Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan takalmi mai tsawon gaske ne koda zamu kwana bakwai a nan ba zan iya gama jawabi ba ina sanar dakai cewa makiyanka ne suka ciyar da wannan doki naka wata ciyawar sihiri don ya haukace yaje ya hallakar da kai lokacin da ya afka dakai cikin tekunne na biyoku cini na aza dokin a kaina naci gaba da tafiya daku kuma na dinga zuko iskar numfashi daga can saman tekun ina feso muku kuna shaka. Hm kaji Aikin sihiri . Wannan shine iyakar bayanin da zan iya yi maka a yanzu sai kuma idan ka sake ganina a karo na biyu koda gama fadin haka sai aljanin ya bace bat bacewarsa keda wuya sai na tashi dokina tsaye na haye kansa na taho nan fada. Nima yanzu da wannan kalami nake muku sallama don haka na sallami kowa ya tafi izuwa gida a sanar da sauran jama a wadanda basu san hallarataba cewa ina nan a raye ban mutu ba nan take fada ta watse jama a suka tafi izuwa gidajensu suna masu farin ciki Al amarinsu waziri Akiyanu kuwa batun bakin ciki a cikin zuciyoyinsu ba sai an fada ba domin yadda sukaga rana haka suka ga dare a wannan rana kashe gari da sassafe sukayi shiri su takwas suka tafi izuwa wani kauye da ake kira BAHUS a sirrance don ziyarar wani maketacin boka wanda ake kira da SHUBURUL UZAB . boka shuburul uzab ya shahara a cikin yankin kasar misra harma ana ganin cewa in banda boka HADIMUL ASUR babu wand aya fishi ilimin tsafi da rana tsaka su waziri suka isa gidan boka shuburul uzab inda suka iske shi tsaye a kofar gidansa ya kura musu idanu yana mamaki koda suka matso daf dashi sai ya dubesu ya tuntsure da dariya yace.. Lale marhaban da manyan baki wadanda na dade ina jiran zuwansu a irin wannan rana........ Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su waziri Akiyanu suka sauko daga kan dawakansu cikin sanyin jiki gaba dayansu suka risina suka kwashi gaisuwa sannan waziri ya dubi boka shuburul uzab cikin nutsuwa yace. Yakai wannan boka mai daraja kai kuwa menene dalilin da yasa kace ka dade kana jiran zuwanmu gareka? Idan har kana son mu ziyarceka me yasa tuntuni baka aika mana muzo ba? Koda jin wannan tambaya sai boka shuburul uzab ya bushe da dariya sannan yace yakai babban waziri ka sani cewa amsar wannan tambaya tana bukatar a saurareta a cikin nutsuwa ku kuwa yanzu gashi babu nutsuwa a tare daku domin kun gaji ainun kuma kuna bukatar abinci da abin sha don haka zaifi kyau mushiga daga cikin gidana ku zauna ku sami nutsuwa tukunna. . Ba tare da wata gardama ba sai su waziri Akiyanu suka bi boka shuburul uzab a baya har izuwa cikin turakarsa da zuwa suka iske an tanadar musu shimfidu da abinci da abin sha irin nasu na sarakai. Kawai sai boka shuburul uzab ya umarcesu da su zauna su kintsa cikinsu shi kuwa sai ya wuce zuwa wani dakin daban bai fito ba sai bayan sun gama kimtsa cikinsu boka shuburul uzab ya zauna a gefe daya yana mai fuskantarsu boka shuburul uzab yace yaku wadannan manyan baki na sani cewa kuna cikin matsanancin bakin ciki bisa rashin samun nasarar hallaka sarki Aminul has? . . Tabbas ba zaku taba samun nasara ba face kun rabashi da wannan sandar tsafi da takalmin sihiri duk duniya babu wanda zai iya taimaka muku ku sami nasarar rabashi da wadannan abubuwa face mutum biyu. Na farko shine boka hadimul Asur sai kuma ni din nan ni kuwa ba zan taimaka muku ba face kunyi mini wani abu guda daya. Cikin matukar mamaki waziri Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace kai kuwa menene abin da kake son muyi maka. Boka shuburul uzab yayi murmushi sannan yace ina son ku sato mini dokin nan na sarki Aminul has wanda yai tafiya dashi a can karkashin teku, domin na ciri wani sinadarin tsafi a jikinsa wanda shi ne zan cika burina na duniya. Cikin mamaki Akiyanu ya dubi boka shuburul uzab yace to ai wannan doki bashi da wani sihiri a jikinsa, boka shuburul uzab ya kyalkyale da dariya yace kaine dai baka sani ba ai sakamakon daukan da wannan guntun Aljanin yayi masa yanzu ya sami sirrikan tsafi guda dari ba daya irin na sadauki awaisu. Akiyanu ya sake tambaya wane ne kuma sadauki Awaise? Boka shuburul uzab yace sanin wannan bashi da wani mahimmanci a gareku yanzu saiku amsa mini muradina kafin na gaya muku hanyar da zakubi ku raba aminul has da ababan dogaronsa. Shin kum amince zaku sato mini dokin. Waziri akiyanu yace kwarai kuwa ai sato wannan doki a garemu abu ne mai sauki tamkar wanke hannu da ruwa, boka shuburul uzab yayi dariya sannan yace to shi kenan sai ku tashi ku tafi izuwa birni na baku kwana biyu rak ku sato wannan doki ku kawo mini kuna kawo mini shi nayi Alkawarin zan gaya muku yadda zakuyi ku raba aminul has da sandarsa da kuma talakawansa na tsafi don ku sami damar hallakashi. Koda gama wannan jawabi sai boka shuburul uzab ya lumshe idanunsa ya bace bat daga cikin turakar koda ganin haka sai suma suka hau dawakansa suka nufi birnin misra. Basu isa cikin gari ba sai da dare ya soma maimakon su rarrabu kowa ya tafi gidansa sai suka sake dunguma gaba daya suka tafi izuwa gidan waziri Akiyanu suka sake sabon zama na musamman don tunanin hanyar da zasu bi su sami nasarar sato wannan doki na sarki Aminul has, abinda su waziri akiyanu basu sani ba shine boka shuburul uzab yaudararsu zaiyi kawai amma a zahirin gaskiya ba zai iya raba sarki Aminul has da abubuwan nan biyu ba. Sihirin da yake so ya cire a cikin jikin dokin Aminul has kuwa shine irin sihirin dake jikin yarinya Alfila yar sadauki Awaisu kuma irinsune a jikin wannan sanda da takalmi na aminul has. Duk abinda wannan guntun Aljanin ya taba da hannayansa sai ya sami wannan sihiri dalilin haka ne dokin Aminul has ya sami wannan sihiri. ++ ++ ++ Acan birnin Askandariyya kuwa lokacin da sarki sahibul hairi yaci gaba da labewa a cikin fadar sarki barusa yana hangen abubuwan dake faruwa kawai sai ya gga wata kyakkyawar mace ta gaban kwatance ta baiyana a gabansa tana mai yi masa murmushi. Har ya yunkura zai bar wajan ta dakatar dashi tace tsaya na nuna maka hanyar da zaka bi kaje inda gatarin sihiri yake in kuwa kabi wata hanya daban halaka zakayi cikin matukar mamaki da rashin yarda sarki sahibul hairi ya dubeta yace ke kuma wacece kuma saboda me zaki nuna mini inda gatarin sihiri yake alhalin kuna son wannan gatari fiye da komai a cikin birnin nan? Kyakkyawar tace babu isashshen lokaci da zan iya maka bayani yanzu amma bayan ka sami nasarar dauko gatarin sihirin zanyi maka bayanin komai. Koda gama fadin haka sai ta jashi izuwa wani sako daban sukaci gaba da tafiya suna ratsa wadansu manyan dakuna har saida suka shige cikin dakuna dari koda suka isa gaban kofa ta dari da daya sai kyakkyawar ta tsaya tace gatarin sihiri na cikin wannan daki a rataye a jikin bango kuma akwai dakaru mutum dubu uku a ciki masu tsaron gatarin wadanda suka kasance karfafa kuma sadaukan gaske yanzu saika shiga cikin dakin ka yaki sadaukan dubu ka karkashesu sannan ka fito na saka a hanyar da zaka fita daga cikin gidan sarautar nan sannan kuma nayi maka jagora izuwa gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya Alfila yar sadaukin duniya Awaisu''. An ya kuwa nima ba zan bisu ba kuwa ganin yadda mace take son raka sarki sahibul hairi?. Koda jin wannan batu sai sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamakin yadda akayi wannan kyakkyawar budurwa ta san dukkan shirinsa har ya budi baki da nufin ya sake yi mata tambaya sai tace dashi. Na gaya maka cewa bamu da isashshen lokaci a yanzu wanda zan yi maka bayanin komai don haka kayi sauri kaje ka dauko gatarin sihirin nan. Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bude wannan kofa ya kunna kai ciki ba tare da fargabar komai ba yana shiga kuwa ya hango gatarin sihiri a rataye a jikin bango sai sheki da walwali yake tsaitsaye a gaban bangon da aka rataye gatarin wadansu murza murzan kartine majiya karfi su dubu uku kowannansu a tube daga shi sai kamfai. Kuma duk suna rike da manyan makamai ababan tsoratarwa wani makamin ma tunda sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin irinsa ba su dai wadannan karti sun ninka sarki sahibul hairi sau uku a girma da cika ido gaba dayansu kansu daya tamkar tagwaye kai kace mace daya ce ta haifesu rana daya. Koda kartin sukaga sarki sahibul hairi ya shigo cikin dakin sai suka yi masa kawanya su duka kowannansu ya kama gyara makaminsa shima sarki sahibul hairi sai ya gyara tsayuwarsa a cikin farin kayan karfe yana jiran yaga wanda zai fara afko masa.. Kamar hadin baki sai suka tasammasa gaba daya a lokaci guda ya zamana kowa na kai masa sara da suka shi kuwa sai ya zama tamkar shaidani a tsakiyarsu yayi ta kare kansa yana mayar musu da martani nan fa aka yi ta gumurzu dauki ba dadi da fafatawa tsakanin sarki sahibul hairi da dakaru masu tsaron gatarin sihiri. Sai da aka shafe sa a biyu a haka subasu barshi ya sami damar isa inda gatarin yake ba shi kuma ya kasa hallaka koda daya daga cikinsu domin idan ya samu sa ar sarar jikinsu ma sai yaga kaamar dutse ya sara babu abinda yake samun su wani abu daya kara firgita sarki sahibul hairi shine ko kadan dakarun basa gajiya kuma basa alamar cewa zasu gaji sarki sahibul hairiya tabbatar da cewa idan akaci gaba da wannan fada a haka zata kai cewa ya gaji sun samu lagonsa . Don haka ya zama wajibi a gareshi yayi tunanin mafita ba zato ba tsammani sai dakarun sukaga ya sauya salon fada dabarar da yayi kuwa itace ya fara tsalle tsalle yana taka kawunansu yana karawa gaba a haka suka rinka kaiwa kafafunsa sara amma saboda zafin namansa sai suka kasa cimmasa bare samunsa . Kafin su ankara ya daka tsalle ya dira akan gangon da aka rataye gatarin sihiri nan take ya yarda takobin hannunsa ya suri gatarin duk da cewa gatarin nada matukar nauyi amma sai gashi da hannu daya ma sarki sahibul hairi ke jujjuyashi. sa adda dakarun sukaga sarki sahibul hairi ya suri gatarin sihiri sai suka sake yin caaa a kansa da nufin su ragargazashi shi kuwa sai yayi amfani da gatarin yaci gaba da saransu wohoho a wannan lokacine labari ya sha bambam domin duk wanda ya sara da gatarin sai dai kaga ya faskarashi gida biyu. .. Sarki sahibul hairi yaci gaba da ragargazarsu tamkar mai yanke kabewa kafin a jima yai fata fata da su babu sauran mutum daya a tsaye gabansa koda yaga ya sami wannan nasara sai ya cika da tsananin murna kawai sai ya saba gatarin a kafadarsa ya bude kofar dakin ya fito. . A wannan lokaci duk jikinsa yayi kaca kaca da jini hatta fuskarsa kuwa sai da ya cire hular karfen dake kansa sannan ya goge jinin akan idanunsa fitarsa ke da wuya sai yaga wannan kyakkyawar budurwa a tsaye tana jiransa koda ta gasnhi rike da gatarin sihiri sai ta tareshi da farin ciki ta kama hannunsa . Faruwar hakan keda wuya sai suka face bat a tare suka bayyana cikin wata babbar turaka wadda akayi matukar kawata da kayan kawa iri iri daga can kuryar kudu an ajiye wani shimfidadden gado na alfarma irin na sarakai kwance akan gadon kuma a lullube cikin mayafi ba wani bane face bawa HALUF yana ta sharar barci tamkar wanda ke dakin matarsa. . Nan fa sarki sahibul hairi ya cika da tsananin mamaki domin shi a saninsa ya baro bawa haluf a can bayan gari toyaya akayi ya shigo har ma ya sami jiki yana barci mai nauyi haka. Koda kyakkyawar budurwar ta fahimci cewa sarki sahibul hairi na mamakin ganin bawansa haluf a cikin wannan turaka sai tayi murmushi sannan ta zauna a gefen gadon tana mai fuskantar sarki sahibul hairi tace dashi. . Yakai wannan jarumi uban jarumai ai saika zauna don ka huta sannan na baka amsoshin tambayoyin da kayi mini dazu sarki sahibul hairi ya dubeta cikin kaduwa yace yanzu ni ina na ga lokacin zama alhalin nayi sata a cikin wannan gidan sarautar kuma na tabbatar da cewa da zarar an ankara cewa an dauke wannan gatari dole ne a bazama nemana'' . Koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta dubi sarki sahibul hairi da wani irin kallo mai tattare da alamomin tambaya tace ka kwantar da hankalinka yakai mai birnin Misra ka sani cewa kana tare da wadda tafi kowa sanin sirrin gidan nan. Gama fadin haka keda wuya sai ta mike tsaye taje kan wani tebul ta dauko tambulan na ruwan inibi tazo Gaban sarki sahibul hairi ta ajiye kofunan ta tsiyaya ruwan inibin a ciki sannan ta dauki kofi guda ta mika masa guda take ta kai kofin bakinta ta fara shan ruwan inibin , ya yinda sarki sahibul hairi yaga ta sha ruwan inibin sai shima ya sha nasa kyakkyawar tayi dariya tace ai nasan cewa in ban shaba kaima ba zaka sha ba domin akwai alamar cewa kana zargi zan iya ha intarka'' . Sarki sahibul hairi yayi murmushi ya ce ai a duniya idan akwai abinda nake tsoro bai wuce kaidin ya mace ba domin zata iya sawa mutum ya rasa mulkinsa dukiyarsa da rayuwarsa gaba daya. . Kyakkyawar tai murmushi tace hakika zancenka dutse ne to amma ina sonka saki jikinka dani domin nai maka alkawarin ba zan cutar dakaiba.sarki sahibul hairi yace to shikenan na gode. Yanzu kafin ki bani labarin komai ina son ki gaya min yadda akayi bawana haluf ya shigo cikin wannan turaka taki har ya kama barci haka tamkar yana cikin dakinsa kyakkyawar na jin wannan tambaya sai tayi murmushi tace na yarda zan baka wannan labari amma dole sai na fara da gabatar da kaina a gareka da farko dai ni sunana gimbiya shukura kuma nice matar sarki barusa mai mulkin wannan birni na Askandariyya. . Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama sarki sahibul hairi ya mike tsaye daga inda yake zaune ya danja da baya yace ke kuwa menene dalilin da ya sa kika ci amanar mijinki har kika taimaka mini na dauko wannan gatarin nasa na sihiri?? . Sa adda gimbiya shukura taji wannan tambaya sai ta bushe da mahaukaciyar dariya tace ai cin amanar maci amana ibadane yakai wannan jarumi kayi sani cewa asalin sarautar birnin nan ta mahaifinace amma tun ina cikin mahaifiyata uban sarki barusa ya kashe mahaifina alhalin ya kasance babban amininsa kuma wazirinsa don wai ya gaji dukiyarsa da karagar mulkinsa A wannan lokaci sarki barusa baifi shekara bakwai ba ni kuwa kamar yadda na gaya maka ko haihuwata ba ayi ba amma mahaifiyata na dauke da cikina wata shida bayan shekara bakwai sai uban sarki barusa ya mutu sakamakon cutar ajali don haka sai barusa ya gajeshi yana da shekara goma sha bakwai a duniya ni kuma a lokacin ina da shekaru goma kacal. . Tun kafin sarki barusa ya hau kan karagar mulki ya shaku dani ainun kuma yake nuna min tsananin kauna A zahiri ina nuna masa kauna amma cikin zuciyata na kanji na tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwata mahaifiyata ta bani labarin cewar a gaban idanunta mahaifin barusa ya kashe mahaifina ya haye kan karagar mulkinsa amma bai san cewa tana labe tana gani ba . Dama mahaifiyar tawa ta lura da cewa baruwa na sona don haka saita rokeni da na yarda na aureshi ko don na samu damar daukar fansar ran mahaifina akansa da wannan manufa a zuciyata na girma na isa aure a lokacin da aka daura mini aure da sarki barusa tsawon shekara shida ina tare dashi bamu samu haihuwa ba kullum sai nayi yunkurin hallakashi amma sai na kasa bisa wannan dalili ne na fake da batun tafiyar neman maganin haihuwa wajen bokaye amma a zahirin gaskiya ba maganin haihuwar nake nema ba .. Dama nake nema wacce zan iya hallaka sarki a cikin yawona neh na hadu da wani shahararren boka wanda ya sanar dani wai ba zan taba samun damar hallaka sarki barusa ba face na mallaki wadansu sirrikan tsafi guda dari ba daya su kuwa wadannan sirrika suna nan a jikin wata karamar yarinya mai suna alfila . Yar wani mashahurin matsafi kuma jarumin gaske ana kiransa da suna awaisu koda naji wannan batu sai na tambayi bokan nace yanzu ya za ayi naje inda wannan yarinya take har na sami sirrikan tsafi daga gareta? . Bokan ya kyalkyale da dariya sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa yace ke yarinya baki isa kije inda wannan yarinya take ba domin tana can cikin wani gida dake tsakiyar tekun bahar zallus mallakin sarkin bokayan aljanu na duniya mai suna shamzubul Azwas. . Yarinya ke dai baki isa kije wannan wuri ba har ki sami ikon shiga cikin wannan gida amma idan kikayi hakuri nan da wadansu yan shekaru kadan akwai wani jarumin sarki da zaizo birninku neman gatarin sihirin da kuke bautawa idan kika taimaka masa ya mallaki gatarin sihirin za ki iya tafiya tare da shi izuwa tsuburin bahar zallus ku shiga har cikin gidan boka shamzubuk Azwas ku dauko yarinya alfila a sannan ne saiki biya bukatarki ta samun surrikan jikinta'' . Lokacin da bokan yazo nan a zancensa sai na tambayeshi nace tayaya zan iya cire sirrikan tsafin daga jikin yarinyar? Koda jin wannan tambaya sai bokan ya bushe da dariya yace ai wannan kuma aikinmu ne na bokaye ba naku ba kedai da kinga kun dauko yarinyar saiki san dabarar da zakiyi ki raaba abokin tafiyar taki da ita ki kawota gareni. . Tunda naji wannan batu sai naji hankalina ya dugunzuma naji cewa ko kadan ban yarda da wannan boka ba da ga wannan rana na dada jajircewa wajan neman ilimin tsafi nayi yawo kasa kasa gari gari ina ziyartar bokaye ina yi musu alheri mai yawa suna koya mini tsafi sannu a hankali nima na zama gawurtacciyar bokanya a sirrance ba tare da mijina ya sani ba. . Don haka a yanzu ina sanar dakai cewa hadimul asur so yake kawai ka Kawo masa wannan yarinyar don cika burin rayuwarsa amma ba dan ya biya maka bukata ba ni a yanzu nayi maka alkawari indai ka taimaka mini muka dauki alfila na ciri sirrikan tsafinta guda dari ba daya zanyi tsafin da zaka zamo attajirin da babu kamarsa a duniya zaka auri wadannan yan mata uku da babu kamarsu a duniya kuma sunanka da mulkinka zasu shahara ko ina cikin duniya. Sa adda gimbiya shukura tazo nan a jawabinta sai sarki sahibul hairi yayi shiru ya shiga tunani mai zurfi yana juya al amarin a ransa daga can saiya dago kai ya dubeta yace. Na gamsu da duk jawabinki kuma na amince zan baki hadin kai domin mu cika burin rayuwarmu yanzu saiki amsa mini tambayar da nayi miki akan yadda akayi bawana yazo cikin turakarki . Har ya kama barci mai nauyi akan gadonki na alfarma nan take gimbiya shukura ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninta da bawa haluf ta zayyana masa har izuwa sa adda ta yaudareshi da batun zata ceci rayuwarsa da ta maigidansa dalilin da yasa ya bata kansa kenan suka kwanta tare shukura tace maganar gaskiya ban tara da bawa haluf dan na samu haihuwa ba sai don kawai naci mutuncin mijina . Kuma naci amanarsa saboda yadda nasan cewa yana tsananin tsanar bakar fata a rayuwar to yau gashi matarsa da yake matukar so fiye da komai a rayuwarsa ta kwanta da bakin fata kuma bawa. . Lokacinda gimbiya shukura tazo nan a zancenta sai takaici da mamaki suka kama sarki sahibul hairi ya jinjina kai yace hakika ku mata ababan tsoro ne domin dafinku da kaidinku yafi na maciji saurin tasiri a jikin dan adam hakika sai yanzu na fuskanci cewa ba karamar ni ima nake ciki ba da banyi aure ba shukura na jin wannan batu saita bushe da dariya tace haka kuma ba karamar ni ima kayi asara ba domin duk mutumin da bai taba yin aure ba ya rasa kaso tamanin cikin dari na dadin duniya. . Zama da su fitina rashinsu kuma asara sarki sahibul hairi ya ce har yanzu dai ban fahimci wannan karatu naki ba abinda nake so dake yanzu mu ajiye wannanzancen komai a gefe daya kawai ki fitar damu daga cikin gidan sarautar nan mu tafi izuwa tsibirin bahar zallus don shiga gidan boka shamzubul azwas mu dauko yarinya alfila gimbiya shukura tayi murmushi tace yanzun nan zan aikata haka amma dai ina mai dada yi maka tuni da cewar ka manta da batun bokanka hadimul asur cewar zai taimakeka idan ka kai masa yarinya alfila tabbas yaudararka zaiyi kawai ya biya tasa bukatar abinda nake so dakai shine ka bani wuka da nama indai muka mallaki alfila tamkar burinmu gaba daya ya cika ne sarki sahibul hairi yayi murmushi yace ai shi kenan na amince da duk abinda kika shirya na baki wuka da nama.. . A zuciyar sarki sahibul hairi ko kadan bai baiwa gimbiya shukura amana ba don haka duk yadda zaiyi ba zai yadda ta rabashi da alfila ba bayan sun daukota daga gidan boka shamzubul azwas acan karshen zuciyar sarki sahibul hairi sai yaji yana wasu wasu dangane da al amarin boka hadimul asur yaji cewa shima bai yarda da shiba kawai akawai alamun cewa shima akwai wani abinda yake so ya mallaka shiyasa yake son mallakar yarinya alfila . Abinda sarki sahibul hairi ya yankewa kansa hukunci shine indai ya sami nasarar dauko yarinya alfila kai tsaye zai tafi da ita zuwa ga mahaifinta sadauki awaisu sannan ya nemi taimakonsa bisa nemo wadannan yan mata uku . Sahibul hairi yace a cikin ransa idan idan har sadauki awaisu ya cika dan halak wanda yasan mutunci kuma har idan kaunar da yake yiwa yarsa dari bisa dari ce to lallai ba zaiki taimakonsa ba idan ya sada shi da alfila . Sahibul hairi na cikin yin wannan tunani gimbiya shukura ta runtse idanunta ta fara karanto wadansu dalasimai na tsafi fara hakan keda wuya saiga wata jibgegiyar halitta ta ratso ta cikin saman rufin dakin kamar haske ta fado a gaban shukura wannan halitta ba komai bace face ALJANU DABARUS. ALjani dabarus na da siffa irin ta bil adama wato yana da hannaye kafafu kirji wuya da kai sai dai kansa rabkeke ne yana da wangamemen baki cike da hakora hancinsa ma wawakeke ne amma idanunsa yan kanana neh ko yaushe jawur suke kamar gauta yana da dogayen kunnuwa wadanda suka kara masa muni fuka fukansa manya ne guda biyu . Koda saukar aljani dabaru a gaban gimbiya shukura sai ya rusuna ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shubata me kike bukata daga gareni? Ki sani cewa a shirye nake na sallama rayuwata don faranta miki shukura ta dubi aljani dabarus tace bukatata dakai kawai itace ka daukeni da wannan jarumin ka kaimu can tsibirin bahar zallus inda gidan boka shamzubul azwas yake koda jin wannan batu sai aljani dabarus ya kwalla ihu ya fadi kasa. Yana birgima da tuba yace kiyi min rai ya shugabata ki yi sani cewa tsakanin mutum ko aljan duk wand aya kusanci gidan boka shamzubul azwas take yake narkewa ya dige ya zama ruwa don haka ina mai rokonki daki sauya min aiki da wata bukatar amma ba wannan ba .... Koda jin wannan batu sai gimbiya shukura ta dakawa aljanu dabaru tsawa tace kai sha saha sha banza ai ba cewa nayi dole saika kaini har kofar gidan ba zaka iya ajiye mu nesa da gidan koda ya kai tafiyar rabin sa a ce mu mun san yadda zamu karasa can kai kuwa saika jiramu a baya inda zaka iya tsayawa Aljani dabarus ya saki murmushin murna yace yauwa yanzu naji kan zance wannan ai ba matsala bace saiku hau bayana mu dau hanya . Koda jin haka sai shukura ta bude wata akwatu ta dauko wata garkuwa ta zinare ta mikawa sarki sahibul hairi tace ka ruke wannan domin zata maka amfani a gidan boka shamzubul azwas ba tare da gardama da fargabar komai ba yasa hannu ya karbi wannan garkuwar da hannun hadu A hannun dama kuwa ya damke gatarin sihiri nan take shukura ta taba kafadar bawa haluf kawai sai ya farka daga barci ya mike zaune zumbur a firgice, amma da yaga sarki sahibul hairi tsaye a gabansa ruke da gatarin sihiri da bakuwar garkuwa sai murna ya kamashi gimbiya shukura ta dubi sarki sahibul hairi tace ai saika hau kan aljani dabarus ka zauna daga gaba dani da haluf mu zauna a bayanka. Sarki sahibul hairi yace wannan ba laifi bane nan take kuwa ya hau kan bayan dabarus ya zauna faruwar hakan keda wuya sai haluf da shukura suka yunkura da nufin suma su hau bayan dabarus: bazato batsammani sai sukaga bangon dakin ya dare gida biyu saiga sarki barbusa ya ratso ta ciki sanye da bakaken kayan yakin nan wadanda sarki sahibul hairi ya gani a gidan karkashin kasa a sakale a jikin bango tare da fararen daya sa da kuma jajaye. ni kaina bayyanar sarki barusa a wannan lokaci ya razanani kamar ba zan iya ci gaba da typing din ba amma nayi ta maza naci gaba... Sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin tsananin bakin ciki idanunsa cike da hawaye yace yake bakar annamimiya maci amana ki sani cewa karyarki tasha karya domin baki isa ki ha inceni ba har ki hada kai da makiyina don a nakastani a rabani da abin dogarona wato gatarin sihiri. . Na dauki so da kauna na gaskiya na baki tun muna yara kanana ashe ke ba kaunata kike ba asalima so kike ki hallakani to kin makara domin na gaba yai gaba na baya sai labari ki sani cewa duk hirar da kukayi yanzu tsakanin ki da wannan sarki duk na gani a cikin madubin tsafina don haka naji dalilin da ya sa kike son ki hallakani don ki dauki fansar mutuwar mahaifinki. . Haba shukura ni idan kika ce dole a kaina zaki dau fansa bakiyi mini adalci ba domin babu sa hannu na akan mutuwar mahaifinki asalima sa adda aka kasheshi ina yaro karami ban san abinda yake faruwa ba ba wai ina fadin haka bane donki janye ra ayinki sai donki sani cewa ke kin cika butulu maci amana haka kuma naji da bakinki kina cewa kin kwana da wannan bakin bawa don kawai kici amanata ki tozarta mutuncina tabbas kin sami nasara bisa hakan amma ki sani nima sai na tozartaki irin tozartawar da ba a taba yiwa wata ya mace ba a duniya kuma saina wulakantaki fiye da kima a cikin wannan birni namu na askandariiya yadda duk mai kaunarki idan ya tuno da abinda nai miki sai ya

Chapter 7 of 19