Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rik’e amana da alk’awari Allah yasa ka gama da duniya lafiya. Idan mun gana magana za ka ji sak’on mu daga wajen Aaima in sha Allah.” Cikin girmamawa ya yi musu godiya daga nan suka yi sallama ya wuce......... Bayan sati d’aya Aaima ta ce masa “su Daddy sun ce yana iya turowa anytime idan sun shirya” Tsakanin Aaima da Junaidu ba zaka iya tantance wanda yafi wani farin ciki ba. Su Kaka da Ya Jamilu ne suka zo suka nemawa Junaidu auren Aaima. A parlourn Daddy aka tarbesu tarba ta mutunci! Cikin mutunta juna suka yad’a manufarsu suka nema aka basu. Wata biyar ciff! Aka saka ranar auren daga nan suka bayar da goronsu da alawa da kud’i nera miliyan d’aya! Aka watse cikin farin ciki barkwanci mutunta juna da nishad’i. …………….. Sai da Sakina ta fara kukan gida tukunna Auwal ya yarda suka dawo a lokacin watansu biyar a k’asashen waje. Ya so ta tsaya su biya Paris dan nan ne kad’ai basu je ba a cikin k’asashen da ake yawan zuwa a d’an shak’ata (Har Hajji da Umaara sun yi) Amman ganin yadda ta d’aga hankalinta sannan ga yanayin condition d’inta yasa kawai ya hak’ura suka dawo. Direct gidansu, Daddy ya ce su wuce dan ta samu ta d’an huta. Tabbas Daddy ya san in ba da kyar ba to kuwa za a yi irinta Granpa da Aslam A shi da d’an cikin jikin Sakina saboda yanda yake jin son jika ko jikar tashi tun kafin su zo duniya a ransa Allah kad’ai ya sani. Ita Sakina har mamaki da kunya ma take yi, haka nan fa takanas! Zai kirata ya yi ta jero mata adduo i ita da babyn sannan ya yi ta turo mata important things akan condition d’inta abunda ya kamata ta ci da wanda bai kamata ta ci ba saboda lafiyarta da babyn… Wasu lokutan ita kam har kukan farin ciki take yi dan gata da soyayyar da Auwal yake nuna mata bata jin she could ever ask for more. Tunda ta lura yana d’an wasa da sallah ta kafa ta tsare sannan ta nuna mishi b’acin ranta! Yanzu sam Auwal ya manta rabon da ya bari lokacin sallah ya wuceshi. Zaman lafiya da k’aunar juna shine definition d’in rayuwar su ga families d’inshi suma hatta Granpa da Mom kiranta suke yi su ji ya lafiyarta da babyn dan Auwal a ranar da ya sani washegari ya kasa rufewa farin ciki yasa sai da ya fad’awa su Mom da Gramma har su Abba tukunna hankalin shi ya kwanta, sai da ya gama sanarwa kuma sai ya d’anji kunya. Idan ka gansu tsaf da su sun yi k’iba sun yi fresh in banda glowing ba abunda suke yi! Gashi sun yi mugun dacewa da juna, kamar ka sace su ka gudu. Gidan da Arshaad ya siya zasu zauna da Huda nan ya mallakawa Auwal, hatta lefe da kayan d’akin suma su Daddy duk suka bashi. Sakina taso biyawa ta ga Huda amman jin yadda Daddy ya damu akan ta huta wai ‘ta hawo jirgi ta yi jigila jigila’ yasa kawai ta hak’ura suka wuce gidan ba dan ranta yaso ba. A hakan ma kuma Daddyn ya ce “zuwa gobe su je asibiti a tabbatar da komai dai lafiya” A chan suka tarar da Gwaggo Asabe tana gyaggyara musu gidan ita da wata mai aiki har girki sai da tayi musu. Suna gama oyoyo d’insu ta sulale ta fice ko sallama bata yi musu ba dan karma su rik’eta saboda ita tun kwanakin baya da Mommy ta tilastamata zama a wajen su Hudan ko kwana d’aya bata iya yi ba ta gudu ta koma gidan Mommy a ranta kuwa ta raya ‘ta gama zama gidan sabbin Amaren nan gaskiya’.......... Aslam, yana tuk’i yana d’an satar kallonta. Ganin tak’i ta yi shiru yasa ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi parking a d’an gefen titi kad’an ya kashe motar ya juyo ya kamo hannunta. Kamr za fashe da kuka ya ce “Hudatie, kukan nan ya isa haka dan Allah. Saboda ke fa na je wai dan ki d’an samu ki shiga mutane amman ni kam na jima ma rabona da shi. Da ace na san kuka za ki d’ebo Allah da ba za mu je ba gaskiya. Ki share hawayenki… Come here.” Ya fad’a hakan yana mai janyota izuwa jikinshi. Da kyar ya samu ta d’an yi shiru kafin ya ce “Ya Aslam matar nan ta bani tausayi..wallahi ba ita ta d’auka ba! Sannan Yaron ina ganin lokacin da Maman shi ta bawa wannnan maid d’in shi a wani lungu wajen ba kowa time d’in ni kuma na fita yin waya da Sakina ne.” Da sauri Aslam ya ce “are you sure?” Cikin tabbatarwa ta d’aga mishi kai alamun ‘eh’. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Tun farko daman maganar sark’ar nan na fahimci makircin mata ne. Wannan maganar Babyn kuma da kika fad’a min yanzu ya sake tabbatar min. Zan je in samu Yash d’in In fad’a masa sannan In tsaya har sai naga an fitar da ita tun kafin a shiga kotu ma. Amman wacce iriyar dak’ik’iyar uwa ce zata yiwa d’an da ta haifa a cikinta haka?” Cikin share hawayenta ta koma gefe ta zauna ta ce “Nima dai abunda na ce kenan, amman wallah yadda naga ta bawa wannan maid d’in Yaron Allah yasa In ga Annabi. Sannan jakar MANNUBIYAn a hannuna take! Ta bani bayan ta d’auki abu a ciki ta ce ‘in rik’e mata bara ta je ta yi chanjin ta dawo’ A gabana ta bud’e ta d’auka abun da zata d’auka, ba komai a cikin jakar sai y’ar k’aramar fasashshiyar wayarta da abunda ta d’auka sai d’ari biyu wallahi. Tana dawowa ko tab’a jakar bata yi ba na ajjiye mata akan cinyarta. Kuma ko da ta dawo d’in babu komai a hannunta haka nan ta nemi waje ta zauna da jakar a gefenta. Tana zama wayarta ta d’au ringin ta bud’e ta d’auka…. Tana gama wayar muka ci gaba da hira take ce min ‘Babanta ne Za’a yi sadakar arbain d’in Mahaifiyarta jibi.’ Daman tun zama na na fahimci tana cikin damuwa, tun farko ita kad’ai a gefe na hango shiyasanya ma na je na zauna kusa da ita Ashe dalilin kenan.......” Cikin jinjina kai Aslam ya ce “shikenan, zan je In samu Yash d’in. I wonder why ya yi believing da sauri haka har ta kai shi ga yi mata wannan wulak’ancin! Yanada zurfin tunani ban san me ya shiga kanshi ba… Anyways zan je in sameshi. Yanzu ki daina kuka share hawayenki kin ji honey…” Cikin share hawaye Hudan ta ce “Ta bani tausayi ne sosai wallah, har da kukanta dama tana bani labarin Mahaifiyarta sai kuma kawai muka ji sanarwa. Ni a ganina lokacin da wajen ya hargitsene aka saka mata sark’ar a cikin jaka saboda tabbas a k’asa muka hango jakar a jefe tana d’auka kuma aka k’araso kanta.” “Hmmm, makircin mata ne kawai.” Cewar Aslam yana mai kunna motar. A hankali Hudan ta ce “D’an Indiya ne? Friend d’in naka, na ji sunansa ‘Yash’.” Murmushi Aslam ya yi kafin ya ce “sunanshi Yashjub, Itama MANNUBIYAn baki ji Manu ake ce mata ba.” Cikin son faranta mata rai da kawar da zancen ya ce “Good news sannan surprise…. Bara dai mu je In munje za ki gani......” Tunda suka shiga gidan suka zauna Aslam ya yi waya ya ce “suna parlour” ta kasa nutsuwa, in banda gyara zama da kalle kalle ba abunda take yi. Ta so ta gane wasu items a cikin gidan kamar waenda suka zab’a ne ita da Sakina lokacin bikinta da Arshaad. Da sauri ta kalli Aslam ta ce “Laaa Ya Aslam Sakina ce ta dawo ko?” Dai dai nan suka k’arasa sauk’owa ita da Auwal. Jikinta ne kawai ya bata tana bayanta ga kuma Aslam yana kallon wajen yana murmushi. Da sauri ta juya sai kuma ta mik’e da gudu ta zagaye kujerar ta tafi zata fad’a jikin Sakinar. Da sauri Auwal ya shiga gaban Sakina tsakaninsu ya tsaya ya ce “a,a,a,a careful!!” Yana d’an zaro ido da d’aga gira da d’an murmushi akan fuskarshi. Da sauri Huda ta ce “Au sorry na manta, Daddy ya Auwal” tana d’an dariya. Dariyar shima ya yi yad’an matsa ai kuwa da sauri Sakina ta rungumeta ta na share hawayen murnar ganin y’ar uwartata. Cikin farin ciki da k’aunar juna suka hau gaggaisawa da tambayar bayan rabuwa. Sun jima suna hira kafin Sakina ta ja Huda suka yi sama. Auwal kuma ya kira Arshaad suka hau video call su uku! Ba k’aramin dad’i suka ji ba da ganin yadda Arshaad d’in ya sake sakewa ya ware sosai kamar komai bai tab’a faruwa ba….. Suna hawa saman Huda ta fara tab’a cikin Sakina tana murna har da kwallarta… Nan suka zauna Huda ta fara zab’an sunayen da zxata sakawa Babyn In sakina ta haihu. Ganin da tayi kamar Sakinar is moody ne yasa ta shiga tambayarta da damuwa akan fuskarta. A hankali Sakina ta ce “Ni inata mita mu ba a cikin estate za mu zauna kusa da ku ba, ashe ba ma a garin zamu zauna ba gaba d’aya.” Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin ta ce “Ai kin san Ya Auwal shi ke da MT d’in Abuja, dole kinga a chan za ki zauna kusa da shi mana Sakina. Za mu dinga zuwa ai ku ma kuma na san za ki dinga zuwa sannan na san maybe ma ya dawo dashi Kano gaba d’aya ko?” A hankali Sakina ta ce “Ai cewa yayi wai a chan Cairo zan yi karatu kuma de! Ni duk kaina a d’aure yake ban ma san wajen zama d’aya tak’ameme ba, ya ce min dai wai zan ji dad’in karatun sosai.” Dariya Huda ta yi kafin ta ce “ashe ya yarda kenan.. Ya Aslam ne ya sama mana karatun mu biyu ni da ke, da yayi mishi maganar da farko sai kamar bai yarda ba ya ce ‘shi yana Abuja family suna Kano ke d’in idan kika yi masa nesa aganinshi abun zai d’anyi wuya’ Shiyasa Ya Aslam ma ya ce min kar In gaya miki yet ki d’aga mishi hankali tunda bai riga ya amince ba. Kinga yanzu kuma ashe ya amince…” Da sauri Sakina ta rungume Huda ta ce “Na ji dad’i da za mu yi karatu tare”. …. Sai da dare ya yi sosai tukunna su Huda suka kama hanyar estate. Aslam sarai ya lura da Huda, yadda duk jikinta ya yi sanyi kuma tabbas ya san damuwarta.. A hankali ya ce “Hudatie kowa fa da lokacinshi, sannan ai lokacima bai wani ja ba, Manu fa matar Yash Indai zan iya tuna lokacin da ya turo min iv d’in bikinsa tou ina jin yanzu shekararta uku da aure! Amman har yanzu bata haihu ba kuma kinga kishiyarta ita har ta haihu Ita kuma tace me? Ga Mommy itama sai da ta yi shekara kusan...” Kukan da ta fashe masa da shi ne ya sanya shi sauk’e ajiyar zuciya yad’an kamo hannunta ya ce “Gaskiya Hudatie zan fara miki bulala! Gaba d’aya kin zama shagwab’abb’iya, abu kad’an kuka?” Cikin kukan ta ce “tou Ya Aslam bakaga ita Manu d’in an yi mata kishiya ba?” “Da sauri Aslam ya ce “Woow!! Good idea Huda, kai! Amma Allah ya yi miki albarka, kin kawo shawara kinga nima sai in k’ara auren kenan! Bara muga..daman ina son k’asar Egypt dan haka y’ar egypt zan fara aurowa sai in auri y’ar indiya sai in je garin Taraba In auro saboda Mommy sai kuma In tafi Chad in auro saboda inyiwa Dad shima kara.” Cikin k’ara sautin kuka Huda ta ce “Ya Aslam ka fa lissafa hud’u kenan, ni kuma a ina za ka saka ni?” Tana tambayar tana sake fashewa da kuka. Cikin dariya k’asa k’asa ya ce “Au haba?? Ok tou bara in cire y’ar indiya tunda kema ai kinada gashi sosai Irin nasu” This time around duka ta fara kai masa…… Cikin tsananin dariya da nishad’in da yake ciki ya ce “Haba mana Hudatie Ubangijine fa ya ce mu yi biyu uku har hud’u indai za mu yi adalci.” Ya fad’i haka yana Parker motar a harabar gidansu dan har sun iso. A hankali ya kamo Hannunta cikin kulawa ya ce “Kinga ni kuwa ba zan iya yin adalci tsakaninki da ko wacce mace ba shiyasa na zab’i in zauna da guda d’aya! Dan nasan muddin na k’ara aure to zan kasance cikin mazan da suke tashi da shanyeyyen b’arin jiki ranar gobe k’iyama.” Kamar wata wawuya sai kuma ta fara murmushi kad’an kad’an tana kuka. A hankali ta kwanta a jikinshi yasa hannu ya yi hugging d’inta. Dariya ya yi kafin ya ce “Irin wannan zafin kishi haka? How much do you love me??” Ya yi mata tambayar yana murza tafin hannunta. A hankali ya ji ta ce “Stars da ruwa kansu inda ace za a iya kirga su tou baza su kai adadin yadda nake k’aunarka ba Ya Aslam.. I love you so much!!! Till eternity I’ll always love you...................” ..BAYAN SHEKARU GOMA!.. Abubuwa da dama sun faru.. An samu cigaba k’ari d’aukaka da farin ciki sannan an samu rashi na rasuwar Gramma Kaka da K’asimu. Shekara biyu Mom ta yi a wajen Innaa, da kyar da fad’a da lallashi da shawarwari aka samu Daddy ya amince ta komo amman fa ya k’ara aure! Dan tana tafiya ko shekara ba a yi ba ya auri wata k’anwar Abokinsa y’ar gayuu Budurwa amman zata kai 35 years Ana kiranta da ‘Kaulat’. Tabbas sai da Mom ta yi da gaske tukunna ta yi kokawa da zuciyarta dan Kaulat ta fita ta ko wacce hanya Kyau! Ilimi! Aji! Kud’i! Gata!! Sannan sai take gani kamar ma Daddyn ya fi son Kaulat d’in a kanta. Amman kuma da ta yi hak’uri bata yi komai ba sai abun ya zo mata da sauk’i dan Kaulat sam babu ruwan ta a waye take sosai kowa nata ne shiyasa ana aurota ma ta siye zuciyar kowa a cikin estate d’in. Mammy kuwa hukuncin life inprisonment aka yanke mata na kisan Ummi dan k’iri k’iri Mommy ta kafa ta tsare tak’i yarda a yi shari’ar case d’inta da Mammy. Mammy ta yi nadama a gaske a prison… Sukan je su ganta dan ba a chanjawa tuwo suna she’s still part of the family. Banda sauk’a da haddar Alqurani, nafila da neman yafiyar Ubangiji ba abunda ta saka a gaba..... Yanayin karatun su Huda wanda Aslam ya tsara akan za su yi a Cairo hakan bai faru ba saboda Mama da Daddy cewa suka yi ‘Huda ta yi BUK tunda a kano Aslam yake Sakina kuma ta yi gwagwalada.’ Mazajen nasu sam! Basu so hakan ba amman ba yadda suka iya haka nan suka amince domin sun san duk abunda babba ya hango Yaro ba zai iya hangowa ba. Cikin sa a suka fara karatun nasu Allah ya taimake su ba a samu strike da delay ba ko sau d’aya har suka kammala karatunsu da first class ba tare da sun samu delay ko tangarda ba. Hudan ta zab’i fannin Paediatric Sakina kuma Gynecologists. Suna kammala karatunsu suka tafi course na k’aro Ilimin sani a fannukansu na shekara bibbuyu a UK. A lokacin both Aslam da Auwal kowa ya bud’e sabbin company d’insa a chan uk d’in dan haka kusan tare suka tafi da mazajensu da ‘ya’yan su har suka kammala! Sai a wannan lokacin ne kuma Arshaad ya yanke shawarar dawowa gida tare da Amaryarsa mai suna ‘Jahad’ y’ar k’asar Saudi Arabiya wadda ya aura last year! Kaff familyn MT babu wanda bai je bikin Arshaad ba har su Ummu, tun a lokacin suka so ya koma gida yak’i yanzu kuma shi da kanshi ya yanke shawarar komawa gida dan he’s pretty sure baya yiwa Huda zazzafar soyayyar da yake yi mata a baya. A ranar da suka dawo Huda da Sakina suka tarar da babbar kyauta daga Granpa wanda ya bud’e musu tangamemen asibiti mai hawa wajen biyar! Ya basu ya ce “su zab’i suna su saka” Da farko sunan Madu suka so su saka amman sai Mama da Ummu suka basu shawarar su saka ‘Mai Turare’ A ranar Granpa ya had’a walimar welcoming Arshaad da Amaryarsa Bud’ewar Asibitin su Huda da kuma saka ranar Sumayya da Shuraim wadda Sumayya ta amince da auren da kyar! Bawai don bata son Shuraim ba sai dan ita a ganinta bai kamata ta auri age mate d’in ta ba...... ......Yau da kanta take so ta je ta d’auko Yaran saboda tana son zuwa wajen Jalila da su, duk da cikin wajen wata bakwai d’in dake a jikinta hakan bai hanata driving da kanta ba. Tunda wuri dama ta kira driver ta ce masa ‘kar ya je, da kanta zata je ta kwaso su’. Tana zuwa tun a bakin gate mai gadin da ya bud’e mata ya ce “ta je da wurwuri office d’in principal yana ta fad’a! Tun d’azu ake kiran layin office d’insu ita da Maman Arshaad amma duk su biyun basa d’auka.” Da sauri ta k’arasa office d’in, tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya ta girgiza kanta a ranta ta ce “Dama na sani” Tana k’arasawa ta kamo kunnen Arshaad ta jaaa da k’arfi ta d’aga shi ya mik’e cikin fushi ta ce “yau ma ko? Wai mai yasa baka jin magana ne?” Da sauri principal d’in ya ce “Mrs Aslam This boy must leave this school gaskiya! We can’t tolerate him anymore!! Wallahi saboda share d’in Dad d’insa a makarantar nan ne yasa muka barshi amman yanzu kam mun gama yanke shawarar sallamarshi. Zamu fitar wa da Dad d’in nasa share d’insa idan yak’i amincewa.” Hudan na shirin fara lallab’asa principal d’in ya katseta ta hanyar cewa “Mun rigafa mun gama magana! Saboda Allah ko malamai bama bari su daki Yaro saboda iyaye basa so amman bamu huta da case ba kullum duk akan Arshaad. Fad’a da zuciyar shi yayi yawa gaskiya.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e sannan ta cikawa Arshaad wanda yake ta faman kumbure kumbure kunne ta mik’awa Anum key d’in motar ta ce “Na san ya girmeku amman kun fishi hankali! Gashi ke da A’ish Ku ja Yaran ku je ku jirani a mota gani nan zuwa.” Har suka fice yana nan a tsaye bai motsa ba dan haka ta daka mishi tsawa ta ce “Bisu kaima ka je ka jirani! Saura kuma idan na fito in ji sabon labari”. Yana fita ta nemi guri ta zauna.. Da kyar da sid’in goshi ta lallab’a principal d’in, dan zuciyarshi ta zo wuya game da lamarin Muhammad Arshaad.... Wani abun mamakin tana fita ta tarar da wani sabon damben! Ko ba a fad’a mata ba ta san waye.. Tun kafin ta k’arasa ta hangoshi akan ruwan cikin wani almajiri yanata kimarshi d’ayan almajirin kuma yana kanshi yana dukan shi amman ko a jikin sa. Da kyar da taimakon wasu samari aka janyeshi daga kan almajirin da ya danne dan shi d’ayan almajirin yana hangota ya matsa gefe. Sosai kuwa ya yiwa almajirin jina jina dan dama a fusace ya ke su kuma suka tab’osa. Sai da ta d’an duddubashi ta ga ba wata matsala tukunna ta basu kud’i ta had’asu da samarin da suka raba damben ta ce ‘su taimaka su kaisu chemist tana da Yara k’ananu a mota’ daga nan ta basu hak’uri ta ce “su bisu su tafi chemist aje ayi masa dressing.” Daga nan Arshaad ya shiga motar ta ja suka wuce daman su Anum ana fara fad’an suka tura su Abbakar suka hana su fita suka rufe motar ba wanda ya fito a cikin su balle a had’a da shi. Gidan Jalilan da bata je ba kenan, haka ta kama hanyar estate da su tana mamakin Arshaad, chan wani murmushi ya sub’uce mata a hankali ta girgiza kanta a ranta ta ce “Sai dai ba d’an Sakina da Auwal ba”. K’ala! Ba ta ce mishi ba. Driving d’inta kawai take yi dan a mugun takure take jinta. Tun da Yaron ya ga an zo gidansu ta lura da yadda yad’an tsorata, aikuwa tana gama parking a compound jikinshi ya fara karkarwa ya ce “Ummi dan Allah kar ki gayawa Ammi komai.” Ko kallonshi Huda bata yi ba ta ce “Ai naga ni ka rainani! Jiyan nan ka gama yi min alk’awari amman fad’a har biyu yau kad’ai? Haba Arshaad!” Shiruu ta yi kamar mai tunanin wani abu kafin ta ce “Ka san wani abu?” Bata jira ya Bata amsa ba ta ce “Na ma daina kiran ka da ‘Arshaad’ daga yau dan baka yi halin mai sunan ka ba wallahi, dan haka chanja maka suna zan yi In maidaka mai sunan me gadi! za ka sha mamaki.” Takaici da zafin zuciya dan har yanzu fushi yake da waenda sukai fad’a yau bai gama hucewa ba yasa ya fashe da kuka. Dai dai nan Auwal Aslam da Arshaad suka shigo compound d’in suna hira suna raha da dariya… Arshaad, yad’an yi k’iba kad’an Auwal kuma ya tara k’asumba da gemu kamu d’aya Aslam kam ba abunda ya k’ara ba abunda ya rage. Tun kafin su k’araso Yaron ya tafi wajen Arshaad da gudu ya fad’a jikinshi ya ce “Uncle kaga wai Ummi za ta maidani mai sunan me gadi!” Sai da sukayi dariya k’asa k’asa tukunna Arshaad d’in ya d’an b’ata rai ya d’auke shi ya ce “Eh to… Ni na bata shawara saboda naga ka cika fad’a sosai.” Ai kuwa nan ya rikice da kuka. Dariya kawai Aslam da Auwal suka yi sukai gaba suka barsu. Sai da Aslam ya k’arasa wajen Huda ya d’an shafa fuskarta da tirtsetsen cikin ta tukun ya ce “Baki je wajen Jalilan ba kenan” Sai da tad’an kalli Arshaad da takwaranshi tukunna ta ce Abhu, Gaskiya ya kamata yau a saka Yaron nan a gaba a yi mishi fad’a sosai wallahi, saboda shi na dawo, dambe har da almajirai a waje sabida Allah.” A hankali Auwal wanda ya d’auka mai sunan Dad ya ce “Mu je ciki yau inga har duka sai ya sha” Ya fad’i hakan yana mai wucewa ciki. Dariya Aslam ya yi ya ce “Kiga yadda yake wani had’e rai kamar ba a wajen shi ya gado ba” “Um um fa! Yarintar shi kad’ai ka gani baka san na mamansa ba” Hudan ta bashi amsa. Murmushi duk suka yi Huda ta wuce shi kuma ya juya wajen su A’ish waenda suka gama kwasar lunch box da jakankunan su. Murmushi ya yi ya d’aga A’ish sama ya ce “Mamana ya school ke ba kya fad’a ai ko?” Sai kuma da sauri ya sauk’eta ya d’auki Anum yana cewa “sorry kakata yi hak’uri na manta na yi alk’awarin yau ke zan fara kulawa.” Da d’an k’arfi Huda ta ce Kar ki yarda ya yi miki dad’in baki” Tana mai wucewa bayan ta kamo hannun Abbakar k’anin su Arshaad wanda yake a kindergarten suka shige ciki… Sakina taso ta yi mishi shegen duka bayan ta gama jin bayanin abunda ya yi yau dan ta zo wuya da halinshi amman sai Aslam ya jata gefe ya yi mata Nasiha.. Nutsatsen fad’a sosai suka taru suka yi mishi dan har Jihad Arshaad ya kira ta zo itama saboda Yaron yad’an shak’u da ita itama dan tun yana zuwa hutu wajen Arshaad a Uk suke video call da ita, lokacin da su Sakina suka tafi course d’insu kuma a gidansa ma ya zauna gaba d’aya ko da yayi aurenma tare suke har lokacin da suka dawo Nigeria tukun ya gudu gidan su Huda dan sam baya san zama waje d’aya da Ammi saboda ya san zai yi laifi itakuma zata dake shi ta yi fushi da shi duk da yanayin rigimarshi amman yana tsananin k’aunar iyayenshi shiyasa baya son yaga tana fushi da shi. Sannan baya son fad’a da duka. Haka nan suka had’u su shidda! Da turanci da Hausa da larabci duk aka yi mishi fad’an. Kuma da alamu fad’an ya shige shi sosai. Tun daga ranar an d’an samu ya nutsu amman ba a yi cikakken wata d’aya ba ya koma ruwa dan haka kawai suka bishi da addua..... Sai da bikin su Shuraim da Sumayya ya rage saura sati tukunna Aaima suka zo dan a Abuja itama take tun aurenta. Ya’yanta uku biyu maza Farouk da Bashir sai auta Aisha. Tun aurensu har kawo yanzu cikin kwanciyar hankali suke sai dai y’ar rigimar Mata da Miji wanda wannan normal ne a ko wanne aure. .... Sai da Ya Ja’afar ya yi shekara biyar tukunna aka samu ya dawo dai dai, idan ka ganshi yanzu ya nutsu sosai kamar ba shi ba. Yana fitowa Junaidu ya bashi jari aka nema mishi mata ya yi aure shima y’ar bazawarar da Baba ya aura y’ar garin Katsina dutsanma bafulatana. Umma har yau tana nan jiya i yau! A nan gidan Baba da Junaidu ya rushe ya sayi filin bayansu ya had’e ya yi musu ginin zamani take itama amman b’angarenta daban ita da masu aikin da Junaidu ya d’auko suke kula da ita. Wani lokacin Huda

Chapter 25 of 26