Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kece da dariyar mugunta, kawai sai ya mike tsaye daga kan karagar mulkin yana mai sauya kamanninsa izuwa ainihin siffar gimbiya shukura matar sarki barusa koda ganin haka sai humaira dasu sarki sahibul hairu suka cika da tsananin mamaki, sahibul hairi yai ajiyar zuciya yace, haba ni fa naji ajikina sa adda na gaisa dake na kama hannunki, tabbas ba hannun namiji na kama ba hannun mace ne, ashe kece kika yaudaremu yaya aka yi kika rigamu zuwa wannan gari harkika yi mana wannan mugun tanadi, kuma yanzu ina alfila da mahaifinta ? Koda jin wannan tambaya sai shukura ta bushe da dariyar mugunta sannan tace ai a halin yanzu tuni yarinya alfila anyi tafiyar kwana arba in da ita a sararin samaniya an tafi da ita can inda baku isa ku jeba har abada naso na sami damar hallakaku cikin ruwan sanyi ba tare da kun ankara ba, amma sai wannan hatsabibiyar humaira ta gano dukkan makircina to idan kun san wata baku san wata ba, lallai idan hagu taki sai a koma dama a yau dai, kuma a yanzu, banga ta yadda zaku iya tsira ba daga sharrina ban ga wanda daga cikinku ya isa ya hanani na zama sarkin sarakunan duniya ba tap ! Babbar Magana Jin wannan kalami yasa Nima AA Misau na dakata a wannan gaba kuma nake cewa Sai allah Ya kaimu gobe zan cigabBANGA WANDA DAGA CIKINKU YA ISA YA HANANI NA ZAMA SARKIN SARAKUNAN DUNIYA BA, Sai nafi dukkanin sarakunan duniya matsayi, mulki da arziki, mutane da aljanu duk sai sun zamo a karkashin ikona ya zamana cewa ina sarrafa duniyar nan gabaki dayanta akan tafin hannuna, batun awaisu da sarkin wannan gari kuwa duk suna cikin mugun hali na tsakanin RAI DA MUTUWA, sai hukuncin da na yanke musu idan naso su rayu , idan naso kuma su hallaka a cikin yan dakiku zan kashesu kafin gimbiya shukura ta rufe bakinta sai humaira ta daka masa tsawa tace ke tsohuwar munafukar Allah, algunguma, maci amanar mijinta kiyi sani cewa ba ayi duniyar nan domin ku kadai ba batattu ma abota shirka da izinin ubangijina ba zaki cika wannan mugun buri naki ba cikin tsananin fushi shukura ta tari numfashin humaira tace aishikenan ga mai fili gamai doki, sainaga wanda ya isa ya hanani ida abin dana soma, nan take shukura ta dakawa wadannan samudawan dakaru nata tsawa tana mai umartarsu dasu afkawa su humaira ai kuwa sai dakarun suka zare makamansu sukayi caa a kansu aka ruguntsume da azababben yaki a tsakiyar fadar shukura ta koma kan karagar mulki ta zauna tana mai harde kafa cikin nishadi ta zuba ido kawai taga yadda karshen wannan yaki zai kasance haka dai wuri ya gama yamutsewa karar karafa da cika dodon kunne gami da ihun mazaje, dakarun suka lullube su humaira suka yanyamesu tamkar an ajiye kwayar hatsi guda daya a tsakiyar miliyoyin tururuwa duk inda humaira da sarki sahibul hairi suka durfafa saidai kaga suna tarwatsa dakarun suna ragargazarsu suna zubewa kasa, amma abin haushi shine dakarun basa mutuwa duk wana ya fadi kasa koda kuwa an daddatsa shi yayi filla fill saikaga komai na jikinsa ya koma ya hade tamkar ba a taba gididdibashi ba, sannan ya mike zumbur ya cigaba da fafatawa al amarin da ya matukar dugunzuma hankalin su sarki sahibul hairi kenan domin sun fahimci cewa wadannan dakaru basa gajiya, kuma muddin aka sami tsawon lokaci ana wannan fafatawa a haka tabbas zasu iya gajiya har dakarun su sami lagonsu Al amarin bawa haluf kuwa tuni a wannan lokaci ya fara gajiya in ba don ma humaira da sarki sahibul hairi na kareshi ba da tuni dakarun sun hallakashi ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin dakarun ya sababa ta bayan bawa haluf ya dankara masa sara a gadon baya da takobi nan take bayan nasa ya dare, jini yai tsartuwa haluf ya kurma uban ihu ya sulale kasa sumamme koda ganin abinda ya faru ga bawa haluf sai sarki sahibul hairi ya fusata ainun yayi kururuwa mai firgita maza wacce tasa dakarun suka jajja da baya a tsorace cikin zafin nama sarki sahibul hairi ya sunkuyo kasa ya dauki takobin bawa haluf ya hada guda biyu kenan a hannunsa ya sake rugawa kan dakarun yaci gaba da saransu tako ina AA Misau Ke magana gabas da yamma kudu da arewa suna zubewa kasa tamkar yana ta adi a gonar kabewa amma duk a banza domin ba sa mutuwa sai dai kaga suna mikewa kamar a sannan aka haliccesu koda aka sake samun gushewar lokaci sai dakarun suka shammaci sahibul hairi suka yankeshi har a waje biyu a lokaci guda yanka na farko a tsakiyar kafarsa ta hagu, daya yankan kuma akan cinyarsa ta dama, duk da juriya irin ta sarki sahibul hairi sai da ya kwala ihu ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa, a lokacinne yaji wani irin jiri ya debeshim idanunsa suka kama lumshewa suna gani dishi dishi kwai sai ya tafi kasa luuu ! Zai kife Ba zato ba tsammani sai yaji an rukoshi da hannu Daya anyi cilli dashi izuwa can saman tudu kusa da karagar mulki inda gimbiya shukura ke zaune Ba wani ne yayi wannan bajinta ba face humaira, cikin zafin nama humaira ta sake daukar bawa haluf wanda ke kwance a kas sumamme tamkar gawa shima ta cillashi inda ta cilla sahibul hairi ya zamana cewa saura ita kadai a tsakiyar wadannan dakaru Kawai sai ta fara jaranta wata addu a ta musamman kuma ta kutsa cikin tsakiyar dakarun taci gaba da gididdibasu Wannan karon kuwa sai labara ya sha banban domin duk wanda ta sara ya fadi kasa baua tashi sai dai kaga ya kama da wuta ya ruburbushe ta zama toka Koda gimbiya shukura ta hango abinda ke faruwa ga dakarunta sai ta fusata ainun ta mike zumbur daga kan karagar da take zaune ta zare takobinta ta daka tsalle daga inta take tamkar an janyeta da majajjawa ta dira a inda bawa haluf yake takaimasa suka da takobinta a cikinsa da nufin ta maidashi gawa Cikin matukar zafin nama sahibul hairi ya daka tsalleya kai masa dauki da nufin ya kade takobin shukura Maimakon takobin tata ta soki bawa haluf sai ta soki sahibul hairi a gefen kirjinsa tabullo ta gadon bayansa Sahibul hairi ya kwala ihu a karo na biyu ihu mai karfin gaske wanda yasa humaira ta juyo a dimauce ta kalli abin da ke faruwa kawai sai tag a sa adda shukura ta zare takobinta dafa cikin kirjin sahibul hairi sannan ta sake daga takobin tata sama zata fille kan sahibul hairi tamkar an harbor kibiya daga cikin baka humaira ra dako wawan tsalle sama ta baro cikin wadannan dakaru Kafin takobin shukura ta kai wuyan sarki sahibuk hairi tuni humaira ta doki kirjin shukura da kafafunta biyu saboda karfin dukan said a shukura tayi tsalle sama ta gwaru da bango ta fado kasa a galabaice jinni na yoyo a hancinta Koda shukura ta shafa hancinta taga jinni sai ta kwarara wani irin uban ihu tankar saukar aradu Take wata irin tsawa ta sauka akan wadannan ragowar dakaru yaki na ta kawai sai duk suka fadi kasa matattu dayansu bai tsira ba Shukura ta mike tsaye a fusace ta tnkari inda humaira take tsaye koda ta kusa zuwa kusa da ita sai ta tsaya suka fara kallon kallo irin wanda ke nuna KAR TA SAN KAR a wannan lokaci sarki sahibuk hairi na kwance a kas magashiyan yana nu,fashi sama sama kai da gani ka san cewa abu ne mawuyaci ya rayu domin har a sannan jinni ne ke bulbulowa ta cikin gefen kirjinsa inda shukura ta sokeshi da takobi Da kyar da makyarkyatar hannu ya cisgi suturar jikinsa ya dora akan raunin kirjin nasa ya danne raunin don tsaida jinni AA Misau Ke Magana Bayan anyi kallon kallo na yan dakiku tsakanin humaira da shukura sai shukura ta bushe da dariya sannan tace yake wannan jaruma mai taurin rai a hatsabibanci kiyi sani cewayau kin gamu da dai dai dake domin niba sarki Barusa bane kuma ni ba shamzubul azwas bane Yadda duk kike tsammani na na wuce nan yau shekarata goma sha uku kenan ina tanadin wannan rana ta haduwa da ke domin tun-tuni nayi bincike a cikin tsafina na gano cewa ke kadai ce zaki iya kawo mini matsala a cikin kokarin cika burina na son zama SARKIN SARAKAN DUNIYA. Hm AA Misau Ke Magana, Ina tabbatar miki da cewa duk abin da kike takama da shi baki fini ba idan karifin damtse ne da jarumtaka kike takama da shi ai yanzu zamu fitar da raini, idan kuwa takamarki ki nemi taimakon ubangijin musulunci to ki sani cewa baki fini sanin ubangijin musulunci ba Ki sani cewa ni asalina na fito ne daga zuri’ar sheik abul nasir na birnin misra, mahaifiyata ce babbar ‘yarsa, don haka an haifeni a cikin musulunci, kuma na girma a cikinsa na sami karatu da ilimi mai yawa a wajen kakana Tun a wannan lokaci bani da burin da ya fi na sami matsayi da daukaka irin wanda babu wani mahaluki daya sameshi a duniya A lokacin da kakana Abdul nasir ya rasu ina da shekara goma sha hudu a duniya kawai sai aka wayi gari aka nemeni aka rasa domin sulalewa nayi na gudu na bar birnin misra a cikin dare Daga wannan rana ba a sake jin duriyata ba sai na bazama a duniya na rinka farautar abubuwa uku Abu na farko shine, ilimin addinin musulunci , duk da cewa na sami mai yawa a wajan kakana, amma sai na ci gaba da neman kari Abu na biyu sai na dinga ziyartar bokaye ina yi musu bauta suna bani iliminsu Abu na uku na dinga koyon fada da yaki a wajan sarkin yaki na kasashe daban daban Sai da na shekara shida ina wannan yawo a duniya ina koyon abubuwa ukun har said a na tabbatar da cewa na sami kowanne isashshe kamar yadda ya kamata sannan na fara bincike a hallarar tsafina akan yadda zan sami nasarar cika babban burina na duniya A cikin binciken nawa ne aka nuna mini cewa bazan taba samun nasara ba face na fara auaran daya daga cikin manyan sarakunan duniya Bisa wannan daliline naje birnin sarki barusa na zamo daya daga cikin dakarunsa na yaki har jarumtakata da kyawuna suka burgeshi ya aureni A wajan sane na sami labarin boka shamzubul azwas da batun yarinya alfila a sannan ne na gano cewa ashe iyakar amfaninsa kenan a wajena wato na san mataki na karshe da zan cika burina Koda na sake yin bincike a tsafi sai aka nuna mini zuwan sarki sahibul hairi domin ya dauki gatarin sihiri na mijina sarki barusa Koda ganin hakan saina cika da farin ciki domin nasan cewa lokaci yayi d azan rabu da sarki barusa na bi sarki sahibul hairi domin na mallaki yariny alafila wacce a jikinta ne zan sami sirrin tsafin da babu kamarsa a duniya Abinda dukkan matsafan duniya basu gano ba shine, yarinya alfila ta taba shan wani tsumin tsafi na sarkin aljanu wanda ya yi zamaninsa kimanin shekaru dubu dari biyu da arba’in baya Shi dai tsumin tsafin a hannun wata jikarsa yake wacce wara rana ta fita yawon shan iska sai ta shiga gonar wani azzalumin bakin aljani ta tsinka amfanin cikinta, ashe yasa guba a jikin duk amfanin gonar saboda maganin masu yi masa sata Ai kuwa sai wannan aljana ta kama aman jinni da kyar ma ta bude fukafukabta tayi sama ta bar cikin gonar ta fada daji tna shure-shure AA Misau Ke Magana A wannan lokaci tsumin tsafin na cikin wata batta dake rayaye a wuyanta, amma saboda dafin day a shigeta yaci karfinta sai ta kasa cire battar tsumin daga wuyanta tasa a bakinta tasha Tana nan kwance a kas tana shure shuren mutuwa sai ga mahaifiyar alfila tazo giftawa ta wajan ta dawo daga daji samo itace A wannan lokaci alfila bata fi shekara biyu bad a haihuwa mahaifiyar na goye da ita a bayanta kuma a sannan rana ta take matuka duk su biyun suna jin kishirwa Mahaifiyar alfila sauri take ta isa cikin agri domin ta nemi ruwa ra shayar da kanta da yarta koda mahaifiyar alfila taga wannan aljana a kwance tana kakarin mutuwa sai ta firgita ainun ta yunkura zata gudu cikin karfin hali aljanar tace kada ki gujeni yake wannan bil’adama a wannan lokaci da nake neman ceto Na rokeki daki zoki cire battar dake wuyana ki budeta ki tsiyaya mini rowan cikinta a bakina Idan kika yi min haka nima zanyi miki sakayya da abinda duk duniyar nan babu mai irinsa Koda jin wannan batu sai mahaifiyar yarinya alfila ta tsaya cak a waje daya Jikinta na karkarwa saboda tsananin tsoro tana tunanin tabi umarnin wannan aljana ko kuma ta gudu Daga can sai ta yanke hukuncin ta taimaki aljanar koda kuwa tarkone tayi mata domin ta cutar da ita Hunnunta na karkarwa taje ta durkusa akan aljanar sannan ta cire nattar daga wuyanta ta budeta tasa mata a baki tasha rowan Faruwar hakan keda wuta sai aljanar tayi kumallo na wannan dafi da taci a jikin amfanin gonar Nan take ta sami lafiya ta mike zaune daram kamar wani abu bai taba samunta ba Aljanar ta dubi mahaifiyar alfila tayi mata godiya sannan sai ta karbi battar daga hannun mahaifiyar alfila ta girgiza taji rowan dake ciki dan kadanne bai wuce makarwa uku ba Aljanar ta girgiza kai gami da ajiyar zuciya tace kinga wannan ruwan dake cikin wannan battar maganin kowacce irin cutace kuma sinadarine na sihirin tsafi wanda babu kamarsa a duniya Wanda duk ya sha wannan tsumi babu wani makami da zaiyi tasiri a jikinsa kuma duk irin matsayin da mutum ke son kaiwa a duniya sai yah au Na gaji da wannan tsumi ne a wajen kakana kuma duk duniya babu mai irinsa sai ni kadai bincike ya nuna cewa nan gaba bazan kara shekara goma ba a duniya zan mutu kinga kenan idan na mutu babu mai sauran wannan sihiri face wanda na baiwa ragowar wannan tsumi yasha saboda haka ni yanzu zan baki ragowar tsumin ki sha albarkacin taimakon da kika yi mini kika ceci rayuwata dama kuma gashi na fuskanci kina fama da kishirwa lallai wannan tsumin zaiyi miki maganin kishirwar Sa adda a;jamar yazo nan a zancenta sai mahaifiyar alfila tce ai duk yadda nake son kaina bai kai yadda nake son wannan yar tawa ba wadda na goya a bayana saboda haka indai kin bani wannan tsumin ita zan baiwa tasha AA Misau Ke Magana Aljanar ta jinjina kai tace ai zabi na gareki amma ki sani cewa duk wanda ya sha wannan tsumin tsakanin keda ita sai ya fuskanci wata matsala guda daya idan kece kika sha tsumin ba zaki yi nisan kwana ba a duniya idan kuwa itace tasha zatayi nisan kwana a duniya amma zata rabu da ke tun tana karama kuma idan ta fara girma matsafan duniya zasu saceta daga wajan ubanta saboda su cire sihirin tsafin dake jikinta amma a karshe sai ta daukaka a duniya Lokacin da aljanar tazo dai dai nan a zancenta sai mahaifiyar alfila tace ai kuwa indai hakane na zabi yata ta sha wannan rowan tsumin Koda jin haka sai aljanar ta bude bakin alfila ta dura mata wannan ragowar rowan tsumin ta shanye, sannan aljanar ta gargadi mahaifiyar alfila akan cewar kada ta kuskura ta gayawa kowa wannan al amari day a faru a tsakaninsu Koda gama fadin haka sai aljanar tab ace bat Daga wannan rana mahaifiyar alfila tayi shiru da bakinta bata taba gayawa kowa ba sai a ranar da ta kwanta cutar ajali Koda ta fahimci cewa ciwonta bana tashi bane sai ta sanar da mijinta sadauki awaisu duk abninda ya faru tsakaninta da wannan aljana a daji Aikuwa wannan shine babban kuskuren da tayi domin inda bata fada masa ba babu yadda za a yi sauran matsafan duniya su san da batun tsumin tsafin dake jikinta har suyi kokarin cireshi daga jikinta Ina son ki sani cewa boka shamzubul azwas shine matsafi na tara wanda yayi kokarin cire sihirin tsafin dake jikin alfila amma sai kuka je kuka tarwatsa masa shiri Yanzu nice matsafiya ta goma wacce zata cire wannan sihirin tsafi daga kikin wannan yarinya kuma ba makawa saina sami nasara domin ku baku isa ku hanani ba………………….. . YANZU NICE MATSAFIYA TA GOMA WACCE ZATA CIRE WANNAN SIHIRIN TSAFI DAGA JIKIN ALFILA KUMA BA MAKAWA SAI NA SAMI NASARA DOMIN KU BAKU ISA KU HANANI BA yake humaira ki dubi abokan tafiyarki Sarki sahibul hairi da bawansa haluf ga su nan duk a kwance magashiyan sun kasance ragowar mutuwa ke kadaice kika rage kuma kike nema ki zame mini matsala, tabbas ba zaki zame mini matsalar ba domin yanzun nan zan hallakaki sannan na tafi can fadata in da aka kai alfila aka ajiye mini na cika burina a kanta koda shikura ta zo nan a zancenta sai humaira ta tari numfashinta ta daka mata tsawa tace yake wannan munafukar Allah hakika ire irenku annobace a doron kasa domin kun san gaskiya kun taketa, kyma irin azabar da Allah zai yi muku idan kuka koma gareshi ta musamman ce lallai ba zan bari ki je ki ida wannan nufi naki ba idan kika ga kin fita daga cikin fadar nan sai dai idan bana numfashi koda jin haka sai shukura ta bushe da dariya tace ai ga fili ga mai doki kuma inda babu kasa nan ake gardamar kokawa nima ba zan yarda na fita daga nan ba face na tabbatar keda abokan tafiyarki babu mai numfashi domin idan na tafi na barku a raye tamkar na kashe maciji ne ban sare kansa ba domin na san sai kun bini har can fadata kun tarwatsa mini shirina kamar yadda kuka tarwatsawa boka shamzubul azwas nasa Yanzu zaki san cewa shirina ba irin na shamzubul azwas bane takadarancina da hatsabibanci na ya ninka nasa sau goma koda gama fadin haka sai shukura ta daga takobinta sama tayi kukan kura ta ruga kan humaira, da ganin haka sai itama humaira ta daga tata takobin ta tareta suka ruguntsume da azababben yaki nan fa shukura ta rinka kaiwa humaira sara da suka cikin tsananin zafin naman da bata taba haduwa da sadaiki mai irinsa ba kuma saboda karfin saran duk sa adda humaira ta kare sai taji kamar katon dutse mai nauyi aka buga mata har sai ta durkushe kasa wani lokacin ma har faduwa kasa take, in ba don itama tana da zafin nama ba da tuni shukura ta hallakata al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira kenan ta tabbatar da cewa lallai yau dai kam ta gamu da gamonta babu abinda ya sa humaira takaici face ganin yadda shukura ke ta karanta addu o'i irin na addinin musulunci a lokacin da take karanto nata addu o'in domin samun nasara a tsakaninsu sahibul hairi dake kwance a can gefe daya yana ganin abindake faruwa sai hankalinsa ya fi na humaira tashi domin zuciyarsa ta karaya bisa ganin yadda wannan gumurzu ke wakana domin fadan ya nuna cewa shukura ce zata sami nasara saboda juma ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta kuma da zarar shukura ta gama hallaka humaira ya san cewa kansu shukura zata dawo wato shida bawa haluf tasu tazo kusa, haka dai humaira da shukura suka ci gaba da fafatawa babu sassauci har tsawon sa a uku shukura bata sami nasarar koda kwarzanar jikin humaira ba saboda tsananin naci da juriya irin na humaira, duk da cewa an fita zafin nama da karfin damtse, a wannan lokaci ne shukura ta fahimci cewa indai fada da makami zasu ci gaba dayi ba zata taba samun nasara akan humaira ba domin ga dukkan alamu ba karamin horo humaira ta samu ba akan sarrafa makaman yaki koda gama aiyana hakan sai shukura ta shammaci humaira ta doki hannunta da kafarta takobin ta subuce kasa itama shukura sai ta yarda tata takobin ta dunkule hannayanta biyu kuma ta gyara tsayuwa ta ce yauwa yanzu ne zamu banbance tsakanin aya da tsakuwa kuma yanzune zakisan cewa ruwa ba sa an kwando bane koda jin haka sai itama humaira ta gyara tsayuwarta kuma ta dunkule hannunta tayi kabbara ta ruga kan shukura ai kuwa itama shukura sai tayi kabbarar ta tareta suka ruguntsume da sabon masifaffen fada ya zamana cewa suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da kafa, fara hakan keda wuya sai humaira ta gane cewa shayi ba ruwa bane domin shukura tafita karfin damtse nesa ba kusa ba nan fa shukura ta rinka gabzawa humaira naushi a fuska da cikinta AA Misau Ke Magana tun humaira na kokarin kare naushin har ta kasa ya zamana cewa tana layi a tsaye tana yin baya taga taga kamar zata fadi, amma sai kaga ta cije ana cikin haka ne shukura ta gabzawa humaira wani katon naushi a fuska har wani gudan jini yayi fitar burgu daga cikin bakin humaira kawai sai ta sulale kasa magashiyan ta kasa koda motsawa bare ta mike tsaye, koda ganin haka sai shukura ta bushe da dariyar farin ciki sannan ta hau kan gadon bayan humaira ta zauna ta kai hannayanta biyu izuwa kanta da nufin ta murde mata wuya, ba zato ba tsammani sai shukura taji an daki bayanta da kafa saboda karfin dukan sai da taji kamar bayan nata ya burme kuma sai tayi tsalle can gefe daya ta fado kasa da fuska ta fasa hanci da baki jini ya kama zuba, a fusace shukura ta waigo don taga wanda yayi mata wannan dukan shammace, ai kuwa sai ta ga ba wani bane face sarki sahibul hairi, yana tsaye amma yana tangadi kamar wanda ya sha giya ya bugu sakamakon jinin dake zuba a Raunin kirjinsa bisa mamaki sai shukura taga sahibul hairi ya durkusa a gaban humaira yana duba lafiyarta jar hawaye na zuba a idanunsa domin a zatonsa ta mutu koda ganin haka sai shukura tayi murmushin mugunta sannan ta mike tsaye zumbur ta dubi sahibul hairi ta bushe da dariyar mugunta tace yau fa ga masoya biyu duk a cikin mugun hali babu wanda zai iya ceton rayuwar wani, lallai daya bayan daya zan kasheku domin ku dandana takaicin kisan gillar da zanyi muku, koda gama fadin haka sai shukura ta daka tsalle daga inda take ta dira a gaban sahibul hairi ta rinka tumurmusashi tamkar ta sami tamola harma tana fyadashi a kasa kaico yaufa ga maza a hannun mata sun kasa tabuka komai a dai dai wannan lokaci ne humaira ta farfado ta dawo haiyacinta koda ta bude idanunta taga yadda shukura ke tumurmusa sahibul hairi harma tana naushinsa akan raunin nan na kirjinsa yana jini yana ihu da kara sar hankalinta ya dugunzuma nan take humaira ta fara kiran sunayen Allah tsarkaka tana yi masa kirari tana cewa ya ubangin da bashi da kishiya kaine kayi alkawari cewar zaka kare addininka da kanka ya allah kada ka bari wannan batacciyar ta sami nasara akanmu domin addininka take son ta dakusar ya allah ka karfafani da karfi irin naka na sami nasara akanta ai kuwa humaira na cikin yin wannan addu a ne sai taji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinta irin wanda bata taba ji ba kawai sai ta mike zumbur itama ta daka tsalle daga daya ta dira a kan shukura ta cakumo gashin kanta ta baya ta rukeshi tamau tayi hajijiya da ita sannan ta fydata a kasa shukura ta baje a kasa cikin wani irin hali mai kama da rabi suma rabi mutuwa domin kanta ma ya fashe jini na zuba a tsammanin humaira shukura ta mutu don haka sai ta ruga kan sahibul hairi a dimauce ta dora kansa akan cinyarta yayinda yake numfashi sama sama kamar zai mutu cikin hanzari humaira ta dauko jakar guzurinta ta foddo wani garin magani ta zuba akan raunin da sarki sahibul hairi ke dashi ya kwalla ihu sakamakon zogi da radadin da yaji humaira ta yagi rigar jikinta ta daure raunin sahibul hairi tamau sannan ta shiga karanta addu o'i tana tofawa akan raunin nasa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta yana diga bisa fuskarsa cikin matukar karfin hali sahibul hairi ya bude idanunsa suka dubi juna sai yace yake ma abociyar kyau da jarumta kiyi sani cewa tsananin ciwon da nake ji a jikina yayi yawa don haka ba zan rayu ba mutuwa zanyi koda jin haka sai humaira ta rube bakin sahibul hairi da tafin hannunta tace yakai abin kauna ba zaka mutu ba har sai ka karbi addinin gaskiya ka sani cewa tun a ranar farko da na ganka naji zuciyata ta kamu da kaunarka don haka ba zanso ka mutu ka barni ba idan har ka karbi tayin soyayyata hannu biyu to ka karbi addinin gaskiya dajin haka sai sahibul hairi ya sake bude baki da kyau ya karanta kalmar shahada kamar yadda yaji humaira ta biyawa yarinya alfila a lokacin da ta musuluntar da ita koda humaira taji sahibul hairi yayi wannan kalma sai ta cika da tsananin farin ciki bata san sa adda ta rungumeshi ba ta fashe da kukan farin ciki AA Misau Ke Magana. A daidai wannan lokaci ne shima bawa haluf ya dawo cikin haiyacinsa koda ya ga shukura a kwance gefe daya cikin jini kuma yaga humaira rungume da maigidansa tana rusa kuksa sai shima ya kama kukan domin a zatonsa maiginda ya mutu dajin sautin kukan bawa haluf sai sahibul hairi ya janye jikinsa daga cikin na humaira ya dubi bawa haluf yace kukan me kakeyi yakai amintaccen bawana ai ban mutu ba domin masoyiyata ta ceto rayuwata koda bawa haluf yaga maigidan sa a raye har yana magana sai ya rarrafo da guiwoyinsa izuwa gareshi suka rungume juna cikin tsananin farin ciki kwatsam ba zato ba tsammani sai suka ji an bushe da dariya koda suka dubi inda shukura ke kwance sai sukaga wajen ya zama wayam babu ita sai jinin kanta da ya zuba a kasa amma sun ga wata guguwa tayi sama ta fice ta cikin rufin dakin, cikin matukar damuwa humaira ta dubi sahibul hairi tace akwai sabon aiki a gabanmu kuma gashi kai da bawa haluf kuna cikin wani irin hali dolene mu zauna a nan har tsawon wadansu kwanaki domin kyi jinyar raunikan jikinku sannan mu tafi neman gimbiya shukura domin mu tarwatsa shirinta mu karbo Alfila yanzu ku jirani anan domin na shiga cikin gidan sarautar nan na nemi inda shukura ta boye mahaifin alfila da sarkinsu, koda gama fadin hakan sai humaira ta mike tsaye ta goge jinin dake bakinta da hancinta sannan ta nausa cikin gidan sarautar, sannu a hankali humaira ta isa har cikin turakar sarki inda ta iske sarki da awaisu a kwance akan gado kuma a daure da sarkokin sihiri nan take humaira ta karanta wata addu a ta tofa musu sai sarkokin sihirin suka bace bata sannan suka dawo cikin haiyacinsu suka mike zumbur a dimauce zasu ruga waje da gudu sai humaira ta daaka musu tsawa nan take ta sanar dasu du abinda ya faru garesu bisa shirin gimbiya shukura kuma ta basu labarin yadda suka zo gurin tare da alfila har shukura ta so ta yaudaresu ta hallakasu da bata sami nasara ba tayi fito na fito daasu aka Kafsa gagarumin yaki bayan tuni tasa aljanu sun dauke alfila sun gudu da ita kuma karkashin yakin sai aljanu ska sake zuwa suka dauke shukura suka tafi da ita bayan ta suma a tsammaninmu ma mutuwa tayi ashe bata mutu ba sa adda su sadauki awaisu suka gama jin wannan labari sai suka cika da tsananin al ajabi kuma hankalin sadauki awaisu ya kara dugunzuma fiye dako yaushe ya ce nikam tun

Chapter 18 of 19