ta sameta,
cikin son fahimtar da ita ta shiga yi mata nuni da yadda Abba yake ta faman zirya….
A hankali Mama ta yi murmushi kafin tace
“Hajiya ni fa dama na gama yanke shawarar ba zan koma gidan Abba ba”
Da mamamki Shuwa take kallonta.
A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Jin ku kawai nake yi Hajiya,
amman yanzu tashi d’aya in na koma cewa za ai kamar Ina jira matarshi ta mutu ne.
Sanann ko bayaga hakama
na riga na gama deciding in dai ba Mahaifinsa bane ya amince da ni to ba zan tab’a komawa ba, ina so Mahaifinsa ya nema mishi aurena kamar yadda ko wanne uba yake yi wa d’ansa
sannan ya yi welcoming d’ina cikin zuri’arshi, ya karb’eni
a matsayin surukarshi kamar yadda ko wanne uban Miji yake yi wa matar d’ansa...
....na san hakan ba zata tab’a kasancewaba
ni kuma In ba hakan yayi ba to ba zan koma ba!
Kinga kuwa babu batun maida auren mu ni da Abba dan na san Mahaifinsa ba zai tab’a amincewa ba
sannan ba zai yi waennan abubuwan da nake kwad’ayin inga yayi min ba.
Shuwa za tayi magana Mama tayi saurin d’aura hannunta a kan bakinta
ta ce ‘dan Allah ta yi shiru, a bar maganar’
Saboda
ita kanta daurewa kawai take yi.
CONTINUATION!.
Driving Aslam yake yi cikin nutsuwa, har suka isa MT estate ba wanda yace k’ala!
Dan kowa akwai abunda yake tunani…
A cikin gidan Granpa ya yi parking, da sauri driver d’inshi ya k’araso ya bud’e mishi motar ya fito cikin kamala
suka nufi cikin gidan direct.
Ba kowa as usual,
har chan sama suka wuce tare..
A hankali Granpa ya d’an kalleshi ya ce “ka fad’awa su Yusuf Ina buk’atar ganin kowa da kowa anan after isha”
“Okay Granpa” Aslam d’in yace daga nan Granpa ya nufi personal parlourn shi wanda zai sadashi da bedroom d’insa.
Da mugun sauri Aslam wanda yake ta faman kame kame ya na rarraba ido ya fad’a d’akin Gramma.....
A zaune ya tadda su suna hira su biyu.
Da sauri duk suka d’ago suna kallon k’ofar ganin yadda ya afko.
Dariya Gramma ta yi kafin tace
“K’araso mana”
Sannan ta mik’e tace
“Granpa ya dawo ko?
Arshaad yace tare kuka fita”
“Eh yana d’akinsa” ya bata amsa sannan yad’an russuna ya gaida ta cike da ladabi.
Sai da ta k’arasa bakin k’ofar tukunna ta d’ago kansa ta amsa sannan tace
“Sannu da zuwa,
ya hanya?”
A hankali yace “Alhamdulillah”
Yana d’an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta.
Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k’ofar dan ta lura idan ta ci gaba da zama a d’akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta.
A hankali ya ke takawa har ya k’arasa inda take ya tsugunna a gabanta.
Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k’ok’arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza samunsu.
A hankali ya kamo hab’arta ya d’ago da fuskarta
yana kallon yadda ta runtse idon da k’arfi!.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I miss you..
Sosai!!!”
Bata bud’e ba kuma bata yi magana ba,
tana nan a yadda take.
A hankali ya fesar da numfashi yace
“Ko you still need more time?”
Sai a lokacin ta bud’e idanunta da suka d’an tara hawaye tace
“Moree time for?”
Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace
“Us!
More time for us..
ranakun da na baki sun yi miki kad’an ko?.
I was so eager to see you
amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba”
A hankali yana kallonta yace “ko arzik’in sannu da zuwa ma ban samu ba.
Ya fad’i hakan yana d’an cika hab’arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta.
Da sauri ta yi k’asa da kanta tana jin yadda k’irjinta yake dukan uku uku.
A hankali ta ji ya ce “Umm??”
Cikin wani kalar yanayi da siga.
Sai da ta sake yin k’asa da kanta tukunna tace
“Ina wuni, ya hanya? Ya aiki?”
Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace
“Lafiya,
hanya Alhamdulillah
Aiki kuma, was terrible!
Na d’an samu matsala
har ya kai ga an rufe company d’ina na chan.”
Da sauri ta d’ago ta kalleshi
kafin tace “Subhanallah.
Garin yaya?”
Ya ji dad’in yadda ta damu da alamarin ba kad’an ba. A hankali ya d’anyi murmushi
cikin son kawar da zancen company d’in yace
“Don’t worry,
ba komai.
Ai inada wani ni da Abba..
Daman bawa ya kan samu abu
at any time kuma ya kan rasa,
wannan yana daga cikin k’addarar bawa,
fata kawai shine ya zamo mai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau”
A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace
“wata biyu baya!,
Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki!
Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu,
Amma yanzu ace dan na rasa company sai in damu?”
Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi.
A hankali k’irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d’ago tana kallonshi.
Har yanzu murmushi yake mata.
Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa!
Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k’arshen bagwaren relationship d’in nasu
a hankali tace
“Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta.
Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d’inta, sai da
yaga ta fara kuka tukunna yad’an dawo dede sannan ya fahimceta!
Dariya ma shi ta basa
dan haka a hankali yayi y’ar dariya kafin yad’an matse hannunta wanda yake a cikin nashi yace
“In ya fad’i hakan, sai yaya?”
Da sauri ta d’ago tana kallon yadda yake mata wani murmushi mai tsada!
Cikin zubar hawaye tace
“Masoya ma wasu in sun lura zaman su tare zai na causing problem hak’ura suke yi da juna, ballantana kuma mu.
Tun kafin abu yayi nisa
azo tun Granpa yana magana shi kad’ai har kowa ya fara gara kawai mu rabu da juna Ya Aslam ka samu wadda kake so ka aura
nima in........”
Da sauri ya d’aura d’ayan hannunshi akan lips d’inta yace “shhh…”
Bai jira jan lokaci ba
yace
“Ni already na samu wadda nake so
Hudatie
bana jin kuma zan sake son wata a gaba sai dai wani ikon Allahn.
Tunda Allah ya bani ke ya gama mini komai.”
A hankali ya cire hannunsa a lips d’inta ya yi cupping fuskarta a cikin palms d’insa biyu ya d’ago da kan da take ta k’ok’arin b’oyewa
yace “open your eyes”.
Gam!! Haka ta sake runtse idanuwan nata
k’irjinta na dukan uku uku da wani kalar mahaukacin sauri.
Cikin matso da fuskarsa daff da tata ta ji yace
“Open your eyes before i kiss you!”
Da sauri ta ware idanuwan nata tarr! Ta zuba su a cikin nasa…..
Kallonta yake yi itanma shi take kallo ta ji yace
“I love you”
Da sauri ta runtse idanunta sai kuma hawaye sharr! Kamar an bud’e fanfo..
A hankali cikin kuka still yana rik’e da face d’inta tace
“Ya Aslam dan Allah kar ka yi haka. Za aga kamar daman chan muna son juna.
Za a ganmu kamar butulu.
Ba sona kake yi ba,
idan muka rabu ka had’u da true love d’inka zaka fahimci hakan. For now dan Allah let’s just end this relationship............”
Muryartace ta mak’ale sakamokon had’e bakinsu da yayi waje d’aya!….
Wani Irin salo ya shiga aika mata da shi wanda ya kusan tarwatse kwakwalwarta.
Sai da ya ji tana shirin sume masa tukunna ya janye a hankali ya bud’e rinannun idanuwanshi, yana maida numfashi, a hankali yace
“Those this feel fake?”
Fashewa tayi da kuka ta fara k’ok’arin kwace fuskarta amman yak’i bata dama
Instead ma kawai sai ya janyo ta izuwa jikinshi yayi hugging d’inta ya shiga shafa bayanta alamun rarrashi
yayinda zuciyoyinsu suke bugawa a tare da mugun k’arfi......
Jin yanda take kuka sannan ta ma k’i ta saurareshi
yasa ya cikata a hankali yace “ki gayawa su Shuraim
Granpa yana son ganin kowa
after sallar isha.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan yaga kamar tana buk’atar fitar tasa......
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
67
Mikiya Writers Association.
Tunda Baba Bashir ya shiga gida yake ta faman kai kawo,
ba wai tunani yake akan wa Mama zata aura tsakanin Baba da Abba ba
a’a
tunani yake yi ta yadda zai fahimtar da Baaba Talatu
dan already ya gama deciding
tunda dama Mama tace ‘saboda Granpa yasa ba zata koma ba’ Gashi kuma yanzu Granpa d’in ya zo da kansa
to kuwa in sha Allah ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga an d’aura auren Mama da Abba.
Kawai shi yanzu damuwar shi Baaba Talatu ce dan ko
jiya da kyar tayi bacci!
Halin da Baba yake ciki ya tada mata hankali ba kad’an ba
so take kawai taga farin cikin shi ta ko wacce hanya
tsananin tausayinsa take yi.
Ya dad’e yana nazari kafin ya d’au hanyar d’akin da Baba yake jinya dan yana ganin gara su fara maganar da shi tukunna.
Yana zuwa ya d’aga hannu kenan zai tura k’ofar ya ji suna magana shi da Ya Jamilu..........
MT ESTATE.
Kamar yadda Granpa ya buk’ata,
ana fitowa a masallaci su Abba suka bi bayanshi
zuwa gidansa..
A nan parlourn suka tarar da Mommy Mammy Gramma Huda da Aaima.
Ko ciki bai shiga ba ya nemi waje ya zauna a kan cousion ya fara bin ahalin nashi da kallo one by one waenda suke nan jere a gabanshi wasu a kan kujera wasu a kan kafet.
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kalla Aslam yace ‘ya bud’e taro da addua’.
Cikin nutsuwa ya jagoranci adduar suka yi suka shafa tukunna Granpa ya gyara zama yace
“Abubuwa uku! Zuwa hud’u ne suka sanya na taraku a nan.
Na farko
Aisha,
Kafin Zainab ta cika ta rok’eni akan in tayata neman yafiya da gafarar ki!
Sannan nima in nema yafiyarki
dan tabbas an zalinceki a baya,
da fatan za ki yafe mana.”
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e
a hankali tace
“Komai ya wuce.
Na yafe na manta da komai
Allah Ubangiji ya ji k’an Zainab ya sa tana aljanna Firdausi.
Ahankali duk suka ce “Ameen”.
Sai da Granpa yad’an lumshe idonshi ya bud’e
tukunna ya kalla setin da Abba da Daddy suke yace
“Yusuf, Yakubu,
kuna iya dawowa estate anytime from now.
Komai ya wuce.”
A hankali Dad wanda tunda suka zauna yake ta k’ok’arin ganin bai bari kwallarshi ta zubo ba ya sa hannu ya goge hawayen da suka samu nasarar zubo masa.
Ahankali kamar had’in baki su duka ukun suka ce
“Alhamdulillah”
A fili, kafin Daddy ya ce “mun gode Granpa
Ka yi hak’uri ka yafe mana.”
D’an guntun murmushi yayi kafin yace
“Ni za ku yafewa
Ina neman.....”
Da sauri Abba ya katseshi ta hanyar cewa
“Dan Allah kar ka rok’emu yafiyar komai,
kai Mahaifinmu ne kuma
d’an Adam ajizi ne,
kasancewarka Mahaifin mu ya sanya tun kafin ka yi mana wani abun ma mun riga da mun yafe maka!
A Yanzu ba abunda muka fi buk’ata kamar yafiya da albarkar ka saboda tabbas na san mun kwashi zunubi ata dalilin k’ok’arin mu na ganin mun nuna maka daidai.
Ka yi hak’uri Daddie a ko da yaushe zan baka hak’uri ne in yi ta baka hak’uri har k’arshen rayuwata”
Ya k’arashe maganar hawaye suna tsilalo masa.
Mik’ewa Granpa yayi ya k’arasa inda yake ya kamo hannunshi ya mik’ar da shi tsaye sanann yace
“Magana ta uku,
na amince maka ka auri Maryam!
Na yi accepting d’inta
sannan ina yi maka albishir d’in d’azu mun je ni da Aslam na nema maka aurenta da kaina kuma an baka!
Ka zab’i gida d’aya a cikin gidajen estate d’innan ko wanne yayi maka
ka gyara mata
dan iyayenta sun ce anytime from now za su nemeni akan batun d’aurin auren.
Sannan Aslam shima ya zab’i d’aya su zauna shi da matarsa Huda!
Allah yayi muku albarka.”
K’ok’ari Abba yake ya rik’e kukan da ya taho mishi
amman sam ya gagara!
Dan haka kawai ya rungume Granpa a jikinshi ya sa kuka kamar wani Yaro.
A hankali Granpa yake murmushi mai had’e da dariya
kafin yace
“So kake ka k’arasa ni ne, Abbana.”
Wannan karon hatta Gramma sai da ta sa kuka…..
A tsakaninsu
Abba Dad Mommy Daddy Gramma sam aka kasa samun wanda zai lallashi wani.
A hankali Daddy shima ya taso yazo ya rungume su su biyun duka, haka shima Dad yana hawaye yace “ba za ayi babu ni ba”
Ya k’araso shima yayi joining hug d’in yana dariya.
Gramma ce ta ce
“Kar fa ku kadashi k’asa”
Tukunna suka cikashi suna murmushi, Dad ya ja mishi k’aramar kujera mara nauyi ta study ya zauna akai,
tukunna suma suka zauna.
Sai da parlourn yad’an yi shiru
tukunna
Granpa ya ci gaba da magana
“I was wrong!
Duk tsahon wannan lokacin ina kan ba dai dai ba
Allah ya ji k’an Zainab
Ita ta fara nasarar nuna min gaskiya sanann bayan dogon nazarin da nayi na fahimceta.”
Shiruu, ya d’anyi kafin ya cigaba da magana
“Na san dukkan nin ku anan kun san yadda nake jin Zainab a raina, ba abunda yake d’aga min hankali irin in na tuna she was killed!
Sanann by an insider.”
Tsit!! Parlourn ya d’auka ko k’arar numfashi bakaji.
Kafin Granpa ya ci gaba da magana
“Tun ranar da ta rasu nayi alk’awarin sai na yi punishing killer d’in no mattaer how smart he or she thinks they are! Dole zan yi bincike in nemo su kuma zan hukuntasu
dan ba zan yarda jinin Ummi ya tafi a banza ba.
30 days guda aka yi ana binciken caterers da waiters d’in da suka yi serving da girkin abincin birthday
and an gano basu da hannu a ciki, sannan an binciki masu gadi kuma an bincika akan
ko sun ga wani abun
shima bamu samu komai ba
shiyasa nace muku its an incider!
Therefore bincike zai fara daga yau yanzun nan!
Ku yi hak’uri amman dole kowa ya amsa tambaya sannan ayi investigating d’inshi including me.
Daga nan banaso inga k’afar kowa a mansion d’in chan inda incidence d’in ya afku
har sai an gama komai..
Menwhile, Aslam”
Granpa ya kira sunan Aslam yana kallon sa.
A hankali ya d’ago idanuwanshi ya kalle
shi sannan yace
“Naaam Granpa”
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Ka je first building by your left
akwai bak’i a parlourn k’asa,
ka taho da su nan.”
A hankali cikin girmamawa Aslam d’in ya mik’e
ya fice…
Ba a yi 20 minutes ba suka shigo shi da wasu maza
su biyar!!
……..Da kyar suka had’iye yawun da ya tokare musu mak’oshi,
In banda “innalillahi wa innailaihirrajiun” ba abunda suke maimaitawa a tare!…….
Gaisawa bak’in suka yi da Granpa kafin yace
“Bismillah,
you can start.”
Ta kan Granpa suka fara…
Tambayoyine suka yi masa
akan relationship d’inshi da marigayiya sannan when last ya ganta?
Akwai misunderstanding d’in da ya tab’a had’asu?
Akwai wani secret ko
magana da ta tab’a gaya masa?
Ta tab’a gaya mishi sun yi fad’a da wani ko wata a cikin estate d’in? d.d.s……….
Daga nan
suka d’auko wani abu kamar na tomb print amman babba
suka ce “ya d’aura hannusa akai duka gaba d’aya biyun”
Hakan yayi, sai da hoton palm da yatsunsa suka fito a kan fuskar computer da suka jona a jiki tukunna sukayi gaba.
Gramma ce next suna gamawa da ita sai Daddy sai Dad sai Aslam, Sudais Shuraim Arshaad Aaima tukunna
Mammy sai ta kusan kuka
dan yana yin yadda suke tambayar tasu ko kana da gaskiya sai ka rikice
kafin wani ya rufe baki wani ya jeho maka wata…
Da akazo kan tambayar ‘ta tab’a fad’a mata sun yi fad’a da wani?’
A take ta hau zuba tana bada labarin yadda Abba baya sonta sannan ta tab’a ce mata sun yi fad’a da huda!
Yana yin maganar tata yasa kawai d’ayan ya tsayar da ita ya d’anyi y’an rubuce rubuce akan takardar ta
yace “shikenan. Ta d’aura hannayenta”.
Successful suka yi suka gama da Abba da Huda
sannan d’ayan ya kunna computer ya ajjiye a gabansu,
ga mamakinsu sukaga Mom da Auwal suma ana yi musu nasu binciken exactly kamar yadda akayi musu.
Ana gamawa suka yiwa Granpa sallama suka fice.
Suna fita tun kafin Granpa ya fara magana Arshaad ya kalli Granpa d’in yace
‘Please idan an gama yana so zai wuce,
Yanada aiyyyuka da ya tara da yawa.’
Sai da Granpa yad’an yi shiru
tukunna yace
“Ok,
you can go.”
Yana fita aka yi addua aka watse kowa ya kama gabanshi…..
A hankali Granpa ya tura k’ofar d’akin Gramma ya shiga,
yana lura da ita tun d’azu
kamar jikin ya motsa dan bata da lafiya dama gashi
ta hanashi ya fad’awa kowa.
Yana shiga da Hudan ya fara tozali tana daddanawa Gramma d’in k’afa
dan zuwa yanzu kam ta gagara b’oye mata ciwon nata.
Hudan tana ganinshi ta sauk’e k’afar Gramma dake a kan cinyarta sannan ta mik’e ta d’an russunar da kanta ta wuce ta fita.
Sai da ya ga fitarta tukunna ya juyo ya fara takawa inda Gramma take nan kwance akan gadon ya zauna a inda Hudan ta tashi ya d’auki k’afafun nata ya d’aura akan cinyarsa!
Tana k’ok’arin mik’ewa ya ce mata
“Stay still”.
A hankali ya shiga matsa mata kamar yadda yaga Hudan tanayi……
Sun d’an jima a haka kafin chan yace
“K’afar dai?
Ba kya feeling kwata kwata?”
A hankali tace
“Ina ji, ba kamar d’azu ba.
Da k’afafuna na fita meeting na shigo nan fa d’azu”
Ta fad’a tana d’an murmushi alamun so take ya bar maganar.
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Maijidda, ko wanne family fa suna da nasu issues d’in!
Ba a kan mu farau ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki.
Kin dai ga yadda d’azu jinin ki ya hau da muka gwada a d’akina, gashi har ba kya feeling side d’in jikinki!
Kar kije ki samu stroke fa,
ki yi hkr ki rungumi k’addara
komai zai dawo normal.”
A hankali ta mik’e ta zauna sannan ta sauk’e k’afafuwan nata k’asa
kafin tace
“Daddie dole in damu.
Ace wai
a cikin zuriata an samu killer!
Taya kake so in kwantar da hankalina?
Bayan ban san k’arshen wannan musibar ba…
Suma fa y’ay’a za su haifa
kuma mugun hali da bak’ar zuciya jini yake bi, sannan Ina
tsoron idan zance ya fito
kar zuriar Ummi suma su zuciya su yi tunanin d’aukar fansa bayan sun girma
duk da kuwa ba Mahaifiyar tasu aka so a kashe ba.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta cigaba da cewa
“Daddie dan Allah idan result ya fito, aka kawo
muka ga wanda muke zxargi d’inne
Dan Allah karka baiyyana sunanshi a gaban kowa
dan Allah.”
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
“That! I cant promise you Maijidda.
Saboda dole In cire rotten seed a cikin family d’ina…
An yi masa laifi
tabbas amman hakan ba zai sa In hak’ura in bar killer d’in Ummi ya tafi free ba!
I’m sorry amman inaso kar ma ki sake yi min maganar nan dan Allah, saboda itace alfarmar ta biyu da na ce miki daman ba zan iya yi miki ba
bayan mallakawa mutum d’aya a cikin su MT.”
A hankali Gramma ta sa hannu ta share hawayenta…
Ajiyar zuciya ya sauk’e sanann ya d’an matsa ya rungumota izuwa jikinsa ya shiga lallashinta da kwantar mata da hankali.
Sai da yaga ta d’an dawo dede
tukunna yace “Yarinyar nan har yau tana nan?
It’s like a nan take dan tare nake ganinku”
Murmushi Gramma ta d’an yi kafin tace
“Ai har nan surukarta ta zo sata tafi da ita amma tayi ta kuka.
Ranar ina jinta tana waya
kamar da y’ar uwarta ne na wajen Maman ta
wai ‘In ta biyewa Aslam suka shantake da juna mutane za su ga kamar daman chan tana sonshi!’
Wai ‘za ayi mata kallon butulu’.
Murmushi Gramma ta sake yi kafin taci gaba
“Ni wallahi dariya ma ta bani”.
Girgiza kai Granpa yayi kafin yace “Dariya ko abun haushi?
Wanann ai shirme ne!
Ita zata ke maida hannun agogo baya.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e yace
“Zan yiwa Aslam magana ya zab’i gida zuwa gobe ya zo ya d’au keys, da sassafe
ki shiryata ki kaita gidanta
in yaso aa gyara a yi mata jeren suna ciki.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, da alamun ransa shima duk a dagule yake.”
Ajiyar zuciya Gramma ta sauk’e kafin ta mik’e ta d’auki wayarta ta danna kiran Mommy...
Washegari da safe,
kamar yadda Granpa ya buk’aci Aslam yazo ya karb’a keys haka aka yi…
Yana zuwa bayan sun gaisa ya cewa Granpa d’in ‘kawai ya zab’a mishi duk wanda yake ganin yayi
Ya gode Allah ya k’ara arzik’i.’
Murmushi Granpa yayi yace “okay”
Sannan ya mik’e ya shiga ciki.
Makullin d’aya daga cikin gidanjen da ba’a tab’a bud’ewa ba ma ya d’auka ya fito.
Ya na fitowa ya gaya mishi gidan da number ya mik’a mishi.
Karb’a Aslam d’in yayi
ya sake yin godiya,
yana shirin mik’ewa Granpa d’in yace
“Ku yi sauk’a.
Gidan sabo ne, ba a tab’a shiga ba.
Sannan yanzun nan Gramma za ta kawo maka matarka
In yaso sai a gyara gidan tana ciki kawai ayi furnishing.”
A hankali Aslam yad’an russunar da kai yace “na gode”Sannan ya mik’e ya fita.
Da murmushi Granpa yake kallonshi har ya b’acewa ganinsa. Ya so bashi dariya yadda yaga kamar ma yau d’in kunyar sa yake ji, zai so
ya ganshi tare da Abba yau d’in yaga ya zai yi….
K’arar wayarsa ce ta katse masa tunani.
Ganin number yasa ya d’aga ya kara a kunnenshi ya yi shiru.
“Assalama alaikom”
Baba Bashir yace.
Ba tare da ya fahimci waye ba
yace
“Ameen
Wa alaikummussalam”
Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e kafin yace
“Kaka ne. Daga b’angaren Maryam Madu, yanzu
Arshaad yayi min texting numberka”
“Okay, okay”
Granpa yace yana gyara zama
kafin yace
“Ya iyali?”
“Alhamdulillah” Kaka yace
sannan ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Na kira ka ne domin in sanar da kai cewa
a duk lokacin da kuka shirya kuna iya zuwa a d’aura aure.”
Sai da Granpa ya lumshe idanuwanshi ya bud’e
tukunna yace
“Weekend Saturday!
Rana ita yau, in sha Allah za mu shirya komai…mu zo.“
“Okay Na gode” Baba Bashir yace.
Murmushi Granpa yayi yace
“Mune da godiya, sai mun
had’u”
Daga nan suka yi sallama suka tsinke kiran.
Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e.
Yana ajjiye wayar ya juya da niyyar fita su ka yi kicib’is da Baaba Talatu!
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara k’ok’arin wuceta domin ya fita.
Da sauri ta tareshi ta hanyar shiga gabanshi, ta
fara hawaye sannan tace
“Mai yasa za ka yi haka?
D’an shekara d’ayan da zai yi da mu shi kake neman maidawa sati d’aya?
Dan na tabbatar muddin aka d’aura auren Maryam a gaban idonshi to tabbas a ranar zai cika!.
Ka barsu mana, ita kanta Maryam d’in ta amince
ta tausayi masa..
Nan da shekara d’aya ma fa ba zaka sake ganin Usman a doran k’asa ba.”
Sai da Kaka ya runtse idanuwanshi tukunna ya bud’e yace “Ke mahaifiyarsa ce,
ki daina yi masa baki haka
Usman ba inda zai je in sha Allah..
Bari kiji in gaya miki
d’azu na je akan In fahimtar da shi ya hak’ura kawai
tunda har ga Granpa ya zo da kanshi, ina zuwa k’ofar d’akin nasa
kin san me na ji suna tattaunawa?”
Cikin share hawaye Baaba Talatu tace
“Amman dai ko meye ne ka ji ai a ganina bai shafi..”
Cikin d’an fad’a fad’a yace
“Ki amsani kawai!
Kin san me na ji suna tattaunawa?”
A hankali ta girgiza kanta
alamun
‘A’a’
Sai da Kaka ya had’iye wani k’ululun takaici
kafin yace
“Akan maganar k’aryar takardun da suka yi na ji suna magana!
For your information
Usman garr!! Ya ke
babu mutuwar da zai yi in sha Allah. So yake kawai Maryam ta koma gidansa
ya cigaba da azabar da ita.
Wallahi Talatu kunyar Yarinyar nan nake ji. Ban tab’a b’oyewa Madu wani abu ba
amman tabbas zan b’oye masa wannan maganar
idan shekara ta zagayo aka ga Usman bai mutuba mu ce
Ikon Allah ne!
Dan ban san ta ina zan fara ce masa
Usman da Jamilu sun yi k’aryar ciwo da mutuwa a Usman d’in
dan kawai su yaudaremu ya aure masa y’a ya ci gaba da azabtar da ita, ba.
Ki dubafa ki gani
tsabar ya san bai kyauta ba
ya ma kasa fitowa a mutum yayi bikon ta dan bai san ta Ina zai fara ba!
Sai da ya had’a da k’aryar ciwon mutuwa..
Wanne irin deceiver ne wannan Yaron????
Kiga fa duk abunda ya yiwa Maryam amma tashi
d’aya ta hak’ura ta ji tausayinshi zata koma ta yi jinyar sa har ya koma ga mahalliccinsa
alhalin shi yana nan yanata yaudarar ta da mu kanmu..”
Cikin katseshi Baaba Talatu tace
“Ai dan ba ka san ya muka yi da Maryam d’in bane, ba ka
san ya akai ta yarda ba!
Ba ka san me na ce mata tukunna ta yarda ba.....”
Cikin tsananin b’acin rai
ya d’aga mata hannu ya ce
“Talatu!!!!”
Jin yadda ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 26