Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana haki kamar wanda yayi race. Hararar ta yayi ya b’ata rai tukunnan yace “ba thank you sai dariya ko?” A hankali tace “thank you” Sai da ya gama hutawa tukunna ya tashi ya d’auko rigar ya cire a leda ya ware ta ya kama hannunta ya mik’ar…. Da sauri tace “Ya Aslam kai fa kai kad’ai ka shirya” “Bari tou In cire nima sai ki tayani, ko?” Yayi mata tambayar yana k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinsa. Da sauri ta rik’e hannunsa tana turo baki sannan ta sunkuyar da kanta k’asa….. Zip d’in rigar har kusan chan k’asa ne dan haka ya zuge shi duka tukunna ya kawo ta wajen kanta ya zura mata sannan ya saki rigar. Ganin yana k’ok’arin sa hannu ya kwance mata bathrobe d’in ta ciki yasa tayi sauri ta matsa ta kwance ta zame hannuwan kafin tayi k’asa da ita duka sannan ta jaa hannun rigar ta saka threequater hannun ta fara k’ok’arin zuge zip d’in…. Ganin bazata iya ba ya sa duk turjewarta haka ta tsaya ya ja mata….. Kwalliyarma da kyar ya barta ta shafa powder ta saka mascara da eye liner amman y’ankunne bracelet anklet takalmi da red lipstic duk shine ya saka mata! Tayi kyau kuwa sosai…, A hankali ya ajjiye lipstic d’in yana kallonta…. Ganin kallon yayi yawa ya sa ta wuce taje ta d’au ribbom d’inta ta yi parkin, ta d’auko wani tauban cap na chantily mai stones red ta saka ta d’auko vail black medium ta rufa a kafad’a……. Aslam, gaba d’aya jikinsa yayi sanyi dan Huda ba k’aramin tafiya tayi da imaninsa ba..duk inda tayi kawai binta yake yi da idanu. A hankali ya d’au wayarsa ya k’arasa inda take ya jaa hannunta suka nufi gaban dressing mirrow suka tsaya… Ta tsaya a gabanshi shi kuma a baya ya rik’e waist d’inta yayi musu hoto. Sun yi kyau kuwa ba kad’an ba kuma sun fito sosai. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya gyara mata mayafin nata ta hanyar maidashi saman kanta kafin yace “Can we talk?” ya fad’a hakan yana me juyo da ita suka yi facing juna kafin ya d’aura hannayensa a kan kafad’unta ya fara magana “Next week, in shaa Allah inaso mu wuce UK! Mun riga mun gama magana da su Abba tun last 2 weeks jiya kuma har su Ummi na gayawa a wajen dinner, yanzu ke kad’ai ya rage baki sani ba. Za ki bini?” Ya k’arashe maganar a hankali. “Um um” Tace tana mai ja da baya ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace “Mai yasa za mu tafi? Me su Ummin suka ce?” Sai da ya lumshe idanuwanshi ya bud’e kafin yace “Arshaad is morethan comfortable! Infact da farko shi ne ma daa zai tafi saboda yace zaman mu under same roof ba zai yiu ba, sai da na yi masa bayani d’azu akan already daman akwai plan d’in tafiyar ta mu tukunna shi ya yarda zai zauna a nan.” Sai da ta gama jin bayanin nasa tukunna tace “Nifa ba saboda Ya Arshaad bane nace A’a ba.” A hankali yace “mai yasa to ba zaki bini ba?” Cikin tarar numfashinsa tace “Ya Aslam kamata fa yayi mu yi focusing akan yadda zamu warware wannan auren! Kar mu bawa su Abba false hope d’in wata rana za mu so juna..” Ta k’arashe maganar tana jin wani nauyi yana sauk’a daga zuciyarta. Janyo ta kawai taji yayi yai huggging d’inta… Sun d’an jima a haka kafin a hankali yace “Za mu tafi UK next week It’s an order” Shiruu, tayi tana mamakin yadda k’irjinsa yake bugawa da kuma yadda gaba d’aya jikinsa yake karkarwa, gashin sai sake rik’eta yake yi da kyau kamar wanda akace za’a kwace ta. So take ta motsa ta gaya mishi itafa ba inda zata je amman kuma kamar wadda aka rufe waa baki, kwata kwata sai ta kasa. Sun jima a haka suka ji ana knocking...... Mommy, tunda tazo take baza ido, so take kawai taga ta Ina za su fito.. Duk da Aslam yana zuwa kullum wajen ta idan ya tashi a office wani lokacin ma kafin ya fita sai ya je amman so take yi kawai ta gansu especially Hudan… Hak’urinta ne ya k’are dan haka ta cewa Ummi “ta je ta kira mata su, da wurwuri take son tafiya su fito su gaisa kafin ta tafi.” Dariya Daddy yayi yace “A’a Mommy ki dai fad’i gaskiya…y’ay’anki kawai kike son gani. Tun d’azu fa nake ganin ki kinata zullo kina lek’en ta Ina za su fito” Ai kuwa gaba d’aya aka saka dariya banda Mammy da Mom Arshaad kam murmushi kawai yayi. Mik’ewa Ummi tayi zata wuce dai dai nan su Shuraim suka sauk’o… Suite d’insu milk masu asalin tsada sai belt da takalmi brown. Ba k’aramin kyau suka yi ba. Wajenta suka fara zuwa suka yi hugging d’inta! Bata san daliliba kawai sai taji hawaye ya zubo mata. A hankali ta dafa kawunan su ta ce “Allah ya yi muku albarka” Daga nan tayi saurin wucewa dan bataso tayi kuka. Nan suka k’arasa inda Dad Mommy Abba Arshaad Mammy Mom da Daddy suke.. Aka fara hotuna bayan an yi wishing d’insu Happy Birthday kowa ya basu gifts d’in da ya shirya musu. Knocking kawai Ummi tayi ta juya dan ta raba kanta da shiga d’akinsu Aslam ita kam...... Bata yi minti d’aya da zama ba suka fito.. Kowa a parlourn zuba musu ido kawai yayi, ba k’aramin kyau da dacewa da juna suka yi ba. Kallo d’aya Arshaad yayi musu ya d’auke kai da sauri Mammy kam tana ganin fitowarsu ta juya kan ma gaba d’aya ta sake tamke fuska. Ba yadda Hudan bata yi da shi akan ya saki mata hannu ba amman fur!! Ya k’i. Haka nan duk sai taji kunya ta lullub’eta especially da suka had’a ido da Mommy wadda take ta zuba murmushi kamar an mata albishir da gidan aljannah… Suna k’arasowa ta mik’e ta kamo hannun Hudan ta fara k’ok’arin janta dan ta zaunar da ita a gefenta. D’agowa tayi suka had’a ido da Aslam! Sai da ta d’anyi dariya tukunna tace “Cikata mana, ko?” Shima kuma sai yaji kunyar Abba da su Dad ta rufeshi dan haka a hankali ya cikata ta zaunar da ita itama ta zauna Aslam ya zauna a gefnta Tun kafin ta fad’a Shuraim ya shiga yi musu hotuna… Abba da Dadddy da Dad ma suka shiga, haka ma Ummi. Ranar dai anshan hotuna kala kala bibbiyu uku uku, daga nan su Shuraim suka fita saboda friends d’insu duk suna waje. Sai wajen 9 su Sakina suka zo, murna a wajen Hudan ba a magana. Suna gama gaisawa da su Abba suka fita compound suka nemi waje suka zauna. Basu dad’e da zama ba aka fara gudanar da program of event. Suna cikin hira su biyu dan Sumayya har ta yi k’awa wata Khairat sun ja gefe anata iyayi da manyance, suka ji an jawo kujera an jona da table d’insu an zauna a gefen su. Tana d’agowa suka had’a ido a take gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa! So take ta cire idanunta a nashi amman ta kasa….. “You came.” Yace yana mai kallon cikin idonta. A hankali tace “Yes” Sai kuma ta mik’e da sauri tace “Hudan muje ki rakani bathroom” Tana mik’ewa ta yi gaba….. Da sauri ya kalli Hudan yace mata “A minute please” Sannan ya mik’e ya bi bayan Sakina wadda tayi hanyar falon su Hudan da sauri. Kwarewa Mammy ta yi, da sauri ta kamo hannun Mom! Tana juyowa ta nuna mata su, tace “Kinga Auwal da Cousin d’in Huda wadda suka zo d’azu Hudan take ta murna d’innan.” Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yadda Auwal yake kiranta yana d’an gudu amman ko alamun zata juyo ma bata yi ba... Tana shiga shima yana shiga! Sai a lokacin ta lura da Huda bata biyo su ba. Da sauri ta had’e hannuwanta biyu waje guda alamun rok’o, tace “Dan girman Allah Ya Auwal ka rabu da ni! Ka fita a harka ta. Me kake so in yi maka? An saka ranar aurena! Nan da 5 month in sha Allah Ina gidan wani me kuma zaka ce min yanzun me kake buk’ata a....” Maganarta ce ta katse sakamokon hawayen da ta ga sun tsinke masa lokaci guda kamar fanfo sai kace wani k’aramin Yaro. A hankali ya durk’usa a gabanta ya had’e hannuwanshi duka biyu shima, yace “Sakina dan girman Allah ki san yadda za kiyi da ni! Wallahi ban san halinda nake ciki ba, ba laifina bane ba, na san na takura ki da yawa amman ba laifina bane ya kamata ki gane. Ya kike so in yi? Wallahi na yi na yi In cire ki a raina amman kullum sonki da k’aunarki k’aruwa kawai suke yi! Ki taimaka kar ki auri wani wallahi zan iya mutuwa. Na ji zan baki time zan baki space amman kar ki auri wani na dan girman Allah. Sannan ki san yadda za kiyi da ni, ki yi min abunda zan ji kin fita a raina. In kikayi min haka kin gama min komai. Na san ba a neman aure cikin aure amman na kasa hak’ura da ke! Ba zan iya ba ki san yadda za ki yi dani dan Allah. I know I’m not making any sense here I can’t loose you kuma tunda kince bakya so na i can’t force you to love me so I can’t love you saboda ni happiness d’inki shine abunda nake so amman fa kar ki ce za ki auri wani. Wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya! Inaga haukacewa zan yi, bana gane komai bana gane kowa sai ke! Ki fita a raina sai in barki Ki fita a zuciyata sai in...........” Kukan da ya taho mishi fiye da na farkon da yake yi ne ya sanya ya kasa ci gaba da magana. Ita kanta Sakina kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa ne ya samu nasarar kufce mata. “Innalillahi wa innailaihirrajiun!!” Suka ji muryar Mom da Mammy a bayansu har da wata k’awar su, suna salati suna tafi. Da sauri Sakina ta share hawayenta ta d’an matsa saboda Auwal d’in ya tashi ya basu damar shigowa amman ko gezau bai yi ba. Wani kallon tsana Mom take watsa mata, kafin cikin tsananin b’acin rai tace “Yanzu ku jinin Madu ashe ba zaku tab’a jin tsoron Allah ba? A haka za ku k’are? Wato Maryam ta yi shine kema zaki biyo ki haukatamin d’a?? To billahilazim na fi k’arfinki! Duk surk’ullen da kika je kika yi ki koma ki je ki wargaza tun kafin In tashi biyowa ta kanki!. Saboda Allah Mammy ku kalli yadda Yarinyar nan ta maida Auwal! Auwal fa!!! Wai yau shine a gaban mace yake kuka haka wiwi da hawaye kamar wani sakare? Wallahi Allah sai yayi mana hisabi da mu da family d’in Madu ranar gobe k’iyama. Wanne irin jarababben abu ne yake yawo a jininku sai kace mayu?” Tayi maganar tana kallon Sakina cikeda tsana wadda itanma ta zuba mata nata dara daran idanuwan da suka rine sukai jaa. Za tayi magana kenan Auwal ya mik’e da kyar ya juya gareta yace “Haba Mom, abubuwan da suke kai na already sun yi yawa Dan Allah kar ki zo kiyi haka kar ki saka ta k’ini completely! Ki koma waje dan girman Allah Magana muke yi, maganar da ta shafemu iya mu biyu tak! Ba wanda ya gayyotoki ke da k’awayen ki nan” Ya k’arashe maganar tari yana kufce masa…” A rikice tace “Auwal na rantse da Allah zan yi maka abunda baka tab’a zato ba! Karankatakaf fad’in duniya ace ka rasa macen da za ka so sai jinin Maryam Jikar Madu da Shuwa? Kasan su waye su kuwa?” Kuka kawai Sakina ta saka ta fara ja da baya… Da sauri Auwal ya juya ya fara binta yana magana yana tari “Ki tsaya.. Don’t mind her.. let’s talk.. Dan Allah.. Sai a sannan Mom ta samu damar shigowa ita da su Mammy. Kamar ma tangad’i Auwal d’in yake yi dan haka suka samu suka wuceshi suka yi kan Sakina! Mom tana zuwa, ta shak’ota tace “You must mind me! In dai kina da hankali kuma kin san darajar uwa a wajen d’anta to ki sani ba zan tab’a barin Auwal ya aurenki ba wallahi! Dan haka ki hak’ura. Ina fatan Huda ta zame miki lesson a rayuwa…..amma idan mahaukaciya ce ke to ki so Auwal ki aureshi dan Allah, wallahi nayi miki alk’awarin sai na lahira ya fiki kwanciyar hankali” Tana gama fad’in haka tayi cilli da ita wanda har ya kaita ga kaiwa k’asa. Kasa motsi Auwal yayi dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi, tabbas ya san halaiyyarsa da kuma Granpa su suka hana Sakina yarda ta auresa amma ya san tana sonshi wanda hakan ne ma yasa ta sanya aka kawo kud’in aurenta da wuri! Duk ya fahimci hakan. Yanzu kuma ga Mom! Ya tabbatar ta gama wargaza masa d’an guntun chance d’in da yake hangowa…. Duk da baya ganinta amman yana iya jiyo setin inda take kuka, dan haka ya fara yunk’urin d’aga k’afarsa domin ya k’arasa wajenta. Yana motsawa kuwa kamar jira ake jiri yace bismillah! Gaba d’aya ganinshi ya d’auke in banda duhu babu abunda yake gani, ga wani mahaukacin juyawa da kanshi yake yi…… Da sauri yasa hannu ya dafe kan nashi yace “wash!!” Da d’an k’arfi. Sai a lokacin hankalin Mom da Mammy da k’awar tasu waenda suka k’arasa suka cigaba da tsigale Sakina suna kiranta da ‘talaka, kwadayayyiya’ Ya koma kan Auwal. Da sauri Mom ta nufesa ganin yana shirin zubewa k’asa amman kafin ta k’arasa har ya fad’i k’asa sumamme.. Dede nan su Daddy Abba da Ummi suka shigo dan dama Ummi kamar ta d’an jiyo hayaniya sama sama… Ba karamin tsorata Mom tayi ba ganin Auwal a k’asa kamar matacce. A haukace ta juya ta koma kan Sakina da take nan durk’ushe tana kuka, ta sake shak’ota ta mik’ar tsaye ta hau magana kamar tab’b’abb’iya “Waenna irin mutane ne ku? Baku da tausayi ne? Dolene sai an so ku? Wallahi na rantse da Allah ko a Birnin sin kika yi mishi asiri yau sai mun je yanzu ba sai gobe ba kin warware shi.” Ta fad’i haka tana k’ok’arin fara janta. Sakina kam banda tari ba abunda take yi gaba d’aya ta fice a haiyyacinta dan ba k’aramar shak’a Mom tayi mata ba. “Adama!!!!” Suka ji muryar Dad cikin tsawa a bayansu. Juyawa Mammy da k’awar tasu suka yi ita kuma Mom ta cika wuyan Sakina ta durk’ushe a wajen ta fashe da kuka. Dede nan Aslam da Huda suka shigo! Da gudu Hudan ta k’arasa inda Sakina take… Cikin tsananin b’acin rai Daddy ya k’arasa inda suke ya d’agota ya fara magana “Baki da hankali ne? Me yake damunki? Wachche irin kwakwalwa ce da ku ne wai? She’s our guest for crying out loud!! Ga babanta chan a waje ya dawo d’aukar su a haka kikeso a fitar mishi da ita ko yaya?” Cikin kuka Mom tace Kallafa Auwal” Ta nuna masa Auwal wanda Abba da Aslam suka ciccib’a za su fitar, cikin kukan taci gaba da magana “Asiri tayi mishi Irin wanda Maryam ta yiwa Abba bani da tantama! Daddy a k’asa fa nazo na tarar da Auwal durk’ushe gaban wannan k’ask’antacciyar yana rok’onta ta soshi ta aureshi yana kuka kamar k’aramin Yaro In ba aikin asiri ba tayaya zaka yi tunanin Auwal zai so wannan k’ask’antacciyar?” Tayi maganar tana nuna Sakina a wulak’ance. “Tayaya aka yi na so ki har na aureki?” Muryar Daddy ta katse mata maganar da ta yunk’uro za ta ci gaba. Da sauri ta juyo tana kallonshi cike da shock! Cikin tsanannin b’acin rai yace “Adama na gaji na gaji da rashin tunanin ki da shirmen ki da son zuciyarki! Na gaji wallahi.. Tsabar idonki ya rufe daga ganin gaskiya you don’t even realize the fact that Auwal ya nutsu tunda ya had’u da Yarinyar nan. Kar ki bari In chanza miki wallahi ba zaki ji dad’ina ba dan kin kaini bango!.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin fushi. Dede nan Aslam wanda ya dawo daga kai Auwal ya dafa Daddy yace “Daddy dan Allah ka yi hak’uri.” A hankali Arshaad wanda ya shigo yanzun shima ya k’araso inda suke yace “Akwai mutane a gidan Daddy, Abba kai yake jira ku kai Auwal asibiti suna mota.” Kallon Mom yayi wadda ta k’ame tun lokacin da ya fara magana.. Kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai yayi tsaki ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace. Yana fita Mammy ta k’araso ta dafa ta tace “Zo mu je” Daga nan ta ja hannunta suka nufi wani d’akin a nan k’asan ita da k’awarta.. Suna shiga kamar jira Mom take ta fashe da kuka tace “Akan Yarinyar chan Daddy ya gaya min wannan maganar?? Waenna irin mutanene su Maryam wai ni Adama…” Cikin katseta Mammy tace “Saboda haka baki ga ta zama ba! Ko kuma ince ba muga ta zama ba har sai mun cire ta a zuciyar auwal!. Sannan akwai wani abunda ya faru na tashin hankali d’azun nan nima na gani amman kar ki damu dama na gama tsara mana mafita tun kafin in zo Sannan itama wannan sai mun yi da gaske tukunna zamu cireta a rayuwar Auwal. Da sauri Mom tace “Kina ganin ciretan zai yiu? Kina gani fa Arshaad bake kad’ai ba har ni d’innan gaba yake yi da ni. In ba asirin aka karya ba ba zamu samu sukuni ba.” Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace “Adama Allah ya jefomu cikin wasu kalar family masu zuciya mai naci dan haka sai mun yi da gaske saboda su na fahimci weakness d’insu mace ce! Ki duba kiga har shi kanshi Granpa d’in duk abun shi kina ga yana yiwa matarsa?” Cikin kuka Mom tace “Kullum addua ta d’aya kar Auwal ya fad’a kaidin mace kamar iyayensa sai gashi rana d’aya ya fad’a, ni Adama ya zan yi? Shi kad’ai gareni! Ita kad’ai fa yake gani ko maida hankali kwana biyun nan na lura ba yayi akan aiki ashe ita ce sila! Kiji Daddy tsabar rashin sanin ciwon kai wai har da ik’irarin Auwal ya nutsu! Shi a ganinshi nutsuwa ce wannan an haukatamin kwakwalwar d’a amma shi yana ik’irarin ya nutsu…” Ta k’arashe maganar tana durk’ushewa a wajen. A hankali Mammy ta k’arasa ta hau lalalshinta, sai da taga tayi shiru tukunna ta matsar da bakinta dede kunnenta ta shiga rad’a mata waensu maganganu. Aslam da Hudan ne suka raka su Sakina har bakin mota bayan sun lallasheta ta yi shiru da kyar! Har da Arshaad. Sanann suka tsaya suka kira Sumayya a wajen k’awarta suka wuce tare. Hudan maganganu ne fal a ranta take so tayi da Sakina amman ganin halin da take ciki kawai yasa suka yi musu godiya ta bari akan In komai ya lafa za suyi chatting. A parlourn suka tarar da Mom Mommy da Mammy da Ummi Dad ya had’asu gaba d’aya da alamun fad’a yake yi musu. Suna shiga Aslam ya cewa Hudan “taje ta had’o masa Coffee mai zafi please” Daga nan ya wuce ciki bayan ta amsa masa da “to” ita kuma ta nufi kitchen d’in direct. Arshaad ma ya wuce d’akinsa. Arshaad yana shiga d’akinsa Mammy ta mik’e ta nufi d’akin dan they have to talk, ta lura in ta biye shi gaba zai yi da ita. D’azu sau biyu tana zuwa d’akin nasa bata sameshi ba. Tana shiga su Dad suka gama zaman nasu suma aka mik’e kowa ya kama gabansa. Ta gama had’awa kenan ta d’auko flask za ta juye wayarta ta fara k’ara! Tana dubawa taga sunan Sakina dan haka tayi saurin amsawa ta kara a kunnenta. Ko sallamarta Sakinar bata amsa ba tace “Hudan d’anyi sauri ki fito kinga akwai sak’on da zan baki ashe na manta.” “Ok” Hudan tace sannan ta kashe wayar ta ajjiye flask d’in ta rufe had’in nata ta fita. Tana fita wani mutum ko wata mata ta/ya shigo ta k’ofar baya sanye cikin bak’ak’en kaya kamar irin na leda d’innan na tare ruwa an rufa har hular saman fuska. Ta chan ciki a fuskar da mask bak’ik’irin, baka ganin komai hatta idanuwan a rufe suke da bak’in glass. Tafin hannu da k’afa kuma duk da bak’ak’en socks….. Wani ruwa aka zaro a cikin syring aka bud’e had’in coffe d’in da Hudan ta gama had’awa aka b’alle kan syringing kamar za a matsa sai kuma aka tsaya aka yi shiruuu! Da alama mutumin ko matar is having second thoughts. Ahankali aka ja wani d’an siririn tsaki aka mayar da murfin aka rufe aka ajjiye syringing a gefe kamar ana tunani… Motsin mutum ya ji ko ta ji dan haka aka yi saurin d’agowa ana kallon k’ofar bayan ta inda aka shigo ai kuwa aka ci sa’ar ganin giftawar inuwar mutum! Lalle kuwa ko waye ya gifta to ta/ya san ya ganshi ko ya ganta! Dan haka da sauri aka bud’e k’ofar bayan aka bi Inuwar da aka gani amman ko da wasa babu alamar mutum a wajen… Har bayan compound sai da ya/ta zazzagaya amman ba kowa. Ya/ta dad’e a tsaye tana/yana tunani kafin chan ya/ta nufi hanyar kitchen d’in da niyyyar d’auke syringing da ta/ya manta akan kanter kitchen d’in kusa da tray da coffe d’in da ya/ta had’a. Tana/yana zuwa tayi/yayi saurin ja da baya sakamokon hango Huda da Ummi a cikin kitchen d’in! Hudan tana juye coffe d’in a cikin flask Ummi kuma ga wani abu a hannunta tana sha suna d’an hira.......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 64 Mikiya Writers Association. Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishi sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba! Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi. Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina. Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace “In fito ko za ki shigo?” Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace “Ki fito Ina? Ina zan shigo?” Turuss! Haka Hudan taja ta tsaya itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace “Sak’on fa da kika ce za ki bani?” Cikin rashin fahimta Sakina tace “Wanne sak’o?” Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyara zuciya tace “Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak’o in zo in karb’a da sauri…” Cikin katseta a d’an firgice Sakina tace “Hudan yi sauri ki koma gida maza maza yanzun nan! Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata sun ga yau kuna taro. Yi maza ki koma ciki da sauri kar ki sake fitowa.” Da sauri kuwa Hudan ta juya k’irjinta yana dukan uku uku! Har da d’an gudu ta shiga had’awa da shi. Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse…. Haka nan ta wuce kitchen d’in jikinta yana karkarwa tana salati. Tana shiga taga kamar an fita ta k’ofar baya! Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa. A hankali ta shiga takawa tana kallon k’ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k’ofar ba a matsa ba! “Huda” Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand’a ta kira sunanta. A mugun tsorace tace “wayyo Allah!!” Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa. Dariya Ummi tayi kafin tace “Matsoraciya!!! Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan… D’azun Dad yake gaya mana Granpa although yana fushi da Aslam akan ki amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK ya bashi kyautar gida da mota a chan. A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had’in coffee d’in Aslam. Murmushi Ummi tayi, ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa “Yauwa coffe d’innan na biyo! Gaba d’aya drinks d’in nasu na yau zak’iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping. Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na.” A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace “Eh. Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan ajjiye mishi a gefen tray d’in in yana so sai ya k’ara. Murmushi Ummi tayi sannan tace “To za a zuba min inshaa ne ko sai na jira an fara kai mishi ya d’iba?” Ta k’arashe tambayar cikin sigar tsokana. Murmushi mai had’e da y’ar dariya Hudan tayi kafin tace “Haba Ummi” Tana mai juyawa ta d’auko cup mai d’an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata. Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace “Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam.” Sunkuyar da kai Hudan tayi…Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta

Chapter 11 of 26