, sai ya dafa kafadarsa ya yi masa murmushi yana mai nuna masa alamun kara masa kwarun gwewa. Ai kuwa sai shima ya zare takobinsa suka hada baya da bada suna waige-waige don kada dodannin su shammacesu. Kamar hadin baki sai dodannin suka ruga gaba dayansu a lokaci guda da nufin suyi musu rubdugu Cikin zafin nama Badakaren ya daka tsalle sama yana mai cafar sarki Sahibul Hairi da hannu daya ya tashi sama da shi, sai gasu a saman Dodannin. Su kuwa Dodannin sai suka yi gware da junansu. Sautin haduwar kawunan Dodannin kamar ana rugurguzo duwatsu. Koda su Badakaren suka wado kan Dodannin sai suka hausu da sara da suka, amma sai hakan ya zamo a banza, domin kaifi da tsini baya tasiri a jikinsu. Nanfa Dodannin suka dinga kaimusu wafta da hannayansu da nufin su cafkesu, amma sabo da tsananin zafin nama irin na Badakaren sai yaki yarda Dodannin su sami nasarar cafke su din. Tabbas in badan kokarin Badakaren ba da tuni Dodannin sun cafke sarki Sahibul Hairi sun halakashi, domin zafin namansu ya fi nashi, na Badakaren yafi nasu. Koda aka dan jima kadan a cikin wannan hali, sai hanlalin Badakaren ya dugunzuma, donin ya san cewa idan aka ci gaba da gumurzu a haka ba tare da ya gani lagon Dodannin ba, komai zai iya faruwa, wato Dodannin za su iya hallakasu shi da sarki Sahibul Hairi. Nan take dabara ta fado masa a rai, ya ce, "bari ya jarraba ya gani. Cikin hanzari Badakaren ya takarlare ya naushi daya daga cikin Dodannin da dukkan karfinsa a cikin kunne. Bisa mamaki sai kawai hannun ya burma cikin kunnan na dama ya bull ta cikin na hagu. Take Dodannan ya sulale kasa matacce. Koda da ganin haka sai shima sarki Sahibula hairi ya jarraba hakan, shima ya sami nasara. Wohoho! Nan fa suka yi ta burma kunnuwan Dodannin suna zubar da su kasa. A wannan lokaci Sarki Sahibul Hairi ya taka muhimmiyar rawa, damin ya kashe Dodannin sama da guda dari shida. Sauran kuma duka Badakaren nan ya kashe su. Bayan sun gama da dodannin sai suka ci gaba da tafiya suna ta haduwa da mugwayan aljanu iri-iri da mugwayan dabbobi suka yi ta fafatawa da su. Basu gushe ba a wannan hali har sai da suka shafe kwana tara. Batun abinci da ruwa basu sami matsala ba, domin guzurin bai kare ba. Amma fa sun sha bakar wahala. Shi dai Badakaren Sau daya wani aljani ya sami nasarar yankarsa a kafada da farcen hannunsa. Amma shi sarki Sahibul Hairi sai da ya kara samun raunuka bakwai a jikinsa. Akwi lokacin da sarki Sahibul Hairi ya suma sau uku, sa'adda suka fafata da wasu mugwayan bakaken aljanu masu siffar jemagu masu yawan gaske masu karfin tsiya da naci. In ba dan Badakaren ya bai wa sarki Sahibul Hairi kariya ba da sai aljanun sun sami nasarar kashe shi. Sai da aka kwana uku ana wannan gumurzu da bakaken aljanun sannan Badakaren ya sami nasarar hallakar da su gaba daya ta hanyar karanta wata addu'a wadda ta zamo sanidiyar konewarsu da wuta kurmus. A ranar kwana na tara ne suka iso wata katuwar fada wadda babu komai a cikinta face tarkacen kayan tsafi iri- iri, wadansu ma tun da sarki Sahibul Hairi yazo duniya bai taba ganin su ba. Babban abinda yafi bawa sarki Sahibul Hairi mamaki shi ne, kowacce irin dabba ta daji akwai kwarangwal dinta a sakale a jikin bangwan fadar. Haka kuma wace irin bishiya ta duniya akwaita a shuke a cikin fadar. Baya da haka sai suka ga wasu manyan kwalabe dirka-dirka guda dari. Kwalaban basu da kofa a jikinsu ta inda za a zura a ciki, amma kuma da ruwa a cikinsu, kuma ga yarinya Alfila a cikin kowacce kwalbar a kwance kamar tana barci ko motsi bata yi. Koda ganin wadannan kwalabe sai sarki Sahibul Hairi da Badakaren suka shiga rudani na rashin fahimtar kowacce ce Alfila ta gaskiya. Sarki Sahibul Hairi ya tafi inda kwalaban suke. Da isarsa sai ya daga takobinsa ya dinga saran kwalaban da nufin ya farfasa su gaba daya ya fito da dukkanin Alfilolin. Maimakon kwalaban su fashe sai takobin sarki Sahibul Hairi ta dinga dakushewa kuma suk sa'adda ya sari kwalben sai takobinsa ta dume da mugun zafi tamkar zata narke, bisa dole ya hakuara ya daina saran kwalaban. Ana cikin haka suka ji an bushe da irin mahaukaciyar dariyar nan wacce aka yi musu tun a ranar farko da suka iso kofar gidan. Ba zato ba tsammani sai suka ga wani shirgegen aljani mai mutukar kwarjini da ban tsoro ya bayyana a gabansu. Fuskar aljanin kamar ta dodannin take, kuma ido daya gareshi manne a tsakiyar goshinsa, a saman idon a kwai murtukeken gashin gira. Inda za a yanko gashin girar a jiyeshi a kasa sai mutun yay kokari zai iya daukarsa. Gangar jikin aljanin irin ta zaki ce cike da zara-zaram gashi. Hannayansa irin na gwagwgwan buri ne. Daga kugumsa zuwa kafafunsa kuwa irin na kada ne. Jelarsa kuwa murtukekiya ce kuma doguwa mai tsananin tsawo wadda takai kusan kamu ashirin. Gaba daya jikin jelar cike yake da kahuhhuna masu tsini da kaifai. A hannunsa na dama akwai dirkekiyar takobi, haka ma fadinta. A hannunsa na hagu kuwa, wata katuwar garkuwa ce wadda za a iya kife mutane hamsin da ita su ji tamkar rumfa aka rufa musu. Aljanin ya dauri kugunsa da wata irin damarar karfe ja. Koda Badakaren ya kurawa jikin damarar idanu sai ya cika da tsananin mamaki. Ba komai ne ya sashi mamaki ba face ganin synayan ubangijin musulunci iri-iri a jiki da kuma wadansu addu'oi kala-kala duk na ma'a bota addinin musulinci. Badakaren yace a cikin zuciyarsa. "wannan fa shine kwaba. Tabbas wannan aljanin kafuri ne, kuma mashiriki ma'abocin tsafi! Ta mene ne gaminsa da wannan damara mai dauke da ayoyin Allah da sunayansa tsarkaka?" Kamar aljanin ya san abinda Badakaren yake ayyanawa a zuciyarsa, sai ya dubeshi ya tuntsure da dariya ya ce. "lale marhaba da jinin imam Sadik. Koda jin wannan batua sai Badakaren ya sha jinin jikinsa. Ya tabbatar da cewa aljanin ya san ko shi waye. Aljani ya sakea bushewa da mahaukaciyar Dariya, sannan ya dubi sarki Sahibul Hairai ya ce, "kaiconka ya kai wannan sarki! Kasani cewa tun daga gida ake yaudararka har izuwa nan fadata ni boka Shanzabul Azwas. Idan baka manta ba bokanka ya gaya maka cewa idan harka mallaki gatarin sihiri zaka iya balle kofar wannan gidan nawa ka shiga? Amma sai gashi gatarin sihirin bai amfana maka komai ba. Wannan Badakaren da kataho tarr da shi a matsayin namiji, to ba namiji bane maca ce. Kuma ita ce babbar 'y ga imam sadik, shugaban ma'abota addinin musulinci na birnin Hairin Nur, sunanta jaruma Humairat. Idan har abin da na fada ba gaskiya bane ta yaye rawaninta ka ga fuskarta". Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya juya ya dubi Badakaren. Nan take Badakaren ya cire rawanin fuskarsa, yayi jifa dashi, sai ga dogon bakin ga shi wuluk mai tsawo da sheki ya zubo kasa. Kyakkyawar fuska abar kwatance ta baiyana. Sabo da tsananin mamaki da takaici sarki Sahibul Hairi bai san sa'adda ya durkusa kasa ga gwewoyinsa. Babban abin takaici shi ne, yanzu ashe duk irin jarumtakarsa da juriyarsa ashe akwai macan da ta fishi? Kuma akan wana dalili Imam Sadik zai yaudareshi ya hadashi da 'yarsa mace a matsayin namiji, gashi tayi abin al'ajabi da har abada ba zai iya ba. Cikin fushi sarki Sahibul Hairi ya dubi jaruma Humairat ya ce, "mai yasa ki ka yaudareni ke da mahaifinki kika biyoni izuwa wannan gagarumin aiki a matsayin ke namiji ce?" Ya yin da Humairat taji wannan tambaya sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce da shi cikin wata zazzakar murya mai dimautarwa, tamkar tana magana da sarewa. "ya kai wannan sarki mai babban buri ka sani idan banrakoka nan ba da babu yadda za ai ka shigo cikin gida nan. Haka kuma idan kasan cewa ni 'ya maca ce ba zaka yarda muyi wannan tafiya tare ba ka sani cewa na biyo ka wannan tafiya ne domin na jaddada addinina a gareka ka gamsu cewa shi ne addinin gaskiya, tun da gashi ka kasa kare kanka daga cikin masifa da ke cikin gidan nan, sai ni ce na kareka da taomakon Ubangijina, wannan abu da ya faru ya isa yasa ka gamsu cewa babu wani abin baytawa da gaskiya face Ubangijin musulinci" .________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________________ure guda daya wata kyakykyawar budurwa wacca babu kamarta a duk fadin junsin aljanu na duniya, ana kiranta da suna Harfiza. Labarin Harfiza ya bazu a ko ina a duniya, kuma har yake- yake anyi akanta, sarakunan aljanu da bokayansu babu abin da basu yi ba akan su mallaketa amma sai gashi boka shaharuz zaman ne ya zamo zakara a cikinsu, wato shi ne kadai ya samu damar mallakarta. Yau shekara tara ke nan da yin auran boka shaharuz zaman da Harfiza amma har yanzu basu sami haihuwa ba. Shaharuz zaman ya san cewa bazai taba samun haihuwa ba a duniya, domin ya yi bincike a cikin tsafinsa, tsafin nasa ya tabbatar masa da hakan, amma ya boyewa Harfiza wannan sirri. Wata rana Harfiza ta ziyarci wani mashahurin Boka a sirrance ba tare da sanin sharuz zaman ba, sai ya sanar da ita wannan sirri. Koda taji hakan sai ta cika da tsananin bakin ciki ta fashe da matsainai cin kuka ta tambayi wannan Boka ta ce, "yanzu ya ya za ai na rabu da mijina Boka shaharuz zaman, domin a halin yanzu na tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwata, sabo da bani da wani buri a duniya wanda yafi na sami Haihuwa." Ya yin sa Bokan ya ji wannan tambaya sai ya yi shiru ya shiga bincike a hallarar tsafinsa. Jim kadan ya dago kai ya kalleta ya ce, "kiyi hakuri akwai lokacin da zaku rabu, amma idan kika bukaci rabuwa da shi a yanzu zai iya hallakaki". Daga wannan rana Harfiza ta rungumi kaddara, amma kullum sai tayi kukan bakin ciki kuma bata taba bari shaharuz zaman ya fahimci halin da take ciki ba. Lokacin da jarumi Saif da aljani Hurbas suka iso sansanin yaki suka dura a gaban dakarunsu sai suka iske ashe tuni Boka shaharuz zaman ya hallara. Koda suka yi arba dashi sai ya daka musu tsawa ya ce, "ya ku kananin halitta, kuyi sani cewa yau kun hadu da zaki sarkin dawa, dan haka daga yau an daina jin duriyarku a doraon kasa. Yanzu nan zamu murkusheku yadda ko tokarku bazata moru ba" . KODA JIN HAKA SAI JARUMI SAIF YA MAIDA MASA DA MARTANIN TSAWAR YA CE "kai tsohon annamimi, babban makiyin Allah, ka sani cewa karyarka ta kare daga yau. A yau ne zamu kawo karshan kafircinka da fasikancinka da dukkan zaluncinka. Tabbas da kai da jama'arka dayansu bazai koma gidansu ba, idan zamu shekara muna wannan yaki duka babu gudu ba ja da baya har sai muga karshanku". Sa'adda jarumi Saif yazo nan a zancensa sai fuskar Boka shaharuz zaman ta kama girgiza kamar za ta zazzago kasa sabo da tsananin fishi, zuciyarsa kuwa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Nan take ya zare takobinsa ya yi nuni da ita izuwa ga dandazon su jarumi Saif, wannan almace ta umarni a afka musu. Ai kuwa nan take kowana 6angare ya taso cikin matsainaicin gudu. Na kan dawakai na sukuwa sukuwa aljanu na kada fuka-fukansu a sama suna tsala gudu, domin a hade a tsakiya. Tun kan a hade ihun mazaje ya cika dajin gaba daya, kura ta tshi ta turnuke a sararin sama tamkar ana rairayar sahara. Kasa kuwa sai ta kama girgiza saboda karfin sukuwar dawakai. Ya yin da aka hade a tsakiya sai aka ruguntsume da azababban yaki mai matukar tashin Hankali. Hakika bala'i ba'asa masa rana, ita ko masifa idan ta tunkaro, to fa babu abinda zai iya lafr da ita face ikon Allah. Lokacin da aka fara wannan masifaffan yaki, sai ya zamana cewa ido bai isa ya yanke hukunci ba, ya fadi 6angaren da yake samun nasara, duk da cewa 6angaran su Boka Sharuz zaman sun nunka su jarumi Saif a yawa. Duk 6angaren da mutun ya duba sai yaga ana yi musu 6arna domin mazaje ne suke zubewa kasa tamkar ana karkadar busassun ganyayen bishiyoyi a daji. Sai da aka kwana aka yini gumurzu sannan dukkanin maya kan suka zama gawa, yarage saura mahaluki uku kawai kacal a filin yakn, wato daga Boka Sharuz zaman sai Jarumi Saif da Aljani Hurbas. A wannan lokaci duk su ukun sun gaji ainun, sai haki suke kamarransu zai fita kuma sunyi carko-carko suna kallon juna kamar zakaru. Hurbas da Saif na tsaye daf da juna shi kuwa Boka Shaharuz zaman na can gefe daya rike da manyan makaman yaki. Tsawon 'yan dakiku suna kallon juna daga can sai Boka Shaharuz zaman ya tuntsure da dariya sannan ya nunasu da tsinin takobi ya ce, "karyarku ta sha karya ya ku manyan abokan gaba. Tabbas yanzu zan zare muku ruhin numfashinku, sannan na yanke kawunanku" Koda jin haka sai jarumi Saif ya daka masa tsawa ya ce, "kai tsohon jahili, kuma babban fasiki ka yi sani cewa babu mai kashewa da rayawa face Ubangijin musulunci. Tabbas kai baka isa ka kashemu ba. Ka sani cewa da izinin Ubangijinmu karfin dantsanka da karfin sihirinka ba zai sa ka sami nasara a kanmu ba, mune da nasara a kanka. A yanzu kuma matarka ta zamo baiwarmu, sannan mu duk kayan sihirinka yadda har abada baza a sake tunawa da kai ba." Boka Shahaz zaman ya bushe da dariyar mugunta ya ce, "ai wannan furci naka da tatsuniy duk matsayinsu daya. Ka sani cewa inda ba kasa nan ake gardamar yin kokawa. Ga fili ga mai doki sai a kasa mu ga wanda zai ci riba ni da ku". Kafin Shaharuz zaman ya gama rufe bakinsa tuni jarumi Saif da Hurbas sun afka masa da dukkan karfinsu shima ya taresu aka fara fafatawa. Koda fara wannan yaki sai Boka shaharuz zaman ya zame musu alakakai suka kasa hallakashi ta farat daya. Domin ne ma yake ya gagaresu duk da cewa suma syn kuntace shi. Babu abinda ya dagawa shaharuz zaman hankali kuma ya bashi mamaki face ganin yadda ko dan kadan ya kasa yiwa jarumi Saif illa. Duk sa'adda ya sari jikinsa ko kuma ya sare shi da makami sai yaji kamar dutsen wuta ya kaiwa hari, domin makanin baya tasiri a jikinsa. Haka kuma tsananin zafin nama Saif din ya hana ya hallaka Hurbas amma duk da haka sai da ya shammaci Hurbas ya dankara masa wawan naushi a wuya. Take Hurbas ya sulale kasa sumamme ko motsin kirki bai kara yi ba. Ya yin da jarumi Saif yaga abinda ya faru da abokinsa kuma amininsa Hurbas, sai ya nutsu. Nan rake ya sake afkawa shaharuz zaman kuma ya tattare dukkan karfinsa suka rikice da sabon artabu. Sai da suka shafe sa'a tara suna yaki amma ko sau daya babu wanda ya yiwa dan uwansa lahani. Al'amarin da ya fusata Boka Shaharuz zaman ke nan, ya fara amfani da karfin sihiri. Duk masifar da ya watswa Saif sai yaga taki kamashi. Bayan Shaharuz zaman ya gama jarraba dukkanin sihirinsa na tsafi akan jarumi Saif basuyi tasiri ba sai suka yarda makamansu suka fara 'yar gwada kwanji. Ko shakka babu Boka shaharuz zaman ya fi karfin Saif a zahiri, domin girmansu da kwarjinsu ma ba daya bane. Za a iya kwatanta banbancinsu da dantsako da muzuru. Amma bisa mamaki sai gashi jarumi Saif nata ragargazar Boka Shaharuz zaman ya dinga jera masa naushi da bugu hannu da kafa. Kafin ya kare wani dukan ya karo masa wasu cikin matukar zafin nama. Nan da nan ya hada masa jini da majina. Kai! Tun Sharuz zaman na iya daga hannayansa har ya kasa, kuma tun yana tsaye sai ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa. Ba wani abu bane ya bawa jarumi Saif wannan gagarumin karfi ba face taimakon wannan damara da ke kugunsa. Lokacin da jarumi Sai yaga ya yi laga-laga da Boka Shaharuz zaman yadda ba zai iya ceton kansa ba sai yazo kansa ya tsaya ya daga takobin sai ya dubeshi a lokacin da jini ke ta zuba daga hancin Shaharuz zaman da bakinsa, iadanunsa na gani dashi-dishi ya ce, "ya kai wannan tsohon Boka, ka tuba ka kar6i addinin gaskiya, yanzu ni kuwa sai na fasa hallaka ka Koda jin wannan batu sai Boka Shaharuz zaman ya bushe da dariyar kafirci. Cikin karfin hali ya bude baki ya ce, "har abada kafiri na kwarai baya musulinta sabo da tsoran mutuwa. Babban abin kunya ne a gareni ace a yau kacini da yaki har na kar6i addininka. Ni kuwa da naji kunyan duniya gara naji tacan lahira! Tur da kai! Tur da addininka.....!!! Kafin harshan Shaharuz zaman ya gama fadar wannan furci tuna jarumi Saif ya yi kabbara ya cire masa kai. Nan take kan ya yi tsalle sama ya fado kasa tum. Faruwar haka ke da wuya sai Aljani Hurbas ya farfado. Koda yaga gawar Boka Shaharuz zaman a gefe daya sai ya cika da tsananin farin ciki, ya mike zumbur ya taho wajan Saif suka rungume juna cikin tsananin farin ciki suna masu godiya ga Allah". Bayan sun nutsu sai suka dubi tulin gawarwakin 'yan uwa musulmi da ke kwance a wajen wadanda suka yi shahada. Saif ya ce, "kamata ya yi mu koma can cikin gari nu debo jama'a domin su zo su tayamu binne gawarwakin nan na shahidai". Hurbas ya ce, "wannan gaskiya ne, to amma muna guntun aiki wanda bamu karasa ba, kuma barinsa na iya janyo mana babbar asara, domin tamkar mun kashe maciji ne bamu sare kansa ba". Koda jin wannan batu sao mamaki ya kama jarumi Saif ya ce, "ya kai aminina me kake nufi da wannan batu? Ban gane munufarka ba." Hurbas ya ce, mun kashe Boka amma bamuje mun kama matarsa ba, kuma bamu kone dukkanin kayan tsafinsa ba, tabbas matarsa zata iya kawo mana harin sumame ". Koda jin wannan batu sai Saif ya jinjina kai ya ce, "hakika kayi gaskiya. Abinda za ai yamzu ni zan koma gari na taho da jama'ar, kai kuma kaje ka kamo matar Shaharuz zaman. Sannan ka bankawa gidan wuta ka tabbatar da cewa komai ya kone ya zama toka". Sa'adda Husbas yaji haka sai ya yi shiru kamar ya ce a'a amma sai ya dubo Saif sai ya ce, "ya kai Abokina hakika nasan cewa zan iya wannan aiki, amma masu iya magana sunce idan kana da kyau ka kara da wanka, me zai hana kabani aran damararka ta yaki a yau naje na wannan gagarumin aiki domin kada nayi kuskure ko kuma na hadu da wani tsautsayi". Ya yin da Saif yaji haka sai ya yi murmushi ya dubi Hurbsas cikin aminci ya ce, "ai ka san abinda zaka karanta ka cire wannan damara daga jikina, don haka bisimillahi". Nan take Hurbas ya biya wata addu'a a zuciyarsa, sannan ya sa hannayansa biyu ya cire wannan damara ya san yata a nasa kugun. Ko sallama bai yiwa Saif ba sai ya bude fuka-fukansa yai sama ya nufi inda gidan Boka Sharuz zaman yake. Gidan Boka Shaharuz zaman an kawata shi ainun fiye da tunanin mai tunani. Domin jama'a da yawa suna yiwa gidan kirari da aljannar duniya. Sabo da babu abinda ba bu a cikinsa na jin dadin duniya. Sai mai cikakken imani ne zai shiga gidan ya kasa mancewa da Allah. Lokacin da aljani Hurbas ya shiga cikin wannan gida yaga irin daular da aka shirya a cikinsa sai ya dimauce ya shiga zancen zuci a lokacin da yake ta shiga sako-sako na gidan yana morewa idanunsa da kallo. Ko ina a gidan fes-fes yake kamar kurra bata ta6a sauka ba, kai ko a kasa mutun ya zuba ruwa a kasa ya sha, domin duk inda kafa zata taka a shinfide yake da lu'u- lu'u. Shuke-shule na kyawawan furanni masu kamshin gaske gasunan burjik ba adadi. Tsuntsaye kuwa kyawawa suma gasu nan har da irin wannan mutun bai ta6a gani ba, kayan marmari kuwa da kayan abinci da abubuwan shaye-shaye suma gasu nan barkatai na alfarma iri'iri, duk bayan munti sittin sai su 6ace sai wasu su sabbi su sake baiyana. Kai da gani kasan cewa aljanu ne ke ta hidima a gidan. Lokacin da Hurbas ya shiga 6angarab da turakar Boka shaharuz zaman take, ya taka luntsumeman kilishin da aka shinfida a ciki sai yaji tamkar ya lwanta ya kama bacci. Haka dai ya daure ya wuce har izuwa cikin dakin inda yayi arba da wani lafcecan gado na zinare mai tsananin kyau da kawatuwa an kerashi da siffar tsuntsun dawisu. Sai yaga wani kwnce akan gadon Harfiza ce tana sanye da fararen tufafi mai shar-shara wanda ke bayyana kyawawan surar jikinta da tsraicinta. Koda aljani Hurbas ya yi arba da ita sai yakara dimaucewa fiye da ko yaushe, ya manta da cewa zuwa ya yi ya kama Harfiza kuma ya kone kyakkyawan gida. Bisa mamaki sai yaga Harfiza ta mike zaune kuma ta kura masa idanu tana yi masa murmushi mai dauke da almomin tambaya. Cikin rawar jiki Hurbas ya karasa gareta ya zauna daf da ita bisa gefab gado cikin Dari-dari. Koda ganin haka Harfiza sai ta dubeshi ta ce, "haba babban jarumi, tsoron me kake alhalin da ni da wannan gida duk mun zama mallakinka? Kayi sani cewa duk abin da ya furu tsakaninka da mijina a filin yaki na gani daga nan a cikin madubin taafi, kuma nayi matukar farin ciki da kuka kashe shi. Domin dama wannan ce ranar da na dade ina jira. Ka sani cewa a duniya babu abinda nake so sama da haihuwa, sho kuwa Boka shaharuz zaman ba zai ta6a Haihuwa ba, amma sai ya 6oye mini wannan sirri sai daga baya na gano hakan bayan ya aureni. Bisa dole na ci gaba da zama da shi domin in ya gane damuwata kasheni zai yi. Yanzu bukatata dakai ita ce ka sadu dani domin in zamo uwar danka". Ya yin da Hurbas yajo wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma, ya dubeta cikin tsananin damuwa ya bude baki zai yi magana sai ta yi masa nuni da ya yi shiru, sannan ta ce, ba sai kayi mini bayani ba, ai na san cewa kayi alkawari ba zaka taba aurar jinsun aljanu ba. To ka kwantar da hankalinka ni bana nufi ka aureni, sai dai ka zamo abokin rayuwa na dan lokaci. Bayan ka biya mini buakatata duk abinda ka ke so zan baka in dai akwai shi a nan duniya. Amma ka sani cewa ba zamu sami nasara da kwanciyar hankali ba face ka bijirewa abokinka Saif. Yanzu sai ka ware wannan damara da ke kugunka ka ajiyeta a gefe daya bayan mun gama shagalimmu sai ka sanya damarar ka koma ga abokinka Saif ka hallakashi, sannan ka dawo gareni mu ci gaba da more rayuwarmu. Sa'adda Harfiza tazo nan a zancenta sai Hurbas yaji gaba daya kaunarta ya mamaye zuciyarsa. Nan take ya cire damarar nan daga kugunsa ya ajiyeta a kasan gadon ya afka ma ta suka shiga lalata. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Al'amarin jarumi Saif kuwa, bayan sun rabu da Hurbas sai ya hau dokinsa ya koma gida inda ya fara tattaro jama'a domin aje sansanin yaki a yiwa mtune sutura. Lokacin da matarsa ta dubeshi taga babu damararsa a kugunsa sai da tsananin tsoro ta ce, "ya kai mijina, ina kuma ka baro damararka a yau? Alhali tunda na aureka ban ta6a gani ka cireta ba". Koda jin wannan batu sai Saif ya bata labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da abokinsa Hurbas. Ya yin da taji haka sai idanunta suka ciko da kwalla ta ce, "ya kai mijina hakika kayi babban kuskure da ka da ka aiyana a ranka cewa abokinka Hurbas ba zai ci amanarka ba. Ka san cewa da yawan aljanu basu da amana kamar yadda shida kansa ya ta6a baka labarin yadda mahaifiyarsa ta ci amanar magaifinsa ta zamo sanadin ajalinsa. Iana tabbatar maka da cewa ina ji ajikina sai Hurbas ya ci amanarka. Ni kam abinda naso shi ne kada kowa ya ta6a wannan damara bayan kai face danmu Sadik. Ko shakka bana yi mun rabu da wannan damara kea nan har abada. Koda fadin haka sai ta fashe da matsanaicin kuka. Shi kuwa Saif ta shiga rarrashinta yana

Chapter 10 of 19