Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsammanin su sarki Sahibul Hairi suka tafi?". Humaira ta ce, "ina kyautata zaton sun shiga daji farauta ne domin su samo mana abincin kalaci". Alfila ta ce, "hakane. Amma dai kuwa sun dade basu dawo ba, tun gashiharrana ta fara takewa, na fara jin yunwa". Da jin haka sai Humaira ta zura hannunta a cikin jakarta ta debo dabino sai ta ga ashe saura guda bakwai kacal! Kawai sai ta mikawa Alfila duka ta ce, "ungo wannan ki ci ko kya rage yunwar, in ya so mu ci gaba da jiran dawowar su sarki Sahibul Hairi". Alfila ta kar6i dabinon ta cinye cikin murna, sannan ta daga butar ruwa ta kwankwada Sai da sa'a biyu ta shude su Humaira na zaune suna jiran dawowar su sarki Sahibul Hairi amma shiru babu su babu labarinsu. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su Humaira ke nan suka yanke shawarar su tashi su bi sawunsu izuwa cikin daji. Har sun mike tsaye suna shirin tafiya ke nan sai suka hango wani katon tsuntsu a can sama ya nufo bakin kogon da suke ciki. Cikin hanzari Humaira ta zare takobinta ta fito kofar kogon tana mai umartar Alfila da cewa kada ta kuskura ta fito daga cikin kogon. Sannan a hankali tsuntsun ya dinga saukowa kasa har ya dire nesa kadan da inda Humaira ta tsaya bai yarda ya kusanceta ba. Abln da ya sa Humaira bata afkawa tsuntsun ba shi ne, ta ga wasikara bakinsa. Nan take tsuntsun ya saki wasikar ta fadi kasa, sannan ya sake bude fuka-fukansayai sama ya bar wajen gaba daya. Cikin hanzaro Humaira ta je ta dauki wasikar ta warwareta a lokacin da Alfila ta fito daga kogon dutsen ta tsaya daf da Humaira ba tare da 6ata lokaci ba Humaira ta fara karanta wasikar a fili kamar haka. Takarda daga sarki Barusa mai cikakken iko zawa ga gimbiya Humaira ma'abociyar addinin musulinci. Ina mai sanar da ke cewa a halin yanzu ina nan a cikin wannan daji da kike kuma na kama sarki Sahibul Hairi da Bawansa Haluf na tsaresu a nan kan katon tsauni wanda babu kamarsa a wannan daji. Na baki kwana daya da yini daya rak ki kawo mini yarinya Lafila. Bajirewa wannan umarni dai-dai yake da salwantar rayukan su sarki Sahibul Hairi. Idan kuwa kika ki zuwa zan zo da kaina na halllakaki na dauki Alfila bayan na kashe su sarki Sahibul Hairi. A karshe ina mai yi miki tuni da cewa ki taho da cikakken shirin yaki domin na tanaji dakaru na musamman masu lakani da GUGUWAR ANNABA. Lokacin da Humaira ta zo nan a karatun wasikar sai tayi jifa da ita cikin tsananin fushi, sannan ta dubi Alfila ta ce, "to mene ne ya shalleni don sarki Barusa ya kama su Sarki Sahibul Hairi? Ai 'yan uwansa kafurai ya kashe". Ya ke Alfila shiga cikin kogon ki dauko mana kayammu mu ci gaba da tafiya domin ni babu komai a gabana face na cika alkawari na kaiki kasarku na sadaki da mahaifinki". Ya yin da Alfila taji wannan batu sai hankalinta ya dugunzuma ta dubi humaira cikin tsananin damuwa ta ce, "ya ke 'yar uwa ina rokonki da kada ki tafi ki bar su Sarki Sahibul Haira a cikin wannan hali na kak na ka yi, domin ni a ganina idan kika yi haka kin yi babbar asara. Dalilina na fadin haka shi ne, ki tuna cewa Sarki Sahibul Hairi ne mai mulkin babbar kasa mai dauke da maliyoyin mutane. Idan har kika ci gaba da jan hankalinsa har kika sami nasara a kansa ya kar6i addinin musulinci tamkar kin musuluntar da dukkanin jama'ar da ke kasansa ne, kin ga kuwa wannan ba karamar nasara ba ce. Abu na biyu da nake son na sanar da ke shi ne, sarki Sahibul Hairi yana mutukar sonki, domin na lura shi yana yawan yi miki wani irin kallo mai nuna tsantsar so da bege. Shun idan ya musulunta ba za ki aureshi ba? Sa'adda gimbiya Humaira taji wannan tambaya sai kunya ta kamata, kuma jakinta yayi sanyi, domin tasan cewa abin da Alfila ta fadi gaskiya ne. Humaira ta yi shiru tana tunanin har izuwa wani lokaci mai dan tsawo, daga can sai ta dubi Alfila tayi murmushi sannan ta ce, "shi kenan 'yar uwata na kar6i shawararkim sabo da haka zamu fara shirin yaji tun daga yau, domin muje mu ceto rayuwar su sarki Sahibul Hairi. Yanzu zo ki rakani cikin daji mu samo wadansu abubuwa". Nan take Humaira ta kama hannun Alfila suka ruga izuwa cikin daji. Sai da Humaira da Alfila suka shafe sa'auku a cikin dajin suna saro itatuwa sannan suka dawo cikin kogon dutse suka hau fere itatuwan suna yin tsini da su. Bayan sun kammala hakansai suka kwashi itatuwan suka fito da wajankogon dutsan suka fara kafa mugwayan tarkuna, suna binne su a cikin karkashin kasa, wasu kuma suka rika dana su a sama cikin bishiyoyi, suna kukkula su da siraran zarurruka wadanda idanu ba zasu ankare da su ba. Tun safe da su Humaira suka fara wannan aiki sai da dare ya raba sannan suka kammala ya zamana cewa sun cika dajin gaba daya da irin wadannan muggan tarkuna ba adadi, kuma su biyu ne kadai suka san a inda kowane tarko yake. Kai bama mutum ba komai kankantar dabba idan ta yi kuskure ta taka wani gurin sai dai kaga ta afka cikin tarkon zai zamo sanadin ajalinta. Bayan sun kammala wannan aiki ne sai Alfila ta dubi Humaira ta ce, "ya ke 'yar uwata yanzu idan Allah ya kaomu gobe wace irin gudummawa zan baki a wannan gagarumin yaki da za kiyi?" ko da jin haka sai mamaki ya kama Humaira ta ce, "ai kin gama bani gudummawa tun da kin taimaka min da hada wannan muggan turaku". Alfila ta cem "a 'a ina son nayi abin da yafi haja, domin na sami lada mai tsika a wajan irin na shashidai, wadanda suka rasa rayukansu a wajandaukakakalmar Allah, kamar yadda kika bani Labari. Lallai a goben nima ina son nayi wannan yaki tare da ke, gashi kuma ni ban ta6a kashe koba kwaro da wannan hannun nawa ba, ke hasalima ban iya sarrafa kowane irin makami ba". Yayin da Humaira taji wannan batu sai tayi murmushi ta ce, "kada ki damu ya 'yar uwata, da izonin Allah a yanzu zan koya miki yadda ake harba kwari". Nan take kuwa Humaira ta baiwa Alfila baka ta rike sannan suka harba ta. Bayan nan sai Humaira ta sassaka mutum-mutumi na ita ce, ta tsaida shi a tsaye can nesa kadan, ta dubi alfila ta ce, "ina so kiyi ta jarraba harbin wannan mutum-mutumin, amma a tsakayar idanunsanake son kwarin ki ya cake". Nan fa Alfila ta samu aikin yi ta yi ta jarraba cake idanun mutummutumin, amma ta kasa. Sai da ta shafe sama da sa'a biyu tana ta jarrabawa sannan daga karshe ta yi nasara. A dai dai wannan lokaci asuba ta riske su. Basu kwanta sunyi barci ba sai bayan sunyi aallar Asuba har Alfijir ya keto, ai kuwa suna kwanciya sai barci mai nauyi ya dauke su, sakamakon gajiya dake jikinsu da kuma dadewar da sukayi a jiyan basu yi barci ba. Bayan rana ta take sosai, suna cikin yin barcin ne a cikin kogon dutsen sai kawai suka ji wani irin gurnani mai ban tsoro. Cikin firgita suka farka, ai kuwa sai Alfila ta yi arba da wani katon biri tsaye a gabanta. Cikin zafin nama Alfila ta dauki kwari da bakanta, ta dana zata harbrshi, sai Humaira ta daka mata tsawa ta haneta. Humaira ta mike tsaye ta nufi inda birin ya ke tsaye va tare da shakkar komai ba, suka tsuarawa juna idanu shi da ita. Al'amarin da ya baiwa Alfila mamaki ke nan, ta fara kiran sunan Humaira tana cewa, "ki daina kusantar wannan birin kada ya cutar dake fa". Ita dai Humaira bata saurari nasihar Alfila ba har ta isa daf da birin ta dafa kafadarsa, kawai sai birin ya risina a gabanta yana mai nuna alamin biyayya. Cikin murna Humaira ta waigo ta dubi Alfila ta ce, "ai wannan birin ba mai cutarwa bane a garemu, domin shi ne wanda ya ceci rayuwar mu ni da sarki Sahibul Hairi a lokacin da mahaifinsa ya kamamu ya kaimu gidansa ya kullemu cilin wani keji, muka kasa budewa mu gudu. Hakika mun samu mataimaki na uku a wannan yaki".Koda jin wannan batu sai fuskar Alfila ta fadada da murmushi, ta cika da farin ciki. Ba tare da 6ata lokaci ba su Humaira suka shiryawa kansu abincin kalaci, suka kimtsa cikinsu. Bisa mamaki sai suka ga wannan bitin yana tande baki, don haka sai suka zuba masa abincin suka mika masa. Ai kuwa sai ya kama ci sosai tamkar ya sami ayaba. sabo da mamaki sai abin ya baiwa Alfila dariya, ta rinka kwakwatawa. ko da birin yaga Alfila na yi masa dariya sai shima ya kwaikwayeta, ya wangame baki zai yi dariyar, amma sai dariyar tasa ta zamo abi. tsoro, domin tayi kama da kukan jaki. Cikin firgici Alfila ta ruga izuwa bayan Humaira ta 6uya, domin azatonta birin so yake ya cutar da ita. Ko da ganin haka sai Humaira ta bushe da dariya, sannan ta dubi Alfila ta ce, "saki jikinki ya ke 'yar uwata, ai ba cutar dake zai yi ba, wasa yake miki shima kwaikwayon dariyar ki ya yi. Nan take sai Humaira ta kama hannun Alfila ta jata izuwa wajan birin ta kama hannun birin ta hada da na Alfila, suka gaisa. Biri. ha jinjina hannun Alfila ya yi dan tsalle yana mai nuna alamun sun zama aboki da kawa. Koda ganin haka sai Alfila ta cika da farin ciki. Nan take Humaira ta shiga cikin kpgo. dutsen ta yk damarar yaki, ta dukkanin makamai a jokinta ta fito, koda ganin haka sai itama Alfila ta shiga ta dakko kwari da. aka ta rataya, dama ta tanadi wani karin kuttun kwari a cike shima ta ratayashi a kafadarata. yayin da wannan birin yaga su Himaiara sun debo makaman yaki sai ya fuskanci cewa lallai yaki zasu tafi, sabo da hama shima sai ya sunkuya ya dauko wadansu dogwayan itatuwa guda biyu,daga fikakke mai tsini, daya ba fikakke ba. ko da gani. haka sai Humaira ta dubi birin tayi murmushi ta cee, "lallai kaima zaka bada gudummawaka a yakin daukaka kalmar Allah ". kamar birin yaji abin da Humaira ta fada sai yayi gurnani kuma ya. risina a gareta. Humaira ta dubi Alfila ta ce, "ni ce zan wuce gaba ke da wannan birin ku bini a baya, duk Inda nasa kafa kuma ku sanya naku. ki yiwa biri. nan birin nan jagora kada ki bari ya wuce ki har mu isa inda za muje mu ceto rayuwar su Sarki Sahibul Hairi. Duk inda na umarceku da tsayawa ku tsaya komai runtsi da tsanani kada ku ketara umarnina kinji ko?" Alfila ta ce, "naji 'yar uwata I. Allah ya yarda ba zamu ketare ba". Koda jin haka sai Humaira ta karanta wadansu addu'oi tana mai neman taimakon Allah, sannan ta wuce gaba ta durfafi cikin dajin tana mai yafito Alfila da hannu. ko da ganin haka sai Alfkla ta. kama ta kama hannun wannan biri ta jashi suka bi bayan Humaira. Duk inda Humaira ta dauke sawuta nan Alfil da birin ke sanya nasu,domin kada su taka inda zasu ta6a mugayen tarkunan da suka kafa. . SARKIN SARAKAI Littafi Na Huɗu (4) Part E. . Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa HAKA DAI SUKA WANZU SUNA TA KETA DAJIN HAR TSAWAN LOKACI, SANNAN SUKA ISO KUSA wannan katon tsauni wanda suka hango gida. dutse a kansa. cikin sauri suka kwanta kasa cikin ciyayi suka 6uya, domin sun hango mugayen halittun nan masu kama da dodanni akan tsaunin rike da makaman yaki suna ta kai kawo akan tsaunin, don tabbatar da. tsaro. Humaiara ta kurawa halittun idanu da kyau ta yi nazarin yawansu ta tabbatar da cewa adadin su ya wuce misali sai ta yi shiru tana tunani. Daga can sai ta dubi Alfila ta ce, "yake 'yar uwata abin da. ake so daku shi ne ku ci gaba da 6uya a nan cikin wannan ciyawa, ni zan tafi na tunkari wannan gida da izinin Allah sai na shiga har cikinsa na fitl da su Sarki Sahibul Haifi, kada ku kuskura ku biyo bayana, ku kawai ku zuba ido da zarar kun hango mu a guje ni da su sarki Sahibul Hairi ku tashi ku ruga baya da gudu izuwa can baki. kogon dutsenmu. Ku tabbatar da cewa baku taka inda tarkunan zasu cutar ba ku ba". Sa'adda Alfila taji wannan batu sai tayi murmushi gami da gyada kai tana mai nuna alamun gamsuwa da fahimta. Nan take Humaira ta goy i wani dankarami. mutum mutumi a bayanta ta daure shi tamau, sannan ta zare takoninta guda biyu ta dirfafi wannan tsauni kai tsaye a guje tana mai kabbara. Tun daga nesa da mugayen halittun nan masu kama da dodanni suka hango Humaira ta taho da gudu izuwa kan tsaunin taka kwala kabbara sai suka fara harbo mata kibau, tamkar ruwan sama ake yi. A nan fa Allah ya nuna ikonsa, domin sai gashi Humaira tana kade kibiyoyin da takobin hannunta, ba'a samu daya data soketa ba, duk da cewa yawan kibiyoyin ya wuce musali. Wasu kibiyoyin ma sai sun taho izuwa kanta sosai, amma sai kaga sun juya akala sunje sun cake a kasa. Kai da ganin wannan al'amari kasan cewa kariya ce daga Allah ba wai dabarar Humaira bace. Lokacin da mugayen halittun suka ga sun kasa harbin Humaira kuma sai dada tunkararsu take, sai suma abin ya basu mamaki, don haka sai da yawansu suka zare takobinsu suka rugo da gudu izuwa kasan tsaunin, domin su tareta tun gabanin ta isa kan tsaunin. Kaico! hakila ta kai mace mai kamar maza, komai jarumtakar namiji idan yaga wadannan mugayen halittu a wannan lokacin dole ya razana saboda sun kasance manya-manya masu kirar sadaukantaka da mutukar muni, sannan gashi yawansu ya wuce misali tamkar fasa kasa suke suna fitowa suna dada karuwa, amma duk da hakan bai sa Humaira ta razana ba bare ta juya da baya, kawai ma sai ta kara karfin gudunta tana ta dauki. ta riske su kafin su risketa Ai kuwa tana shiga cikinsu ta hausu da sara da suka, su kuma suka yanyameta suna masu kai mata hare-haren, amma saboda karfi da zafin nama irin na Humaira sai gashi tana daddatsasu suna zubewa kasa tamkar tana sassabe a gona. Duk inda ta sa gaba sai kaga tana samarwa da kanta hanya, kuma bata fasa gudum ba, suka rasa yadda zasuyi da ita. inbadda ihun halittun babu abi. da kunne ke ji sai karar karafa. Nan fa Humaira ta ci gaba da saran halittun, sai dai kaga sassan jikinsu na shawagi a sama, jini kuwa ya rinka tsartuwa a sama daga kofofin jikinsu yana fantsama da malala a kas. kafin kafi. Humaira ta isa kan tsaunin gaba daya jikinta ya rine da jini har fuskarta tamkar wadda aka tsoma a cikin kogin jini. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki face yadda mugayan halittun suke da mugun naci, gashi sjna ganin Humaira na ta kashe 'yan uwansu amma ko tsoro basa ji, sai dada rugowa suke izuwa gareta. Da karfin tsiya Humaira ta iso har gaban kofar gidan dutsan da ke kan tsaunin. Da zuwa tayi arba da kofar gidan a rufe kuma an ginatane da wani mulmulallan karfe wanda daga ciki yana dauke da skatoci guda tara, wanda dole sai an zaresu sannan kofar zata budu. koda Humaira tayi nazarin kofar taga bazata budu ba da karfin damtse, sai ta shiga karanta wata addu'a da ban ta musamman tana mai ci gaba da yaki harta kusa ta iso daf da kofar. Da zuwanta sai tasa kafarta guda ta naushi kofar, take kofar ta tum6uko daga jikin ginin dutsan ta fadi kasa rikica. Gaba daya sai da gida. ya girgiza tamkar zai ruguje. Ganin wannan abu daya faru dukkanin mugayen halittun suka firgita ainun da jarumtakar Humaira suka jajja baya daga gareta, suka kama nokewa. Humaira ta wuce kai tsaye izuwa cikin gidan tana dube-dube. Duk wannan gumurzu da ta sha fama haryanzu tana goye da wannan mutummutumi a bayanta, kuma a lullu6e yake ba'a ganin ko menene. Da shigar Humaira ciki. gidan sai tayi arba da sarki Barusa zaune bisa kasaitacciyar karagar mulki yana kallonta cikin murmushi. Kawai sai ya mike tsaye ya kama yi mata jinjina, yana mai cewa, "Lale marhaban da babbar jaruma, 'yar ma'abota addinin musulinci. Bani abin. da nake bukata kema na baki abin da kikazo nema". Humaira ta kalli Barusa cikin raini ta ce, "ta ya ya zan baka abin da kake bukata alhalin ni kuma banga wanda nazo dominsa ba?". Koda jin sai sarki Barusa ya kalli shugaban wadannan mugayan halittu dake tsaye daf da shi. Take shima ya dubi wadansu yaransa guda biyu sai sukaje izuwa cikin wata kofa. Jim kadan sai gasu sun fito da sarki Sahibul Hairi da Bwa Haluf a daure tamau, cikin wannan murtukekiyar sarkar karfe ta sihiri Kallo daya Humaira taiwa darki Sahinul Hairi ta fuskanci sun sha muguwar wuya, domin duk jikinsu rauni ne, kai da gqni kasan sun sha bakar azaba. In badan ma an tukesu ba bazasu iya tsayawa bisa duga-dugansu ba, domin layi suke yi kamar zasu 6ingire kasa. cikin tsananin fushi Humaira ta kwance goyon da ke bayanta ta cillawa sarki Barusa mutum-mutumin a kirjinasa tana mai daka nasa tsawa ta ce, "Ban zo da Alfila ba kuma sai na tafi dasu sarki Sahibul Hairi". ko da jin haka sai sarki Barusa ya fusata ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa, kamar zata kone. Daga can kuma sai ya fashe da mahaukaciyar dariya ya ce, "yanzu ni zaki rainawa hankali kizo mini da mutum-mutumi a matsayin Alfila, kuma ki ce zaki daukesu sarki Sahibul Jairi ki tafi dasu. To ai shikenan ga fili ga mai doki, muzuba mu gani, ina. son inga yadda zaki tafi dasu alhali. ina numfashi a doro. kasa". ko da jin sai Humairat ta nufi inda su sarki Sahinul Hairi suke tsaye. Ai kuwa sai mutagun halittun suka yunkura zasu sake afka mata, sai sarki Barusa ya daka musu tsawa, suka ja baya. sai da ha rage saura baifi taku uku ba tsakanin Humaira da su sarki Sahinul Hairi, sai Barusa ya daka tsalle sama daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga baka. Tun a saman ya zare takobinsa ya kawa Humaira mummunan sara a wuya da nufin tsinka mata kai, in. a dan humaira tayi sauri ta sunkuya ba da tini ya gama da ita, amma sai takobin tasa ta sati iska, duk da haka sai da ya juya ya gabza mata naushi a fuska Take hakorin Humaira guda na tsakiyar sama yayi futar burtu daga cikin bakinta. Jini yayi tsartuwa ta fadi kasa a galabaice, domin ba'a ta6a yi mata irin wannan mugun naushi ba a rayuwarta, tabbas tasan cewa ta hadu da namijin kwarai. Ko da ganin wannan abu da ya faru ga gimbiya Humaira sai hankalin sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif ya dugunzuma ainun, suka saduda, domin sun fuskanci cewa Humaira baza ta iya ceto rayiwarsu ba a wajan sarki Barusa. Barusa ya bushe da dariyar mugunta a lokacin da ya fara kewaye Huaira wacce ke kwance a kas, shi kima na kewayeta yana bugun kasa da yakoninsa. ya ce, "maza ki fada mini inda kika 6oye yarinya Alfila ko kuma yanzun nan na sare kansu sarki Sahinul Hairi da Bawansa a gaban idanunki, sannan na dawo kanki". Sa'adda Humaira taji wannan batu sai tayi murmushi sannan ta goge jinin dake zu a bakinta ta dubi sarki Barusa ta ce, "ai kada mage ba yanka bane, zaifi kyau ka fara sare kaina tukunna idan har zaka iya, kafin kayi tunanin sare kan wasu". Kafin Barua yace wani abu tuni Humaira ta mike taaye zumbur ta gyara tsayuwarta, kuma ta daga takobinta guda biyu tana mai fuskantarsa. koda ganin haka sai Barusa ya kurma uban ihu mai firgita mazaje a filin yaki, sannan yariga kanta da dukkan karfinsa. Suka ruguntsume da azababban yaki, ya zamana cawa suna kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin nama, juriya da bajinta. koda fara wannan artabu sai Humaira ta raina kanta, domin kafin saran Barusa ya ninka nata sau uku, haka ma zafin namansa, domin a duk sa'adda da yakai mata sara ta kare da takobinta sai ta durkushe kasa dakyar kuma ta maida martani. Haka dai suka ci gaba da yin wannan gumurzu. har tsawon sa'a guda ya zamana cewa dayan su bai sami rauni ko guda daya ba amma a sannan Humaira ta gaji Likis. Shi kuwa Barusa tamkar ma a sannan ya fara gumurzu. Koda Himaira ta fahinci in dai taci gaba da wannan fada a haka sai Barusa ya sami nasara a kanta sai ta sauya salon fada ta fata guje-guje da tsalle-tsalle tana wahalar da Barusa. Nan da nan ya fara haki wato gajiya ta riskeshi. Kawai dai ya tsaya cak! a waje daya ya ki ci gaba da binta kuma ya yi jifa da takobinsa ya lumshe idanunsa yana mai karanta dalasuman tsafi sai ga kibiyoyin tsafi sun fitu da cikin hannayansa. Duk kibiyar da ta nufeta sai ta kone kurmus ta zama toka. Haka dai Barusa ya yi ta watsawa Humaira mugwayan abubuwa don ya hallakata amma bai sami nasara ba har tsawon rabin sa'a. Ana cikin haka ne Humaira ta sake yin wata addu'ar sai gidan gaba daya ya kama rugujewa, duwatsu suka dinga wadowa kasa suna danne wadannan mugwayan halittun suna mutuwa. Al'amarin da ya firgita kowa ke nan aka shiga guje-guje kowa yana kokarin ficewa daga cikin gidan har shi kansa sarki Barusa kuwa. Damar da Humaira ta samu ke nan ta karanta wata addu'ar ta shafa sarkar data daure su sarki Sahibul Hairi, take sarkar ta bace 6at! daga jikinsu. Nan take su ukun suka ruga waje da gudu a lokacin da ginin gaba daya ya karasa rugurgujewa ya nutse izuwa kafkashin tsaunin. Humaira Sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif suka gangaro kasan dutsan a guje a lokacin da shi kansa tsaunin ya kama girgiza gaba dayansa yana shirin yin bindiga ya farfashe. A wannan lokacine su Humaira suk yi arba da sarki Barusa tare da mugayan halittun a tsaitsaye a can gefe daya suna nesa da tsaunin. Koda su Barusa suka hango su Humaira suna sakkowa daga kan tsaunin sai suka rugo izuwa kansu suna harbo musu kibiyoyi. Nan fa aka kasa azababban tsere, Humaira ce a kangaba, sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf na biye da ita. Tana cikin gudun ne ta waigo ta dubi su sarki Sahibul Hairi, ta ce da su, "Duk inda kukaga na dauke sawina to ku sanya naku. Kada ku kus kura ku dorashi wani gurin daban. Ai kuwa sai suka bi wannan umarni har suka iso gurin da Humaira ta bar Alfila da Birin nan a la6e cikin ciyawa. Gama fadin haka ke da wuya sai ga su sarki Barusa sun iso, kwai sai suka tsaya daga nesa kadan aka kara kallonkallo. Dama tuni sarki Sahibul Hairi da Bawa Halif sun sami makaman yaki sun ruke. shi dai sarki Sahibul Hairi wadansu addina guda biyh ya rike, shi kuwa Bawa Haluf takobi da garkuwa ya rike. Alfila tana rike da kwarinta ta dana baka, shikuwa birin yana ruke da itatuwa guda biyu daya mai tsini daya mara tsini. A dai-dai wannan lokacine tunani ya fadowa sarki Sahibul Hairi a cikin zuciyarsa ya ce, "wai shin shi sarki Barusa wana irin sabon shiri ya yi ne alhalin ni kai na a can baya na sami nasara a kansa amma yanzu gashi na ga ya gagari wacce ta gagareni?" Bayan an yi kallon-kallo tsakanin sarki Barusa da Humaira sai Barusa ya daga hannusa sama yana mai bada umarni a afka musu. Nan take mugayan halittun nan suka zare muggan makamansu suka ruga kansu sarki Sarki Sahibul Hairi suna ruri da kururuwa. Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf, Alfila da birin suma sai suka ruga kan mugayan halittun suka ruguntsume da azababben yaki. . AA Misau Ke Magana SHIN WAZAI SAMI NASARA A WANNAN AZABABBAN YAKI DA AKE GWAZAWA. . SHIN SARKI SAHINUL HAIRI ZAI CIMMA BURISA KUWA. . WACCE SHAWARA ZAI YANKE AKAN KARBAR ADDININ MUSULINCI? . A WANE HALI SARKIN BARAYI ZAI KASAN CE TUNDA ANBATA MASA TARIHINSA NA SATA? . A WANE HALI AMINUL HAS YAKE CIKI. . Mu Hadu A Littafin Sarkin SARKIN SARAKAI Littafi Na Biyar (5). Don jin Karahen wannan littafin Sarkin sarakai Littafi na Hudu 4 Na Abdulaziz Sani m Gini Typing:- Alamin Ahmed Misau Ebook creator:- Shuraih 99% . You can download more Adventure hausaebooks at http://shuraih.waphall.com Domin downloading na wasu littatafanmu amatsayin eboook sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan adireshi www.shuraih.waphall.com SARKIN SARAKAI Littafi Na Biyar (5) Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Shuraih Usman Daga:- http://hausaebooks.cf . Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini AA Misau Ke Magana . Labari ya isowa AA Misau cewa.. LOKACIN DA AKA RUGUNTSUME DA AZABABBAN YAKI TSAKANIN wadannan Halittu da sarki Sahibul Hairi, sai gurin gaba daya yaruguntsume yazama babu Kyan gani, banda ihun Halittun da karar karafuna babu abinda make iya ji. kura kuwa ta turnuke dajin gaba daya. Nan sarki Sahibul Hairi, da Bawa Haluf da yarinya Alfila suka zame musu alakakai, domin duk Inda suka durfafa sai kaga Halittun suna zubewa kasa. A duk lokacin da sarki Sahibul Hairi ya sari Halittun sai kaga suna rabewa biyu yana tsargesu idan wiyansu ya Sara sai dai kaga Wiyan ya fita fit yayi same sannan ya fado kasa. Shima wanan gwaggwan birin haka ya rinka ragargazar Halittun da wadannan dogayan itatuwa guda biyu da ke hannunsa. Ita kuwa yarinya Alfita kan wata doguwar bishiya mai tsawon gaske ta hau harta isa izuwa karshanta sannan ta ci gaba da harbin Halittun da bakanta tana sakar musu kibiyoyi, sai dai kaga kibiyoyi na cakewa a cikin idanun Halittun, ko a wiya ta samesu sai kaga sun fadi kasa matattu. Duke wannan Abu da ke faruwa sarki Barusa da jaruma Humaira na tsaye a can gefe da gefe suna kallon juna kuma suna kallon abida ke faruwa. Koda sarki barusa yaga irin gagarumar barnar da akai masa, wato yaga wannan Dakar nasa suna zubewa kasa ya zamana cewa a kaso uku babu kaso biyu sai ya harzuka ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa sanna ya rugo inda jaruma Humaira ke tsaye domin ayi ta ta kare. Ya yin da Humaira taga sarki Barusa ya dirfafo a guje rike da takobinsa sai itama ta ruga gareshi tana mai kwala kabbara Kuma ta zare takubbinta guda biyu. Suna haduwa suka kacame da azababban yaki suna masu kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama, juriya da bajinta. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda suke da mutukar zafin name tankar jikinsu bana jini da tsoka bane, kai kace na karfe ne. Sai

Chapter 15 of 19