Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iska mai karfi da sanyi ke kadawa koda haluf yaji sanyi yayi masa yawa sai yahada wuta a bakin tantin ya zauna yana jin dumi jim kadan da faruwar haka sai shima ya fara gyan gyadi yana jin wannan hali ne wadannan gabza gabzan mutane suka fara ketowa ta cikin duhun dare daga cikin bishiyoyi suka durfafo wannan tanti nasu sarki sahibul hairi sudai wadannan mutane sun kasance karti majiya karfi adadinsu yakai dubu dukkaninsu sanye suke da walkin fata kuma damatsansu cike suke da gurayen tsafi kowannensu na dauke da muggan makaman yaki kuma ya murtuke fuska dajan shuni kai wannan mutane dai matukar kwarjini da ban tsoro suke dan ko a mafarki mutun ya gansu sau daya har abada ba zai daina tunawa dasuba . NIMA KAINA SAIDA NAYI MAFARKINSU Cikin sanda mutanen suka iso daf da bawa haluf wanda ke ta sharar barci bai san abindake faruwa ba da zuwansu sai babbansu ya dubi mutum uku yayi musu inkiya dasu duba cikin tantin nan take kuwa mutum ukun suka shiga cikin tantin sai gashi sun fito dauke da sarki sahibul hairi a kan shimfidarsa yanata shara barci shima baima san cewa an fito dashi ba daga cikin tantin Al amarin da ya baiwa shugaban mutanen dariya kenan ya takarkare ya saki mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki karfin dariyar ne ya farkar da sarki sahibul hairi da bawa haluf daga barci koda haluf yayi arba da wadannan karti ababan tsoro saiya firgice ya yunkura da nufin ya ruga da gudu shubana kartin ya dakawa bawa haluf tsawa yace tsaya nan inda kake ko yanzun nan takobina ta sha jininka Jin wannan batune yasa haluf ya dada rudewa ya fadi kasa yana makyarkyata bai san sa adda ya saki fitsari a wando ba shi kuwa sarki sahibul hairi koda ya farka ya bude idanunsa yaga wadannan zakwakuran karti saiya kare musu kallo ya kwanta yana mai lumshe idanu da nufin yaci gaba da barcinsa tamkar baisan da tsayuwar kartin ba al amarin da ya bawa shugaban kartin mamaki kenan kuma ya fusatashi kawai ya sake dokawa sarki sahibul hairi tsawa kai waye har da zaka bude idanu ka ganmu amma baka tsorata ba? Na rantse da darajar wannan sana a tamu ta fashi yau shekara ashirin kenan muna wannan aiki ama bamu taba haduwa da wani mahaluki ba face ya razana da ganinmu kai kuwa gashi harma kwanciya kake a gabanmu da nufin yin barci, Sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya mike zaune ya fuskanci shugaban yan fashin yace yaku wadannan kartin banza masu sana ar banza kuyi sani cewa baza kusan komu suwaye ba face kunci gaba da hanamu yin barcinmu koda gama fadinhaka sai sarki ya koma ya kwanta ya sake lumshe idanu cikin tsananin fushi da kuma zafin nama shugaban kartin ya zare wata lafceciyar takobi ya kaiwa sarki sara a ciki da nufin ya tsinkashi gida biyu kafin takobin ta dira a jikin sarki sahubul hairi tuni ya goce yai tsalle can gefe daya tamkar an janyeshi da majaujawa gaba daya kartin saida sukayi mamakin wannan zafin nama da jarumtaka tashi hm kunji manyan sadaukan duniya sarki SAHIBUL HAIRI .Shugaban yan fashin ya sake rugawa da gudu kan sarki sahibul hairi da nufin ya sake kai masa sara shikuwa sai ya daka tsalle sama ya doki kirjinsa da kafa guda karfin dukanne yasa shugaban kartin yai sama ya fado kasa ya baje kamar an shanya tsumma koda ganin haka saigaba dayan dakarun nan suka zare maka mansu sukayi kan sarki sahibul hairi babu wanda ya kula da batun bawa Haluf wanda ya bude baki yana kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki nanfa karti da sarki sahibul hairi suka kacame da azababben yaki suna kai masa sara da suka yana gocewa amma duk wanda ya nausa saikaga ya zube kasa sumamme wani lokacin kuma in ya kama hannun mutum ko kafarsa sai dai kaji ya karya basss! Tamkar ya karya silin kara babu abinda zai baiwa mutum mamaki face tsananin zafin naman sarki sahibul hairi da iya kauciya da zilliya sai da aka shafe kusan rabin sa a yana turmutsa yan fashin nan amma baiyi tunanin zare makami ba da makaman nasu suka dinga sarar junansu saida yacewa gaba dayansu su dubu sun zube kasa daga matattu sai sumammu sai karyayyu shi kuwa shugaban yan fashin nan kirjinsa ya karye bai iya motsawa ba bare ya samu ikon tashi sa adda bawa haluf yaga irin wannan tsabar sadaukantaka ta mai gidansa sarki saiya cika da mamaki dukda cewa yasha jin labari a birnin misra cewa indai aka fita filin yaki sarki bai taba kasa samun galaba ba akan abokan gaba Ance idan ya fusata ma yana shafe sa a bakwai yana yaki bai gajiba kuma a duk rayuwarsa baitaba gudu ba ko juyawa abokan gaba baya yayinda sarki sahibul hairi ya gama da dukkanin yan fashin saiya dauki shimfidarsa ya koma cikin tantinsa yayi kwanciyarsa nan da nan barci ya sake kwasheshi harda minshari tamkar baiyi wahalar komai ba shikuwa bawa haluf sai idanunsa suka kekashe saboda ganin wannan masifa har gari ya waye bai sake rintsawa ba wannan shine abinda ya faru ga sarki sahibul hairi da bawa haluf bayan sun baro birnin misra da nufin zuwa birnin Askandariyya don dakko gatarin sihiri ++ A cAN birnin misra kuwa tun sa adda sarki sahibul hairi ya sallami fadawansa akan cewa ya barwa Galadima Aminul has rikon kasa sai gaba dayansu suka taru a gidan waziri Akiyanu da tsakar dare suka shiga tattaunawa ta sirri kan yadda zasu bullowa wannan lamari Waziri akiyanu ne ya fara mikewa tsaye yace yaku yan majalisar birnin misra kun sani cewa talauci ya zauta sarkinmu har ya bazama cikin duniya neman arziki labari ya isar mana cewa duk duniya babu matsafi kamar boka shamzul azwas kuma babu wani mahaluki daya taba shiga cikin wannan fada tasa wadda ke can tsuburin bahar zallas amma haukan sarkinmu da tunaninsa na shirme ya yanke hukuncin zuwa can don dauko yarinya Alfila ko shakka babu Ajalin sarki yazo dole ne ya hallaka a kokarin shiga gidan boka shamzubul azwas kaibama shiga fadar boka shamzubul azwas ba ai zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariyya ma tafi karfinsa bare har ya shiga ya dauko gatarin sihirinsu duk abinda sarki ke takama dashi walau jarumta ko tsafi dakarun sarki barusa sun ninkashi sau goma lallai idan ya shiga wannan fada saiya zama gawa wannan bayani da nayi muku yaisa ku tabbatar da cewa sarki ya tafi kenan har abada ba zai dawo ba a raye saidai gawarsa tazo yanzu gashi munaji muna gani ya bayar da karagarsa ga Aminul has mutumin da gaba dayanmu mun fishi cancanta da karagar mulkin yanzu wacce shawara kuke da ita bisa wannan lamari? Sa adda waziri akiyanu yazo nan a zancensa sai gaba daya yan majalisar su bakwai sukayi shiru aka rasa wanda zaice wani abu daga can sai wani dattijo waishi KILZAM ya gyara murya yace juyin mulki na farat daya a cikin wannan dare ! Ina nufin musa aje gidansa a kashe shi kuma a hallaka iyalansa gaba daya inyaso gobe da safe saimu nada ka sarki mu kuma ka raba mana mukamai waziri Akiyanu ya jinjina kai yace kaima kazo da shawara mai kyau amma kuma akwai matsala matsalar kuwa itace gaba dayan jama ar gari sun san cewa sarki ya bawa Aminul has rikon gari idan aka wayi gari akaga an kashe shi kuma har na hau mulki nan da nan za ayi zargin cewa ninaje nasa aka kashe shi lallai ba zamuyi gaggawar hallaka shiba dolene mu tsaya muyi tunani da hangen nesa don kada jama a suyi mana tawaye yanzu mu bari ya fara mulkin muga iya gudun ruwansa lallai nayi muku alkawarin cewa saina dawo mana da mulkin kama karya irin wanda muka saba dashi Ada kafin hawan sarki sahibul hairi' koda jin wannan batu sai farin ciki ya kama gaba dayan yan majalisar suka aminta da wannan shawara ta waziri Akiyanu sannan taro ya watse kowa ya tafi izuwa gidansa a sirrance ++ Al amarin magajin karagar mulki kuwa wato Aminul has tun sa adda sarki ya sallameshi a matsayin ya bashi rikon kasa sai ya tafi izuwa gidansa yana mai matukar farin ciki mara misaltuwa koda dawowarsa gida sai ya iske matarsa SHULAIBA tsaye a harabar gidan tana wasa da wadansu tsuntsaye dake cikin keji tsuntsayen sun kasance yan kanana ababan sha awa masu launin ruwan Kwai Tsuntsayen sun kasance yan kanana ababan sha awa masu launin ruwan kwai sulaiba ta kasance kyakkyawar mace mai karancin shekaru domin bata haura ashirin ba tun tana da shekara tara ta auri Aminul has har yanzu bata taba samun haihuwa ba koda shigowar aminul has cikin harabar gidan ya hango shulaiba a cikin nishadi saiyaji ya kara cika da farin ciki ka tsaye suka nufi juna kowannensa na murmushi ta tarbeshi cikin murna tana mai cewa yakai mijina yau kuma wanne farin cikineya samemu naga ka shigo da walwala ba kamar yadda ka saba ba kullum sa adda aminul has yaji wannan tambaya sai yakama hannayen shulaiba ya rike sannan yace ya abar kaunata kiyi sani cewa daga yau na zama sarkin birnin misra'' koda jin wannan batu sai shulaiba ta dago idonta a firgice ta soma ja da baya fuskarta cike da alamomin tsoro da fargaba ba zato ba tsammani sai idonta suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye al amarin da yayi matukar tayarda hankalin Aminul has ke nan ya matso daf da ita ya sake rike hannayenta yace yake matata ina dalilin zubar wannan hawaye naki shulaiba tayi ajiyar zuciya tace yakai mijina hakika kayi ganganci kuma kayi babban kuskure harda ka bari ka karbi rikon kasar nan a hannun sarki domin kuwa yanzu ne zaka tara makiya masu yawan gaske yanzu ne rayuwanmu zata zamo a cikin mugun hadari domin farautarta za a shiga yi ka san irin mulkin da sarki yake yi a kasar nan mulkine wanda talakawa ke so amma kuma su sarakai basa so, ina tabbatar maka da cewa wannan tafiya da sarki yayi damace babba ga sarakunan kasar nan wacce suka samu donsu dawo da mulkin zalunci da murdiya na sani cewa kai baka da irin ra ayinsu , ra ayinka irin na sarki sahibul hairi ne lallai duk yadda zasuyi suga bayanka sai sunyi ina mai shawartarka daka hakura da wannan matsayi ka mika musu abinsu yayinda shulaiba tazo nan a zancenta sai hankalin aminul has ya dugunzuma ya rasa abindake masa dadi a duniya domin tabbas ya san cewa duk abinda ta fada gaskiya ne aminul has ya sunkuyar da kansa kas yana mai tunani zuwa dan lokaci daga can kuma saiya dagao ya dubeta a lokacin shima idanunsa suka ciko da kwalla yace yake abar begena dare da rana ina sonki tuna cewa yau shekara goma sha daya kenan dayin auranmu amma har yanzu bamu sami magaji ba ki tuna cewa akan wannan matsala muka je wajan boka Hadimul Asur yayi mana bincike inda ya sanar damu akan cewa bazamu taba samun haihuwa ba face mun kwanta akan gadon sarautar kasar nan sau sittin yau ga dama ta samu donme zakice mu barta? Nikam na yarda na hakura da wannan mulkin amma bayan cikar kwanaki sittin akan gadon sarautar sa adsa aminul hass yazo nan a zancensa sai hankalin shulaiba ya kara dugunzuma fiye da koyaushe ta fashe da kuka tana me cewa hakika azzaluman kasar nan bazasu bari muyi kwana sittin ba a cikin gidan sarautar kasar nan face sun rabamu da rayuwarmu cikin tsananin tausayi aminul has yasa hannu ya gogewa shulaiba hawayanta yace ki kwantar da hankalinki abar kaunata ki tuna cewa daga yau gaba dayan dakarun sarki sahibul hairi masu tsaron lafiyarsa sun dawo karkashina ina nufin zasuci gaba da tsaron lafiyata kamar yadda suke tsaron tasa kinga kuwa ashe babu abinda ya isa ya taba lafiyata kodajin wannan batu sai shulaiba tayi yake tace haba mijina ashe ka manta da karin maganar da akace 'makashinka na jikinka' ina tabbatar maka da cewa da dangari akanci gari su dakarun da kake takama dasu aidasune za a hada kai aci amanarka yayinda aminul has yaji haka sai yayi shiruyana tunani domin ko shakka babu haka abin yake bayan dan gajeran tunani sai ya sake duban shulaiba yace ki tuna cewa mahaifinki shine mutuminda yafi kowa hikima da hangen nesa a cikin birnin misra kafin rasuwar mahaifinki saida ya zamana cewa babu abinda za a zartar face an nemi shawararsa kuma bai taba bayar da gurguwar shawara ba hatta yake yaken da ake fita ance shine yake sanar da sarki hanyoyinda ake bi a samu nasara cikin gaggawa A tarihin kasar nan babu wanda yafi mahaifinki sanin sirrin mutanen kasar da sirrin gidan sarauta yake matata nikam na sani cewa babu yadda za ayi barewa tayi gudu danta yayi rarrafe yanzu wacce shawara zaki bani wacce zata kaimu ga iya kare kanmu daga sharrin makiya har izuwa lokacinda sarki zai dawo daga wannan tafiya na damka masa amanarsa? Lokacinda aminul has ya tuno mata da mahaifinta mutuminda ake kira ABU HAKIM nan take tashiga tunani mai zurfi abu hakin ya kasance shahararren mutum ko ina a cikin birnin misra ya kasance mutum mai hangen nesa kakkaifar kwakwalwa tarin ilimi da basira saida abu hakim ya shekara sittin a duniya sannan ajali ya riskeshi abu hakim nada tsatstsauran ra ayin rayuwa fiye da sarki domin har ya rasu bai mallaki dukiyarda ta kai darajar dinare goma ba suturarsa guda biyuce kacan sai takalminsa na fada guda daya sai kuma wata sandarsa wacce duk inda ka ganshi yana tare da ita yana dogara duk da kasancewarsa ba tsoho baDuk da kasancewarsa ba tsohoba jama a sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake dogara sanda a duk sa adda yake tafiya alhali bai tsufa ba har Abu hakim ya rasu babu wanda yasan dalilin da yasa yake amfani da wannan sandan Lokacinda cutar Ajali ta kama abu hakim a wannan lokaci tuni matarsa ta dade da rasuwa kuma ta bar masa ya guda daya wato shulaiba saboda aminci da kaunar dake tsakanin sarki sahibul hairi da abu hakim saiyasa aka kawo shi cikin gidan sarauta ya zamana cewa shi da kansa yake jinyarsa sannan kuma yasa aka dinga kula da shulaiba tamkar yar cikinsa bayan kamar wata hudu da faruwar haka sai ciow ya kara tsanani wani yammaci sarki sahibul hairi da shulaiba na zaune a gaban abu hakim sun zuba masa ido suna kwalla sbd ganin halinda yake ciki sai abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya dubi shulaiba ya fashe da kuka koda ganin haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma yace yakai aminin mahaifina shin zaka iya gaya min dalilin da yasa ka dubeni kayi murmushi amma da ka dubi shulaiba saika fashe da kuka sa adda abu hakim yaji wannan tambaya saiya gyada kai yana mai alamun cewa zai iya amsa tambayar cikin karfin hali ya bude baki yace yakai wannan sarki mai adalci zanso ka tashi kafaduna ka jingina bayana a wannan gado da nake kwance domin naji dadin sanardakai abinda zai amfani rayuwarka data yata nan gaba koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya mike da sauri ya kama kafadun abu hakim ya tashe shi zaune ya jingina bayansa a jikin marikin gadon koda gama hakan sai abu hakim ya kira sunan shulaiba yace taho gareni yake yata shulaiba ta fada kan kirjinsa ya rungumeta a lokacinda duk su biyun suka fashe da kuka al amarinda ya sa sarki cikin tsananin tausayinsu kenan shima bai san sa adda ya fara kuka ba jim kadan sai abu hakim ya dubi shulaiba yace yake yata kiyi hakuri domin ciwonnan nawa bana tashi bane amma ki sani cewa ko a bayan raina baki da wani gata koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki sahibul hairi yace haba yakai wannan aminin abbana saboda me kake irin wannan furuci alhali ina raye a matsayin sarkin misra Abu hakim ya dago kai ya dubi sarki sahibul hairi a lokacinda hawaye ya subuto masa yace yakai dan aminina ina mai bakin cikin sanar dakai cewa nan gaba awasu shekaru masu zuwa saikashiga cikin wani irin mummunan hali na rashi harta kai cewa ba zaka iya daukar nauyin kanka ba bare ka dauki nauyin wani dukda cewa kana matsayin sarki A wannan lokaci jama a zasu gujeka musamman fadawanka abokanka sauran sarakai zasu kyamaceka su dinga yi maka ba a da isgilanci ka kasance mai hakuri a duk matsayin da ka tsinci kanka kuma ka jajirce wajen neman mafita amanar da zan bar maka itace ga yata shulaiba lallai ka aurar da ita ga mafi soyuwa a ranka daga cikin fadawanka wanda ka tabbatar da cewa yana kaunarka dari bisa dari kuma lallai kada ka aurar da ita a lokacin da ta haura shekara tara a duniya ina nufin ka aurar da ita nan da shekara biyu. Sa adda abu hakim yazo nan a zancensa sai sarki ya cika da tsananin mamaki yace haba ya aminin abbana saboda me kace zanyi talauci alhalin ina da matsayin sarkin misra kuma taya za ayi kace na aurar da yarka a lokacinda take shekara tara alhalin ba a taba yin haka ba a garinnan? Abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yace shin ka yarda cewa kafin rasuwar mahaifinka bashi da abokin shawara wanda ya fini sarki yace gaskiya ne Abu hakim yace shin na taba baka shawara wacce ka bita kaga ba dai dai ba sarki yace A'a to abind anake so ka gane shine abinda na sani har abada ba zaka saniba face na sanar dakai abinda zan hango har abada ba zaka iya hangoshi ba abinda nake so aidakai shine ka kiyaye da duk abubuwanda na fada maka a baya kuma kayi aiki dasu idan kana so ka cimma nasara a rayuwarka lokacin da abu hakim yazo nan a zancensa sai ya janye shulaiba daga kan kirjinsa ya dubeta yace yake yata ki sani cewa nitalaka ne babu abinda zan bar miki na daga dukiya amma zan bar miki wadansu abubuwa guda biyu wadanda indai kina tare dasu har abada keda mijinki ba zakuyi talauci ba kuma babu wani tsautsayi da zai hau kanku wadannan abubuwa biyu ba komai bane face sandata da kuma takalmina nan take Abu hakim ya dauko takalminsa a karkashin gadonda yake kwance gami da sandarsa ya mikawa shulaiba ta karba sannan yace ki boye wadannan abubuwa biyu da kyau har zuwa ranar da kikaga mijinki ya sami babban matsayi a kasar nan to a sannan ne zaki dauki wannan sanda da takalmin ki bashi kuma ki umarceshi da yayi amfani dasu ko yaushe dare da rana koda kuwa yana kwance ne a kan gadonsa ina nufin kada ya kuskura yacire wannan takalmin daga kafarsa face zai shiga kewaye ita kuwa wannan sanda ko barci zaiyi ya ajiyeta a daf dashi lokacinda shulaiba tazo dai dai nan a tunaninta Sai aminul has ya girgiza kafadunta yace Wai shin wanne irin tunani kike yi ne haka?? 009. SARKIN SARAKAI BOOK1 < . Aminul has ya girgizata yace tunanin me kikeyine haka kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura koda tadawo cikin hayyacinta saita dubi Aminul has tace ka jirani Anan karka matsa ko ina zan shiga daki na fito nan take shulaiba ta juya ta nufi cikin dakinta shi kuwa sai yabita da kallo kawai jim kadan saiga shulaiba ta dawo rike da shohuwar takalmi a hannunta koda ta iso gaban Aminul has saita tsaya suka kurawa juna ido yana mai mamakin ganin tada wadannan tsofaffin abubuwa biyu shulaiba tayi murmushi mai taushi a gareshi tace yakai mijina shin kayi imani da kaunar da nake maka cewa ta cika dari bisa dari? Aminul has yace babu kokwanto ga hakan shulaiba tace idan har kayi imani da hakan toka rike wannan takalmi da wannan sanda daga yau ka kasance a tare dasu dare da rana ya zamana cewa babu abindake rabaka dasu hatta kwanciya bacci face idan zaka shiga kewaye tabbas idanka kiyaye da haka babu tsautsayin da zai sameka kodajin wannan batu sai aminul has ya kurawa wannan sanda da takalmi idanu kawai ya karbesu ya rungumesu a kirjinsa yana mai cewa hakika na gamsu cewa wadannan abubuwa biyu sun fito daga hannun wanda ba za a taba mantawa dashiba lallai zaki sameni mai kiyayewa da umarninki. Nan take aminul has ya cire takalmin dake kafarsa ya saka wannan tsofaffi sannan ya dogara wannan sanda ya nufi cikin turakarsa yana mai waigen shulaiba suna yiwa juna murmushi. Wannan shine abinda ya faru tsakanin aminul has da matarsa shulaiba bayan ya karbi rikon kasar misra daga hannun sarki sahibul hairi ++ Al'amarin sarki sahibul hairi da bawa haluf kuwa tun da sarki ya kama barci a cikin tantinsa bai farka ba saida gari ya waye har rana ta iske koda budewar idanunsa sai yaji rurin gagarumar wuta a wajen tantinsa cikin sauri ya mike tsaye ya fita waje da hanzari yana mai zare takobinsa don tsammanin ko wadansu yan fashi ne suka kawo sumame da fitowarsa saiyaga ashe bawa haluf ne ya tara gawarwakin yan fashin da ya kashe jiya a waje daya ya kunna musu wuta, sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya yafito bawa haluf da hannu cikin hanzari haluf ya rugo gareshi suka koma cikin tantin tare da shigarsa sai haluf yaga ashe har sarki ya fiddo abincin kalaci ya shirya shi bisa faranti. Sarki ya dubi haluf yace ina son muyi sauri mu gama kalaci domin muci gaba da tafiya ka san cewa a kalla nan gaba sai mun kwana talatin da bakwai kafin mu isa birnin Askandariyya ba tare da gardamar komai ba bawa haluf yabi umarni suka zauna tare suna masu fuskantar juna suna cikin cin abincin ne sarki sahibul hairi ya lura idanun bawa haluf yaga sunyi jawur kawai sai yayi murmushi yace yakai haluf kai kuwa menene ya hanaka yin barci jiya da daddare?. Koda jin wannan tambaya sai haluf yayi ajiyar zuciya yace ya shugabana hakika jiya naga bala'in da bantaba gani ba kuma naga jarumtaka a wajenka wacce inda zanje na bayar da labarinta baza a gasgata ni ba hakika ka cika sadauki uban sadaukai ka sani cewa ko a yanzu idan na runtse idanuna sai nayi ta ganin yadda ka dinga karya barayin jiya kana sawa suna sare kawunansu da soke juna. Yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan batu saiya bushe da dariya yace yakai haluf hakika inda kana nan a lokacin da nayi wani yaki da mutanen birnin Rum da wata kila kwakwalwarka ta birkice ka sami tabin hankali A rayuwata ban taba yin yakin da na sha bakar wahala ba kamarsa domin saida na kwana na yini ina yaki ba tare da na sami damar hutawa ba daidai da dakika daya a wannan yakine na shiga tsakiyar abokan gaba mutum dubu dari uku ni kadai suka yanyameni suna kawo mini sara da suka nima ina maida martani A tsawon kwana da yinin ne nayi musu mummunar barna na kashe mutum dubu dari da talatin A wannan yaki gaba dayan dakaruna mutum dubu dari biyu da hamsin saida aka kashe su ni kadaine na rage Lokacinda abokan gaba sukaga inatayi musu barna amma sun kasa cimmani sai suka kara kaimi suna kokarin hallakani ta kowanne hali amma saina zame musu alakakai kaini kaina a wannan yaki saida na tausayawa abokan gaban saboda irin kisan gillar da nake musu. Wani lokacin idan na sari mutum saidai kaga gangar jikinta tsage gida biyu bari da bari duk inda nasa gaba sai daikaga sassan jikin bil'adama suna yawo a sararin sama gaba dayan jikina saida ya rine da jini ba a ganin komai sai idanuna tamkar anyi mini wanka a kogin jini babu abinda zai baka tausayi face ganin yawan gawarwakin a zube tuli a filin yakin tamkar yabanya a gona lokacin da muka kwana muka yini muna wannan yakin ya zamana cewa na kasa karar da abokan gaba sukuma sun kasa cimmani sai gajiya ta fara riskata a sannanne fa abokan gaba suka fara samun lagona har aka yi min sara uku a gadon bayana kuma aka sokeni a kwibin hagu na cikina nan fa jini ya fara zuba a jikina koda naga zan hallaka saina kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba dayan abokan gabar suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa . Ai kuwa sai suka biyoni cikin matsanancin gudu amma na gaba yai gaba na baya sai labari lokacin da nake wannan gudu ina yinsane cikin takaici domin a rayuwata ban taba guduwa ba daga filin yaki yau gashi bala'i yakai har gudu ya zamadole a gareni inba haka ba kuwa na rasa rayuwata shidai wannan yaki muna yinsa ne a wani daji wanda ake kira BAHARUL SHARUL dajin na dauke da manyan tsaunuka da manyan koguna inda ruwa ke bulbulowa daga cikin duwatsu yana kwaranya yana gudu sa adda abokan gaba suka tasoni a gaba na ga babu matsera kawai saina durfafi wani katon tsauni wanda nidai a rayuwata ban taba ganin tsauni mai tsawonsa ba ina kyautata zaton cewa duk duniya babu tsauni mai fadi da tsawonsa nan fa naci gaba da gudu suna biye dani har muka isa can saman tsaunin muka kureshi koda na leqo kasan tsaunin na ga zurfinsa sai zuciyata ta bugu abokan gaba kuwa sai suka ja dinga a bayana suka fara kyakyata dariya don sun tabbatar da cewa duk wanda ya fada daaga saman wannan tsauni sunansa gawa. Nanfa na tsaya ina tunani a raina nace hakika idan ajalina ya tabbata a hannun abokan gaba an rusa mini tunkahona da darajata a idanun duniya kawai saina sake lekawa kasan tsaunin naga yadda ruwa ke kwarara kasa sanna na yanke hukuncin na daka tsalle na sallamo kasa ko dai na rayu ko na mutu kafin nayi hakan saina juya na dubi abokan gaba nayi murmushi nace idan akwai da namijin da ya isa a cikinku ya biyoni inda zan tafi' kafin abokan gaba suyi wani yunkuri na daka tsalle na sallamo izuwa kasan tsauni lokaci guda abokan gaba suka rugo izuwa karshen tsaunin suka yi cirko cirko suna masu lekowa kasa don suga irin mutuwar da zanyi saboda nisan dake tsakanin saman tsaunin da kasansa sai da dakika dari uku ta shude sannan na iso kasa cikin kogi saura kiris kuwa kaina ya fado kan wani dutse amma sai kafata ta bugi wani wuri a jikin tsaunin saina sauya wuri na nutse izuwa can karkashin kogi. A wannan lokaci na suma bansan halinda nake cikiba kawai sai farkawa nayi na ganni a gabar kogi a can wani daji daban koda na tsinci kaina a raye sai murna ta kamani nan take na mike tsaye na tafi neman itatuwan da zan sarrafa na yiwa raunikan jikina magani saida na shafe kwana sittin ina tafiya a

Chapter 2 of 19