Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuka Huda tace “Allah Ummi kin isa” Mik’ewa tsaye Ummin tayi kafin tace “Idan har na isa to ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida ki gyara d’akin ki wanke toilet kafin ya dawo. Wallahi na manta yaushe zan ce na tab’a ganin Aslam yana gyaran d’aki amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k’i yarda saboda ya san nan d’in turakarku ce bai kamata a shiga ba. Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?. Ki tashi kije ki koma sannan idan ya dawo ki bashi hak’uri tare da alk’awarin ba zaki sake ba… In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad’a.” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin. Sai da Hudan taci kukan ta ta godewa Allah tukunna ta tashi ta sauk’a k’asan… Ta yarda zata zauna a d’akin amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam! Auren su ba na soyayya bane ba Infact k’ok’arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu so ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba bayan ba son juna suke yi ba so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d’insa……. Tana shiga d’akin k’amshin turarensa ya mata sallama, a hankali ta shak’a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b’acin ran da take ciki kuma yana d’an raguwa. Bud’e idanuwanta tayi ta shiga k’arewa d’akin kallo tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub’uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya zabga mata sannan yace “Ba zaki je ba!” ya juya ya fice. A hankali tace “Dama maza ma sun iya harara?” Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d’akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa. Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf. A wajen Ummi taje ta karb’o kasko da turaren wuta ta saka a d’akin sannan ta shiga kitchen ta had’a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita. Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama. Tana cikin jerawa Ummi ta sauk’o, dariya tayi kafin tace “Fad’a na ne? Ko kuma biyayyar aure? Ko dai bribe d’in a barki ki fita gobe??” Turo baki Hudan tayi sannan ta d’anyi murmushi. A hankali Ummi ta k’araso inda take ta dafa kafad’arta sannan tace “Na gode Huda. Kin nunamin nima na isa da ke” Ta yi maganar tana murmushi. Murmushi mai had’e da dariya tayi sannan ta fad’a jikinta tayi hugging nata tace “Ummina kin isa mana” A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k’aramin burgesu yayi ba kuwa, dan haka Shuraim ya k’araso ya yi joining hug d’in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k’afa shi ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special… Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k’araso yayi hugging d’inta. Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik’e da nashi a waje guda sannan ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a cikin nata kafin ta fara magana “Na san ba wani girman su Shuraim kika yi sosai ba amman dan Allah Huda ko bayan raina ki zame musu uwa ki yi musu dukkkannin abunda zan yi, ba su da kamarki a duk fad’in duniyar nan.” Da sauri Huda ta toshe mata baki da hannunta Idonta ya cicciko da kwalla tace “Ummi ki daina dan Allah kar ki d’agamin hankali da yammar nan! Bana son irin wannan maganar in sha Allah babu inda zaki je ki barmu muna tare...” Kukan da ya kufce mata ne ya hanata kasa k’arasa maganar tata. A hankali Shuraim ya yi hugging d’inta sannan ya d’ago idanuwanshi da suka taru da kwalla ya kalli Ummi yace “Ummi Ki daina irin wannan maganar please, muna tare happy family together forever in sha Allah” Ya fad’i hakan yana murmushi. Murmushi Sudais yayi sannan yace “Group hug!” Ya had’asu duka yayi hugging yana dariyar son ganin ya kawar da sad moment d’in. Suma duk dariyar suka saka suna sharar kwalla. Sun d’an jima a haka tukunna Shuraim ya jaa kujerar ya zauna yana cewa “Let me eat small.. Yau haddar pages biyu nayi, tunda muka tashi a English section nake abu d’aya amman dukda haka sai da Mu’allim ya rankwasheni, duk cikina ya zuge….” Tray d’in Aslam ya shiga k’ok’arin janyowa, nan Ummi ta hanashi ta hanyar buge masa hannu. Hudan na dariya ta shiga ta d’auko musu nasu wanda ta saka a cooler. Nan kuwa suka hau ci suna santi dan ana bud’e cooler Sudais ma ya dawo yace “ya fasa tafiya saman” Dariya kawai suka yi musu daga nan Ummi ta d’an jaa ta gefe tace “One last thing Taje ta yi wanka ta shirya.. Yana zuwa idan ya ga ta yi miishi kwalliya nan da nan zai barta maybe ma ya barta ta kwana, haka ake yiwa maza….tayi sauri maza maza taje ta shirya yana..” Tun kafin Ummi ta gama magana Huda ta wuce sama d’auko kayanta…kunya da kuma son aikata abunda Ummin tace ne ya sanya ta kasa tsayawa taji k’arshen maganar. Kamar yadda ta had’a akwatinta ta hau da shi saman hakanan ta had’oshi harda kayayyakinta waenda ta d’an d’auraye ta shanya, ta kwaso ta sauk’o da su. Ba iya d’akin ba Hatta parlourn zuwa yanzu ya d’auki k’amshin turaren wuta. Tana shiga ta ajjiye akwatin ta fad’a tayi wanka tayi brush ta d’auro alwallar Magrib dan ta gabato, ta fito d’aure da d’an guntun towel saboda bathrobe d’in da ya had’a ya wanke a washinne machine ya shanya tare da inner wears d’insa har yanzu bata gama bushewa ba. Wani had’add’en d’inkin doguwar riga A shape ta fitar, kalar atamfar royal blue an yi mata d’inki irin mai stones d’innan… A hankali ta ware bra da pant sannan ta kinkimi akwatin nata ta nufi wardrobe Bud’ewa tayi ta sa akwatin nata a chan k’asa sakamokon kayansa da ta gani a jere a side har biyu! A ranta tace “Wato har wasu kayanma ya sake kwasowa Ummi tana chan tanata cewa In dawo d’akin bayan shi gashi partyn shi ma yake yi ya samu freedom” Kamar tana ganinshi haka ta ke kallon kayan tana zabga musu harara… Idanunta ne suka sauk’a abkan wata takarda kamar poster haka a ta chan k’asan takardar taga an rubuta ‘2021 tournament mathematics competition Winner NTIC’ Da k’arfi taji gabanta ya buga! Da sauri tasa hannu ta zaro sticker……..tun bata kai ga k’arasa zarowa ba ta fahimci ita d’in ce da gaske! A hankali ta cirota daga k’asan kayan nasa tana kallo tana sake kallon hotonta da sunanta b’aro b’aro a sama ‘Maryam Huda Muhammad’ Ga award d’inta a hannunta da medal d’inta tana murmushi… Kanta ne ya d’aure ta fara k’ok’arin juya takardar dan kamar da tana zarowa taga rubutu a bayan da biro. “Bincike fa babu kyau” Taji muryarsa a bayanta daff da ita!. Bata san lokacin da ya shigo ba amman ta d’anji k’amshin turaren da yake tashi ata jikin kayanshi ya k’aru a d’akin. Kwakwalwar ta already a cunkushe take ga tarin mamaki gashi dama duhu ya d’an farayi bata kunna globe ba tana d’anjin tsoro hakan ya sanya da taji mutum da murya a bayanta ta kwala ihun da ita kanta sai da ta d’an tsorota…. Da sauri ya juyo da ita ya sa tafin hannunshi akan bakinta yace “Shiiii.” Da sauri itama ta sanya dukkanin k’arfinta ta b’intike hannunshi daga bakinta kafin tace “Ya Aslam banaso Allah ka daina” Ta fad’i hakan tana k’ok’arin kare jikinta a rikice dan ba k’aramin kunyar towel d’in take yi ba. Dariya ma shi ta basa Yarinyar da ya gama k’arewa kallo ba tare da ta san ya shigo ba itace take wani kakkare jikinta… Wani d’an guntun murmushin gefen baki yayi sannan ya kama towel d’in ta sama yace “Idan ban daina ba fa? What will you do? Yaji za ki sake yi min ki gudu sama , ko me?” Ya fad’i hakan yana d’an jan towel d’in kad’an kamar zai fisge. Cikin tsananin tashin hankali ta sake kurma wani ihun a karo na biyu…. Ido cikin cikin suke kallon juna, so take ta d’auke idanunta a cikin nashi amman ta kasa sakamokon sak’onnin da yake aika mata daga kwayar idanuwan nasa. A hankali ya bud’e baki zai yi magana yaji an turo k’ofar d’akin da d’an k’arfi an shigo..................... 5 MINUTES BEFORE NOW. Ummi, sauk’owarta kenan daga sama zata d’auki abu a kitchen, sam bata san Aslam ya dawo ba. Tana shiga kitchen d’in taji kamar an shigo dan haka ta d’au abunda take buk’ata ta fito tana kallon k’ofa… Sakin lemon hannun nata tayi ya fad’i k’asa cike da mamaki da murna tace “Arshaad!! Sai kuma ta k’arasa da sauri bakin k’ofar inda yake tsaye ta hau dudduba shi tana murmushi fuskarta cike da murna da farin ciki. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 63 Mikiya Writers Association. Murmushi Arshaad ya yi kafin a hankali yace “Ummi, na same ku lafiya?” Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi. “Alhamdulillah” tace, sannan ta d’aura da cewa “where have you been?”. Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali yace “Bara in d’an huta” Ya fad’i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi! Gabanta ne taji yad’an buga! Gashi babu damar ta tsayar da shi ko ta hanashi wucewa, a k’asan ranta tace “Anya kuwa zaman su Aslam da Arshaad zai yiu a waje d’aya?…” Tana cikin wannan tunanin ta jiyo ihun Hudan! Dakatawa Arshaad yayi ya juyo ya kalleta kafin yace “Kamar muryar Huda..” Shiruuu, Ummi ta d’anyi, chaan kuma ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tace “Eh, suna nan, Granpa refuse to accept them” Ya bud’e baki kenan zai yi magana suka sake jiyo ihunta a karo na biyu.. Ita Ummi har ga Allah tayi tunanin wani abun ne ya sameta dan batayi zaton Aslam d’in ya dawo ba! Shiyasa tayi saurin nufar d’akin, ba tare da b’ata lokaci ba shima Arshaad ya bi bayanta da sauri…. NOW. Wardrobe d’in a setin k’ofar yake a ta tsaye! Shiyasa suna shiga suka gansu…. Da mugun sauri Arshaad ya juya Ummi kuwa da kyar kunya ta barta ta iya jan y’an k’afafunta ta bar wajen. Ko kyallin Arshaad bata gani ba, ga de akwatinsa nan a tsakar parlourn inda ya barshi… Wucewa tayi sama da sauri dan ji tayi kamar za a bud’e k’ofar d’akin su Hudan a fito. Achan d’akin kuwa su Ummi suna fita Huda tasa kuka! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin Ya Arshaad wanda suka had’a ido dashi! Shikenan ta san yanzu zai ce taci amanar sa ta gama! Bayan ko sati uku ba ayi da yin bikin ba…… Shiruu, Aslam ya d’anyi yana kallonta ta rufe idonta tana kuka ta duk’unk’une a tsaye waje d’aya, ajiyar zuciya ya sauk’e…..a hankali taji kamar ya bar wajen. Addua take yi Allah yasa fita zai yi, ai kuwa a hankali taji ya bud’e k’ofar ya fita. Tana bud’e ido taga ita kad’ai, ajiyar zuciya ta hau sauk’ewa a jejjere, da kyar ta samu ta d’an nutsu tukunna ta soma k’ok’arin barin wajen.. Poster da ta sub’uce a hannunta d’azu ta taka! Kalla tayi ta sake kallo kamar tanason yin nazarin wani abun chan kuma sai ta lumshe idonta ta bud’e kawai ta d’auka ta mayar inda ta ganta. Jikinta duk a sanyaye hakan nan ta samu ta shirya da kyar ta nemi waje ta zauna. Aslam yana fita ya fara k’arewa falon kallo kamar akwai abunda yake nema. Yana cikin kallon parlourn Idanuwanshi suka sauk’a akan trolley madaidaici. Wani yawu ya had’iye mai d’an d’aci tukunna ya furzar da iska ya nufi d’akin da yake da tabbacin Arshaad d’in yana a ciki. Knocking ya tsaya ya d’anyi, jin shiru yasa ya tura k’ofar ya shiga… Ganin ba kowa ya sanya yayi tunanin to ko dai ba nan d’in ya shigo ba, har zai juya sai ya jiyo motsin ruwa a toilet. A hankali ya sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya nemi waje ya zauna a bakin gadon. Morethan 10 minutes Arshaad ya d’auka a band’akin bayan shigowar Aslam. Har Aslam d’in ya fara tunanin lek’awa a ransa yana tunanin ‘maybe ko baya ciki an yi mistake d’in barin fanfo a kunne ne’ sai kuma yaji an kashe tap d’in! Still sai da ya k’ara 2 minute tukunna ya fito ya na tsane fuskarsa da towel…. A tunanin Aslam wanka Arshaad d’in yayi amman fitowar da yayi sanye da kayan jikinshi ne ya sa ya fahimci ba wanka yayi ba sai dai ko alwallah dan gashi ya nad’e dogon hannun white shirt d’in jikinsa gashin hannunsa a kwakkwance sajensa da sumarsa suka duk a jik’e. Murmushin da Arshaad d’in yayi masa ne ya katseshi daga nazarin da ya fad’a. A hankali ya mik’e tsaye yana kallonshi har ya k’araso inda yake tsaye. Aslam yana shirin yi masa magana yaji yace “Sorry.. Ban san kuna tare ba Ummi and I tot wani abun ne ya sameta shiyasa mu....” “Where have you been??” Muryar Aslam d’in ta katseshi. “Maldives” Ya bashi amsa a tak’aice sanann ya d’an wuce sa yayi hanyar fita yana ci gaba da cewa “Already na riga na yi arranging komai for honeymoon” Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Arshaad, i.......” Da sauri Arshaad yace “Let’s pray! Naji har an kusan shiga masallaci.” Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice. Aslam ya dad’e a tsaye kafin ya samu ya iya motsawa daga inda yake shima ya fice. Bai sameshi a wajen ba sai a masallacin, a gefensa ya tsaya suka yi sallar, sai da sukazo fita tukunna suka had’u da su Shuraim.. Suna ganin Arshaad d’in suka nufeshi suka yi hugging nashi cikin tsananin farin ciki..Sudais yana dariya yace “Ashe baka manta ba” Murmushi yayi kafin yace mishi “Ai na gaya maka last year daman ko Ina inane zan dawo ayi celebrating this year da ni” Murmushi dukkansu suka yi suka nufi gida. Suna shiga su Shuraim suka yi sama shi kuma Arshaad ya jaa akwatin shi ya nufi d’akin da ya zab’awa kanshi. Bai san Aslam yana tare da shi ba sai da ya shiga d’akin ya juyo zai rufe k’ofar! tukunna suka yi ido biyu. A bud’e kawai ya bar mishi k’ofar daga nan ya juya ya jaa trolley d’insa ya kai ya ajjiye. Yana juyowa ya ga Aslam d’in still a tsaye, murmushi yayi kafin yace “Ka k’araso ka zauna mana” “Arshaad listen, we have...” Cikin katseshi Arshaad d’in yace “We have to talk ko? About Huda! Aure! And everything right?” Numfashi ya fesar kafin ya cigaba “Akan me to za muyi maganan abunda ya riga ya faru ya wuce?” Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ba abun magana kam gaskiya, i ust want to know how you feel about us, together, and everything sannan kai! Are you ok??” Murmushi Arshaad yayi mai had’e da dariya kafin yace “Aslam i feel fine! Sannan I’m Ok. Tunda har ka ga na dawo Nigeria Kano to I’m Ok Aslam. So kawai abunda zan gaya maka shine kar ka dubani kace zaka yi affecting relationship d’inku negatively, ni ban ma san kuna gidan nan ba da a hotel zan zauna zuwa jibi inzo a yi birthday da ni daga nan in nemi inda zan je saboda I still can’t face Mammy! Sannan ba zan iya zama a tsakiyarsu ita da Dad suna fad’a kamar Annabi da kafiri ba. But still zuwa jibi zan san yadda zan yi in sha Allah….” Da sauri Aslam ya matso inda yake yace “No, you don’t have to. Kar ka je ko ina…” Cikin katseshi Arshaad yace “I’m sorry to say this amman after yadda kake feeling guilty right now akan halalin ka saboda ka san na ganku i definitely need to go! Kuna buk’atar air, in fact your relationship is somehow complicated dan haka kuna buk’atar time da space In other for you two to build a healthy and happy marriage.. If I can’t help banga dalilin da zai sa in zauna a tsakiyarku ba ina sakaku kuna feeling somehow. Zan iya rantse maka akan cewa I have moved on! And na manta da komai na cire Hudan a raina completely but na san ba lalle ka yarda ba, itama ba lalle ta yarda ba, za ku dinga gani kamar ko in kun yi abu zai sa inji ba dad’i ko wani abu makamancin haka wanda hakan zai sa ku kasa sabawa da kuma sakewa da juna, ni kuma har ga Allah ba zan so hakan ba, therefore i think i need to stay away for some months ko a year haka.. Maybe nima idan na tashi dawowa In dawo da tawa bride d’in” Ya k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarsa. A hankali Aslam ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yasa hannu ya janyoshi jikinshi yayi huggin nashi..... K’arar wayarsa ce ta sanya shi cika Arshaad d’in yad’an matsa sannan ya zaro wayar ya d’auka yasa a kunnenshi yace “Auwal” D’an jimm! Yayi, chan kuma yace “what for?” A hankali kuma sai yayi murmushi yace “Bara mu fito, Arshaad is home ma.” Bai jira jin me Auwal d’in zai ce ba ya katse kiran ya d’ago yana kallon Arshaad kafin yace “Mu je, Auwal ne” Bai musa shi ba ya bi bayanshi suka fita…… A babban parlourn suka sameshi, zaune cikin d’aya daga cikin set d’in kujerun dake a parlourn. Yana hango su ya taso, duk da halinda yake ciki hakan bai hanashi k’arasawa yayi welcoming Arshaad warmly ba. Aslam ne ya katse su ta hanyar cewa “Mai ya faru ne? You sound worried! Yanzun ma kuma you look worried” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Tana Ina please? Bani da energy…..” Gaba kawai Aslam d’in yayi shi kuma ya bishi a baya. Suna zuwa k’ofar d’akin nasu ya murza ya shiga Auwal d’in kuma ya tsaya a waje. A zaune ya sameta, ta rafka uban tagumi…sanye cikin doguwar rigar da ta fitar d’azun zata saka. A rayuwarshi blue is one of his favorite colours, gashi blue d’in mai d’an duhu wanda ya taimaka wajen fito da ainahin kyawun farar fatarta..Yanayin dim light d’in dake kunne a d’akin ne ya taimakawa stones d’in jikin rigar tata wajen yin kyalkyali na musamman mai d’aukar ido da hankali… Normal d’aurin d’ankwali tayi irin na ture ka ga tsiya wanda ya fitar da uban tulin gashinta da ta tufke ta nannad’eshi a k’eyarta. Ba komai a fuskarta ko mai bata shafa ba amman kalar kyan da tayi masa yau dole ya bada tukuici!. A hankali k’asa k’asa yadda ta tabbatar ba zai ji ba tace “Ni fa bana son kallo” Tana mai d’auke kanta daga gareshi had’i da d’an turo baki. Murmushi kawai yayi sannan ya tako gabanta ya tsaya yace “Saboda me yasa bakya son kallon?” Runtse idanuwanta tayi, a ranta tace “Wannan ko maciji albarka” Batai auni ba taji yasa hannunshi a nata ya mik’ar da ita tsaye yana kallon rigar jikinta kafin ya maida idanunsa a kan d’ankwalin, murmushi yayi yace “D’aurin masifaffu dama yafi yiwa masu tsiwa kyau.” Haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa d’agowa da kuma kasa cewa komai, still bata san daliliba amman maganar tasa ba k’aramin dad’i tayi mata ba! A take taji haushin shi da fushin da take yi da shi suna d’an raguwa… Ya jima yana kallonta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ki je Auwal yana parlour yana jiranki, muryarsa har rawa take yi, da alama emergency ne.” Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya dan ta san me ya kawo shi. Sai da ya sake cewa “Ki je” Tukunna ta iya jan k’afafuwanta ta d’anyi baya kad’an ta yadda ta tabbatar ba zata gogeshi in ta zo wucewa ba sannan ta wuce. Har ta kusan k’ofa taji yace “ungo” Tana juyowa ta ganshi a kusa da ita yana bata hijab d’inta. Tsayawa tayi bata matso ba balle yayi tunanin zata saka… A hankali ya matsa inda take yana kallonta itan ma shi take kallokafin ta yi k’asa da kanta kamar d’azu. Yanayin yadda ta yi d’aurin tabbas in ya saka mata a haka zai iya shak’eta shiyasa yasa hannu ya zare d’ankwalin ya rik’e a hannunsa So yake ya saka mata hijabin amman kyau da shek’in da gashin yayi da kuma yanayin parking d’in da tayi ne ya yi mugun tafiya da imaninshi dan haka ya tsaya ya shagalta da kallo…. A hankali yaji tace “Bara in je, ka ce ce emergency ne” Ba tare da ta d’ago kanta ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauk’e kafin a hankali ya ware hijabin kamar baya so..sai da ya nemo fuskar hijab d’in tukunna ya ajjiye d’an kwalin nata a gefe ya sa hannuwanshi duka biyu ya bud’a ya kawo dede setin fuskarta yace “Raise your face” Tana d’agowa suka had’a ido yana kallonta itan ma shi take kallo ta cikin hijabin. A hankali ya matsar da hijabin yasa mata a fuska sannan ya d’an jashi ya zauna dede kafin ya ida warewa ya sakar mata shi ya rufe ilahirin jikinta. Tana shirin wucewa taji yayi cupping fuskarta yad’an matso kusa da ita. A zabure ta d’ago tana kallonshi shima ita d’in yake kallo kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya kai lips d’insa dede goshinta ya sakar mata light peck d’in da ya sanya ilahirin jikinta d’aukar rawa! A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matsar da bakinsa a dede setin kunnenta yace “You look beautiful tonight” Yana gama fad’in haka ya cikata ya wuce toilet dan yana buk’atar yad’an watsa ruwa kafin lokacin dinner, garin yau akwai zafi sannan shi kanshi kwana biyun nan yana saurin jin zafin yanayin dauriyace kawai yake yi. Da kyar ta samu k’irjinta ya d’an ragu da bugawa sannan ta d’an dedeta kanta ta fita wajen Auwal. Tare ta tadda su a parlourn shi da Arshaad. Gaba d’aya sai ta tsinci kanta da diriricewa kamar mara gaskiya, ta tsaya. Tun sanda ta fito Arshaad ya ganta, ganin duk ta rikice ta kasa k’arasowa ne yasa yace “ko In baku guri ne?” Ya fad’i hakan da d’an k’arfi ta yadda ya san za ta jiyo sa. Da sauri ta d’ago ta kalli inda suke, suna had’a ido ya sakar mata lallausan murmushi sannan ya sake maimaita tambayar tasa. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta fara takawa ta isa inda suke ba tare da ta sake yarda sun had’a ido da Arshaad d’in ba. Murmushi kawai yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga daddanawa…., Tana zama Auwal ya juyo gaba d’ayanshi gareta ko gaisawa bai iya tsayawa sun yi ba yace “Dan Allah da gaske gobe za a kawo kud’in auren Sakina?” Ba k’aramin tausayi ya bata ba dan har wata kwalla taga ta taru a idanuwanshi.. A hankali tace “Ya Auwal duk abunda kaga Allah bai yi ba muddin ka yi addu’a to ba alkhairi bane, ka kwantar da hankalinka zaka samu wadda ta fita in sha Allah.” Cikin katseta yace “Da gaske ne kenan” A hankali muryarshi na d’an rawa. D’agowa tayi da niyyar sake bashi hak’urin ya rungumi k’addara kawai taga hawaye bibbiyu suna zubo masa! Da sauri ta runtse idonta tace “Ya Auwal dan Allah ka daina mana, ka rungumi k’addara kayi adduar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi” Bud’e baki yayi da niyyar yin magana sai kuma ya kasa, da sauri ya tashi ya fita a side d’in gaba d’aya ba tare da ya sake waiwayon su ba. Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana jin tsananin tausayin Auwal a ranta. Kamar ance ta d’ago, tana d’agowa suka had’a ido da Arshaad, murmushi ya sake sakar mata kafin yace “Abun tausayi, ko?” Sunkuyar da kanta tayi a hankali ta d’aga kan alamar “Eh” Yana shirin yin magana Ummi ta sauk’o! Har ga Allah haka kurum sai ta tsinci kanta da rashin jin dad’in ganinsu a zaune su biyu. Tana zuwa ta nemi guri ta zauna kusada Huda ta kamo hannunta k’asa k’asa tace “Huda tunda ba ku kad’ai bane a gidan, ku dinga saka key a k’ofar ku mana. Wallahi ban san ta ina zan fara kallon Aslam ba” Da sauri Huda ta sunkuyar da kanta k’asa sosai wanda hakan har sai da ya sanya Ummi ta d’anyi murmushi. Sarai Arshaad ya ji abunda suka ce amman bai nuna musu ba! Hasalima chatting d’insa kawai yake yi yana murmushi. Ganin hirar tata ba zata yiu da Hudan ba yasa ta juyo ga Arshaad tace “Ka je wajen Mammy?” Sai da yad’an k’ura mata ido, kamar ma bai ji abinda tace ba tukunna yad’an gyara zaman shi ya maida wayar

Chapter 9 of 26