Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
best day of his life!. Sai da budurwar gefen nashi ta sake cewa “Lamido crescent” Cikin rangwad’a da kashe murya tukunna ya jiyo ta dan gaba d’aya hankalinshi yana kan Sakina. “Okay” Kawai yace yana mai karya kan motar dan har sun fara gocewa daga hanyar da za ta kaisu Lamido Crescent d’in. Da mamaki Sakina ta mik’e ta zauna da kyau tana kallon yadda ya juya akalar motar ya d’au hanyar Lamido Crescent. Bata gama shan mamaki ba sai da taji budurwa tana cewa “Ko za ka saka min digits d’inka! Sai mu dinga gaisawa” Murmushi mai had’e da dariya yayi yana mai kallon fuskar Sakina wadda tashi d’aya idanuwanta suka cicciko da hawaye kamar zata fashe da kuka! Har ga Allah yad’an ji tausayinta amma yana so yayi comfirming a yau d’innan sannan idan ma bata saniba to yana so yau ta san tana son shi. Dan haka ya juya yana kallon Yarinyar gefen nashi cikin wani kalar voice yace “Yes sure, kamar kin shiga zuciyata dan nima i was just about to ask for your number” Tana shirin yin magana suka ji Sakina tace “Um, idan ka sha kwana za mu sauk’a” Da saura Khadija ta juyo tace mata “Ke da wa??” Cikin fushi Sakina tace “Ni da ke! Idan kuma ba zaki sauk’a ba to ni zan sauka! Kina gani fa sai ya kaita tukunna zai dawo ya kaimu saboda ga gantalallu.” Ya so dannewa amman sai da dariya tayi nasarar sub’uce mishi, hakan kuwa ba k’aramin sake tunzura Sakina yayi ba dan haka a zuciye ta sa hannu zata bud’e k’ofar motar a hakan ta tana tafiya ba tare da ta jira an tsaya d’in ba. Shi kuma Auwal yayi maza ya danna lock! Murmushi Yarinyar gaban motar tayi kafin tace “Kaga dear mu je ka fara ajjiye su, in yaso sai ka dawo ka kaini daga baya” “Alright” Auwal d’in yace daga nan taga ya saka signal yana shirin juya kan motar, a cikin ranta sai kuma ta raya ‘Kuma fa idan ya sauk’e su tare daga shi sai ita zasu dawo a motar, a hanya su yi ta hira!’ Dan haka da sauri sai tace “Da yake ke gantalalliyarce ba? Kin gwammaci a kaimu sannan a dawo da ke?” Yarinyar taji zafin maganar ba kad’an ba amman gudun kar ta zubar da girmanta a gaban sabon saurayinta yasa taja bakinta tayi shiru ta kawar da kai!. Rai a d’an b’ace Auwal d’in ya juyo yace “Sakina saboda ku fa tazo bikin nan! Wanne irin attitude ne haka?” Cikin fushi da bala’i tace “Ban sani ba!” Tana mai kauda kai. Gani tayi ya juya kawai yana shirin d’aukar hanyar gandun albasa dan haka tace “Wallahi baku isa ba! Ka fara kaita ka ajjiye ta tukunna ka kaimu.” Shiru ne ya biyo baya a motar kafin Auwal ya juya ya nufi hanyar Lamido Cresent zuciyarshi fess… Ganin yadda suka bawa iska ajiyarta suka shiga hirarasu kamar irin sun shekara da sanin juna d’innan ne ya sake tunzura Sakina tun ba ma da Yarinyar tazo sauk’a ba Auwal d’in har da wani ce mata “yana isa gida zai kirata in sha Allah” Ita dai Sakina da kyar take iya jan numfashi, wani irin tuk’uk’i take ji zuciyarta tana yi mata, bata tab’a jin b’acin rai da haushin mutun irin na yau ba! Ji take kamar ta rufesu da duka daga shi har ita..... Da k’arfi taji gabanta yayi wani mummunan fad’uwa..tabbas abunda take ji kishi ne! Kishin Auwal take yi, kenan sonshi take yi? Innalillahi wa innailaihirrajiun How? Taya ta bari haka ta faru da ita? A take sai kuma ta fara jin haushin kanta…tayaya ma zata nuna ta ji haushi k’iri k’iri har haka Allah dai yasa shima Auwal d’in bai fahimci abunda ta fahimta ba…. Ba tare da yace wata ta dawo gaba ba Ya ja motarshi yayi gaba yana waving wannan Yarinyar da suka sauk’e.. Yana d’aukar hanya yayi deleting number d’in nata da ya karb’a sannan ya danna mata block! Sai da suka yi tafiya mai d’an nisa sannan ya d’an juyo kad’an ya kalli Khadija yace “Y’ar uwar, dan Allah ki zama alk’alin mu” Ya fad’i hakan yana maida hankalin shi akan driving d’in da yake yi. Murmushi Khadija tayi kafin tace “ok Ina jin ka” Sai da yad’an juya ya kalli Sakina yaga yanda ta kumbura kafin yayi dariya yace “2 months kenan yanzu, Ina bin Sakina da proposal amman tak’i accepting. Inaso ki gaya min me kika fahimta a attitude d’inta na yanzu a game da ni? Please.” Murmushi Khadija tayi zuciyarta d’aya, a abinda ta fahimta tace “Kishi!” Dai dai nan yayi parking a k’ofar gidan Madu. Da sauri ta bud’e ta fito! Shima shi da Khadija suka fito suna yi mata dariya. Ganin tana k’ok’arin wucewa ne yasa yayi saurin rik’o vail d’inta Khadija kuma tayi masa ‘sai da safe’ ta wuce Ya amsa yana dariya dan still dariyar bata gama sakinsa ba saboda ba k’aramin nishad’i yake ji ba…. Cikin tsananin farin ciki ya dawo ta gabanta ya tsaya yace “Okay, no more pretends, kawai ki yarda.....” Maganarsace ta mak’ale sakamokon had’a ido da suka yi, da sauri ya matso kusa da ita yana cewa “Subahanallah Sakina daga wasa? Yi hak’uri, goge hawayen dan Allah na daina” Ya fada yana shirin sa hannu ya share mata hawayen nata duk ya rud’e. Da sauri ta buge mishi hannun sai kuma wani sabon kukan ya taho mata wannan karon har da sauti! Cikin kukan tace “Cika mini mayafi” Da sauri ya cika yana “Sorry Sakina, wasa ne fa. Naji to ba kya kishina…” Wucewa kawai yaga tayi ba tare da ta waiwayeshi ba ta fad’a cikin gidan ta rufo k’ofar gate d’in da sauri.... A hanyar shiga parlourn taga Khadija tana jiranta su shiga tare amman kawai ta wuceta ta shige, ko kallon inda take bata sake yi ba. Bata yarda sun had’a ido da su Ummu da ragowar mutanen parlourn da suke zaune suna hira kamar rana ba! Haka nan ta wuce su da sauri bayan tace musu “Ina wuni” Bata damu da jiran amsar su ba, ta haye sama abunta. D’akin da suke kwana ita da Khadija da Hudan ta shiga, tana shiga ta ajjiye vail da jakarta ta fad’a toilet da sauri ta saka sakata Sai a lokacin ta samu damar sakin kukan da ya mak’ale mata….. Kuka take tun k’arfinta kamar ranta zai fita, tabbas son auwal take yi wanda ita kanta bata san ya akayi soyayarshi tayi mata mugun kamu har haka ba! Gashi bata tashi farga ba sai yau kuma babban abun takaicin shine shima ya fahimta, Infact ko waye ma yaga yadda ta dinga acting ai dole ya fahimta tunda gashi ita kanta ta dalilin hakan ne ma yasa ta gane tana k’aunarsa. Ba abunda yafi k’ular da ita irin yadda ta zubar da girmanta ta fito k’arara ba tare da ta sakaya ba, kuma wani abun mamakin shine har yanzu zuciyarta tak’i yin sanyi haushi da zafin budurwar nan k’awar su take ji..ji take yi kamar ta hau watsapp yanzunnan ta gaggaya mata magana.. “Damn it! Tabbas Ina son Auwal” Ta furta a fili tana mai fashewa da kuka. Ko Auwal ne kad’ai d’a Namiji a duniyar nan ta riga ta yiwa kanta alk’awarin ba zata tab’a auren sa ba! Tun ranar farko da ya furta mata yana sonta Infact ta san ma ba aurene ya kawoshi wajenta ba, idan ma aurenne ita kam ba zata tab’a iyawa ba! Tayaya zata yarda ta zama surukar Granpa da wannan Mom d’in tasa da suka b’oye Huda! Har gobe tana tuno wasu abubuwan da taji a bakin su Baaba Talatu waenda Granpa d’in ya yiwa Mama tun farkon auren su da Abba besides ita tun kafin ta kai haka take adduar Ubangiji ya tsareta daga auren womanizer! Auwal kuwa ta san yaci uwar womanizer ma tunda gashi har d’a Jalila take shirin ajjiye mishi…. Tana kuka ta yanke shawarar abunda zata yi, duk da kuwa ta san zata sha wahala amman its the right thing to do. Da kyar ta iya cire kayanta ta yi wanka, ta na fitowa ko goge jikinta bata yi ba ta d’au waya ta kira Ashraff…. Tun lokacin da suka fara dating yake cewa yana so ya turo bare ma da yaji zancen bikin Huda, ya so ace an had’a da nasu Ita tak’i yarda.. Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba tace masa “Anytime from now yana iya yiwa Mahaifinsa magana sai a fara maganar auren nasu” Ba k’aramin murna Ashraff yayi ba, tana jin yadda yake ta faman zumud’i da rawar kai a cikin wayar Ita dai sai murmushi kawai take yi, k’arshema kasa hak’ura yayi yace mata “Bara yaje ya duba idan Daddyn nasu bai kwantaba sai yayi mishi maganar yanzun” Da kyar da sid’in goshi ta lallab’ashi dan 12 ma ta kusa tace yayi hak’uri ya bari gobe ya sameshi da safe ayi maganar. Ba dan yaso ba ya hak’ura… Ya yi ta janta da hira, ganin kamar a gajiye take dan daga ‘um’ sai ‘um’um’ take iya amsashi da su ya sanya kawai yace mata “ta huta” dan shi tunaninshi bashi yayi gajiyar biki ce take d’awainiya da ita. Tana ajjiye wayar Khadija na shigowa, nan ta tusa ta gaba da zancen Auwal… “Ta soshi mana, yana da hankali daga gani, ga kyau, gashi zata zauna kusa da Huda… Waye waye” Ita dai Sakina k’arshe juya mata baya tayi, tayi mata banza kamar tayi bacci, ganin haka yasa Khadijah kashe fitila, abunku da mai k’aramin ciki tuni tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita! Sakina kuwa yadda taga rana haka taga dare Wani abun mamakin shine duk wani labari da plans da Ashraff ya gama gaya mata na bayan aurensu yanzun she can’t help it but to picture it ita da Auwal! K’ok’ari take yi ta danna k’iyayyar shi a cikin zuciyarta sai dai abunda bata saniba ta riga ta makara dan already zazzafar soyayyarshi ta riga ta rinjayi y’ar guntuwar k’iyayyar da take k’ok’arin dannawa zuciyarta ta k’arfi da yaji..... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 57 Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal. A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya ga su Sakina sun fito daga ciki. Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking…. A hankali kamar mai kuka yaji tace “Sakina shigo mana” Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo Ai ita a nan ma zata kwana yau’. A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e kafin ya murza handle d’in ya tura k’ofar ya shiga da sallama. Da sauri ta d’ago jin muryar Namiji!… Duk da su Sakina sun ja mata mayafinta kafin su fita amman tana iya hangoshi! Har yanzun shadda ce a jikinshi abunda bata tab’a ganiba kenan. Sai taga yayi mata mugun kyau! Tsayi kamala surar jikinshi ta cikakkaen lafiyayyen Namiji ta fito sosai… A take zuciyarta ta hau bugawa da sauri da sauri..... Takowa yake yi izuwa bakin gadon wanda hakan da yake yi ji take kamar a kan zuciyarta yake yin tafiyar.. Duk taku d’aya sai taji tamkar numfashinta zai d’auke ne! Hakan yasa ta fara ja da baya.. Yana matsowa ita kuma tana ja baya. Aslam shi bai ma lura da yadda take ja da bayan ba har sai da yaga sun kai edge d’in gado tana neman mik’ewa, dan shi har ga Allah ba abunda idanuwanshi suke gane mishi sai ita, ruhinta! shiyasa sam bai lura da movement d’inta ba… Yana isowa dab da ita, ya jaa ya tsaya a bakin gadon. Ita kuma sai k’ok’ari take ta mik’e amman k’afarsa da side drawer sun tokare ta gashi har ta kai jikin fuskar gadon so ba daman ci gaba da matsawa… A hankali taga yana d’an sukuyowa….ji take yi kamar ta bud’e murya ta kurma ihu! Ko kuma ta tashi ta yi tsalle ta fad’a tsakiyar gadon daga nan ta samu ta sauk’a ta d’ayan side d’in… Ita har ga Allah tun farkon had’uwar ta da shi, sam! Bata k’aunar zama a kusa da shi (Aslam) Saboda muddin suna tare no matter how she tries kwata kwata zuciyarta bata barin wannan mahaukacin gudun data rasa dalilinsa! Gashi bata san dalilin da ya sa yaketa matsowa kusa da ita ba.. Ita fa yanzu abunda ya kamace su shine su nutsu su yi tunanin ya za suyi da rayuwarsu da wannan auren da aka k’ulla musu shiyasa duk a rud’e sannan a rikice take kuma gashi yanzu ya zo ya sake rikitata…… Tana cikin wannan tunanin ta ji fuskarsa daff da tata! A hankali taji yasa hannu ya yaye lullub’in laffayar fuskarta.. Had’a idanu suka yi! Da k’arfi zuciyoyinmu suka buga a tare! Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya sak’ale kwayar idanuwanshi da tata sannan yace “Assalam alaiki, Maryama.” Da mugun k’arfi ta runtse idanuwanta sannan dai dai nan hawayen da bata san dalilinsu ba suka b’alle mata a take. A hankali ya hau yi mata kallon k’urilla…. Cikakkiyar minti d’aya ya d’auka yana kallon fuskarta kafin da kyar ya samu ya iya kokawa da zuciyarshi ya d’auke idanunsa yana mai lumshe su.. Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauk’e wadda itama bata san lokacin da ta sauk’e tata siririyar ajiyar zuciyar ba sakamokon numfashinsa mai d’umi da dad’in shak’a da ya ziyarci hancinta wanda har zuciyarta sai da ta amsa! Hakan ne kuma ya haifar mata da sauk’e ajiyar zuciyar da bata shirya wa ba… A hankali ta ji sauk’ar wani lallausar tafin hannu kamar na jarirai mai mugun taushi a kan kumatunta! A mugun zabure ta bud’e idanuwanta da suka k’ank’ance suka yi jaa ta zuba masa su.. Bai damu da kallon da take yi masa ba! Kallonta kawai yake yi yana goge mata hawayen nata… Idanuwansa da ya zuba mata ya kafeta da su ne ya sanya ta runtse nata idanuwan jikinta na wani mugun rawa!. Wata ajiyar zuciyar kawai ya sake sauk’ewa...yana gama goge hawayen ya mik’e da sauri dan ba k’aramin kokawa yake yi da zuciyarsa ba tun lokacin da ya shigo! Sai da ya lumshe ido na some seconds tukunna ya bud’e yace “Ki taso mu je kici abinci” Kafin ya rufe bakinsa tace “N na na k’oshi” Tana mai jan numfashi har yanzu jikinta bai daina rawa ba. Be ce mata komai ba, ya sa kai ya fice a d’akin. Minti kad’an ya dawo da ledojin da Auwal ya shigo da su.. Gefenta ya nema waje ya zauna a bakin gadon! A hankali ya bud’e ledojin ya d’aura akan stool kafin yace “Oya, gashi ki ci. Akwai wani abun da kike buk’ata?” Da sauri ta girgiza kai alamar ‘a’a’. A hankali ya mik’e yace “Sai da safe” Tun kafin ya rufe bakinshi tace “Allah ya kaimu” Don so take ya fita. Shima lura da hakan da yayi ne dama ya sanya kawai ya mik’e d’in. Ajiyar zuciya ya sauk’e kamar zai ce wani abun sai kuma kawai yace “Allah ya tashe mu lafiya” Yana mai juyawa ya fita daga d’akin gaba d’aya” Yana fita ta sauk’e wata wawiyar ajiyar zuciya… Har ta d’an zauna sai kuma ta mik’e da sauri ta isa bakin k’ofar ta murza key ta zare ta taho da shi ta ajjiye a kan side drawer tana ta tunani…. Ta dad’e bata sha mamaki irin na yau ba! Yadda yake yin abu kan sa tsaye sannan kamar bashi da wata damuwa abun yayi mugun d’aure mata kai! Dubafa yadda ya wani zauna a kusa da ita sannan har da wani share mata hawaye.. Ita tana tunanin sai ta yi kusan kwanaki ma bata ganshiba daga nan ya bata takarda yace taje ta auri Arshaad d’inta Amman kalli abunda yayi tun yau.. Ba abunda yafi d’aure mata kai irin siyan bakin da aka yi sai kace waenda suka yi auren soyayya… Harga Allah yunwa take ji sosai ma kuwa amman d’aurewar da kanta yayi ne ya sanya ta mayar da kajin cikin ledarsu ta had’a da ledar drinks d’in ta saka a d’an k’aramin fridge d’in data gani a d’akin. Da kyar ta lallab’a ta yaye laffayar jikin ta ta ninke, ta shiga toilet ta d’auro alwala tazo ta nemi waje ta zauna dan already sun yi sallolinsu Magrib da Isha ita da su Sakina. A ranta ta gama ayyanawa tabbas idan aka yi d’an kwana biyu taji Aslam bai yi mata wata magana ba to ita kam zata tareshi da zancen ya saketa! Idan ma Mahaifiyar Ya Arshaad ta hana aurensu to zata hak’ura ta rungumi k’addara tayi facing karatunta idan Allah ya fito mata da wani ta yi aurenta amman ita kam ba zata iya zama da wannan murd’ad’d’en mutumin da bashi da alk’ibla ba! Infact tayaya ma zata zauna da mutumin da kullum in dai suna tare sai taji zuciyarta tana barazanar fashewa haka kurum salon yaje ya fasa mata zuciya a banza ya yiwa Mama da Abba da su Sakina asara, Inaa ba zai yiu ba! Da wannan tunanin ta kwanta akan lallausan gadon tana mai lumshe ido… Nan kuma ta fad’a tunanin Arshaad! Tana yi tana istighfari amma sam ta kasa dainawa. Tabbas sai ka rasa abu kake gane yawan son da kake yi mishi! A lokacin da take tare da Arshaad bata san tana sonshi haka ba sai yanxu da ta san In ba da kyar ba to ta rasa shi kenan har abada! Dan muddin Mahaifiyarsa bata basu go ahead ba to ita kuma tayi alk’awarin ko sonshi zai kasheta ba zata tab’a aurensa ba tare da albarkar ta ba! Besides sai ma ta fara nemo mafita akan wannan auren! She has to do something fast saboda taga take taken Aslam kamar shi zai iya hak’ura ya zauna da ita don ya faranta ran su Abba Kuma ta tabbata idan hakan ta faru to haka za su k’are rayuwarsu ba soyayya tunda ita dai zuciya d’aya Allah ya bata kuma ta riga ta damk’awa Ya Arshaad shima kuma Aslam d’in ta tabbata bai ya k’aunarta sai dai ya kawai ya zauna da ita saboda ba yadda ya iya To Ina riba? Garama shi Namiji ne anytime idan ya had’u da wadda yake so zai aura Ita fa? An cuceta an cuci Ya Arshaad d’inta..how she wish she can see him now..tana so taga halin da yake a ciki, bawan Allah d’azu ba kalar zargin da batayi mishi ba ashe fin k’arfinsa aka yi…. Bata san lokacin da wani mugun kuka ya kufce mata da k’arfi ba.…… Tunani da kuka basu barta ta rintsaba sai around 2:00am tukunna bacci ya kwasheta wanda bata yishi cikin dad’in rai ba. Kafin asuba ta farka sakamokon mugun ciwon kan da ya rufar mata, da zazzafan zazzab’i ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai in banda rawar sanyi ba abunda take yi..... Tanaji ana kiran sallah k’ok’ari take yi ta samu ta tashi amma sam ta gagara.... A b’angaren Aslam shima bai samu yayi ishashshen bacci ba kusan kwana yayi yana nafila.. A nan kan daddumar ya samu bacci ya saceshi. Kiran sallar farko da aka maka a masallacin cikin estate d’in ne ya farkar da shi, dan haka ya mik’e ya shige bathroom… Sai da yayi wanka ya d’auro alwala sannan ya fito ya d’an kimtsa ya zura jallabiya ya gabatar da fajr nafl, ya zauna karatu. Yana idarwa ana tada sallah dan haka a gurguje ya fice ya nufi mosque.. Ya so ya duba Huda amman gudun kar ya makara yasa ya fita da niyyar ana idarwa zai dawo ya duba ta. Azkar kawai yayi daga nan ya fito daga masallacin. A k’ofa suka had’u da Dad dan haka suka jera yana d’an yi mishi nasiha har suka iso gidan.. Jan hankalinshi yake sake yi akan ya rik’e amana dan Allah kar ya wulak’anta matar da suka zab’a masa, ya taushi zuciyarshi ya bata dukkan hakkin ta da kulawa wata rana zai k’aunaceta in sha Alla… Shi dai Aslam da ‘to’ ‘in sha Allah’ kawai yake ta binshi dan ya rasa dalilin da yasa zuciyarshi taketa faman azalzalarshi akan yaje ya dubata.. Sam ya kasa sukuni ballantana ya samu ya bawa Dad d’in hankalinshi.. Da kyar ya samu Dad ya barshi ya wuce side d’inshi, bayan yace mishi “ya tabbatar sun je sun samu Granpa”… ..saboda ta watsapp yaji yace mishi zai nemeshi tun jiya amman har yau shiru, kar aje ko fushi yayi shi kuma har ga Allah baya so ya je ya sameshi gudun rigimarshi yake kuma bai san a wanna mataki ya saka maganar auren Aslam d’in ba gara idan Aslam d’in yaje da kanshi maybe abun yazo da sauk’i… Da ‘to’ Aslam ya amsashi sannan suka yi sallama ya wuce side d’inshi yana dariya da mamakin Dad d’in k’iri k’iri ya hango tsoro a tartare da shi..wato sun yi abu amman kuma suna tsoro shine bara su tura shi.. Da wanna tunanin ya Isa bakin k’ofar d’akin da Huda take ciki ya d’anyi knocking sannan ya murza handle d’in da niyyar turawa amman k’ofar sai ta k’i motsi, a hankali yad’an sake yin knocking amman still yaji shiru… Yayi mata knocking yafi sau biyar amma yaji shiru dan haka ya d’an sassauta murya ya matsar da fuskarshi jikin k’ofar ya fara kiran sunanta… A take gabanshi ya yanke ya fad’i! Dan in dai kunnuwanshi sun ji mishi dede to kamar sheshshek’a da jan numfashi yake jiyowa yana tashi daga d’akin! Da mugun sauri ya koma d’akinsa ya d’auko spare key sannan yazo ya zura ya murza ya tura da sauri ya shiga A k’udundune ya hangota a kwance tana rawar sanyi Da sauri ya k’arasa ya d’agota ya zaunar sannan ya fara shafa goshinta wanda ya ji ya d’auki zafi ba na wasa ba. A firgice yake kallonta, gaba d’aya ta jik’e da gumi kamar an watsa mata ruwa, pillow ya jawo ya kwantar da ita sannan ya mik’e ya nufi toilet ya jik’o towel ya fito.. Hannuwanta da tafin k’afarta sai saman goshinta ya shiga shafawa towel d’in amman kamar k’ara mata zazzab’in ma yake yi dan haka kawai ya mik’e ya je d’akinsa ya d’au waya ya kira Doctor tukunna ya dawo ya ci gaba da goga mata… ji yake kamar yayi kuka gani yake yi duk laifinshine dan inda a d’aki d’aya suke da tun farkon zazzab’in nata zai yi noticing ya san abun yi….. A hankali ya ga tana bud’e idonta, da sauri ya matso yace “sannu ya jikin?” A hankali ta shiga motsa bakinta a lamun magana take son yi.. Hannunshi yasa a a gefen kumatunta yana kallonta kafin yace “me kikeso? Tell me. Yanzu Doctor zai zoo kin ji, sannu” ya k’arashe maganar a hankali yana kallon bakinta da take k’ok’arin yin magana.. Murmushi ya ga ta fara kafin yaji tace “Ya Arshaad! yaushe ka zo? Ina ka tafi ka bar ni?” Tana mai kallon cikin idanunsa. Da sauri sannan da mugun k’arfi Aslam ya runtse idanuwanshi..... Magana take yi amman ba ya fahimta, babu abunda yake iya ji sai ‘Ya Arshaad’ d’in da take ta ambata a duk k’arshe ko farkon maganarta!….. Ya so ya zauna ya cigaba da shafa mata jik’akk’en towel d’in a samu fever d’inta ya sauk’a amman sai ya kasa! A hankali ya mik’e tsaye daga kan gadon yana ganin dishi dishi…, Ji yayi kawai ta fashe da kuka sannan ta fara k’ok’arin ruk’o hannunshi, cikin kukan tace “Dan Allah kar ka tafi, mu zauna a cikin mafarkin nan da nake yi ni da kai har abada, kar ka tafi ka barni bana so in farka idan kuma zan farka to sai ka yi min alk’awarin zaka dawo gar....” Wucewa yayi da sauri ya fice a d’akin ya barta nan tana ta faman surutai.. Da kyar ya iya kai kanshi d’aki yana zuwa ya dafa bango da d’ayan hannunsa d’ayan kuma ya dafa goshinsa yana jin yadda zuciyarshi take harbawa da tafarfasa tamkar zata fashe! Sunayen Allah ya hau karantowa sannan ya fara k’ok’arin controlling kanshi… Tabbas ya san zafin zazzab’i ne ya sanya ta take hallucinating amman hakan bai hanashi jin kamar zai mutu ba! Da kyar ya samu ya zaro waya ya kira Mommy yace mata “ta zo Hudan bata da lafiya” Daga nan ya lallab’a ya koma bakin gado ya zauna ya jingina bayanshi a fuskar gadon ya lumshe idanuwanshi..... Kamar yadda su Umma suka tsara! Yau da sassafe k’arfe 7:00 na safe Anty Zainab ta biyo mata suka kama hanya… Tafiyar awa uku ce ta kaisu d’an k’aramin k’auyen da za su je wanda tsaf In ka tsaya zaka iya k’irga gidajen wajen kaff d’insu. Wani gida isolated a chan nesa suka nufa, a dai dai hanyar gidan akwai wata y’ar majalisar wasu matasa a k’asan wata k’atotuwar bishiyar mangoro dai dai suna zuwa za su wuce wani a cikinsu yace “Ga wasu b’atattun yau ma sun zo” Sarai sun ji

Chapter 3 of 26