Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka muka je wajen shi. Har da cewa ko dan halin da nake ciki zai yi mini aiki mai zafi! Shege ashe yaudarata ya kuma yi ya saka min rai Allah sai ya saka min wallahi” Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka.. Duk sai tausayinta ya lullub’e Anty Zainab, a hankali tazo ta zauna a gefenta kafin tace “Yanzu menene abun yi? Kuka ba zai kawo mana solution ba.” Hawayenta ta goge sannan ta mik’e tace “komawa za muyi! Ai ta inda aka bi aka hau tanan ake sauk’a. Wallah ko dai ya lalata auren kafin ta tare ko kuma ya biya ni kud’ina” Ta fad’a haka tana mai yafa mayafinta wanda ta d’auka yanzun. Da sauri Anty Zainab ta mik’e ta tsaya a gabanta sannan tace “Sadiya ki nutsu dan Allah. Na tabbata kafin mu k’arasa wajen nan mai uban nisa Huda ta riga ta shak’i iskar gidan Arshaad. Yanzu ni dai indai zan baki shawara ki d’auka to ki hak’ura da raba auren nan! Kinga fa yadda muka yi ta k’ok’arin rabawarnan yak’i rabuwa to maybe wani babban rabo ne a tsakaninsu Allah ne ma yake son mu shiyasa ya barmu da ranmu, kar muje mu sake yin wani yunk’urin, muje garin neman gira mu rasa idanuwanu.” Cikin tsananin b’acin rai Umma tace “To matsoraciya! Kin san Allah wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru amman aure kam na raba shi na gama billahilazim! Ai In na barsu ma To Maryam taci riba kenan! Idan zaki ci gaba da taimaka min to na gode, idan kuma ba za ki ci gaba ba to kina iya yin tafiyarki dan ni nan kin ganni wallahi sai inda k’arfina ya k’are! Na tabbatar inda ace Khadija ce take cikin halin da Jalila take ciki da kema sai inda k’arfin ki ya k’are!”. Anty Zainab taji zafin maganar amman kawai sai ta basar duba da halin da Umman take ciki kwana biyu..Jafar a haukace! Junaidu ya b’ata!! Baba ya gudu!!! Jalila kuma gata chan itama sai a hankali, sannan duk fad’in duniyar nan ita kad’ai Umman ta gayawa Jalilan cikine da ita amman har Laraba bata sani ba Umman tace ‘In ta fad’a mata tana iya gayawa su Hansai, daga nan su kuma su yayata ayi ta munafurci a cikin unguwa da dangi’ Waennan dalilan su suka sanya itama Anty Zainab d’in tayi sticking by her side take taimaka mata sannan tana tsananin jin tausayin k’awartata, shiyasa yanzu ma Mta kaawar da haushin da taji tace “Sadiya yadda na d’auki Jalila haka na d’auki su Khadija. Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kar muje muyi ba daidaiba cikin rashin sani.” Da sauri Umma tace “Hankali na ba zai tab’a kwanciya ba Zainab! Ina cikin tsananin tashin hankali.. Jiya da Jalila ta kira ni gaya miki ne ban yi ba dan kaina ya d’au chaji ba kad’an ba! Cikin jikinta ya zube, garin haukarta taje ta fad’o daga matattakala. Kinga yanzu shi Yaron Auwal babu maganar karb’ar kud’i a hannunshi kuma na tabbatar nan da kwana kad’an uwar nan tashi mara mutunci itama tsayayyiyar kanta zata auno Jalila gidan nan! Ni na ma yi mamakin da ta barta har yanzu dan kwata kwata ba shiri suke yi ba! Gashi ke kin san yadda Jalila take matuk’ar k’aunar Arshaad sannan a haka kike tunanin zan bar Huda taje ta zauna tare da Arshaad a gaban idon Jalila? Tana ji tana gani? Da wanne Yarinyar nan za taji saboda Allah? Sannan ni kaina me nayi ne haka a rayuwa da mugayen abubuwa suketa fad’o mini haka?” Ta k’arashe tana mai fashewa da mugun kuka. Rungumeta Anty Zainab tayi ta shiga lallashinta Sai da taji tayi shiru tukunna tace “Sadiya ki nutsu ki bani hankalinki dan Allah mu yi magana” Kamar wata k’aramar Yarinya haka Umma ta hau share hawayenta tana d’aga kai duk ta rikice, ta manta rabon da ta shiga kwatankwacin tashin hankali irin wannan. Sai da ta nutsu sannan Anty Zainab tace “Anjima idan na dawo daga raka Huda zan zo mu koma wajen mutumin nan, akwai wani ma shima za muje wajenshi. I’m sorry to say amma raba auren Huda da Arshaad ba zai yiu ba Sadiya tunda an riga an d’aura. Yanzu mu bar Huda mu ji da Jalila duk bala’i idan za muyi yawo tsirara mu san yanda za ayi a sati mai kamawa a aurawa Arshaad Jalila. Ke kin san wacece Jalila da kuma yadda take son Arshaad da taimakonta da taimakonmu na tabbatar Huda ba zata yi wata biyu a gidan Arshaad ba. Na tabbatar hakan sai yafi yiwa Maryam zafi akan yanzu a fasa kai Huda gidanta kai tsaye!. Yanzu ki cewa Jalila ta daure ta jure ta kauda kanta, za mu yi nasara in shaa Allah.” BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 56 Sakina ce ta yi knocking aka bata izinin shiga, tana shiga tace musu “Masu d’aukar Amarya sun zo, suna k’asa.” Dumm!! Haka k’irjinsa ya buga hatta Shuwa. Cikin dauriya Ummu ta cewa Sakinan “ta je, ga su nan zuwa” Kallon ta Hudan tayi da idanuwanta da suka k’ank’ance suna zubar hawaye, da sauri ta juya ta fita tana share tata kwallar.. Shuwa na hannun damanta Ummu kuma ta ruk’ota ta gefen hannun hagu, a haka suka sakata a tsakiya suka sauk’o parlourn da ita fuskarta a lullub’e. Kauda kai Mommy ta yi ta share kwallar farin cikin data zubo mata! A hankali ta mik’e ta k’arasa wajensu ta kamo hannun Huda ta kawota kan kujerar da take akai gefenta ta zaunar da ita sannan itama ta samu waje ta zauna kusa da ita. Ummi ce ta mik’e itama ta isa 3 seater da suke zaune su biyu ta zauna a kusa da Huda ta kamo hannunta tana murmushi (ya zamana sun sakata a tsakiya ita da Mommy ) Tsakin da Mom ta yi sai da ya d’an fito fili ba tare da ita kanta ta san zai fito d’inba! Da sauri ta wayance ta sake yin wani sound kamar wadda abu ya mak’alewa a hak’ori sannan ta shiga gaida su Shuwa tana mai k’arewa gidan kallo! Dukda cewa gidan yana da girma gashi mai bene amman hakan bai hana Mom yiwa gidan kallon k’ask’anci ba. Gaggaisawa aka shiga yi cikin barkwanci da mutunta juna, daga nan aka damk’awa su Mommy amanar Huda suka amsa hannu bibbiyu suna masu farin ciki… Mik’ewa aka fara yi da niyyar tafiya amman Amarya furr! Ta k’i mik’ewa.. Da kyar Ummi tasa hannu ta d’agota sannan ta jawo ta jikinta ta rungume ta shiga lallashinta tana cewa “muje mana dota. Yi hak’uri kinji, kowa da haka ya fara.” Cikin kuka, da muryarta wadda ta dad’e da dishashewa ta cewa Ummin “Ban yi sallama da Mama ba. Dan Allah ku kaini wajenta. Zan biku amman sai na fara yiwa Mama sallama.” Lumshe ido Ummi tayi tana jin yadda k’irjinta ya fara bugawa da sauri da sauri… A hankali ta juya ta sanarwa su Mommy abunda Hudan tace Murmushi Shuwa tayi kafin ta cewa Ummu “ta tashi ta kamata su kaita mota. Za suyi sallamar a waya.” Sai da suka yi da gaske kuwa tukunna suka iya janyeta. Tana kuka tana komai haka suka fitar da ita aka sanyata a mota Ummu da Ummi suka sakata a tsakiya Ummi sai faman lallashinta take yi..... Inda Mama take Mommy ta tambaya bayan fitar su. Sakina ce ta kaita har d’akin sannan ta juya ta fita dan itama tana so ta raka Amarya. Mota guda suka yi ita da k’awayensu su hud’u waenda suka zo rakiyar Amarya. A zaune Mommy ta sami Mama a bakin gado tana ta sharar hawaye.. Sai da ta k’arasa inda take ta dafa kafad’arta tukunna ma Maman ta san mutum ya shigo! Murmushi Mommyn tayi ta zauna a gefenta sannan tace “Ai gara da Hajiya tace a tafi da ita ba sai kun yi sallama ba dan na san daa ta shigo ta ganki a haka to da sake tab’arb’arewa al’amarin zai yi” Kukan Mama ne ya tsananta a hankali ta juyo ta kama hannunta tana sheshshek’a tace “Mommy, ga amanar Huda! Dan Allah ki kular min da ita. Ina tausayawa Huda dan ban san ya zaman nasu zai kasance ba saboda na san duk su biyun basa k’aunar juna amman kuma idan na tuna ke ce surukar ta sai hankalina ya d’an kwanta na san at least ko da ace bata samu soyayyar Miji ba na san zata samu ta Mahaifiyarshi Hakan zai d’an rage mata rad’ad’i da damuwa. Naso ace Huda ta auri mai k’aunarta amman kuma k’addara ta riga fata.” Ta k’arashe maganar tana mai fashewa da kuka. Murmushi Mommy tayi kafin tace “Share hawayenki, ki d’ago ki bani hankalinki.” Da kyar Mama ta iya tsayar da kukan nata sannan ta d’ago tana mai kallon Mommy da idanuwanta da suka k’ank’ance sukai jaa. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace “Ki daina cewa Aslam ba ya k’aunar Huda! Dan zan iya rantse miki ko shi kanshi Arshaad d’in ba ya yi mata kwatankwacin son da Aslam yake mata.” D’an zaro ido Mama tayi tana kallonta da alamun mamaki. “Kwarai kuwa” Shine abunda Mommy tace sannan ta d’aura da cewa “Tunda na warke, although ban zauna da Aslam ba ban kuma san yanayin shi sosai ba amman tashi d’aya na fahimci yana cikin matsananciyar damuwa! Kullum yana fama da zazzab’i da hawan jini, anyi anyi da shi akan ya fad’i damuwar shi amma yak’i fad’awa kowa. Sai da yaga yana shirin mutuwa tukunna ya zo ya samemu ni da Dad yace mana ‘yana neman alfarmar mu barshi ya tafi uk ya d’an yi y’an kwanaki’ Mu kuma ganin rashin dacewar hakan ne ya sanya muka hanashi tafiya. Bayan Dad ya fita ne na lallab’ashi akan ya fad’amin damuwarshi.. Da kyar ya iya gaya min dan shi har ga Allah kunya yake ji… ‘He knows he’s selfish ta ko wanne b’angare amma ya rasa yadda zai yi ya yakice soyayyar Huda a cikin zuciyarshi.’ Yace min ‘tun ranar da ya fara ganinta tun ba yanzu ba Allah ya d’aura masa matsannciyar soyayyarta! Kuma dede da rana d’aya k’aunarta bata tab’a raguwa a zuciyarsa ba instead k’aruwa ma take yi. Baya iya bacci baya iya yin komai cikin nutsuwa idan ba hotonta ya saka a gaba ba yayi ta kalla.’ A ranar yace min ‘Muddin muka barshi aka d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi tou tabbas zai iya rasa ranshi! Dan haka shiyasa yana ganin gara yayi nesa sosai kuma yana rok’ona ko da an d’aura auren to kar In fad’a mishi, ko ya tambayeni kawai ince mishi nima ban sani ba’. Naji matuk’ar tausayin Aslam a wannan lokacin tabbas, ba na so ya zama coward shiyasa na hana shi tafiya na rok’esa Allah da Annabi ya zauna..idan yayi facing ya tabbatar da ta sub’uce mishi forever hakan will make him stronger and zai cire hope yayi moving on. Ya yarda zai zauna bayan ya tabbatar min idan bai mutu a ranar ba to zai iya samun heart attack! Ni kuma na duk’ufa gayawa Ubangiji Ya saka mishi sassauci da dangana sanann ya zab’awa Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu. Tun jiya na hango silver lining. Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d’aurin auren! Idan an d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope! Idan kuma an d’aura da shi to falillahil hamdu.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba “Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to tabbas na san ba k’aramin so yake yi mata ba! Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak’ura! Na san Aslam tun yana Yaro k’arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie? All that I’m trying to point out miki anan shine Hudan ta tafi gidan wanda yake k’aunarta matuk’a! Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi.........” Direct MT estate aka wuce da ita... Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d’in Aslam sai tashin k’amshin turaren wuta yake yi. Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d’akuna ukun akwai gadaje masu kyau! Parlourn ma yana d’auke da duk wani abun buk’ata. Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa. Tun a gate na estate d’in Anty Zainab taji inama bata zo ba! Gashi mata y’an Maiduguri da suka shigo mota d’aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi suna “Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya” ita kuma tanajin kamar ranta zai fita! Sannan kanta ya d’an juye dan cewa aka yi gidanta ita kad’ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!. A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba to ba zata tab’a gaya mata ba! Sun sha yin fad’a da ita Khadijar ba sau d’aya ba akan su Hudan. Ummi da Ummu ne suka ruk’ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta shiga da bismillah da k’afar dama, haka ma k’ofar side d’in Aslam da tazo shiga! Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka. Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah. Bayan an d’an ragu a d’akin Ummu ta k’ara mata da nitsatsiyar nasiha! Basu wani dad’e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma mota kawai aka kai dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa…… Jama’a da friends d’insu in banda santin estate d’in da side d’inta ba abunda suke yi, a haka kowa ya watse. Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d’insu guda biyu da suka zauna dan ragowar cewa suka yi ‘za su wuce saboda basa so su yi dare’….. Da kyar da sid’in goshi Huda ta d’an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina ta yi shiru ta bud’e fuskarta. Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu Istigfari kawai take tayi saboda sam! Tunanin Arshaad yak’i fita daga ranta. Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d’in Mommy. Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d’in suka shigo. Mik’ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa “ta dawo ta zauna Nasiha za su yiwa Ango!”…. Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar daga nan Dad ya mik’e yayi musu sai da safe. Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki. Mommy ce tace “To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana. K’awayenta fa kai suke jira su tafi” Kamar zai yi kuka yace “Mommy siyan baki kuma? Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu, Ina son ganin Arshaad first.” Ya fad’a yana mai mik’ewa zai fita. “Baya nan” Yaji muryar Mommy. Da mamaki ya juyo kafin yace “Ina ya je?” “No body knows” Mommy ta fad’a tana mai mik’ewa ta k’araso inda yake. “Baka farin cikine? Yau?” D’an Satar kallon Gwaggo Asabe yayi yaga hankalinta sam baya kansu…. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Mommy ba wanda ya kaini farin ciki a kaff fad’in duniyar nan a yau! Amman no matter how i tried sam! Na kasa ignoring some facts ne, If I were in Arshaad shoes I would have die by now. Gara ka san abu ba naka bane ba tun farko akan ka saka rai kuma azo baka samuba daga k’arshe.” Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta shafa fuskarshi ta d’anyi murmushi a ranta ta raya ‘Inama ace kowa irin zuciyar Aslam d’inta gareshi, da duniya ta zauna lafiya’…. Muryarsa ce ta katseta jin yana cewa “Bara inje In fara nemansa” “Ka fara zuwa ko kai da Auwal ne ya rakaka ko? Karka janyo mata abun magana mana a wajen k’awayenta” Sunkuyar da kai yayi chaan! Ya d’ago yace “okay” Sarai Mommy ta san ba iya kiran Auwal d’in zai yi ba shiyasa ta yanke shawarar ta kirashi da kanta. Yana d’aki. Shi kad’ai… Ya gwada kiran Arshaad yafi sau nawa amma baya d’auka! K’arshema kashe wayoyinshi yayi dan in ya kira sai dai yaji ance switchoff! Babban abubda yafi damunshi shine rashin sanin inda Arshaad d’in yake… Suna dawowa gidansu ya nufa Aaima ce take fad’a mishi yadda suka yi d’azun dan haka hankalinshi a tashe ya fita nemanshi amman ba inda bai dubaba ya nemeshi ya rasa! Yana a haka kiran Mommy ya shigo wayarsa. Bayan sun gaisa ne tace “Yazo ya raka Aslam wajen Amarya, k’awayenta suna jiransu ba su tafi ba sannan ya d’an taho da snacks da kaji” Da “to” ya amsa ta daga nan suka yi sallama. Ko da suka gama wayar sai da ya kusan minti biyar yana tunani tukunna ya mik’e ya fita…. Kamar Mommy ta sani Aslam yana fita d’akin shi ya nufa ya zauna shi kad’ai yanata tunani.. Chan kuma ya zaro waya ya fara gwada kiran Arshaad amman sai yaji a kashe! Har ga Allah yana son Huda fiye da tunani dan inda ace bai sameta ba to da bai san ya zata kasance da shi ba amman kuma yana matuk’ar jin tausayin Arshaad! Bai san me yake going through ba! A fili yace “Wannan wacce irin k’addara ce? Ya Allah Astaghfirullah.” Ya jima tukun yaji knocking. Izinin shigowa ya bada ba tare da ya san wanene ba. Kallon kallo suka tsaya yi wa juna shi da Auwal bayan ya shigo, chaan kuma Auwal d’in ya k’araso yazo ya zauna kusa da shi. Ko gaisawa ba suyi ba ya fara magana “Yanzu ya za mu yi? Su Abba sun k’ulla abunda zai iya janyo babbar matsala su Mommy su kuma naga kamar they are okay with it! Ko ka san yanzun nan ta kirani wai In taho da kajin Amarya muje in rakaka a yi siyan baki As if ba abunda ya faru. Aslam na san kaima baka son auren nan amma idan kace za kayi shiru ko kuma kace bara ka yiwa su Abba biyayya dan kar su ji ba dad’i to akwai matsala fa! I can’t even begin to tell you yadda Arshaad yake son Huda. You have to speak tun kafin a lalata muku future ku duka ukun. Dubafa yadda kayi fainting amman bayin Allah n nan ba wanda a cikinsu yayi yunk’urin yace a raba auren! Duba kaga Arshaad is no where to be found amma ba wanda ya damu! Ita kanta Huda na san ba zata ganu ba yanzu, Iya event d’insu da bai je ba jiya sai da ta shiga tashin hankali! Ku yi ending abun nan tun kafin ya janyo matsala Aslam kar ka yi shiru ka cuci kanka.” Tun da Auwal ya fara magana Aslam ya kafeshi da idanuwa, sai da ya kai aya sannan ya d’auke idanunsa daga kansa ya mik’e tsaye kafin yace “Like Mommy said! Mu je ayi siyan bakin, a samu a mayar da friends d’inta gida.” Yana gama fad’in haka ya wuce yayi gaba. Jiki a sanyaye haka Auwal ya mik’e ya d’auki ledar da ya shigo da ita ya bi bayanshi yana mamakin firgici, b’acin rai da tsananin tashin hankalin da ya hango a kwayar idanun Aslam d’in. Auwal ne ya kira Sakina… Kamar ba zata d’auka ba sai kuma ta d’aga. Tana d’auka bai jira jin tsiwarta ba yace “Muna parlour, ku fito” Tana ajjiye wayar, ta fad’a musu dan haka suka mik’e suka fita. Yadda al’ada take ake siyan baki haka aka yi.. 500 thousand suka yi demanding Auwal kuma ya basu 1M! Kud’in k’in shiga account d’aya yayi tashi d’aya sai da suka bada account wajen uku tukunna ya juye musu..... K’awayensu kasa hak’uri suka yi sai da d’ayar ta d’an matso k’asa k’asa ta tambayi Sakina “ya akai aka samu chanjen Ango ne?” “Haka al’adar mu take! Muna yin Angon bogi a wasu events d’in” Haka kawai tace musu daga nan ta kauda kai. Tabbas bata gamsu da ita ba amman ganin yadda ta turb’une fuska kuma ta san halinta hakan ya sa kawai ta hak’ura ta koma gefe ta ja bakinta ta yi shiru. Ita kuwa Sakina ba wani abun bane ya sake tunzurata sai d’ayar k’awar tasu wadda ta lura da ita tun da aka fara siyan bakin! In banda rawar kai da shishshigewa Auwal ba abunda ta saka a gaba. Duk da ta lura da yadda yake d’an basar da ita..... Har aka yi siyan bakin aka gama in banda gaisuwa ba abunda ya shiga tsakanin su da Aslam. Ana gamawa ba tare da b’ata lokaci ba dan dare yayi Auwal yace “su taso a maidasu gida” Dan dauriya kawai yake yi amman baya jin dad’i, kamar shi ne Arshaad haka yake jinshi gaba d’aya jikinshi yayi sanyi, kana ganinshi ka san baya jin dad’i duk yayi wani iri gashi kanshi sai faman ciwo yake yi. Ganin ba zai iya kaisu shi kad’ai ba yasa bayan sun fita ya nemi layin drivers d’in estate d’in mutum biyu yace “su zo akwai ragowar mutane su taya shi maida su” Cikin minti k’alilan suka shigo da motocin compound d’in gidan su Aslam su biyu. Tun kafin su gama parking ya bud’e gaban motar shi ya juyo yana kallon Sakina, suna had’a ido yace mata “bismillah” D’auke kai tayi ta kama hannnun Khadija ta fara ja tana cewa “Zo mu je mu shiga wachchar..” Da sauri wannan k’awar tasu tazo ta wuce ta gaban Sakina ta shige gaban motar Auwal d’in inda ya bud’ewa Sakina ta zauna kafin ta juyo tana wani shu’umin murmushi tace mishi “thankyou” Sakina bata san ya aka yi ba kawai ganinta tayi a bakin motar a tsaye! Batare da ta kalleshiba ta bud’e baya ta shiga ta zauna Khadijah ma ganin ta cikata ta nufi motar ya sanya ta biyota itama ta shiga ta zauna ta rufe matar dan tafiyarsu d’aya. Ragowar y’an mata biyun kuma suka shiga motocin drivers d’in. K’amewa Auwal yayi a wajen ya kasa motsi, mamaki fal a ranshi, da kyar bayan ragowar motocin sun fita ya samu ya ja k’afafuwansa ya shiga ya tada motar…… Da gangan ya saita madubin gaban motar daidai fuskarta aikuwa ya ga ta had’e rai kamar an aiko mata da sak’on mutuwa! A take ya ji dariya ta taso masa, anya kuwa abunda yake tunani shi d’in ne? Sakina fa!? Kenan daman ta san tana sonshi amma take ta faman wahalar da shi haka? Woow!! Allah yasa to hakan ne dan in dai kuwa hakan ne da gaske to tabbas sai ya fi ko wanne d’an Adam farin ciki a fad’in duniya….. Haka nan shi kad’ai yana ta sak’e sak’e a ransa sai faman murmushi yake yi shi kad’ai yana driving wanda hakan kuma ba k’aramin tafiya da imanin k’awar tasu wadda ta shigo ta zauna a gaba gefen shi yayi ba. Sakina tana ganinta har wani juyawa tayi tana facing Auwal d’in tana murmushi itama, ji tayi kamar ta shak’o ta! In banda tafarfasa babu abunda zuciyarta take yi tun lokacin da k’awar tasu ta shige motar ta zauna har kawo yanzu.. Numfashinta har wani d’ad’d’aukewa yake yi! Itafa daman tun a school ta tsani Yarinyar nan dan ko ishashshen shiri ma basa yi gata da k’aryar kud’i tun suna school dan duk waya idan ta fito a hannunta ake fara gani (ta yi sneaking ta shigo da ita) Gata da shegen rawar kai da son a sani shiyasa kwata kwata ita Yarinyar bata yi mata ba! Ko inviting d’inta basu yi ba daga ita har Huda amma ba event d’in da bata zo ba! Kalleta ba dangin Iya bare na Baba amman itace har kusan 11 a waje! Ta taho kawo Amaryar da ba wani shiri suke yi ba... Kamar idanuwanta za su fad’o haka ta tak’ark’are take zabgawa Yarinyar harara…. Sarai Auwal yana sane da ita don yana kallonta! Wani farin ciki yake ji kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha. Wai da gaske Sakina kishinsa take yi har haka? Tayay to zai tabbatar? Ya yiwa kansa tanbayar. Wani malalacin murmushi ya saki ta gefen bakinshi… A hankali ya juyo ya kalli k’awar tasu wadda ita ma shi d’in take kallo, tun ranar cocktail ya tafi da imaninta, jiya har mafarkinshi ta yi! Yau kuwa ba zata bari ya sub’uce mata ba in sha Allah… Murmushi ya sakar mata ganin itama shi d’in take kallo, a hankali but yadda ya san Sakina za ta ji yace “Hey dear beautiful, where to?” Da sauri ta koma baya ta jingina da jikin kujera jin zuciyarta zata faso waje. Wani sanyi Auwal yake ji yana ratsa shi dan yana kallonta duk ta cikin glass, he won’t lie this is the

Chapter 2 of 26