Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuri sai hanyar daya biyo ta shafe ya zamana cewa babu batun komawa da baya babu gaba sahibul hairi ya gyara tsayuwarsa yana wulkila idanuwansa izuwa kowanne bango yana jiran duk abinda zai baiyana gareshi bazato ba tsammani sai ya ga wadansu irin gabza gabzan dodanni suna ta fitowa ta cikin gango tamkar haske suna yi masa kawanya Adadin dodannin yakai dari biyar kuma kowannensu yana rike da zabgegiyar makami kai koda guda daya daga cikinsu aka turo birnin Misra zai iya tarwatsa birnin gaba daya wasu da majaujawa ce mai kula kulan tsini wanda girman makaman kadai yafina bil adama bare kuma su kansu don haka lokacin da dodannin sukayi masa kawanya sai ya zamo dan mitsitsi a tsakiyarsu don dayansu ma zai iya tatsileshi da kafa daya babu abinda zai firgita mutum face irin munin fuskokin dodannin don idan mutum ya cika kura musu idanu zuciyarsa zata iya tashi kumallo bayan dodannin sun gama yiwa sarki sahibul hairi kawanya sai suka kama karkada makamansu suna jujjuyasu koda ganin haka sai shima sarki sahibul hairi ya kama wasa takobin hannunsa yana jujjuyata . Lokaci guda dodannin suka kawo masa wawan duka da sara da makamansu cikin zafin nama sarki sahibul hairi ya daka tsalle sama har saida ya tabo rufin saman dakin koda makaman dodannin suka bugi kasa sai suka haifar da wawakeken rami tamkar rijiyar da karti hamsin suka kwana suna hakwa A sama sarki sahibul hairi ya fara saran dodannin amma sai yaji kamar karfe yake sara don har tartsatsin wutane ke tashi nan fa dodannin sukayi ta kai masa sara da suka yana zukewa kuma shima bai fasa saran su ba tuni hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma domin ya san cewa idan aka jima ana wannan artabu gajiya zaiyi in kuma ya gaji take dodannin zasu gama dashi Lokacinda dodannin sukaga sarki sahibul hairi na wahalar dasu ya zame musu alakakai sai suka fara wani irin sabon gurnani mai tsananin kara wanda ka iya sa kunnan mutum ya dode ba shiri sarki sahibul hairi ya yagi rigar jikinsa ya nannadata a kansa wato ya rufe kunnuwansa yaci gaba da artabu amma dukda haka saida kunnuwansa sukayi dum ! Kamar an zuba masa ruwa a ciki ana cikin wannan gumurzu ne daya daga cikin dodannin ya yagi kirjin sarki sahibul hairi da faratan hannunsa guda uku.. . Take wajan ya dare tamkar an sareshi da takobi uku a lokaci guda har saida jini yai tartsatsu sarki sahibul hairi ya kwarar uban ihi saboda tsananin jin zafin da yayi ya fado kasa magashiyan . Koda ganin haka sai dodannin sukayi ca a kansa gaba daya da mugun nifi kowannansu ya zaro faratan hannunsa da nufin su yi tsire da gangar jikinsa cikin tsananin zafin nama sarki sahibul hairi yayi katantanwa a tsakiyarsu yana filfila takobinsa ya fice fit ta karkashin kafafuwansu . Lokacinda suka kawo masa suka da faratanne bisa tsaursayi wani daga cikinsu ya caki wani da farce a tsakiyar kai take wanda aka caka aka kansa ya huje saiga jini yai tsira sama take ya sulale kasa matacce . Wani kuma da ya soki wani a hannu sai ya tsinke masa hannu koda sarki sahibul hairi ya fahimci abinda ya faru sai yayi wata irin yar dungure a kasa ya mirgina sau goma a cikin dakika daya ya suri guntulallen hannun dodon da ya guntule ya mai dashi makaminsa . Ai kuwa sai fada ya sauya salo domin da farcen hannun dodannin ya dinga yiwa dodannin barna wato yayi ta saran jikinsu jini na zuba amma saboda naci da taurin kai saikaga sunyi girgiza sun ci gaba da kokarin hallakashi babu abinda zai burge mmutum kuma ya bashi mamaki face yadda sarki sahibul hairi ke yin wannan yaki cikin matukar karfin hali da juriya domin tuni jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin dake zuba a kirjinsa amma duk da haka yaki yarda ya fadi kasa kuma bai fasa ci gaba da ragargaza su ba abindake tayar masa da hankali shine basa mutuwa . Saida aka shafe sa a ana wannan artabu ya kasa kashe dodannin su kuma sun kasa hallakashi amma kuma suma sun fara nakasa shi domin sun yayyankeshi da kaifin faratansu gaba daya jikinsa yai fata fata da jini kamar yadda nasu yayi A wannan lokacin ne sarki sahibul hairi da dodannin suka kamalayi kamar wadanda suka sha giya suka bugu Wohoho hakika idan namiji ya cika namiji baya faduwa kasa banza sai dai ayi ragas sai da ya rage saura kiris ayi mutuwar kasko sai sarki sahibul hairi ya sami nasarar sukar tsakiyar kan daya daga cikinsu nan take kuwa dodon ya sulale kasa matacce . Koda ganin haka sai sahibul hairi ya tabbatar da cewa ruhin dodannin a tsakiyar kansu yake nan fa ya ringa tsalle a kansu kamar dan biri cikin zafin nama tamkar walkiya yana ta soka musu farcen a tsakiyar kawunansu sai gashi dodannin suna sulalewa kasa matattu tamkar ana sassabe a gona cikin abinda bai wuce dakika dari da sittin ba gaba daya dodannin suka zama gawa . Koda ya gama kashe dodannin sai shima ya sulale kasa sumamme sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan sa'a biyu farkawarsa keda wuya sai yaji kirjinsa na yi masa azababben zugi da radadi koda ya dubi kirjin yaga wannan lafcecen yanka guda uku sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da cewa wannan rauni zai iya zama sanadin ajalinsa don har yanzu jini na zuba a jikin rauninnan fa ya fara tunanin hanyar da zaibi ya yiwa kansa magani yana cikin hakan ne wata dabara ta fado masa da jan ciki ya rarrafa yaje kan gawar dodo guda ya cisgi gashin kansa sili uku sannan ya dauki guntulallen hannun dodon ya sa a bakinsa ya fisgi farce guda sannan yayi amfani da wani farcen ya yanke wannan farcen da ya cisge har saida ya mayar dashi dan siriri kamar allura . Da wannan allura da kuma silin gashin dodon ya dinke raunin dake kirjinsa guda uku bayan ya kammala dinke raunikan ne ya jingina bayansa a jikin bango yai shiru yana hutawa da tunani tabbas yanzu dai ya san cewa ba zai iya shiga cikin daki na biyar ba face ya zauna yayi jinyar raninsa a kalla kwana bakwai . Abin tambayar anan ya za ayi ya rayu har tsawon kwana bakwai a cikin wannan daki baci basha? Kai idan ma akwai abinci da sha ai gawan dodannin ma idan ta rube warinta kadai ya isa ya kashe shi wai shin ma masifu nawa ne suka rage a gabansa kafin ya samu ya fita daga cikin wannan wuri na karkashin kasa? Koda yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta karaya nadama ta sake zo masa a karo na biyu ya fara sabon tunani . Lokacin da sarki sahibul hairi yayi tunani har tunanin ya ishe shi sai yace da kansa kai wannan banzan ba zai fishsheni da komai ba abinda zai fishsheni kawai shine na yi tunanin hanyar da zan iya rayuwa a cikin wannan daki har tsawon kwana bakwai . Sarki sahibul hairi ya shiga sabon tunani ai kuwa bai dade ba yana wannan tunani sai dabara ta fado masa cikin karfin hali ya mike tsaye yana kama gawarwakin dodannin yana zuba su cikin ramin nan da suka yi sakamakon kawo masa sara da makamansu sai bayan ya zuba fiye da rabin gawar a ciki ya fuskanci cewar ramin ba zai cinye dukkanin gawar ba bisa dole ya sake fito da gawarwakin ya shiga aikin daddatsa gawarwakin gutsun gutsun sai dai ya yi sa a biyar yana wannan aiki sannan ya gama daddatsa su duka. Daya gama sai ya kwashi kadan daga cikin sassan jikin dodannin ya ajiye gefe guda kuma ya saro kofaton dodo guda biyu ya ajiye da yai haka sai ya dure gangar jikin dodannin duka a cikin ramin sannan ya kama bako kasa yana watsawa cikin ramin har saida ya binne wannan sassan jiki duka a cikin ramin . A sannan ne fa ya gaji likis kuma ya jike sharkaf da gumi kamar an tsamoshi daga kogi saida ya huta tsawon rabin sa a sannan ya sake mikewa yaje gaban kofaton dodon da ya ajiye ya tsugunna kawai sai ya maida kofaton kyastu ya dinga goga daya akan daya har izuwa tsawon lokaci sannan yayi sa a wuta ta kama a jikin naman dodon daya hada waje daya . Kawai sai ya kurawa wutar da naman idanu har saida naman ya babbake gaba daya kawai sai ya kama cin naman dodon yana ci yana zubar da hawaye ba komai ne ya haddasa wannan hawaye ba face tsananin rashin dadin naman dodon da kuma tsananin takaicin da ya tsinci kansa a ciki ya tuna cewa shifa sarki ne guda amma yau gashi ya tsinci kansa a cikin wannan mugun hali har ma yaci danyen naman zaki kuma yaci naman dodo haka dai sarki sahibul hairi yaci gaba da cin wannan naman cikin matukar juriya har saida yaji cikinsa ya cika yana gamawa kuma sai yaji kishirwa ta addabeshi a sannan ne fa ya gane kuskurensa domin ko kadan baiyi tunanin hanyar da zai magance kishi ba . Bisa dole ya kama kwankwadar jinin dodannin nan da ya malala a kasa cikin dakin nan ma saida ya sha ya ishe shi sannan ya bingire kasa cikin jini ya kama barcin dole Allah sarki ita masifa ba a samata rana ita kuwa kazar wahala indai mutum ya yankota to sai ya fige abarsa . HAKa dai sarki sahibul hairi yaci gaba da rayuwa a cikin wannan daki na hudu har izuwa tsawon kwana bakwai ya zamana cewa bashi da abinci sai wannan babbakakken naman dodon daya tanada ruwan shanshi kuwa wannan jini ne nasu har saida jinin ya daskare amma bai daina shansa ba ahaka duk da cewa jinin yana wari da karni mai tayar da zuciya . A ranar kwana na bakwai ne sarki sahibul hairi yaji kwarin jikinsa kuma wannan rauni na kirjinsa ya kame nan take sarki sahibul hairi ya mike tsaye ya sungumi gatari daya daga cikin na dodannin nan da ya kashe shi kansa saida ya hada karfinsa waje guda sannan ya iya daga gatarin sama . Nan fa ya shiga saran bango domin ya samarwa da kansa hanya ta fita bai gushe ba yana saran bangon har saida yayi sa a uku ta shude sannan ya sami nasarar fasa garun kofa ta samu kawai sai ya yarda gatarin ya kunna kai cikin daki na biyar . Shidai wannan daki na biyar ya bambanta sosai da sauran dakunan hudun da ya wuce a cikinsu domin ko kadan babu duhu a cikinsa a haskake yake fayau kamar rana babu komai a cikin dakin face wasu manyan akwatuna guda bakwai wadanda aka rufesu ruf da wani irin murjejen kwado mai kaurin gaske kafin mutum ya iya sareshi sai ya jike sharkaf da gumi . Koda sarki sahibul hairi yayi arba da wadannan akwatunan sai yayi tsaki yace '' To meye gamina da wadanna akwatuna Ai ni hanya kawai nake nema da zan fita daga cikin karkashin kasar nan '' koda gama wannan furuci sai ya koma da baya izuwa wannan daki na hudu ya dauko gatarin nan ya dawo ya kama saran bangon daki na biyar din don ya sami hanya koda ya fara saran bangon sai yaji kamar karfe yake sara koda ya kara kaimi sai bakin gatarin ya kama dakushewa al amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan amma saboda naci bai fasa sara ba har saida ya gaji likis yaga babu alamar nasara sannan yayi jifa da gatarin ya tsugunna a kasa cikin alamun bakin ciki da karayar zuciya . Ya kurawa wadannan akwatunan bakwai idanu ya shiga tunani'' to wai in banda abinka ai gatarin sihiri kazo nema babu mamaki ma yana cikin daya daga cikin akwatunan nan don haka me zai hana ka jarraba bubbude su ka gani '' . Wata zuciyar kuma sai tace kai kada ka bude akwatin nan domin wata kila wasu masifunne aka tanada a ciki haka dai sahibul hairi yayi ta tunani iri iri ya kasa yanke hukunci daga can sai ya mike tsaye yaje ya kwankwasa akwatin farko baiji alamar akwai wani abu a ciki ba . Ya kara kunnansa a jikin akwatin nanma yaji shiru babu alamar wani motsi a ciki kawai sai ya mike tsaye yaje ya dauko gatarin nan ya kama saran kwadon makullin akwatin ta farko aikuwa bai dade ba yana saran ya bincineshi . Sarki sahibul hairi ya sunkuya ya cire kubar sannan ya daga murfin akwatin dagowar ke da wuya sai yaji wasu abubuwa kaman kwari sun yi fitar burgu daga cikin wannan akwatin sun doki fuskarsa saboda karfin dukan saida yayi sama ya gwaru da rufin saman dakin ya fado kasa a galabaice . Ba wasu abubuwa bane suka fito daga cikin wannan akwatu face wasu yan kananan aljanu wadanda girmansu bai wuce na fara ba Adadinsu yakai miliyan daya su duka suna wata irin kara mara dadin ji . Kafin sarki sahibul hairi yayi wani yunkuri tuni sun sureshi sunyi sama dashi suka rinka gwarashi a jikin bango basu saukeshi ba saida sukaga sun farfasa masa kai da jiki ya suma . Bayan sun sauke shi ya rikito kasa sai suka rinka curewa waje guda da kadan kadan kafin su gama curewa sai sarki sahibul hairi ya farfado koda ya gama kyallara idanunsa ya hango wadannan kananan aljanu suna curewa a waje guda ba tare da sanin abinda suke shirin yi masa ba sai hankalinsa ya dugunzuma tabbas ya san cewa ba zai iya yin fada da wadannan aljanun ba kawai sai ya yunkura cikin zafin nama ya dauki . Akwatin da suka fito daga ciki ya kifa a kansu ta rufe su fuf to amma ya rufe daki ya kulle da barawo domin akwai ragowar kimanin guda dubu da bai rufe dasu ba duk da cewa ya zauna akan akwatin sai da suka ringa girgiza suna kokarin jefar dashi daga kanta don su fito waje shikuwa sai ya yi amfani da dukkan karfinsa wajen danne akwatin yayinda ragowar aljanun suka ga an danne yan uwansu a cikin akwatin sai suka tasamma sarki sahibul hairi suna kai masa cizo da yakushi nan fa sarki sahibul hairi ya raba karfinsa da hankalinsa gida biyu . Ya zamana cewayana yaki da wadannan aljanu dubu kuma yanaci gaba da kokarin danne wannan akwatin wadda ya zauna a kanta. Sudai wadannan aljanu suna da fuka fukai don haka shawagi sukeyi kawai akan sarki sahibul hairi suna kai masa hari tako ina shi kuwa ya wanzu yana kai musu sara cikin zafin nama da takobinsa takobin bata iya yi musu komai amma karfin dukan da yake shine yake kadar dasu su fadi kasa. Ana cikin wannan dauki ba dadi ne daya daga cikin aljanun ya sami nasarar kafa hakoransa akan kafar sarki sahibul hairi aikuwa koda ya ciza sai ya finciko. Sai ga gudan tsokar nama a bakinsa tsananin zafi da zugin da sarki sahibul hairi yaji ne yasa ya kwala kara mai karfin tsiya. Wadda ta firgita aljanun suka ja da baya a dai dai wannan lokaci ne ya lura da cewa aljanun da ya danne a cikin akwatin da yake kai sun daina motsi koda ya sunkuya kansa sai yaga jini na malalowa waje. Cikin sauri ya daga akwatin sai yaga ashe gaba daya aljanun sun mutu. Ba wani abu bane ya kashe wadannan aljanun face rashin iskar da zasu shaka numfashi A farko kafin sarki sahibul hairi ya bude wannan akwati a saman murfinta akwai hudoji masu yawa wadanda koda mutum ya leka ta cikinsu ba zai iya hango abin dake ciki ba sirrin ruhin wadannan aljanu shine ko yaya suka daina shakar iska a duniya sai jikinsu ya kama daddarewa shi yasa da aka kullesu a cikin wannan akwatin aka hurhuda samanta. . Sa adda sarki sahibul hairi ya kifesu da akwatin a kasa ba sa shakar numfashi shiyasa suka mutu lokacin da sauran aljanun guda dubu sukaga gaba daya yan uwansu sun mutu sai suka harzuka suka sake afakawa sark sahibul hairi da nufin su hallakashi farat daya shi kuwa sai yaci gaba da makesu da wannan takobi tasa.amma duk wanda ya fadi kasa sai ya sake tasowa tamkar babu abinda ya sameshi sai da aka shafe sa a hudu ana wannan gumurzu in banda rauni na farko da aka yiwa sarki sahibul hairi a kafa babu abinda ya sameshi amma kuma gajiya ta fara riskarsa . Su kuwa wadannan aljanun kamar ma a sannane suka fara fafatawa koda sarki sahibul hairi ya fuskanci cewa idan fa akaci gaba da wannan fada izuwa wani lokaci zasu hallakashi sai ya sauya shawara cikin zafin nama ya suri wannan akwatin ya ruke a hannunsa duk aljanin da ya make a sama suka fado kasa kafin su yunkura su sake tasowa sai ya kifesu da wannan akwati ya take akwatin da kafarsa guda yana mai ci gaba da saran sauran ba zai daga akwatin ba har saiyaga jini na fitowa daga karkashinta a haka a haka har sarki sahibul hairi ya samu da kyar da sidin goshi ya karar da wadannan aljanun duka . Nan fa ya tsugunna kasa yana numfashi sama sama cikin karfin hali ya yagi rigarsa ya daure wannan rauni dake kafadara don tsaida jinin sannan ya kurawa ragowar akwatunan shida idanu yana shawara a cikin zuciyarsa akan ya budesu ko kuwa kada ya bude. Wata zuciyar tace dashi ''ya za ayi kaci gaba da bude wadannan akwatuna alhali baka san masifar dake cikinsu ba''. Wata zuciyar tace dashi kuma' ++ to idan baka bude akwatunan ba me zakayi tunda baka da wani zabi wand ayafi hakan''. Koda gama wannan tunani sai ya mike tsaye yaje kan akwati ta biyu ya dauki gatarin nan ya kuma saran kwadon sannu a hankali ya bincine kwadon yasa hannu ya zareshi ya daga murgin akwatin sama faruwar hakan keda wuya saiga wata katuwar kunama ta fito daga ciki tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba gainin kunama mai girma kamarta ba . Koda kunamar tayi arba da shi sai ta tasammasa tana wurkila kafafuwanta guda goma sha biyu masu fitar da dafi ga kuma kaifin farata. Sarki sahibul hairi ya kama ja da baya ita kuma taci gaba da binsa har sai da ya kure a jikin bango. Nan fa suka fara mugun artabu ya zamana cewa tana kawo masa suka da kafafuwanta ta ko ina shi kuma yana kare kansa gami da kai mata suka amma duk inda ya soka a jikinta sai yaji kamar dutse ya soka ko kwarzanewa bata yi Al amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan. Ya tabbatar da cewa bashi da wata sauran dabara face yayi iya yinsa inda karfinsa ya kare shi kenan haka dai aka ci gaba da fafatawa kunamar ta kasa hallaka sarki sahibul hairi shima ya kasa cutar da ita har izuwa tsawon lokaci ana cikin hakane kunamar tayi masa wata irin mahaukaciyar sura tayi sama dashi ta makashi a jikin bango ya fado kasa . Cikin tsananin galabaita harma yaji ba zai iya tashi ba koda ganin haka sai kunamar ta taho gareshi cikin tafiyar kasaita da nufin ta caka masa kafafunta shida ta zuba masa dafi... ... . Koda ta iso daf da shi ta daga kafafuwan nata sama zata cakeshi sai ya yunkura cikin zafin nama ya daka tsalle ya haye samanta kawai sai ya kama naushin idanunta da hannunsa guda ita kuwa ta rinka kawo masa suka da kafafunta yana kadasu da takobinsa nan fa suka yi ta wutsil wutsil da mirgin mirgin ya zamana cewa ta kasa cafkoshi shi kuma ya kasa burma idanunta . Koda ganin wanki hula zai kaishi dare sai ya fusata ya dunkule hannunsa ya tattaro karfinsa duka ya gabzawa kunamar mahaukacin naushi a ido take kwayar idon ta fashe hannunsa ya lume a cikin idon tamkar an zura guga a rijiya saiga jini na bulbulowa nan fa kunamar ta kama tamagungun. . Cikin hanzari sarki sahibul hairi yya daka tsalle ya dira a kasa daga kanta kunamar taci gaba da birgima a kasa tana wani irin gurnani da kakarin mutuwa tun tana motsi sai data sandare komai na jikinta ya daina aiki. . A sannan ne hankalin sarki sahibul hairi ya dawo jikinsa ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya kurawa gawar kunamar idanu jim kadan sai kuma ya dubi akwati ta uku ya fara tunanin budeta sarki sahibul hairi ya mike tsaye yaje kan akwatin. . Har ya sunkuya zai dauki gatari ya sare makullin sai ya fasa kawai sai ya dauki gatarin ya wuce izuwa kan akwatin kashe ya kama saranta koda ya balle makullin ya budeta sai yaga wani irin haske ya fito daga cikinta ta bugi jikin bango take zanen kofar ya fitar da kansa sai ga wata kofa ta bayyana kuma ta bude kanta wanda ta cikinta ne za a iya shiga cikin daki na shida sarki sahibul hairi ya kurawa kofar idanu cikin tsananin mamaki yace '' Oh! Na yankewa kaina wahala yanzu inda na bude sauran akwatunan can da yanzu ina cikin masifa. . Gama fadin hakan keda wuya ya yarda gatarin dake hannunsa ya dauki takobin ya kunna kai cikin wannan kofa ta shiga da shigarsa kofar sai ya tsinci kansa a cikin wata wangamemiyar fada wadda aka kawatata ainun da abubuwan ban sha awa komai dake cikin fadar an sassakashi ne da dutsen lu'u lu'u don haka fadar ta haskake da sheki da walwali . Sarki sahibul hairi yaci gaba da tafiya a cikin fadar yana wuce wadansu gumaka wadanda aka yi su cikin siffofin dukkanin sarakunan da suka mulki birnin Askandariyya sarki sahibul hairi yaci gaba da tafiya a cikin fadar nan yana kallon abubuwan al ajabi iri iri ba tare da ya taba komai ba . Kwatsam sai ya hango wani karamin baho na zinare a tsakiyarsa an kera wani kyakkyawan dawisu na karfe ruwa na diga daga cikin bakin dawisun yana zuba a cikin bahon har ya dan taru mamaki ya kama sarki sahibul hairi bisa yadda makerin wannan dawisu da bahon yayi basira wajan sassakasu . Abinda yafi bashi mamaki shine ta ina wannan ruwa yake shiga cikin jikin dawisun har yake digowa kasa ta cikin bakinsa sarki sahibul hairi ya zagaye bahon yaga babu ta inda ake zuba ruwan sai ya dada cika da mamaki kawai sai sha awar dawisun ta debeshi ya dafa kansa faruwar hakan keda wuya sai wadansu kibiyoyi suka rinka cillo kansu ta ko ina zasu soke sarki sahibul hairi. Cikin zafin nama ya rinka karkade kibiyoyin amma sai yaga kibiyoyin sunki karewa saboda haka sai ya zabura ya kama gudu a cikin katon dakin yana gudu yana karkade kibiyoyin ta gaba ta baya. Hakika in ba don sarki sahibul hairi ya kasance mai tsananin zafin nama ba da tuni sama da kibiyoyi dari sun cake a jikinsa duk da zafin namansa sai da kibiyoyi uku suka cakeshi. Har ya fada bayan wani gunki ya labe kibiyar farko a cinya ta cakeshi ta biyu a bayansa wajan kuibin kafadar hagu ta uku kuwa a hannunsa na dama. Cikin tsananin galabaita ya fadi sharam!! A bayan gunkin a sannan ne kuma kibiyoyin suka daina cillo kansu daga inda suke fitowa cikin tsananin dauriya sarki sahibul hairi ya zare kibiyar dake jikin hannunsa jini yai tsartuwa yana mai rusa ihu saboda tsabar zafi da zugi A haka ya zare kibiya ta biyu da ta uku sannan kuma ya daure inda kibiyoyin suka cakeshi da tsumman rigarsa dan tsaida jini gama yin hakan ke da wuya sai yaji jiri ya debeshi nan take ya sulale kasa sumamme. . Sarki sahibul hairi bai farfado ba sai bayan rabin sa a yana bude idanu ya tsinci kansa anan inda yake. Wato a bayan wannan gunki kawai sai ya mike tsaye da kyar yaci gaba da tafiya a cikin katuwar fadar saida yayi doguwar tafiya sannan ya kure karshenta ba tare da ya sake shiga wani hadarin ba kawai saiyaga wadansu kayan yaki kala uku na karfe a rataye a jikin bango. . Daya bakine daya fari daya kuma ja kowannensu rigane da wando da hula kuma da takalmi har da takobi sarki sahibul hairi ya kurawa kayan yakin idanu yana shawarar wanda ya kamata ya dauka ya sanya a jikinsa da ya dubi bakaken kayan da farko sai yace.. Kai shifa bakin abu duk inda yake ba abin sha awa bane kuma kalace mai nuna mugunta don haka bazansa bakin ba. Ya dubi jajayen yace. Shikuma jan abu ai kalace ta ban tsoro mai nuna alamun tashin hankali don haka bazansa jaba. Ya dubi farin yace. Yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don haka zu sansa..... Sarki sahibul hairi ya ci gaba da cewa yauwa fari kalace ta adalci da nuna alamun tausayi don haka su zansa ba tare da fargabar komai ba sai ya dauki fararen kayan ya sanya a jikinsa tsaf wohoho duk wanda yaga sarki sahibul hairi a cikin wannan shiga ta fafaren kayan yaki dole ne ya bashi sha awa kuma ya bashi tsoro saboda sunyi masa kyau matuka kuma sun kara bayyana kwarjininsa a fili . Gama sa tufafin ke da wuya sai yaga wata kofar ta bayyana a jikin bango kai tsaye ya nufi kofar ya shiga cikinta sai gashi yana ratsawa ta cikin wadansu kofofi wannan na bin wannan tun yana irga kofofin har sai da ya gaji ya daina nan fa sarki sahibul hairi yayi ta ganin abubuwan tsoro iri iri da abubuwan mamaki kala kala amma duk inda yazo sai yaga ya wuce lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba mamaki ya turnuke sarki sahibul hairi . Abin da bai sani ba shine duk wanda yasa wadannan fararen kaya na yaki babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya ganinsa kai hatta tsuntsaye da dabbobi ma bazasu iya ganinsa ba face mutum daya kwal a duniya ba wani bane face sarki barusa mai birnin Askandariyya . Sai da sarki sahibul hairi ya wuce kofofi dubu tara da dari tara sannan ya iso gaban wata matattakalar kasa koda ganin wannan matattakalar sai murna ta kama sahibul hairi kai tsaye ya khau kanta ya kama tafiya har ya iso karshenta inda yaga wata kofar koda ya bude kofar saiya hango cikin fadar sarki barusa ga jama a nan a cike an kewaye sarki barusa ana fadanci . A lokacin wani mai baiwa sarki labari na zaune a gabansa yana ta sharara labari mai ban dariya sarki barusa na ta kyakyatawa saboda karfin dariyar tasa ma kiris ya rage bai fado kasa ba daga kan karagar mulkinsa cikin sauri sarki sahibul hairi ya fito daga cikin dakin ya kulle kofar ba tare da kowa ya ganshi ba sannan

Chapter 5 of 19