Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kukanta tace “saboda Allah tsofai tsofai da ni amman wai ni Baban Khadija ya rufe ido ya dank’ara wa saki har uku! Saboda tsabar idonshi sun rufe ya ma manta da biyun da ya tab’a yi mini”. Da mugun k’arfi gaban Umma ya yanke ya fad’i! Saboda lokaci d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji Tabbas ita ce ta tafka kuskure abun kuma ya koma kan Anty Zainab! Wadda daga rakiya gashi yanzu ta janyo mata….. Tana cikin wannan tunanin Anty Zainab d’in ta sauk’o ta matso kusa da ita kafin tace “Yi maza Sadiya d’au waya ki kirawo Jalila mu ji…Anya kuwa an yi auren nan? Ko dai zurma mu su Maryam suka yi? Dan wallahi masifarnan tana fad’omin maganar Malamin nan na jiya na tuna. Yi sauri Sadiya ki kirata mu ji, ta bincika mana sosai.. In dai maganarshi gaskiya ce to mu samu mu koma mishi a san abun yi tun da wuri! Kin ji Sadiya! Dan Allah kirawo ta mu ji……” Cikin In Ina Umma tace “Tt ta tam! Amman d’azun nan ma mun yi waya da ita kuma ta tabbatar min da cewa an yi auren.” Hannu biyu Anty Zainab ta d’aura a kai kafin tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun Me ya faru da ni tou???” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e jikinta na rawa tace “To wai ke me ya had’a ku ne?” Cikin kuka Anty Zainab tace “Aure wai mutumin nan zai yi! Yarinya k’arama dan tsabar cin fuska shine bai gaya min ba, sai d’azu tukunna Baaba Talatu ta kirani take gaya min, ashe wai ita sun sani ita da Shuwa shine suka b’oye min wai dan kar in d’aga hankalina inzo inyi wani shirmen.. Sadiya abunda zai baki mamaki wallahi tallahi kawai zuwa nayi nace mishi ‘Ya zai yi min haka? Me yasa ya b’oye min? Ai da ya gaya min tun da wuri’ Kar ki k’ara kar ki rage daga haka kawai sai ya hau masifa, k’arshe yace In tattara in tafi ya sauk’e igiyoyinsa na aure kaff ukun da suke a kaina! Wai ya san in dai amaryar tasa tazo ba zan barta ta zauna ba. Ko kayana bai barni na kwasa ba da magariba dan bala’i ko kwana bai bari nayi ba ya kad’oni har da rufe gidansa. Ita kuma Baaba da na je mata daga jin magana bata tsaya taji ba’asi ba kawai ta hau fad’a! Wai ai laifi na ne, daman shiyasa suka k’i gaya min, ai ba a kaina Miji ya fara k’are aure ba, ai yanzu gashi na janyowa su Sadik haka yanzu zai dawo daga boarding ya tarar ba Maman shi a gidan K’iri k’iri Yaro ko secondary school bai gamaba amma ina k’ok’arin maidashi maraya, har su Khadija ma da suke gidan Miji sai ta shafesu… Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, k’arshe ma ko zama bata barni nayi ba itama ta koreni!” Da sauri Umma tace “Yanzu kenan a nan za ki zauna?” Cikin share hawaye Anty Zainab tace “To ya zan yi? Ina zan je? Port harcourt ko Ina?” Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Ki kwantar da hankalinki, zai mayar da ke, kin ji ko, In sha Allah.” Cikin kuka Anty Zainab tace “Baban Khadija fa babban d’an ka’ida ne ke kin sani ba zai tab’a bari mu zauna da saki ukun nan ba” Cikin yin k’asa da murya Umma tace “Ki kwantar da hankalinki, za mu nemi mafita In sha Allah. Sannan ko hauka muke ba zamu bar auren nan ba yasin sai dai in me taurin ruhi ce kamar Maryam wadda ta nace sai da kyar! Tukunna aka samu ta bar gidan nan, to kinga idan irinta ce ba yanda muka iya dole mu barta amman shima sai mun ci ubanta wallahi. Maza basa kyautawa wallahi sam! Saboda Allah Ina ma lefin ya d’auko miki mai d’an shekaru. Fisabilillahi Ina Baban Khadija Ina sa’ar su Khadija?Tsofai tsofai da shi.” Da sauri Anty Zainab tace “Kuma budurwa!” Cikin karb’e zancen Umma tace “Ba zai ma yiu ba fa Wallahi! Dole mu san abun yi. Ki kwantar da hankalin kar ki saka damuwa a ranki, zamu nemi mafita. Bai isa ba wallahi, kin ji. Su Shuwan nan suna bani mamaki, daga an yi magana suce wani wai kar mutum yayi shirme in za ai mishi kishiya waye waye… Bayan su basu san zafinta ba! Tunda duk cikinsu babu wadda Mijinta ya tab’a yin koda budurwa ne a waje, sun kafa sun tsare nasu mazajen amman sun iya tak’ark’arewa suna yiwa mutum nasiha akan kishiya tsabar renin wayo! Su bar waenda suka san zafin kishiya su yi magana mana ba wai su tsayayyun matan da suka kafe mazajensu ba…” Ita dai Anty Zainab mik’ewa tayi ta isa kan gado ta kwanta ta juyawa Umma baya, dan taga abun nata kamar ya fara zama cin fuska kuma. Tana jinta tana ta bambami daga k’arshe ta yi shiru ta gyarawa Ya Ja’afar wanda yayi bacci kwanciyar sa ta lullub’e sa tazo ta nemi waje gefen Anty Zainab itama ta kwanta….. Ta gama rayawa a ranta gobe zata koma wajen mutumin nan tayi masa maganar Anty Zainab asan abun yi dan gaskiya tayi mugun tausaya mata. Amman kuma abunda yasa tayi shiru bata gaya mata gaskiyar lamarin yanzu ba shine ta lura aikin mutumin kamar yakan iya juyewa kuma waiwaye! Tunda gashi na Huda ya koma kan Anty Zainab d’in , dukda ya fad’a musu dama amma still kamata yayi ace aurenta da Aslam ne ya mutu ba wai na Anty Zainab ba tunda de Hudan aka yiwa abun so it doesn’t matter ko waye Mijin nata ita ya kamata a sako…. Kanta ya kulle dole ta koma wajenshi amman ba zata bari suje da Anty Zainab ba dan yadda take a rikicen nan haka kurum taje ta tunzura mutumin yayi mata nata aikin aje garin gyara nata a tab’o na Jalila da bai gama had’uwa ba. Ko da ace zata gaya mata Hudan ba Arshaad ta auraba to sai ta tabbatar Mutumin ya gama yi musu aiki mai kyau! An d’aura auren Jalila da Arshaad ta kamashi sosai ta samu fada a wajenshi tukunna, saboda kar aje aiki ya had’a masa biyu yak’i concentrating akan na Jalila sosai, ko kuma kuma yaje ya gyara na Anty Zainab wani abun ya samu na Jalila…. A ranar dai haka suka yi bacci duk su biyun rabi da rabi. Su Hudan suna shiga a parlourn suka tarar da Ummi da su Shuraim sunata shirya dining tare da masu aiki. Ummi tana ganinsu ta k’arasa inda suke tayi hugging Hudan tana mata sannu da zuwa. Cikin girmamawa suka gaisheta ita da Aslam, ta amsa musu da kulawa, daga nan suka gaisa da su Sudais, murna kuwa a wajen su kamar suyi me tunba ma da suka ganta har da akwati ba’ Su suka ja mata suka kai mata har d’aki Abba yaso su zauna a sama amman Aslam yace “a barsu a d’akin bak’i” shi da cewa ma yayi ita akai mata nata kayan sama shi a barshi zai zauna a d’akin bak’i, shiyasa kawai Abban yace “a kai mata akwatin ta nan d’akin bak’in”. Ita dai Huda so take tace ‘a barta ta tafi d’akinta’ amman bata san ta ina zata fara ba! Ta san a idon duniya da su Abba Aslam mijinta ne amman taya ake expecting tayi sharing d’aki da shi bayan ga d’akuna birjik kala kala a gidan. Su kuwa su Daddy dama tun kafin su fita daga gidan bayan Gramma ta kirasu suka gama deciding akan zasu san yadda za suyi su taho nan gidan ita da Aslam d’in daga nan kuma su ajjiyesu shi da Hudan a waje d’aya, dan sun lura tabbas sai sun d’an taka rawa a relationship d’in nasu tukunna za a samu su ma fara magana mai tsayi da hira a tsakaninsu. Abba ne ya umarcesu da su je su yi alwala ayi sallah kafin ayi dinner. Hudan so take su had’a ido da shi amman bata samu wannan damar ba. Abba kuwa sarai ya ganta shiyasa ya maida hankalinshi gaba d’aya kan Dad suka shiga hira…. Ganin ta a tsaya ne ya sanya Ummi ta k’araso inda take ta rik’e mata hannu tana murmushi kafin tace “Muje to nan d’inma in rakaki. Naga kin tsaya. Aslam muje In taka ma Amaryar taka, kunyar mu take ji naga alama” Juyawa kawai yayi ya fara tafiya. Ita kuma Ummi ta ja hannun Huda suka nufi d’akin.. A bakin k’ofar bayan taga shigewar Aslam ta ja ta tirje sannan ta kalli Ummi kamar za tayi kuka tace “Ummi wai nima a nan d’akin zamu zauna kuma ni da shi?” Dariya sosai ta bawa Ummin amman sai ta dake ta d’an b’ata rai kafin tace “Eh mana! So kike ya zauna shi kad’ai? Wa zai dinga gyara d’akin yana wanke band’aki? Ko so kike a dinga tura mishi su Linder suna shigar masa anyhow?” Da sauri tace “Ummi zan dinga zuwa kullum da safe ina mishi Allah” B’ata rai sosai Ummin tayi this time around kafin tace “Zamu b’ata da ke fa! Dole anan zaki zauna Huda. So kike idan yana buk’atar wani abu urgent sai ya nemoki kenan? Kinga, gara ki shirya fa dan hatta girki ma sai kin dinga yi masa nashi special ko da kala d’aya ne Breakfast Lunch da Dinner Kullum! Ko kin d’auka auren wasa ne?” Tabbas ta san da waennan abubuwan dan sai da Shuwa ta tsara mata komai amman ita dai a tunanin ta su Ummi da Abba zasu d’aga mata k’afa tunda ai ba shi takeso ba kuma sun sani…… Wani k’ululun takaicine ya tokare mata mak’oshi! Tayaya ma za ace saboda zata dinga yi mishi aikace aikace da abubuwa har wani kuma sai ta zauna da shi a d’aki d’aya dole! Sai kace wani baby.. Ji tayi Ummi ta ja hannunta sun shige d’akin sannann ta mayar a k’ofar ta rufe. Sai da ta kaita kan gado tukunna tace “Ki yi sallah ku fito dinner” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin........ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 59 Sai da Ummi ta fita tukunna Huda ta fahimci Aslam baya d’akin…har ta fara murna sai kuma ta ji k’arar ruwa a toilet. Kamar mara gaskiya haka ta zauna ta k’ame a guri d’aya har ya fito. Kallonta kawai yayi ya d’auke kai, ya fita. Sai a sannan ta sauk’e k’akk’arfar ajiyar zuciya sannan ta zabgawa k’ofar da ya bi ya fice harara kafin itama ta mik’e ta shiga toilet d’in tayi alwallah ta fito ta tayar da sallah.. Ta jima tana adduar Allah ya dawo da Ya Arshaad, watak’il idan su Abba suka ga idonshi su raba wannan auren, ta samu ta auri wanda take so itama yake sonta. Bayan ta shafa ta mik’e ta fita zuwa dining. Ummi da su Shuraim ne kawai akai, da alamun su Abba basu dawo daga mosque ba, Ummi tana ganinta tace “Ai yanzu nake shirin mik’ewa in lek’o ki, na ji shiru” Murmushi tayi ta k’arasa wajen, har ga Allah Ummi tana burge ta Ubangiji yana son bayin sa masu tuba bayan sun fahimci sun yi kuskure. Tana zuwa ta ja kujerar gefenta ta zauna suka fara hira ita da su Shuraim waenda suke a opposite d’insu ita da Ummi. Ko 5 minutes bata yi da zama ba su Abba suka shigo.. Opposite d’insu Abba ya zauna , ga mamakin Huda sai taga Aslam ya ja kujerar gefenta shima ya zauna! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Abba ba dan har kasa b’oye farin cikin sa yayi ya fara zuba murmushi… Ummi itama murmushin tayi kafin ta mik’e ta zagayo inda suke ta fara serving nasu.. Har ta gama Hudan tana zaune kyam! Sai da Ummin ta dawo tukunna k’asa k’asa tace mata “Ta tashi ta zubawa Aslam mana” A hankali ta mik’e dan ita har ga Allah wani abun ma kunyar Abba take ji.. Jiki ba kwari ta hau serving nashi, tana gamawa ta tura masa komai gabansa itama ta zubawa kanta abinci kala d’aya kawai d’an kad’an. Baka jin k’arar komai sai cokula.. Although ba Hudan bace ta dafa abincin amma yadda tayi serving nashi da yanda take zaune kusa da shi tabbas zai iya cewa this is the best dinner da ya tab’a having a rayuwarsa! Lokaci lokaci yake lumshe ido yana sauk’e ajiyar zuciya ba tare da kowa ya lura da shi ba. Abba ne ya fara jan tissue ya goge bakinsa ya sha ruwa yace “Alhamdulillah” daga nan ya mik’e ya juya ya nufi hanyar fita. Yadda ta san zai ji xeji, Ummi tace “Abba fita zaka yi ne?”. Bai juyo ba, be kuma kalleta ba kawai yasa kai ya fice. Ajjiye spoon d’insa Shuraim yayi ya mik’e ya bar wajen gaba d’aya ba tare da ya k’arasa cin abincin nasa ba. Jikin Ummi ba k’aramin sanyi yayi ba, ta san cewa tunda ta dawo Abba baya kulata amma tayi tunanin tunda a gaban su hudan ne zai kulata yau, ta samu ta d’an ji sanyi a ranta. A b’angaren Huda kuwa, ba k’aramin kunya taji ba shiyasa itama kwata kwata ta kasa ci gaba da zama a wajen dan bata so su had’a ido da Ummin, ta lura da yadda Shuraim ya had’a rai ya mik’e ya bar wajen, dan haka tana mik’ewa ta nufi sama side d’insu.. Tana shiga ta tarar da shi yana kuka! Da sauri ta k’arasa inda yake zaune akan gadon ta zauna ta kamo hannunsa, k’ok’arin mik’ewa ya fara yi dan haka da sauri tace “Shuraim wait, let’s talk mana. Ka daina kuka ka fad’amin me yake damunka, ka ji?” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya share hawayenshi kafin yace mata “ba komai” kawai. B’ata rai tayi sanann tace “To shikenan! Bara kaga in tashi in tafi kuma ina sauk’a zan d’auki akwatina in bar gidan nan gaba d’aya in dai baka gaya min ba. Sannan sai na gayawa Abba da Ummi kana d’aki kanata kuka” Sai da ya gyara zamanshi ya fuskanceta sannan yace “Abba ne! Ya tsani Ummi. Tun lokacin data dawo daga tafiya baya kulata baya yi mata magana kwata kwata. Idan ita ta kula shima sai dai yayi mata banza ya wuce kamar yadda yayi yanzun. Kullum sai naga Ummi tana kuka not once sometimes a rana sai tayi kuka sau wajen biyar shi kuma he don’t care! Ban san meyasa Abba ya tsani Ummi ba, dama chan baya sonta yanzu kuma ya sake tsanarta!” Da sauri Huda tasa hannunta ta toshe masa baki, sannan tace “kar ka ce haka Shuraim, kar in sake jin irin haka a bakinka. Abba bai tsani Ummi ba, ka ji ko? Kawai maybe su d’anyi fad’a ne kad’an amman na san za su shirya soon, ka ji? Ka daina sakawa a ranka zasu shirya ya zama kamar basu tab’a yin fad’aba in sha Allah soon kuma, ka ji ko?” Still kuka yake yi, dan haka Huda tayi ta lallashinshi har sai da ta samu yayi shiru ta tilasta masa ya k’ara cin cookie a d’akin dan bai wani ci abinci sosai a k’asan ba tukunna ta mik’e ta d’auko mishi tooth brush d’inshi da bathrobe ta bashi tace yaje yayi wanka yazo ya kwanta idan ma game yake son yi sai su yi tare. Shuraim a zuciyarshi ya ji ya sake jin k’aunar Hudan, yadda ta tsaya take k’ok’arin taga yayi farin ciki hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba. Karb’a yayi ya fad’a toilet d’in ita kuma ta jona ps ta fara yi musu settings… Sai a lokacin Ummi ta bar bakin d’akin tana rik’e kukan da ya taho mata... Tana shiga d’akinta ta saki kukan, tabbas tayi kuskuren da ita kanta ba zata tab’a yafewa kanta ba! Kalla fa yadda Hudan take da hankali take k’aunar jininta amman haka nan tayi depriving d’inta childhood mai dad’i! Ta rabata da Mahaifinta! Ta sanyata ita da uwarta a k’unci basu ji ba basu gani ba duk saboda So da Burin mallakar Mijin da a yanzu ta riga ta hak’ura dan ta san ba zai tab’a accepting d’inta ba…. Ummi ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita, tabbas zata samu lokaci ta ware ta rok’i Abba ya barta ta je taga Mama ta nemi yafiyarta sannan zata ta nemi yafiyar Hudan itama dan kwata kwata ta kasa sukuni tana jin zafi da dana sanin abunda ta aikata a baya Inama ana dawo da hannun agogo baya....... Abba Yana fita direct side d’in Daddy ya nufa, yana shiga ya tarar da su suma suna dinner su uku abunsu. ………Yanzu Mom ta samu sauk’in Jalila biyayya take yi mata kamar zatai mata sujjada! Duk abinda tace shi take yi sannan ta maida kanta k’asa kamar wata y’ar aiki, yau ma ana gama abinci ta d’iba ta wuce d’akinta har da cewa Mom d’in ‘ko akwai aikin da take so ayi mata?’ Murmushi kawai Mom d’in tayi mata sannan tace ‘ba komai’ already a ranta ta riga ta gama shiryawa akan gobe gobe za tayi mata korar kare! In sha Allah……. Kujera Abba ya ja ya zauna kusa da Daddy. Duk da ya k’oshi amma sai da Daddy ya saka shi yad’an tab’a wani abun. Auwal ne ya fara mik’ewa saboda yana da tulin aikin da yake son yi and yanaso yau ma ya sake gwada sa’ar shi ko Allah zai sa Sakina ta amsa wayarshi. Dan haka yayi musu ‘sai da safe’ ya wuce sama. Daga nan itama Mom ta mik’e suka fara tattare dining d’in ita da mai aikinta.. Tana shigewa Abba ya dubi Daddy yace “Daddy magana na zo mu yi akan Maryam!” Juyowa Daddy yayi ya bashi dukkannin attention d’insa kafin yace “Ina sauraronka, what about her?” Soundin so worried and disturbed Abba yace “Har yanzu bata d’aukar waya ta! Bata replying messages d’ina.. I think kawai mu je mu samu su Abba Madun maybe shi zai iya bata shawara ta d’auka” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace “Abba, I know what you are going through amma sai nake ganin kamar Maryam tana buk’atar more time kafin komai. Ka duba kaga irin abunda Mijinta yayi mata sannan na san ta san Granpa ya sallame mu daga estate saboda Huda kuma na san yanzun ma Huda zata iya gaya mata ya sake korarta! Gaskiya bana jin su kansu su Abba Madun za su goya mana baya ko da ace mun je mun same su da wannan maganar. Let’s assume ma sun goya mana bayan ni na san Maryam ba zata tab’a yarda ba a yanzu, kuma kaga idan suka bata shawara itama ta basu nata uzuri dole fa in aka auna aka duba za a ga ta fimu gaskiya ne. Sannan Granpa! Allah kad’ai ya san irin yawan y’an kallon da zamu kwasa da shi idan Maryam ta dawo gidan nan a yanzu!. Bawai zan yi backing out bane in daina goya maka baya ba not at all Abba, all I’m saying shine Ka kwantar da hankalinka mu d’an jira kad’an tukunna, na san dole Granpa zai sauk’o kwanan nan tunda yanzu case d’in ya shafi har Aslam, kaga daga nan sai mu san abun yi”. Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace “Na ji kuma na fahimceka. Amman nima inaso ka fahimceni… Daddy, Idan akwai abinda na sani wanda yake dahir! To shine ko da ace Granpa ya huce mun koma yayi accepting d’inmu da Huda to fa ba zai tab’a accepting Maryam ba kuma idan aka taso da zancen wani sabon case d’inne zai kuma b’ullowa, kaga kenan an koma square 1! So ni a gani na this is the right time da ya kamata muje ayi magana a gyara komai, In yaso idan ma ya hak’ura kaga already Maryam tana nan so babu yadda zai yi. And another thing is wannan Usman d’in! Na san yanzu baya nan saboda iyayensa sun ce ko k’afar gidan da Maryam take kar ya taka amma fa su suka haife shi, shekarun baya Maryam d’in ta tab’a bani labarin yadda Mahaifiyarsa ta murzawa idanuwanta toka ta fifita farin cikin d’anta akan na kowa, so yanzu idan ya dawo ya nuna musu bai hak’ura ba na tabbata hak’uri kawai za a bayar kuma na san Maryam ba zata iya ce musu a’a ba.. Waennan dalilai Daddy su saka sanya kaga hankalina duk ya tashi! I don’t want to loose her again.” Ya k’arashe maganar kamar zai yi kuka. Gaba d’aya sai tausayinsa ya rufe Daddy dan haka yace “Ba komai, In sha Allah ba zaka rasata ba. Za muje d’in, in Allah ya kaimu ko gobe da yamma ne idan na tashi a aiki zan biyo company d’in naku sai mu wuce.” Sai a sannan Abba yayi murmushi yace “Thank you Daddy” Murmushi shima Daddy yayi daga nan suka shiga tattaunawa……. Tunda suka fara magana Mom ta lab’e a kitchen, babu abunda bata ji ba, gaba d’aya ta hada gumi kamar ita akace za a k’arowa kishiya. Sai da su Daddy suka bar dining d’in tukunna ta samu ta fito ta haye sama da niyyar d’aukar mayafinta ta nufi wajen Ummi amma sai aka yi rashin sa’a Daddy ya rik’e ta, ta so ya d’an fita ko ita ya barta taje ko parlour ne tayi waya amman k’iri k’iri ya kafa ya tsare yayi kane kane! Ba yadda ta iya haka ta hak’ura ta bari akan gobe suna fita office zata je ta samu Ummin…. Sai da Sudais yayi bacci tukunna suka yi sallama da Shuraim wanda zuwa yanzun ya ware kamar ba shi ne yake ta kuka d’azu ba! Haka nan ta fito ta barshi yana game d’in. Ta so ta wuce d’akinta kawai amman sai akai rashin sa’a suka had’u da Abba tana fitowa daga parlourn nasu. Ajiyar zuciya ta sauk’e dan daman tana son ganinshi, duk da bata san ta Ina zata fara ba but they need to talk. Kallonta yayi ya kalla inda yaga ta nufa, da sauri ta fara kame kame “Um daman zz n” Cikin katseta yace “It’s late, bara in je In kwanta. Good night.” Har ya wuce yaji tace “Abba” Juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa. K’arasawa tayi inda yake a tsaye tana wasa da fingers d’inta. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Talk mana, Um?” Yana mai bata full attention d’insa. Da kyar ta iya ce masa “Abba daman it’s about Ummi” B’ata rai yayi sosai kamar bai tab’a dariya ba! Kamar ta sani dama tak’i yarda ta kalleshi taci gaba da magana “Abba dan Allah ka daina yi mata abunda kake yi, ka dinga kulata please Abba kar..” Cikin katseta yace “Ita Ummin tace miki bana kula ta?” Da sauri ta d’ago ta hau girgiza kai kafin kanta tsaye tace “Shuraim ne, d’azu ko abinci bai k’arasa ci ba ya bar dining d’in. Ina hawowa na ganshi yana ta kuka, da kyar na lallab’ashi.. Abba if this continues zamu iya samun matsala da brothers d’ina a gaba musamman ma idan suka k’ara wayo suka fahimci duk ata dalilina ne kake yi mata hakan. Dan Allah Abba ka daina Ubangiji ma ana yi mishi laifi ya yafe Ummi ta gane kuskurenta..kalla yadda take yi min, Abba please ko dan neman zaman lafiyarmu ni da su Shuraim ka dai na yi mata haka, no matter yanda muke ni da su uwa uwa ce! Ko ni idan naga ana yiwa Mama haka akansu ba zan ji dad’i ba. Please Abba dan Allah” Ta fad’i hakan tana me matsowa ta kama hannunshi a nata ta rik’e. Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e ...Tabbas abunda Huda ta fad’a gaskiya ne, shi kansa saboda su Shuraim d’inne ma yasa yake sassauta mata abubuwan da ya shirya zai yi mata tunda ta nace sai ta zauna da shi! Ummi tayi masa abubuwan da baya jin zai iya yafe mata, yana so ya yafe amman ya kasa, but kamar yadda Hudan ta fad’a kar aje a samu matsala ya raba kan y’any’ansa da kanshi dan haka dole zai dinga danne zuciyarsa…… A hankali yaji Hudan ta sake cewa “please Abba” Kamar zata yi kuka. Murmushi yayi ya zare hannunsa a nata ya shafa kumatunta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya.. Baya jin akwai uban da yake yi wa y’arsa irin son da yake yiwa Huda, she’s just like her Mom everything hatta halayyersu iri d’aya ce! Kalla yadda take yiwa kishiyar Mamanta campaign dan kawai kar ayi hurting kowa. A hankali yana kallonta yace “Naji na daina I promise” Murmushi ta fara mai had’a da dariya kafin tace “Thank you Abba” Jingina kai yayi shima yana murmushin yace “Ai kin iya campaign dole in hak’ura, amma inaso nima kiyi min campaign a wajen Mamanki!” Da sauri ta sunkuyar da kanta dan ita kunya ya bata. Dariya yayi kafin yayi kalar tausayi yace “Please princess Tak’i d’aukar wayana. Ko bakya so ta dawo nan ku zauna tare? Kin fi so koma gidan Usman?”. Da sauri ta girgiza kai. A hankali yace

Chapter 5 of 26