na fahimci
K’arya
Yaudara
Da tsoro
a lamarin Ashraff.
Inaso ka zo mu je mu samu Mahaifinsa
a nan na tabbatar in dai mutumin kirki ne
to gaskiya za ta fito k’arara!
But first
sai na fara kulle asibitin nan da mai asibitin tunda karb’ar cin hanci ya maida sana’a”
Bai gama rufe bakinshi ba
Likitan ya shigo!
Sai da ya kallesu one by one
tukunna ya k’arasa inda Ummu take ya shiga yi mata bayani akan wasu takardu da ya shigo da su yanzu….
“Case d’in Sakina fa is severe!
In ba a fitar da ita
a yau ko gobe ba
tou tabbas
za a samu babbar matsala!
Shima sai yanzu ya ke ganin wannan result d’in bayan ya tsananta bincike…..”
Kasa magana Abba yayi
tsabar mamaki da takaici
dan haka kawai ya turawa commisioner of police message
tare da adress d’in asibitin daga nan ya cewa Baban Sakina “ya zo su je..”
Suna fita ya ce mishi su wuce gidansu Ashraff.
A motar Abba ya yiwa Baban Sakina k’arin haske akan abunda ya fahimta game da Ashraff d’in kuma aka ci
sa a Baban Sakinan ya fahimceshi.
Ba Baban Sakina ba hatta Abba sai da ya cika da mamaki
da suka k’arasa k’ofar gidan
suka tarar da tafkeken masallacin juma’an dake a jikin gidan cike da jama’a
anata shige da fice.
A hankali da kamala suka kutsa kai suka shige ciki, sakamokon hango Mahaifin Ashraff ya gilma ciki sanye cikin shiga ta alfarma.
Ba su gama tunanain meke faruwa ba
suka ji a loudspeaker ana
“An d’aura auren Ashraff Muhammad Bashir
Da Suhailat Yusuf Tanko
a kan sadaki naira dubu d’ari uku
lakadan ba ajalan ba.”
Kallon kallo suka hau yi
kafin su hau kallon jamaar one by one…
Chaan! Suka hango Baban Ashraff d’in da suka biyo cikin masalllacin, yana ta fara a yana gaisa wa da wasu Abokanayen sa na jiki jiki
waenda suka samu damar halartar d’aurin auren gaggawan da aka gaiyyacesu.
Yana ganin Baban Sakina hankalinshi ya d’an tashi! Dan a iya saninshi
bai gaiyyaceshi
besides auren ma ai secret aka yishi to
me kuma ya faru?!
Bai gama dawowa dede ba
suka k’arasa wajen shi da Abba suka zauna a kusa da shi.
Abba ne ya iya bashi hannu suka yi musabaha
Baban Sakina kuwa da kyar ya iya ce mishi
“Barkanmu..
Dan Allah d’an yi min elaborating abunda na ji an fad’a
yanzu.”
Sai da Baban Ashraff d’in ya d’an kalli gefe da gefen shi
tukunna ya mik’e ya ja su gefe
ya fara magana k’asa k’asa
“Kasan me ya faru ne?
Yaron yanzu sai a hankali wallahi….”
Sai kuma ya d’an yi shiru kafin ya fesar da numfashi ya ci gaba da cewa
“Shi Ashraff an d’an samu matsala ya je ya yaudari wata Yarinyar oga na
wanda shi ya siya min takardar kujerar sanatan da nake mulka a yanzu! Hatta campaign shi yake taimaka min da komai.
Kaga ni d’an siyasa ne
In na yi mishi butulci ban kyauta ba kuma siyasata za ta samu matsala tunda party d’inmu d’aya.
Jiya Yayar Yarinyar ta kira Mahaifiyarshi direct…
To kasan mata abun nasu sai a hankali, a take sai ta yi mata fata fata kuma ta ce ‘ba dai Ashraff d’inta ba’.
Tofa shine Yaran su kuma suka je suka samu Mahaifinsu
da Mahaifiyarsu suka fad’i komai.
Adress da sunana kawai ya karb’a ya gano Ashraff d’ana ne!
Yau da safe sai ganin shi na yi.
Baban sakina ko kaine a situation d’in da nake
na san dole ka yi abunda nayi.
Amman ka kwantar da hankalinka
Aure tsakanin Ashraff da Sakina babu fashi! In sha Allah lokacin da muka d’iba yana cika za a d’aura musu aure.
Jiya sai cikin dare Ashraff ya dawo gidan nan
a hargitse wallahi ya bani tsoro
kuma hakan ya sanya na sake fahimtar yana tsananin k’aunar y’arka dan na san tabbas labarin ta ji suka d’an samu matsala shiyasa ya damu har haka..
Kar ka ce za ka yi interfering
dan Allah kar kace za ka yi komai ka barsu,
dan Ashraff jiya har d’an k’aramin hauka ya yi!
Idan ka ce za ka hanashi Sakina ban san ya za ai ba”.
Cikin tsananin b’acin rai Baban Sakina ya ce
“A jiyan da ya dawo muku a haukace ka san me ya je ya yi?”
Bai jira jin amsarshi ba
ya ce
“K’wamushe mini y’a ya je ya yi!
Ya kaita wani asibiti suka had’a baki da mai asibitin aka manna mata ciwon hauka!
Yanzu haka da ka ganmu
da farko shirin d’aura musu aure shi da ita muke yi
saboda ya ce ya san wani k’warerren Likita
A New York
Inkuma aka barta ba a kaita wajen Likitan da wuri ba
to zata iya mutuwa.”
A firgice Baban Ashraff d’in ya ce
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Sai kuma ya dafe kanshi
kafin ya d’ago ya ce
“Kayi hak’uri Alhaji Muhammad
Ashraff yayi laifi
amman wannan yana yi maka nuni da abunda hanashi ita ka iya jawowa!
Na tabbatar tsorata yayi
shiyasa yayi hakan!
Yanzu ka kwantar da hankalinka
zan yi mishi magana
ba zai k’araba
In sha Allah
Lokaci yana yi za a d’aura musu aure
a samu a zauna lafiya”.
Shi kam Abba dariya ma Mutumin ya so ya bashi…
Yana shirin yin magana ya ji Baban Sakina ya ce
“Unfortunately, Alhaji ka yi hak’uri amman itama Sakina akwai wanda na ga ya fi dacewa ta aura!
Za mu dawo muku da duk wasu kud’ad’en ku
da kaya
dan na janye maganar aurenta da Ashraff gaskiya!
Bawai saboda Ashraff ya yi aure ba..not at all.
Zan yi hakan ne saboda yadda na ga kana shakkar Mahaifin Yarinyar da ka aurawa d’anka a yau
na tabbar idan ya ce kar a yiwa y’arsa kishiya to ba za ka bari ba.
Cikin b’acin rai mutumin ya ce
“Wai Alhaji Muhammad ya mutum kamar ni da girma na ina yi maka magana har da magiya amma kana yi min musu???”
Ciki sauk’e ajiyar zuciya Baban Sakina ya ce
“Shiyasa zan barka In bar maka d’anka
dan ba zan iya musun rashin gaskiya da kai ba”
Yana gama fad’in haka ya wuce inda ya ga limama, ya same shi ya gaya mishi wata magana kafin ya dawo inda Abba yake tsaye shi da Baban Ashraff ya ce masa
“Kana da sadakin da zaka bayar na Auwal ko sai ka je banki?”
Kallonshi Abba ya yi a d’an rikice sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yana murmushi
kafin ya ce
“akwai a mota,
bara in je in d’auko”.
Ko minti biyar bai yi ba ya dawo….
Alokacin limamin har ya d’an tara jama’a an zazzauna.
Yana zuwa bayan an shirya komai ya mik’a sadaki
ya yiwa Auwal wakili…a take aka d’aura auren
Auwal Yusuf Umar Farouk MT
Da
Amaryarsa Sakinat Muhammad
a kan sadaki naira dubu d’ari biyu
lakadan ba ajalan ba.
Ana gamawa Baban Ashraff ya juya ya fita fuuuuu!
Daman tun d’azu ko zama kasa yi yayi
yana mamakin tsaurin ido da taurin kai
Irin na wannan talakan mutumin............
Ana shafa Fatiha
Abba ya bayar aka siyo alawowi a shagon gefen su
aka zo aka rarraba
aka watse..
A take ya kira su Dad ya sanar da su good news.
Kasa hak’ura suka yi
suka ce ya bawa Baban Sakina wayar
Shi kam har d’an kunyar irin godiyar da suka dinga yi mishi ya ji, daga nan suka yi sallama
suka nufi wajen Granpa domin sanar da shi.
Su Abba kuma suka koma asibiti wajen Sakina.
Suna shiga dede suka tarar ta farfad’o amman Mama da Ummu sun danneta
Likitan yana k’ok’arin sake sank’ama mata wata allurar yana cewa
“Ai dama na gaya muku!
Ku duba fa kugani
irin abubuwan da take yi
if possible a wuce da ita kawai
Yau!
Tunda na ji Yaron ya san garin da Likitan, shi zai yi komai dan haka komai zai zo da sauk’i.”
Da sauri Baban Sakina ya je ya kwab’e allurar daga hannunshi!
Yana shirin yin magana y’an sanda suka shigo.
Babban su ne
ya k’araso ya karanto mishi laifinshi....
Tabbas Likitan ya san Ashraff zai fito da shi tunda ba ayau suka fara harka da shi ba!
Yasha kawo mishi mata ya cire musu ciki amman duk da haka sai da ya ji gabanshi ya fad’i!
Da kyar ya dake
ya bi bayansu salin alin
bayan ya turawa Ashraff d’in message….
Suna fita Sakina ta ce “wallahi Abba k’alau nake, Ashraff munafuki ne! Shi ne ya shak’a min hanky d’insa wanda Allah kad’ai ya san girman kwayar da ya saka a jiki
shiyasa nake jin k’aik’ayi a kaina kuma yanzu na daina.
Dan Allah ku fahimceni
Munafuki ne!
Baba dan Allah kar ku kaini wajen Likitan mahaukata……”
Matsawa inda take Baban nata yayi a hankali ya dafa kanta ya ce “ba komai
komai ya wuce
ki kwantar da hankalinki
kin ji?
Mun yarda da ke
Aaima ta fad’a mana komai ai”
Kallonshi kawai Ummu da Mama suke yi….:
A hankali cikin nutsuwa ya karanto musu yadda suka je suka tarar ana d’aurawa Ashraff aure da komai
da kuma yadda suma suka d’aura auren Sakina da Auwal a yau…..
Wani sassanyan murmushi ne ya sub’ucewa Mama a hankali ta ce “Alhamdulillah”
Abba da yake kallonta ne ya ce
“Ma sha Allah.”
Yana sakin nashi murmushin.
Sakina kuwa wani irin kuka ta saki.......
Direct parlourn Granpa
Dad da Daddy suka nufa.
a nan suka iskeshi shi da Gramma yana jik’a towel yana d’aura mata a ajiki.
Ba yadda suka iya haka suka sanar da y’ay’an nasu rashin lafiyar Gramma d’in
wanda hawan jinine yake neman yi mata illa tun rasuwar Ummi….
Ba k’aramin tashin hankali su Dad suka shiga ba kuwa.
Da kyar!
Granpa da Gramma d’in suka lallab’asu suka d’an nutsu
bayan sun gama shiryawa akan za a fitar da Gramma d’in waje ta d’an huta ta samu change of environment
ko da na wata d’aya ne
ta yarda.
Sai da Granpa ya tambayesu
tukunna suka tuno da zancen Auwal da Sakina
dan haka suka zaiyyano musu labari tiryan tiryan…..
Mik’ewa Gramma ta yi
ta zauna tana murmushi ta ce
“Alhamdulillah na samu
another grand in-law
Allah ya sanya albarka
dama inata addua wallahi
saboda Yarinyar ta shiga raina tun a ranar da suka zo za a kai Huda.
Barka Alhamdulillah.
Auwal sai ya warke ai yanzu
Ja’iri mai ciwon so.”
Dariya duk suka yi har da Granpa kafin Granpa d’in ya ce
“Yanzu abunda zai faru shine..
Ku fara shirye shiryen visar har da na ita matar Auwal d’in,
Yahaya
ka kirawo Kakan ta
ka sanar da shi cewa
Duba da yanayin halin da Mijinta yake ciki
muna so mu tura mishi ita da wurwuri!
At least a samu ya warke da wuri ja’irin.”
Dariya duk suka yi nan ma
kafin Granpa ya ce
“Sai ta wuce as soon as possible
mu kuma idan mun yi welcomin Maryam sai mu wuce da washe gari ko?”
Ya fad’i maganar yana dafa kafad’un Gramma.
Murmushi kawai ta yi ta sunkuyar da kanta
dan duk sai ta ji ya bata kunya.
Daddy ne ya ce
“Inyeee..
Grand honeymoon za.....”
Bai k’arasa ba
Gramma ta d’auko throw pillow ta buga mishi!
Da sauri suka mik’e suka fita shi da Dad
suna dariya.
A hankali Gramma ta kwanta a jikinsa tana sauk’e ajiyar zuciya kafin
ta ce
“Thank you Daddie”
Murmushi kawai yayi
yana me shafa kanta
a chan k’asan zuciyarsa kuma yana regretting
abubuwan da ya yiyyi.. ashe haka happines d’in frank family life yake
amman
ya dinga depriving kanshi da zuri’arsa ba tare da ya sani ba?
Tabbas miskilanci da mugun hali bashi da rana....................
BULAMA ✍️
Bismillahirrahmanirrahim
So da Buri
Free Book
71
Barkanmu da sallah Al’ummar Musulmi🥰
Allah ya maimaita mana, Ameen.
Abba Madu yana gama waya da Dad
Motar su Baban Sakina tana yin parking.
Sai da Baban Sakina ya raka su har ciki
tukunna ya ce
“Bari ya je ya samu d’an uwanshi ya sanar da shi halin da ake ciki.”
Yana fita su kuma suka fara korawa Shuwa bayani….
Har ga Allah Shuwa ta ji dad’in hakan..at least su duka ukun za su zauna a family d’aya.
Basu damu da gyangyad’i da jirin da take yi ba (dan allurai da abun da Ashraff ya shak’a mata masu k’arfi ne sosai)
Haka suka duk’ufa wajen gyarata
Ita kam anayi ma tanata baccin ta.
Sai dare tukunna Huda ta samu ta kira Mama
Gramma Ummu da Abba ta gaidasu.
Suna gama waya da Abba
ta fara jiyo motsi dan haka tayi sauri ta runtse idanuwanta
kamar mai bacci.
Dama ya bata dinner ta ci ta yi sallah tukunna ya fita bayan ya ce mata “bara ya je ya d’an yi aiki”
Dan in dai yana gabanta to ya san ba abunda zai iya tab’ukawa.
Yana ganin yadda ta lumshe idanun nata ya fahimci ba bacci take yi ba!
Murmushi kawai ya yi ya k’arasa y’an abubuwan da zai yi ya hayo kan gadon. Tashi d’aya ya lura da yadda jikinta ya hau b’ari dukda kuwa baccin k’aryar da take shararawa
amman he cant help it!
Ba k’aramin k’ok’ari ma ya yi aka kawo yanzun ba.
Addua ya yi ya tofa ya shafa mata shima ya shafa.
Jin an shafa mata addua ya sanya hankalinta yad’an kwanta a tunaninta kyaleta za ayi amman inaa
nan take ta ji sabon labari…
Babu daman kwacewa
dan yau ma Aslam d’in da gaskensa ya zo mata kamar jiya.
Babu kalar magiyar da bata yi amman yayi mata kunnen uwar shegu!……
Ga rad’ad’i ga azaba ga ciwon kai ga rashin bacci
shiyasa kafin asuba zazzab’i ya rufeta, ruf!.
Shi ya kira family Doctor ta zo da sassafe ta yi mata allurai harda k’arin ruwa tukunna ta d’an ji dama dama…
Ba abunda yafi bata tsoro irin yadda ya sake zuwan mata yauma kamar jiya da shekaran jiya.
Ita kam har mamaki da tsoro ya fara bata dan idan yana
wani abun kamar wani mai aljanu..yanzun zaka ganshi garau amman yana d’aukar hanya zai birkice sam baya ji baya gani.
Bashi da aiki sai dai ya bata abinci ya yi ta lallab’ata yana faman lallashinta yana kula da ita, ya yi ta gaya mata kalaman soyayya yana lallashinta
Idan dare yayi kuma a koma ruwa......
Tun a washegarin ranar
aka shirya musu komai na tafiya.
Basu wani sha wahalar yiwa Sakina komai ba
saboda Dad ne akan komai.
Auwal, bai san da labarin ba
dan ko da aka gayawa Mom
da ta ga jikin nasa yad’an nutsu kamar ya sani
sannan nan da kwana biyu Sakinar zata zo
sai kawai ta barshi akan sai ta zo d’in ya ganta
kawai a surprise
Another thing kuma tana tunanin in dai Auwal ya ji an aura masa Sakina kuma tana Nigeria tou tabbas zai iya tsige oxygen d’in ya dawo gida ko bai gama warkewa ba.....
Tun lokacin da aka ce ‘visar su ta fito gobe zata wuce’
Take kuka! Har yau da safe..Shuwa da su Baaba Talatu da Ummu ne
sai kuma matar wan Mijin Ummu sai wata distant cousin d’insa, suka shirya za su kaita MT.
Suna cikin shiri Anty Zainab ta shigo ita da su Khadija waenda zuwansu kenan.
Da mamaki Mama take kallon Anty Zainab d’in wadda duk
ta rame ta lalace jikinta yayi mugun sanyi kamar ba itaba
ko dan ta jima bata ganta ba
dan ko ranar da Kaka ya kirata ta je bata ganta ba
tana d’aki wai tana bacci.
Inda Mama take Anty Zainab ta nufa tana zuwa ta rungume ta sai kuma ta fashe da kuka!.
Duk tsayawa suka yi suna kallonta da mamaki.
A hankali Mama ta zaro ta daga jikinta kafin ta ce
“Haba Zainab kuka kuma?”
Cikin share hawayenta ta ce
“Dole in yi kuka Maryam!
Dole in yi takaici da bak’in cikin abubuwan da na aikata..
Na yi miki laifi na yi kuskure wanda a yanzu nake matuk’ar danasani, sam! Na kasa nutsuwa na kasa yafewa kaina.”
Sai da ta share hawayenta wasu suna sake zubowa tukunna ta d’aura da cewa
“Yanzu haka daga gidan me unguwa nake..na je na fad’a masa gaskiyar laifin da na yi miki
sharrin da na yi miki
wanda yayi sanadiyyar har aka koroki a makaranta..
Na gayawa Kaka shima gaskiya.
Ki tayani neman yafiyar Abba dan Allah Maryam
kema ki yafe min
na yi kuskure
Sadiya ta cuceni! Wallahi duk hud’ubarta ce ta sanya na juyawa aminiyata
baya”
Ta k’arashe maganar tana fashewa da wani sabon kukan.
A hankali Mama ta yi hugging d’inta tana murmushi kafin ta ce “Zainab! Har ga Allah ba zan ce miki zan iya mantawa da abunda kika yi mini ba a lokaci guda ba, dan zan
iya cewa ke ce ummulabaisin fad’a na da su Abba.
Amman maganar yafiya kam
wannan na yafe miki Allah ya yafe mana gaba d’aya.
Sanna ki yi k’ok’ari ki yafewa Sadiya itama ko ba komai kar abun ya yi mata yawa
saboda ko da bakin y’an layi aka barta ya isheta!
Dan kowa idan ya tashi magana ita, kowa matsalarsa Sadiya…
Idan mu bamu yafe mata mun yi mata fatan alkhairi ba wa zai yi?”.
Wani sabon kukan Anty Zainab ta fashe dashi tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Mama.
Da kyar su Shuwa da Ummu har Maman suka samu suka lallasheta ta nemi waje ta zauna tana gunjin kuka.
Basu kai ga fara magana ba
Madu ya shigo ya ce “Su fito da Sakina ga motocin MT sun k’araso”
Sai a lokacin ta saki kukanta mai sauti….
Haka nan tana kuka tana komai Mommy da Mammy suna shigowa aka d’auketa aka fita da ita.
Tana shiga motar motocin suka d’auki hanyar MT.
A b’angaren Gramma aka ajjiyeta.
Hudan, daman ta san da zuwan nasu dan basu ma dad’e da gama waya da Sakinar ba, shiyasa tana jin shigowar motoci ta lek’a ta sama da yake gidantane a farko farko yasa ta hango su.
Tama manta da ciwon kafa da na jikin da take yi…Haka nan tana takawa tana d’an d’ingishi ta nufi hanya..
Da kyar ta iya sauk’a daga benen farko kawai sai ta durk’usa a wajen ta saki kuka…
A haka Aslam ya shigo ya sameta.
A rikice ya k’arasa ya hau tambayar ta ‘me ya sauk’o da ita?’.
Ko kallon sa bata yi ba
ta mik’e kawai ta fara k’ok’arin wucewa wanda sai a lokacin ne ya gane matsalarta…
Dariya da tausayinta ne suka rufeshi amman ya dake ya b’ata rai ya ciccib’eta.
Duk kalar rigima da yakushin da take yi mishi da kuka bai diretaba sai da ya kaita kan gadon tukunna.
A hankali ya zauna ya kamo hannunta tana shirin mik’ewa ya ce “Ki nutsu.
Kin san dai Sakina ba zata tab’a wucewa ba tare da ta zo ta yi miki sallama ba ko?
Ki kwantar da hankalinki
yanzu ma da na ajjiye su na ji suna cewa duk za su shigo miki kafin su wuce”
Shiru ya yi yana kallonta still kafin ya ce
“Yanzu ke idan aka barki a haka a wannan yanayin naki za ki je gaban su Ummun?”.
Sai a lokacin kanta ya d’an d’au chaji. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin ta ce
“Ya Aslam tou dan Allah ka je ka taho da su, kar su k’i zuwa.”
Sai da ya d’an yi shiruu tukunna ya kamo hannunta ya rik’e ya d’anyi kisssing sannan ya ce
“Okay love,
amman ki nutsu kin ji”
D’an d’aga masa kai ta yi alamun ‘okay’.
Ya d’an jima yana kallonta yana murmushi
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya
a hankali ya ce “Alhamdulillah”tukunna ya mik’e ya fice
a ranshi yana tunanin ta yadda Hudan take so ya je ya sake fuskantar su Ummu!
Shi fa da kyar ma ya iya tsayawa suka gaisa
especially ma Mama lokacin da ta rako Sakina har k’ofa,
wata irriyar kunyarsu yake ji gaba d’ayansu. Shi kam gaskiya idan Mama ta k’araso estate d’inma bai san taya za su kaya ba.
Cikin ikon Allah yana sauk’a parlourn chan k’asa
Khadija da Yayarta suka shigo tare da Gramma da Sakina, dan Sakinar tunda taga su Ummu za su tafi ta sake d’aga hankalinta
shine Gramma ta ce ‘bara ta yi bribing d’inta ta kaita wajen y’ar uwarta’.
A parlourn sama Gramma ta ajjiyeta bata k’arasa chan sama ba ta juya ta fice
dan tashi d’aya ta fahimci Aslam d’in baya so ta had’u da Hudan.
Ba kunya haka ya kinkimeta bayan ya koma sama wajenta wai zai kaita wajensu.
Da kyar sai da ta saka mishi kuka tukunna ya sauk’e ta
ta yi practicing tafiyar da zata yi a gabanshi ta d’an dedeta yanayinta dan duk tayi kalar da duk mai hankalin da ya ganta sai ta tona masa asiri ne, ga kuma ciwon k’afa da na jikin da suka taru suka sauk’ar mata da d’ingishi.
Sannan ya kama mata hannu ya d’an karata a jikinsa
suka sauk’a tare.
Suna tahowa Khadija ta fara yi mata dariyar tsokana k’asa k’asa
Sarai Hudan ta fahimceta amman ta basar dan bata shirya biye mata ba
Ita a ganinta wannan lamarin da take ciki jaje ya kamata ayi mata ba tsokana ba
dan ita komai ya wuce tunaninta.
A kusa da Sakina ya ajjiyeta
kafin ya ce
“Su zama ready
nan da 2 hours su Sakinar za su wuce
In sha Allah”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita.
Yana fita Huda ta fad’a jikin Sakina ta yi hugging d’inta.
A hankali ta ji Sakinar ta sa kuka, d’agowa ta yi ta d’an b’ata rai itama idonta yana kawo kwalla ta ce
“Haba mana dan Allah ki daina kar ki saka ni kuka nima”
Ta fad’i haka ragowar hawayenta yana zubowa.
Murmushi su Khadija ita da yayarta suka yi
kafin Yayartata ta ce “to yanzu wa zai lallashi wani?”
A hankali Huda wadda taga d’an rashin kyautawarta
ta juya ta yi hugging Khadijar
sannan ta kamo hannun Yayar khadijah daga inda take zaune ta ce “ina wuni”
A hankali tana murmushi dan itama yanzu duk ta sauk’o ta ce “Alhamdulillah, gida yayi kyau Huda Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya”
A hankali ta juya cikin d’an tsokana da dauriya ta yayewa Sakina fuskarta, dan har yanzu fuskar tata a rufe take cikin mayafin laffayar da aka nad’a mata.
Da kyar ta iya daurewa batayi kuka ba, fuskar nan tayi dagaje dagaje ta yi jajawur
kana gani ka san ta ci uban kuka bana wasa ba, daman tun shekaran jiya da suke waya take jin yanayin muryarta a dashe.
Cikin son sakata nishad’i
ta ce
“Haba mana Sakina, ki daina
kuka, kinga fuskarki kuwa?
Gashi duk kin yi wani laushi kamar ba ke ba.
Ai ba wai zama za ku yi achan d’in ba har abada, yana warkewa fa za ku dawo in sha Allah…Ni kumafaa daa? da zan tafi chan wani gari ba ke kika yi ta bani kwarin guiwa ba?”
Ta k’arashe a hankali daga nan ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana.
Su Khadija ne suka saka baki, suka taru suka yi ta lallab’ata
har sai da ta d’an sake ta bar hawayen ta d’an kwantar da hankalinta tukunna
suka d’an shiga hira a hankali.
Khadijah ce ta ce
“Gaskiya Huda gidan ki ya had’u over!
Kalla kuma kaya koina duk girman gidan.
Bara mu lek’a mu kashe kwarkwatar idonmu”
Ta fad’i haka tana ajjiye mayafinta ta mik’e.
Itama yayartata mik’ewa ta yi.
Hudan har ta mik’e ta d’an fara takawa za ta bisu Khadija ta kamo hannunta ta zaunar da ita ta ce “zauna mai tafiyar ta’ta’taaa mun san hanya”
Duka Huda ta kai mata ta yi saurin gocewa tana dariya
suka nufi k’asa ita da yayar tata.
Banda dukan uku uku ba abunda k’irjin Sakina yake yi
daman tun d’azu ta d’an tsorata da yanayin tafiyar tata da ta gani.
Maganar da Huda ta fara yi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani da tsoron data tafi. A hankali ta juyo tana kallonta jin tana cewa
“Ya Arshaad ya sake guduwa..
Ba a san inda yake ba!
D’azu inaji Ya Aslam suna maganar shi da Dad a waya
da na tambayeshi kuma sai ya k’i gaya min komi, kamar ma haushi ya ji.”
Ta k’arashe maganar cikin karyewar zuciya.
A hankali Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce
“Hudan
I can’t even begin to imagine what Ya Arshaad is goin through! Dauriya ce kawai yake yi dan haka idan ya ga ba zai iya zama ba ya nuna yanaso zai tafi
ya kamata ku bashi space
ku barshi ya tafin.
Kuma dan Allah ki daina nuna damuwarki over a kan Ya Arshaad a gaban Ya Aslam…Yes! Na san dole abun is somehow amman ki d’an dunga daurewa har Allah ya yaye miki son shi a zuciyarki
ki manta da shi ki rungumi Mijin da Allah ya zab’a miki ku zauna lafiya
dan na san Ya Aslam yana sonki wallahi tun a mansion d’in chan naso In fahimci wani abun
shiru kawai na yi miki.”
Shiruuu, Hudan ta yi kamar tana tunanin wani abu
kafin chan ta ce
“Yauwa Sakina, kin san
wani abun
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 26