Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka yi makaranta secondary ajinsu d’aya! To irin sun d’an shak’u d’innan kamar besties haka suke. Wata rana Ina tunawa muna level 1 lokacin ya zo kawo mata ziyara (shi bestyn nata) sai suka zo shi da wani Abokinsa mai suna ‘Sageer’ Tun da Sageer ya kyalla ido ya ga Suhailat tashi d’aya ya ji yana sonta! Kasa ma hak’ura yayi mu koma a lokacin dayake ni na rakata, a take yake cewa Abokin nasa shifa ya ga mahad’in shi! Bai bar wajen ba sai da number da address d’in gidansu Suhaila na nan Kano. To ashe itama Suhailan duk kanwar ja ce dan muna komawa d’aki itama ta haukace mun haka nan ta dinga yabon kyawun Sageer d’in da had’uwar shi sanann ta sanar da ni yanda ya samu kyakkyawan gurbi a cikin zuciyarta. Kafin wata d’aya Soyayya da shak’uwa mai zafi ta shiga tsakanin Suhaila da Sageer... A Dawowar da nayi kafin exams lokacin bikinku da Ya Arshaad, kafin In koma wani mumunnan alamari ya afku ata dalilin rashin wayon Suhaila! Ta biyewa soyayya ta mallakawa Sageer kanta gaba d’aya bayan ya d’auketa sun je sun yi court marriage sai kace wasu marasa mafad’i! A cewar sa hakan zai sanya ta yarda da shi ta aminta ita zai rayu da har abada tunda ita a tsarin gidansu Mace sai tayi phd tukunna take yin aure! Haka nan Babansu yake da wannan muguwar ak’idar, shi kuma Sageer ya ce ‘in dai ita kad’ai zai so kuma ita kad’ai zai aura zai kula to ya kamata ta fahimci a yanayin tsarin halittarshi ta d’a Namiji ba zai iya yi mata wanann dogon jiran ba’. In tak’aice muku labari dai ciki yana yin wata d’aya ya baiyyana kanshi a jikin Suhaila! Dan tsananin laulayin da take yi ya sanya hatta matan dake gefen d’akin mu sai da suka soma fahimtar wani abu game da wannan k’addarerren cikin! Dan ta ce babu kalar protection d’in da ba suyi using ba. Ba yadda muka iya haka muka rufa mata asiri mu uku muka nufi asibiti da ita dan tace idan Baban ta ya san labarin wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i! Yadda kika ga Granpa to haka itama Babanta yake da mugun tsauri! Kuma ita abun nata ma duka biyu za a iya cewa dan Mahaifiyarta itama hakan take da tsauri. Muna zuwa muka zubewa Likitan kud’i muka gaya mishi flushing muke so a yi mata duk da tanata ce mana ance ‘tana da matsala cikin ba zai fita ba’ Amman still muka zab’i mu gwada sa’ar mu.. Bayan y’an gwaje gwaje unfortunately Likitan ya zaunar da mu yayi mana cikakken bayani akan cikin nan ba zai fita ba! Saboda tanada matsala kuma in dai ance za a cire d’in tou it’s either ta mutu ko kuma ta samu uterus failure. Bamu da wani zab’in da ya wuce mu nemi Sageer duk da kuwa ta ce mana ‘tun last zuwanshi da ta ce mishi tana da ciki ya d’auke ta ya kaita asibiti aka gaya mishi abunda aka gaya mana! Kwana d’aya kawai yayi mata a gidan da suke had’uwa daga nan ya k’ara gaba kuma tun daga ranar ko wayarshi ta kira a kashe take jin ta. Although bai nuna mata komai ba dan faram faram ma suka rabu ko amai idan ta yi shi yake kwashewa ya gyara gurin yanata faman jera mata sannu’. Wani babban tashin hankali da abun al’ajabin da muka fuskanta shine Hatta gidansu Sageer da address d’insu da ya bayar a garin Gombe gaba d’aya fake ne! Hatta sunan Babanshi Alhaji Bashir mai galon da ya fad’a mana gaba d’aya k’arya ne. Har Gombe d’aya a cikinmu ta rok’i saurayinta ya je ya bincika mana amman babu abu d’aya da yake gaskiya a cikin labarin Sageer! Komai fabricating kawai yayi. Da muka fahimci haka sai muka koma wajen Bestien ta, to shima dai ta wajen na sa duk sammakal dan ce mana ya yi shima Iyakar wannan information d’in da muka sani akan Sageer shima shi kad’ai ya sani, ya ce a wajen ball suka had’u suka fara shiri suka d’anyi business tare ranar kuma suna tare ya ce masa zai je wajen k’awar shi shine yace zai rakashi. Shi bestyn nata ma cewa yayi wai ‘mu yi ta addua gaba d’ayan mu maybe aljani ko maye muka had’u da Allah ya tak’aita’.” Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e sannan ta ci gaba da cewa “To yau dai Allah ya had’ani da Sageer!” Bata gama rufe bakinta ba ta mik’a musu hoton data nemo a wayar tata tun d’azu……… Sakina ce ta fara karb’ar wayar tana kallonta kafin ta sauk’e idonta a kan wayar. A hankali Huda ta ce “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Bayan itama ta l’eka ta gani. Sakina kuwa lumshe idonta kawai ta yi ta bud’e ta kalli Aaima idonta jazir tap kwalla ta ce “Aaima are you sure??” “Very sure Sakina! Ki yi ta sliding za ki ga pictures da videos d’insu kala kala irin wannnan shi da Suhaila. Daga nan ki gaya min Idan wannan bawan Allahn ba Ashraff bane ba.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 69 Mikiya Writers Association. Kai kana ganin fuskokinsu ka san suna cikin tashin hankali ba na wasa ba. Kallo suke suna sake kallan pictures d’in amman ba ta inda za su ce ba Ashraff bane ba. A hankali Sakina ta mik’a mata wayarta sannan ta ce “yana Ina?” Ta yi mata tambayar tana k’ok’arin mik’ewa tsaye. Cikin ruk’o hannunta Aaima ta ce “Ya tafi” Sannan ta d’aura da cewa “Mai aiki nasa taje har chan waje ta shigo da shi parlourn Mammy. Abunda ya bani mamaki ya kuma d’aure min kai shine yadda ya nuna kamar irin kwata kwata babu alamun yama tab’a ganina d’in nan sannan kuma he looks calm and innocent! Kasa hak’ura na yi bayan mun gaisa na ce mishi “Sageer” Amman sai na ga yana kallona da mamaki! Ganin da nayi ban ma san abunyi next ba yasa kawai na ce masa ‘ya tafi, dan Allah yayi hak’uri wani abun ya taso min urgent!’ Cikin fahimta ya nuna min ba damuwa ya mik’e ya tafi. Sakina kaina ya d’aure saboda a ganina inda ace Sageer d’in ne to da ko a idanunsa zan fahimci firgici! Da d’an alamun wani abun dole zai nuna amman kuma ko twins banajin za su iya zama super identical haka kamar shi da sageer.. Hatta fa yanayin magana kallo tafiya komai nasu iri d’aya ne..” Cikin katseta Sakina ta ce “Kar ki damu Aaima, ba wani Sageer sunanshi Ashraff! Shine! Raina miki hankali kawai yayi. Ga Abokin sa nan ma Abbakar a wanann hoton.” Da sauri Aaima ta karb’i wayar ta kalla sai kuma ta ce “Ai shine Saddik d’in” “Hmm” Kawai Sakina ta ce tana mai dialing numbershi a wayarta. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin tace “Kuma kin san abunda zai sa ma mu sake gasgata shi d’in ne… Ranar farko da suka fara zuwa a ranar da ya had’u da Suhaila da ya ce mata ‘I’m Sageer by name’ Sai da Abokin nashi ya juya a zabure yana kallonshi sai kuma na ga ya fara murmushi yana girgiza kai.” Dede nan Ashraff ya amsa call d’in Sakina… Daman a handsfree ta saka “Hello baby” Suka ji ya fad’a. Sai da Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta ce “Ashraff ko Sageer?” “My god!! Waye ne Sageer d’innan ne? Kin san i was just about to call you sai kika kira… That cousin of yours she looks confuse! Tana ganina ta ce min Sageer itama. Ask her ta yi miki bayani please dan i d.........” Cikin katseshi ta ce “Dakata Ashraff! Ba ita bace confused, ni ce! Bayani kuma ba ita za ta yi min ba kaine!. So I’m all ears Ina so inji ta yadda ka chanja sunan ka da kuma yanda kake planing zaka yi da mu Ni da Suhaila da kuma d’an cikinta” “Oh Noooo! Innalillahi wa innailaihirrajiun Sakina haba mana. Tana ina ita cousin d’in taku? Bata wayar please… Wallahi daman yadda na ga tayi na san akwai matsala, waye Sageer? Wacece Suhaila? Ciki kuma a Ina?. Sakina na riga na gaya miki y’an mata biyu kawai na yi dating b4 you and duk na nuna miki pictures d’insu, please Sakina kar ki biye mata i think akwai confusion a lamarinta amman wallahi ni ban san wani Sageer ba, bata wayar please”. Fashewa kawai ya ji Sakinar ta yi da kuka, cikin kukan ta ce “Haba Ashraff! Despite abunda ka yi da k’aryar da ka yi still kana so ka ci gaba da b’oye b’oye? Wat have i ever done to you to deserve this?” “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kawai ta ji yanata maimaitawa kafin ya ce “Shikenan Sakina, na gane! Yanzu na fahimci komai… Kina neman hanyar da za ki zillemun ki auri Auwal d’in da kike ta tunani kullum ko? Ko kina tunanin ban saniba ne? Idan ba kya sona ki fito fili kawai ki gaya min ki daina yi min kwana kwana! Bawai ku had’a baki ba ku k’ulla min sharrin abu mai muni haka ba. Wallahi tallahi kin ji de na rantse miki ni ban san wani Sageer ba ban san wacece Suhaila ba sanann wallahi Sakina da gaske nake sonki ba yaudara a ciki! Ke kad’ai ce a cikin zuciyata” Ya fad’i haka yana me fashewa da kuka kamar k’aramin Yaro sai kuma ta ji ya kashe wayar, kiit!. Ashraff, yana kashe wayar ya kira Saddik yana d’auka bai jira jin me zai ce ba ya ce “Saddik, I’m doomed….” Sanann ya hau koro mishi bayani hankalinshi a mugun tashe. Shiruu Saddik d’in yayi bayan ya gama ji kafin ya ce “Listen closely Ashraff..................” Gaba d’ayansu hankalinsu a tashe yake, bama su san ta Ina za su fara ba. Aaima ce ta yanke shawarar kiran Suhailar dan haka ta d’au waya ta shiga sunanta ta danna call…… An fi thirty minutes tukunna aka samu layinta ya fita daga busy ta amsa kiran Aaiman. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin ta ce “Da wa kike waya haka?” Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce “Wata friend d’ita ce” Shiruu, Aaiman ta yi tana tunanin wacece k’awar Suhaila haka da bata san ta ba… Sanin ba wannan ne a gabansu ba ya sa kawai ta kawar da zancen ta hanyar bata labarin Sageer Ashraff from A -Z kafin ta ce “Yanzu ko gidan su idan kinaso zamu iya zuwa dan Sakina ta ce ta san gidan kuma zata bamu adress har number Mamansa.” Cikin katseta Suhailan ta ce “Mun gama case d’in Sageer fa! Ki manta kawai please, kar ki sake yi min maganarsa” A rikice Aaiman ta ce “Kin gama case d’insa da cikinsa a jikinki??” “Please Aaima” Shine kawai abunda Suhaila ta ce. Aaima za ta yi magana kawai ta ji ta katse kiran. Kasa cire wayar daga kunnenta Aaiman ta yi, da kyar ta d’ago tana kallonsu still da wayar kare a kunnenta. Kirane ya shigo wayartata dan haka ta d’an zabura saboda a kunnenta wayar take har yanzu… Tana ganin mai kiran nata ta d’auka da sauri ta ce “yauwa Khadija kin san me yake faruwa? Yanzun nan....” Cikin katseta Khadijar ta ce “Sageer, yanzun nan ya kira Suhaila…. Suna fara magana ta tashi ta shiga bathroom, haka kawai na ji inaso in yi mata lab’e saboda na san kusan wata nawa ana neman shi sai yau kawai muga ya kirata. A yadda na fahimta Its like akwai wadda zai aura a yanzu! Wai family d’insu sun zab’a masa shiyasa ma ya d’auke k’afa amman yayi mata alk’awarin aure nan da wata biyar muddin ta yi shiru. Ban gama dawowa daga mamaki ba na ji conversation d’in ku a waya yanzu. Meyene yake faruwa?”. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e rai a b’ace ta ce “Wato shine Ashraff d’in ta tabbata kenan!…” Nan ta d’an yi briefing Khadija a kan case d’in sannan ta ce “Khadija Suhaila tana son Ashraff ba zata tab’a iya k’etare umarninshi ba! Dan haka yanzu aiki yana a hannunki.. Ki taimaki y’ar uwar ki tunda ni dai kinji yadda muka yi da ita. Zan turo miki number Mamansa yanzu daga nan ki kirata ki yi mata bayanin komai! Lokacin b’oye b’oye ya wuce dole iyaye su shiga case d’innan. Mugun tantiri ne Ashraff d’innan wallahi! Kin san yadda ya nuna kuwa kamar bai sanni ba amman kalli har ya kirawota munafuki d’an iska! Kuma wallahi k’arya yake yi shi ya ga Sakina ya ce yana sonta ba wani had’asu da akayi Infact Families d’insu ma basu san juna ba sai ata dalilin ita Sakinar da shi Ashraff d’in. Wanne irin rashin wayone haka Suhaila take yi! Dan bayan soyayya tabbas akwai dak’ik’anci a cikin lamarinta, saboda Allah ace wai Mutumin da yayi maka wannan abun tashi d’aya ya dawo ya kalallame ka kuma ka yarda? Duk da ban san me ya ce mata ba amman ai ya kamata ta tambayeshi dalilin da ya sa ya bamu fake adress ko?” A hankali Khadija ta ce “Tabbas” Sannan ta ce ‘Ta tura mata number Maman ashraff d’in ta kirata yanzu ba sai anjima ba kafin Suhaila ta dawo d’akin.” Da “to” ta amsa sannan ta katse kiran kafin ta kallesu ta ce “Yayar Suhailan ce, Itama ta san da zancen. Ina number Maman nashi?” Kamar yadda Sakina ta fad’a haka ta bada number Maman Ashraff bayan sun kwantar mata da hankali da kyar! Dan da cewa ta yi sai ta je ta sameshi a duk inda yake! Hudan ma harda y’ar kwallarta ganin yadda Sakinar duk ta firgice ta fita haiyyacinta tana ta kuka wiwi. Gaba d’aya sun gigita da lamarin Ashraff. .......... Suna zaune a d’akin wata maid ta shigo musu da abinci kala kala.. Aaima da Huda ne suka d’an ci Sakina kam har yanzu hankalinta a tashe yake, ashe ita ta yi gudun gara ne ta tadda zago ba tare da ta sani ba… Sai bayan sallar Magrib tukunna Junaidu ya kirata ya ce “taje yana waje, su wuce.” Aaima ce ta rakata har bakin mota bayan sun sha kukan su ita da Huda sannan sun d’an yi mata y’ar guntuwar Nasiha suma, dan itama Aaiman ba komawa za ta yi ba sunyi sallama kenan saboda ta san Huda tsaf sai ta rik’eta kamar yadda ta kanainaye Sakina. Duk da halinda Sakina take ciki sai da ta fahimci kallon da Aaima da Junaidu suke yiwa juna! Tun d’azu dama da za a kawo Huda ta d’an lura yanzu kuma ta sake tabbatarwa dan har tana yiwa Junaidun magana ma bai sani ba. Kasa hak’ura tayi bayan sun d’au hanya ta ce “Ya Junaidu ko dai In had’aku ne?” Wani lallausan murmushi ta ga ya yi kafin ya ce “A’a fa Sakina, tuwon girma ai miyarsa nama! Idan na d’auko wannan ina da wajen ajjiyeta ne?” Da sauri Sakina ta ce “Ya Junaidu ranar nan fa na ji Kaka yana cewa Gidajen ka wajen biyar a Kano kawai ga motoci ga filaye.” Dariya ya yi this time around sanann ya ce “Ki bar maganar nan.. Although har ga Allah i felt something towards her very strong amman tunda na rasa Huda i don’t think zan yi aure idan ma zan yi d’in to gaskiya ba nan kusa ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e tana kallon yadda fuskarsa ta chanja lokaci guda. Daga haka motar ta d’auki shiruuu kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, har ya kaita k’ofar gidan nasu ya ajjiyeta. Tana sauk’a yayi reverse ya juya dan akwai ayyuka da dama akanshi. Tana shirin tura gate d’in gidan ta ji ya ce “Sakina” Da sauri ta juyo! Daman taga kamar motarshi a parke d’an gaba kad’an. Ganin sa d’in ne kuwa yasa ta had’e fuska tamau! Kafin ta ce “Naam, Sageer.” A hankali ya k’araso inda take, sai da hasken globe d’in k’ofar gidan nasu ya haska fuskarshi da kyau tukunna ta lura da abun mamaki.. Gani tayi yana kuka wiwi fuskarshi har ta kumbure da alamun ya dad’e yana yi. Tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa “Sakina komai Aaima ta fad’a muku gaskiyane nine Sageer! Amman asalin sunana Ashraff. Ba zan b’oye miki ba… Har ga Allah tun farkon had’uwata da Yarinyar na ji ina sonta amman ba so na aure ba sha’awace kawai irin wadda shed’an kan saka a zuk’atan waenda ya yi nasara. Na san Abbakar Abokina ne tun Yarinta. Muna barin gurin ya tambayeni ‘dalilin b’oye mata asalin sunana da na yi’ Ban b’oye mishi ba na fad’a mishi k’udurina a kanta! Ya ji ba dad’i kuma yaso nusar da ni amman da yake shed’an ya riga yayi galaba a kaina yasa sam ban ji ba.” Matsowa ya sake yi kusa da ita wanda hakan yasa ta d’an ja baya. Cikin kuka kamar Yaro ya ce “Sakina na yi laifi, na san na yi laifi! Amman dan Allah ki fahimceni ki fahimci k’aunar da nake yi miki ta tsakani da Allah ce. Ki duba kiga yadda ita na fad’a mata fake adress fake suna and everything Ke kuma na fad’a miki komai nawa! Har waya kuke yi da Mamana. Dan Allah kar ki bari a rabamu, ki toshe kunnuwanki, fight for our love! Ko wanne d’an Adam ajizi ne ni ga nawa mistake d’in dan Allah ki fahimceni kin ga gashi na fad’a miki komai ban b’oye miki ba, ki yi min adalci Sakina.” Girgiza kai kawai Sakina ta yi sannan ta share hawayenta ta ce “Meyasa ka zab’i ka gaya min yanzu? Saboda an kira Maman ku ko? Kuma ka san dole case zai taso… Bara ka ji Ashraff magana d’aya kawai zan iya gaya maka saboda at this stage ba zan ma iya tolerating ganinka ba! Saboda abubuwan da ka yi sunada yawa ban san ta Ina zan iya farawaba… Abunda nake so ince kuma nake so ka fahimceni da kyau tunda naga kana da sharp brain shiine Ba zan aureka ba!” A gigice ya d’ago yana kallonta. “Kwarai!! Babu wannan maganar. Ga responsibility d’inka chan ‘Suhailat’ Ka koma gareta ka nemi yafiya ku haifi d’anku ku zauna lafiya ku reneshi a tare!” Tana gama fad’in haka ta juya zata shige gidan ya yi saurin ruk’o hannunta. A mugun fusace ta juyo bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani irin mahaukacin mari jikinta har karkarwa yake yi ta ce “Na rantse maka da Allah idan baka bar nan ba zan iya yi maka illa! Dan duk abunda na raruma sai na maka ma saboda raina ya kai k’ololuwa wajen b’aci! Audacity d’inka shi yafi komai d’aga min hankali Ashraff! Ka ma raina min hankali wallahi! How kake tunanin.....” Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da magana chan kuma ta ce “Kaga! Just go, kama gabanka. Like i said Idan na ce zan yi maganar abubuwan da ka yi da renin wayon da ka zo da shi yanzu to ba zan iya jurar ganinka k’alau akan k’afafuwanka ba! So just leave!!!!” Ta k’arashe maganar cikin tsawa sannan ta juya ta tura zata shige cikin gidan ta ji ya ruk’ota! Za ta yi magana ta ji ya toshe mata baki da hanci da wani handkerchief.... Sai dare tukunna Granpa ya tara su Dad da Gramma ya fad’a musu d’aurin auren Maryam da Abba next week in sha Allah. A ranar Abba kasa bacci yayi yadda ya ga rana haka ya ga dare! Daga k’arshema ma ji yayi cheecks d’inshi sun fara ciwo tsabar murmushi. Tun ba ma da ya kira Mama ta kula shi sosai ba. Kaka ma ya samu Madu, babu alamun wasa a fuskarshi yace “In dai har yanzu yana yi mishi kallon Mahaifi a wajen Maryam to ya sani ya saka ranarta! Rana ita yau su Granpa za su zo a d’aura aure. Kuma dan girman Allah kar ya tambayeshi dalili ko ya yi mishi musu indai yana buk’atar Abotar su ta d’aure har k’arshen rayuwarsu.” Murmushi kawai Madu yayi kafin ya ce “Kaka ai Abotar mu har aljannah in sha Allah ba abunda zan bari ya shiga tsakani dan haka duk abunda ka yanke na goyi bayanka blindfolded….duk da ban san dalilinka ba amman i trust you kuma zan yi sopporting d’inka d’ari bisa d’ari! So dan Allah kar ma ka sako maganar lalacewar Abotar mu Allah ya kaimu ranar asabar d’in da rai da lafiya.” Ya k’arashe maganar yana murmushi. Duk fushin da Kaka ya kwaso daga gida sai ya ji gaba d’aya ya kau. Dan haka yad’an sake suka shiga tattauna abunda ya shafi alamuransu mostly a kan Jalila. Kafin daga baya ya nemi ganin Mama itama…. Same yada ya yiwa Madu itama haka yayi mata kafin ya d’aura da cewa “Indai ta d’auke shi a matsayin uba har yanzu tou kar ta yi mishi jayayya kawai yanaso ta amince da abunda ya zo da shi” Daga anan ya d’aura mata da Nasiha akan ‘kar ta rik’e Abba a ranta komai ya wuce su zauna su yi rayuwarsu kamar farko Allah yayi musu albarka.’ A hankali ta ce “ameen” sannnan ta yi mishi godiya daga nan ta mik’e ta fita. Wata nannauyar ajiyar zuciya Kaka ya sauk’e yana jin wani nauyi yana sauk’ar mishi tun kafin ya kai ga sauk’ewa gaba d’aya……. Tana zaune a kan darduma ta idar da sallar isha kenan Gwaggo Asabe ta shigo da akwati sai kuma Mommy da ragowar masu aiki mata duk da akwatuna… Tun tana iya irga su har ta hak’ura ta tsaya kawai a tsaye bayan ta mik’e ta gaidasu cikin girmamawa. Sai da aka jere akwatunan tukunna suka yi mata sai da safe suka juya suka fita suka barta nan a daskare. Ta fi minti uku kafin ta samu ta k’arasa bakin gadon ta zauna still idanunta a kan akwatunan. Da sallama ya turo k’ofar ya shigo! Da leda a hannunshi. Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ja hular alkyabbar ta rufe fuskartata. Murmushi yayi kafin ya k’araso inda take nan bakin gadon ya zauna ya kamo hannunta cikin nashi ya rik’e ya d’an murza kafin ya ce “Sai na yi siyan fuska shima?” Dariya Hausar tashi ta bata dan haka ta d’an saki murmushi wanda har sai da ya jiyo sautin shi. A hankali ya ajjiye ledojin dake nan rik’e a hannunshi kafin ya sauk’o gabanta yad’an durk’usa tukunna ya sa hannu ya janye hular alkyabbar. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Ma sha Allah” Sai kuma ya sake cewa “Kukan me kika yi?” A hankali ta girgiza kanta alamun ‘ba komai’ Tana jin bugun zuciyarta yana kara tsananta!. Cikin son ya tashi a gaban ta ta ce “Akwatunan menenen wannan?” Murmushi yayi yad’an sunkuyar da kanshi k’asa ya ciji lips d’inshi kafin ya d’ago da kanshi yana kallonta tukun ya fara magana “Ai dama sai da na cewa Mommy ta yafe min a barni ba sai na yi ba amman ta saka ni kashe uban miliyoyi akan lefe! Yau kusan wata biyu kenan tana ta tatsemin aljihu. Ga shi ke kanki bama ki so ba ko? Mu mayar mu karb’o kud’in mu?” Sai yanzu ta d’ago ta kalleshi “Ma sha Allah” ta fad’a a ranta.. Tunda ya shigo dama ta lura da fararen kaya ne a jikinshi kaftan, sai yanzu taga ashe har hular kansa itama fara ce tas! A ranta ta ce “Manyan kaya sun fi yi maka kyau” Cikin katseta ta ji ya ce “Kwalliya ya biya kud’in sabulu kenan! Tunda gashi har an saki baki ana kallona” Ya fad’a yana murmushi gefen baki da d’age mata gira. Da sauri ta d’auke idonta da kyar. Cikin son kawar da zance ta ce “Ya Aslam wasa wasa fa kanada rowa, tun ba yau ba na fuskanci haka” Dariya sosai yayi kafin ya ce “Ai kin fini rowa! Tunda gashi ana ta yi mini rowar zuciya.” Ya fad’i maganar yana k’ok’arin yin zaman dirshen akan kafet d’in gaban gadon ( a gabanta) Yana zama, bata san lokacin da ta yi sauri itama ta sauk’o ta zauna a gabansa ba har guiwowinsu suna gogar juna. Sai kuma ta fara k’ok’arin janyewa… Hannuwanshi ya saka ya rik’e cinyar tata ta yadda ba zata iya motsawa ba! Yana jin wani yanayi na daban ya na shigar shi… A hankali yana d’an murmushi ya ce “I love this respect da kike min Hudatie, Thank you.” Sunkuyar da kanta ta yi kawai ta kasa cewa komai. A hankali yana kallonta ya ce “Baki ce komai ba. Akan maganar mu da muka fara a d’akin Gramma”. Da sauri ta ce “Ya Aslam dan Allah ka daina bana son maganar. Kuma ni dai ka d’auke hannunka.” Gefe ya kalla yayi wani murmushin gefen baki.. Bata gama fahimtar murmushi da jinjina kan me yake yi ba ta ga ya mik’e tana shirin yin magana ya sunkuya ya d’auketa! Sai da ya k’arasa wajen sofa tukunna ya zauna ya d’aura ta a kan cinyarshi kafin ya ce “Bud’e idon sannan ki ja numfashi Matsoraciya kawai… In kika sake yi min musu ko kika ce kar In tab’aki Allah sai na nuna miki matsayina a wajenki.” A hankali ta bud’e idonta tana kallon k’asa.. Hankalinta In yayi dubu tou ya tashi! Tanajin yadda jikinsa yake d’an rawa kad’an kad’an ga zuciyarshi tana iya feeling bugunta! A hankali ta ji ya ce “Unhm ina jinki. Say something anything… i told you how I feel. Let’s

Chapter 17 of 26