Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata first class a sa’ar miji a duniya, ko kuma ma ta ce ita kam ta fi kowa sa’ar Miji a duniya…...Tsantsar zallar k’auna da kulawa had’e da tattali yake bata baya duba shekarunsu sam dan shi idan ya tashi gwada mata soyayya kamar wasu teenagers haka yake ganinsu shi da ita........ A b’angaren Mommy itama bata bawa Aaima reason d’in da zatayi missing Mammy ba, kulawa da shak’uwa ce a tsakaninsu ta musamman dan ita Mommy ce mata ta yi ta d’auketa a matsayin best friend d’inta......... ........ Kamar kullum yadda suka saba yau ma Sakina ta kirata suka shiga hirarsu gwanin ban sha’awa duk da kuwa Sakinar ba wani dad’i take ji ba saboda murar da take ta faman mata on and off! Ta rasa sukuni gaba d’aya sanyin garin ya isheta. Jin yanayinta da muryarta da kuma rashin lafiyar da take ta yi kwana biyu ya sanya Hudan ta ce “Maman baby je ki kwanta ki huta Allah ya sauwake.” Ta k’arashe maganar da d’an dariya k’asa k’asa sannan tana addu’ar Allah yasa harsashenta akan Sakinar ya zamo gaskiya ne. “Ok na gode sai da safe” Sakinan ta ce..Ba ta kashe wayar ba ta d’an yi shiruu kamar mai tunani sai kuma ta kwashe da dariya kafin ta ce “Ai ni sai yanzu ma na fahimceki! Tab! Inaaa ba wannan tukunna wallahi iyaka mura ce kawai take damu na.” Cikin rashin fahimta Huda ta ce “Ba kince an sallameku ba?” Dariya Sakina ta yi ta ce “to kuma daga an sallamemu sai me?” Bata jira amsar ta ba tana dariya ta ce “Eh, an sallamemu dan jikin nashi ya yi kyau amman muna lek’awa, kullum, check up”. Shiruuu, Huda ta yi kafin ta ce “Anya kuwa Sakina?” Sai da Sakina ta yi dariya sosai tukunna ta ce mata “Allah da gaske, babu komai ma fa tsakaninmu har yanzu sai dai hira kawai da tsantsar kulawa da soyayyyar da yake gwada min. Da sauri Hudan ta ce “Kai!” Cikin murmushi Sakina ta ce “Kin san Allah nima kaina ina mamakin shi, ba daban ina fahimtar yanayin sa ba tou da sai in iya cewa ma bashi da lafiya…Ban san dalilinsa ba kinga ni kuwa ai bazan ce gani ba! Besides ni nama fi son haka.” Ajiyar zuciya Hudan ta sauk’e kafin ta ce “Kuma bai chanja miki ba? As in ba ya wani fushi da ke” “Ko d’aya, wallahi kulawar ma da yake bani ni kaina banyi tunanin ta ba kawai dai maybe shi tsarinshine haka ko kuma dai wani abun besides ai bamu fa wani dad’e ba so it’s not an issue.” “Shikenan tou, ki gaidashi” Shine abunda Huda ta ce. Daga nan suka yi sallama suka kashe wayar. Murmushi kawai ta yi tana duba wayar, a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya ta shiga tunani ....Kullum tare suke kwana, a jikinsa take yin bacci, tana jin yanayin bugun zuciyarshi da yadda yanayinsa yake alamun lafiyarsa k’alau kuma a k’age yake amman in banda hug ba abunda ya tab’a shiga tsakaninsu…… Sam bata san ya shigo d’akin ba dan yaje siyo musu milkshake a chan k’asan hotel d’in da akeyi wani mai dad’i! Sai da ta ji ya kwanta a bayanta tukunna ta yunk’ura da sauri tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa “Sakina I love you fisabilillah Ba wai wani abu daban ba! Shiyasa kika ga ban yi yunk’urin komai ba saboda Ina so ne har sai kin fahimci hakan, kin yarda dani, kin saki jiki dani tukunna. Na san zan takura amman yadda nake jin ki a raina tsaf zan iya rayuwa dake a haka muddin baki gama fahimtar kalar k’aunar da nake yi miki ba……..” A hankali ta juyo sosai tana kallonshi suka yi facing juna a kwancen! Kasa cewa komai ta yi kawai sai ta sunkuyar da kanta k’asa kafin chaan! Ta ce “Ya Auwal na yarda da kai na yarda da chanjin da na gani a tattare da kai. Tunda har kaga na aureka tou yarda da k’auna ce ta kawo hakan. Sannan zan rayu da kai a ko wanne hali.…..” Yadda ta ga yana kallonta ne ya sanya ta yi saurin b’oye fuskarta a k’irjin shi dan tashi d’aya sai ta ji duk kunya ta lullub’eta. Murmushi ya yi yad’an shafa kanta, a hankali ya yi kissing kan nata yana mai shak’ar k’amshin da yake fitarwa kafin ya shiga binta da wani mayen kallo k’irjinsa yana bugawa da masifar gudu…. Sannu a hankali yanayinsa yana k’arasa sauyawa ya sa hannu ya janyota ya saka ta a jikinsa sosai!. Sai da numfashinta ya kusan d’aukewa sakamokon wasu sak’onnin da ya shiga aika mata waenda suka girmi hankali da wayonta. Da sauri cike da tsoro da fargaba muryarta na rawa ta ce “Dan Allah!!! Ni fa da nace haka bawai ina nufin yanzu ba.” Ko sauraronta Auwal bashi da niyyar yi, dan tun kafin a je ko’ina notikan kansa suka kwance hankali ya fara barin gangar jikinsa… Tabbas ya yarda kuma ya sake tabbatarwa ‘kamilalliyar mace daban ta ke! Sannan matar sunna sinadarinta na musamman ne’ Gashi kuma abun sai ya taru ya had’e masa da giyar zazzafan feelings da soyayyar da yake yi mata, shi yasa ya manta kowa ya manta komai hatta shi da karankansa ya manta kansa. A ranar Huda ta sha Allah ya isa dan ita ce ta kirata a waya har ta janyo mata wannan jalalar. Sam bata tab’a tunnanin zatayi rai ba dan Mr Auwal sai da ya yi mata dalla dalla…….. Tun daga ranar kuwa ta rasa nutsuwa da sukuni. Daga nan ma Las Vegas suka wuce Honeey moon… Auwal shi kad’ai yake k’ibarsa yana enjoyment d’inshi Ita kam in banda rama ba abunda take yi dan kwata kwata ba enjoying garin take yi ba dan ita gani take ma kamar su suke tunzurashi yin wasu abubuwan......... Da kyar Aaiima ta iya samun Abba ta yi masa maganar Junaidu dan zuwa wannan lokacin kam soyayya mai k’arfin gaske ta k’ullu a tsakaninsu. Abba ne ya samu su Dad ya yi musu bayani su kuma suka ce a tambayi su Mama indai har ba shi da wani mugun hali sai a shirya komai dan kasancewarsa d’a ga Usman hakan ba shi zai sanya su shiga tsakanin Aaima da farin cikin ta ba dan k’iri k’iri ta nuna shi take matuk’ar so!. Sannan su a ganinsu yanzu Aaiman abar tausayi ce duk da kuwa sun san idan suka ce rashin Mammy yana a cikin matsallolin Aaima ba su yiwa Mommy adalci ba duba da yadda take iyakar k’arshen k’ok’arinta wajen ganin Aaiman bata rasa komaiba amman kuma uwa dole daban take. Dan haka za su yi k’ok’ari wajen ganin sun taimaka farin ciki ya wanzu a rayuwarta na dindindin...... Tabbas Mama ta ji dad’in wannan had’in dan haka tashi d’aya ta faiyyacewa Abba halayen Junaidu wanda tun tasowarta dashi bata tab’a ganin shi da wani mummunan hali ba sai dai mai kyau sannan yanada zuciyar nema da amana ga sanin ya kamata….. Abba ma ya ji dad’in jin haka dan haka ya ce “bara ya je kawai ya samu su Dad ayi komai a gama. Kafin Aaiima ta tafi rubuta finals d’inta a saka rana, tana dawowa a d’aura aure in shaa Allah.” A hankali Mama ta ce “Amman fa Abba akwai wani abu guda d’aya! Kasan case d’in Junaidu na zaman jail wanda tunda ya je ya dawo ya kud’ance! Kud’i na ban mamaki…. Last week ma sai da aka sake gano Gidaje da kadarorinsa dan shi b’oyewa yake yi..a iyaka Kano fa Gidajensa masu matuk’ar kyau da tsada sun fi ashirin ga kadarori ga filaye wanda bamu san source of income d’inshi ba! Inda hali gaskiya a d’an yi mishi tambayoyi akan wannan lamari a bincika. Naji dai kwanaki su Abba Madu sun ce sun yi mishi tambaya amman banji sun ce ga amsar da ya bayar ba.” Jinjina kai Abba ya yi daga nan ya ce ‘zai nemi zama da Junaidun ko zuwa gobene in shaa Allah, su tattauna.” .....Har gida kuwa Junaidun ya zo ya sameshi bayan ya ce masa ‘ya zo yana son ganinsa’ Shi da Daddy ya tarar dan haka ya gaidasu cikin girmamawa suka amsa masa da kulawa. Ba tare da b’oye b’oye ba Abba ya ce “sun san bashi da wani mummunan hali amman kuma suna buk’atar sanin kwakkwaran source of income d’inshi” A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara basu labari.... “A lokacin da aka sallame ni daga prision………… Mun fito mun kama hanya, bamu kai ga zuwa inda za mu je ba cikina ya b’aci! Dan haka na nemi alfarmar su tsaya in d’an yi uzuri. Suna tsayawa na fita… Ina kutsa kai cikin d’ajin kamar an ce in juyo nan na ga wasu maza da mask su uku sun nufi motar. Duk sai da suka fito da y’an motar suka dubasu amman sam babu abunda suke nema wanda sai daga baya na gane waenda Arshaad ya tura ne kuma ni suke nema. Kamar na sani a lokacin sai na b’oye kaina. Bayan na b’oye kaina su kuma suka gama dube duben su suka tafi. Su kuma Abokanan tafiyar tawa inaga tsorata suka yi dan ina shirin fitowa naga duk sun shige motar suna shirin tafiya. Da sauri na yunk’ura zan tafi na ji an rik’e min k’afa! Sai da gabana ya fad’i da na juya dan ni sam ban lura akwai tsoho ma a wajen ba a durkushe sai da ya rik’o nin. Cikin kuka tsohon ya ce “bawan Allah ko baiwar Allah dan Allah taimakon musulunci zan mutu yunwa nake ji.” Da sauri na ce “Baba dan Allah Abokanan tafiya ta za su tafi ka cikani In wuce.” Cikin kuka tsohon ya ce “yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah” Haka nan inaji ina na gani na kama hannunshi ya mik’e su kuma Abokanayen tafiyar tawa suka wuce dan maybe sunga na dad’e su kuwa a tsorace suke. Na ji takaici sosai amman yadda tsohon nan yake karkawa da kuka yasa kawai na yanke shawarar In taimakeshi. Sai da muka fara tafiya na fahimci ashe makaho ne! Haka muka yi ta kutsawa dan hanyar ba jama’a sosai har muka iske wata mai k’osai da kunu na siya da d’an kud’in da aka bani in yi na mota na bashi ya ci ya sha. A hankali muna zaune a wajen ya ce “in bashi labarina” Haka kurum ban sanshi ba amman na tsinci kaina da fad’a mishi komai na rayuwata har kawo yanzu. A hankali ya ce “kuma kana ganin ba kai ake nema ba kuwa!?. Ka zo mu je Gidana ka d’an b’uya kafin kwana biyu sai ka wuce gudun kar ka je suna nan har yanzu ka fita a kamaka.” Tsoro ya sanya ni na amincewa wannan tsohon, dan a yadda naga mutanen nan babu kalar imani a tattare da su. Gidan nasa y’ar bukka ce sai band’aki wanda aka yishi da langa langa a gefe sai wani murhu da rijiya. Sam babu wani katanga ko wani abun da yake nuni da wajen keb’antacce ne. Y’ar bukkartashi muka shiga muka zauna anan yake ce mini “Matarsa ta rasu watan da ya mutu, Allah bai bashi d’a ba! Danginsa kuma duk sun guje shi saboda basa son d’awainiya.” Atake na ji tausayin bawan Allahn nan ya rufe ni, kuma a take muka saba shak’uwa ta shiga tsakaninmu….. Kwana na biyu a wajensa, na siya mishi abinci da d’an abun da ba a rasa ba duk a cikin kud’in da aka bani a lissafina idan na tashi ni sai In d’auki drop har gidan Abokina ya biya. Ban b’oyewa tsohon nan ba na ce masa “muma ba wasu masu arzik’i baneba, ba daban haka ba da na tafi da shi” dan na lura yana cikin kad’aici da buk’atar taimako “kuma akwai abubuwa da dama a kaina amman dai bara mugani in shaa Allah idan na koma gida na yi settling zan dawo in duba shi. Dan nima a yanzu Ina matuk’ar buk’atar kud’i.” Daga nan na nemo wata mata a gefe na rok’eta akan “dan Allah ta d’an dinga lek’ashi” Ita kam Matar mamakima ta dinga yi dan a cewarta “duk zaman ta a k’auyen ita bata san da shi ba”. Bayan Matar wuce ne muka yi sallama muna ji kamar kar mu rabu… A bakin bukkar tashi Ina fitowa na ci karo da wani mutum cikin suite! Da akwati a hannunshi, kamar yana cikin sauri, ya nuna min hotonshi da wannan tsohon kamar lokacin tun suna samari ya ce min “an ce yana nan! Da kyar da wuya ya samu location d’insa, dan Allah na san shi?” Ba tare da b’ata lokaci ba na ce masa “eh” Dan haka mutumin ya ce mini “sun tab’a yin businesses da tsohon ne, tsohon ya aminta da shi amman shi sai ya gudar masa da kud’insa so tun daga lokacin abubuwa basu yi mishi kyau ba! Shiyasa ya yanke shawarar dawo mishi da dukiyarsa.” Ya d’aura da cewa “Dan Allah in bashi in ce masa ya ce sunanshi Kabir, Alhaji Kabir. Ya taimaka ya yafe masa” Yana min maganar ne shi duk a tunaninsa ma ni d’an tsohon ne. Jin muryar tsohon ya fito yasa ya yi sauri ya yi min sallama a cewarsa ‘ba zai iya facing d’insa ba dan kunyarshi yake ji.’ Duk da nace ya d’an tsaya ko ruwa ne ya sha saboda naga inba magana ya yi ba tsohon ba zai gane shi ba dan ba gani yake yi ba, amma sam yak’i yarda, ya damk’a min akwatin yana d’an waiwayowa yana kallon tsohon har ya shige motarshi driver ya ja suka tafi. Akwatin na ja na kai d’aki na fito na kama hannun tsohon muka shiga ciki na zauna. Na zuge akwatin ba tare da na ce komai ba. Sai da gabana ya yanke ya fad’i dan gabaki d’aya akwatin cike yake da mak’udan kud’ad’e dollars! A hankali na ji tsohon ya ce “Kai da waye d’azu a waje?” Cikin In inaa na ce “wani mutum ne ya zo neman ka! Ya ce kun tab’a yin buisiness kai da shi ya gudar maka da kud’i.” Shirruuu tsohon nan ya yi kafin chaan! Ya yi murmushi ya ce “na kasa tunawa” Kafin ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya ce “Akwai abunda ban gaya maka ba… Inada sabara a kwakwalwata shiyasa ma kaga wasu lokutan Ina zama ina yin kuka ni kad’ai. Wani makwafcina anan ya d’auke ni satin baya ya kaini asibiti aka tabbatar da cewa ‘ba zan k’ara sati uku a duniya ba!’.” A take wani tsananin tausayinshi ya lullub’e ni! Ga dai kud’ad’e nan ya samu bayan ya sha wahalar rayuwa amman a lokacin da kud’ad’en suka riskeshi sai ya zamana ba za su yi mishi amfanin komai ba. Ban san lokacin da kuka ya kufce mini ba!. Jin ina kuka yasa tshon ya hau tambayata “menene? Mai ya faru? Me ye a cikin jakar? Ko wani abun tsoron na gani?” Shiru na d’anyi kafin ince mishi “Kud’i ne a ciki, Dollars.” Shiruuu na ji ya yi… Ya jima tukunna ya ce “Ka taimakeni ko masallatai ne in gina dan Allah. Saboda kaga ni ba ido da lafiya gare ni ba. Bana bukatar ka gina min gida ko wani abu daga kud’in tunda kaga ba lallae inga k’arshen aikin bama kawai dai ka rik’e Allah ka tayani gyara lahirata ta hanyar gina masallatai da islamiyoyi a k’auyukan nan.” A lokacin tabbas ina son komawa gida amman kuma wannan tsohon yana buk’atar taimakona a yanzu sannan inaso a ida auren Huda da Arshaad kafin In koma dan tabbas na kasa cire ta a cikin zuciyata kuma na riga na d’auki alk’awarin ba zan aureta ba! Tunda na lura sam bana cikin zuciyarta tun ranar da ta ce min Arshaad zata aura k’ok’ari kawai nake yi inga na fitar da ita a raina saboda no matter how much I love her ba zan tab’a iya zama da ita idan bata ra’ayi na ba! Amman kuma bana buk’atar a aurar da ita a gaban Idona sannan still ina jin fargabar fitowata duba da sharrin da aka yi min da kuma waenda nake tunanin ni suke nema..A ganina gara In d’an fahimci abubuwa daga b’oye kafin a kaini lahira tun da ban san waye yake farautata ba! Sannan aikin da zan yiwa wannan tsoho tabbas lada zan samu… Shiyasa a take na yanke shawarar jifan tsuntsu biyu da dutse daya.... ...Haka nan na tsaya tsayin daka wajen taimaka masa kamar yadda ya buk’ata aka shiga gina masallatai a duk k’auyukan da makarantun islamiyya gini mai kyau da had’uwa, na ban mamaki. Tabbas Ina da buk’atar kud’i amman ban tab’a yunk’urin d’aukar ko naira biyar ba! Apart from kud’in motar da yace In dinga d’auka a ciki dana abinci da shelter. Akwai kud’i sannan na samu maaikata masu yawa sosai dan ko wanne k’auye masu ginin daban suke shiyasa kafin wata uku aka fara shirin kammalawa. Ba abunda yafi sakani farin ciki irin yadda Allah ya arawa wannan tsohon tsawon rai har na tsawon lokacin da aka zo kammalawa duk da dai jikin nashi sai a hankali. Ranar da na kammala aikin da washegari ya tashi da tsananin ciwo wanda kana gani ka san sai a hankali kawai. A wannan bukkar tashi muke har kawo wannan lokacin amman fa muna cin mai kyau mu sha mai kyau. Ina ganin yana yin jikin nashi na ce “bara inje In nemo mai abun hawa a kaishi asibiti cikin gaggawa” Amman sai ya rik’eni ya rok’eni akan in tsaya akwai maganar da yake so ya yi da ni. Abu na farko da ya fara tambayata shine sunana! Duk tsawon lokutan nan Yaro yake kirana da shi ni kuma in kirashi da Baba. Sai da mutanen last k’auyen da aka yiwa masallaci suka tambayeni ‘suna son rubuta sunanshi’ Tukunna da kyar ya ce min sunanshi ‘Alhaji Kabir mai fetur’ ....Ahankali na ce mishi “sunanan ‘Junaidu’.” Da kyar cikin tsananin ciwon da yake ciki ya iya ce min “in d’auko masa wata y’ar jaka” Ya yi maganar yana mai yi min nuni da wajen da jakar take! Tabbas na shiga rud’ani saboda yadda ya juya ya nuna min jakar yasa na fahimci yana gani..... Ina d’aukowa ya ce “In bud’e” Ko da na bud’e d’in wasu takardu ne a ciki da waya had’ad’d’iya mai kyau da tsada. Wayar ya umarceni da in d’auko, in yi dialing number dana ga an yi saving da ‘barrister’. Haka akayi, tana shiga bugu d’aya ana biyu aka d’aga! Cikin girmamawa na ji ance “sir” Da mamaki na kalli tsohon wanda shi kuma yake mik’a min hannu alamun in bashi wayar… Kaina bai gama d’aurewa ba sai da na ji kalar turancin da tsohon yake yi inda cikin harshen turanci na ji yana cewa wannan wanda suke waya “Suna kusa ko? To su yi sauri suzo yanzu.” Tsoro da firgici suka sanya na mik’e da sauri na fara ja da baya. A hankali tsohon nan ya ce “Dan Allah kada ka ji tsoron komai. Matso kusa in baka wani d’an tak’aitaccen labari.” Da farko k’in yarda na yi in matsa d’in dan ni a tunanina ko d’an shan jini ne ko kuma d’an 419 bare ma da na tuno da mak’udan kud’ad’en da aka kawo mishi gaba d’aya sai na sake duburbucewa. Da kyar da sid’in goshi ya lallab’ani na matsa kusa da shi. Ina zama ya ce min “Kar ka ji tsorona d’ana, Ni ba macuci bane ba” Bai bani damar yin magana ba ya cigaba da cewa “Kamar yadda na fad’a maka da farko Allah bai bani haihu wa ba. Na kasance attajiri na gaske dan a k’asar nan idan akwai waenda suka fini kud’i tou bana jin za su fi mutum biyu! Arzik’i na ya samo asali ne daga sana’ar man fetur, da na samu Ubangiji ya sanya mini albarka harkar tawa ta bud’e sai na fad’a sana’a Business ko wanne iri ne zan yishi kuma da ikon Allah Ina farawa sai ya habb’aka ya yi albarka ta ban mamaki. Ni asalina maraya ne, tun Ina gidan marayu muke soyayya da matata da na ce maka ta rasu watan baya. Ina matuk’ar k’aunarta sai dai kuma kishiyoyinta suka zamo silar da ya sanya bata ji dad’i a rayuwarta ba! Ta rayu cikin tsananin k’unci da azabar rayuwa. Ni mutum ne wanda yake son mutane masu amana, bayan son da nake yi wa uwar gidanaa tsoron Allah da amanarta ne suka k’ara min tsananin k’aunarta. Apart from her bana jin akwai wanda ya tab’a rik’e mun amana yayi mun abu tsakaninshi da Allah sai kai Junaidu. Na sha adopting Yara in rik’esu tsakani da Allah amman kowa idan ya lek’a ya hango tarin dukiyata sai ya nemi cutar da ni! Rabinsu ma buri suke kawai suga sun halaka ni. Da taimakon Allah da taimakon uwar gidana nake tsere wasu tarkunan wanda fahimtar da aka yi tana taimaka min ne yasa aka shiga tsakaninmu na juya mata baya.” Cikin kuka ya ce “Ban tashi gane gaskiya ba sai a ranar da zata bar duniya tukunna aka samu asirce asircen suka bar jikina na ganta a matsayin masoyiyata instead of da da nake ganinta as my enemy. Na yi kuka ma yi takaici! Saboda ita take d’awainiya da ni idan ciwona ya motsa Ina kyararta Ina komai ashe itama bata da lafiya. Duk da na saki ragowar mata na biyun da na fahimci laifin su ne sannan na bata hak’uri ta ce ta yafe min amman na kasa yafewa kaina! A ranar da zata bar duniya maimakon ni in lallasheta A dead bed d’inta sai ya samana ita take lallashina. Na yi rashi tabbas sannan na san na rasa mutum d’aya tak da ya tab’a rik’e mun amana. Ita ce ta ce min ‘In kwantar da hankalina zan samu wanda zai rik’en amana kamar ita I should mark her words.’ Bayan ta rasu da kwana biyu.. daman tun kafin a shiga tsakanin mu na yanke shawarar ‘zan damk’awa mutum mai amana guda d’aya rabin dukiya ta idan na samu kenan, rabi kuma in rarraba a gidan marayu, ba wai kuma masu kula da gidan marayun zan bawa in ce su raba musu ba A’a Yaran gidan marayun zan bud’ewa account each In saka musu kud’insu a ciki saboda yadda duniya ta lalace tsaf mutane za su iya danne kud’in dan na ga yadda mutum yake komawa akan dukiya….. Saboda haka na fara searching….. A yadda na je maka a haka nake zuwama mutane amman har da waenda suka mareni! Mutum d’aya na samu kafin kai ya taimaka min kamar yanda ka yi sai dai shi ana kawo kud’i kamar yanda aka kawo aka baka ya gudu! Ko lek’e na bai sake yi ba.......” ....... Muna cikin wannan zancen Mutannen da ya kira suka k’araso. Manyan lauyoyine da kuma wani babba a efcc. Da mamaki nake kallonsu. Ban san sanda hawaye suka zubo mini ba! Jin yana musu bayani akan yadda ya yi alk’awarin bawa mai kyakkaywar zuciya dukiyarsa. Hope takardun sun zama ready? Saboda gani nan” Ya yi maganar yana nuna ni ya ce “Nine successor d’insa” A take suka ce “eh, komai is ready” Sannan suka mik’o min takardu suka ce “in yi signing.” Da farko kasawa na yi saboda yadda mamaki aljabi da tsoron Allah ya lullubeni, sai da tsohon ya rik’e mun hannu tukunna na dawo dede na shiga signing takardun da kwakwalwa ta ta kasa d’aukar d’umbin kud’ad’en da idanuwa na suke gane min!. Ina gama cike wadannan tsohon ya ce “yaso ya rabawa marayun kud’ad’en da kanshi amman kuma bashi da isheshen lokaci so zai d’aura wannan nauyin a kaina” Nan ma wasu takardun na cike na kud’i shima dede adadin wanda aka gama mallakamin wanda zan rabawa marayun nan. Jakar da d’azu ya ce ‘In d’auko in bashi waya a ciki’ Ita kuma filayene da gidaje da gidajen man fetur d’insa, ya ce min “I should consider it shikuma as thankyou from him, dan bai san ta Ina zai fara yi min godiya ba! Na tabbatar da maganar matarshi sannan na bashi hope na cika mishi burinshi.” Daga nan duk ya saka na yi signing Ina kuka yana kuka. Sannan ya bada will d’in nine d’ansa sannan ya rok’eni ‘ko bayan ranshi in dinga yi mishi addua dan Allah.’ Ganin numfashinshi yana d’aukewa yasa na kinkimeshi muka kai shi motar da mutanen nan suka zo a ciki amman Ina kwantar da shi a seat d’in baya na ji yayi kalmar shahada a hankali sannan jikinshi ya sake...... Na yi kuka matuk’a..... Ban yi k’asa a guiwa ba, tundaga Adamawa har Abuja sai da na je da kaina na fara rarrabawa marayun nan rabin kud’ad’en shi da na yi alk’awari wanda har yau ina kan aikin.” A hankali Junaidu ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce “Wannan shine sanadin arzik’i na. Babu k’arya k’ari ko ragi a cikin labarina.” ...... A hankali su Abba suka sauk’e ajiyar zuciya bayan sun gama saurarenshi kafin Abba ya ce “Tabbas Junaidu samun irinka a zamanin yanzu sai an tona. Allah ya yi maka albarka. Ka cigaba da

Chapter 24 of 26