Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mamaki? Ashe Ya Aslam ya sanni tun kafin yazo gidanmu shi da Ya Arshaad............” Nan ta zaiyyane mata labarin da ya bata da kuma yadda yake nanata mata yana ‘tsananin k’aunarta’ yake kuma gwada mata. Da zaman da suka yi a chan gidan da komai…… Murmushi kawai Sakina ta yi kafin ta ce “Hudan you are lucky, Very lucky! Ban yiwa Ya Arshaad adalci ba amman inaso ki rubuta ki ajjiye ni Sakina na ce ‘Ya Aslam ya fi k’aunarki Akan Ya Arshaad’ Sannan Huda dan Allah ki daina pushing d’insa away ki janyo abunki ku rungumi juna, Allah ya bawa Ya Arshaad shima tashi wadda zai so. Ki nutsu, ki fahimci karatun soyayyarsu su biyun duk true love suke yi miki that I’m sure of amman ko waye yaji labarinku ya san Ya Aslam ya fi k’aunarki although Ya Arshaad shima has sacrificed a lot for you sannan shine ya reneki kika zama mutum therefore na san ba lalle ki iya mantawa da halaccinsa ba wanda ni kaina ba zan tab’a mantawa ba amman Huda soyayyarki da Ya Aslam daban take a cikin labarin soyayya! Ki nutsu kar ki cuci kanki dan kema kina son abunki fahimta ne kawai baki yi ba.” Hudan na shirin yin magana Aaima ta hawo. A kan 3 seater da suke zaune ta zauna kafin ta ce “Anty Huda da Anty Sakina, kinga na kasa hak’ura sai da na sake biyoki ko?” Ta fad’i maganar tana kallon Sakina. Murmushi kawai Sakina ta yi ta kamo hannunta. “Crying bride” Aaiman ta ce tana d’an lakatar hancinta, sannan ta d’aura da cewa “Amarefa sun daina kuka yanzu” A hankali Sakina ta d’an kwanta a jikinta ta ce “Thank you Aaima. A lot!” Murmushi Aaiman ta yi kafin ta ce “Ba komai Sakina, Allah yasa mu dace. Ni dai yanzu matsalata shine wannan kukan da kike yi, ki daina pls, ko kun zo tafiya kar ki sake yin wani kuka Ya Auwal raina ki zai yi! Bar ganin bashi da lafiya Allah idan ya tusoki gaba ko hmm.. Gara ki nuna mishi kema Amaryar zamani ce” Duk murmushi suka yi kafin Huda ta ce “Aaima Allah duk ranar da za a kaiiki gidanki idan kika yi kuka ni kad’ai na san me zan yi miki” Murmushi ta yi ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce “Speaking of which..Ina son tambayarku wani abu amman kunyar ku nake ji” Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da tafukan hannunta. Dariya duk sukayi dan yadda ta yi d’in dole ka yi dariya. Cikin dariyar Hudan ta ce “Mene pls?” Sai da ta d’an dara itama kafin ta ce “Sakina wanda ya maidaki gida shekaran jiya wachchar Brothern ku ne?” “Woow!!” Sakina ta ce da d’an k’arfi tana d’an zaro idanu waje kafin ta ce “An gama! Ai harma na hango ranar d’aurin auren ku. Kin san shima sai da ya ce min he felt something..” Wani ihu Aaima ta yi a hankali sosai irin na jin dad’in nan kafin ta ce “Shikenan…” sai kuma ta sunkuyar da kanta ita ala dole ta ji kunya, k’arshe ma tashi ta yi ta tafi bayan ta yi hugging Sakina ta ce mata “A kula da Ya Auwal plss Allah ya bar k’auna sai kun dawo” Tana fita Sakina ta zaro waya zata kira Junaidu Hudan ta rik’e mata hannu. Da d’an mamaki ta juya tana kallonta kafin ta ce “mai ya faru?” A hankali Huda ta ce “Sakina Aaima bata yi deserving suruka da k’anwar Miji irin Umma da Jalila ba. Shiruuu Sakina ta yi itama duk sai jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ce “Tabbas” Dede nan su Khadija suka hawo suna haki Yayar Khadijan ce ta ce “Hudan wannan tour a gidanki ai aiki ne!” Sai kuma ta ce “Na ga d’akin da zan zauna idan na zo yi miki wankan jego a chan ma muka shantake Gadon laushi Allah yasa dai idan nazo kar in yi ta bacci dan gadon nan duniya ne.” Dariya Khadija ta yi kafin ta ce “Ai kuwa ki shirya dan alamu sun nuna nan da wata tara cif za ki dawo zaman jegon. Duk dariya suka yi banda Huda wadda hankalinta ya fara tashi dan ta ga yamma ta fara yi. Sai da suka huta tukunna suka mik’e suka dudduba saman chan sama kuwa suka ce basu isa su shiga turakar sabbin maaurata ba haka kurum su ganewa kansu. Haka nan Khadijah ta tisa Hudan a gaba sai shak’iyanci take yi mata Hudan kuwa kamar ta yi kuka dan ita kad’ai ta san halin da take ciki. Suna a haka Gwaggo Asabe ta shigo, abun dariya suna had’a ido da Sakina kawai sa Sakinar ta saka kuka…. Dakyar aka lallab’ata aka rarrasheta suka yi sallama da Huda tana kuka itama tana kuka Gwaggo Asabe da su Khadija suka yi mata rakiya har bakin mota su kuma su Khadijan aka saka driver ya maidasu gida daman sun yiwa Huda sallama, ta so ta basu ko d’an inner wears ne na sa rana da ake rabawa, ganin a yanda suka tafi yasa ta yanke shawarar kai musu har gida in shaa Allah. Aslam, ne ya kai su Sakina har airport, ita da Daddy za su yi tafiyar wanda yaketa janta da hira da barkwanci ba ruwanshi da wani batun surukantaka, sai da ya ga ta d’an sake tukunna ya ji dad’i… Haka har jirginsu yayi taking off. Duk dauriyar Sakina sai da idonta ya cicciko sanann ta k’ank’ame kujerar da take kai, sai da jirginsu ya dedeta ya lula sararin samaniya tukunna ta samu nutsuwa Daddy yana ta tsokanarta. Washegari da daddare Granpa ya nemi ganin kowa! A lokacn jikin Huda ya d’an yi sauk’i tafiyar ma ba laifi dan k’afar tata ma da sauk’i dan haka suka tafi tare ita da Aslam. A chan suka tarar da kowa. Suna zuwa Huda jikin Mommy wadda ta fara mik’o mata hannu taje ta fad’a. Sai da suka gaisa cikin so da tattali tukunna ta mik’e ta nufi inda Aslam yake a gaban Granpa. “Hmm” kawai Mammmy ta ce ta yi d’an mitsitsin tsaki sannan ta kauda kai. Cikin kulawa Granpa ya amsa gaisuwar tata ya na mai tambayarta “ya sabon guri?” “Alhamdulillah” ta ce ba tare da ta iya d’agowa ba dan gaba d’ayansu kunyarsu take ji. Sai da kowa ya zauna tukunna Granpa ya kalli Dad ya ce masa “Ina Muhammad?” Cikin tsananin tashin hankali da rashin jin dad’i dan su already sun san case d’in tun 3 days ago shi da su A hankali Dad d’in ya ce “Bamu gansa ba since” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e, shi kansa bai san ta Ina ma zai fara ba. A hankali ya ce “Yi musu waya su shigo za a nemoshi.........” Mutanen nan da suka zo suka d’auki sample na tomb print d’insu sukayi musu tambayoyi sune suka shigo. Dukkan su waje suka nema suka zazzauna bayan sun kai wani file gaban Granpa sun ajjiye. A hankali Granpa ya kalli Dad ya ce “Kirawo Yusuf! Duk da ya san komai ya kamata a yi komai da su har Auwal da Adama” Computer d’in parlourn ya yi using ya kira Daddy..,, Mom na gefensa a lokacin suna cin abinci, yana ganin kiran ya ji gabnsa ya yanke ya fad’i! Dan haka ya ture abincin ya d’auka ya ajjiye wayar a gabansu shi da mom. Bayan y’an gaishe gaishe Granpa ya ce “Ina Auwal?” Suka ce “su suna hotel su Auwal kuma suna asibiti” Kamar zai ce ‘a kirashi shima’ sai kuma kawai ya ce ‘a barsu kawai’ Daga nan ya yi gyaran murya ya fara magana….. “Last week waennan mutane sunzo sun karb’a tombprint d’in kowa! Na san ba lalle kun san dalilin d’aukar tombprint d’inba dan haka bara in yi muku bayani.” A hankali Aslam ya mik’e ya ce “Granpa, please excuse me” Kana ganin fuskarsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. Cikin no nonsense face Granpa ya yi amfani da kakkausar muryar wajen ce masa “Koma ka zauna!” Babu alamun wasa a tattare da shi. A hankali Aslam ya koma ya zauna yana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere jijiyoyin kansa duk sun baiyyana…Ya rasa wanne irin taurin kai ne Granpa yake da shi! Shi sam bai yi tunanin wannan maganar za ayi ba da wallahi ba zai zo ba! Shi a tunanin sa sun riga sun gama kashe case shi da su granpa d’in da su Abba har abada……. Muryar Granpa d’in ce ta katseshi jin ya ci gaba da magana yana cewa “Dalilin da ya sanya aka d’auki tombprint d’inku ba komai bane ba illa… A lokacin da ake bincike an yi nasarar samun yatsun mutum biyu da palm a jikin tukunyar da Huda ta dafa coffee wanda kamata yayi a samu tombprint d’inta ita kad’ai tunda hatta Ummi ta ce bata tab’a tukunyar ba ma Ita ta zuba mata da kanta.” Kwarewa Mammy ta yi da k’arfi wanda duk ya janyo hankalin jama’a kanta. Da sauri Aaima ta je ta matso ruwa a dispenser ta kai mata suka shiga shafa mata baya ita da Mommy tana sha tukunna ta d’an dawo dede. Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa “Bincike yana tafiya bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k’arfi ne a ciki sannan har da shinkafar b’era. Sai kuma still aka samu gidan allura a cikin dustbin d’in kitchen d’in wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba face poison d’in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d’in. Tou a jikin syringe d’inma kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d’in wan..........” Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen gaba d’aya sai kallo ya koma kansa. Shiruu parlourn ya d’auka na y’an mintuna kafin ya ce “Assalam alaikom, sorry I’m late” Bai jira jin me za su ce ba ya k’arasa gaban officer d’in kawai ya mik’a mishi hannayensa duka biyu. Kuka Dad ya saka kawai ya mik’e ya fita. A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k’asa wasu zafafan hawaye suka zubo masa. Da mamaki Mommy ta mik’e ta k’arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce “Arshaad me ye haka ?” Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d’aya! A hankali yana kallonta ya ce “Mommy ni ne! Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k’arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi! Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d’aya abun ya fad’a kan Ummi dan haka dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana kowa ya tafi officer please arrest me” Ya k’arashe maganar yana sake juyawa ya mik’awa officern hannuwanshi duka biyu kamar farko. Mik’ewa kawai officer d’in ya yi ya zaro ankwa. Ba k’aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d’inba cikin fushi ta cewa officer “meyene haka yake faruwa?” Kafin ta juya ga Arshaad ta ce “Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba!” Ta fad’i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa “Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi! Na san ba halin ka baneba pushing d’inka aka yi kayi hak’uri ka dawo Arshaad d’in da muka sani” Cikin kukan ta k’arasa gaban Granpa ta ce “Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba! Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad ransa ne ya b’aci zuciya ce ta kaishi ba laifinsa bane ba.” Gani tayi kawai mutumin yana k’ok’arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye ankwar, da sauri ta mik’e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad’a ta cewa mutumin “Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka maka mari!” Runtse ido Arshaad ya yi da k’arfi kafin ya samu ya bud’e ya juyo da Mommy ya ya kama kafad’unta duka biyu ya fara magana cikin d’aci Idanuwanshi jajawur “Mommy ba laifi d’aya bane a kaina okay?! Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all evidences are against me so just let it go this is wat i deserve. Dan Allah.” K’amewa kawai ta yi tana kallonshi. A hankali Aslam ya k’araso wajen ya dafa shi ya ce Arshaad! Ka juya ka fita a parlourn nan zan san abun yi please. Dan Allah ka tafi kawai! Meye ma ya kawo ka nan in the first place?!” Ya fad’i hakan cikin d’an d’aga murya. A hankali Huda wadda ta k’araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce “Ya Arshaad me ya had’aka da Ya Junaidu?” Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce “Kin tuna sharrin da aka yi masa akan case d’in Chief Justice!? Sannan akaso a sake d’auke shi bayan an sakeshi? Those that ring a bell??” A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce “Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine! Dan Allah Ya Arshaad” Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce “It was all me!” Wani irin kuka ta fashe da shi ta durk’ushe a wajen cikin kukan ta ce “How?? Why???” Ranshi a tsananin b’ace ya ce Why? Tambayata ma kike yi ‘why’!? Bara ki ji dalili ‘It was all because of you’ And bari ki ji abunda ya faru… Naga take taken Junaidu At that very day kuma kema naga kamar kina k’aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman hankalina a matuk’ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d’ina Jamil! Sai na samu suna tattaunawa akan wata magana…Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b’oye mishi komai ba na fad’a mishi damuwa ta. Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce ‘in bashi number da information d’in Junaidun kawai’. Abun ya zo mana da sauk’i saboda already best friend d’in Junaidun Yaron Abokin nawa ne Jamil. A time d’in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace ‘a san yadda za a yi min da Junaidu’ Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi.” Cikin d’aci ya ce “Kinsan wani abu?” Be jira jin me zata ce ba ya ce “Ban damu ba! Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda Idanuwana sun rufe I was just selfish and bad! And happy tunda Junaidu ya b’ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi yunk’urin raba mu. Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba bayan an sake shi na sa a d’auko mini shi.” Yana kallonta ya sake cewa “Kinsan wani abu?” Nan ma be jira amsa ba ya d’aura da cewa “Ko da aka ce motar su ta kama da wuta Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad’i ba ban kuma fad’awa kowa na san wani abu ba! Na take komai na rufe idona duk dan inga na mallakeki! I was bad! Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni.” Cikin fushi Aslam ya ce “Ba za a bari ba! Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau Kaga hakan yana nuni da still akwai good in you Arshaad you felt guilty which is good.” A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce “For your information nine na janyo aka rufe maka company d’in takalman ka! Is there any good in me left?” Ya fad’i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi. A hankali ya ji Aslam d’in ya ce “I know Arshaad na san komai! Tun kafin In tafi a time d’in da aka kirani na fahimci kai ne So dan Allah maganar nan ya wuce please”. Cikin katseshi ya ce “Na so In kashe ka! Ka bar duniya gaba d’aya In auri matarka! Is there any good in me? Still kana da hope a kaina ........” “Ina za ki je?” D’in da Granpa ya ce ne yasa gaba d’ayansu suka juya suna kallon k’ofar da Mammy ta nufa sad’af sad’af zata fice. A hankali Mom wadda tun d’azu take magana ba a jinta tace “I have something to say” Da d’an k’arfi. Duk juyawa akayi aka zubawa screen d’in ido, suna kallonta Idonta sharkaf da hawaye ta ce “Arshaad baka so kashe Aslam ba! Ka dai yi yunk’urin yin hakan amman kuma baka aikata ba saboda baka so ba....…… A ranar birthday d’in su Shuraim! Bayan Dad ya gama yi mana fad’a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious! Sannan burin da na d’aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab’arb’arewa tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu! Hankalina bai sake tashi ba sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d’in takardun MT da Granpa ya mallakawa Aslam a d’akin ka a ranar Lokacin da ta shiga kai kuma ka fita ka barta a d’akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d’inba kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba. A take take ce min ‘Komai ya zo mana k’arshe ni da ita! Amman ta samo mana solution dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!.. Dan haka yanzu it’s either I’m with her ko kuma I’m doomed’. Sai da muka keb’e mu biyu tukun ta yi min bayanin abunda za a yi shine… ‘Ga shinkafar b’era nan daman ita da shirin ta ta zo gara kawai a yita ta k’are!’. Dukda a lokacin i was furious amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k’arshe tukunna na yarda but still sai na ce mata ‘Gara mu zuba iyaka wadda zata la’antashi ko ta sakashi doguwar jinya dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba’. D’ari bisa d’ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata”. Ta fad’i hakan tana fashewa da kuka. Da sauri Mammy ta k’araso wajen ta ce “bana son munafurci! Munafuka ai da ke aka yi....” Wata mahaukaciyar tsawa Dad ya daka mata ya ce “wallahi idan kika sake yin magana sai na kasheki da hannuna kafin a tafi da ke gidan yari!” In a serious tone Granpa shima ya ce mata “Ki nutsu! Ko In saka a fasa miki kai da bindiga” Sannan ya juya ya cewa Mom “Continue” Cikin kuka Mom ta ci gaba da magana “Muna tunanin ta yadda za mu shiga d’akin su Aslam mu zuba a lemon cikin fridge d’in da yake a d’akin nasu ko mu zuba a ruwa ya sha sai Allah ya kawo sauk’i muka ji ya cewa Huda “ta had’a mishi coffe” Hudan na shigewa kitchen aka fara watsewa, muma muka fita Mammy ta cewa Dad ‘zata tafi tare da k’awarta ta ajjiyeta a bakin gate yanzu’. A gaban sa ta shiga motar kawar tata, motarsu shi da Aisha tana fita ta fito ta yiwa k’awartata sallama muka zagaya baya ta ce min ‘in tsaya a nan baya in tabbatar babu wanda ya ganta In yi keeping mata watch daga nan ita kuma zata shiga ta aiki Huda ko kuma dai ta d’an ja hankalinta ta watsa gudun kar idan zance ya fito Huda ta ce ita ce ta aiketa’. Har zata juya na rik’o hannunta na ce mata ‘ta zuba d’an mitsitsi kawai dan Allah’ A gabana ta nuna min d’an k’aramin da zata zuba wanda na tabbar ko b’era ba lallae ya iya kashewa ba! Na so ta bani ragowar amman sai ta ce ‘ko dai ban yarda da ita bane ba?’ Shiyasa kawai na yi trusting d’inta na barta ta wuce. Kafin Mammy ta zagaya ina zuwa bakin k’ofar kitchen d’in ta baya sai na ga Hudan ta fita! Ina shirin kiran Mammy a waya naga an shigo.. Wallahi Arshaad fuskarka da jikin ka a rufe suke ko’ina amman tashi d’aya na gane ka. A tunanina bakin ku d’aya kaida Mammmy sai da na ga ka zaro allurar da bata cikin tsarin mu tukunna gabana ya fara fad’uwa. Ba k’aramin sanyi na ji ba da naga har ka bud’e allurar zaka zuba kuma sai naga ka yi tsaki ka rufe ka mayar ka ajjiye alamun ka fasa”. A take gaba d’aya kowa a falon aka ce “Alhamdulillah” Cikin kuka ta ce “Garin lek’en ka da nake ta yi yasa har ka gannni ka fito ba tare da ka d’auke allurar ba. A cikin filawowi na b’uya kana wucewa na zagaya ta k’ofar parlour zan shiga kitchen d’in tun a bakin main door na parlourn na hango Huda tana shirin shiga kithchen d’in amman ban hango Mammy a kitchen d’inba wadda na tabbatar ita ce ta had’a da allurar da ba lalle ta gama sanin ta mecece ba ma da shinkafar b’erar ta matse gaba d’aya a cikin coffee d’in wanda sanadiyyar hakan ne na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo a duniya. Da sauri na fita na zagaya baya. Ina zuwa bayan kitchen d’in na ga Mammy a wajen tanata gumi, ta ce min ‘ta zuba amma fa saura kad’an Huda ta kamata’. Jin kamar tahowar mutum ta bayan mu ne ya sanya kawai muka yi sauri muka bi ta gaba muka bar wajen. Na saka driver ya mik’a Mammy estate ni kuma na koma part d’ina.” Cikin kuka ta ce “Arshaad ba kai za a kama ba Mu za a kama…baka da laifin komai”. Da sauri Mammy ta ce “Ke dai za a kama munafuka!! K’arya take yi min, duk abunda ta fad’a k’arya ne wallahi.” A hankali Arshaad ya lumshe idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo masa. Mom bata damu ba ta ce “Another things… Although ban san waye ya turo Mommy daga bene ba but Mammy nake zargi dan na ji tana waya rannan kamar da malaminta ne tana cewa ‘a sake toshe mata baki a goge mata tunani kar ta tona mata asiri kafin ta san abun yi next da ita’ da kuma na tambayeta sai ta k’i gaya min komai dan haka bani da tabbas amman tabbas na san wanenen musabbabin ciwon nata tun farko Mammmy ce ta yi mata asiri! Har wajen bokan da yayi aikin idan kuna so zan kaiku. Shiyasa tun a cell Mommy tana warkewa mu bama ma saniba Ita kuma Mammy ta fara mugayen mafarkai Inaga sauk’ar da akeyi a gidan nan kullum ne ya sanya abun bai koma kanta ba ta samu mafarkan suka barta.” A hankali Aslam ya ce “Ita ta turo ta daga bene” Kafin ya kalli Mommy ya ce “Mommy ranar da naje zan ce miki Ina son tafiya Uk ana i jibi auren su Arshaad… Pretending kawai na yi dan ban san ta Ina zan fara ba sannan naji kin ce peace da kwanciyar hankali kawai kike buk’ata a yanzu Amman tabbas na ji conversation d’inku ke da Dad.” Mom ce ta sake cewa “Sannan mammy.....” Da sauri Mommy ta k’arasa gaban screen d’in ta had’e hannuwanta biyu ta ce “Dan Allah dan Annabi Adama ki yi shiru” Sai kuma ta fashe da wani sabon kuka. A hankali Granpa ya ce “kowa ya zauna” Ba ayi minti uku ba duk suka zazzauna har Arshaad da Granpa ya sake ce mishi “Muhammad zauna kaima” Da kyar Granpa ya samu ya ci gaba da magana…. “daZa mu yi amfani da tombprint mu hukunta mai laifi… Second hannun da ya fito a jikin tukunya apart from na Huda hannun Rukayya ne! Sannan ya sake fitowa a jikin syrinji tare da na Arshaad wanda na tabbatar kafin ya saka safar da Adama ta fad’a ne ya yi mistake ya rik’e dan bai fito a jikin tukunya ko murfin ta ba. Ya fahimci hakan inaga tun a ranar da aka d’auka samples d’in shiyasa ya yanke shawarar ya gudu! Ban kuma san me ya dawo da shi ba dan haka yanzu inaso ka fad’i gaskiya da gaskiya tun da an san komai kuma muma mun fahimci komai. Kaga waennan manyan y’an sanda da ss ne kar ka cuci kanka ka yi bayanin da zasu d’auki rahoto dan na yi alk’awari sai na hukunta duk wani mai hannu a kisan Ummi!. Shin maganar da Adama ta fad’a gaskiya ce?” A hankali Arshaad ya girgiza kanshi kafin ya ce “Ba haka bane ba! Ni ne na zuba! Ni na yi hacking wayar Sakina na kira Huda waje tana fita ni kuma na je na zuba! Dama inada wannan plan d’in a raina tun dawowata saboda na fahimci Aslam yana son auren shima. Granpa na rok’eka da girman Allah ka barsu su tafi da ni.” Tsabar takaici Aslam bai san lokacin da ya shak’o sa ba ya ce “Meyene ribar ka Idan an tafi da kai? Me za ka ji a jail!? Arshaad

Chapter 20 of 26