sa
ba wannan ne a gabansu ba dan haka suka wuce suka yi cikin gidan….
Sai da suka d’an jirashi ya karya sannan ya samu damar ganinsu. Suna shiga suka nemi waje suka zauna.
Da kyar Umma ta iya ce mishi “Ina kwana”
Bata jira amsawar shi ba
ta hau zuba…
Har da cewa da ya san ba zai yi aikin ba tun jiya da bai ce ta k’ara mishi kud’i ba!
Sai da Anty Zainab ta d’an zungureta tukunna aka samu ta yi shiru.
Gyaran murya Anty Zainab d’in tayi sannan tace
“Ni a ganina yanzu aikin gama ya riga ya gama,
tunda har ta tare.
Yanzu abunda muke so shine a tabbatar da auren Jalila da shi Arshaad d’in
sannan a san yadda za a yi a taimakawa Jalila ta fitar da Huda daga gidan!”
Shiruuu, mutumin ya d’ab yi ya lumshe idanuwanshi..
Chaan! Ya bud’e, ya kalleta yace
“Na riga fa na yi abunda zan yi!
Kun tabbatar anyi auren ita Huda da shi Arshaad d’in kuwa?
Dan ni gaskiya bincikena bai nuna min an yi ba.”
Da sauri Umma tace
“Shirme kenan!
To bari kaji..
Jiya ma a gidanshi ta kwana k’arshen magana kenan.
Kuma na tabbatar idan aka bincika ma yanzu haka ciki gareta!
In dai binciken tsakani da Allah za a yi”.
Murmushi kawai yayi
kafin yace “shikenan.
Ku d’an jira ni”
Daga nan ya mik’e ya
fita.
Kamar minti biyar haka
ya dawo…
Wata bak’ar laya kawai
ya mik’o musu bayan ya zauna
Anty Zainab ce tasa hannu ta karb’a dan ita Umma in banda tura baki da kumbure kumbure ba abunda take yi.
Sai da ta karb’a sannan yace
“Ku nutsu! Ku bani dukkan hankalinku!
Dan kunga wannan abun da na baku shine kankat!
Amman muddin kuka yi ganganci aka samu matsala
to abun zai dawo kanku ne!
Kun amince?”
“Eh”
Suka had’a baki duk su biyun.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sake cewa
“Shawara itace..
Ku sake bincikawa
ku tabbatar an yi auren
dan in dai basa tare kuma
akayi wannan aikin mai zafi to
idan ya tafi bai samesu ba kan ku zai dawo! Bi ma’ana
Auren d’aya daga cikinku ne zai mutu.”
Murmushin takaici Umma tayi
kafin tace
“Mallan”
Yace “Na’am” tace “fad’a mana yadda za ayi amfani da ita kawai!
Maganar tare kam
Huda da arshaad suna tare.”
“To shikenan.
Aikin ba mai wani wahala bane ba, ita wannan abar dana baku
cikin dare za a tashi a k’ona ta k’urmus! Shikenan
Ko wanne irin kalar aure aka k’ulla musu
sai sun rabu!
Rabuwa ta har abada, idan har kinga sun dawo sun zauna
to sai dai in za a iya maida layarnan ta koma dede yadda take kafin a k’onata!.
Sannan shi kuma wannan” yayi maganar yana basu wani turare
kafin yace
“Ita Jalilar za ki bawa ta shafa a jikinta, ta tabbatar shi Yaron ya shak’a da Mahaifiyarsa da Mahaifinsa da duk wani wanda zai iya shige mishi gaba wajen auren, in sha Allah ba za ayi awa 24 ba za a d’aura musu aure.”
Sai a sannan Umma tayi murmushi tace
“sun gode”
Daga nan
suka d’anyi wasu maganganun ragowar matsalolinsu….
Sun d’an jima tukun suka mik’e suka fara shirin tafiya..
Har suka fita Malamin nan yana ta nanata musu “su tabbatar sun yi conforming auren Huda da Arshaad kafin su yi amfani da layar na”.
Zuciyoyinmu fess haka suka fito
Umma ta karb’a kayan ta danna a jaka
suka wuce.....
A gigice Mommy ta shiga d’akin Huda!
Hakan yayi dai dai da k’arasowar Doc shima.
Aslam bai bari Mommy ta gansa ba, suna zuwa k’ofar d’akin shi da Doc d’in ya fara jiyo muryarta a rikice tana yiwa Huda magana dan
haka yana nunawa Doc d’akin ya juya ya koma d’akinsa.
Sai da ta sha allurai sannan aka jona mata drip tukunna ta fara gane waye a kanta.
Mommy kuwa da ta samu Huda ta d’an farfad’o
sai ta hau fushi da Aslam.
Bawan Allah shi kam bai ma san tana yi ba yana
d’aki yana fama.
Ita da Gwaggo Asabe ne suka yi jinya, kafin dare ta d’an warware amman ba sosai ba
Sai a sannan ta samu ta kira su Mama….Lokacin ita d’aya ce a d’akin
Gwaggo Asabe ta tafi kitchen
Ita kuma Mommy taje shiryawa Dad table….
Ba yadda bata yi dasu ba akan su turo mata Sakina bata jin dad’in zaman ita d’aya
amman sam suka k’i
suka ce “in ita bata da hankali to su suna da shi” K’arshema fad’a suka rufeta da shi
Mama tayi ta gama ta bawa Ummu itama ta yi nata ta mik’awa Shuwa!
Haka nan ta hak’ura ba yadda ta iya.
Bata ce musu bata da lafiya ba dan karsu d’aga hankalinsu.
Mommy a d’akin suka kwana tare da
Ita da Gwaggo Asabe.
Ita Huda har mamakin tattali da k’aunar da Mommy da Gwaggo Asabe suke nuna mata take yi, ko tari tayi nan
da nan hankalinsu zai tashi,
ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda Mommy take cika bathtub da ruwan d’umi tace ta shiga, a ranar sai da tayi mata sitbath yafi sau biyar!.
Ita dai abun mamaki yake bata har ga Allah, gashi duk da ba wai son Aslam take yi ba
amma sai ta tsinci kanta da mugun kunyar Mommy da Gwaggo Asaben,
sam ta kasa sakewa a d’akin.
Da kyar ta d’an samu bacci kad’an, daga nan ta farka idonta ya bushe, sam ta kasa komawa dan haka ta mik’e tayi alwallah ta fito ta d’au hijabi a cikin akwatin kayanta da tazo dashi ta tada sallah.
Shima Aslam bai samu wani isheshshen bacci ba, so
yake yaje yaga jikin nata
amma d’azu k’iri k’iri Mommy ta hanashi shiga d’akin da suka had’u a k’ofa!
Kuma tak’i kulashi. Kafin ya kwanta ya kirata yafi sau nawa amman tak’i d’auka, dan
haka shima da yaga ya kasa baccin sai ya mik’e ya fara jero nafilfili…..
A Daren ranar ne kuma Umma ta k’ona layarta!
Bayan ta yiwa Jalila waya tayi mata kwatancen mansion d’in da suke ita kuma tayi
mata alk’awarin ‘gobe da safe zata zo mata ta sak’on da zai saka ta auri Arshaad’ Sannan tace mata “ta kwantar da hankalinta zata fitar da Huda a gidan in shaa Allah”
Sai a sannan Jalila ta d’an nutsu dan tun jiya da taji a wajen Umman an kai Huda gidan Arshaad shikenan ta birkice ta susuce ko bacci bata yi ba sai kuka take
ta yi duk ta fita hayyacinta.
Ba k’aramin dad’i taji a rantaba kuwa.
Haka ta kwanta zuciyarta fess
tana kwanciya bacci mai mugun dad’i yayi awon gaba da ita!
Wanda ta dad’e bata yi ba.
Washegari da sassafe y’ay’an Gwaggwo Asabe su biyu suka iso, da y’an yaransu k’anana.
Yadda Gwaggo Asabe take da kirki haka suna y’ay’anta.
Sai a sannan Huda ta d’an sake ta d’anji sauk’i dan
a cikin wuni d’aya suka saba
ta sake sosai da su, hakan
kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa su Mommy ba.
Da yamma jikin nata da d’an kwari dan haka Mommy tace “ta shirya ta fito main parlour kar zaman d’akin ya gundureta.
Suna zaune da yamman
Huda na gefen Mommy akan kujera 3 seater a zaune ana hira a main parlour Aslam ya fito!
Mommy tana ganinshi ta kauda kai gefe ta had’e rai.
Dariya Gwaggo Asabe tayi
tana tuna yadda d’azu ma yazo tayi hakan, ba
yadda basu yi da ita ba amman tak’i kulashi
k’arshe sai hak’ura yayi ya tafi kamar zai yi kuka..
Ita kam Huda rabon ta da shi tun ranar da aka kawota shekaran jiya
da yayi mata sai da safe ya fita bayan ya kawo mata kaji.
Gefen Mommy yazo ya zauna ya kamo hannunta ya b’ata rai kamar zai yi kuka.
Bata kula shi ba bata kuma kwace hannunta ba
amman ko kallon inda yake bata yi ba.
Yaran Gwaggo Asabe
Karima da Laurat ne
Suka hau tsokanarshi
dama sun saba.
Daganan kuma aka hau gaggaisawa
Karimar Yaranta uku maza itace Babba
sai Laurat tana da twins y’an biyu mace da Namiji..
Aslam yana mugun son Yara dan haka ya sake yayi ta wasa da Yaran sunata yi mishi surutunsu na shirme.
Da ido Gwaggo Asabe tayiwa Huda sign bayan sun had’a ido.
Duk sai taji kunya ta rufeta,
ita tama manta ashe basu gaisa ba!
A hankali ta d’an kalleshi kafin tace
“Ina wuni”
Sai da ya ajjiye k’aramin Yaron Karima akan kafet
sannan ya juyo yana kallonta yace
“Alhamdulillah,
ya jikin?”
Sunkuyar da kanta tayi kafin tace
“Alhamdulillah”
Hannun Mommy da yake a cikin nashi yad’an damk’e kafin yace
“Mommy bara mujewa Granpa”
Bata kula shi ba.
Hakan yasa ya mik’e tsaye yana mai sakin hannun nata yana murmushi kafin ya cewa Huda
“D’auko hijabin ki mu je”
Juyawa tayi ta d’an kalli Mommy.
Muryar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “ku je mana.
Yi maza ki d’auko hijabin.”
Ko da ta fito parlourn bata same shi ba, Gwaggo Asabe ce tace mata “yana compound”
“To” tace sannan tacewa Mommy “yace za mu fita”
Sai a sannann
Mommyn tace
“A dawo lafiya”
Tanaji gabanta yana fad’uwa!
Dan bata san ya had’uwar Huda da Granpa zata kasance ba.
Su Karima ta juya ta cewa “sai ta dawo” da Gwaggo Asabe
sannan ta sa kai ta fita.
A tsaye ta hango shi chan bakin gate dan haka ta k’arasa..
Tunda ta taho ta lura da irin kallon da yake yi mata
har ta k’araso inda yake ta tsaya.
Sai da suka yi kusan 1 minute ba wanda ya motsa a cikin su
kafin yace
“Jikin da sauk’i sosai ko?”
“Um”
Kawai tace mishi
dan ita haushima ya bata
meye nashi na wani nanata tambayar!
Bayan already ya riga ya tambayeta tun a ciki.
Yanaso ya tambayeta ko akwai abun da take buk’ata
amman ya lura kamar bata son yawan maganr tasu
dan haka ya rabu da ita kawai,
yace “muje” yana mai juyawa.
A jere suke tafiya
gwanin burgewa… Har suka k’arasa gate d’in gidan Granpa.
Cikin girmamawa mai gadin ya bud’e musu gate d’in suka wuce bayan ya gaidasu.
A k’asa Aslam suka tsaya ya kira Granpa ya bashi izinin hawa tukunna suka hau!
Gaban Huda na dukan uku uku..
A chan sama suka sameshi,
Parlournsa!
Yana zaune a kan kujera ya baza takardu yana dubawa…
Tunda suka shigo ya d’ago ya kafe Huda da ido!
Hudan kasa k’arasowa tayi sakamokon yadda fad’uwar gabanta ya tsananta
saboda yadda taga Granpa ya kafeta da ido…
Har Aslam ya kusan k’arasawa inda yake sai
kuma yaji kamar bata tare da shi dan haka ya juya.
A chan farkon parlourn ya ganta tsaye ta sunkuyar da kanta.
Granpa ya kalla sanan ya juya ya kalleta, d’an
lumshe idanunsa yayi ya bud’e
tukunna ya koma ya je
inda take a tsaye, bata yi
auni ba kawai taji ya kamo hannunta!
Da sauri ta d’ago zata yi magana taga ya tsareta da kyawawan idanuwanshi,
a hankali taji yace
“Muje mana” still yana kallonta
sannan da kyar ya samu ya iya zare idanuwanshi a nata ya juya ya fara tafiya…
Tsintar k’afafuwanta kawai tayi suna takawa suna binshi.
Sai da suka k’arasa gaban Granpa sannan yace mata “ta zauna”
Shima ya ja ya zauna a kan kafet.
A hankali yace
“Granpa Good afternoon.”
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
“Ya aiki?
Ya sabon company?”
A hankali Aslam d’in yace mishi
“Alhamdulillah,
komai Alhamdulillah.”
Juyawa Granpa yayi ya kalli Huda kafin yace
mata
“You can leave now!
Na riga na san an yi aurenku
da Aslam ba tare da consent d’ina ba!
So kije kawai ki jira sakamokon ki.”
Da sauri Aslam ya d’ago idanuwanshi ya zuba mishi,
zai yi magana Granpa ya d’aga mishi hannu, cikin d’an karaji ya cewa Huda
“Leave!
Kar In sake ganin ki a nan.”
Jikinta na wani irin mahaukacin rawa ta mik’e, da sauri Aslam shima ya mik’e ya kamo hannunta sannan
ya juyo yace
“Granpa matata fa na kawo maka..”
Cikin katseshi yace
“Aslam ba zan tab’a yarda da wannan auren ba!
Tun jiya nake expecting d’inka,
i have a lot to discuss with you.
Despite da fact that an yi auren ba tare da consent d’ina ba
I can’t believe Yahaya da Aisha suna da guts d’in kwasota ita da y’an kawota su kawo mini cikin estate!
Ranar inaji har wajen 12am ana yi min shige da fice a estate.
You are very naive Aslam
baka san halin mata ba…
Ni na san Maryam itace zata k’ullawa Yakubu shi kuma yayi taking advantage d’in innocence d’inka ya mak’ala maka useless daughter d’insa….”
Da k’arfi Aslam yace
“Grandpa!!!!”
K’ura masa ido Granpa yayi na kusan 1 minute
haka shima Aslam d’in!
Shi kanshi Granpa yayi mugun mamakin b’acin ran da ya hango a cikin idanuwan Aslam d’in…
Ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin ya janyo sandarshi ya dogara ya mik’e tsaye ya tako gaban Aslam wanda yake rik’e da hannun Huda yace
“Allah ya isa tsakanina da Maryam!”
Wani mugun kuka Huda ta fashe dashi ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin na Aslam amman gam! Ya rik’eta
as if his life depends on her hands…
Sam Granpa bai damuda
kukan nata ba yaci gaba da magana
“I loose Yakubu because of her
and now I think I’m going to loose you
duk a ta dalilinta!
In banda tsabar rainin hankali
tayaya za a d’aura maka aure da y’arta tashi d’aya babu shirin babu sanarwa a cikin rana d’aya?
Ya akai aka fasa d’aurawa da Muhammad?
Anyways
bani da intrest d’in sauraron bayanin kowa, zab’i ne kaima
zan baka kamar yadda
na bawa Yakubu…
Mun riga mun gama magana ni da Maryam
30 years ago akan
babu ita babu family d’ina!
So ba zan tab’a chanja decision d’ina ba ni
matter who gets in the way
Idan zan zama ni kad’ai a duniyar nan to zan
rayu muddin kuka ce bayan maryam za ku bi ba zan damu ba
I can survive alone.
Yusuf da Yakubu sun zab’a abunda suke so, yanzu
kai ya rage!
Duk da kuwa Ina matuk’ar jin ciwo da zafi saboda
Aslam kaine backbone d’in family d’ina kai ne na fi ji
da a kaf cikin zuri’ata!
Na san ka san da hakan
amman hakan ba zai hanani ce maka
‘Ba zan tab’a accepting matarka a estate d’innan ba!
Sannan within 4 hours ka fitar min da ita tun kafiin bad luck d’in Maryam ya shafi zuriata’ ba.”
Nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace
“Granpa!
Gaskiya d’aci ne da ita..
Abunda kake yi is not right.
No matter how yo try fa
wallahi ko ta ina aka bi aka zagayo sai an samu jininka a jikin Huda!
Da ita kanta Anty maryam d’in
you can never change that.”
Da k’arfi Granpa yace
“Shut up!!”
Bai yi shiru ba yaci gaba
“Idan kace babu ruwan ka da Anty Maryam ba zaka tab’a cewa ba ruwan ka da Huda ba tunda jikar ka ce
y’ar gidan Abba!
Ba yadda zaka yi
dole fa tana cikin zuriarka itama.”
Cikin b’acin rai yace
“Aslam I’m warning you,
keep quite!!!”
Still bai yi shirun ba
ya ci gaba
“You need to wake up!
Ka cire hatred a cikin ranka,
Anty Maryam ta rigada ta shigo cikin rayuwarka cikin zuriarka cikin family d’inka ta yi
dumu dumu babu yadda za kayi idan har kuwa kace zaka tsameta to tabbas zaka yiwa wannan family d’in babban gi’bi!
The sooner you accept that the bett..….”
Tassss!!!!!
K’arar marin da Granpa ya d’auke Aslam da shi
ya karad’e ilahirin makeken parlourn….
Tsit!! Haka parlourn yayi shiruuu, hatta kukan Huda d’aukewa yayi.
Shafa wajen da aka mareshi yayi kafin ya d’ago da jajayen idanuwanshi yace “kar ka damu
Nan da 4 hour zan fitar da matata daga eatate d’inka in sha Allah Granpa.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya ja hannun Huda suka nufi k’ofa…..
A bakin k’ofar suka ci karo da Gramma da wasu books a hannunta..
Kallon ta kawai Aslam yayi,
ba tare da yace komai ba ya kauce ya ja Hudan wadda take ta faman kuka suka fice
dan sam ya kasa ma yin magana kuma ga dukkan alamu Gramma ta ji komai.
Basu tarar da kowa a main parlour ba dan Magariba har tayi, sai da ya kaita d’akin da aka ajjiye ta tukunna ya cika mata hannu yace
“D’auki abunda kike buk’ata mu tafi”
Cikin kuka tace
“Ina?”
Kallonta yayi ya d’auke kai yace
“Ki d’au abunda kike buk’ata nace!”
Still tana kuka tace
“Ya Aslam ba inda zan bika fa!
Infact kawai ni ka maidani wajen Mama!
Kar kaje kaima ka samu matsala da Granpa.”
Ba tare da ya kalleta ba yace
“Hudan for the last time!
Ki d’au abunda kike da buk’ata
If not zan jaki mu tafi empty handed.”
Ya k’arashe maganar yana mai juyowa ya kalleta..
Kallon shi tayi still shima itan yake kallon cikin muryar kuka tace
“Babufa inda zan je da kai!
Ka maidani gidan Mama in yi rayuwata a chan”
Cikin b’acin rai ya k’araso inda take kamar zai maketa yace
“Baki da hankaline?
Da auren nawa akan ki zan maidake gidan Maman da suka kawoki nan shekaran jiya jiya?!”
Cikin kuka tace
“Ai ba auren gaskiya bane ba!
Besides daman ni inaso ince maka ka sakeni!
Ya Aslam baka sona nima bana sonka! Ba zan iya wannan zaman ba.
Su kansu su Abba a wannan karon basu k’ulla abunda zai yiu ba!
So kawai mu nemawa kanmu mafita kayi hanyar ka in yi tawa, ka samu ka zauna lafiya da Granpa.”
Aslam bai san lokacin da ya kamo kafad’unta ya manna ta da bango ba
cikin tsananin b’acin rai yace
“Ni kike cewa in sakeki!
Eh?”
Ya k’arashe tambayar cikin tsawa.
Dai dai nan Mommy da Dad suka shigo.
Da sauri Mommy ta k’arasa ta kwace Hudan wadda ta fara galabaita daga ruk’on da yayi mata tana jera mata sannu.
Cikin tsananin b’acin rai
ta d’ago bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani gigitaccen mari.
Dai dai nan Abba da Daddy suma suka k’araso, har da
Auwal wanda ya tuk’o su.
Da sauri Abba ya k’araso yana cewa
“Haba Mommy,
me yayi haka?”
Daddy ma k’arasowa yayi yana tambayar “me yake faruwa?”
Bata amsa kowa daga cikin su ba ta wuce ta fita daga d’akin.
Ganin Aslam d’in yak’i kulasu ya sa Abba ya k’arasa wajen Huda da take ta faman kuka ya janyota ya rungume ya shiga lallashinta…
Da kyar aka samu tayi shiru.
Tukunna Dad yace
“Gramma ce ta kira ku kuma?”
“Eh” kawai Abba yace
still yana rik’e da Huda.
Daddy ne ya dubi Dad kafin yace
“Bara mu tafi da su kawai
Za mu san abun yi daga nan”
Da sauri Aslam yace
“A’a Dad.
Ina da gida a nan.
Za mu tafi kawai kar ku damu.”
Dafa shi Abba yayi, sai da ya juyo ya kalleshi
tukunna yace mishi
“Muje ko Aslam,
kar ka yi gardama.........”
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
58
Lumshe idanuwansa yayi kawai ya bud’e daganan ya juya ya fita ba tare da yace musu komai ba.
Direct sama d’akin Mommy ya wuce..
A tsaye ya sameta tana ta faman safa da marwa.
Tana juyowa suka had’a ido, ckin b’acin rai tace
“Juya ka fita Aslam, ba na son ganinka!
Juya ka fita na ce.
Anya Aslam kana son Yarinyar nan kamar yadda ka fad’a kuwa?”
Bai fitan ba, ya k’araso inda take kawai yayi hugging d’inta.
Sai da ta tsorata da jin yadda jikinsa yake rawa…
Da sauri ta sa hannu ta d’ago sa, suna had’a ido yace
“Mommy cewa fa tayi in saketa!!”
Kallonsa tayi na some minutes kafin tace
“Shiyasa kake neman illatata?
Are you okay kuwa?.
Na san Huda matarka ce but dukda haka duba da abunda ka yi mata shekaran jiya ana kawota sannan kasa kai ka fita ba tare da ka bata kulawar da ta kamata ba! Sannan d’azu kalli fa yadda ka buga ta da bango kuma kana ganin yadda ruk’on da kayi mata yake neman cutar da ita but baka damu ba!
A gaskiya
Aslam hakan ya sanya na fara kokwanto fa, dan inda ace son gaskiya kake yi mata ai at least ka iya jira ku d’an saba tukunna kafin komai
amman ga wahalar biki da ta zuciya sannan kai kum...”
Da sauri yace “Haba Mommy”
Sai kuma ya sunkuyar da kanshi k’asa yana ji kamar k’asa ta tsage ya shiga..
Kamar zai yi kuka yace
“Wallahi ba abunda nayi mata.
Bama a d’akin na kwana ba ranar..”
Kasa ci gaba da tsayawa a gabanta yayi dan haka kawai ya juya yace
“Mun tafi”
daga nan yayi sauri ya fita.
A hankali Mommy ta fara smiling..a take ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Tabbas soyayyar shi ga Huda da ta dasawa aya gaskiya ce!
Dan haka ta bisu da fatan alkhairi, amma duk da
haka zata kora mishi warning akan kar ya sake attempting abunda ta ga yayi mata d’azun….
A mota ya tarar da su Dad dan haka shima ya wuce tasa ya shiga suka nufi gate
Gwaggo Asabe da su Karima suna d’aga musu hannu har suka fice…
Kamar su jawo Huda su hanata tafiya haka suke ji amma
duba da yadda su Dad d’in suke kamar a d’an firgice yasa suka bari akan za su tambayi Mommy idan ta sauk’o.
Ba yadda Aslam bai yi ba akan su bari Huda ta zauna a side d’in Daddy ba amman furr suka k’i amincewa…
Gashi daga k’arshema Dad d’in cewa yayi shima sai dai ya koma gidan da zama dan ba zai barta ita kad’ai ba..
Kamar yayi kuka, saboda duk
sun bi sun d’aureshi da jijiyoyin jikinshi ta ko’ina, haka nan
ya hak’ura kawai akan zai zauna a nan d’in ba dan yana so ba sai dan babu yadda ya iya.
Jalila, tana garden lokacin da suka shigo. Ganin motoci
ya sanya tayi sauri ta shige kitchen ta lab’e a jikin window tana hangen su tana jin su…
Allah kuwa ya taimake ta suka yi parking a kusan windown side d’in kitchen d’in Daddy,
dan yana kusa da main k’ofar shiga side d’in Abba.
Tabbas! Idan har kunnuwanta sun jiye mata dede tou kuwa Huda da Aslam mata da miji ne! To amma tayaya hakan ta faru? How??… Gaba d’aya kanta ya kulle.
Tana cikin wannan taradd’ad’in ta ji Auwal ya shigo suna magana shi da Mom, da sauri ta koma jikin k’ofar ta lab’e……….
“Wai nan suka dawo?”
Taji muryar Mom.
“Yeah, Granpa ya sake yin what he is really good at!”
Taji Auwal d’in ya bata amsa.
Da sauri Mom tace
“To kuma ai Daddy ya ce min shekaran jiya da safe sai da suka tura mishi sak’o bayan d’aurin auren Huda da Aslam d’in, ya ce musu ‘okay’
Mai ya faru yanzu kuma?”
Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace
Mom ce musu fa kawai yayi ‘okay’
Dama ni na san akwai case a k’asa!.
Mammy ita ta lalata komai wallahi, da ace ta bar Arshaad ya auri Hudan cikin sauk’i da duk haka bata faru ba. An yi miki magana kema akan ki ganar da ita amman da yake ba k’aunar Huda kike yi ba
shiyasa kik’ak’i ki ce komai!
Kuma still gashi dai Hudan surukarku ce kuma y’arku!
Dan abunda yayi Abba shi yayi su Dad
Kuma abunda yayi Arshaad shi yayi Aslam dan haka kinga babu riba kenan sai dai sake tarwatsa family ma da kuka yi
dan yadda Granpa ya rufe ido ya gurzawa Aslam to wallahi kowa ya kuka da kanshi.”
Yana gama fad’in haka ya wuce ya nufi side d’insa….
Tunda Mom take a estate d’in nan bata tab’a jin farin ciki irin na wannan ranar ba!
Dan har goshinta ta saka a k’asa tayi sujjada bayan wucewar Auwal… Arshaad ya gudu Aslam kuma sun yi fad’a shi da Granpa in sha Allah
she‘ll make sure it stays like this har izuwa lokacin da za a mallakawa Auwal d’inta MT!..
A b’angaren Jalila kuwa
ba k’aramin k’ok’ari tayi ba wajen hana kanta kurma Ihun murna! Bayan ta doka wani uban tsalle, sannan ta fara juyi tana tik’ar rawa.
Sai da ta lek’a taga Mom bata parlourn tukunna ta fito tab
wuce d’akinta a ranta tana
“Wato idan kana da uwa a duniyar nan ba wanda ya kaika gata!”.
Tana shiga d’akin bata yi wata wata ba ta d’auki wayarta ta fara kiran Umma……
Tana d’aki a zaune tana goge wa Ya Ja’afar jiki kiran Jalila ya shigo…
D’auka tayi ta saka a speaker ta ajjiye a gefe, za ta
cigaba da abunda take yi.
Ko gaisuwa babu Jalila tace
“Ummana albishirinki”
Da sauri ta ajjiye towel d’in hannunta ta d’au wayar jiki na rawa tace
“Goro”
…Nan Jalila ta shiga zayyano mata kaff abunda taji ta gani yanzunnan…..
Shiruuu, Umma tayi, tana shirin yin magana ta yi an shigo ana kuka.
Kamar an hankad’o Anty Zainab haka ta shiga d’akin a hargitse kamar mahaukaciya!
A gigice Umma take kallon ta,
sai da ta bari ta nemi waje ta zauna tukunna tace
“Zainab lafiya kuwa??”
Cikin kuka tace
“Ba lafiya ba! Sadiya
na shiga uku!!”
Da sauri Umman tace
“subahanallah mai ya faru?”
Ta yi mata tambayar tana me d’aukar wayar ta kashe ta ajjiye a gefe.
Da kyar Anty Zainab ta d’an tsayar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 26